Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina jin zuciya na ba dadin rabuwan da zan sake yi dasu sai kuma wani lokaci mai tsawo kila na sake ganin su.

****** ********* ******
Wanan ganin da mama tai min ya matukar tayar mata da hankali sosai gashi don samun guri wai harda kyauta kudi nai masu har dari biyar.
Wa ma yasan abinda nabawa uwata a daki don haka tun da safe tai sammakon barin gidan zuwa gidan aminiyar ta larai bamu da nisa sosai da ita.
Tana shiga suka gaisa larai tana ganin ta tasan akwai abinda ya faru don duk tai mata sakko haka agida da akwai matsala ke nan gare ta.
Tace may kuma ya faru mutumiyar tace bari kedai larai nai wa kaina abinda ya koma min ciki wallahi.
A zato na na hada auren yarinyat nan da garbati don na kawar da ita da uwar ta daga farin cikin da suke ciki .
Ashe ban sani ba na dauko wuka ne na dabawa kaina a ciki dana sani daya daga cikin wa yan nan shashashun yaran na cina mashi.
Kin koga yadda yarinyar nan Rahama ta koma Larai ?
Wai yau har Rahama ce da kanta tabani kyautan dari biyar cas kin gashi gashi nan .
Ta baje tayi kyau ta wani murje ta kara haske da ita kamar mai aure a birni yanzu fa uwarta ma bata cikin matsalan komai a gidan nan don sai bushashan ta takeyi.
Jin tai shiru larai tace da ita to ai baki san wani abuba ne Lauratu idan da yar taki kika bashi sabanin haka zaki gani fa.
Da sauri take kallon Lairai don jin abinda tace tace eh haka nane mana don kinga halin su ba daya ba da ita Rahaman.
Yadda nake jin labari fa ita yarinyar ce ta sai wa kanta zaman lafiya da kowa a gidan.
Don ko sabuwa dake hauka da farko yanzu ta aje shi gefe don mutuncin yarinyar a kan su ta dauke su tankar iyayyen ta ne bata je masu a tsaye ba.
Kin ga kuwa banga dan ki ko daya da zai shiga ya mayar da kanshi kamar bawa ba a gare su don a zauna lafiya.
Dama hakane dan hakin da ka raina sai yazo ya tsone ma ido shiya sa tun farko da kika zo min da maganan wanan hafin nace dake kinyi babban kuskure amma alokacin har haushina kikaji don may na fadi haka.
Kina ganin ke kin cuta masu ne baki san taimakawa rayuwan su kikayi ba ke .
Tace bari larai sabon atamfane ma fa ta daura a jikin ta kuma bana cikin lafen ta ba ne don nasan kayan lefen nata.
Gaskiya yaya sallah ya munafunce ni don da yasan akwai ci a wanan auren shine yaki jona daya daga cikin diyan shi.
Nan dai sukai ta kulle kullen su har take cewa duk yadda zatayi ta goga min bakin jini a gidan nan sai tayi don bazata bari tana kallo ina cikin daula ba dani da uwa ta.
Da tasan hakane da bala mai faci zata hada aurena dashi naje ko abincin ci ya gagare ni.
Kamar yadda ta kulla haka ta samu wata aminiyar sabuwa take fada mata wai suna may suka saka min ido ina yadda naga dama a gidan Alhaji gashi sai dinke dinke yake min kullun kuma yanawa uwata aike ba kakautawa.
Irin zancen da sabuwa ke so ke nan ranan da sakon ya samay ta nan ta haukacewa mutane a gida da masifa inda take shiga ba nan take fita ba ga miji kwance a daki ba lafiya amma ta tayarwa mutane da hankali.
Haka yasa shi daurewa yafito katakata dashi yana cewa ke Sabuwa kin ishe ni da masifa da tashin hankali a gida.
Ke lokacin da kika zo gidan nan haka wa yanda kika sama a gidan su kai maki ne shi ?
Don haka daga yau na sake jin hayaniyar ki a gidan nan kowa yaya ne nai alkawarin sai kin bargidan ko akan waye haba kin ishe ni Sabuwa kin kai min ko ina.
Ba a kan ki aka fara kishiya ba ke ba wasu ne kika zo kika sama a gidan bane wai ko su ba mata bane da basu daga hankalin su ba ga shigowa cikin su.
Duk abinda ke fadan wai nayi wa yarinyar nan nayi mata sabuwa sai kizo ki kwata ke ma in na karfi ne ?
Ya juya zai koma daki ya yanke jiki ya fadi tun take mata da yaran gida aka saka kururuwa a gidan aka kwasa sai asibitin birni
Kwanan shi biyar a ka dawo dashi ba hannu ba kafa tare dashi abu kuma ya koma kasa sabo.
Wanan faduwar ya dawo da ciwo sabo gare shi hawan jini yazo ya shiga ciki kuma da sauran ciwar wukan zamani da ba, a rasawa.
Aiko yaran gida da matan su suka saka ta a gaba sai tabar gidan nan ko suyi mata dan karen dukan tsiya su kora ta.
Ganin zasu iya mata abinda suka furta a kan ta yasa ta sulale ta bar gidan baki alaikum tun basu illanta ta ba.
Haka ya sa suka dan sarara mata don ficewan ta gidan ya dan rage masu zafinta da suke ji a lokacin.
Kusan kwanan kin da tayi bata gidan duk fama da jikin Alhaji akeyi don jikin yaki mai dadi sosai a lokacin.
Haka nan ko yaushe cikin jike jike da dafe dafen magani ake mai wani ai mai tausa wani kuma dafa mai yasha.
Muna faman sintiri yi mai sannu a duk dakin da yake haka za, a kwashe shi tara tara zuwa dakin.
Ranan sai ga Sabuwa ta dawo wai iyayyenta ne suka zo suka bada hakkuri akai.
Washegarin da ta dawo ne ina dakina ina barcin safe misalin karfe sha dayan rana na gama dafawa mama hausatu shimkafa da wanken sana an ta.
Shine na dan kwata don na huta a raina can a cikin barci na nake jin ana sallama a daidai kofan dakina.
Firgigit na falka ina amsa sallaman tare da fadin shigo daga ciki ina kokarin saukowa a saman gado.
Lokacin suka shigo dakin Anty Sa,ade na ce daga birni tayi shigan ta na yan gayu ga kamshi na tashi daga jikin su.
Tana tare da wata yar matashiyar budurwa tare da ita sai diyan ta biyu da take tafe dasu.
Ban san lokacin da na yanka wani uban ihu ba na makale mata a jikin ta ina cewa wai ni Rahama yau ina zan saka kaina.
Sai kuma na fashe da kuka a lokaci daya na durkushe a kasa daidai kafan ta ina rusa kuka gwanin ban tausayi.
Naji tace yau ga tsiya taron da zakiyi min kuma ke nan Ramana daga gani na kuma sai ki saka kuka haka ?
Tace wa budurwan da suke tare maryam tashi mu tafi wanan bata son zamana a nan.
Da sauri cikin kuka nace anty don Allah kiyi hakkuri na daina ina kokarin share hawayen dake fuskana a lokacin.
Nashiga daukan yaran ina cewa kai Fatima kece kika girma haka na taba hannun babban dan ta sai ya jaye daga gare ni.
Nace baka san ni ba ko kokaga na zama wata bakauya dani ko ina fadi ina dariya tare da kallon fuskan yaron.
Nan muka shiga gaisawa dasu cikin murna da jin dadi ina tambayan ta yaushe tazo garin namu ?
Tace ikon Allah Ramana ke ce yau haka a dakin auren ki gaskiya naji mamaki da mama ke fada min wai aure zakiyi sai ko gashi na tabbatar da hakan yau da nazo dakin ki na gani.
Murmushi nayi tare da fita daga dakin da sauri na fita zuwa bakin randan ruwa na na kasa na debo masu run shi a cikin kofin silver mai marfi.
Nakawo masu ba laifin sun karba sun dan kora ruwan suka aje kofin amma yaran su sunki shan ruwan sai turanci suke da uwar su da dayan budurwan da suka shigo da ita gidan.
Tambaya na take ina maigidan naki ne mama tace muna yana fama da jiki wai Allah ya sauwaka ya bashi lafiya.
Mun dan taba hira dasu wanda akan karatuna ne nake mata ina fada mata cewa nawa karatun ya rushe ke nan tunda zaman gidan nan da nakeyi ba fashi a cikin shi.
Tace komai ai na Allah ne baki san ko watarana zai yarda kije gaba ba ai nace cafdi anty bako a gidan nan ba.
Tace muje kikaini na gaidashi da sauran abokan zaman naki ko ?
Ban bata lokaci ba na mike muka nufi dakin mama hauwa inda yake kwance a ranan.
Kwance yake yana ganin mu yake kokarin mikewa zaune sai dai bai iyawa dole ya koma ya kwanta yana masu sannu da zuwa.
Kusa dashi naje ina cewa Alhaji anty na ce ta birni da nake baka labari tazo ganin mu yau.
Hannu yake daga mata alaman yana masu sannu da zuwa yai matukar bamu tausayi gaba dayan mu a dakin.
Gashi dai ya na son yin magana amma babu halin yin haka a gare shi sai in maganan ya zo mai yake samu yayi shi.
Muryan anty ce ke fadin an kaishi asibiti kuwa a hakan da yake kwance a daki ?
Mama tace an kai shi sai dai ba wani babban likita ne suka samu gani ba suka dawo wai akwai tsada ga ganin likitan.
Haba komai tsadan shi ai sai a kashi a ji halin da yake ciki yafi wanan kumshe shin da akayi haka a gida yana wanan wahalan haka.
Tace yana da yara manya ne maza suka ce mata eh tace idan suna kusa ina son magana dasu don Allah.
Daga haka muka fita na kaisu dakin mama hausatu tabata dubu biyar dakin sabuwa ma haka da mama hauwa.
Ai sai aka shiga saka mata albarka kwando kwando a ranan muka koma dakina kafin su yaya Hadi suzo gidan.
Tace gaskiya Ramana mijin ki ya bani tausayi mutum yana wahala haka an kunsheshi a gida ba wani maganin kwarai gare shi.
Kiyi hakkuri kinji duk wanan jerabawa ne daga Allah kici gaba da biyayyan dakike yi Allah ba zai bari ki tabe ga banza ba a rayuwan ki.
Muna cikin maganan ne sai ga yaya Hadi babban dan Alhaji yana sallama daga kofan shiya na.
Na fita naga shine nace mai ya iso itama na fada mata zuwan shi nan tafita daga waje gurin shi suka gaisa.
Take cewa dama tana so ne idan sun yarda sai akaishi asibitin can birni don zata koma ga jibi kunga sai ku isa ina can amma sai abinda kuka gani ga hakan.
Yai godiya yace sun gode zai yi shawara da sauran yan uwan shi takawo dubu hamsin taba shi tace ayi amfani dashi idan zasu zo din.
Da zata tafi tabani dubu ashirin wai na dinga amfani dashi tunda mijina da zai bani baida lafiya yanzu.
Sau mutanen gidan ta basu dubu goma wai su raba haba sai gida ya kaure da bakin albarka kowa na saka mata albarka agidan suka wuce muna kallon su.
Basu ki ba bayan shawaran da sukayi sun yake cewa tunda za, a taimaka masu gara su kaishi su gani kawai zaifi .
Haka su ka yanke shawara bayan kwana biyu da tafiyan ta suma suka take mata baya sai garin kano ganin likita.
Basu sha wahala ba don ta basu lanban wayan ta idan sunzo su kirata don ta sani.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE.


IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA YAR UWA KADA KIBA WA WANDA BAI BIYA BA PLEASE DON AMANA NAUYI GARESA, ,

13
Shirin kwanciya sukayi tana saye cikin kayan barcin ta sun matukar karban jikin ta sai hullan da ta saka a kan ta don kariya.
Har wanan lokacin mijin ya fahinci tana cikin damu wanda bai wuce nasaba akan yaran ta ne da zaman su ke hannun kishiyan ta.
Tsaye yake saitin window dakin yana waya daga inda take kwance tana kallon shi.
Tun yana wayan a hankali har yakai ya fara daga muryan shi yana cewa.
Wai ke mahaukaciyar ina ce haihun ki nawa a gidana don a sani na ai kina haihuwa har ma yaushe ne kika haihu wai ?
Bata ji may ake cewa dashi ba don ba handfree wayan shi yake ba a lokacin ta fahinci indai zaiyi waya bai saka handfree ba da kishiyoyin tane yake waya wani lokacin.
Muryan shi taji yana fada a hasale yana fadin wai ke hindatu wata irin mace ce wacce a kullun sai ta fito da sabon sallon tashin hankali a rayuwan ta kada dai a zauna lafiya.
To ki sani na fada maki banda kudin zuwa Germany ganin wani likita kan neman ciki duk shekaran yar ki nawa da zaki tayar da hankalin ki kan wai neman ciki yar just three years take nema fa yanzu.
To ki sani duk abinda kikaga dama kiyi amma amma ni bada kudina ba cikin wanan shirmay naki.
Daga haka ya katse wayan tare da jan tsuki ya nufo gadon don ya kwanta shima.
Yana kwantawa yaji muryan salihan matar nashi mai son shi da kaunar shi tsakani da Allah na fadin.
Hindatu ce ko ?
Yace a hasale itace mana.
Anya kishin hundatu ko akwai imani a cikin sa heartbeat ?
Yace nima abinda nake tunane ke nan ko dai tana da matsalan kwakwalwane .
In ba haka ba yaya da ganin wata da ciki duk tabi hankalin ta ta tayar ga banza ?
Ta manta cewa Allah ne ke bayarwa ba mutum ke badawa ba da kan sa.
Tace to ai ba fada zakai mata ba tunda abinda take so ne sai ka lalashe ta a wuce gurin.
Yace oho na tsaya mata sanya ta ci gaba da min rashin hankali da ta saba ke nan ko ?
Tace ba haka bane hankalinta ne ya tashi bata cikin natsuwa ne yakawo hakan .
Yace matar da bata damu da damuwan kowa ba kan ta kawai ta sani ita a rayuwan ta.
Tace hakkuri dai zakayi ka rarasheta kada ta jefa kan ta cikin wani hali kuma na daban.
Yace na fada maki ki bar wanan yarinyar kawai samun daurin gindi tayi a gurin daddy shiya sa take min abinda taga dama.
A can kuma gida Nigeria inda Hindatu take zaune gaban mahaifiyan ta tana rusa kuka.
Mahaifiyan nata tace na fada maki kibi a hankali kin san halin mijin ku da murdaden hali baida saukin fahinta ko kadan.
Maza ki kirashi ki kara bashi hakkuri tun bai ce zai dauki wani mataki ba a kan ki.
Uwar tace maza kira min shi nai magana dashi don nasan yanzu yana can hasale duk inda yake.
Mama yanzu fa dare ne a can wata kilama sun kwata a lokacin nan ko.
Dama dai baki son zaman lafiya aike baki san maza sai da lalashi ba kina ganin komai dole daddy sa ya sa shi dole a kanki.
Sai dana fada maki kada ki kirashi yanzu kiyi hakkuri har su dawo don sai ya fahinci kan wanan matar tashi kike wanan haukan haka?
Mama ni kunyan kiran sa fa nake ji na fada maki kin kuma ji amsan daya bani har da ce min wai ni mahaukaciya ce.
Kira min shi kibani shi nace maki aini dole ya ta tsaya ta saurare ni ko.
Dole Hindatu ta kira layin mijin nasu har wayan ta katse ba a dauka ba .
Uwar ta rude iya rudewa don tana gudun mahaifin hindatun yaji yai masu tsiya.
Sake kira min shi inji uwar cikin kidimaywa taje magana fuskan ta kan yarta.
Dole hindatu takara kiran shi yana ji yaki dagawa sai Saade ne ta daga kiran tare da mika mai wayan ya kalla cikin hasala tare da kara mai a kunnen shi.
Mama ya dauka Hindatun tace tana mikawa uwar wayan
Muryan mahaifiyarta yaji a wayan yasa shi dan gyarawa cikin muryan ladabi yana cewa
Yusuf nice a layin,
Yace na gane mama kuna lafiya yaya mutanen gida tace duk muna lafiya.
Yusuf dama kan zancen da kukayi da yarinyar nan ne nake son maka magana .
Yace mama idan wanan zancen ne ni na gama magana na ba hannuna acikin wanan magana.
Har yaushe ta haihu da zata dauku tashin hankali tasakawa ranta haka ?
Uwar tace na sani Yusuf nasan da haka ai rigimane kawai irin na yarinyar nan don shi ciki ai rabo ne.
Don haka kayi hakkuri abar wanan zancen don bana son ko mahaifin ta ya san da wanan zancen haka.
Don Allah kayi hakkuri kasan halin kowa da irin nashi tunanen hakan yana damun tane yasa take wanan haukan haka.
Inji Saade ke bashi hakkuri bayan sun gama wayan da mahaifiyar hindatu din.
Yace ba komai bane ke jawo min haka sai wullakancin da sukaga daddy da hajiya suna min akan su amma yarinya zata gane kuren ta wallahi.

****** ********* ******
Mama ce daki da baba cikin tausan murya take cewa yanzu malam haka zaka bari wanan daman ya wuce mu a gidan nan.
Allah ya rufa maka asiri sai masu hannu da shunin gari ke zuwa neman yar nan don sa, an ta.
Amma ita da uwarta basu fahinci nasaran haka ba don basu da fahinta akai.
Wancan auren da tayi da suka samu dadin su da wasu kaci ko wanna ma idan yai dadi ai sune zasu ci abinsu muna kallo.
Dadin baki mai ratsa zuciya mama kewa baba kullun akan maganan tun bai yarda ba har takai ya amince da zancen ta ya shiga zuciyar shi ya zauna daram ya kafe zai ba Jatau ni.
Ko ina so ko ban so dole ne na amince da zabin shi tunda shine keda Alhakin zaba min miji ai.
Ranan da baba ya koma dakin Inna sai gashi ya fito mata da zancen wai maganan Rahama da Jatau fa yana nan don haka sai ku fara shiri akan aure nan bada dadewa ba za, ayi.
Take ran Inna ya baci idanuwan ta sun sauya launi cikin bacin rai take cewa .
Malam da ba dakai na haifi yarinyar nan ba sai nace kana hassada da ita ko kiyayya don irin kiyayyan da kake gwadawa yarinya yai matukar yawa a gidan nan.
Yanzu kai ko kunya baka ji garin nan aji zaka kara aurar da yarinyar nan ga wani tsoho don kudi don abin hannun su kukewa kwadai.
Yanzu Asiya ni kike kallin idona kice saboda kwadan abin hannu nake aurar da yarinyar nan.
Inna ta ma rasa may zata ce da shi saboda takaicin daya rufe ta a lokacin.
Cikin bacin rai take cewa ai ba karya na fadi ba don duk wanda ma yaji haka yasan abinda kukewa ke nan.
Yanzu wancan auren abinda ta samu wa ya amfana dashi ba kai ba ina gidan ne kawai kila zata tsira dashi.
Don haka wallahi wanan karon bazan yarda da cin zalun din yarinyar nan da ake muna ba.
Har nawa yarinyar nan take da za, a dinga mata haka ina ga yayyin ta nan zube a gida su ko zancen su ba ayi.
Yace to tunda kin isa da ita duk matakin da zaki dauka kan wanan zance sai ki dauka mu gani tunda kin isa ke .
Wasa wasa magana har takai ga daga murya tsakanin su sai ga mama da ta dade tana sauraren su ta saka baki daga waje tana fadin
Malam kada ka biye mata kasan va hankali ke ga Asiya ba don son abinda yarta ke so ya rufe mata ido bata hangen abinda kaje ya dawo.
Cikin fushi baba yace mata ki kyale ni da ita Lauratu wallahi Asiya kin yi karya dake da yarki ku mai dani mutumin banza a gari.
Duk iskancin da budewan idon ku da kuke ganin kuna dashi yanzu baku kai ni ba don haka ku ci gaba da min rashin da, a ke da yar ki ku gani a gidan nan.
Indan kunce haka kuka dauko sai kun kwammace rashin zaman ku gidan nan dani.
Kallon shi Inna tayi shekeke tace dashi ai kasan kaine keda rayuwan mu a hannun ka .
Indai kan wanan zancen ne sai dai ajimu don nai magana akan hakkin ya ta ai ba haramun bane ko ?
Kuke samun riban auren da takeyi shi yasa kuke son kara tursasa mata sai tayi wanan din taje ta ciwo maku kasuwa gidan.
Duk masifan baba yana ganin ta haukace mai sai jikin shi yai sanyi yasan duk yadda akayi akwai abinda ta digora dashi take hakan don ba halinta bane haka.
Aikin banza inji mama tace may ye bamu sani ba wani dare ne kuma jemage bai gani ba.
Auren da sai anyi kifi kowa zakewa da jin dadi shine har za, a tsaya ana muna tijara akan shi.
Malam ka kwantar da hankalin ka kana nan zakaga yadda take rawan kafa da jiki ita a dole yarta ta samu gurin zama.
Idan ni ban yi rawan kafa ba ai ke sai kiyi tunda ke ma kina da yaya dakin ki sai ki bashi daya daga ciki a wuce gurin.
Tana fadin haka ta koma ta kwanta abinta tare da watsawa baba harara tana fadin don an mayar dakai haka bari a turo ka kai min cin mutunci ko.
Tun ranan da akai fadan nan ina wuta mama da baba su jefa mu ni da Innata.
Duk wani kule kulle da makirci shi mama take kullawa akan zancen sai cin kudin Jatau takeyi tana bushashan ta a cikin gida ita da diyan ta kawai.
Duk wani hanya da baba zai fahinta mama ta toshe shi har yakai ta fara dan fita zuwa gurin malaman ta wai a kulle muna baki duk mu ukun sai abinda tace kawai za, ayi.
Haka Inna take cikin tashin hankali kan zancen don ta fahinci idan bata yi da gaske ba babu makawa sai anyi wanan auren gamin gan bizan dani da Jatau.
Kullun tana hanyan gidan mama Altine kan magana daya duk tafita hayacin ta.
Gashi mama taci kudin shi yakai dubu ashirin da biyar tana karba wai tana bani tana kuma kamun kafa da sauran.
Bata san cewa komai nashi a lissafe yake mai ba don ba mutun ci ne dashi ba akan dukiyan shi ko kusa bai taka kafan Alhaji Garbati ba gurin tara abin hannun shi ba.
Amma mutane don baya ci sai suke gani yafi garbatin ma tara dukiya a garin.
Wata rana ina fitowa zan shiga gidan mama sai ganin shi nayi a kofan gidan mu don kusan a nan yake wuni.
Yana gani na ya fara washe baki ya na dan soshe soshe kamar mara gaskiya.
Ya dan tafo duduke kusa dani yana cewa a, a mutumiyar barka da fitowa ashe yau nazo a sa, a zan gan ki ashe ?
Wani kallo nai mai nace yauwa sannu baba .
Yayi dariya hakoran shi da wanda babu da rinanun sauran dake cikin bakin shi suka baiyyana a fili.
Cikin dariya yake cewa ai ni yanzu ba babane gurin ki zaki dai iya kira na da ango ango mai

Please Login or Register in order to submit comment