Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yace ai ban taba sanin rashin kunyan ta ya kai haka ba sai yau din nan ni zatace wai zata shake ko ta make ni ?
Ita har yaushe ta sanki ta san dadinki haka anty tai dariya tana cewa bar min yarinya na please kada ka damay ta.
Ya dan dago kai yana hararan ta yace cikin kutawa zata gane bata da wayo wallahi.
May zakai mata besty ?
Anty ta tambaya cikin son sanin abinda zai aiwatar a kaina yace ina ruwan ki amma ai naga ni ba ruwana da shiga harkan ta balle ta min wanan mumunan shedan haka.
Idan baka shiga harkan ta ba ai kashiga na anty ta ko itako nice bata so taga kana batawa din.
Bata makin may nayi ni din, tace bukatana a kan ta mana gareka ?
Shine ta fahinci kana sani bacin rai a dan lokacin nan wanda da tasan dalili nasan da ta fi fushi dani bisa gareka.
Ai idan baki barima sani zatazo tayi tunda harkin jawo karamar yarinya tana fadin bakaken magana na batanci haka akaina.
Maynene maganan bataci data fada a nan kuma daga tana fadin ra, ayin ta kawai kuma.
Oh wanan ba bakar magana bane a gurin ki ko har kina dariya haka don bake ta bata ba ke nan.
Haukan Ramane baka sani ba kuma besty ai Rama tunda ta watse mama lauratu a kaina tun tana yar ficiciyar ta nasan bata wasa bace akaina.
Yayi kyau yace tare da mayar da hankalin shi ga abinda yakeyi bai kara magana ba.
Ashe ma kana da layinta a wayan ka ban sani ba ai na dauka baka dashi.
Kallon ta yayi yace kamar yaya ina da layinta bake kika bani ba a baya.
Tace ni kuwa kadai tuna amma bani ba dai kan Rama dake tsoron ka kamar may zanbaka layin ta kuma?
Yace a, a bata tsoro na da batace zata makeni ba ai wanda kake tsoro ai baka ko gigin furta kalami mai sauki a kan shi balle wanan.
Gaskiya ni dai ban san kana da layin ta ba sai yau din nan danagani a wayan ka yanzu.
Cikin basarwa yace to wai samay idan ina da layinta ba, a gida na take zaune ba don na samu layin ta kuma wani matsalane kece dai baki san ina dashi ba dai.
Wani kallon zargi tai mashi tare da kawar da kanta tana mamakin shi ita zaiwa muna funci don ya saci wayan Rama a wayan ta ko may ?
Bayan gashi Rama ta fada da bakinta da layin ya kirata shekaran jiya kenan lanba ya dauka daya dauki wayan ta ranan.
Shine girman kai ba zai iya bari ya tambayeta ba sai ya dauki wayan ta don muna funcin maza ya kwasa.
Baibada kafan ta sake mai maganan ba ita ma bata sake bi takan maganan ba ido tasa mai taga gudun shi kawai.
Amma abinda mamaki fa ji yadda take binshi akan zancen yarinyar nan yake wani basar yau kuma don yana son nombata shine zai munafunce ta damay yake son taji a rayuwan tane.
A yadda ra san shi miskili bata taba zaton zai iya yin haka ba amma sai gashi ita da idon ta ta gan shi kuma ya basar to may yake nufi da hakan ne wai ?
Amma kuma ko ma may ye ai ai yarinyar dai ta fada min in ma har wani magana ne yai mata ai da Rama ta fada mata.
Kawai don kana son jin lafiyan iyalinka shine kuma sai ka munafunce ni don girman kai irin na besty nasan dai ba wani abu a tsakanin su sai tambayan lafiyan su kawai da zai yi, amma yana jin girman kan fada min hakan.

********* ********* *********
Abu kamar wasa sai gashi irin matsin da Ibrahim ke yawan kirana dashi a waya yasa har na fara dan sake jiki dashi a lokacin.
Don zai kira waya yace na bawa kowa su gaisa har gajiye da muke tare sai sunyi waya da ita idan ya kira.
Sai dai a waya kawai nake bari yaji ni bana yarda mu hadu a fili dashi don warning din anty da daddy da sukai min a kan shi.
Hakan bai damun shi bai kuma hana shi kirana bayan dan wani lokaci shi dai kokari yake ya samu ya kafa gwaunatin shi gareni kawai.
A haka har muka sharare kwanaki kwanki ya koma makwanni makwani ya share watan ni muna shakuwa tawaya dashi kawai.
Sai faman shiri muke na dawowan mutanen gidan komai mun wanke mun goge munyiwa shiyan kwalla ni da gajiye gwanin ban sha, awa dashi.
Dawowan nasu a lokacin ya samu nasaba ne da aiken da Alhajin shi ke mai na aurar da yaran yan uwasu da za, ayi.
Ciki harda sisters din Ibrahim su biyu da zaa auran a lokacin dinkin duk event din da za, ayi Ibrahim yai muna shi har Gajiye da anty da bata kasan.
Dawowan dare sukayi muna duk da dare ne bai hana mutum ya fahinci sauyin rayuwan da suka samu ba gaba dayan su.
Abu ga yanayi ba guda ba da nan sun yi kyau sun koma freshen dasu ga lissafina dai watan su na shidda suke ciki dan dama daddy yazo dubai a lokacin suna can.
Muma mun samu labari ne don matan gidan da suka tafi can bamu sani ba saida aka bugo waya ana tambayana ko an bar husna a gurin mu gida kamar yadda daddy ya bukata ayi.
Nace husna anty maman ta bata nan ne take cewa ai basa nan yau kwanan su uku da zuwa Dubai don besty ma yana can wani aiki ya kaishi.
Nace to gaskiya bata nan amma anty shine daddy bai kawo muna ke ba nan tace Rama kiyi hakkuri lafiya na yafi komai a gareku likita nake gani anan akwai magani da alluran da ake min duk karshen wata ne.
Kinga idan nace nadawo na kuma koma akwai wahala haka a gareni nace hakane gaskiya tace to kuyi hakkuri ai na kusa dawowa din.
Sai gashi bayan wata biyu din Allah ya dawo muna dasu lafiya muna zaune falon anty kunnuwan mu yana sauraren isowar su mussanman ma danaga an hada hadari basu iso ba sai nai tunanen haka din ne kawai bazasu dawo a ranan ba ashe sun tsaya clearing din kayan su ne a lokacin.
Da murna mukayi waje da gudu don jin dirin motar su data tsaya sai dana dan tsaya don naga ta bangaren da zanga farin cikin rayuwana tafito a ciki.
Dayan bangaren nagane ta ta bude mota tafito da gudu na kwasa nai gurin ta da murna na na rugumay ta duk wani dadi ya kumay ni sosai a raina.
Gaba dayan su sun yi matukar kyau dasu na karbi jinior dake barci muka shige ciki ni ban ko tsaya gaida daddy ba ma.
Hakan ya matukar ci mashi rai danayi nan muka baje a falo tare da gabatar mata da abinda muka shirya mata don bamu sa daddy zaici anan ba tun da ga matan shi a gida.
Hira ya dauke muna hankali anty bata ko ci abincin ba shigowan daddy part din yasa mu natsuwa a lokacin.
Ya sauya kayan jikin shi zuwa doguwar rigar jallabiya mai laushi da santsi daganin shi a galabaice yake a lokacin.
Kujeran three seater dake falon ya nufa ya zauna tare da dan kishingidewa yana kallon yaran shi.
Sai yanzu dana gan shi abinda ya faru a cikin waya ya dawo min sabo a raina.
Muryan anty naji tana cewa dani Rama kin ko gaida daddy da dawo don banji kin gaidashi ba ni ?
Sai lokacin ya dago daga ruguman da yaiwa Amira yana fadin ta gaidani ko ta shake ni tunda bata kauna na a duniya.
Mikewa nayi tare da tsugunnawa kusa dashi ina gaidashi anty take cewa haba besty aiko Rama mai kaunarka ne jifa yadda muka samay su hankali a kwance ba matsalan komai.
Kaina na sadda a kasa nace sannu da zuwa daddy yaya hanya kokarin kauda kan shi yake kamar bai son ganina a lokacin.
Balle ni dake ji a lokacin kamar kasa ya bude in shige don kun ya
Gaba daya hankalin anty yana akaman ga kunya ya rufeni na rasa abinda zan dafa naji sauki a lokacin.
Banda zabi banda na kwashi tsuman kafana na shige daga ciki don takuran da nayi a gurin.
Ina kuma zaki baki bani abinci ba Rama naji muryan ta tana fada min hakan.
Dole na dawo na shiga jawo kayan abincin a gaban su take cewa zuba ma daddy nasan baici komai ba kila.
Sai lokacin na dan kalleshi don inji may zaice akan abincin yayin da anty sai faman kashe mu da idon ta takeyi kawai.
Na bude kulolin tare da dan tambayan may zan zuba masu kallon shi tayi tana cewa dear may zakaci ne wai ?
Duk abinda aka zuba min zanci yunwa nake ji sosai wallahi ko barci na kasa kwanci nayi don ban samu an hada min komai ba a gidan.
Haka ya sauko suka zauna kasa shi da anty ba su ko hau dining ba suka shiga loda abinci a cikin su.
Sai da anty ta cika cikin ta take cewa dashi kan shi na duke yana faman kai loman tuwo a bakin shi ina nan ina kwasan kaya zuwa dakin ta dasu.
Rama zo mana ki zubawa daddy fruit's ya kara dashi, don nasan yana matukar sha, awan shi sosai a ran shi.
Wani irin faduwan gaba naji irin mai shirin tarwatsa zuciyar bawa a lokacin.
A sanyaye na karaso gurin da suke tare da durkusawa gaban kayan ba abinda nake tsoro kamar ya tayar da zancen kuma again.
Har na bude zan fara zubawa naji yana cewa No tabarshi zan diba kata ta turmujeni dashi kamar yadda tace zatai min ranan.
Dukar da kaina nayi kasa kamar nace wayyo ni Allah a lokacin saboda gigicewa namike da sauri simi simi na bar falon na shige dakin ta ban fito ba har sai lokacin da naji ya fice.
Anty ta shigo daki ta samay ni ina rikici da jinior wai shi ya manta da mu ko duk wanda ya tabashi sai ya sa kuka wai bai san mu ba.
Tace kai jinior kada fa kaiwa Anty Rahma butulci kaine kuma yau kake mata kiuya nace ai barshi in yazo ya sauko nima nace ban san ka ba.
Nace akwashe kayan kingamane a falo tace kwashe kedai Rama daddyn ku ya hanaki tsaya ko ?
Nace cikin shagwaba ai wallahi anty duk kece kin san yana kusa kika barni ina ta zuba surutu ni yanzu ma wani ido zan kallesshi wallahi duk na shiga rudu.
Tace akan may fita batun shi ki basar da zancen kin ji yayi ya gama ya dawo hanya ai baison gaskiyya ne ai shiyasa.
In bashiba may ye na tsayawa mutane wani kwanaye kwanaye can kuma kan gaskiya.

********* ********* *********
Tun ranan bani yarda na hadu da da daddy agidan Allah kuma ya taimakeni bamu ma haduwa koda zai shigo nina fita ko kuma ya fita nina shigo gidan.
Ga bukinsu ya kusa lokacin da anty ta dawo ta fahinci rawan kan da Ibrahim yakeyi a kaina amma takawo ido ta saka min taga gudun mu dashi tun da ban fada mata komai ba gamay dashi din data dawo.
Nadai nuna mata dinkunan dayai muna na event din da zasuyi a gidan su harda nata a cikin tai godiya kawai.
Ranan da yazo gaida anty bana gida shine take mai godiya kan dinkin da yai muna yai dariya yana washe bakin jin dadi.
Tace amma Ibrahim ban son yar haka dakai fa bayan kasan akwai wacce zaka aura a familu ku shine kuma zaka batawa yar uwata nata lokacin.
Ya shafa kai yana murmushi tare da cewa Anty nifa namiji ne ina da right din da zan zabi matar da nake so da kaina ba sai anzaba min ba.
Kuma bayan haka kada ki manta da cewa zan iya aje mace hudu a lokaci daya ida naso yin haka so ni banga wani abin damuwa ba anan sai da sai idan baki son bani ita ne kawai don na rasa gane kan yarinyar gaba daya wallahi gashi ina mutuwan son ta.
Ban sani ba ko akwai wanda take so ne amma kuma ga dan fahintana kamar bata da kowa a kasa yanzun haka.
Anty tace gaskiya Ibrahim don bani kasan ne har haka ya faru daku don bazan ba da goyon bayan hakan ba gaskiya.
Cikin mamaki yake kallon anty don jin kalamin ta yake cewa akwai matsala ga hakan ne ko may ?
Tace akwai shi don akwai wanda Rama zata aura a gaskiya ina ga sai dai kayi hakkuri please.
Nan daddy ya shigo ya samay su don ganin motar Ibrahim da yayi a waje yana ganin shi suka shiga gaisawa dashi.
Yake cewa yanzu naga motan ka dana shigo nasan kana nan ke nan yaya wurin su gwago din ina suna lafiya dai ko ?
Yace a kasalance lafiya suke daddy yace yaya kuma na gan ka a hakan dakai ?
Ya kakaro murmushi a fuskan shi yace nazo gurin antyn nan nawa mugana kuma banji kwari gwiwa ba a gurin ta.
Don Allah bros ka saka muna baki ta yarde min na samu hadin kan kaunan ta don naji ta fara min wani kwanaye kwanaye haka.
Tsaki daddy yayi yana cewa maganan ku ce wanan amma wai kai ina yarinyar da akace an, ma zabi a gida a baya.
Yace yaya shike nan don wanan reason din banda halin na nemi wata da nake so kuma a ra,ayina ko may ?
Matsalarka ne wanan ni ba ruwana da wanan shirmay amma kuma ai naga kai har uku ka aje bros kuma kusan lokaci daya ko?
Anty har hudu ma zai aje aiba daya kuke dashi Ibrahim don Allah na fada ma gaskiya bana son kaja min matsala dani da yarinyar nan ga Iyayyen ka.
Sunyi ta fafatawa da ita karshe dai yamike yai masu sallama don daddy najin su yana ishishire ya dafe goshin shi da hannu daya kamar wanda kan shi ke mai ciwo.
Bayan fitan Ibrahim din yake cewa na dawo gurin maganan motar kuce da suka iso don wa yan nan su damay ni da kai kara kan mota ko yaushe cikin korafina suke na sai wa sister din ki mota ban saya masu ba su.
Nima ai hakan yafi min kwanciyan hakali tunda ba rasawa kayi ba kan ada abinda zaka saya masu din.
Bai tanka mata ba sai gyara kwanciyar da yayi kawai a yadda yake a furin tare da ci gaba da dafe kan shi.

Ibrahim yana fita gidan ya kira wayana ina gani naki dauka don ina hanyan dawowa gida a lokacin ganin yai min kira biyu yasa na daga wayan tare da rage saurin da nakeyi ina sauraran shi.
Yana cewa kina inane nake cewa school yace yanzu naje gaida anty ki sai dai banji dadin zancen da muka tatauna ba da ita don haka nake so idan kin koma kikira tambayan ki nake sonyi tsakani da Allah kuma nake son ki bani amsa Rahama nace sai na isa din zan kiraka.
Tafe nake ina tunanen wani magane wanan yakeson ya tambayeni tsakani da Allah ?
Kodai anty ta fada mai cewa na taba aure ne yake son ji daga bakina idan gaskiya ne tunda ba maiganina ya dauka wai na taba aure a rayuwana.
Naja tsaki nace a raina wani aure macan yanzu dana fahinci may ye aure nake gani aini renoma aka kaiwa Garbati ni kawai a lokacin.
Ban dauka yana part din namu ba shigo da fara, ata a fuska ina cewa anty na nadawo sannu da gida.
Ganin mutum kawai nayi kimkam zaune a part din mu kamar yadda yake abaya.
Ina wuni daddy nace mai cikin sanyin murya batare da ya dago hannu kawai ya daga min yana cewa lafiya.
Nai saurin shigewa ciki ban tsaya ba ban jima da shigowa ya mike tare da fadin ni zan fita ke nan tai mashi a dawo lafiya yafice kawai bau amsa mata ba.
Kirana takeyi daga falo inda take nafito da sauri ina gyara hijjab din jikina na samu daddy yafice a lokacin daga part din na zauna muna gausawa take tambayana Zarah nace tanan lafiya sai dai cikin tane ke bata wahala yanzu ba kullun take samun fitowa ba sosai.
Wai wanan ciki na zamani ko ga wanda ya saba ai wahalane balle mai sabon shiga haka kamar Zarah din abune na farko a gurin ta.
Tace yanzu mutumin ki ya fita daga gidan nan ai nace wake nan anty tace dani Ibrahim mana ban yi magana ba kuma ban nuna mata ai ya kirani ba ma.
Mun dai dan yi hiran yara namike ina cewa wai ina Gajiye ta shiga ne take cewa ina jin tana baya tana aiki a can namike nace ina zuwa anty .
Kayan jikina na rage na gyara dakin kwanan mu tsab nafito na gyara na anty na koma falo inda take zauna waya na samu takeyi na ci gaba da gyara don yamma yayi sosai a lokacin.
Mutanen ki fa za, a fashe masu haushi gobe motar mu zasu shigo gidan nan bayan ta gama waya naji muryan ta.
Da sauri na juyo gareta nace kai anty da gaske amma naji dadin hakan wallahi don ko ranan nan bakwanan sai da akai min gorin shi.
Anty Zulfa sai da nazo kusa inda take da kawar ta take cewa babu dangin iya babu na baba amma kin san sun iya tsafi ai yan kauye ta asirce mijin da matan gaba daya har wanan motar aida gani kin san ba don Allah aka saya mata shi ba.
Anty tai dariya tace kai kishi dangin hauka da kurciya yanzu su gani suke asiri ki kai muna kenan ko ?
Nace Allah ai yasan gaskiya ni ban ma san yadda ake zuwa gidan malam ba ko boka wallahi don ba, a taba zuwa dani ba.
Muna nan ina aiki muna hira yaran suka shigo gida gap da magariba nan gida ya rude kuma na shige na dauro alwala don duk abinda nake bani jiran sallah ya rigani.
Sai bayan na sallamay kamar jira Ibrahim yake ya kirani na katse adduan da nakeyi ina sauraren shi inda yafara da cewa.
Rahama don Allah ina son ki fada min gaskiya don na kasa samun natsuwa a tare dani.
Nace namay fa yace anty ki ta fada min akwai wanda kikaiwa alkawari don haka nafita batunki.
Nace ni gaskiya ban sani ba kila dai itace tai min miji din ko amma kaima ai baka fada min kana da wacce zaka aura ba da farko.
Ko ban da miji wanan dalili ba zai bari na yarda dakai ba uncle don komai nason gaskiya ai.
Wani shock yaji don baiso nasan da zancen ba a yanzu yace kai may zai sa Saade tai min haka ne wai ?
Na fada mata wanan shirmay su hajiyane kawai amma ni mata saina zabawa kaina gaskiya.
Muna nan muna ta takaddama dashi har akai kiran sallah muka kashe wayan .
Ina idarwa ya sake kirana nace don Allah dai the game is over kowa Allah ya bashi rabon sa dama ni ban sa aka ba ai inajin yana fadin Rahama kada muyi haka dake ki tsaya mu fahinci juna na kashe waya kawai gaba daya.

Washegari ba school sai ga motar su ya iso gidan misalin goma na safe ya kira kowan su yazo waje kowace da kalar nata daga ciki akwai ja a kwai baki da issh colour.
Key din bakar ya mikawa anty tace tagode yaba Zulfa key din jan ita ma godiya tayi sai Hindatu ta tashi da Assh colour din.
Take ta nuna ita bakar take so a gurin yace sai ki dawo min da key dina ki jira bakar tazo maki ko ?
Ta gane baka yai mata don haka ta mike a hasale babu godiya tabar falon yaja dogon tsaki yace yayi kyau.
Murna muka shiga yi sosai yace idan suna so su bayar da tsufin kyauta ga wanda suke son ba.
Haka yan uwa da abokan arziki suka shiga zuwa taya su murna da farin ciki samun karuwa da sukayi.
Damun da Ibrahim yake min yasa na kashe wayana gaba daya kada anty fahinci wani abu tai min fada akan shi.
Ya koma kamar wanda ya tabu don ya turo maigadi ya fada min gashi a waje yana jirana bayan sallah magariba ban so fita ba sai da naga anty ta tsura min ido yasa na mike tare da zura hijjab dina na fita daga gidan.
Yana tsaye jingine da bayan motar shi ya harde hannayensa a kirjinnshi na iso da sallamta a gurin ya motsa kamar zai zo ya rungumay ni sai kuma naga yaja baya kadan.
Yana cewa Rahama idon ki ke nan kwatakwata kin hanani zaman lafiya a garin nan kina neman caza min kai haka why why ?
Ki natsu ki bani hadin kai mu cin ma manufar mu na rantse maki yarinyar da suke magana akai banine nace ina son ta ba hada ni da ita iyayye sukayi.
Natare shi da cewa bin nagaba kuma bin Allah ba don haka biyayya ga iyayye yazama dole.
Don Allah uncle ka bari muyi rabuwan lafiya dakai batare da rayuka sun baci ba so kake kajawa antyna wani sabon matsala ga family din ku kuma bayan wanda take ciki a yanzu.
Dagakata don Allah ki saurare ni ina son inji daga bakin ki kina sona ko bakya sona ?
Shiru nayi tare da dukar da kaina ina wasa da yan yatsun hannu na a hankali.
Shiko ya tsura min ido yana sauraren abinda zance mai jin nayi shiru yasa ya maimaita tambayan shi cikin kura min ido.
Kafin nai maga hasken motar dake tafe get din gidan ne da aka dallo muna sai da na kare fuskana don yawan hasken daya kashe min ido.
Shima sai da ya kare nashu fuskan don hasken yai mai yawa a idon shi.
Yace a hasale who is this baste, , , , sai yai shiru inaga yagane motar maigidan ne tafe a lokacin.
Yake cewa haba bros wanan ai bai dace ba gaskiya bazaice bai gane mune a tsaye ba ai.
Nace amma gidan shi ne tunda bai taba ganin hakaba anan dole ne ya bincika ko su waye a gurin ai.
Ya furzo iska a bakin shi tare da dunkule hannun shi yana kaiwa daya naushi yake cewa ke nake saurare fa.
Nace wanan duk babu shi don baida amfani jin amsa ta kawai kowa yai biyayya ga magaban ta shi.
Yanisa yana cewa naji zan baki lokaci zan dawo naji amsan da kike yake

Please Login or Register in order to submit comment