Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun fitan su zuwa sallah.
Yana saye da manyan kaya a jikin shi farare kal dasu da hullan shi da ya dace da aikin da akaiwa kayan dake jikin shi.
Kayan sun matukar karban jikin shi sosai yadine mai matukar tsada sajen fuskanshi ya kwanta qa fuskan shi lun lub ya kara mai kyau da kwarjini sosai.
Gefe na dan rakube ina cewa sannu da dawowa daddy barka da sallah ?
Yace an sha ruwa lafiya Allah ya maimaita muna nan naji gajiye tana gaida shi kamar yadda na gaida shi.
Ya saka hannu a aljihun shi ya ciro bandir din yan dubu daya daya ya kirga ya fara mikawa Gajiye ya tana godiya ya kirgo ya miko min na rusunna nakarba ina godiya.
Saiga Farida itama tana gaida shi itama ya bata nata ta karba tana kallon hannuwana.
Ya shige dakin anty yajima sai gashi yafito yanayin shi ya sauya ga yadda ya shiga dakin don gajiye na mashi a huta lafiya bai amsa mata ba yafita da zafin rai.
Kusan hakan ne ke faruwa dasu yanzu ba kamar yadda suke ba a baya a tsakanin su da zai fito da fara,a.
Lokacin ina cirewa nasir fararen kayan dake jikin shi zaici abinci don nayi mai mutumin shi watau masa da miya yaji kayan hadi yayi laudi sosai.
Saida yaron ya fara cin abinci ina gyara mai zama naji anty na kwala min kira da sauri na mike zuwa amsa kiran nata.
Zaune take ta caba kwaliya nagani na fada takecewa dani don Allah ku fara fita da abinci falon daddy yanzu.
Nace gaba daya zamu kai tace kukai duk abinda kuka shirya mai ba tsaya ma munyi magana ba ya fice yana fushi daga maganan gaskiya kawai.
Nake cewa anty don Allah kibar batawa daddy rai tunda shima baya son a bata maki tace barni dashi kawai Rama baison maganan gaskiya ne shi.
Naiwa jinior daya falka daga barci wasa yana washe baki yana min dariya nace bari na je na dawo na dauke ka kaji.
Tace zai je gaida daddy ne shima nace cikin washe baki anty yanzun daddy ya bamu barka da sallah a falo ni dasu Gajiye da Farida.
Tace ya riga ni baku ke nan don yanzu nake da niyar ba kowan ku dama nace to anty bari mu dawo sai kibamu naki ke nan.
Mun kwashi kayan sai falon maigidan a can muka samu hindatu tare dashi itama ta caba kwalliya ba laifi tayi kyau sosai.
Wasu abokan harkan shi ne yan chaina su biyu tare da wasu masu zubin iyamurai suka shigo falon cikin raha da dariya.
Anty na bayan mu nan suka fara gaisawa da bakin da alaman ta san su dama ga yadda take gaisawa dasu din cikin sanayya.
Mun kara shigowa da wasu kayan abincin a lokacin duk sina zaune har Zulfa ma ta shigo gaida bakin nasu da sukazo masu yawon sallah.
Wanda naji sun kira da mr Benjamen daga cikin bakaken fatan ke cewa woow kubani wanan beautiful sister din mana naku hajiya.
Sai aka kwashe da dariya ban da su Hindatu a gurin yace I realy mean it gaskiya idan zaku bani ita ina so don na huta da gorin ku hakana naki aure har yanzu.
Raina na hade a lokacin don jin haushin kafiri wai ni yake so haka sai anty ce ke cewa ai ba addinin ka daya da ita ba.
Kaga babu aure tsakanin ka da ita yace ba matsala ai in har tana sona zan barta tayi addinin ta nima nayi nawa ba shi ke nan ba.
Bamu hakan mu ga addinin mu indai kai mace ne ita namiji zaka iya aurenta .
Yace kai addinin ku fa akwai hikima a cikin sa sosai watau shi na miji a wani addini baida dama ya auri wata mace na daban daga cikin addinin ku ko ?
Anty tace hakane Mr Benjemen yace gaskiya I love the girl wallahi kuyi hakkuri ku bani ita mana please.
Daddy ne ya katse su ta hanya cewa su fara cin abincin da aka jera masu ko don su samu su tattauna abinda ya kawo su yi.
Nikan zamu fita don mun gama abinda mu keyi mutumin ke cewa damu muzo mu karbi goron sallah mu.
Farida ce ta karasa nikan kallon mai kama dana tsana da daddy ya jefoni dashi sau daya yasa duk na rikice a gurin .
Nafara hanyan fita naji mutumin nacewa beauty zomana ki karba please kada kiyi min rowan wanan beautyfubeautiful face din naki please.
Juyawa kawai nayi na bar falo do ba zan iya jure irin kallon tsanan da ake min ba haka na ga shi ya hade rai kamar bai taba murmushi ba balle dariya a duniya.
Farida ce tazi min da kudi masu yawa wai mutumin yace a bani goron sallah na kuma yace wai abashi nomban waya na amma daddy ya koro ta gurin.
Anty dake kusa dashi zaune ta shake murya tana cewa dashi yadda shi kadai zai iyajin abinda take fadi.
Malam idan kai baka so ka bari masu so su taya mana wanan hade rai na may ye haka kuma ?
Wani kallo ya watso mata tare da tsuki yana cewa baki da hankali nake gani yanzu sai nakaiki an auna ki gaskiya.
Suko sauran matan sun zaci wani zancen soyayya suke a lokacin take kowan su ta hade ran ta tasha toka fuska ba fara, a zulfa ta fara cewa ita zata tafi ke nan su huta lafiya.
Hindatu ma tamike tana masu sallama anty ce tare da mutanen dama ita sukafi sani don shi benjemen abokin karatun su ne tun a makaranta suke tare da daddy din da ita.
Bata jima ba tai masu sallama tafito inda sauran suka bata alheri mai yawa wai su raba gaba dayan su har mu.
Ta dawo da kudin a hannun ta nan ta zauna falo tana magana taga ban cikin dadin rai take tambayan may kuma ya faru dani haka ne ?
Cikin bata rai nake cewa haba anty kafiri zaice yana sona don ya raina min hankali dariya farida ke min tace kinga sai muje church musha rawa ke nan.
Maka nakai mata a baya daga inda nake take cewa daga fadin gaskiya yaga abinda keyi mai ne mana ke wani namiji zaiganki haka bai rola maki ba.
Muna zaune anty ke cewa dani raba kudin nan daidai har ku da wa yan can akai masu nasu kisaka Gajiye datasha aiki a cikin rabon ita ma .
Sai gashi kowa ya tashi da kusan ashirin ashirin su anty da abokan zama ta na cirewa ashirin ashirin sauran har nacire muna na kuma cirewa sauran yan aikin su hindatu dubu biyar biyar a ciki.
Nai mata bayanin yadda na kasa tace kin kyauta haka ake so suma ai su lasa ko ?
Tace Farida takai masu nasu har yan aikin nasu abasu nasu don ni bata son ta turani gurin su inba dole ba.
Farida nakai kudin tamikawa kowa har yan aikin sai Hindatu tace da ita may nene wanan ana nufin iya kudin da suka bamu ke nan ko may wai ?
Farida tacd shi nagani nima don a gabana aka raba tace na kawo wa kowa nashi nakine wanan.
Tace ke may kika sani koma kinbsani ne aiba zaki fadi ba don kan ku daya kwadai ya rufe maku ido kamar wata tsiya ake kulla maku banda aikin wahala da kuke mata.
Fita tayi ta barta tana bakaken magana a falon ta ta dawo ta fadawa anty abinda tace da ita da takai masu.
Anty wanan irin abin nake gudu wallahi duk yadda kayi baka fita a gurin su na boye na gane may wai ?
Run gumay nake da Nasir da yai barci a jikina idona akan tv dake aiki ana wasan barka da sallah yara nata mika gaisuwan su ga yan uwa da abokan arziki sai ga daddy ya shigo falon nan muka shiga gaidashi yana amsa muna cikin basarwa.
Guri ya samu ya zauna a falon tare da cewa shi wanan baya barci sai a saman jikine ?
Anty tace haka ta saba masu dashi wallahi ai akwai aki randa Rama ta bar gidan nan ga yaran nan .
Yace yanzu wanan ta samay ni wai kudin da su John suka baku ba a raba daidai ba yaya akayine wai ?
Salati anty ta saka tacd kai wanan abin wai damay yai kamane tace Allah yasa gasu a zaune kai maganan nan fada mai Rama yadda kika raba kudin.
Nafara koro mai yadda nai kasafi tace to kaji don ni ita namikawa nace tafitar da na kowa har masu aikin su sai da Rama ta fitarwa da nasu amma kuma suce wai hakan baiyi ba.
Yace nasan ai bazakiyi abinda bai dace ba akai zargine kawai irin nasu takeyi ina laifi anba kowa yasamu.
Anty tace ni idan bai mata ba sai na hada da nawa duk ta rike bashi ke nan ba.
Yamike yana cewa akan may zaki bata nata wata fi idan bata so ba sai ta dawo maki dashi ba dama ai ba donta aka bayar ba don wa yanda sukai aiki ne suka ba da.
Ya fara tafiya yake cewa ke je shimfede yaron nan hakana ya kwanta ku daina bata shi dayawa ace yaro bai barci sai a jiki zaiyi barci kamar wanan.
Na daga yaron tare da jan kafana da duk yai sanyi na fice rugumay da yaron a kafada na zuwa dakin mu.
Ya juya gurin anty yana cewa kema ki dinga mata fada ta daina shagwabasu haka mana abin yai yawa wallahi.
Rama da yaran nan ne sai Allah nagaji na sa mata ido dasu kagan su na yanzu basu iya zama sai a saman jikin ta sun riga ta saba masu da hakan ko .
Nima dana shiga shirin kwanciya na fara yi bayan na shimfide yaron sai dai nasan ko na kwanta a lokacin dole na fito don rufe guri saboda anty a gurin maigida zata kwana ranan.
Ban jima da kwanciya ba naji muryan anty tana cewa dani har kin kwanta ne haka da wuri Rama ?
Ko fadan da daddy ku yayi na yaran kike wa fushi kuma ai gaskiya ya fada girma fa yaran keyi ke ko kina dada shagwabasu haka.
Zama tayi a bakin gadon da nake kwance tana fuskantana sai duk nabi na tsargu da kallon da take min a lokacin .
Tace yafara takurawa rayuwan ki ko a gidan nan da sauri nace wa anty ina mikewa zaune daga kwancen da nake tace dani daddy ku mana .
Kallon mamaki nai mata nai wani tsuru tsuru dani nace a hankali cikin karfin hali anty daddy ne zai matsa min kuma ?
Dake dashi anty ai a karkashin ku nake don may bazan gode maku ba balle ni anty wani matsi daddy ke min a gidan nan mutumin da zan share kwanaki ban gani ba idan ba ya shigo nan wani sain na gan shi ba.
Ni idan bakuyi min fada anty ai abin bakyau kuma duk yadda kuka zartan dani ai a karkashin ku nake kuma ni wallahi ma banji yai fada ba a kan yaran nan.
Tace na dauka shine kika shigewa daki ai kina fushi don maganan da yayi din ?
Nai murmushi nace kai anty wai fushi kuma kin san yau tun hudu idon mu biyu nagajine kawai shiyasa na dawo na kwanta ni da mutumina kada ya falka yaji bana kusa dashi.
Ta mike tsaye tana fadi ai na sani tace nidai tasi kafin jaririn naki ya falka din Allah ki shirya min yarona mu tafi ki rufe kofa.
Tare muka fito daga dakin da ita zuwa dakin ta ina gana sakawa yaron over roll take cewa dani ta fito daga bandaki ke nan.
Rama yadda kika saba yi muna wanan dawainiyar kina kula dani da yaran nan da zuciya daya ina gujewa ranan da zakice zaki bar mu wallahi.
Shiyasa nake kokarin ganin baki barmu ba har abada mu zauna dake cikin farin ciki da jin dadi amma bazaki gane ba ke yanzu.
Shima din da yake ganin yaran kina ahagwaba su ai bai ganewa ne yanzu ne suke samun kulawa irun na uwa daya dace yaro ya samu.
Yaushe suka samu kula irin haka a gurina kullun yau ciwo gobe lafiya nake sai in share watan ni ma basu ganni ba suna zaune ana gwada masu ukuba gurin kishiya.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA HAKKIN AMANA YANA KAN KI DON ALLAH NA GANIN KI YAR UWA, , , , ,

29
Bukin sallah akeyi don haka gidan bai rabuwa da baki ta ko ina shigowa akeyi wanda kusan yan uwan dangin mai gidan ne ke shigowa yawon barka da sallah gidan.
Farida kan washe garin sallah ta hada abin arzikin ta sai ganin ta mukayi tana cewa anty ni zan tafi gida.
Anty take cewa yau din nan Farida babu ko magana ta da yi murmushi tana gyara jakar kayan ta dake kafadan tana cewa akwai friends dina da muke yawon sallah tare dasu sune suke ta damuna da kira tun jiya.
Daga inda nake zaune ina mata murmushi nace yanzu kina nufin tafiya zakiyi ki barni gashi munce zamu gida Zarah yawon sallah.
Tace tafiyan ta kama ne nayi shi ai Idan ta tafi saina rakaki Rahma inji Gajiye nace shike nan kuwa Gajiye mu dawo idan kin zo mu baki labari ai.
Namike na rakata har bakin get da kayan ta Hamza driver ne ya tafi da ita gida a lokacin .
Na dawo na samu gajiye na magana da anty take cewa tun jiya da dare take fushi ban san may akai mata ba dai.
Ranan dai ce min tayi wai ita da take yar uwar maigidan ma ba, a kulata kamar yadda ake kula Rahma a gidan nan.
Anty tace kyale mahaukaci kune baku gane may take nufi ba fa ita adole wurin nan daddy ku take so.
Lokaci daya mukace ita Faridan ke son daddy anty tayi yaya da daddy idan ma yace yana son ta.
Kai amma Farida bata da kunya mutum mai mata haka kamar daddy zatace wai tana kyarkyaran shi a gaban matan shi.
Gajiye Tace yau she ma zai so mace haka kamar Farida wanda keda mata irin haka a gida.
Anty tace kada kuce haka ita rayuwan duniya haka take dama kuma Allah yafimu sanin abin daya dace a rayuwan mu don haka idan da aure a tsakanin shi da wata a gidan nan cikin ku sai ayi ai.
Kallon mamaki naiwa anty wai ita anty wata irin mace ce mai saukin kai ne irin haka ?
Hakan fa ranan da Hindatu tai muna kazafi sai budan baki tayi wai zatai farin ciki idan daddy ya aure ni.
Ko wace mace na kishin mijin ta karara a fili amma ita anty sam bata nuna kishin mijin ta irin na sauran mata da sukeyi.
Gajiye tace haba hajiya ina Farida ina shiga tsakiyan ku kishi yaushe ma Alhaji zai tsaya kallon wata Farida can.
Anty tace kai Gajiye akwai ki da wani magana wallahi ai kamar yadda yaro yake dan son jiki zagi ko duka bai sawa yaro natsuwa haka na miji yake shima.
Namiji da zaran mace ta iya tattalin shi tasan takon halaiyan shi shike nan idan tana da hakkuri ta gama da namiji yi nayi bari na bari sai kiji zama ya dore ana wance ta asirce mijin ta sai abinda tace da shi.
Yanzu ki duba fadan daddy akan Nasir da Amira duk wanda ke gidan nan yaran nan basu saba dashi ba kamar Rama a gidan don may don ita ta zauna da yan uwanta a gida tasan ta ja yaro a jikin tw baki taba jin Rama ta zagi yaro ko tai fada dashi a gidan nan.
Sai dai ta nuna masu soyayya da cusa masu tsoron Allah ta hanyan yi masu nasiha idan sunyi abinda ba daidai ba tare da basu labarin da zai tsoratar dasu bazasu sake maimaita abin da sukayi ba.
Kin ga ai ta taimaka muna sosai gurin gyara tarbiyan yaran nan da basu samu ba a gare mu a baya da yaushe yaron gidan nan zai tsaya gaida babba can.
Ni kinga in ba yanzu dana dan samu lafiya ba gajiye bana zama a kasan nan haka ko yaushe nike nan bin jirgi zuwa ganin likitana a waje.
Gajiye tace hajiya wai may ke damun kin ne hakana don Allah ?
Murmushi anty tayi yanayin ta ya juye a lokaci daya batare da tai magana ba tace gani nan dai gajiye abin sai Allah kawai yau ace wanan gobe ace wanan ke damuna.
Yanzu haka ko azumin da na dan yi ne tun jiya nake jin alaman ciwon nan na son taso min wallahi.
Da sauri nace subbahanallahi anty ai gara kije asibiti kagin ya matsa maki don Allah tai murmushi tace Rama ai nasha magani koda safen nan shine na dan ji saukin shi ai.
Nayi shiru ina tunanen matsalan anty na mace mai kawaici da karamci irin anty samun ta a wanan zamanin sai an tona .
Ku shirya anjima ina son muje gaida Abbana da sallah don yana gida yanzu nasan bai fara fita ba tunda sallah ne.
Bana son zuwa gida idan Abba baya gida saboda yadda ake min a gidan shiya kikaga bai faye zuwa ba idan ba wani dalili mai karfi ba zai kaini gidan.
Gajiye ce ke cewa matan gidan fa ba suna nan ba tai murmushi tace sunan Gajiye kin san muna cikin lokacin da kowa nasa ya sani yanzu.
Ba kowane zai iya kula dan kishiya ba ni ko zama ma basu yi da uwata ba amma sun dauki tsanan duniya sun saka min a rayuwan su.
Don hanin da sukayi Abba na tausaya min rashin uwar da na taso ban dashi a gidan har yakai shi kan shi Abban ya fahinci basu kaunana ko kadan a gidan.
Zarah ce kawai nake dan hurda da ita cikin yan uwana duk sun hurewa diyan su kunne akaina wallahi.
Mikewa nayi zan shige anty ke cewa ina kuma zaki Rama nace naji kin ce zamu gaida daddy shine zan hada mashi cake da wani abin.
Tace ikon Allah yaya kika san Abba yana son cake sosai Rama nace ranan naji yana magana an mashi cake ba dadi ai.
Nan na shige na fara hada cake din na kuma gasa mai nama na peppeying din shi da kyau na hada fruits salad mai dadi na sa a fridge zuwa azahar har na kammala na shiga wanka ina wanka nake tunanen maganan anty akan Farida.
Lalai biri yai kama da mutum don ko motan da daddy ya saya min sai da tai fushi sosai a kan shi tama dauke kafan ta a gidan a lokacin sai daga baya ta dawo kuma.
Idan muna zaune da ita takama magana ke nan Rahama mutum ya samu miji irin daddy ai ya more rayuwan shi tun dai idan matan shi sukai mai wani abu.
Ta shiga tsaki da korafi ke nan sai nai mata magana nace ina ruwan ki mutum da matan sa ke may ya shafe ki a ciki.
Baki ganewa ne Rahma ita anty Zulfau tana ganin kamar tafi kowa cikin dangine da ya aure ta inba aure mukkadari ba ina ita ina shi mace haka kamar uwarta ba kiba ba wani zati da za, a gani ace wai matar shi ce.
A lokacin sai nake dauka don tana yar uwarsu ce take jin haushin abin da ake mashi ashe ita abin ba haka yake ba a gurin ta.
Nafito na shiga da yaran na kara yi masu wanka bamu fito ba sai dana gyara su tsab muka fito na samu ita anty bata ma shirya ba tana kwance da taimakona ta samu ta shirya ina shirya jinior take cewa daddy yace shi zai kai mu ai.
Ban ji dadin haka ba naso mu fita da ita kawai don mu dan yi yawo saboda mu ga gari da bukin sallah da akeyi.
Na fito da kayan dana hada tana gani tace ikon Allah Rahama ashe yau zaki saka Abba cikin farin ciki dama yana min korafin nabar kawo mai abinda nake mashi a da can baya.
Muna fitowa dauke da basket biyu ni na dauki dayan Gajiye ta dauko dayan yana cikin mota mu yake jira ya bude buth din motan na saka kayan a ciki.
Na koma na karbo jinior dake hannun anty suna fitowa kamar kullun motar shi bakajin komai sai sautin tashin kira, a a cikin sa ta tsaya ta rufe kofan shiga part din mu ta miko min keys din na kada a handbag dina.
Tana gaba nida gajiye da yaran muna baya nan muka gaida shi ya amsa muna kamar dole.
Yaja mota muka fara tafiya suna hira shi da matar shi nima a baya yaran sun matsa min sai da nai magana dasu har nabiye masu muna hira muma da gajiye.
Uguwar su anty tsohon gari ne don gidajen dake unguwar zaka fahinci haka dagani suma gidan nasu daga baya akai mai kwaskwarima na zamani .
Sai gidan ya haska uguwar sosai dashi da wasu gidaje daga cikin unguwar.
Nan dai muka fito muka shiga ciki a falo muka samu Abban yana tare da wasu dattawa a zaune yan uwan shi.
Muka zube kasa har daddy muna gaida shi yake cewa Alhaji Yusuf ka dawo ne kuma Allah dai yai maka albarka kin gane shi nan idan har yana garin nan sai yazo ya gaidani wallahi jiya nan yake da yaran nan sun zo gaidani da sallah.
Yafi min sauran mazan yan uwan ki sau dubu wallahi shiyasa nake jin shi kamar ni na haifi abina Saade don yanzu ma kusan ya karbe maki nine ai .
Tace kai haba Abba akwai wanda ya isa ya karbe min kai kuwa yace to tsaya kiyi wasa nan dai yaja yan jikokin shi yana wasa dasu wasan jika da kaka.
Nan yake fada masu cewa kwana biyu ba, a karasa azumi dashi ba ai don jikin nashi ya motsa mai.
Anty tace dashi ai Abba nima haka nake tun jiya wallahi tafiyan nan ma dai na karfin hali nayi don nasan yanzu ne ake samun ka a gida.
Daddy yace amma Abba da ka daure idan zamu fita atafi dakai kaga likita kaima a can yace kai haba wani likita zan je gani har waje Allah dai ya yayye kawai za, ace yanzu.
Rama baki ba Abba tsara ban ki ba mana sai lokacin na dan motsa shima Abban ya kallo inda yaji an ambaci sunana yace au itace yarinyar da kuke rikicin akan ta ke nan ko ?
Rikici kuma nace a raina sai kuma nake cewa killa zan cen fitinan su hindatu ne a kaina yakawo ga kunnen Abba din.


Please Login or Register in order to submit comment