Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manya ba sai ansan da nema ba sai dai aji daurin aure kawai.
Take labari ya karade gari mama na gyaran dawan da zatai madu abincin dare sai ga larai kawar ta tazo da labarin .
Nan suka shiga gulma akai suna fafin dama kwadai yasa ta watsar da auren ta don taje hangen nisa gashi ta fada gidan mai gari ai taje su kulu matan maigari sunan nan ta samay su.
Lairai tace amma dai kin san taci aba dai ko a hankan gidan maigari fa akwai hutu lauranta kuma akwai ci da sha ba kamar ku nan ba.
Sheri kuma zakiyi min inji mama tace ai ba sheri bane sai gaskiya ina zaki taba hada auren maigari dana gidan ku laurantu kuma ko acan fa amarya take.
Gashi duk matan shi sun girmay mata ga shekaru kinga ko yanzu amarya take shatafa kuma ta bar maki sudaden mijin ki ki jika kisha ke kadai yadda kike so.
Larai nagane dai magana kika zo sola min ba wai gulma ya kawo ki ba tace ai babu soka magana anan sai gaskiya ke dama maigarin kika cuna ma Lawisa ai da yafi mata auren wanan tsohon da takeyi sai aukin susuka kawai kamar bajimi.
Ran mama duk a hasale yake dama basu haduwa gulman su basuyi fada ba tsakanin su haka dai suka rabu baram baram.
Da dare da baba ya dawo mama ta tare shi da zancen auren inna da maigari.
Ran baba yai matukar baci da jin wanan labarin yace amma ko maigari bai kyauta min ba yanzu haka zai min na saki matana ina kokarin mayar da ita sai ya aure ta.
Nan dai mama taita zuga shi wai sai ya kwace diyan shi kada ya yarda aje agola dasu gidan wani yace ai haka za, ayi bazan yarda aje min da yarana yawon agolan gidan masu gari ba.
Mama tace ita dai Rahama ka barta can gurin yawon duniya ke nan kuma ko ?
Kamar yaya yawon duniya kuma shi akace maki tanayi a can inda take yanzu ne ?
Idan ba yawon duniya taje yi ba gidan yan uwanka take ko na uwar ta da zata je ta share guri ta zauna can ba labarin komai tare dasu.
Shiru baba yayi yashiga nazarin maganganun da mama ke zuga shi akai bai sake tanka mata ba don ran shi yai kololuwan baci sosai a lokacin.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA HAKKIN AMANA YANA KAN KI YAR UWA DON AMANA NE ALLAH NA GANIN KI YAR UWA, , ,

24
Monday mun koma makaranta bayan an gama shagalin buki na watsar da zancen auren Inna da na saka a raina har yaso ya damay ni sosai.
Banda kawa ko daya ni kadai ce ke al, amari na don babu wacce na sani a school din balle na je na daukowa kaina wahala.
Idan ban class ina massalaci naje yin sallah sai kuma idan anzo daukana da yamma zan koma gida.
Da zaran na dawo banda wani time sai zancen aikin gida girki da gyaran shiyan mu.
Sai ma wani lokaci kowa yayi barci an barni ina aiki ni kadai don gudun kada na makara washefgari ke sa sai na rarage aiyukana nake kwantawa.
Gashi yanzu na san gari wani lokaci ni anty take aike gurin yan uwanta ko abokan ta ban ta samun matsala da kowa nata ba sai mutun daya daga cikin sisters din ta da tace dani don Allah idan mijinta yana gida anty ta daina aiko ni.
A gabana ta fadawa anty hakan sai naji anty tayi dariya tace ina da gaskiya na sister in bake ba wa zai aje wanan zukekiyar budurwa haka a gidan shi mijin shi na gani kullun ya kyaleta.
Don dai daddy su Amira ba irin mijina bane aida yanzu ya fara kai mata hari bada sanin ki ba na dauka zanga canji kan wanan maganan da sister tayi a kaina amma sai naga anty ko a jikin ta ita.
Haka yasa naiwa kaina kiyamallaini idan daddy yana gari bana yarda mu hadu dashi ta ko ina ina part din mu kumshe sai ko idan nafito zuwa school anty bata taba hankalta da hakan da nakeyi ba don ita zuciyar ta fes yake akaina.
Wasa, wasa sai da Zulfa ta kwashe wata daya agidan su mama Zulai ta ga abin bana wasa bane ta nemi sulhu da kanta don da farko takafe sai daddy yaje biko da kan shi ta fada mai son ranta Zulfa zata dawo dakin ta.
Sai taga sam diyar ta bata gaban shi idan sun tambaya sai dai taji ai yazo ya tafi ko ace ai baya ma kasan sam ga baki daya.
Wanan karon ma basu kasan shida Hindatu sun tafi kasashen turawa don sun kai sati da tafiya gaba daya yaran suna gurin mu a gida.
Hindatu bataso barin yarta hannun anty ba amma daddy ya kafe ga haka shine ra, ayin shi sai dai idan zata fasa tafiyan ne ga baki daya dole ba yadda zatayi ta bar yarinyar a hannun anty.
Mama zulai ta je gidan hajiyan su daddy inda hajiyan ta kira yan uwasu kaf suka hadu a gidan ta sannan aka aika kiran mama Laraba.
Tana zuwa ta fahinci zance ne akan yaransu zasu aiwatar a lokacin, da farko mama zulai ta soma yabawa mama Laraba magana masu zafi sai da hajiyan ta tsawata mata.
Take cewa idan har sulhu kikazo nema ki bari ai magana na fahinta a tsakanin ku don wanan abin da kuka dauko hanya ne na koyawa yaran mu wani mugun akida a tsakanin su.
Aure dai ne Allah ya hada a tsakanin yaran mu sai hakkuri da junan mu yanzu kada ku bari shedan ya rude ku mu bata zumuncin mu.
Gaskiya wanan karon hajiya ta turza don bata tsamaci jin haka ba daga hajiya din.
Dole ta sasauta kalamin ta ga yar uwarta nan mama Laraba take cewa Zulai ni banda abincewa don ko a haka alhamdullahi don zumunci yai min rana banda da namiji babba kuma banda arziki amma dan yar uwana ya gwada min ni wata abuce mai daraja a cikin ku.
Ban sa Alhaji karami ya kori yarki a gidan auren ta ba asalima ni baiji wanan magana daga bakina ba don dashi da Hindatu duk diya nane.
Yadda zan dauki Alhajin haka zan dauki hindatu a matsayi ya a gare ni idan naga tayi abinda ba daidai ba na fada mata ta gyara don goben ta.
Cin mutuncin da kukai min keda yar ki daga gyara kayan ka bai taba damuna ba a raina don ni na tsaya a matsayin da Allah ya tsayar dani a cikin na bandashi.
Kuma na dade ina bin shi Alhaji karami yayi hakkuri ya dawo da matar shi dakin shi a wuce gurin wanan dalilin yasa yanzu ma ya daina zuwa gurina ya kuma ko daina kirana ga waya yadda yake min kullun.
Don haka idan har kuna zargina akan wanan zancen kun dai dauki Alhakina ne kawai shi Alhaji karami baya manta mafari ne shiya sa yai min wanan gatan da kuke gani kamar asiri ne mashi na jaye shi dafa alaka da kowance daga cikin ku don har wasun ku na cewa na asirce ce shi harda ita yaya ina kokarin rabawa da dan ta.
Wanda abin ko kusa ba hakana bane shakuwan dake tsakani na dashine tun yana dan karamin shi yakai mu ga haka yanzu ada ai bai wanka ya bushe yana gurina kuma kowan ku ta sani anan.
Sai yanzu ne da ya zama wani abu kuma zan mai asiri na jaye shi daga mahaifan shi komay ?
Muryan mijin hajuya ne baban daddy ya leko falin yana cewa yin haka ma babban kuskure ne gare ku gaba dayan ku nan wa ya gwada wa Alhaji shi dan shi a baya kamar yadda laraba ta gwada mai.
Laraba zata iyayiwa Alhaji laru da kudin ta ba tare da mu nan mun sani ba sai daga baya mu samu labarin hakan a furin shi ko a wani wajen sai yanzu da Allah ya maidashi mutum ne kuke son ku nuna mata bata isa ba da danta.
Kinyi kuskure Zulai gurin nuna son kanki dakikayi wa yar uwarki idan dashi ba jarumin maza bane yai maki haka kina ganin diyan ki kaf akwai wanda zai kara kallon daya daga cikin ku nan da daraja a idon shi.
Sai sauran uwayen dake zaune suka ce hakane fa Alhaji gaskiya anyi babban kuskure sai dai Allah ya kyauta kawai za, a ce a gyara gaba.
Alhaji yace uhum haka nake sin ji don fa abinda kukayi ba abin alheri ba ne don takai har yarki ta fara kyamatar shigan ku gidan dan ku duk kun san da hahakan.
Nan sauran suka shiga fadin albarkacin bakin su akan haka mama zulai ta kwatakes ba bakin magana don babu gaskiya.
Karshe dai Alhajin su dady ne ya shirya tsakanin tare da kara fahintar dasu karfin zumunci da kuma sakaci da zumunci sukai godiya aka fahinci juna yasa akakira Zulfa dake dakin hajiya tana sauraren su tun farko ta roki iyayyen nata gafara kamar yadda mijin ta yake bukata haka akayi ta tsugunba tsakiyan su tace tasan tayi kuskure don Allah a yafe mata sukai mata dan nasiha tai godiya tamike tabarsu a gurin.
Sai lokacin Alhaji yace tau yanzu laraba aiki ya rage naki don kin san halin dakin da tauri tsiya sai kikirashi don yaji da kunnuwan shi gaku a hade an sulhunta asamu yarinyan nan ta koma dakin ta hakana.
Shiya kira daddy da wayan shi ya na ganin kiran Alhajin ya dauka lokacin suna tare da hindatu kwance saman gado tana dan shafan shi a hankali kiran yashigo mai.
Da sauri ya daga yana mai gaida mahaifin nashi cikin ladabi nan yake ce mai bani ke magana da kai ba uwar ka ce Laraba da yan uwan ta gasu ya mikawa mama laraba wayan takarba da sallama.
Saida ta tambaye shi uaya suke can yace Alhamdullahi tace ya gaida hindatu din nan take cewa Alhaji karami zancen matarka zulfame gamu nan gaba dayan mu mun hadu a gidan yaya kan maganan don Allah muna mai baka hakkuri komai ya wuce tsakani ka maida matar ka dakin ta hakana don Allah.
Yace mama idan fa zulfa da mama basu baki hakkuri ba kan cin zarafin da sukai maki wallahi bazan hakkura ba.
Tace haba dana komai ya wuce nace ma gamuna gaba dayan mu yaya da Alhaji sun sulhunta komai a tsakanin mu ai.
Yace to shike nan ta karbi makullin ta a hannun Saade zan fada mata inda na aje mata su ta koma kafin na dawo.
Mama Zulai bataso ace diyar ta takoma ba haka zikau sai yazo yaje inda suke amma jin amsan shi yasa tasan ba inda zai tafi ya gama maganan shi ke nan .
Mama tai mashi godiya tare da mai nasiha ya tai hakkuri da iyalin shi don mata sai hakkuri komai girman su sukai sallama ya kashe wayan kowa najin yadda sukayi ko banza mama lataba ta kara wankuwa a zukatan masu zargin ta a cikin su.
Nan Alhajin su daddy yace gobe yake so mama zulai ta mayar da zulfa dakinta don yau yamma yayi shiyasa ba zau ce ta koma yau din ba gidan ta.
Akai sallama bayan yai wa kowan su alheri suka watse kowa ta kama gaban ta cikin jin dadin samun sulhu a tsakanin su yanzu.
Hindatu dake kwance a gefen mijinta tana jin komai ranta ya baci don dai ita bataso dawowan Zulfa ba don zaman kishi ke nan bataki ace anbarta daga ita sai shi ba agidan duk sauran su watse ba.
Balle wanan yanayin jin dadin da suke ciki a tafiyan da sukayi ji take dama a kullun su kasance a haka tsakanin su dayafi mata komai dadi a rayuwan ta.
Ya fahinci bataji dadi ba don yadda ta sauya a lokaci daya ga yadda suke dafarko dashi.
Yace kai mata mata wai duk haka suke da bakin kishine gaba dayan su ko may babu wacce ke son ta bude ido taga wata a tare dashi dan dama Saade ce bata faye wanan halin ba sosai a kan su itama tana dan taba nata idan abin ya mota mata ai?
Mu dai washe gari sai ga yar aikin Zulfa tashigo tana cewa mama Amira ance na karbo keys a hannun ki already anty ta kwaso keys din yana hannun ta ta ce min na dauko saman drower din ta na bata na dauko na mika mata tafice daga part din.
Nace wa anty sun dawo ke nan anty tace ai kin ga shahidi tunda sun karbi key nasan sunyi yadda yake bukata ne shiya sa ya sauko yanzu.
Basu da tunane ne abinda yai mama laraba shiyasu don abu daya suke a gare shi amma sai take ganin ita uwar yanzu tafi mama laraba power a gare shi dole ta haukan ta ta taka yadda take so.
Ba afi minti goma ba sai ga yar aikin ta dawo tace ance tazo ta dauki hanifa anty tace dani kwaso masu kayan su ki basu ki kira mata yar tazo.
Na kwaso na kira hanifa tazo ana kiran ta tana fitowa taga yar aikin part din su sai ta saka rikici tana fadin ita bata zuwa katshe ma ta ruga da gudu ta boye wani gurin na daban.
Anty tace a barta idan tai barci za, a kawo matar tafita can sai ga zulfan da kanta tashigo ba laifi tayi sallama nan suka gaisa da anty tana wani cicika tana basarwa ita kadai tace ina Hanifan take ne ?
Ai da ki barta idan tayi barci sai Rama ta kawo maki ita zaifi don yanzu idon ta biyu rikici kawai zatayi maki.
Tayi mana wayo gareta balle ai da batace zata zauna nan ba na dawo dama rashi na a gidane ai ya kawo tana inbanda nakasa may take anan din haka ?
Nakasa kuma anty ta tambaya cikin mamaki tasake cewa Hanifa din ce ke nakashe anan kowa?
Ni dai tazo muje ban son dogon zance daga dawowa na yanzu don Allah kuma ace ga abinda mutum yayi again.
Anty tace kina so kan Zulfa inda a nakshe take ai da yanzu da kiia dawo batace zata zauna nan ba taki binki wai may yasa ku baku son a zauna lafiya ne wai.
Lafiya lafiya dawa dake aike ma kin san ba zaman lafiya tsakani na dake Saade nida kika aure ma mijin da zan aura tun muna yara saboda son kai irin naki kika raba ni dashi da karfi da yaji har kina ganin akwai wani zaman lafiya tsakanina dake yanzu.
Tau ai sai kice mijin naki ya sake ni tunda nakine ban sani ba na shiga rayuwan ki dashi kinga sai kisa ya sallamay na bar maki mijin ki.
Ban san yaya akayi ba daga inda nake tsaye nace anty babu inda zaki din an samay ki da mijin ki ne wallahi wanan ai rashin mutunci ne duk wahalan da akai maki da ta kuma kizo kina kokarin zagin ta haka ?
Ke kefa baki da kunya waya saka bakin ki a cikin zancen mu ni ba saar yin ki bace yarinya don da yarki nakeyi itace saana na.
Rama yi shiru kyale ta neman nayi takeyi kije kiji da abinda ke tare dake ni banda likacin haukan ki yanzu.
Aiko ranta yai matukar baci da kalman haukan da anty tace da ita tafara balai wai sai anfito mata da yarta kowa ma ya rike nashi ai kowa na dashi.
Tafara shiga dakuna neman Hanifa anty ta mike tsaye tace wanan kuma shine bazan lamunta ba kada ki kara shiga min daki ko daya anan .
Tace idan na shiga fa may zakiyi tace wallahi wallahi zan maki abinda baki taba zaton ina iya maki ba yanzun nan kuwa.
Ke bafa ku kadai ne kuka iya hauka ba kowa ma ya iya cin mutunci Zulfa ina raga makine don zumuncin dake tsakanin ki da mijina kawai.
Mijinki gyara dai malama kice mijin mu yanzu kuma ai an wuce wanan tun 1900 sai dai kice mijin mu kawai.
Yarinya daine ko to bazan bayar ba tunda bake kiban ita ba ki bari wanda ya kawo ta yazo ya dauke ta da hannun shi idan kuma kin isa bisimilah ki shiga min daki ki gani wallahi ke har tijara kika iya ko hauka haka.
Sunyi cin mutunci sosai da gori sai da anty ta daga waya ta kira mijin nasu niko ina tsaye gefe jira nake kawai ta taba anty ta sha kokuwan yan kauye dama na dade ban yi ba tun da na bar zuwa diban ruwan da mama ke turani na barkokuwa a can bakin rijiya.
Ganin sun fara magana anty tana cewa heart beat kaiwa matarka magana ta fita min a part kafin nai mata cin mutuncin dayafi wanda tazo min dashi.
Yace a hasale Zulfa kuma again wai may zulfa take daukan kanta ne wai nan dau anty ke fada mai yadda sukayi ni dai ban san lokacin da ta sulale ba tabar part din da anty zata barni da naja yar ta nakai mata abinta don ba wani tsiya take muna ba ban da ahagwaba ga fitsarin kwance sai na saka mata permpers da girman ta.
Wayan mahaifiyarta ya kira a hasale tana dagawa yake cewa mama kijawa yar ki kunne wallahi nagaji da fitinan da take saka zuciya na koda yaushe a gidana da matana wallahi zan iya datse iyagiyar auren ta akaina bada bata lokaci ba don ta kaini makura wallahi.
Hankalin mama zulai yatashi tana bashi hakkuri bai tsaya sauraren ta ba ya kashe wayan ya kira mama laraba da hajiyan shi cikin hasala ya fada masu zai saki zulfa yau din nan.
Gaba dayan su su uku sai gasu a gidan nan aka tarasu falon anty ana tambayan baasi anty ta koro magana ta fada masu.
Hajiya tace Zulfa banda abinki ai da yarinyar bata jin dadi da batace bata komawa gurin ki ba yadda kikayi baki kyauta ba gaskiya ina laifin wanda ya rike ma da.
Sai kawai ta sa kuka tana cewa ita komai tayi sai ace batai daidai ba kowa ta fahinci yanzu an tsane ta bamu tsane kiba baki fadan kan gaskiya ne zulfa.
Maihaifiyarta tai mata tas tace kuma tabar yar in mijin su ya dawo shida ya kawo ta ai dole ya dauke ta ya mayar mata da abinta can.
Suka ba anty hakkuri don a zauna lafiya suka tagi kowa na fadin albarkacin bakinshi uwar taja mata kunne ra fada mata yace zai sake ta ayau din nan.
Tace saki fa mama tace wallahi haka yace min jin kalman saki yasa ta shiga hankalinta da dare sai gata wai tazo ba anty hakkuri anty tace ai ya wuce ko a faki gaba dai don yaro na kowa ne ai.

****** ********* ******

Rashin dawowan dady ne ya hana tafiyana gida gashi munyi hutu kamar yadda anty tace zan tafi gida idan mun samu hutu lokacin har anty tayi arbain ko da haihuwa amma daddy bai dawo ba suna can da hindatu kasan turawa.
Ni dai ban san may kuma zan tsaya jiran Daddy yi ba ni da zani gida gurin iyayyena a lokacin.
Basu dawo ba sai ana saura sati daya mu koma school suka dawo da safe suka sauka garin.
Gida ya kaure da murna don duk yara suna gidan a lokacin ana hutu ko ina makarantuni gaba daya.
Nidai ban saka su a ido ba ina ciki ina aiyukan na lokacin Farida ta shigo gurin mu tai muna kwana biyu a bakinta nake jin wai hindatu ta hadu tai wani irin kyau da ita har daddy din shima yai kiba ya kara haske sosai.
A raina nace ai dole ya katare ya bar min anty na nan da wahalan yaran da ba a ko gode mata ba dole suyi kiban su ba suna can hankalin su a kwance abinsu.
Ta damay ni da zancen su wanda ita bata san ina taya antyna kishin hakan bane a cikin rai da ta isheni da zancen na ce haba Farida labarin ya isa haka mana yanzu bagata ta dawo cikin yan uwa anjima kadan kina iya jin muryan ta inda sune masu fitinan tsiyan nan ni fa basu burgeni don rashin mutuncin su.
Dariya tai min tana cewa ke ko ba ai maki abin arziki idan baki so ba fa Rahama ?
Na dauki kayan wankin yara dana kwasa na shige dasu dakin mu na barta nan zaune a falo tana kallo.
Yaran duk basa nan suna gun daddy da ya dawo haka yasa nai aikina a tsanake har tsawon dan lokaci na koma falo na kwashi na anty na nufi dakin ta dashi.
Ban san yana cikin dakin ba a lokacin don da ban shiga ba ina shiga ban jira amsa sallama taba na fada dakin ina cewa anty wai ko kin san yau saura sati da yan kwanaki mu koma schoo, , ,
Maganan ta makale min ganin daddy danayi zaune tare da matan shi a saman gado tana kwance ya zauna ya raba hannayen shi a tsakiyan ta yadda take a kwance din yai mata runfa suna magana.
Da sauri na juya zan koma inda na fito muryan anty ne kece ina kuma zaki rama kun gaisa da daddy ne da ya dawo.
Cikin jin kunya ga kaya a hannuna haka na tsuguna ina cewa sannu da dawowa daddy andawo lafiya yaya hanya ?
A hankali batare da ya gyara zama a yadda na samay su ba ya amsa min gaisuwa na.
Na aje kayan da sauri na juya zan fita daga dakin muryan anty ne ke cewa Ramana don Allah duba can ki dauko coffee ki hada mashi mai zafi kwarai.
Nace tau anty na matsu na bar dakin don a takure nake nako kasa daga idona na kara kallon yanayin da suke ciki a lokacin.
Nace akwai ma ruwan zafin dana jona yanzu zan hada abu dashi tace ta juyo min sai ki hada mai please .
Na koma kitchen da sauri na juye ruwan da har ya tausa ko a cikin dan karamin flaska din da take mai amfani dashi na hada cup na kawo masu shi.
Yanzu na samu sun gyara zaman su tana zaune da kyau tana bawa dan ta nono shi kuma yana wasa da kafan yaron saida na tsaya daga kofa aka bani izinin shigowa dakin na shiga.
Tace dani yauwa sannu Rama da kokari don Allah hada mashi coffee wai dashi zai tafi can gurin shi.
Na hada kamar yadda ta umurce ni nace da ita an hada wanan karon shine yai godiya yace nagode Rahama ya mike tare da mika hannu na miko mai.
Har yakai kofa take cewa dashi dama Rama ta matsu kadawo tana son shiga garin su ta dubo gida nice na hanata kada su tafi su barni ni kadai don nasan mama ma kafar Rama kafarta.
Tsayawa yayi tare da juyo yana kallon

Please Login or Register in order to submit comment