Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kabiru ya samo maki yar aiki da zata dinga taimaka maki da aiyukan gida sai ki samu hutawa haka wa ranki don Allah.
Murmushi nayi nace godiya nake daddyn mu sai dai tai min gyaran gida da sauran aiki amma banda girki gaskiya don ni tun a kan Saliha na sasuda da zancen yan aiki a raina.
Na kawar da zancen da cewa dashi kunyi waya da Hamza jiya ya isa lafiya ko ?
Yace wallahi ban samu kiran shi ba sai gashi shi ya kirani yana fada min ya isa da karfe goma sha daya na dare.
Nace maza dai basu damu da tafiyan dare ba su nikan ina zan iya tafiya a cikin dare haka na ?
Yace antyn ki ma ta kirani dazun da yamman nan ina hanya nace Allah sarki suna lafiya ko nayi kewan su Nasir wallahi jiya jiyan nan.
Yace suma ai dole suyi kewan ku anty ki dai ce ke fadan da ta saba dani wai may nake nufi da tafiyan dana shirya maki ?
Da sauri na dago ina kalon shi don son jin amsan daya bata din?
Yace nace da ita ai ba wurina kika zo aikin ki ya kawo ki kai Zulfa ce dai ma nake ganin batai min wani korafi ba akan hakan sosai don ta basar da maganan ita.
Nace a sanyaye nima ta kirani tai min korafi wai nazo da Aisha da Atika ban fada mata zanzo dasu ba.
Yace to may take nufi da ba za, a zo dasu ba watake son ya kama maki yaron ko idan an barsu a can duba maki su zatayi ?
Nace sai hakkuri alamari amma ai yanzu da sauki don ta rage wani abin ai yana tafiya yace kadama ta rage ita zai dama ai.
Yace ni zan karasa masallaci can kasa kada a fara sallah badani ba don wurin akwai nisa da nan kadan nai mashi adawo lafiya ya fice.
Na kwalawa Aisha kira ta amsa tafito dauke da baba a hannun ta nace don Allah aje wanan sarkin kiuyan ki sa muna turaren wuta kamshi ya dauki gidan.
Daga haka na wuce zuwa dakin dana gyara a matsayin nawa na fara shirin yin sallah don lokaci ya gaba to sosai na magariba.

********* ********* *********
Ranan monday na shirya zuwa camp ban tafi da baba maigidan ne ma da kan shi ya sauke ni inda na samu har dalibai ire iren mu sun fara taruwa a wurin sosai.
Bai tafi ba sai da yai min komai ya tabbatar banda matsala yai min sallama ya tafi yake cewa idan na gama na kirashi yazo ya dauke ni tunda ban san gari ba anan.
Har yamma muna wurin muna tashi na kira daddy don na samu ni har angama min komai nawa yanzu posting zan jira fitowan shi.
Daddy ya iso muka kama hanya sai gida a yadda nai tunanen zan samu yaron ya jigaita sai na samay shi hankali a kwance don dama ya saba da su Aisha ko ga madara da idan yai kuka zata bashi yasha.
Nima ranan nagaji sosai ban tsaya ba nafara tafiya ne naji Aisha tace dani Anty an fa kawo yar aikin dazun da kika fita.
Da sauri na juyo nace da ita tou har an kawo ta tana ina tace tana dakin mu tare da Atika nace bari nai wanka idan nai sallah sai na fito mu gaisa da ita.
Na shige ban zauna ba na fada ban daki na watsa ruwa a jikina ina fitowa wanka ne waya na ya dauki kara na karasa da sauri na dauka kada ya tsunke.
Gajiye ce ke kirana a lokacin don haka nai murmushi muka shiga gaisawa na tambaye ta mijin ta tace dani yana lafiya tace wallahi hajiya gidan sai ya koma ba dadi da baku nan .
Kun tafi kun barni ni kadai sai matan gidan masu ji da kan su babu dadi wallahi hajiya.
Nace kai Gajiye baga anty nan ba ki dinga shiga kuna dan gaisawa mana ai zaki ji dan saukin kadaicin naki.
Tace wa ni hajiya don Allah rufa min asiri matar dake zargina may zan mata nayi fari a gurin ta ko ke ai hakkurin ki ne yasa kuke tare har yanzu.
Nace to yaya zanyi Gajiye ai binta ya zama min dole kada nazama butulu gareta nice fa mai laifi ni da na aure mata mijin ta yanzu.
Kinga kuwa ai ba zan yarda ace a kaina aka samu matsala ba haka da ita sai dai tai tayi wata rana zata gane gaskiya da kan ta.
Tace humm hajiya Rahama jiya fa bayan tafiyan ku bakiga haukan da akasha gidan nan ba malam musa da kanshi ke fada min yaga anata gungu gungu a gidan yasan kuma akan tafiyan naki ne.
Nace ai yanzu kan su ake ji ni kan Allah yai min gyadan dogo na samu na dan tsere na kwana biyu sai suci kan su kuma yanzu ai.
Mun dan dauki lokaci muna hira bayan mun gama na kashe wayan ne na tayar da sallah don nasan an fara sallah a wani wurin don yanayin sallah garin ba daya ba da namu can kano.
Sai da nagama komai nafito falo jin nafito sai ga su Aisha da Atika da yar aikin mu ashe yarinyar gwari ce yar budurwa zata kai Aisha ko ta girmayta sai dai gajera ne ba a gane shekarun ta sosai.
Ta zube kasa tana gaida ni na amsa mata tare da tambayan ta anzo lafiya tace lafiya ma nace yaya sunan ki tace Helen take amma ana kiran ta da Lami ne nace yayi.
Nace da ita don Allah ina son ki rike ni amana kamar yadda muma zamu zauna dake amana anan tace yes ma.
Nace aikin ki a nan shine zaki dinga muna shara da wanke wanke da sauran yan aiyuka amma banda girki tace ok ma nagode.
Nan dai tana batin wurin daddy ya dawo daga masallaci ya zauna anan falo inda ya samay ni a zaune.
Yana cewa na dauko mai system din shi a daki na mike naje na dauko mai na kawo mai na samu ya zauna a gaban abinci zai fara cin don mun shirya maikomai dama.
Kai a gaskiya sai ince dole ne wasu mata suke kishi don zama da miji ke kadai akwai dadi don ban san haka ba sai yanzu da muke zaune daga ni sai daddy da yarana kawai sai yadda naso dashi ya koma mun kamar wani narkake dashi sai yadda nake so a gidan .
Ai ko ba komai dai na morewa rayuwana na kwana biyu ga hakan kafin na koma ga turke na mai cabo cikin zama da kishiyoyi.
Ranan muna zaune da dare baba yana gefen shi yana aiki sai ga wayan shi na ringin sai kusan zai katse ne ya dauka ashe hindatu ce takirashi.
Jin muryan yaron dake wasa mai kama da kuka a kusa dashi yasa tana daukan waya tace dashi indai cutane ai sai ka matsa don cin amana mu ba aje damu ba sai a dauki wace ake ganin tafi mu daraja don son kai kawai.
You are very stupid yace da ita abinda ya jawo hankalin mu ke nan na dago kai da sauri ina kallon shi yace don rashin mutunci sai ki kira wayana kina min maganan banza don rashin hankali nazo da ita ke ma ai sai kizo din mara hankali kawai.
Ido na tsura mai dana fahinci da wata daga cikin matan shine yake waya sai na kawar da kaina gefe daya ina duba tv dake aiki a falon.
Ya gama yaja tsuki bai min magana ba nima ban yi ba nasan dai maganan dayace bai wuce akaina ake mai korafi ba don jin abinda ya fadi.
Satin mu biyu daddy ya shirya ya tafi kano ranan da ya sauka sai da akai fitina tsakanin Zulfa da hindatu kan rabon abinda yaje dashi.
Itako anty na dama jiran shi take da ta karbi girki ba komai tai magana a kan shi ba sai zance na data nuna bacin ran ta akan dauke ni da yayi ya tafi dani Abuja da sunan wai na tafi aiki .
Ranan dai sunyi ba dadi inda yace da ita yanzu ke bakiji kunya ba ace wai ke , ke wanan korafin don rashin godiyan Allah gareki.
Tace may ye na rashin godiyan Allah din ga haka kishiya fa ka dauka kake tare da ita ka bari a nan wai ni tsuhuwa ko may kake nufi dayin hakan ?
Nasan da yardan ka don ka cuta min ka bata kwarin gwiwan zuwa Abuja don yin bautar kasa may nene ba ayi a kano da akeyin shi a Abuja kawai.
Yace ke Saade na kaishi din sai may kema tunda Rahama ta tafi kema sai ki shirya aiki tafi ko tunda ta zama maki abin gasa yanzu.
Nan dai ya mata kaca kaca kin san halin maza akan abinda suke so ba a taba gane kan su sai su borewa mutum.
Ba anty kadai ba kusan kowa yai mai wanan korafin dan tafiya na Abuja yace suma sai su shirya suje bautar kasan sai a zauna lafiya .
Ita Zulfa diploma tayi ita ko hindatu NCE ne da ita ta tsaya a nan sai anty da tare sukai bautan kasan su dashi a lokaci daya.
Wanan borewan da yayi dole sukai shiru da zancen amma yasha kara agun magabata amsa daya yake basu shi bautar kasa Rahama taje yi a can dole sai ai shiru ba bakin magana kuma don kowa yasan da bautar kasan da akeyi.
Kwanan shi goma sha biyu ya dawo garin inda ya samu na shiryawa dawowan nashi kamar zan tari wani bako ta ko ina na shirya mai.
Ranan kamar ba gun wasu matan daddy yafito ba cab don bamu ragawa junan mu ba sai da muka bar juna don kan mu waahegari ma bai barni ba sai daya debi rabon shi a gare ni.
Na hada mai break fast mai dadi yaci ya fita ban fito ba na kwanta don akwai gajiya sosai a tare dani sai sha biyu da rabi na falka nai wanka na shirya na fiti falo ko ina tsab helen ta gyara shi ba wani makusa a gidan.
Bayan na karya ne nace Atika ta dauki min waya na ina budewa naga sakon da aka turo min na posting din mu da akayi.
Inda aka turani babban asibitin dake garin Abuja don aiki dasu naji dadi sosai da gakan don nasan zan karu sosai ga wanan ci gaban dana samu.
Da murna na kira daddy ina fada mashi inda aka turani bautar kasan abinda ban sani ba daddy ne ashe ya shiga yafita na samu aka turani wurin.
Jin yadda nake farin ciki bayan mun gama wayan ya kalli wayan nashi yai murmushi yace Allah sarki waban yarinyar akwai sauran kurciya a kanta dai har yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA, A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , , ,
69
Bayan komai nawa na bautan kasan ya kammala nagama daga MBBS zuwa housemanship dina wanda komai a cikin gata akai min shi shine sai kuma ga posting ya biyo baya inda aka tura ne asibiti gashi kuma maigidan ya matukar tausaya min ga hakan.
Don yasan ba wani gata ke gare ni ba ta ko ina iyayyena basu tare a guri daya ban tare da mahaifina haka ma yan uwan haihuwa na muke da su.
Matar da nake jin sauki a gunta ta dauke ni kamar kowa nawa yanzu kishi yasa mun raba hannun riga da ita .
Ya zama wajibi ya tallafawa rayuwan wanan yarinyar don sun tauye ta shida Saade a rayuwan ta.
Ni kaina na san an an min gata don sai jefi jefi nake fita zuwa camp a lokacin don execuse a wurin dake nuna ni matar aure ce mai karamin goyo tare dani.
Komai yanzu idan akwai kudi zai sai wa mutum gata a wurin jama, a don ni kaina na san an gwada min galihu so sai a wanan fannin.
Mun yi waya da Zarah take fada min suma sun gama har anyi posting fin su ko tana a cikin kano bata fita ba.
Bayan mun dan taba hira na dan bata labarin sabon rayuwan da nake ciki tai dariya tace ai maza sun fi mu wayo Rahama gaskiya daddy yana son ki sosai tunda har yai maki wanan hanyan.
Yanzu matsala zai dinga shigo maku sai kiyi ta hakkuri kada ki yarda a shiga tsakanin ku don korafi zai mai yawa idan kuma ke a fannin ki bai samun kwanciyan hankali ba abin mamaki bane kiga canji daga gare shi don mace shuumace.
Nace haka dai Inna ta take fada min kullun mukai waya insha Allahu zan zamo mai hakkuri da juriya daga duk wani kalubalin da zan gani a zama nan tare da shi.
Mun gama waya dashi na kira anty nake fada mata mun gama zaman camp har an yi posting din mu ko.
Banji tai min wani farincikin hakan ba nima dama ban yi tsan manin hakan ba a wurin ta don ba sabon abu bane gare ta.
Sai dai rashi na a gidan ta fara shiga wani hali sai take ganin ashe ba karamin amfani zamana yake mata ba a gidan don gashi dan rashi na da tayi na kwana biyu abubuwa na son jagule mata ko ta fanin yara abin yana son yafi karfin ta yanzu.
Gashi idan ba yar aikin ta ta dan samu zama da ita ba babu wanda zatai magana dashi haka zata wuni zur ita kadai a part din yara suna makaranta.
Sai yanzu ta san ba karamin rana Rahama take dashi ba a gurin ta bata kara tabbatar da hakan ba sai ranan da ta wuni ba lafiya duk gidan ba wanda yazo gaida ita haka ta wuni zur a kwance ita kadai don mai aikin ta irin matan nan ne masu kama da doleye sai dai ta wuni tana aiki ba magana .
Gajiye dai kan shigo su gaisa da safe daga haka kuma sai wani safiyan idan ta shigo gashi ita kanta ba dadin girkin mai aikin take ji ba da nake gari ne wani lokaci idan yaran sunce suna son cin abu kaza zatace kuje ku fadawa little mum tai maku.
Yanzu ko little mum tayi nisa dasu yaran sun dawo daga school Amira ta dawo da ciwon kai haka ta samu uwar ba lafiya babu mai kama wani tun yarinyar na ciwon kai har ta koma mata maleria ta rasa yarda zatayi ta tura Nasir ya kira Gajiye ya samu wai Gajiye bata nan ta fita unguwa.
Abu ya taru yai mata yawa gata a kwance ita babu moriya nan ta tuna halaiya irin na Rahama da ace tana nan ne yau suke haka ita da yarta da yanzu tana nan tana fadi tashi a kan su sannu yana zuwa yana dawowa garesu da kulawa yadda ya dace a kan su.
Rahama ko batace ba idan taga abinda ya dace ita da kan ta zatayi mata shi batare da ta sani ba za, a aikata shi.
Yanzu ne tasan ta rabu da wani babban bangare na rayunwanta yarinya mai matukar alheri a gareta da taimakawa ko sau daya bata taba nufinta da sherin da ada take ganin kamar abinda take mata da wani manufa take mata shi.
Son kai kawai yasa ta ta tsani yar mutanen da tasan kimarta da darajan ta, sam Rahama bata gajiya da kyautata mata dan bata taba gajiya da laluran ta dana yaran ta akanta.
Abinda taiwa Rahama kan graduation din yaran ta ne ya fado mata a rai ta sani sarai Rahama zata iya masu fiye da abinda tai masu a lokacin in har tana dashi amma ta rufe ido saboda tasha zuga tai mata cin mutunci.
Hakan da tayi bai hana taci gaba da kyautata mata ba da yaran ta amma ita da guda daya da Allah yabawa Rahama a gidan taki jinin ta bude ido taga yaton a idon ta tana jin haushi da takaicin yaron kamar ta shake shi.
Tun tana yi a boye har ta bari yarinyar ta fahinci hakan da takewa gudan jinin ta duk abinda take gwadawa yaron bai hana yarinyar taci gaba da so nata diyan ba tsakani da Allah.
Ta gyara kwanciyar ta wasu hawaye masu dumi suka biyo idon ta tace ni Saade wai yaushe na koma haka ne Allah ina rokon ka daka rage min wanan zafin kishin haka a raina.
Ta lumshe idanuwan ta kalamin Rahama ne ke dawo mata a rai da take cewa ba zantaba cutan ki ba anty a rayuwa idan ban soki ba bazan ki ba ko wanii naki don kece silar farin cikina a yau.
Amma sai take ganin a lokacin dadin baki ne irin na yaudara kawai take mata baya ta gama cuta mata mijinta da take matukar so yau yana kokarin nuna ma duniya akwai mazauni Rahama a zuciyar shi.
Yau gashi da ranta tana ji tana gani daga karshe Rahama ta barta kuma tana can tare da mijin zaman ta lafiya ta barsu nan suci kansu a tsakanin su.
Yau da Rahama tana gari da yanzu daga ita har yarinyar sun san abin yi ko gashi bata da wani dabara a hakan.
Idan bako tayi da zaran Rahama ta sani ta shiga da wainiya da shi ke nan har sai ya wuce idan babba ne zata saya mai sunan shi kaikoma saan tane zata girmama duk wanda yazo gareta ta dauke shi kuma da mutunci.
Amma yanzu da bata nan ranan ma da tai baki Hindatu na ganin su tai kamar zata buge su da mota tazo ta wuce su kamar bata gan su ba ma tayi tashige abinta.
Nan take ta tuna da daddin Rahama a gareta tace da Rahama ce da murna zata tare su tana haba haba dasu tana farin ciki da zuwan su harsu tafi.
Tana cikin wanan tunanen ne abin ikon Allah taji wayan ta na ringing har ya katse bata iya dagawa ba can kuma kira ya kara shigo mata da kyat ta iya daukan wayan sunan Rahama tagani a screen din wayan yanuna mata da Rama.
Ta dauka cikin dauri jin Sallaman ta kawai mun fara gaisawa na katse da cewa anty may ya faru baki jin dadi ne ta dan kakaro murmushi da kyat tace hakane Rama.
Nace subbahanallahi kin ko sha magani tace nasha sai dai bai barni ba ciwon har yanzu, ya salam nace anty kije asibiti mana a dubaki .
Tace dare ya somayi Rama nace haba anty ina Nasir abashi waya muyi magana dashi tace yafita baidawo ba.
Nace bani Amira anty, tace wallahi tunda yamma ta dawo ba lafiya ita ma tana can kwance jiki ya gashe mata hankali yai matukar tashi nace anty shine kuke zaune a gida haka.
Kashe wayan nayi take na kira wayan Hamza na fada mai cikin tashin hankali da ya je gida ya dauki anty da Amira zuwa asibiti don Allah.
Bai bata lokaci ba ya isa gidan da shiga ya nufi wurinta inda ya fada mata nice na turo shi ya kaita asibiti.
Bataki ta shirya ita da yarinyar suka tafi asibiti inda likita yai mata fada may yasa tabar Amira har jikin yai mata nisa haka ?
Nan dai akai masu allurai da magani da ita da yar Hamza ya dawo dasu gida mai gidan bai nan yai tafiya kasar Sudan a lokaci wayan shi kuma baya shiga.
Ina sallah ishai ya bugo waya gaisawa kawai mukayi nake fada mai zancen rashin lafiyan anty amma sunje asibiti an basu magani sun sha.
Nan nake fada mashi cewa harda Amira bata da lafiya yace bari ya kirata yaji yanzu mukai sallama ya kashe wayan .
Tana kwance ya kira layin ta sun gaisa yake cewa yanzu Rahama ke fada min keda Amira duk ba lafiya to yaya jikin tace Alhamdullahi mun samu lafiya Rahama ta turo hamza ya kaimu asibiti ai.
Yace yanzu ke idan da batai wanan dabaran ba haka zaku zauna da ciwo a gida yana cin ku sai yai nisa kuma ki sa mutane a wani hali.
Fada yayi sosai bata dai ce dashi komai ba yai mata Allah kar lafiya sukai sallama ya kashe wayan tai tsuki tana cewa kaman ya damu da mutane yanzu.
Kafin ya kira ai saida ya fara kiranta nasan shine take fada mai bamu da lafiya ya bugo min yanzu yana wani fadan karya haka.
Ban kwanta ba sai da nai mata yaya jikin da Allah ya bata lafiya mukai sallama na kashe wayan tana mai bani tausayi a raina.
Da safe ma tun da na idar da sallah na kirata muka gaisa na tambaye ta jikin ta tace taji sauki harta samu barci jiya sosai.
Nace a bani Amira don Allah mu gaisa sai da aka dauki lokaci duk wayan na a kunne aka kaiwa Amira nai mata yaya jikin tace da sauki nace ta karya da wuri tasha magani.
Ta dai amsa min kamar bata so ban damu ba nai mata Allah kara sauki nace ta gaida yan uwan ta tace zasu ji.
Haka na wuni akai akai ina mata ya jikin har dai nagane kamar tagaji da jina na daina kiran nata hakana tunda ta samu lafiya yanzu.

********* ********* *********
Muna zaune a falo gaba dayan mu har helen da kan zauna a tare damu idan ta gama aikin ta don ban matsa mata kada na zo na cutawa yar mutane gata ko banza ba musulma bace.
Karatu muke da Atika da ke assignment din ta don ta fara karatu yanzu har Aisha takan je wurin daukan lesson idan ina up.
Mamakin yadda yarinyar take da saurin daukan karatu nake gashi dai daga sama ta fara amma tana iya hada kalmomi yanzu da kan ta.
Sai nake gani da yanzu tana kauye a haka wanan basiran nata zai tafi ga banza bata amfana dashi ba sai tallan koko kawai da uwayen su ke sanaan yi kullun safe.
Wanda saura yan uwan su shi suke yi yanzu a kauyen babu karatu a tare dasu wanda ko a dakin su ne zai amfane su nan gaba.
Rokon Allah nake a zuciya na akan zurian da Allah zai bani nan gaba su ma Allah ya basu hazaka akan karatu na addini dana bokon baki daya.
Mun gama sai muka dan shiga hiran dasu Aisha da helen keyi wai sun fita sun ga wata mace ta raba sadaka da kan ta a hanya kuma kudi yan dubu take bayarwa.
Nace injin dai baku tsaya karba ba don kun san yanzu duniya ta baci zakkaga mutum da fuska kamar na Annabi ne shi amma yana da wata manufa a tare dashi a zuciyar shi.
Sallaman daddy ne mukaji a tsakiyan falon bai fada min zai dawo ba a ranan sai fanin shi mukayi kawai ya dawo a ranan a kuma wanan lokacin.


Please Login or Register in order to submit comment