Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamaki da tausayi yadda take magana gwanin ban tausayi wai duk akan mijin ta na sunna take wanan maganan haka.
Yadda kuka yazo mata takeyi shiya kara karyar min da zuciya na bani ba har inna da Attu dake gurin sai da suka karya da zancen ta.
Tausayin anty ya kamani sosai na fada saman jikin ta ina cewa anty zan yi komai a kan ki indai har yin hakan shine zai zama farin cikin rayuwan ki.
Rugumay ni tayi cikin kuka take cewa insha Allahu Rahama ba zakiyi nadaman wanan auren ba don Yusuf mijine abin alfari ga ko wace mace data samay shi a duniyan nan.
Sai bayan an natsune take cewa da Attu to yaya za, a bani ita ne mukoma ko yaya za, ayi yanzu ?
Attu tace a, a hajiya dadai kiyi hakkuri ki barta har ta dan kara samun natsuwa idan kun aje ranan da zata tare kinga sai azo a dauketa akaita dakin ta kin ga haka ma gata ne gare ta don asan tana da asali kodon gori wata rana kin san mu mata ba tabbas ke gare mu ba.
Anty tace ba laifi hakan ma yayi ai ba matsala sai dai tarewan nata ba zai dauki wani tsawon lokaci ba a yadda nake so don karatun ta duk abinda za, ayi nan da sati mai zuwa insha Allahu za, ayi shi.
Anyi sallama da ita ni dai ban fito ba duk da ina jin muryan bashir ta kyauren su Attu yana min sheri ina daki naki fitowa waje naji tashin motar su suka tafi.
Nan suka bar mu inna da Attu na kara bani hakkuri na daure ko don wanan matar na kwantar da hankalina akan ta.
Inna ta tafi gida take fadawa maigidan ta ai ina gidan iyayyenta nan ta samay ni shiya ta dade hakana.

********* ********* *********
A gaji ta dawo gida don ta dade batai tafiya haka ba sai bayan tayi sallah magariba ne Gajiye ta kawo mata abinci taci tasha magani.
Daga inda take zaune ta daga kai ta kalli yaran ta suka bata tausayi yadda rashi na, na dan lokaci yasa duk suka shiga damuwa haka inga yau ace nabar gidan gaba daya nayi aure a wani gurin yaya zasu kasance masu hakan.
Tafito daga wanka ne maigidan ya shigo ya samay ta bai mata sannu da zuwa ba sai take cewa dashi haba besty yaya zanbi ma amarya na dawo kuma babu ko sannu.
Yace na aike kine wanan matsalar ki ce don ke kika zabi yin haka nikin tuna min ma dazu mama Laraba tazo gida nan bakya nan.
Da sauri ta dago tana cewa dashi Allah sarki mun sha banban ke nan da ita yace hakane.
Tazo ne wai akan tarewan wanan yarinyar tana son taji ina za,a ajeta dakuma wai maganan kayan lefe.
Nan dai ya fata mata a furguje yadda sukayi da mama Laraba din taji yace part din dake kusa da ita za, a ajeni da sauri tace dashi na dauka ai ko zaka gyara mata wancan gidan da muka fito zaifi ta sake jikin ta ai.
Yace ba; da ra, ayin yin haka ga iyalina idan zata zauna nan inda kowa yake ta zauna don ba fin wani tayi ba nakuma yi magana da masu gyaran guri zasu zo su duba part din kowa suyi abinda ya dace suyi.
Sai zancen kayan lefen da tayi zan baki kudi ki hado abindaya dace ayi idan basu isa ba sai ki fada min na kara maku.
Sam Anty bataso wanan shawaran nashi ba nace wai na zauna a part din dake kusa da nata ba taso ya kaini wani gurin da bata ganin abinda zai gudana a tsakanin mu.
Don ita kadai tasan irin taushe zuciyar ta datake yi kan wanan matsalar shine mafita ga rayuwan ta kawai harta amince da yin hakan gare ta.
Amma babu yadda ta iya shike da gidan shi yadda ya tsara dole hakan zata daure ayi shi.
Sai bayan fitan shine mama tashigo dakin dama magana nacin ta tun fitan mama Laraba gidan ta barta da tunanen matsalan may ke damun anty ne wai harta yanke wanan danyen hukuncin a kan ta haka ?
Tace da ita magana nake sin muyi Saade ni uwarki ne baki da wanda zaki iya fadawa damuwanki bayan ni yanzu ina son ki fada min gaskiya wani matsala ne ke damun ki a rayuwa har kika yankewa kanki wanan shawara ki aura wa mijin ki yarinyar da kika tayar kamar diyarki a duniya.
Maimakon ta bata amsa sai kawai ta saka mata kuka itama mama kuka takama sukayi mai isar su subiyu a cikin daki babu mai basu hakkuri.
Can cikin muryan kuka take cewa mama ina da matsala a rayuwa na wanda ba kowane yasani ba sai mijina da mahaifina.
Da sauri mama ta tsagaita da kukan ta tana sauraren yar nata tace mama wanan matsala yasa naga kafin mai rabawa ya rabani da yaran nan nai masu gata na nema masu uwar goyo na gari da ko a bayana zata iya rike min yarana.
Nasan halin mahaifin su bazai taba yarda wani nawa ya dauki yaran nan ba ya rike a gurin shi dole dai a gidan nan zasu zauna.
Zaman su da wa yan nan matan mama hatsarine babba ina rayema basu sosu ba balle ace yau na fadi na mutu.
Ganin dacewan Rama ga wanan matsayin ne yasa na yanke shawaran hada ta aure da shi ko bani raye dai yarana nada wacce zata rike min su tsakani da Allah.
Ban san kuma bayana wazai kwaso masu ba yace ta zauna min da yarana ba ban san irin tarbiyan ta ba da zata basu.
Shiyasa kikaga na zabin yin haka amatsayin madogara babba a gareni ko a bayana bazasu wullakanta ba.
Shin wai may ke damun ki ne haka kike kirawa kanki mutuwa Saade ciwo aiba mutuwa bane ko sai mai lafiya ma ya tafi yabar maiciwo a duniya.
Ki fada min may ke damun rayuwan ki Saade ta dago kai ta kalli mama da ta tsura mata ido tana son jin karin bayani dafa gareta.
Tace mama in dauke da cutan sickle da farko shi likitoci sukace yake damuna har ya zama min coronic sai daga bayan nan bayan mun koma suke ce min kuma ya koma min Cancer.
A razane mama tace bari kira min wanan balain shine fa akace ya kashe uwar ki a baya can.
Tace cikin hadiye miyaun bakin ciki mama shine ke damun rayuwana don ma maigidan yana tsaye sosai a kaina ne da kuma ita Rama dana samu ta tsaya min gurin kulawa dani sosai aida ban kaiba killa ma.
Kuka mama ta saka wiwi tana salati tana fadin ta shiga uku yanzu Saade kina da wanan matsala kike boye min shi a rayuwan ki kuka suka saka a tare ba maiba wani hakkuri a cikin su.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA A YAFE MAKI BA DABARA YA SAURA GA MAI TSORON HADUWAN SHI DA ALLAH KAN HAKKIN WANI, , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH ZAI SAKA MUNA AKANKI DON BAKI DA TSORON HADUWA DA SHI KAN HAKKIN WANI ALLAH NAGANIN KI IN BAMU GANIN KI, , ,

39
Jin fitinan nasu yaki karewa sai gaba yakeyi a tsakanin su ga su mama na ta tsawata masu amma basu daina ba.
Tsam namike tsaye na gyara lafaya na da kyau tare da dan fara takawa na nufi hanyan fita daga falon daddy da su mama suka bini da ido.
Ina kai kofa naji zulfau nacewa anty idan ma kin ba da goyon baya ne ai muna haka to dake za, a fara don kowa ai yana da kishi bamu kadai wanan yakin zai ci ba a gidan nan.
Anty tace sai dai kun makara a, i don gashi an fara daku kun kasa hade fushin ku a gaban ta kuna tonawa kanku asirin zuciyar ku.
Aure ne dai anyi shi inma mutum yace iya gatse ya iya ya sara agaban yan amin aiku kuka fara furta hakan yan amin kuma suka amsa maku.
Kalaman nasu ba dadin fadi amsan da suka bata ina ficewa mama tace kun gani karamar yarinya tafiku hankali da sanin ya kamata gashi ta fice bata iya tsayawa sauraren ku.
Ina zuwa na samu yan uwana zaune a falo suna kallon tv suka ban tausayi mutanen mu na kauye akwai son kallo gare su.
Nashiga daki nan nasamu Attu da matar maigari uwargidan su inna ta zaune a dakin Nasir da Amira kwance saman gado da alama jirana suke sukai barci.
Na gaida su na gyarawa yaran kwanciyan su na zauna gefe daya suke cewa dani ga ferfesu nan da shayi Gajiye takawo kowa kuma yasha cikin su.
Attu ke tambayana injin ba matsala dai ko na kwashe abinda ke faruwa na fada masu take cewa ni nasan akwai aiki ai.
Matar mai gari Abu tace ba wani matsala ai mama idan ta iya zama dasu sai a zauna lafiya ki fita batun su kada ki biyewa haukan su don dama dole ne sai sunji zafin abin tunda anan kike zaune dasu.
Kusa da Nasir na koma na kwanta na kura mai ido kaman shi da daddy sak nake gani yau har kamar ma ya baci.
Tsakiyan yaran na kwanta kewan su na kwana biyu yana shigana a hankali.
Idanuwana suna a lumshe muryan Anty ne ya ratso kunnuwa na tana fadin a, a ashe akwai aiki kuwa yaran nan yanzu nan suka zo suka kwanta.
Mama Abu tace da ita kin san yaro ida yaga fuska can yake tun fitan ku muna nan dasu har barci ya kwashe su gurin shigowan tane ta gyara masu kwanciya ai.
Na bude idona tare da dan mikewa kadan nace sannu anty tace sai na juya ban ganki ba falon murmushi nayi na dukar da kaina kasa kawai.
Tace basu son a zauna lafiya idan ba anyi fitina ba su basu jin dadin rayuwan su ko yaushe daga magana ta fahinta sai kice zaki ba yarinya kashi shine ai ya hasala ni ai tasan halin Rama sarai.
Take tambayan babu wani abinda ake bukata ko mama tace a, a Alhamdullahi hajiya mun gode wallahi.
Dukowa tayi inda nake zaune cikin rada tace dani shirya na kai ki gurin angon ki ko ?
Da sauri na turo mata baki gaba nace kai haba anty cikin yar shagaba tace dake may kike nufi haka za, a zura maki ido komay ?
Yarinya kinzo hannu ke nan ai may za, a fasa sallah ko salati ai kinzo hannu sai ki shirya don daddy ba wasa.
Take idanuwa na ya ciko da kwalla tace daga magana sai kuka ashe akwai aiki kuwa Rama.
Kwanta gaki ga mutanen ki ai ba yau ba sai baki sun tafi ai mu fara two two days dai ne aka tsayar da magana idan kin gama Amarcin ki yanzu su mama suka yanke hukunci don da wa yancan sunce sai dai ayi one one day yadda muka saba abaya.
Jin ta kawai nakeyi harta gama tai muna sallama takai kofa nace anty ta juyo nace maganin kifa ?
Tai murmushi tace ai dole insha Rama yau yadda nagaji din nan tun safe ban zauna ba fa sai dai gobe muyi maganan komai idan baki sun tafi.
Washegari da safe sai ga anty a dakin ta shigo Gajiye na biye a bayan ta da jakkar bako.
Ta samu guri ta zauna ina shafawa Amira mai ajiki nan na shiga gaida ita take cewa da mu.
Attu ga maigidan nan zai shigo gaida ku don zaiyi tafiya ne yau tafiya ya kama shi.
Nan suka shiga gyarawa can mukaji muryan shi yana gaida mutanen dake falo daga nan anty taimai jagora zuwa daki inda nake tare dasu Attu suka shiga gaisawa dashi yana tsugunne kamar yadda suriki kewa surukan shi girmamawa.
Nasir dake tsaye saman gado yace daddy see me here with my mum, she is now back.
Mummy tace itama tazama matarka bazata kara barin mu ba again yariko min hannu yana tambayana wai hakane.
Kunya duk ya rufe ni a lokacin ya mike yana cewa su gaida gida ya gode ai mashi godiya gurin maigari da babana.
Bayan fitan shi ne anty ta dan rakashi can sai gata tadawo dakin take cewa da Attu ga sakon godiya daga gurin maigidan.
Tace Gajiye fitar da turamay nan ta miko kudi tana cewa gashi kowa turmi ne da dubu biyar yace kuyi hakkuri dashi ba yawa.
Haba nan guri ya rude kowa da irin adduan da yake jerowa akan aure da maigidan nai magana da Gajiye ta dauko min wasu kayana a part din Anty nan na ba su Rukaiyya da Lawisa da suwaiba yan uwana har ma da wasu daga cikin uan rakiyana.
Sai nasiha suke min na zaman lafiya anty tashigo take cewa nazo na yafa mayafi nabi bayanta muka dan tsaya daga dogon coridor dake tsakanin part din ta da nawa.
Tace dama kujerun nan da aka kwashe daga part dina nake son a kwashe kayan akaiwa inna su can kauye nata sai tabawa wanan abokiyar zaman nata don naga matar na da mutunci sosai.
Kasa nakai na tsugunna a gaban ta ina godiya takai haba may ye aciki ai yiwa kaine hakan ni zan iya biyan ku abinda kike min ne don haka sai ki fadawa Attu ta fada mata ta kwashe kayan zuwa jibi za, a shigo mata dasu.
Na kara mata godiya ta dafani ta wuce zuwa nata sasshen nabi bayan ta da kallon tausayawa.
Ina shiga na samu Attu da mama Abu nake fada mata sakon anty tai murna sosai da farin ciki tana cewa kaji arziki ba muma arziki ya shafe mu.
Nan dai ina kallo akazo Gajiye ke fada masu mota yazo nace wa mama Abu da baba bazaiyi fada ba da an barmin Fatima ta dan kwana min biyu nan tare dani.
Attu tace abari idan sun koma sai aiwa magari magana wanda yaje kai kaya sai yadawo min da ita idan ya amince da haka sukai min sallama ina kallo yan uwa na suka tafi suka barni gidan da nake wa kallon gidan danger.
Suna fita na fara gyaran dakin sai ga su Zaraha da Nafisa sun shigo gidan da kaya niki niki sakon da suka sayo min.
Aikin da suka samu inayi ne suka karba da taimakon su na gyara duk inda bakin su ka bata suka saka kayan kamshi a ko ina a part din.
Nan suka baje min kayan da suka sayo min balaifi nima kayan su ban sha, awa sosai sai wasu abubuwan da Zarah ta kawo min wai na amfanin mata ne.
Karba nayi cikin ya mutse fuskana tare da mata wani irin kallon raini nace wanan fa na may ye shi ?
Tace sa mai gida kuwa ke nan kingan shi nan kamar yankan wuka yake wallahi.
Don sai kin toshe bakin namiji nima sister din mamana tazo min da shi tsaraba daga bargu.
Nace kai zarah ni wani miji can zai min kuwa dan Allah kibar wanan shirmay mutum da mata haka dirka dirka har may zai kalla a nan.
Nidai gani ga Allah kawai ban san yaya rayuwana zai kayya ba cikin wanan gidan.
Kamar yaya ke ba mace bace Rahama may kika rasa da ake nema a gurin mace wanda baki dashi a jikin ki sai dai idan kin yi rowan haka gare shi.
Ni wai may yasa mutane basu da magana ne sai irin wanan zancen shi ke nan da anyi aure, ba wani magana sai maganan cudanya da miji.
Tace to may ye auren Rahama may kuma akewa kishin ba wanan ba duk shine dai tsananin kishin ai wanan dan jijiyan guda kawai.
Nace Allah dai ya shiry ki Zarah don ban da kunya sai naje yin wani kakale ga daddy na kalleshi da wani ido ke nan ?
Tace anya kuwa Rahama wai ni da kikecewa wai kin taba aure kin ko san harka kuwa a rayuwan ki.
Mace ko dan fleeling bata da shi akan namiji hakamar wara dakila can dake haka ?
Nace don Allah zarah bar zancen nan barsu da mijin su suyi ta kayan abinsu nikan ai a matsayin yar aiki nake gare su.
Nace jiya fa hindatu cewa tayi kashi ma zata bani a gidan nan basai taga na shiga harkan mijin ta ba zata kai ga dukana din.
Kece ko may shiga harkan shi Rahama don yanzu ke amarya ce shar gaki baki taba haihuwa ba komai naki a tsaye yake kamar baki taba aure ba.
Nafisa tace kardai nace jiya jiya har kun fara da matan gidan nan nace sun dai fara, su da basu danayi sai zancen miji ko yaushe.
Umm, umm fa kada muzo muna jin ana cewa kunji abinda honey yai mun watarana .
Nace waye honey din daddy din kowa don Allah kice Allah kin tuba Zarah don banda kunya zan kira daddy dina da honey komay ?
Tace ai zancen daddy ya kare don yanzu sai sabon suna kin taba jin inda daddy ya danne diyar shi a tarihi.
Tsuki nayi na mike tare da kwashe kayan naje na boye kada anty ta shigo girshi dakin ta gansu naji kunya.
Ina dawowa da magana daya Zarah ta tare ni dashi tace idan zaki kwanta ki tabbatar da kunlun kin yi tsarki da ruwan dumi a tsarkin ki.
Ki samu mai masu kanshi ko yaushe kina shafawa a tsakanin cinyoyin ki don kin san guri ne da baya samun iska ko yaushe.
Shiko namiji duk sanda bukata ta ya biro mai baida lokacin a garshi sai ya biya yake samun natsuwa tare dashi.
Kada ki din tsayawa miji kerere idan yana neman bukata ke koda ma baya neman komai a garki ki kasan ce mai yanga da sallon kina yauki yadda hakalin shi zai daga dake.
Gaki da abinda akasarin maza ke so a jikin mace nono kina dan dinga bankaro mai kirjin ki yadda hankalin shi zai dinga dagawa.
Don Allah dai Zarah ki bar wanan zance haka please tace naki bari rigunan nan da aka sayo maki ko ba wani abu zaki dauka ba kina dan dukawa cikin stely yadda nonowan ki zasu dinga baiyyana a gare shi.
Koda zani kika daura ya kasance boons dinki sun fito da kyau fili gashi dama daddy kine sai ki samu wanan daman kina mai shagwaba irin na da da uwar shi ko yaushe kina manne da jikin shi.
Haka zai kara jawo maku shakuwa sosai a tsakanin ku ya kasance yana cin abinci kina zaune kina dan kara mai ruwa ko miya ko gyara mai bakin shi.
Zarah please stop that rubish wanan magana naki da may yai kamane wai please ?
Tace da gaskiya mana tace idan kuma kunzo kwanciya kiyi kokari hannun ki yadan taba ciyan shi ko tsakiyar bayan shi kin gama gamawa dashi yarinya.
Ke classic baby ce don haka ki zamo may son yawan romace da dan magana cikin sexy voice yadda zai rude ya rasa inda zai sa kan shi akan ki.
Oh my Allah Zarah ashe haka kike tace har nafi nan yarinya ki dinga tabbatar da kin mai sallaman da zai tafi ko ina ne yana dauke da tunanen ki a ran shi sai yaji ki a kusa dashi ya samu natsuwa a ran shi.
Kina dai nufin in yi haka in shaga tsakanin shi harda anty na ke nan ko Zarah ?
Tace bance ba ai ita anty ta daban ce amma dai ai a fagen miji ake yanzu kowa tashi tafishe shi kawai .
Nace badai ko da anty na ba cikin wanan plan din tace indai har zakiyi din ai sai ki cire ta ciki ko ?
Har tsawon wani lokaci sukai min sallama suka tafi na koma ni kadai a shiyan zaman kadaici ya damay ni su Nasir sun tafi makaran ta a lokacin.
Na rufo kofa part din na nufi part din anty Gajiye kawai na samu tana aiki take cewa dani ai Anty ta dan kwanta don jikin ta ba dadi karfin hali kawai takeyi.
Ban zauna ba na shiga taya ta aiki kamar yadda na saba yi har dakin muni dasu Nasir sai da na gyara komai gurin ya koma neat har falo sai da na gyara shi yadda nake mai.
Na koma dakin mu na zauna sai ga gajiye da abinci takawo min daki ban iya ci ba na dan taba kadan na barshi nan.
Tafito daga wanka take cewa dani Rahama ba kici abincin ba ta zauna daga gefena tana cewa dani.
Haba Rahama may yazo da bai wuce ba wanan abin fa ba laifinki bane wacce kike jiwa ta fada maki da yardan ta akai hakan ai to may zai sa kina sakawa ran ki damuwa haka ?
Don Allah ki kwantar da hankalin ki ki rugumi mijin ki da hannu bibiyu kada kizo ki fadawa sabon Allah alhakin mijin ki dana yar uwar ki ya kama ki.
Hawaye naji ya zo min tace sake jiki zakiyi yadda take son ganin ki ki zama mai biyayya a mijin ki da abokan zaman ki in har kin cire komai a ranki zakiga abin yazo maki da sauki.
Muryan anty ne ke kiran Gajiye a falo alaman ta tashi ke nan daga barci daga inda take muna jin tana cewa Gajiye kin ko kaiwa Rama abinci taci ?
Tave hajiya aiga ta nan ma zaune tun dazun take nan ita ma tai gyara gida da kan ta sai dai taki cin abinci wallahi.
Ina Raman take ne ta tambaya na amsa da na,am anty nafito ina gyara gyalen kaina da kyau.
Tace a, a wai har yanzu kina fama da wanan mayafin haka kamar wata bakuwa dake ?
May yasa baki ci abincin ba ne wai ko har anzu baki hakkura da kaddaran ubangiji bane a kan ki ?
Idan har kina son mu shirya dake Rama wallahi sai kin saki jikin ki kinyi biyayya ga mijinki da sauran abokan zaman ki.
Ni dai indon ni ne na fada maki da sani na da yardana akai komai da kika fani don may wai ba zaki saki ranki ba ki zauna lafiya a dakin ki.
Bazaki taba samun kan mijinki ba Rama idan bakin bada hadin kai akan hakan ba rashinyin hakan gareki kuma kamar rainawa da hukuncin Allah akanki da magana .
Haka kuma zaki iya jefa kanki ga halaka da fushin ubangiji a kan ki don haka noroke ki Allah Rama ki zauna lafiya da mijin ki kiyi biya.
Na dago kai ina mata kallon mamaki ta miko min hannu tana fadin zo nan yar kaunata.
Ba mussu na nufota kamar karamar yarinya na zauna gap da ita ta dan rugumoni tana

Please Login or Register in order to submit comment