Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai.
Ba abinda yai min tsinanen zafi akan maganan mama da diyan ta a gidan mu.
Garbati yasa aka gina min daki mai girma da fadi yadda zai isheni aka kewaye shiyan daban cikin na iyalin shi can gefe daya an shafa farar kasa yaji sai kyali yakeyi.
Haka ya kara bankantawa iyalin shi rai sosai har suka so tayar da hankalin su.
Amma da ya basu dan wani abu suma suyi gyara sai baki ya mutu murus kowa ta shiga sha, anin gaban ta da diyan ta amma kishin yana nan daram a ran su.
Duk inda yabi sai ba, a ake mai na ya fado gari ya zarta maza zai bare yarinyar dalleliya a ledan ta sai ya washe baki cikin jin dadi yana dariya.
Mama ko sai auki fadawa mutane karya da gaskiya takeyi akan zancen bukin tana zunden inna ta.
Inna ta duk tabi ta ramay sai dan wuya daga ita sai uwar dakin ta mama altine suke shirin bukin sai yan uwan su tsiraru da sukaji suka gani.
Ko su ba wai sun san shirin da Inna da mama altine sukayi min bane haka ake tafiyan a dunkule.
Gaba daya daga inna har baba babu wani mai kwanciyan hankali dama ma inna dake nuna halin ko in kula da bukin.
Idan ka cire mama da yaran ta wanda su ko a kwalar rigan su bai shafe su ba.
Ta dai zuga shi ya zugu yanzu kuma ta saka mai ido yaji kunya dan kudin sadakina da aka kawo dashi ne yake kokarin sayen komai.
Na dan gadon katakon da za, a sai min ma ya gagara daga karshe ganin haka tasa inna dabaran cewa yaba mama altine kudin ta shiga birni ko na hannu ne ta sayo min.
Tayi hakane don idan kudin ya shiga hannun su sai su san dabara mama altine ne ce ta koya mata wannan dabaran.
Baiki shawaran Inna ba tamika masu dan abinda ya saura takaiwa mama altine ta shirya sai birni da kudin daga karshe anty ce ta cika aka sayi min saitin gado da dan wardrove da katifa har da karin tarkace.
Wanan matar ba abinda zamuce mata sai dai Allah ya bata lafiya ya shirya mata zurian ta da albarkan sa kawai.
Ganin babu komai a dakin inna ta yasa mama ta samu baba da zancen da yamma bayan ya dawo gida take cewa.
Yanzu malam kana ganin haka zaku kai yarinyar na aure babban gida irin haka babu komai da uwarta ta tana da mata na fita kunya kaima sai nake ganin a furin ka hakan ne ?
Baba da yanzu ya fahinci mama so take taga wallen shi kuma tasan sirin abin sai ya boye mata ba su mama kudin sadakin da yayi yace anyi auren ne ko kikaga uwarta ta kaita hakana ?
Haka yasa taji haushi taja bakin ta ta tsuke ta bar zancen sai ido tana cewa ni dama taimakon ku naso nayi ko mu tafi gida tumba dillaliya adan samu abinda aka tsintar mata gurin ta in yaso bayan bukin abinda aka samu sai abata kudin ta.
Baba yace ko tabarma Allah ya hore mata daga gare ni sai na kaita dashi .
Yafice abin shi gidan ya barta nan tana mashi dariyar mumuke ta baya tana an daiji kunya wallahi anyi shigewa ai ciki amma ba, a iya fitar da yarinya kunya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE NA FADA IDAN BAKI BIYA BA KIKA KARANTA MIN NOVEL NA BARKI GA ALLAH.

IDAN KIN BIYA KIKA TURA MIN NOVEL WANI GROUP KO KIKA BA WA WANDA BAI BIYA BA KE MA NA BARKI GA ALLAH DON KINCI AMANATA ALLAH ZAI SAKA MIN A KAN INSHA ALLAHU WACE TASAN BAZATA IYA RIKE AMANA BA DON ALLAH TAI MAGANA NA BATA KUDIN TA TAFITA MIN GROUP DON AMANA NAUYI GARE SHI ABINDA KA RAINA SAI YA HANAKA KETARE SIRADI GOBE KIYAMA ALLAH YA BAMU IKON RIKON AMANA A TSAKANIN MU.
DON NAGA NOVEL DINA A WANI GROUP KUMA NASAN WACE TA FITAR DON BATAI MAGANA BA NA BARTA GA ALLAH DON ALLAH SHEDA NE GA ALKAWARIN MU DA KU, ,

6
Ranan da na zana jerabawan karshe na na secondarya rana ce da ya kamata nai mafarin ciki a raina don kowa ka gani a cikin mu yana cikin farin ciki da jin dadi a ran shi.
Sai dai ni a gareni sabanin hakane don ya kasance min kamar rana na bakin ciki a gare ni.
Lokaci daya yanayi na ya sauya min naji duniya tai min kunci a raina komai ganin sa nake yai min baki a raina a dalilin tunawan da nayi wanan jin dadin rayuwan ya kusa yanke min.
Don wanan auren jarabtan da na tsinci rayuwana dashi na auren tsoho da mahaifina zai min a lokaci daya haka, batare da yai la, akari da irin rayuwan da zanje gidan miji na tarar.
Wanda yau baifi saura kwana goma ba naje gidan Alhaji garbati a matsayin matar auren shi nima a gidan.
Juyawa nayi zuwa staff room don nai sallama da malam mutumin da yai tsaye a kaina har nakai wanan matsayin na yau a gare ni.
Malam yana ganina yace a, a Rahama an kanmala ko ?
Maimakon na nuna farin ciki na sai na kai durkushe a gaban shi na fara kuka yace subbahanallahi Rahama lafiya dai ko ?
Cikin kuka nafara cewa malam nazo ne nai maku godiya akan tsaya min da kukayi har na kai ga wanan ranan ga karatuna.
Sai dai kuma gashi guri na ba zai kai na zama likitan da nake son zama ba na taimakawa yan garin mu kamar yadda nake da gurin haka a rayuwana.
Mahaifina ya yanke min wanan gurin nawa ta bayar dani aure ga wanda yaso yau saura kwana goma ayi bikina akaini.
Subbahanallahi inji malam yace yaushe haka ya faru kuma Rahama waye kuma miji ?
Sai na dan kakaro murmushi a fuskana nakw cewa malam an kwana biyu da hakan ba kuma kowa bane mijin sai Alhaji Garbati dan bida na garin nan.
Shi da sauran malamai da suke saurare na cikin tausayi sukace garbati dai garbati wanan tsohon mutumin da muka sani ?
Nace shi malam ,
Malamai suka ce kai amma mahaifin ki ya cuce rayuwan ki Rahama ga wanan tsohonbzai bada ke dan kwadayi ko don may ?
A hankali nace nima ban sani ba malam na mike ina masu godiya na ke masu sallama na tafi,
Nan na barsu da mamaki kowa na fadin albarkacin bakin shi a kaina na nufi gida.
Na shiga gida da sallama na na gaida da su mama da na samu tana raba abinci a tsakar gida.
Nan na shige dakin inna na kwabe uniform din jikina fita nayi na debi ruwa don na watsa naji dadi jikina.
Mama ta bini da harara wai dan ruwan da zasuyi aiki dashine kuma zan kwashe nai wanka don ni nafi kowa tsabta ko may ?
Ina ban daki na fara watsa ruwa ne naji mama tana rafka salati haka yasa nasan ba lafiya ba ke nan.
Nai saurin watsa sauran ruwan a jikina na fito da sauri nan na samay su tsaye cirko cirko sai fada mama takeyi ita kadai Inna ta tana tsaye a bakin kofan ta itama fuskan ta a cikin damuwa yake.
Na karaso inda take ina fadin Inna lafiya ko may ya faru kuma ?
Kafin mama ta bani amsa take cewa dani wai angon ki ne ba lafiya gashi can an kwashe shi zuwa asibitin birni yanzu.
Gabana ne naji ya yanke ya fadi min ras ras nace shi Alhaji garbatin ne da kan shi baida lafiya ?
Mama tace idan bashi ba da uban ki ko bakiji may nace bane ni.
Allah ya sauwa nace na watsa ruwa a kafana dana rage a sauran roban da na fito dashi ban daki da nai wanka.
Nashige dakin mu kawai na fara sallah bayan na idar ina jin mama tana karasa aikin ta sai faman mita takeyi akan zancen ita kadai a tsakar gida.
Na juya inda inna take zaune cikin damuwa nace inna may ya samay shi ne ?
Take cewa dani yanzu nima nake jin zancen a gurin yaya wai ya kwana biyu yana irin wanan ciwon dama.
Allah ya sauwaka nace, naci gaba da kwalliya na ba abinda ya damu raina ko kadan.
Sai bayan dawowan babane muka samu labari wai ashe ya kwana biyu yana irin wanan lalurar .
Fitsari ne ke mai wahalan fita idan zaiyi sai kuma yanzu da suka tafi asibiti ake cewa harda hawan jini yana da shi.
Mama sai cewa tayi Allah ya cece mu ga farar kafa mu kan ?
Kamar yaya farar kafa kuma baba ya tambaye ta hakanan ?
Tace to yau saura sati a saka lalle haka ya kasance dashi ai sai ace yar mu ce zata shiga da farar kafa gidan shi .
Ki kadai fadi yanzu inji baba lalurar da kowa yasan ashe yana dashi dama shine zaki fadi haka ?
Tace ai idan ni ban fada ba iyalinshi su fada tunda koda yake dashi duniya basu sani ba sai yanzu .
Lauratu wai may yasa baki son a zauna lafiya ne ke duk abinda zai kawo fitina a tsakani kin san yadda zaki jawo shi.
Idan da yar cikin ki ce za, a kai gidan ai baza, ki fadi haka ba akan ta.
Allah ma ya tsare ya ta da wanan rayuwan gaskiya ne baka son a fadi kuma in ni ban fada ba duniya zasu fada ai.
Baba yace yanzu na gane may kike nufi akan yarinyar nan mutane suna fada min ban yarda ba amma yau na yarda da hakan.
Nan dai suka fara halin nasu na sa in sa a tsakanin su wanda ba mai shiga don ko mutum ya shiga sai yai kunya don ajima kadan zakaga sun shirya ne.
Bayan an sallamo Alhaji garbati ne daga asibiti ya turo kiran babana yana son magana dashi.
Baba baiyi nauyin kafa ba ya tafi amsa kiran da Alhaji Garbati yake mai a kofan gidan shi inda akai mai shimfida mutane suna zuwa gaida shi da jiki baba ya samay shi.
Bayan sun gaisa yai mashi yaya jikin shi da sauran iyalin shi ?
Ya bukaci da sauran mutanen dake gurin yana son ganawa da babana akan wani magana sun san alakal dake a tsakanin su don haka suka basu guri.
Alhaji garbati ya sake gaida babana yake cewa ya aika a kira shi ne don su yi magana akan zancen auren shi dani.
Yace bai san ko don matsalan da ya samay shi za, a iya daga bukin har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya sai ayi.
Baba yace haba Alhaji ai kowa yasan lalurar ciwo inda yin ba zai zama matsala ba sai ayi din a wuce gurin.
Alhaji yace amma duk da haka da a shawarci yarinyar da uwarta aji ta bakin su don kada azo ayi daga baya kuma a zo a samu matsala ya biyo baya.
Baba yace hakan ma shawara ne zai je yayi shawara da ni da uwata yaji ra, ayin mu ga hakan.
Nan dai sukai sallama baba yai mai fatan samun lafiya ya tafi ya barshi a gurin da ya samay shi a zaune.
Baba ya dawo ya samay ni da inna ta a daki muna hiran mu cikin jin dadi tai muna sallama ya shigo daga ciki.
Nan ya samu guri ya zauna ya na mike zan bar dakin yake cewa dawo ki zauna magana zamuyi daku.
Na koma na zauna cikin natsuwa a inda nake yace dama akan zancen auren Rahamane yanzu Alhaju garbati ya kira ni gidan sa mukai magana.
Jin abinda ya fadi yasa muka natsu daga ni har inna ta muna sauraren shi muji may zai fada muna.
Kaf yadda sukayi da Alhajin ya fada muna tare da tambayan mu may ye ra,ayin mu akai mu ?
Inna tace to malam ko dai an daga bukin nan ai ba fasawa za, ayi ba ko ?
Don may ba, a ayi a haka ba kowa ya huta da kace nace akai asan ayi an gama ta zaunu a dakin ta.
Baba yace ke Rahama may kika ce shiru nayi ni may zance tunda bani ce da ikon kaina ba.
Baba ya sake maimaita tambayan shi a gare ni a hankali nace baba abinda Inna ta fada gaskiya ne ayi kowa ya huta kawai.
Baba yace to madalla Rahama Allah yai maki albarka yasa haka shine alheri a gare ki.
Sai kiyi ta hakkuri da halin rayuwan da zaki tsunci kanki a gidan don kin san manyan mata zaki sama a gidan.
Idan kin je masu da taushi yadda na san ki sai kiji dadin zama dasu har iyalin su.
Amma idan kince zaki nuna masu halinku na diyan yau sai ki samu matsala dasu har iyalin su.
Mama da taji muryan baba a dakin mu ta kasa zaune ra kasa tsaye akan tana son jin may akeyi a dakin wanda ba, a son ta sani.
Sai ta hau fadin tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ka doka ai wanda yaci shi ka biya don dai nasan bai wuce ance garbati yace a mayar mai da komai nasa ba ya fasa.
Wanan rufa rufan wa za aiwa shi wa zai kwashi mai farar kafa ya jefa a cikin iyalin shi .
Baba dai ya fito bai kula ta ya fita da dare ya koma ya fadawa garbati yadda sukayi da iyalin shi.
Shiru yayi yana nazari maganan baba na irin halarcin da sukai mai don shi a rayuwan shi yana son kasancewa da wanan yarinyar a rayuwan shi.
Don haka ba, a fasa komai na shirin buki ba akaci gaba da gudanar da shirin da za, ayi.
Mama a zaton ta an fasa ne ne sai da taga yan uwan Inna suna shige da fice ta fahinci akwai zancen bukin ke nan.
Nan kuma hankalinta ya tashi ta sulale har gidan garbati taje a cikin dare ta gana da matan shi take fada masu mugun kalamai na batanci akaina da uwata.

****** ********* ******
Ranan kamu aka saka ni a lalle kamar yadda akewa ko wace budurwa kamu.
Duk wanda ya ganni ko inna ta yasan bamu a cikin walwala ana dai sha, ani ne kawai na bukin ba cikin dadin rai ba.
Gidan mama altine nake zaune da kawayena don a gidan mu babu fili ga magan ganun mama da basu da dadin ji.
Ya kasance washe gari daurin aure nan mama ta dora a tsakar gida ga dakin Inna tab da yan uwan ta sai cewa mama take ita bata gane ba fa.
Ace har yanzu ba, a fito da kayan amarya ba aje zuwa jere ko sai mutane sun watse ne za, a tafi jeren kamar marasa gaskiya.
Wata daga cikin yan uwan Inna ta fito tana bata amsa da cewa in ma mutane sun watse ai ko wasuwasun mu zamu iya gyara dakin yar mu.
Ballanta na rana muke jira yai sanyi mu tafi don bamu fada gidan mutane da rana tsaka ba kamar mun gaji da yar ta mu.
Dole mama taja bakin ta tai shiru ta kyale su dai gani ai duk abin da akewa taratara din ake boyo yau rana ce da bata karya sai dai uwar diya tai kunya.
Sai zuwa karfe biyar mutane suka fara shiga gidan mama Altine suna kwaso kayan da aka saya min na aure.
Wata daga cikin kawayen mama da ta gaiyyata suzo saka ido ta shigo tana cewa mama.
Ke laure wai kayan da naga ana fitowa dasu gidan mai kuli na waye ba dai kayan yar taki bace haka?
Ni duk garin nan ban taba ganin yarinyar da akaiwa kaya haka ba ?
Kinko ga kayan kamar ma na kamfani ne fa don a cikin ledan su ma suke, ga wasu irin manyan zannuwan gado da na fani kamar na makka dasu didin didin dasu.
Gaban mama ya fadi tace ke haule wai da gaskiya kike ko ba, a baki ga komai nakai gida ba tace idan karya nake fita ki ganewa idon ki ai.
Mama bata saya ba taja wani raggan zani dake shaye a igiya ta nufi kofan gida da saurin ta.
Aiko tana lekawa tai tozali da kujerun da ake fitowa dasu tace kan uban nan ni za, aiwa munafunci ke nan.
Watau malam yana da kudin yin wanan kayan haka wa yar shi.
Shine ya barni da yara a zunbule a daki sun kai sun kawo ga girma kuma ba manema suka rasa ba.
Da kyat kawayen ta suka samu ta natsu suka jata zuwa cikin gida dakin ta suna tausan ta akan idan tai haka taba da kan ta.
Nan dai aka shiga shirin buki ba wanda ya tsaya kula mama da haukan ta da takeyi ta kasa boye hassadan ta a fili.
Bayan sallah jumma, a aka daura aure duk dai ba wani shagali akayi ba tunda ba auren saurayi da budurwa bane, amma an ci ansha an koshi.
Da yamma aka dauke ni sai gidan Alhaji garbati gida ne babban gida mai cike da iyali fiye da arbain a gidan.
Sai da aka kaini dakina na dan zauna na yan mintina akace na taso akaini dakin uwayen gidan.
Dakin uwargidan mama salla aka fara kaini dattijuwa ce sosai don ta manyanta sosai ba sai an fadi ba itace ta wanke shi ya wanke ta.
Nan iyayyena suke fada mata cewa ga amanan yarsu nan sun kawo masu da fatan zata rike masu ni amana idan nayi ba daidai ba don Allah ta tsawata man.
Tace kada suji komai ai da na kowa ne da fatan nima zan masu biyayya yadda ya dace karami yai wa babba.
Suka ce insha Allahu in wanan ne baza, a samu matsalan komai ba a kaina.
Nan dai suka mike suka bar dakin ina biye a bayan su sai dakin mai bi mata itama dai acan ba matsala sai cewan da tayi na daiyi hakkuri don su yara ne da su sa, a na dama wa yanda suka girmay ni.
Mun bar dakin zuwa dakin wacce nake biwa ita ma din tana zaune da mutane da yaran ta bayan an gaisa aka fada mata zaman lafiya ake nema a gare mu.
Sai cewa tayi haba zaman lafiya a tsakanin kishiya da kishiya ai sai dai zama na ki goga in goga tasan gidan da ta shigo ai har ta yar da ra kutso kai don kwadai ita da iyayyen ta.
Ai babu wani zaman lafiya illa tazo ga tukunya nan lamba ashirin ta tuka mu tuka da ita don yau an zama daya.
Daya daga cikin yan uwan mama tace to shi ke nan Allah ya bata ikin iya tukawa kamar yadda kowa keyi a gidan.
Muka bar dakin muna jin ta tana yadda bakaken magana wai haka kawai an koso yarinya karama don jaraba an kawo masu a g raino a gida ace wai an basu amana.
Dakina aka mayar dani aka zaunar dani a saman gadona da ya sha gyara nan aka shiga jero min nasiha na zaman lafiya har sai da na rasa na kamawa.
Sukai min sallama suka fice gidan suka bar ni ni kadai a daki nai tsuru tsuru dani kamar manya.
Ban san lokacin da wani kukan bakin ciki yazo min ba ga daki har daki amma ba ango a gurin ba gidan zaman lafiya a nan.
Ina nan zaune a takure ni kadai a dakin naji sallama muryan mama naji uwargidan garbati na amsa mata sallaman ta a sanyaye.
Tana dauke da wani zani kamar bargo na rufa da tocila a hannun ta na mike tsaye ina cewa sannu mama.
Tace a, a Rahama ke kadai ce a dakin ashe to ga kayan kwanciyar angon ki na kawo maki idan kin kare girkin ki zakikaiwa wace zata karbi girki kayan ita ma a dakin ta.
Bayani take min amma gabana sai faduwa yake min a lokacin na rasa fahintar komai da take fada min har ta fita tabar dakin ban fahince ta ba.
Na kalli kayan data aje min a bakin gado tare da kura masu ido ina nazarin su.
Na koma daga can kuryan dakin na zauna sama kujera tare da kara bin dakin wanda yake mallakina da kallo.
Sai faman tunanen irin rayuwan da zanyi a gidan nakeyi ga maganan Sabuwa da ya tsorata ni da tace wai ni kishiya nake a gare ta.
Baifi minti sha biyar ba da fitan mama din uwargidan shi sai na ji motsi alaman za, a shigo dakin nawa.
Mamace again tare da maigidan nasu tana mashi jagora kallo daya zakai mai kasan baida cikkaken lafiya a tare da shi don yanayin tafiyan shi ma kawai ya nuna hakan.
Da sallama ta shigo dakin yana biye a bayan ta ban iya amsa sallaman ba don girman su da nake gani.
Tace Rahama ga anginki na kawo maki kin san dai yanayin da yake ciki da fatan zaki lalaba muna shi dai.
Murmushi naji yayi ta juya ta fice daga dakin na mike daga inda nake na durkusa kasa nace a cikin sanyin murya ina wuni baba .
Murmushi yayi yakai zaune a inda na tashi ya dan kalle ni yace yaya hidimar buki amarya ?
Ban iya cewa komai ba sai sada kaina da nayi a kasa kawai babban rigar dake jikin shi naga yana kokarin cirewa tare da aje hular kan shi a gefe daya.
Da alaman dama kayan sun ishe shi a jikin shi yake cewa dani sai kuma ga angon naki da matsala amarya.
Sai lokacin na dan kalleshi naga duk ya ramay ya fada sosai ga yadda na san shi da farko.
Dan tashi mana amarya ki miko min kayan can na saman gado na sauya ko ?
Gurin da kayan suke na kalla tare mikewa zuwa daukowa na kawo mai na durkusa tare da bashi kayan.
Ganin da nayi yana kokarin sauya kayan ne a gabana yasa nai saurin fita daga kofana na tsaya sai dana tabbatar da ya gama na shiga dakin.
Yace yauwa zo ki zauna ko dauko ledan can ki dan samu kici wani abu daga ciki don nasan kina tare da yunwa.
Nace a koshe nake baba sai da Inna ta tabani abinci naci kafin na baro gida dazun.
Yayi shiru yana kallo na tare da nazarina sai kuma fuskan shi da na dan ga yanayin sa ya sauya a lokaci daya.
Yace amma wanan din hakkin ki ne na yau da ya dace na baki ai na kawo maki.
Nace a koshe nake shiyasa.
Yace to ni miko min na danci kafin na kwanta ko ?
Duk a takure nake a lokacin don yanayin yadda ya ke zaune cikin doguwar rigar jallabiya yasa nake kara jin nauyin shi sosai.
To zo mana ki zauna nan amarya gaki tsaye kin kasa sukuni ko ?
Gabana yai mumunan faduwa nace a raina wanan tsohon may yake nufi nazo na zauna zaman sa, a da sa, a dashi ko may ?
Nayi maza na juya can daga gefe nakai zaune a kasa tare da

Please Login or Register in order to submit comment