Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abba itace fa kagan ta nan amma shine wai yake daukan magana a shirmay nakeyi yin shi daddy ne yace damu ku dan bamu guri Gajiye mu gana da Abba haka yasa nafi kowa saurin mikewa na bar gurin muka shiga daga ciki don dama nasan gidan muna zuwa da anty wani lokaci.
Dakin wacce nake ganin ita ce uwar gida a gidan muka fara shiga muka gaida ita sai dayan dakin don su biyu ne a gidan.
Kamar sauran gidaje su ma da alama ba wani zaman hadin kai kamar sauran gidajen da ake tsara akidar kishi a ciki.
Muna barin gurin daddy yace ban san abinda ke damun saade ba ta matsa min akan maganan yarinyar nan har tana kokarin ganin mun samu sabani a tsakanin mu.
Murmushin manya Abba yayi tare da jawo basket din abincin da mu kazo dashi a gaban shi yana dan budewa.
Yace in ban da abinka Alhaji Yusuf yo tunda kaji har mace ta bude baki da kanta tace ka aura mata kishiya ai tana da hujjan yin hakan.
Ai sai ka bari mu saurari hujjan ta muji yanzu ko anty ta nisa tace hujja na akan haka daddy ba wani dalili bane sai ganin da nayi rayuwan yarinyar ya cancan ci hakan a gare mu.
Kamar yaya Saade inji Abban ya tambaye ta sai hawaye ya fara zubo mata a idon ta a hankali tace dashi.
Abba idan kai la, akari da yadda yanayi yake yau ciwo gobe lafiya yarana suna bukatan taimako suna bukatan kasancewa tare da mai son su tsakani da Allah.
Shi kan shi ai yana bukatan kwanciyan hankali tare dashi wanda kwata kwata tunda na fara ciwon nan babu shi a tare dashi.
Amma idan ya auri Rahama ko bayan bani ina da yakinin yarana dashi suna da mai rike min su a tsakani da Allah kuma ai Abba wanan abin da nake son yayi kamar taimakon kan mu da kan mu ne za, a yi shi.
Ni dai take jiyewa nikuma wallahi harga Allah na yafe ma ya auri yarinyar nan ta zauna damu babu komai a raina na burbushin kishin ta a tare dani sai kuka ya kubce mata a take a gurin .
A, a a haba Saade may yakawo kuka kuma ana magana na fahinta anan magana zaki tsaya ayi a fahinci juna ko ?
Abba ya kasa fahintar manufata akan yin wanan shawaran danayi ni kuma ina jiyewa makomar bayana ne a gidan.
Haba Saade ai ciwo bashine mutuwa ba ga yadda wa yancan likitocin naku masu jajjayen kunnuwa sukace a baya wa ya dauka zaki kai wanan lokacin.
Bagashi Allah da hikimar shi ba har da rabon haihuwa kin samu a hakan kuma aikwai may yine bayan Allah.
Ki kwantar da hankalinki kiyi nazarin abin da kike kokarin shiryawa kada daga baya kuma kizo abin ya damay ki .
Aure ne fa shi sha, ani na aure ana son kwanciyan hankali da natsuwa a cikin sa kada kuma ayi garaje abu yazo ya koma maki ciki daga baya.
Abba na riga nai nazari sosai akan halaiyar yarinyar babu wani matsalan da za, a samu a ciki da yardan ubangiji.
To maji ita yarinyar tasan da wanan magana ne a yanzu haka ga abin da kike shirin yi a kan ta ?
Tace cikin girgiza kan ta bata sani ba Abba don ina son ne shi mu daidaita dashi kafin na tun kare ta da zancen tukun.
Don insha Allahu Rahma mai kaunata ce bazata ki abin da nake so da ita ba tunda taimako na zatayi ga hakan.
Murmushi Abban ya dan karayi yace kai Saade ban taba ganin mace maitaushi kamar ki ba don taushin ki har yafi na mahaifiyar ki baki rageta da komai ba a duniyan nan.
Yanzu kai Alhaji Yusuf kaji hujjan ta dabara ta rage naka tun da ita ke bukatan yin hakan gareta.
Daddy ya numfasa da karfi yace Abba kaji abinda take fadi wai hujjata ke nan a koda yaushe.
Ita burin ta ke nan shiyasa take kokarin hasasa muna rashin zaman lafiya akan wanan magana da ta a ranta don nata manufan kawai.
Tace eh shine burina don ni abinda zai fishe mu nan gaba nakewa bawai son zuciya ba.
Hakan ne naga yafi dacewa ayi don samun mafita a rayuwan mu shiya kaji na matsa da maganan.
Abba yace wanan shine abin da ake fadi idan kana son kama uwa to kaso dan ta da zuciya daya shine nan.
Ita wanan yarinyar na lura ta yi amfani da imanin ki ne gurin gwadawa diyan ki son da take masu da zuciya daya amma baki ganin idan ta shiga ta samu nata watarana zata iya watsar da naki yaran ta kama nata.
Daddy yace hakane Abba ba wani abu takewa wanan ba nikuma ban dauke shi a hujjju da zata sani abin da ban da niyya ba akan shi.
Yanzun dai da ita da kai kuje ku kara sasanta kan ku a kan zancen amma ni Alhaji yusuf ai naga wanan kamar kai aka taimakawa.
Don hujjan Saade gaskiya abin dubawa ne kaje kai nazari zanji daga gareka yadda kuka kaya daga baya.
Allah ya tabbatar da Alherin sa Allah kuma yau maku albarka yasa wa zuria albarka dayyaba.
Suka karba da amin Abba daddy yace amma ni Abba naso ne ai mata magana ta fita wanan zancen don Allah kada mu samu matsala akan shi nan gaba.
Abba ya daga mai hannu yace na fahinci manufar hikiman saadatu ga hakan kaje kai nazarin maganan ta da basira ko zaka fahinci manufarta anan.
Sukai sallama ta mike tashiga gida gaida gaida mutanen gidan kamar kullun babu wani kyakyawan taro da ta samu garesu sun dai gaisa da ita kadaran kada ham tai masu barka da sallah tare da fatan Allah ya maimaita muna takawo kudi ta basu barka da sallah sukakarba da godiya babu addua a kai mata kin shi sai su don kishi harda matatta.
Muna dakin sister din ta murja don school din mu daya da ita muna dan mutnci a school da ita.
Haka yas in nazo gidan sai nanemay ta mun gaisa da ita duk saurin damukeyi.
Su ma yan uwanta tai masu alheri muka fito bayan daddy ya bugo mata waya yana waje a lokacin.
Tun shigowan aanty gurin mu na fahinci tayi kuka sai naji ba dadi a raina don kusan haka take yanzu kawai sI naji ba daddy a raina.
Wani irin hattenes din daddy naji ya tsirgu min a zuciya na ban san rikicin da ke hada su da anty ba yanzu yake yawan bata mata rai haka ko wani lokaci.
Hakan ya haifar min da kuncin zuciya a lokaci daya wanda ya sa naji sam bani ma kaunan ganin shi a lokacin.
Don idan abin sa naki ji ni a yanzu shine a taba anty da yaran take mutum zaiga bacin raina lokaci guda.
Tunda muka shiga motan har muka kai gida babu wanda yai magana a cikin mu ana tayawa ni na fara fita ban tsaya jiran kowa ba na wuce ciki fuuu dani ina jin Amira na kirana amm ban tsaya ba na shige dauke da jinior a hannu na.
Ina daki naji shigowan su suma na fara kokarin cire kwaliyan dake jikinana sarka da awarwaro hannu na sai dai ban cire tufafin ba .
Nan sauran yaran suka samay ni muka baje dasu kilishin da Abba ya bamu ne suke ci don duk mukaje gidan sau ya bamu kumshin kolishi mai yawa mu zo gida dashi.
Gajiye ta shigo dakin tana cewa wai may kuma ya samay ki ne Rahama naga tun a gidan su hajiya yanayin ki ya sake lokaci daya.
Babu komai gajiye haka kawai najini ahakakilagajiyan aikin danayi ne ya ja min jin hakan.
Gajiyan aiki kan nasakihaka akwai dai koma may ye kiyiwa kanki fada ki daina saka damuwa a ranki don Allah, kin yi karama da tunane balle ma ban ga abinda akai maki ba da zaki saka damuwa a ranki.
Nace gajiye bana son ganin bacin ran anty na ko kadan wallahi baki lura da yanayin anty na ba da tashigo cikin gidan su kiduba irin yadda matan gidan ma suka karbe ta kamar ba yar gidan ba gajiye ai wanan dole mutum ya kamu da ciwo.
Zama tayi kusa da ni tare da kura min ido tace a hankali kamar may rada tace Rahama ki rufawa kan ki asiri kada ki jefa rayuwan ki ga matsalan da bai shafe ki ba don kin ga wanan mtsalace da ta shafi rayuwan auren su da gidan ba abinda ya shafe ki bane.
Lalai Rahama ke yarinya ce karama har yanzu baki san mayye duniya ba amma ina ke ina saka damuwan wani a ranki har ya damay ki haka.
Yau na tabtar da cewa yadda hajiya take kaunan ki haka ne kema kike kaunan ta da zuciya daya a ran ki.
Altine ta fada min dama irin kaunan da kukewa junan ku a baya ban tabatar da hakan ba sai zuwana gidan nan na fahinci cewa abinda ma altine ta fada min a kan ku yafi karfin hakan.
Don haka dai don Allah kibi a sannun kada yazo ya zama maki matsala daga baya.
Ina sauraren ta har ta kai karshen maganan ta na saukar da ajiyan zuciya a hankali nace nagode Gajiye tace dole ne na fada maki gaskiya don ke tawa ce Rahama.
Mikewa nayi zuwa dakin anty na samay ta ta idar da sallah tana zaune ishishire da kafafuwan ta tana dan murzan su a hankali.
Ina shiga nake cewa antu kafan ne ke tauna kuma take cewa wallahi yanzu nake son kiran ki dama ki dan shafa min magani ga kafan.
Maganin na dauko nafara murza mata kafanta a hankali tana dan lumshe idanuwan ta da alaman tana jin dadin yadda nake mata din.
Maigidan ne ya shigo ya samay mu a hakan yake cewa tun bai karaso ba kafan ne kuma ya fara tauna take cewa shine nace Rama ta tausa min tun bai damay ni ba.
Kamata dai yayi nai muna bukin wani sati mu fita zuwa ganin likita tun bai matsa maki ba shiyasa ban so kiyi azumin nan ba wallahi ke kina ganin kamar kin samu lafiya ne amma kika dage sai kinyi din.
Yai dan tsaki tare da dan dukawa daidai saitin kafan nata shi ma yana cewa gaba daya ne yake tauna ko iya nan ne kawai.
Ganin ya tsugun na gaf da mu yasa ni dan mikewa da nufin barin gurin sai yake cewa No zauna abinki zan fitane may kuke so a sayo maku ne zan dan fita .
Tace Rama akwai abinda muke bukata ne a nan ko nace sheltox ne kawai nake ganin ya kare muna tace sai may kuma nake cewa inaga madaran daya rage zai kai kwana uku kila.
Tace amma ki tuna kada kuma daga baya aza a tuna ya mike yana ce ta barshi dai zan fita kawai na sayo komai.
Ya mike tare da fice tace dashi sai kadawo ke nan baza mu rufe part ba sai ka dawo din yace yayi kyai.
Yana fita ina abinda nake ban bari ashe ta kura min ido ni ban sani ba sai naji tana cewa dani Rama may kuma daddy yai maki kike sha mai toka ne haka wai ?
Gabana ne ya fadi don ban yi zaton zata fahince ni ba zancen Gajiye ne ya fado min a rai da take cewa kada na shiga maganan miji da mata don ban san abinda ya hada su ba ai.
Nake cewa anty may kika gani ne halan tace barshi kawai amma naga daddy bai canci hakan ba ne na kara bata raina nace amma anty may kike mai da koyaushe yanzu yake yawan ganin laifinki haka bayan irin kokarin kyautata mashin da kikeyi ko yaushe a gidan nan.
Kai Rama dama nasan maganan ke nan don kinga nai kuka dazun komay ?
Magana ce kawai mukeyi dashi shine haushi ya kamani har nayi kukan amma ba wani abu bane da kike zargi.
Rama wai yaya zakiyi randa akace babu antyn nan taki ne wai a duniyan nan gabana nane naji ya wani mugun faduwa ras ras mai makon nai magana sai kawai hawaye shar yazo min mikewa nayi zuwa dakin mu can na kafa kai ga filo ina ta rusan kuka sai danayi mai isata nan na dunkule har barci ya dauke ni a gurin.
Gajiye ne ta rufe part a ranan bayan daddy ya dawo ya kawo muna sayyayan da yayo muna ko wani part ya kai masu nasu kayan bukatan .



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANI HAKKIN AMANA YA NA KAN KI DON ALLAH NA GANIN KI YAR UWA, , , , , , , , , ,

30
Wasa wasa jikin Anty yaki dadi kwanakin nan haka yasa na mayar da hankalina gurin jinyan ta a lokacin.
Mun godewa Allah bai wani tashi mata sosai irin da yake matukar kaita kwance ba sosai.
Haka yasa koda yaushe daddy yana , makale da ita koda yaje abuja ne zai dawo bayan kwana biyu sai shirin fita sukeyi waje.
Ranan da yai wani dawo ne yake sheda mata ranan jumma,a zasu wuce don haka ki shirya.
Nan aka shiga shirin tafiya wanda akasari nice akewa sayayyan abinda za, a bar muna na amfanin mu a gidan.
Komai da zamu bukata ba sai mun takura ba an saya muna a gidan an zube muna shi.
Ana gobe zasu tafi ina manne da anty ban son abinda zai daga ni kusa da ita ko kadan.
Take cewa taso ta yaye jinior amma daddy yace da saura nace anty aida kin yayye shi kibar min shi zan ji kewan shi sosai idan kun tafi.
Take cewa ai da zata barshi ne sai dai ta dauko mama Altine tazo ta zauna damu a gida kada ya bata min tsarin karatuna.
Tun da asuba sun shirya tafiya, idon mu biyu har yaran take cewa dani tare da miko min kudi masu yawa karbi wanan ki aje don bukata idan ya taso maku bana nan.
Nace da ita anty wani bukata zamuyi da kudi bayan komai kun tanadar muna a gidan akwai shi tace karbi dai ku aje indan an kwana biyu ki dinga kai yaran yawo kuna sayen abinda suke bukata kada ki bari su shige kewan komai nace insha Allahu anty.
Muka fito da kayan su waye nan tace damu zata ta sallami sauran mutanen gidan nan ta wuce tare da yaran ta kowani part sai da ta shiga tai masu sallama.
Muna tsatsaye a haraban gidan tafito sai naji wasu hawaye sun zo min a lokaci daya naji wani tukukin bakin ciki da tashin hankali ya toshe min zuciyana idona ya rufe anty na fadin to Rama ubangiji Allah ya sada mu da alherin sa don Allah kiyi ta hakkuri da yaran nan na barki maki su amana a hannun ki.
Koda ta juyo don mu hada ido sai taga kuka nakeyi nan ta tako ta karaso gare ni ta rungumay ni take itama ta fara kukan a wurin.
Kuka mukeyi sosai sai da muka ba duk wanda ke gurin tausayi gajiye itama kukan takeyi tana dan share hawaye da bayan hannun ta.
Daddy yana zaune cikin mota ta ya kura muna ido tausayi mu ke bashi, sosai yana mamakin bai taba ganin so da shakuwa irin haka ba a rayuwan wasu kamar namu.
Ganin bamu da niyar sake juna ga yara har sun fara kuka yasa yafito daga mota hannun shi na saye a cikin aljihun wandon shi.
Yazo inda muke a hankali ya jawo hannun matar shi yana ce is ok please kuyi hakkuri hakana, kamar wacce zata tafi, baza ta dawo ba wanan kukan haka.
Ina tsaye muna kallon suka ja mota aka fita dasu daga haraban gidan ranan haka muka wuni suku suku damu.
Da kyat na samu yaran suka sake jikin su don ban sha wani wahala ba gurin ganin na samu sun sauko.
Da dare ina shirin kwanciya ne wayan anty ya shigo min ina ganin bakon nomba nasan cewa itace na dauka da murnana na yaran suka taru suka rufa min muka shiga gaisawa dasu.
Har daddy sai da ya gaisa da yaran yai hira dasu sosai kamar ba kudi ake kashewa ba.
Washegarin tafiyan su na shirya yaran don an koma schools dani dasu bamu dauki lokaci ba mukai sallama da Gajiye tare da kara jaddda mata takula ma anty da part din ta duk da na rufe duk inda ya kamata na rufo a part din muka fice zuwa makaran ta.
Can muka hade da Zarah take ta min korafi wai anyi sallah amma naki neman ta har aka kare wasan sallah.
Hakkuri na bata tare da fada mata cewa cewa anty na bata da lafiya yanzu haka ma an fita da ita zuwa ganin likita waje.
Ta tausayawa anty tare da fatan Allah ya bata lafiya takece aiko taga na ramay sosai a lokacin.
Murmushi nai mata don bani wani dogon magana da ita wanda ya shafi shirin gidan su anty na.
Haka mukaci gaba da gudanar da rayuwan mu dagani sai yaran babu rana daya da Hindatu ko Zulfa suka leko part din da sunan sunzo su duba mu suga wani hali muke ciki nida yaran .
Da farko ina shiga na gaidasu da kwana amma da naga bamu gaban su gaba daya sai muka daina ba ruwan su damu muma ba ruwan mu dasu a gidan.
Yau ban shiga school ba muna zaune a falo Gajiye ta mike tana cewa zata shiga ta hada miya don tayi abinci tunda rana.
Hankalina naga handout dina da nake karan tawa jikina saye da wani bakin, dongon riga ya dan matseni sosai ya fitar min da surar jikina da kyau kaina babu ko dan kwali akai.
Naji ana nocking din kofan part din mu kafin na nace yes naji an turo kofan an shigo .
Dago kai nayi naga waye mai shigowan a lokacin wani matashi shine ya shigo saurayi ne da ganin shi gashi da matukar kwarji a tare dashi.
Abu daya ne ya dan raba su da daddy shine shi gajere ne amma fari ne sol kamar daddy.
Kamar su da daddy yayi matukar yawa sosai da gani ba sai an fada ma ba akwai alaka ta jini a tsakanin su.
Karasowa yake tsakiyan falon haka yasa namike tsaye daga inda nake zaune tare da mashi sannu da zuwa.
Kallon mamaki nake mai a lokacin don yadda ya shigo muna kai tsaye ga shi da ganin sa ka san boko ya huda shi sosai.
Fuskan shi a sake yakarasa ya samu kujera ya zauna sai bayan ya zauna yake cewa dani barka dai yan mata nan na shiga gaidashi a cikin mutunci.
Bin part din yake da ido zuwa can yake cewa ya naji gidan kamar masu gidan basa nan ?
Na bashi amsa da cewa eh basa nan sunyi tafiya sai mu da yara ne kawai a gidan.
For how long zasu kai a can na bi bayan kujera ina cewa ina ga zasu dauki lokaci a can don sunje ganin likita ne a can.
Matsalan Saade ke nan na gyada kai a hankali tare da fadi a raunane da eyyh.
Yace Allah ya bata lafiya ?
Nace amin yamike yana cewa ni zan koma dama na sauka garin ne nake cewa bari nazo na gaidasu.
Nace to barin kawo ma ruwa ka dan sha ko kada ka tafi baka sha komai ba agidan.
Yace na dauka ai rowa zakiyi min don naga kamar kina tsorona baki sanni ba ko ?
Nace gaskiya ban san ka ba.
Yace nima ban san ki ba ai ke sister din Saade ne ko ?
Na ce dashi eh anty nace ita.
Yace ni brother din Yusuf ne maigidan nan mamana da dadd din shi thesame mother thesame dadd suke.
Nace Allah sarki bari na dauko ma ruwan na wuce zuwa kitchen can na samu gajiye nake fada mata anyi bako ne yanzu.
Na dauko goran ruwa da kwalin juice hade da cup a wani dan ture na kawo mai falin.
Bayan na aje mai na koma inda nake zaune da farko na zauna a kujera muna fuskantar juna dashi.
Yace amma ban san Saade na da sister ba haka da farko ?
Nai dan yake ina cewa bazakan sani ba don ba a nan nake zaune da farko.
Daga ina kike daga kai nayi ina kallon shi don tambayan yai min tsauri da yawa nagaji ma da hiran don ban saba tsayawa magana da maza ba mai tsayi.
Na bashi amsa a takaice tare da daukan takardana ina cewa daga kauye nake.
Anya kuwa sam bakiyi kama da yar kauye ba nagani a nan ?.
Nace shi dan kauye har wani kama ne dashi dama can ?
Yace well koma dai daga ina kike ni dai nidai nasan bada kauye kike ba don banga alama ba anan.
Ya na tsiyayya ruwa a cup yake cewa koma may ye dai ni dama nazo ne na duba su don na dade bani kasan nan shekara na bakwai bana nan sai shekaran jiya na dawo shine nace bari nazo na duba su dama.
Nace Allah sarki tare da bude takarduna danake karan tawa ya dauki cup din da ruwan yana tsiyayawa a cup din a hankali yakai cup din bakin shi, yafara shan ruwan yana min kallon kurullla na dago kaina don jikina ya bani yana kallona ne dama.
Yai saurin kawar da idon shi a gareni yayi murmushi yana cewa kina karatu ke nan naga kin mayar da hankalinki ka alama handout ne kike karan tawa ko ?
Cikin basarwa nake cewa dashi eh ina karatu ne anan b u k nake ya mike daga inda yake ya nufo gurin da nake zaune tare da mika hannu alaman na miko mai takardan ya gani.
Ya dan duba yana kada kai yace ok da alama dai zamuyi babban likita ke nan a gidan nan nan gaba.
Nace eh to kusan haka din ne in Allah yardan muna da hakan, na bashi amsa.
Yayi murmushi tare da cewa wonderful .
Shekara nawa kenan kike yanzu da farawa nace ?
Nace karshen shekara ta biyu nake zan shiga na uku ke nan insha Allahu nan bada jimawa ba.
Masha Allahu hakan yana da kyau Allah yasa mu ci amfanin aikin da ake karantawa a family baki daya.
Nace amin a sanyayye tare da gyara zama na saboda yadda yazo gap dani ya tsaya a gaba na haka.
Nan yake cewa karatu sai an daure balle irin wanan naku mai tsawon shekaru haka don haka sai ki dage ki mayar da hankalinki sosai don amfanin ki nan gaba.


Please Login or Register in order to submit comment