Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga hakan don haka nake son natsuwa da hakkuri a tare da ke.
Kaina ya kara daurewa tunane ya gagareni don ban san wani mumunan kaddara take shirin sheda min ba yanzu.
Sai kallon ta nake don magana take min mai kama da nasiha kuma da zuciya daya take maganan nata.
Kallon tayi tare da kiran sunana na dago kaina muka hada ido cikin murmushi tace Rama yau an daura maki aure da daddy akan sadaki dubu dari sauran bayani zakiji shi daga baya a gurina.
Da kyat na iya bude bakina danaji harshena yai mugun nauyi tare da juyawan da kaina keyi a lokaci guda.
Da kyat furucin da ke son fito min a bakina ya fito a lokacin nace nace haba haba anty wanan irin wasan bai dace ba tsakani dake don Allah anty ki daina wanan wasan haka please.
Anty wani irin wasa ne haka ke da bakinki zaki bude kimin wanan wasan da da wani yai min shi yau bake ba mairabani dashi wallahi sai Allah.
Daddy ubana yayana mai kula da duk wani damuwa na da lalurama kun rike ni tankar yarda kuka haifa da cikin ku har zakiyi min wanan bakin wasan da wani ido zan iya kallon ki a duniya duk da wasa ne irin maki anty.
Idanuwan ta suka ciki da kwallah ta matso daga inda take zaune tare da kamo hannuwa na ta hada cikin nata tana cewa dani babu wasa ga magana na Rama.
Ni nan da kike gani nina yarda da hakan kuma na shirya komai yadda za ai nasara .
Nasan komai mukkaddarine kawai tofa yawuna, nayi kawai a cikin maganan don tani Allah ya nufa zancen zai fito.
Don tunda kikafa haka Allah ya nufa tun fil,azal da akwai aure a tsakanin ku kin ga ba wani mahalunkin da ya isa ya hana yuyuwan hakan a tsakanin ku don nufin Allah ba wanda ya isa yace a, a acikin sa.
Ni banda abinda zance sai dai na godewa Allah da bai doro min gardama ko hassada akan hakan ba.
Don zai yuyu maganan tazo min ta bazata na tayar da hankalina akai na nuna rashin amincewa na rabo da hakki yazo ya kawar dani kamar yadda ake fadin rabo na kashewa kuma yana rayawa don alkawarin Allah baya taba tashi akan abu.
Rama kada kiyi zato ko tsanmani bani kishin mijina ne wallahi ina son Yusuf kuma ina kishin shi to amma shi kishi aikin banza ne.
In kinga ana kishi na hauka akan abu to babu kwanciyan hankaline da adalci a tsakani .
Ni ina son mijina ina kuma son kwanciyan hankalin shi duk wani tuntiya da zanyi akan yusuf idan baida walwala ko kwanciyan hankali a tare dashi aikin banza ne gare ni.
Da yaje ya dauko wata can wacce bamu san ta ba bamu san halinda zata zo muna dashi ba ai gara ke dana sani kika san mu zauna tare har mai rabawa ya raba mu.
Hawayene fal ya cika min fuskana wanda ko gurjin kuka na kasa fasawa a lokacin don na fahinci iya gaskiyan ta take fada min yanzu.
Rugumay ni tayi zuwa jikina ta itama kukan take yi ina cewa why why anty zakuyi min haka?
Anty wanan shine son da kike tunkahon kina min ko shine kaunar da kike nuna min ko yaushe akaina.
Rama ki daure ki fahince ni ban yi haka da nufin kuntata maki ba ko rashin son ki nayi hakane don jin dadin rayuwan ki danamu baki daya.
Kuka nake sosai wanda har ya jawo hankalin Gajiye gare mu lalashin duniyan nan da ban baki anty da gajiye sunyi min na saurare su amma nakasa yin shiru sai .
Itama kukan ne ya kubce mata har Gajiye din dake bamu hakkuri duk da bata san may ke faruwa ba a lokacin.
Mikewa nayi kafafuwana basu daukana na nufi dakin mu takawa nakeyi amma ba wai ina gane ida nake tafiya bane sosai.
Ban karasa kaiwa bakin gado ba idona naji ya rufe a gurin na yanke jiki na fadi somamiya dani ba motsi Allah yasa Gajiye ta biyo bayana tana ganin haka ta yanka ihu da karfi shiyasa anty fitowa dakin ta da gudu.
Yadda ta samay ni ya tayar mata da hankali ruwa tasa gajiye ta debo mai sanyi suka zuba min ina bude ido na ganni saman jikin ta na bude baki zanyi magana sai kuma na kara somay wa karo na biyu wanan karon kan na dade ban farfado ba daga suman danayi.
Daddy ne ya shigo part din guriin ta ya samau su a cikin tashin hankali haka duk ta rude sai kuka takeyi tana fadin don Allah Rahama ki tashi kada ki mutu ki barni da dawainiya a duniya.
Ranshi bace bayan ya dade tsaye akaina ya kallon yadda nake yace da ita dama batasan da zancen ba ke nan komay ?
Tace cikin kuka bata sani ba shiya yanzu na fada mata cikin hikima don ta fahince ni ba sai taji ga wani ba.
Tsaki yaja tare da juyawa don shima zuwa yanzu yanajin zuciyar shi kamar zai tsage daga jikin shi ya fito da wani zaiji fitan da ta dauko mashi ko halin da yar mutane ke ciki.
Nan ya daga waya ya kira likitan shi yazo da gagawa yana da mara lafiya a gidan shi.
Sai gurin karfe hudu na samu dan natsuwa likitan yace a barni na samu hutu sosai.
Haka yasa anty tasa gajiye ta kamani zuwa dakin ta ta kwantar dani a saman gadon ta.
Falon shi ya koma bayan likitan da Bashir sun tafi a gajiye yake don haka ya shiga falon tare da rage nauyin babban rigar dake a jikin shi yana kokatin cirewa Zulfa ta shigo falon a hargitse take lokacin.
Kallo daya yai mata ya kawar da kan shi a gare ta don shirye yake ga duk wanda ya tare da magana a lokacin.
Tace bayan ta zauna yanzu nake jin wani magana wanda ban ma tsaya karasa sauraren shi ba na nufo nan.
Kafin ya bata amsa saiga hindatu itama ta shigo cikin tashin hankali yanayinya kawai zaka kallaka fahince ta da kyau.
Kallon ta yayi ya mayar da kan shi ga masangalin kijeran da yake zaune tare da karkada kafan shi a hankali idanuwan shi a lumshe.
Baba husna may naji labari a yanzu wai kayi aure naji ko may auren kuma wacece wanan karuwan da ka kwaso muna gidan nan .
Wallahi koma wacece tayi ganganci shigowa gidan nan cikin mu don in tana takama ita karuwa ce ta iya kwatan zuciyar mazan mutane takai karshe wallahi don sai zaman gidan nan ya mata zafi wallahi.
Magana take cikin zafin rai bata san cewa har ya mike ba sai saukan marin da ya gigita ne taji akan fuskan ta kawai.
Dafe gurin tayi tare da mai kallo cikin mamaki nunata yayi da yatsar hannun shi yana cewa fice min daga falo mara hankali kawai.
A gabana zaki kira diyar mutane kuma matata da sunan karuwa don bakin kishin ki duk waya kaini ga wanan abin bake ba ina wanan maganan yafito ba a bakin ki ba.
Aure nayi ba wai kuka ji ba na yi aure yau din nan kuma ba wata bace na aura sai Rahama dake gidan nan zaune tare da ku ita na aura don ku sani.
Lokaci daya suke hada baki gurin fadin Rahama Rahama dai Rahaman Saade kake nufi ko wa ?
Yace akwai wata Rahama a gidan nan bayan ita ne da kuka sani a gidan nan zaune tare da mu ?
Shewa Zulfa ta sa tare da tafa hannun tace yau gaskiya yayi halinsa zargi ya kare kafito fili ka nunawa duniya zargin da ake maku.
Yace cikin bacin rai kinga yau zargi ai ya kare ko tunda ta zama matata kuma amarya na.
Lalai Saade takai makira a gidan nan ko da yake ita cikin ta yayi ai idan tana ganin takawo ta cikin mune sai data gama karanta halayen mu kaf sannan ta aura maka ita a matsayin mata kuma kishiyan mu.
Look duk wacce ke son kanta da lafiya agidan nan ta rufawa kanta asiri ta fice min daga falo idan ba haka ba rayuka zai baci yanzu wallahi.
Fuskan shi babu alaman sauki ko wasa a cikin sa haka yasa kowan su tafice tana yaba magana cikin kishi da bakar tsana zuwa gare mu.
Suna fita yabi bayan su da harara tare da jan tsuki ya dafe kan shi dake sara mai a ranshi yace wanan masifa da may yai kama ne wai ?
Kafin wani lokaci labarin auren yabi yan uwa da abokan arziki kowa yaji.
Gadan su daddy kuwa hajiya kamar zatayi haula don fitina sai Allah ya isa take ja wa Saadatu da mahaifinta.
Saida Alhaji yaji abin yai yawa ne ya sa mata waigi ta hayan daka mata tsawa tare da cewa idan ya kajin tai magana akan wanan aure ko ta tayarwa daddy da hankali sai tabar maigidan shi.
Alhaji akan auren wanan yarinyar yau har zaka bude baki kace na barma gidan ka ?
Yace isan baki bargidan ba ma kikace zaki yiwa Allah isgili kan abinda ya tsara sai rabo ya kashe ki.
Jikin ta yai matukar sanyi sosai don dama ta zugu tahau akan lalai sai ta sa dan ta ya datse wanan aure don bata ga amfanin shi ba ita.
Gida ya cika da yan uwan Zulfa da hindatu sai shige da fice sukeyi duk da daren yayi a lokacin.
Sin zugu iya zuguwa don jaka suka dauki shawaran sai sun kuntata min a cikin gidan nan ta yadda sai na raina kaina nayi dana sanin shiga rayuwan su danayi.
Don cewa sukayi wai asirine naiwa daddy na fitar mai da hankalinshi gareshi har ya aure ni.
Ni dai ina kwance alluran barcin da likita yai min yasani yin barci mai nauyi har ban inda nake ba a lokacin.
Anty na dakin sai faman zuwa take tana dubawa ko ina motsi a lokacin amma ban falka ba har zuwa dare.
Sai can cikin dare na falka ina falkawa na mike zaune tare da bin dakin da kallo ta ko ina.
A hankali na mike zuwa ban daki sai ga ta tashigo dakin take cewa Rama kin falka ke nan sannu yaya jikin naki ?
Dakyat na iya bude bakina da naji yai min nauyi da kuma daci nace Alhamdullahi.
Ina zaki nace alwala zan yi anty tace tozaki iya ko na taimaka maki ne ?
Nace zan iya a takaice na bata amsa na shige ban dakin can na zauna na darji kuka na nafito na ta da sallah.
Na idar kuma na shiga sabon kuka a wurin anty da Gajiye ne a kaina suka shiga bani baki cikin lalashi da nasiha.
Nan na dunkule tana cewa na tashi na haugado nace nan ma yayi min ai.
Haka muka kwana hankali tashe bazan iya cewa ranan akwai wanda yai barcin dadi ba in ka debe yaran gidan.
Washe gari duk da banjin dadi kamar yadda na saba na tashi na hadawa yara abin karyawan su tare da yin duk wani aikin dana saba yi duk safe.
Ina gamawa na koma dakin mu na dunkule na shiga rera kukan da ya zama min no control yanzu a idona.
Nasir yana falkawa yazo inda nake kwance ya dunkule a bayana gashi wani irin matsanacin zazzabi nake jin yana damuna da ciwon kai mai tsanani ban ko iya kwakwaran motsi don wahala.
Da kyat hakana na daure na tashi naiwa yaran wanka na shirya su sai dai ranan ban iya tsayawa na sallamay su ba yadda na saba yi masu kullun.
Anty ce ke tambayan gajiye ko ina kwance tace na dai tashi nayi aiki ina can kuma na kwanta .
Tace cikin zaro ido yanzu duk yadda Rama ta kwana a wahalce saida kuma tayi aiki da safen nan.
Gajiye tace nace ta bari takine hajiya sai da tayi yanzu kuma tana kwance don yau yaran ma sunga daban a gidan ta kasa kaisu bakin mota.
Tea ta hada mai kauri ta aje falo can kuryan daki ina dunkule ta samay ni ta tayar dani nazo na karya zan yi magana tace dani ban son musu fa.
Nafito na zauna a kasa tare da dunkule kafana guri daya na tsurawa shayin ido kawai tace dauki mana kisha Rama.
Na dauka na kurba kada n naji shi kamar ruwan magani yadda bakina yake komai bana son sha a lokacin.
Mama Altine ce ta shigo gida da ganin ta zakasan ba cikin hankalinta take ba a lokacin .
Mutum zai dauka ko a kano ta kwana don uban samakon da ta bugo nayi mamakin inda ta samu abin hawa haka dasafe ta bugo wanan uban sammakon haka.
Sannu da zuwa muke mata fuskanta a daure tamau dashi babu walwala a cikin sa.
Inda nake zaune a takure gaban anty ta watsa min harara tsana ne karara a idon ta da take min.
Take na soke kaina a kasa sai hawaye shar ya zubo min kaina a duke a kasa na kasa dago ido na kalle ta murya a raunane nace da ita mama sannu da zuwa.
Ta amsa min ciki ciki ba yadda muka saba ba da ita da take jina kamar itace ta haife ni a baya.
Anty ta shiga taron ta cikin nuna jin dadi da ganin ta tare da tambayan ta mama anan kika kwana ne ko kuwa ?
Tace agida na dai na kwana da yake na kwana da shirin tafiyan ne na bugo sammako mashin aka dauko ni dashi har zuwa bakin titi.
Sai lokacin nadago kaina na kalle ta nake mamakin jin wai mashin ta hawo zuwa bakin titi daga kauyen mu da wanan safiyan haka.
Ina naga sukunin zama wanan wanan mara amanan ta sakani a damuwa yadda naga dare jiya haka naga safiya ban iya runtsawa ba wallahi.
Wanan tashin hankalin da may yai kama Saade may kuke shiryawa ne haka ba tunane a cikin sa keda mijin ki da wanan ja,irar yarinyar.
Mikewa nayi zuwa dakin tabini da harara tana cewa Albasa baiyi halin ruwa ba wallahi yarinya a sakaki innuwa kice zaki kai mutum rana ke.
Haba haba mama damay yarinyar nan zataji bafa laifin Rama bane wanan maganan yadda kikaji maganan haka taji shi wallahi.
Asalima ke kin riga ta ma jin maganan don ita sai baya anyi angama nake sanar da ita.
Tun jiya a birkice take muna na rasa gane kan ta gaba daya taki kwantar da hankalinta tafahince ni.
May zata fahinta bayan tariga ta san tsiyan da ta shugawa mutane ni yanzu da wani ido zan kalli mutane dashi sai ta fashe da wani irin kuka.
Mama don Allah ki kwantar da hankali ki, ki fahince ni, may zan fahinta Saade anan mun dauko tsintarciyar mage mun saka ajikin mu.
Yau Ramane za, ace wai kishiyar ki a gidan nan komay ban taba tunanen yariyar zatayi muna wanan irin yankan kaunar ba.
Irin aibanta ni da mama yau takeyi har tana kokarin hadawa da iyayyena yasa naji duk duniyan baki daya ya kara min kunci a raina.
Mama don Allah kibar zagin yarinyar nan ni na bada wanan shawaran saboda ina da hujjan yin hakan danay ga baki dayan mu gidan nan.
Salati mama ta saka tace kina da hankali kuwa Saade yanzu har ki kalli idona kice da hannun ki da bakin ki kika saka ai maki kishiya.
Wa yan nan ma da kuke tare dasu yaya kuka iya da juna balle ki kara daukowa kanki wani sabon wahala kuma ?
Mama Rama insha Allahu alheri ne a gare mu ba yadda kike tunane bane da yardan ubangiji.
Mama tace ita kishiyar kikewa wanan shedan haka Saade yaufa duk wani so da kauna dake tsakanin ku ya koma kiyayya ke nan tunda kun zama kishiyoyin junan ku kuma.
Saade ni har mamaki kike bani wallahi waiko banza yarinyar nan tabar ki kin fasan mutum yanzu abin tsoro ne.
Mama wallahi ba abinda Rama tai min yadda kike tunane nice dai naga dacewan hakan na bada goyon bayan ayi din.
Daga daki nace a raina lalai duniya da ban mamaki yake ni wani irin so anty ke min haka har yakai takai ga hadani da mijin ta abin alfaharin rayuwan ta da kaunan ta yadda nasan zaman takewar su a cikin so da kaunan junan su suke ko yaushe.
Samun irin mata kamar anty a wanan zamanin mace ma,abociya karamci ga mazan auren su tare da jiye masu jin dadin rayuwan su don bukatan su kawai.
Samun irin su anty yanzu gaskiya sai an tona a duniya don babu macen da zata iya sadakar da rayuwan mijin ta akan wata can.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA YAR UWA DON BA, A YAFE MAKI BA, , ,

IDAN KIN TURAWA WANDA BAIBIYA BA ALLAH YA SAKA MUNA A KANKI YAR UWA, , ,
36
Ina daga daki inajin yadda mama ke ci gaba da aibantani ga anty tana fadin dama ta dade tana shakkan faruwan haka a gare mu .
Don son da kikewa yarinyar nan yai muni Saade shi so haukane da har zaki yi wanan danyen hukuncin a kanki.
Maganan Lauratu ya tabbata ke nan in ma bakine itace tai maki shi don ta furta dama tunda mukazo da ita sai tai muna abinda har mu mutu bazamu mantaba a rayuwan mu to gashi ko tayi yau.
Nan dai mama take ta aibantani da iyyena cikin daga murya yadda zan iya ji daga inda nake a dakin mu zaune a takure.
Hankalina idan yai dubu ya tashi kuka nake ni daya a daki ina fadin koma may zaki fada yau mama a kaina na cancanci hakan a gareku da duk wani nakuma.
Baku duk duniya ma na ci a zageni a zargeni a matsayin rikkakan yar cin amana a gare ku.
Shike nan yau so da kaunar da anty ke gwada min ya tashi a tutar babu tunda kaddara aure ya gitta a tsakanin mijin ta dani.
Aure aure fa waini da daddy yau wai daddy ne mijin sunna na da nake aure wanda zanyi zaman rayuwa irin wanda ma aurata ke yi a tsakanin su.
Wanan bakin auren yau yaraba tsakani na da matar data zamay min matsayin uwa da ubana a duniya tai ma rayuwa na tsaye gurin ganin ya inganta.
Yau banda wani martaba ga idon duk wanda yaji wanan kaddaran a kaina babu ma wanda zai dauke shi wai kaddara ne haka.
Mikewa nayi na fara hada kayana duk abinda nake bukata sai dai babu abinda na dauka daga cikin abinda anty da mijin ta suka saya min a gidan.
Na jawo wani dan karamin jakkar kayana na cusa a ciki na mayar na tura a karkashin gado ina mai ci gaba da sauraren maganan mama a falo da takeyi.
Gajiye ta shigo dakin ta samu ina kuka take cewa dani Rahama ashe abinda ya faru ke nan dake, yanzu nake jin haka a gurin mama da tazo ai.
Kiyi hakkuri tunda ba yin kanki bane haka Allah ya nufa dake sai dai ita mama ta bani mamaki gaskiya wanan magana da takeyi haka bayan tasan koke wacece ta san kuma abinda zaki iya da wanda baki iyawa.
Na share hawaye na a hankali cikin dakushewar murya nake cewa Gajiye bari mama ta fadi don itace silar hadani da Anty a rayuwana.
Yau kuma ga irin kaddaran daya gitta tsakanina da anty wai muna a matsayin zaman miji daya da ita.
Gajiye tace amma ai duk wanda yaji idan ya saurara yasan baki da laifi a cikin zancen nan Rahama,
Haba gajiye wanan magana wani mai hankaline ba zai konawa rai ba duk wanda yaji dole ne ya zarge ni gajiye.
Yaya zan zauna da daddy mijin anty a matsayi wai mijin sunna a gare ni sai na sake sake wani kuka mai tsuma zuciyar duk mai sauraren ta.
Ni yanzu ai tankar daidai nake da mujiya a cikin alumma don nasan duk inda na shiga Gajiye nunani za, ayi a matsayin yar cin amana.
Rahama ki daina wanan maganan haka ki zamo cikin bayi masu rungumar kaddara akan su walau mai kyau ko mara kyau.
Nace Gajiye na yadda da kaddaran auren mijin matar data rikeni kamar yar cikin ta riko irin na fisabillahi ba kisa ba munafunci a cikin sa.
Yau shine zan zauna wai a matsayin kishiya a gurin ta kema kin san hakan ai ba zai taba yuyu ba gaskiya.
Dagani har gajiye kuka muke a dakin can muka jiyo muryan anty tana kiranta a falo da sauri tamike ta fita tabarni tana share hawaye a fuskan ta a hankali.
Ganin gajiye na sharan hawaye yasa anty ta fahinci kuka mukeyi a dakin dagani har ita.
Tace ba dai kuka, kuka shiga daki kunayi ba gajiye kiramin Rama don Allah so take tajawa kan ta ciwo ko may kuma ?
Gajiye ta dawo dakin ta samay ni na daga kai sama ina kallon rufing din dakin take fada min kiran da ake min ta juya tafita daga dakin
Mama ko har lokacin bata fasa aibantani ba da iyayye sai bata hakkuri anty keyi a falon
Munan kalamai na aibanci da mama Altine ke fadi a kaina yasa na rutse ido daga inda nake kwance a daki cikin dafe bakina kada sautin kukana yafito
Bata kuma fasa fadan ba cikin daga harshen ta ta yadda zagin da maganan da takeyi zai iso gare ni.
Hankalina idan ya kai dubu ya tashi ban san lokacin da na mike ba cikin sanda na tura kofan dakin yadda bazan iya jin kalaman mama ba a kaina.
Komai da ya kasance anty ko mijin ta ne suka saya min shi ban dauka ba na boye kayan ina jiran na samu kafa ne kawai na balle daga gidan.
Kuka nake ina tunane akan rayuwana ina fadi a raina shike nan burina ba zai cika ba a rayuna nida karatu kuma sai wani ikon Allah don idan na samu nabar gidan nan har abada bazan sake waigo shi ba.
Ban taba tunanen rayuwa na zai kare a haka ba ba tare da gurina akan karatuna ya cika ba.
Gajiye ta turo kofan ta kura min ido tace ya kamata kibarwa Allah wanan alamarin haka Rahama, dafa yarda da umurnin hajiya hakan ya faru.
Gajiy asanadin mama nasan anty yau gashi an wayi gari na zamo maciyiya amana a gare su bazasu taba yarda cewa bada sani na haka ya faru a gareni ba.
Don haka ba mama ba duk wani shakiki na anty yau na zamo mai laifi ne da bakin jini a gurin shi.
Gajiye da mutuwa nayi daya fiye min ganin wanan bakin ranan a rayuna ranan da za, ace ni Rahama wai na hada mijin sunna da Anty Anty da take kamar uwa da uba a gurina.
Matar da ta rike ni

Please Login or Register in order to submit comment