Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyar masu tsadan nan bakiga na dauko su nan ba.
Da sauri ta miko min rigar tana fadin wallahi nikan wacan din nake so a bar mata wanan din na fasa son shi.
Atika ne kawai nake ganin dogon rigar nan baiyiwa sai Amira tace ida bai mata ba sai abar min don Allah mum na dauki riganunan ina dubawa sai na jefawa Atila dake kusa dani karamin kuma yana da kyau sai duk yara sukayo kan ta wai zasu kwace ta fado min tana fadin anty boye min don Allah sai duk suka danne ni wai zasu kwace rigan mun shagala muna ta ihuce ihucen mu a dakin ya shigo duk yaran na saman kaina suna son kwace rigar a hannu na don wani lokaci haka mukanyi wanan wasan dasu.
Muryan shi mukaji yana fadin kai wanan wasan fa haka zaku jin mata ciwo ne ko may duk suka daga suna numfashi nima dai dariya nake masu nace kyalesu Atika duk wanda ya kwace maki sai na hada maki da nashi ki hada biyu.
Suka fice daya bayan daya daga dakin don ganin shi ya shigo dakin sai bayan sun gama fita daga dakin ne yake cewa dani kin shige cikin yara kuna mugun wasa haka kamar wata karamar yarinya dake.
Nace ina kokarin jawo dan kwalina daya cire dama may nake ba yarinyar ba kaine dai baka gani yanzu don kaga na tsufa maka.
Baki ya dan mayde yace ni zan tafi magariba ya gabato sai dai da safe ke nan don Allah kisa Nasir ya rufe gida idan tara yayi.
Nace za a rufe ai insha Allahu har ya fara tafiya yace dazun Raliya ta shigo tace wai duk baku tare ta ba daga ke har Zulfa may yasa zakuyi mata haka Rahama ?
Nace ikon Allah so take na goya ta ko may ta shigo nai mata sannu da zuwa da yaya hanya may kuma take so nai mata bayan wanan.
Yace har ma kun gaishe ta ashe nace wallahi na gaida ita da zuwa shigowan doctor Fatima ma yasa muka barta falon muka shiga dakin anty ganin kayan da akazo dasu.
Yace to ni yanzu ma ina shiri ta bugo tana fada wai tazo matana sun mata wullakanci a gidana.
Nace shiya kawota dama tsegumin in bashi ba ai naga har tazo ta koma bata shigowa gidan nan.
Yace ni zan tafi nace sai da safe har yakai kofa nace gobe in Allah ya kaimu fa Su Amira zasu tafi sayen form din Jam sai dai dana yace wallahi shi bai son yin karatu a kasan nan.
Ya juyo yana kallona tare da fadin sai ina zai tafi baida hankali ne killa kamar Nasir zan sake shi kadai zuwa wani kasa karatu .
Baiji da kyau bane idan baiyi ba sai ya zauna gida ba gashi ga gidan yai ta zama mana nace haba daddy yarona fa yanzu yakai big boy ne fa.
Tsuki yaja ta sake ce min sai da safe yana tafiya yake fadin idan na dawo na samu bai tafi ba sai na bata mashi rai gobe..
Nace ba a ko bata mai rai tare zamu je ya cika a zauna lafiya gobe din yace ato dadai yafi maku sauki kan.
Da kyat na lalashi Nasir da ya bari muje ya cika ya bi umurmin daddy isan ya fara yi a na daga baya sai ka tafi inda kake so lokacin ka dan girma.
Zulfa ta shigo ta samay shi yana cika yana batsewa ta samuna baki na samu da kyat na shawo kan shi da nasiha da komai ya yarda dani.
Tare din muka tafi dasu suka cika form din don dole Nasir din ya cika saboda ubam yace ba zai kaishi waje karatu ba yanzu sai ida ya kara girma.
Koda ya dawo gidan bamu nan mu fita lokacin ashe da wuri ya dawo gidan ba yadda ya saba hantsewa ba idan yana can.
Sai da na shiga na dan huta na fito zuwa wuri shi na samay shi kwance rigingine ba barci yakeyi ba daga kofa na tsaya nake cewa dashi .
Ina kwana ya dan juyo yana cewa dani har kun dawo nace eh munyi sakkone don mu samu da wuri da rana zan tafi aiki ne in Allah ya kaimu anjima.
Har na juya zan fita nace ashe yau da wuri kadawo haka yace eh nadawo bakin hana a barni na huta ba kowa sai zargina yake wai nina saya maki mota.
Nace Ya Subbahanallah kuma dai shikuma aka kulla yanzu kuma nace dole suce haka don ina yar matsiyata ko ita da ta sai nata kwanaki wa yai magana ko don ni yanzu na saya shine abin magana don ba a son agan ni da karuwa ko ?
Bai dai yi magana ba ns juya na fita raina a bace nace wai may matan nan ke nufi dani ne kodan ya kasance ban iya karyan duniya ba ni da watace aiko da sun sha haushi wallahi don da komai na gani saya zanyi na shigo dashi gidan.
Allah bai dora min irin wanan rayuwan na kwasan banza da wofi ba shiyasa har suka samu daman zargina idan sun ga nayi abu.
Kwantawa nayi har na fara barci sai ga Aisha tazo wai inzo daddy yana kirana a falon shi take ce min naga Amarya ma tazo duk suna falin zaune nace tau.
Sai da na dan bata lokaci na fito falon na samay su zaune suna jiran fitowan nawa na karso da sallama na na samu wuri na zauna kowa sai cika take tana batsewa a cikin su.
Yace yauwa kun hadu ko dama ba komai yasa nace kuzo nan ba sai maganan motar Rahama da kuka gani kuke zargin ko nine nan na saya matashi da kudina na munafunce ku.
Da sauri na dago kaina nace motar tawa ake zargi kuma hannu ya daga min alamar nai shiru na barshi ya gama sai na kada kai kawai tare da gyara zamana.
Yace yanzu gaku ga ta kuji daga bakinta idan nine na saya mata ko na taimaka mata da koda kwandala ga sayen motar nan da tayi.
Kafin nai magana sai zulfa tace haba haba dai yaya ai wanan maganan ma haka bai dace ba koda kaine ma ka saya mata motar ai ba laifi bane balle Rahama ai ba wacce za a zarga bane yanzu don an ganta da wani abu a cikin mu.
Duk mu nan fa mun san aikin Rahama ban ga dalilin da zai sa mu dorawa kan mu wahala bayan mun an zata iya sayen abin da ma yafi wanan din.
Humm umm inji Hindatu ina ruwan karere kina nufin ke nan yanzu Rahama tafi aji ko may kike nufi da maganan ta.
In ma bata fi mu aji ba ai yanzu dai kunji ba shi ya saya mata mota ba don haka ya kamata ku bawa kan ku lafiya muyi fatan muma Allah ya bamu abin yiwa kan mu.
Haba sai ko sukai cikin ta da masifa ni may zance tun da Allah yai min gata an karba min zancen sai naji Raliya na fadin wa za aiwa burgan aiki ko wa akafi aji ni wallahi kar nake kallon mace don nasan wanan plan din ba yau ba kada ku mai damu kananan yara mana .
A raina nace zaki gane shayi ruwa madam don zan gwada maki na fiki iya bariki in shi kike takama.


To yan uwa kun bani mamaki sosai wallahi kunce sai na bace ban fada maku uzurina yanzu kuma na fada maku amma hakan baiyi ba saida na samu marasa hakkuri da basu yarda da kaddara ba suna sake min magana yadda ran su ke so.
Idan kuna ganin maganan da kukai ta fadi a gamay dani shine adalcin zama ko kuma zaku iya sani yi dole sai ku matsa kuyi tayi .
Masu cewa ba zasu sake shiga group dina na ba matsala guban wani zuman wani sai Allah ya kawo masu hakkuri dani da yadda nake dama ko yanzu ina tare dasu sun dade suna hakkuri da rayuwa don sun san ba ni nai kaina ba nima yar adam ce kamar kowa acikin ku.
Yadda kuke da uzuri haka nake da uzuri nima amma masu hankali a cikin mu sun san da hakan.
Masu fadin kudi suka biya don na zauna ba hutu naita rubata masu labari akan dari uku sunyi kuskure zan iya mutum kudin shi yaje inda za, a dadada mashi ran shi.
Ni ina can ina neman waya don na faranta maku rai ku kuna nan kuna ta aibanta ni don rashin hakkuri da son kai irin na wasu.
Ina mai karaba wanda suka fahinci matsala na hakkuri ba kullun ne zaku dinga jina ba haka zan ta maneji har sauki yazo muna da fatan zaku fahince ni yan uwa nagode


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
92

Ubangiji Allah ya jikan anty yai mata rahama yasa ta huta yasa aljannan fidausi ne makomarta.
Wanan mata bazan taba mantawa da ita ba a rayuwana duk wani rudin shedan da ya shiga a tsakanin mu lokacin dan zaman da mukayi a rayuwan ta bana taba jin zafin ta ko haushin ta.
Saboda irin rayuwan da ta gina ma rayuwana a baya wanda har tawa mutuwar tazo ba zan daina amfana da abin da tai min ba.
Shiyasa har gobe ina jin jinin ta kamar duk abinda nai masu ban masu wanda ita tai min ha sai dai na kwatanta kawai iya yina.
Don abin da yasa nakewa mai karatu wanan bayan shine tun da suka fara cecekucen su zauna nake cikin kamala da sanin ciwon kai tankar ba dani ake wanan badakalar ba.
Wanda yadda nake zaune cikin natsu ya jawo daddy mai da hankalin shi a kaina yana kallon yadda nake zaune ba abinda ya damay ni sai ma jan ajin da nake tankar ba da ni ake zancen ba.
Don ban biyewa haukan kishi nai wani dogon hayaniya yadda ya tsamaci zanyi ba da farko.
Wanan kuma zaki iya tuna training din da anty ta fara kaini na koyon zaman duniya tun farkon zuwa na wurin ta.
Banga amfanin shi ba sai yanzu da girma yazo min na san ciwon kaina nake amfani da irin darasin da na koya a wurin.
Watau mace ta zamo kamila mai jan aji da natsuwa ba ko yaushe a cikin hayaniya ba da watsar da kai.
Raliya da yake mai ilimi ce ta san duniya sai yadda na mayar dasu wasu bi can ya bata mata rai don kishin yanayi na da jan aji ya tsone mata ido.
Bata taba sanin na koma classic lady ba sai dan ganin da tai min din nan sau biyu baya dawowa na yasa ta gane cewa akwai aji sosai a gareni.
Don na waye nasan duniya na san ciwon kaina komai nawa a natse nake aiwatar dashi ba kamar sauran ba.
Take wani zafin kishina ya rufe mata zuciyar ta gashi taga akaina ake fitina amma sai waya nake kallo ina dan murmushi can na nisa nake cewa iya kar maganan ke na dama don ni zan tafi na shirya ina da theater da karfe hudu da zanyi.
Na mike tsaye daga inda nake zaune na juya gun hindatu na ce Hindatu idan kina ganin komai daddy ne ke maki a rayuwa har kike zargin haka take muna muna kina hada dan karamin banga a gida don tayar da hankalin mutane to aiki babba na gaban ki kuwa don zaki tabbata cikin wanan halin.
Ina fadin haka na juya na fara tafiya ina fadin Allah ya bamu alheri anty Zulfa don Allah ki bar bata bakin ki hakana.
Don wanan bazata taba daina halin ta na sheri ba tana tauye rayuwan ta dana wasu ni yanzu banda lokacin bata wa wurin kallon abinda wata keyi naci gaban ta.
Aiko ta shiga bakin ta don har na shiga daki na rufe tana faman surfa ruwan balain data saba yi bata ko gajiya ita da fitina shiyasa take kullun cikin bakin rai.
Sai bayan na dawo ne da dare Amira ke fada min ai dazun fada kuma ya sarke a tsakanin Raliya da Hindatu kafin ta bar gidan.
Kai Allah dai ya sauwaka ita wai bata tunanen yanzu yarta ta girma ne tana ganin abinda takeyi gashi gidan wani zata wata rana.
Aisha dake shimfide baba tace ai ihisan din ce tai mata magana shine har ta daina fitinan suka shiga daki.
Amira tace ai dai taji kunya a gaban daddy Anty tace mata kece kika fada min shiya sai motan don tun bai aure ta ba yake maku haka ya saya mata abu kuna kallo.
Nace ji sheri fa banda motan da daddy ya saya min lokacin don zuwa makaranta yaushe ya taba sai min wani abu ni kadai.
Amira tace maman kafin ta rasu ko yaushe maganan ta shine kunyar ki take ji takance gashi an zugata ta kasa fahintar ki yanzu gasu Nasir a wajen ki tankar ke kika haife su don abinda Maman ihisan take masu anan duk yaran na fada mata da yadda kike tarewa ba ki bari tai masu sheri.
Shine fa takance ita bata san may zatai maki ta wanke laifin ta ba a gareki .
Nace Allah sarki antyna ni bata da laifin komai a wurina ni abinda tai min har na mutu bazan taba saka mata shi ba a rayuwana.

********* ********* *********
Azumi yana gabatowa kowa na shirin zuwan shi munyo odan kaya sosai ni da anty Zulfa inda ta tura kano da sauran wurare don a sayar mata muna daukowa indiya da chaina.
Ranan muna cikin daki anty Zulfa muna kallon kayan da aka shigo mata dasu sai shirya kayan su Aisha da Amira da Atika ke faman yi.
Zaune nake a saman dogon kujera sai ga Jinior ya shigo yana fadin daddy yana neman mu a falo nida maman baby yadda suke kiran anty Zulfa ke nan.
Mun fito yana kishingide a saman center carpet yaran duk sun rufe shi yana biye masu suna son kwatan abu a hannun shi.
Sai Hindatu da ke zaune daga gefen shi ta hade rai da alama yaran sun damay ta ke nan da hayaniyar su da sukeyi da uban nasu.
Mun zauna tare da gaidashi sai dan wurin Zulfa hanif ya nufo uwarshi yana fadin mama baba ya sayo muna.
Tace ai ku kenan kuyi ta faman shan zaki yana biye maku kuma bai daina saya maku kullun sai dankanoma kuke fama dashi.
Dan kanoma ko lalacewa ya mai da yara kamar wasu diyan zinare can yai zaune a cikin su yana wasu abubuwan da bai dace ba dasu.
A yanzu ko naga ko a baya haka yake da yaran shi kowa yasan halin yaya a kan yaran shi sai dai in yaran na yanzu ne ba a son ya zauna ya fahince su kuma muji.
Daddy Jinior tace kana neman mu ko na fadi hakane don kada zancen su yai nisa sosai a wurin don sun dauko sake layi.
Ya gyara zaman shi tare da dago Abdul daga jikin shi ya rugumay yaron yana dan buga bayan shi a hankali yace.
Kin shirya saurarena ke nan baki biyewa wannan haukan ba don banga dalilin dan magana kadan sai an mayar dashi dogo ya zama na fitina ba ko yaushe.
Ayi hakkuri inji Zulfa tace abin hassada ne ba a raina shi a gidan nan in bashi ba yaro kuma ace ana hassada da zama da uban shi.
Idan basu mamay ka ba wazasu mama suji sanyi a ran su bayan kai da mu da suka sani nace anty abar zancen don Allah hakana.
Mun yi shiru can yace dama ina son fada maku ne ba zai muyi azumi a gidan nan ba don na samu wani wuri a cikin nan maitama ne.
Kowan mu yai tsit yana sauraren shi yace gida ne babba da kowan ku zai samu walawa a cikin sa yadda yake so.
Part na farko mutum biyu ne zasu zauna cikin sa shima dayan hakane da sauri zulfa tace har Raliya ke nan nan zata dawo da zama ita ma ?
Yace ai kinji nace kowan ku sai kunje kunga gidan ke Zulfa zaki zauna tare da Rahama a bangare guda haka ma ita hindatu da Raliya sai su zauna a dayan bangaren.
Nace yaran fa daddy ?
Yai dan murmushi yace uwar yara inda kike ai dole dake zasu zauna dayan part din yafi girma don akwai extract dakuna har biyu sai shi dan naki akwai dakin shi a kasa shima nawa dakin sama zan zauna.
Dama dai ka gama tsarawa ne ko mu fada muna kawai kakeyi yanzu inji hindatu ta fadi haka a hasale.
Shi ya bata amsa da fadin eh na tsara komai fada maku nakeyi don umurni nake bayarwa ba wai ra, ayi ba.
Shiru mukayi gaba dayan mu sai Zulfa ce tace dashi zuwa yaushe zamu koma sai yake cewa nan da sati mai zuwa insha Allahu.
Kunga kafin azumi kun dan saba da wurin ke nan Allah yakai munace tare da fadin Allah ubangiji yasa mu koma a sa, a gabadaya kowa yace amin .
Ina kokarin mikewa ne yake cewa ga wuri yayi nisa ban san yadda zakuyi da wa yan nan kayan naku ba ?
Don ba abinda zaku dauka a nan din komai na sa an saka maku a can iri daya don ban son wani korafi ya biyo baya kuma.
Zulfa tace dashi ai wanan ba matsala bane yaya ko motar company ku ba sai kasa ya kwashe muna ba zuwa kano.
Hindatu tace shine ai yace idan kun shirya su wanan baida matsala sai kowa ta fadi inda za a sauke mata nata.
Tun daga wanan ranan aka fara shirin komawa sabon gida ba wani hira sai na komawan mu can sabon wurin kowa keyi.
Ban zauna ba ni aiki ya sha min kai sosai a lokacin sai ga helen ta dawo ta girma ita ma sosai a lokacin don tunda ba karatu takeyi ba nasan ta kusa aure ke nan
A wurin Zulfa nake samun labarin wai anyi fitina dashi da Raliya tace bazata koma ba can inda take zata zauna ita.
Tace karshe ma ashe cewa yayi dole ta nemi transfer ta dawo da aikin ta nan Abuja inda kowa yake yanzu dai ban san yadda suka kare ba.
Ai bazata so ta dawo nan ba tunda can yafi mata samu nan kuwa kinga idan ta dawo dole kasa zata koma tunda akwai na gaba da ita da yawa.
Tace a dama ai galihu ne kawai irin na mutanen mu har takewa mutane sallon wai ita saura kiris takai manager yanzu.
Yanzu akai mu gani mana in kaiwa banza ne nasan dai ba karamin kwasa zasuyi ba kan hakan matar da ta saba haka take kamar faransi ba oda ina zata iya zaman gida yadda yake so.
Ni dai ina jin ta nasan koni haka akaita zagina a baya ban ma sani ba ko yanzu ai ban debe tsanmani don kishiya sunar ta kishiya ai.
Ranan Laraba da ya zagayo ya kwashi yara ya fara kaiwa shi da Sani da motocin mu da duk wanin abinda za, a bukata sai mu da bamu tafi ba mun tsaya sai an kwashe kayan kowa a gaban idon shi.
Bayan an gama ya dauke mu shida zulfa a gaba ni da hindatu muna baya sai hadiyan rai takeyi ban san may ya bata mata rai ba a lokacin tundai safe take hakana a gidan.
Gida ne babba mai kyau ga tsari shigen ginan mu na na can kano sai dai wanan din ya nuna mai aikin wayewa da akayi na zamani.
Mun shiga da addua da godewa Allah yaran ne suke nuna muna ga inda daddy yace namu ne duk komai iri daya ne har ginan wanan dai dakunan da aka kara biyu sune banbancin mu.
Amma bayan hakan komai iri daya ne kowan mu zata tashi da dakuna biyu a bangaren ta.
Abin yaiwa kowan mu dadi sosai nace Zulfa ta fara zaben inda take so sai bayan ta zaba na farkon ta dauka ni kuma na dauki wanda ke daga ciki ni yafi min sauki ma don hayaniya da ban so sosai idan ina resache.
Wata sabuwa Hindatu ce tazo tana fadin kuji min wanan tsohuwar wofi din duk sai muka waiga gunta muna kallon ta sai take cewa wai fa Raliya ke fadin ita bazata zauna part daya dani ba sai dai wai a hada ta da Rahama su zauna wuri daya watau mu tsofin mata ya hade mu wuri guda ke nan.
Kuji min tsohuwar banza mai mayar da kanta baya don Allah wai kamar Raliya ke cewa wai mune tsofin mata jifa don Allah.
Dariya zulfa tai mata tace haba haba dai ke da mutumiyar taki kuma za a ji kan ku ai bai dace ba haka ku dai sasanta kan ku acan.
Tace bari Zulfa matar nan ta bani haushi wallahi bata san ina dakin ha ta bugo mai waya tana wanan maganan.
Ai ban bari takai karshe ba nace ke tsohuwar banza wace bata san may takeyi ba wa ye tsohuwar bake ba ke ba a gujeki ba shine ke zaki guji wani.
Dariya ta bani sosai har na kasa hadewa sai da na fasa shi nace da ita amarya ce fa maman Ihisan tace kai amma dai ke amaryan may can.
Haihuwar ta hudu fa har da bari tace min wanda ma aka sani ke nan fa na boye wayasan su.
Tunda shima uban aiki bai san hakan ba sai daga baya don ta boye mai komai da farko akan zancen diyan nata.
Nace kai hudu fa kikace tace wallahi Allah ko kuma dasu zata dawo nan gidan wai da sauri Zulfa tace wani gidan ?
Tace ai sai kiyi tunda uban aikin ya yarda mu may zamuce na san dai akwai tsiya kan a gidan nan don ban yarda agola sufi min diya na.
Dariya sosai muke mata har taji haushin mu tace ai dole kuyi mun dariya tunda baku aka taba.
To maman ihisan aiko mu ba a bari ba don gidan gaba daya ne kila tsarin zaman a tare bai mata ba ta bullo ta wanan tsigar kuma.
Kuma wallahi dole ta zauna ba tunda ba fin kowa tayi ba ta zo a zauna in kasa akaci a kwaba tare a hade shi.
Zulfa ta kallo inda nake tai min signal da idon ta wai nai shiru nace yanzu dai ai gamu gani ko tunda dai namu dama idone mai daki shiyasan in da ruwa ke mai yoyo.
Ta dan jima tana ta tonon asiri har ta gaji ta koma wurin ta Amira tace wai mummy ku baku san tana da yara bane dama ?
Nace nifa ban san komai bz a kanta kin san ba ta dade ba na tafi germany shiyasa ban ma damu da nasan komai ba

Please Login or Register in order to submit comment