Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan in ban manta ba sunan mahaifin anty ke nan ya sakawa yaron ni dai amin nace tare da fatan Allah yasa yaron ya biyo asalin mai sunan na gaskiya sahabi kuma suriki ga mazon rahama.
Ya dago bayan ya aje yaron yace dani ga yaran nan sunzo ke nan anan zasu zauna sai hutu zasu dinga zuwa gun uwayen su suna ganin su.
Nace Allah ya taya mu riko yace dani amin sai ayi hakkuri duk da kin saba dasu yanzu akwai dan canji ga baya sai an kai zuciya nesa ga wasu abubu na su.
Nace ba komai in sha Allahu zaa kiyayye da yardan ubangiji da ai na kowa ne bana mutum guda bane dama.
Yace ya gode yafice daga dakin nafito falo don in basu masaukin da zasu zauna saboda akwai baki a gidan.
Dakin da suka taba zama nan na sake ba su Nasir sunji dadin hakan sosai don na fahinci suna son dakin tun lokacin da nace dasu shine daidai da samari kofan shigowa su kuma suna ganin sun kai samari din yanzu.
Ihisan ce da nace ta zauna da su Aisha ta kawo min gardama wai ba zata zauna da su ba do bata zama da yan aiki.
Nace to kiyi hakkuri ku zauna idan su mama sun koma sai ki kama daki daya daga cikin dakunan bashi ke nan ba duk da nasan tai karama da zama daki ita kadai .
Aiko tace ita bata san haka ba sai dai na bata nata dakin ko ta zauna a falo nan mama ta saka baki tai cikin ta da fada har uban ya fito ya samu ana wanan rikicin haka.
Yake tambayan may ye mama ta fada mai komai dake faruwa yace idan hakane su su Aisha su koma daki daya da helen sai a gyara mata wancan din da helen ke ciki.
Duk da raina ya baci sai ban nuna komai ba ga haka nasa suka gyara mata takoma ciki aka zauna lafiya duk da nasan yaran zasu takura zama da kafira a daki daya.
Washe gari da safebayan nai wanka na shirya ina zaune ina cin abinci mama na daga gefe na tana gyaran wani ganye a roba da zata hada muna na kunun kanwa tace dani.
Rahama nace naam mama tare da dago kaina tace abinda nake so dake shine kikara hakkuri akan zaman yaran nan a tare dake.
Musanman ma wanan yarinyar da kike gani tunda kikaga ta fara tsiyataku irin haka tasha hudubar shedan sosai a kan ki ne.
Don haka don Allah Rahama na rokeki da kikai zuciyar ki nisa akan zaman yaran nan dake don wani babban rikici ne ya dauko maki kuma anan.
Kin san maza su basu gane haka sai in abu ya faru dasu ne hankalin kan kawo wuta cewa sunyi kuskure wani ma ko ya gane bai gyarawa don suna takama iko a hannun su yake.
Nace in sha Allahu mama zan fake don nima na fahinci yarinyar tazo da wani manufa akaina tun zuwan ta na lura da hakan gareta.
Tun da aka gyarawa yarinyar daki bata fitowa falo sai idan ta fito cin abinci tana gamawa kuma zata koma daki ta zauna ita kadai.
Ban damu ba sai harkokina na suna nake don ban tsaya binta kanta ba tukun nakama shaanina kawai muka barta yadda ta ware kanta gare mu.
Monday ya kaisu makaranta nai arziki harda Atika ya hada ya mayar can duk ko da tsadan makarantan amma yai min wanan karar haka.
Shiyasa nake son daddy sosai wurin irin wanan halin nashi na karanci ga dan kowa don nima haka yai min a baya.
Saura kwana uku suna Zarah da maigyaran harka suka iso Abuja da tarin abin arzikin su washe gari basu zauna ba suka fara shirye shiryen abinda zasuyi na sunan komai da yakamata ace anty ce tai min sai ga abokan arziki sunyi tsaye sun fitar dani kunya da taimakon Faiza kawata komai ya kammala masu don su ba wai sanin garin sukayi ba.
Da yamma yan suna daga kano suka iso yan kauyen mu da kuma yan uwan daddy maza da mata gida ya cika da baki tako ina jama, a ne a gidan.
Nai mamaki yadda mutane sukazo min haka Suwaibana bata samu zuwa ba don ance tana jinyar mijinta Jatau baida lafiya sosai.
Ta ban tausayi yadda ake min labarin suna fama a can gashi basu da mai taimaka masu duk da yake a kwance ya tsuke bakin aljihun shi tam bai sayen ko magani dashi suna matukar wahala sosai.
Nace da Rukkaiya shine aka rasa wanda zai bugo waya ya fada min halin da take ciki ga yara ga lalurar miji da wani zataji kuma ?
Ranan suna daddy ya baiyanawa jama, a sunan yaro Aliyu sai ranan suna anty Zulfau ta iso tare da wasu yan uwanta su hudu.
Ta girgiza kwarai da ganin irin daular duniyan da muke ciki a zaune take mood din ta ya sauya tun kan ma ta shiga gidan.
Abokan tafiyan ta na kara zugata wai dankari kune aka bari ashe a can kuna gafin gida ga inda arziki yake nan jibge.
An mayar daku wa yanda basu iya cin duniya ba ke nan an kawo wace ta iya ci an ajeta ana itace matar gaban mota an mayar daku tsofi da karfi da yaji.
Naji isowar su amma sai banga sun shigo gidan ba nake tambaya akecewa suna waje tukun basu shigo ciki ko.
Can sai gasu sun shigo ina saye cikin wani dogon rigan din kin Dubai da gyalen shi iri daya masu ruwan kore da milki a jikin su.
Sannu da zuwa nake masu a take yadda suka amsa min a wullakance sai na fahinci da akwai magana a tare dasu.
Nan dai aka cika su da abin motsa baki kala kala a gaban su sai faman bin gidan da kallo sukeyi suna mayde baki.
Can buki yayi buki a kace ana nema na a waje nafito lokacin na sauya kayan dake jikina zuwa wani hadaden lece maron colour.
Nace ance ana magana dani ko wake nema na Zulfa tace dani nice nace gani anty kina son wani abune ko may ?
Tace eh k dakin maigidan nake nema dama nace to sai
tambayan yai min wani banbarakwai nace sai dai a rofe kofan nashi yake don jama, a.
Tace to aban key din nace a, a anty ga dai daki can na gyara maku don zuwan ku shida kan shi ya rufe kofan da zaifita don jama, a da sukai yawa a gidan.
Tace ban gane ba may kike nufi nace ba komai sai dai ki bari idan ya dawo sai ya bude maki ki shiga ko ?
Tace ikon Allah dakin mijin ma Rahama hanani shiga zakiyi ko may ikon naki da mulkin har ya kai can ban sani ba ashe ?
Nai murmushi babu bacin rai nace ban kai can ba amma sai dai kiyi hakkuri don Allah don key yana a hannun shi ya fita dashi.
Ta juyo fuuu ta wuce dakin da suka sauka sai bin mu da idanuwa mutane ke yi don anji may muke a wurin.
Gun mama taje da fadan ta sai da suka gama sauraren ta mama Rakiya tace da ita haba Zulfa may yakaiki wanan maganan kuma haka a bainar jama, a keda kikazo abin arziki kuma ?
Ki bari mana idan mijin naku ya dawo sai ki tafi amma ko nice yanzu ya rufe kofan shi bazan baki key ba tunda baa nan kike zaune ba tare damu.
Tace kuma wai su mama sun goya mata baya ai mata cin mutunci nan dai suka taru sukai mata fada ashe komawanta daki takira shi a waya ta kwashi karya da gaskiya ta fada mai.
Anci an sha anyi shagali harda walima akayi wa, azi wa mata aka dan raba abinda aka sayowa jama, a a wurin.
Yan asibitin mu sun min kara sosai don sunzo wurin sunan harda wanda ma ban zaci zasu zo wurin ba sun zo tayani murna sun kuma koma da abin arziki a hannun su.
Sai dare ya dawo gida lokacin yan gari sun rage sai mu da bakin mu yasu yasun mu muka rage a gidan.
Muna dakina dasu Zarah mun baje sai hiran sunan mukeyi sai ga ihisan wai nazo daddy yana kirana.
Na saka hijjab dina na fita don nasan daddy yana dakin shi a lokacin ban kawo komai a raina ba nai sallama na shiga dakin sai ganin Zulfa nayi a zaune cikin rashi damuwa nace da ita ashe kina nan anty ya gajiya.
Sai naji bata amsa min ba na gaidashi da dawowa ya amsa min tare da cewa wai may ke faruwa ne yanzu Zulfa ta samay ni da wani zance koma ince tun ina can ta buga min waya lokacin muna meeting ban jiba sosai.
Cikin mamaki na juya gareta ina cewa may akayi kuma ban fahinta ba ni yace dakata Rahama don na kawo ki nan ke kadai bashi zai jawo kiwa matana cin mutunci ba abainan jama, a haka daga tambaya sai ki rufe ido ki dinga gaya mata maganan banza haka a bainar jama, a.
Kin fita ne ko a tsaanin ki ke kadai keda gidan ne da wata bata da ikon zuwa tayi yadda ranta ke so a gidan.
Yaushe kika fara halin rashin mutunci irin haka ban sani ba kada na karajin qanan halin a gida don bazan lamunta a wullakanta min mata na ba ko kadan kin sani.
Idanuwa na rutse a hankali na mayar da hawayen dake son zubo min a lokacin don ba zan yarda kishi taga bacin raina na bukatan ta ya biya.
Nace ayi hakkuri duk da ban san abinda nayi ba amma tayi hakkuri don ni tazo garin nan bazan so tace nai mata wani abin bacin rai ba .
Ina fadan haka ban tsaya ba na juya na bar dakin raina a bace a daki nake mayarwa Zarah abinda ya faru tace dama shi ya kawo ta taga ta bata maki sha, ani ba komai hakan bai samu ba ta hadaki da miji yaci maki mutunci a gabanta.
Nace ba komai ta dauki bashi in dai ban cuce ta ba bata barin garin nan Allah bai tona mata asiri ba ai a gaban shi.
Washe gari ban bi ta kansu ba an hada abin karyawa wanda wasu masuyi na kudi nabawa aikin yi har abinci su suka kawo muna ban fito ba sai rana nafito na gaisa da mutane har ita din Zulfa saida na leka dakin da suke na gaida ita da bakin ta.
Sai wani kallon banza suke min anty na bata zo ba amma taimin aike na abinda zata bamu wanda kayan baby ne da nawa masu kyau da tsada ta aiko muna dashi tace tunda yaro yaci sunan mahaifinta Aliyu.
Sai washe gari yan suna suka shiga kasuwa da gari bayan sun huta sunyo sayayya sosai a kasuwan.
Sun dawo suka fara shirin tafiya tun basu tafi ba na fara kewan su a gidan sako sosai na shiryawa iyayyena da yan uwa na da basu samu zuwa ba misanman ma Suwaiba na dake cikin wani hali na ban tausayi.
Sun shirya tsab da safe zasu wuce ina kallon yadda Zulfa ke nuna min ita fa matace kuma tana da iko da gidan mijin ta sau yadda taso.
Ban kula ba ban damu ba daga ita har mijin daya share ni a gaban bakina duk da banda Zarah da maigyaran harka ba wanda yasan halin da nake ciki a gidan.
Zaune muke muna hiran mu a dakina duk da dare yayi har wasu sun fara barci a gidan sai sama sama muka dinga jin hayaniya na tashi.
Bamu damu damu saurara ba da farko sai dai da muke jin muryan daddy yana tashi muka kashe kunnuwan mu wurin saurare.
Fada ne sosai tsakanin daddy da Zulfa ke tashi yana fadin wallahi idan har baki fito min da kayana ba sai ran ki yai matukar baci.
Ko allura na bai taba bacewa ba a gidan nan sai yanzu zan nemi abu in rasa shi nidawa ke dakin bayan nidake ke kwana a ciki.
Daga inda hajiyan harka take kishingide ta mike zaune tana cewa lalai Rahama kin cika yar halak wallahi.
Fadane fa ake a gidan nan nace matsalar suce hajiya ni ba abinda ya damay ni da sha, anin su su suka sani.
Muryan mama Laraba yasa muka kara saurarawa tace bakiji ne Zulfa tun farko dakika zo may muka fada maki ranan da kikaiwa yarinyar nan wullakanci a gaban kowa don tace kawai key baya hannuta yana hannun maigidan.
Nan fa faban bakinta kika rufe ido kina mata cin mutunci son ran ki ashe ke da wani manufa kika sa sai a bude maki dakin duk da hanakin da mukayi.
Tace mama aiba ni kadai keda key din ba sherine kawai aka kulla min don a bata min suna kawai wallahi amma ni ina ruwana da kayan shi.
Yace kina nufin Rahama ce ta shigo ta daukar min abu bayan sun dade a wurin bata dauka ba sai yanzu.
Mama tace kai amma Zulfa baki biyo nono ba wallahi sai dai a yabe mu da fada amma ba mugun hali ba dan hannu.
Ta juya rai a bace inda mama take tace mama may kike nufi kema satan zaki dafa min ko may ?
Yace rashin kunya zaki mata yanzu ko may tace ba rashin kunya sai gaskiya tunda dai dama kowa yasan yanzu mama don anga Rahama na nan sai wani shishige mata akeyi don ana zaton itace mai shi.
Ihsan da suke dakin ta ta kumaji plan din su ta fito tace a a anty ba ruwa little mum ga maganan ku naafaji hiran ku ranan da kike basu labarin kinga white gold a dakin daddy masu yawa.
Akace ki diba sai yanzun kuma zakice wai ba ke bace tai salati tace yanzu ihisan ni zakiwa sheri abin naki har yakai can ashe ?
Nan dai duk gidan yai tsit ana sauraren fitinar su sai dai ba wanda ya fito sai sauraren su da akeyi kawai a sauran dakunan kamar yadda muma muke sauraren su din a inda muke zaune.
Duk yadda daddy ya buga taki fito mai da kayan shi su mama sukace ya kyaleta Allah ya tona asirin mai shi bai so ba haka ya yarda yabar zancen rai bace mai.
Ni dai a bangare na Allah ya fitar min da hakkin kazafin da taimin ya hau kai ba tare daya bincika ba gashi abinda ya wakana a tsakanin su yanzu.
Washe gari tunda safe suka bar garin tare da sauran bakin da suka zo sai gidan ya koma muna tsit iyamu aka bari dasu mama kawai agidan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BZ ONLINE NOVEL NE, , , ,

76
Tun tafiyan bakin mu su Aisha suka gyara min gida ko ina ya rage daga ni sai yara dasu mama da zasu zauna har zuwa lokacin da zanyi arbain kafin su wuce.
Har wanan lokacin iyakana da daddy ina kwana ko shi daga kofa zan tsaya na gaida dashi na bar dakin wani lokaci ma a falo zamu hade ko ina barci zai fice daga gidan sai in yadawo nai mai sannu da zuwa daga inda nake.
Ban bin shi baya balle na daukowa kaina magana ko wani sabon fitina, nayi hakane don na kama kaina akan komai dama sati biyu aka bani a wurin bautar kasa na don haka lokaci kawai nake jira na koma.
Banda matsala da yaran da ya kawo min sosai Jinior dai ne da Ihisan keda dan matsala kuma basu wuni a gida in sun fita tun safe acan zasu wuni sai shidda na yamma zasu iso gida.
Ina ganin shiru ya dan damay shi ne ko yaya ban sani ba dama can shi dai ba gwanin zama bane ai hira dashi don ko yaushe zaka samay shi busy ne.
Na kan yi mamakin yadda yakan samu lokaci a baya yana hira da hindatu ko don yawan nacin ta ne tafi mu nacewa ban sani ba.
Case din shi da Zulf sai da iyayye suka sa masu baki daya je gida tafito mai da dutsen shi don yasan cewa ita ta dauke su.
Tasha fada sosai a gurin iyayyen su sai datace ba itace ta dauko da hannun ta ba Rafia ce kaunar ta data shiga dakin tana ciki ta dauka aka kuma bincika haka din ne sannan ta samu sasauci a gurin shi.

********* ********* *********
Tun bayan haihuwa na ban faye fitowa falo ba ina dakina ko barci ko wani abin tunda bana sallah a lokacin.
Ina kwance a dakina don tun yamma dana dan leka su mama a falo na dawo daki kafin magariba ban sake fitowa ba har tara da wani abu na dare.
Yanayin rayuwa ta tun haihuwa na gaba daya ya sake min bana son yawan hayaniya haka kuma bana yawan zama cikin mutane sosai.
Dama da yara nafi sakewa ko a baya ban faye shiga cikin manya ba ina zama ana suraitai don nakan rasa may zan fada wani lokacin .
Kwance nake sai dai ba barci nakeyi ba idona kawai na rufe na dora tsintsiyar hannuna a fuskana.
Idanuwa dake rufe bai hanani sanin ya shigo dakin nawa ba don kamshin turaren shi dana shaka a lokacin .
A hankali na bude idanuwa na da suke rufe da farko yana saye da hannuwan shi duka biyu a cikin aljihun wandon shi dake jikin shi.
Yana ganin na bude idanuwa sai ya karasa takowa zuwa inda nake kwance tare da kura min idanuwan shi duka biyu a inda nake kwancen.
"Rahama,
Na amsa da naam ba tare da ko na motsa jikina ba daga yadda ya samay ni a kwance din da farko saman gado.
May kike nufi ne da yin hakan da kika dauko yi a gidan nan yanzu bayan kin san duk wanda ke gidan nan a katshin ki yake zama sai ki shige daki ki bar mutane a falo suna zama.
Na fahinci tun ranan da akai maganan nan da Zulfau kika dauki bakin rai kika sawa zuciyar ki haka kada kice ko ban fahinci may kike nufi bane fa ?
Kin daina kulani kin daina kula duk wani wanda ke gidan nan yanzu kamar yadda kikeyi a baya can ?
Wasu kwalla ne masu zafi suka silalo a idanuwana, na tuna yadda ya rufe idon shi yai min tas ranan akan gaskiya na a gaban matar shi.
Idan kuwa ban kama kaina na tsaya a matsayina ba ai wata rana zan iya kai kaina inda Allah bai kaini ba wurin karanbani na.
Lafiyan ki ana magana baki bani amsa ba sai ki kama zubar min da hawaye haka kamar wacee akaiwa wani abu daga magana kawai.
A hankali na iya bude bakina da kyat nace don Allah daddy ka barni a matsayi na a dakina wanda ka bani agidan nake zaune bana son shiga hakkin da banawa ba ni kadai a gidan mutane.
Yace haka kikace ko nace hakan aka fada min ai koka mantane ranan abinda ka fada min a gaban matar ka akan na tsaya a matsayina kuma banfi kowa iko da gidan ba.
Yace wanan ne hujjan ki dama na sani sai dai kina da aiki idan kikace ke baki mantuwa da sabani idan anyi.
Ba rashin mantuwa bane sai tunatar dani wani matsayin da nake ciki wanda naso na manta shi a baya can.
Yace cikin kada kan shi ok yayi kyau tunda haka kikace ba matsala yasa kai ya fita na bishi da kallo har yabace min da gani na share kwallan fuskana tare da gyara kwanciya na.
Ina kwancen ban daga ba sai gashi ya sake shigowa dakin a karo na biyu wanan lokacin ya sauya kayan dake jikin shi zuwa rigar barci.
Take kuma ganin shi yasa gabana ya soma halbawa a hankali, da kyat na tatara natsuwa na wuri daya har ya karaso inda nake kwance.
Muryan shi naji yana fadin Rahama kin ban matukar mamaki da kalaman da kika fada min a yanzu kafin na fita.
Bayan aure na dake sai nake daukan zan samu natsuwa da kwanciyan hankali a gare ki ganin irin tarbiyan dake gare ki.
Sai kuma irin yadda rashin kwanciyan hankali ya yawaita a tsakanin ki da abokan zaman ki daya biyo baya musanman ma Saade da Allah kadai yasan sirin ku a baya sai ga sabani yazo yana yawan shiga a tsakanin ku kuma.
Wanan dalilin yasa naga gara na raba ku ko za, a samu zaman lafiya da kowan ku shine dalilin da nai dubaran dauko ki zuwa nan garin na kawo ki inda babu kowa naki ko nawa sai abokan arzikin da Allah ya hada mu dasu anan.
Duk da hakan da nayi Rahama ke nan na kasa sama muna farin ciki gayin haka don gashi har yakai a gaban iyayyen mu kina son su fahinci akwai wani matsala a tsakani dake a yadda kike yi din nan.
Kina nufin ko nuna masu ni na kasa sama maki farin ciki da kwanciyar hankalin da mutane suke hasashen kina a cikin sa a nan din.
Jin yayi shiru yasa nace dashi, daddy ni bakai min komai ba fa kuma ba wai nayi wani abu bane a sani kawai dai na kama kaina ne ga tunin da akai min a matsayina.
Yace tuni akan may yanzu ke kinga yadace a yadda zulfa ta gaya min anyi na tsaya nagoyi bayan ki batare da na dauki mataki ba ai sai ace dani gaskiya ne nafi karkata akan ki kamar yarda ake fadi din.
Nace aini da kai mun san fadi ne kawai amma may akai min wanda su ba ai masu shi ba sai dai suce ina nan garin a tare da kai ni kuma ban hana kowa zuwa ba ai tunda suma gidan mijin su ne nan din.
Murmushi yayi yace keda bakin ki don bacin rai kike fadin wai wata tazo ku zauna da ita anan din ?
Nace in Allah yayi akwai wacce zata zo mu zauna dani dakai ai duk bamu isa mu hana ba daddy .
Daddy Allah ne fa mai tsarawa bawan sa rayuwan da zai yi a duniya ba wai tsarin bawa bane duk mai zama tazo mu zauna mana.
Don ka ne nake ganin wa yan nan abubuwan daddy baka tsaya bincike ba ka rufe idanuwan ka ka sauke min masifa akaina yadda kake so don kawai ka gyarawa matar ka rai.
Dariya magana na ya bashi yace idan na san yadda ake tsayawa gyarawa mace rai ai kin fi kowa sanin hakan gare ni ke dai kice matsalana daukan mataki batare da na tsaya bincike ba kawai.
Nace ni ko may ye yanzu ai ya wuce sai dai ka sani Allah ya na tare da mai gaskiya ko yaushe banga dalilin da da hannun ka ka rufe kofan ka ba da zata zo ita tace na bude mata dakin dan

Please Login or Register in order to submit comment