Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muna sannu da zuwa tana daki sai yar aikin ta kawai na gani a waje don matar babu ruwan ta da saka kanta ga harkan kowa ba kamar hanne da tai zama da ita bace a baya wanan ta girmay wa hanne sosai tasan ciwon kanta.
Ni dai na shiga daki naji fitina ya barke a tsakanin su inda nake jin muryoyin su yana tashi.
Ban fito ba amma ina jin komai tunda gida daya ne tana fada wai banfi kowa ba da zai barni ina fita wurin aiki.
Sai ga Aisha ta shigo dakin nan take labarta min maganganun da tayi da bana nan.
Nace kyaleta sai dai kare ya mutu da haushin kura don nagaba yayi gaba ko na baya sai labari.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,
83
Ranan sunyi fada sosai a tsakanin su ina jin yadda take surfa min zagi daga dakina amma ban taka masu ba tunda badani take masifan ba.
Saboda yara na fito falo don na duba su don tunda na dawo ina dakina ina hutawa saida nai sallah na fito inda suke na duba su.
Muna zaune tare dasu suna min hiran baba yadda ya kwashe a makaranta karon shi na farko.
Munyi dariya sosai muna cikin dariya ne sai gata ta fito daga dakin ta a hasale take don har lokacin tana jin masifa a tare da ita.
Wa za,a gwadawa boko ni da naga alhudahuda sarkin karatu ana gwada min yin karatu mace bata fu mu balle a fifitata a gare mu sai a san wanda za za, a bari gadin gida.
Ni dai ban kulata ba taci gaba da cewa in asiri ne ai gida mutum yazo mu zuba kafan wando daya da mutum mu gani a gidan nan.
Kamar nace da ita ai munzuba ba yau ba tunda wani dadi naji a wurin ku tun shigowa na gidan kowa da irin nata surfan a kaina ai.
Amma saboda maganan da mukayi dashi a mota naja bakina nai shiru ban taka mata har tayi ta gaji ta shige ciki.
Case dai har yakai gun iyayye ban san yaya akayi ba kwana biyu naga sun shirya a tsakanin su nace miji da mata ke nan tsakanin su sai Allah.
Naci gaba da zuwa aikina hankali kwance sallah babba na gaba towa don yazo gab a lokaci sai shirye shiryen sallah ake ko ina.
Haka ne muma a gidan mu sai faman shirin sallah mukeyi ba babba ba yaro kowa na zumudin zuwan wanan lokacin kamar yadda ko wani musulmi ke fatan ganin shekara ta zagayo irin hakan.
Ranan ya dawo yake fada muna mu shirya ranan laraba zamu tafi kano sallah gaba dayan mu gidan nai saa ina up a lokacin da tafiyan zai kama ke nan.
Don har mu tafi mu dawo ina da dan lokaci a wanan season din na bukin sallah da za, a yi din.
Nan kowa ya shiga shiri ni dai a raina ban so ba don nasan babu abinda zamu je yi sai fitina a tsakanin mu a can.
Amma da yake babu yadda zan yi dole na hakkura na shirya ba tare da na nuna komai ba a fili.
Ranan da zamu tafi lokaci da da duk wani musulmi idan ka gan shi busy yake ba kama hannun yaro ga kowa.
Tafiyan da zamuyi ranan ya kama nice keda girki don haka nai muna abincin da zamuci a mota don yara.
Mun fito har lokacin hindatu bata fito ba sai na zauna gaban motan don ganin nice mai girki sai bayan wani lokaci tafito tana shan kamshi.
Gaban motar inda nake zaune tazo ta tsaya a kaina ni dai bance da ita komai ba sai shine bayan ya gama rufe ko ina na gidan ya karaso gare mu.
Yace a, a ya baki shiga ba ke yake cewa da ita tai mai wani irin kallo tace a ina kake son na zauna yace ba wuri ne a motan halan ?
Tace a saman kanta kake son na hau na zauna ko may ko baka gani ne kai ?
Yace ya salam hindatu may yasa kike son rigima ne ke ko yaushe ina kin san komai kuma kusan kece kika kawo wanan matsala mai girki ce zata zauna a gaba indan irin tafiyan nan ya kama .
Tace nan ai ba kano bane ko kuma ai acan din ne nai magana ba a abuja don haka sai kasan yadda zakayi.
Ya dan kallo inda nake zaune na rungumay haidar a jikina yana shan nono muka hada ido naga yanayin shi ya shiga rudani sosai.
Tsam na daga yaron daga jikina na fito daga motan na bude gidan baya na shiga tare da rufo kofan da nake daga gefen shi.
Ta sauke ajiyan zuciya cikin fisgan jikin ta takai zaune sai ya zagaya ya zauna mazaunin driver don shi da kan shi zai ja motar da muke ciki inda Hamza yazo zai kwashi yara da yan aikin mu.
Sai daya zauna ya juyo inda take zaune yace koma baya ki zauna ke ma, tace saboda may ?
Yace haka nace ko baki ji bane ba matar da zata juyani yadda ranta ke so wallahi kin ji na fada maki.
Bata fita ba tai zaune ya jiwo idanuwan shi sun canza kala yace ba dake nake magana ba kina bata muna lokaci haka ?
Taja tsuki ta fice daga motan ranta a bace ta dawo inda nake zaune a baya ta zauna tare da jawo ganbun motar da karfin tsiya ta rufe gwaram.
Ya kada kai tare da kutawa ya fara jan motan sannu aa hankaki muke fita garin har lokacin ba wanda yai magana sai dai idan zai tsaya ya sai wani abu ya fita daga motan kuma komai daban daban yake sayowa kowan mu baya hadawa.
Ba mu isa kano ba sai uku na rana don haka kowan mu a gajiye yake duk da haka ban wuce part dina ba sai da na fara zuwa mu gaisa da anty.
Ina ganin ta gabana yai mugun faduwa nace anty lafiya kike kuwa tai dan murmushi tace Rama ina ko naga lafiya yau na kai sati biyu ina fama da jiki sosai amma yanzu Alhamdullahi na samu sauki ai.
Nai mata sannu tare da tambayan mutanen gida tace duk suna lafiya ban jima ba na mike zuwa nawa sasshen don na dan huta.
Na samu gajiye a falo tazo taron mu muka gaisa nai mata yaya gida ta kawo abincin da tai muna don taron mu nan na bar su Aisha suna ci na shige ciki don na rage kayan jikina.
Nai wanka nai sallah na sauya kayan jikina zuwa dogon riga na fito falon don na danci abincin da akkai muna.
Gajiye ta sake dawowa nan muka zauna muna ta zabga hira da ita nacee gaskiya Gajiye banji dadin ganin anty ba ga kwanaki da muka zo tayi kyau sosai amma yanzu duk taa ramay wallahi.
Tace bari hajiya ai yanzu ma taji sauki ke nan idan da ga satin da ya wuce ne ai abin ba kyau taji jiki sosai wallahi.
Nace Allah ubangiji ya bata lafiya tace amin na zauna naci abincin sai dai ba wani mai yawa ba sosai ba don raina ba dadi tun fitinan mu na safe.
A bakin Gajiye nake ji irin yawan fitinan dake faruwa a nan din inda take fada min komai nace kai kishi dai baiyi ba wallahi gashi kuma a jinin mu yake.
Ban fito ba sai bayan ishai don mun dan tsaya yan gyare gyare a shiyan don wuri ba mutum raggage ne sosai ba kamar yadda idan akwai mutum yake tsab ba.
Na samu anty zaune da yaran ta sun kewaye ta sai faman zuba mata hira suke Nasir yana kwance a three seater ya daga kafan shi daya ya tokare bango dashi.
Ina shigowa bayan nai mata sannu tare da mata mun samay su lafiya sai na juya wurin jinior daya manne ma jikin nata.
Nace kai kuma big man may ye haka baka ganin bata jin dadi kawani manne mata haka kamar zaka koma ciki da kai ?
Ta dan shafo kan yaron tai murmushi tace kai haba Rama yaro yaga uwar shi kice kuma kada ya manne min nace yana nan yana aikin shi zuba ko.
Tai dariya tace yana bani labarin fitinar uwar su ne kai wanan bata bari a zauna lafiya ki dai ta hakkuri da kowa Rama nagode kwarai wallahi yaro sai hakkuri kokai uwar shi balle yana ganin baka haife shi ba.
Murmushi nayi na dan dukar da kaina nace anty aiko ba wani matsala a bangaresu wallahi don suna da dadin zama gashi suna maida hankalin su sosai ga karatu.
Tace kai Rama ai in kan yaran nan ne baki taba bari a fadi don Allah Rama yadda kika rike min su amana ko bayan raina ki rike min su haka don yaro sai hakkuri .
Nace haba anty tare da abinki zaku raka har tsufa insha Allahu Allah dai ya baki lafiya tace kai Rahama ho tsufa yanzu ganin tsufa ai sai dace.
Tace da ace ba a gunki suke ba hankali baya taba kwanciya da zaman su can da wata amma kinga yanzu ko da banji komai a wurin su baa hankalina a kwance yake don ko a nan suke ya tsaya haka balle ni yaushe nake ta yaro ma can .
Kin ganshi harda wani sallo yazo min wai shi a can mummy su bata bari su kwanta sai sunyi wanka da dare sai sunyi kaza da kaza don iyayi.
Dariya nayi kawai tace ubangiji ya raya maki naki zurian su taso tare da yan uwan su kunya naji ban iya cewa amin ba a fili a gaban ta.
Sai kuma muka dauko hiran aikina take cewa dani kwanaki waban da ta maida kowa irin ta ai ta bugo tana fada muna wai ga abinda yai maki ya barki kina aiki mu muna gida.
Don haka sai mu hada mai kai tace idan ita ta manta aini bazan taba mantawa ba ina aikina amma saboda su dole na aje nabi ra, ayin su.
Sau nawa yana bamu kudin jari tunda sunce su sana,a zasuyi amma kudin ya kare har dubai ta fara zuwa ban san ya akayi ba kuma ta daina.
Ita kanta yasha bata kudi fiye da kowan mu idan sunyi tafiya amma sai a rasa ina kudin ke shigewa haka ?
Yanzu dai naji akan aikin ki wai suma sai ya nema masu aiki yace ya basu right kowa ya nema kema bashi ya nema maki ba ai.
Nai murmushi nace anty ni bani bakin ciki da aikin kowa wallahi tunda ba a jikina kudin zaifito ba balle.
Ranan munyi hira sosai har dare ya soma nai mata saida safe na koma wuri na inda dama a gajiye nake na samu har yaran sun kwanta muka rufe part din sai safe.
Da safe na fara raba dan tsaraban da nazo dashi na aikawa Zulfa abinda nazo masu dashi ita da yarta nai mamaki da tace a dawo min dashi sun gode don ba halinta bane.
Ashe tasha zugi sun hada kai kan zancen aiki akan lalai suma sai ya nema masu aikin yi kamar yadda nakeyi haushin hakane yasa tace a dawo min da kayana.
Ban damu ba na karbi abina na ci gaba da aikawa masu so suka karba da godiya da murna da fatan alheri.
Kagin a fara kiciniyar aikin sallah na shirya da yamma zuwa gaida iyayyen daddy da sauran mutane kada nazo ban samu zuwa da wuri ba nai laifi gin hajiyan daddy din don tana son a bata girma sosai a rayuwan ta.
Na samay su zaune a falo na gaidasu taja yan jikokinta a jiki tana masu wasa tace dani Rahama ga yaran kamar sun saba dani mana basu da kiuya ko kadan.
Muna gidan sai ga daddy yai mamakin ganin mu yace nan kuka zo ashe nace eh muka gaidashi Alhajin shi yace shi yasa nake son yar tawa ai akwaita da hankali.
Kaga ta kawo muna yara mu gan su gasu har suna batun kwace min mata na don tun shigowan su suke manne da ita sai shigowan ka suka yo gun ka.
Murmushi yayi Alhaji yace yaya jikin ita Saade yayi sauki ko ?
Yace ta samu sauki ina son idan an gama sallah na fita da ita waje don sai nake ganin wanan ciwon nata ne ke son dawo mata kuma.
Subbahanallahi Allah dai yasa ba shi bane don bani son wanan mugun cutan yace kagab ta nan Alhaji dama zuwan da muka taba yi lagos ta sayo mata wani maganin gargajiye shi tai amfani dashi tun lokacin ya lafa.
Yanzu kuma ai Rahama batayi karan banin zuwa bata wani magani ba kuma can tunda ta riga ta zarga ta inji hajiyan daddy ke fadin hakan.
Alhajin yace haba saboda may ai tsakani da Allah ta ke mata taimako ai bai gajiya ga bawa idan ya tashi yi.
Nace ai a lagos ne mun shiga kasuwa naga maimaganin yana talla nai mai magana yabani yanzu ma ban gane wurin ai don an dade.
Allah dai ya bata lafiya inji Alhaji ya fadi cikin damuwa da abin sai hajiyan tace dama ina son ganin ku gashi Allah ya kawo ku yau.
Tace ba komai bane sai zancen sauran matan ka akan aiki da yar uwar su keyi su ka hana su korafi yai yawa daga iyayyen su don Allah suma ka sama masu aikin a bar wanan zancen hakana inda hali.
Yace hajiya ni banaki bane ai tun farko idan baki manta ba sai da na basu baki sukace Sana,a za suyi su naba kowa jari don uin sanaan don dama ni ba aikin nake so ba gare su.
Hajiya macr mai hankali da sanin ya kamata ake bari ta fita aiki ba wacce zata fita ba kimtsi ba sanin ya kamata ba don nasan kan aikin nan zamu iya samun matsala dasu watarana.
Tace na daice ka sama masu aikin kowa ya huta don uwar ita hindu har waya ta bugo min tana son yi min tijara ranan.
Don haka kaji abinda na fada ma yace itama bani na sama mata ba ai don haka kowan su ya gwada saan shi ya nemawa kan shi don ni yanzu ban ma san ta idan zan fita neman wani aiki ba can.
Kada ki manta da halinsu hajiya sai na samo kuma suce ai bashi suke so ba zan daibawa kowa baki ta fara idan ta samu din shike nan ko ?
Ni dai ina duke ban dago kaina ba a inda nake ina sauraren su ban jima ba namike nace zan je na gaida Abban anty dasu Zarah.
Sai dare muka dawo gidan a gajiye na dawo din haka ko wurin anty ban samu shiga ba ranan mukai wanka bayan munci abinci sai barci.
Ranan jajibur ma ba sauki a gidan fitina ne akan wai an yanka sa sai yabawa maigadi mijin Gajiye kafafuna da kai don ya san raba shi gareshi fitina ne.
Aiko suka ce dawa Allah ya hada su bada shi ba don gajiye na yar uwana zai masu haka aiba su kadai bane mabukata akwai masu so da yawa a gari .
Shine ya kawo masu fitina akayi kaca kaca a tsakanin su nikan ban fito ba sai labari nake ji don muna ciki muna aikin sallah saboda su Aisha bazasu iya min yadda nake so ba idan na barsu.
Sai da mama Laraba ta shigo gidan ba shiri ta tsawata masu suka daina wanan fitinan da suka sa a ran su.
Bayan tagama dasu ne ta shigo wurin mu take cewa jiya na shiga barka ance kin shigo baki samay ni ba ai nace eh mama tace harda tsaraba haka maiyawa Rahama mun gode Allah ya raya maki yan diyan ki ya tsare muna su nace amin mama don yanzu mun saba saboda dan zaman da mukayi da ita.
Na dibar mata nama mai yawa nace taje ta kara don ya yanka masu sa ita da sauran yan uwanta taita godiya tana cewa ke gashi kin bani naman da saboda kai da kafa wasu ke ta masifa a gidan.
Na dai yi dan murmushi kawai tare da tambayanta su anty Fatima yar ta yar Farida tace suna can uguwar su mai nisa shiyasa bata ganin mutane ai yanzu tunda suka koma can din.
Tace bari ta shiga taga jikin anty nai mata sai anjima ta tafi ta dan jima wurinta suna hira kan matsalolin gidan ta tafi daga baya.
Washe gari sallah muka tashi mun gama aiyukan mu don tun dare muka hada komai shiyasa muka samu saukin aiki ranan sallah.
Daddy ya shigo da kanshi har part din nawa yana saye cikin wani shadda gezena sai maiko take faman yi fara tare da yaran shi maza yayi don fita sallah idi.
Ya samu na shirya yaran ya dauki haidar bayan mun gaisa mun mashi barka da sallah.
Suka fice gidan aiko yana fita da yaran ya samu Nasir da jinior na jiran shi ya fito saiga hindatu ta rako wata kaunarta da aka aiko gunta.
Ta ce lalaima don bata san da kayan ba sai yau da ta gani a jikin su munafunci dai baya karewa a gidan nan su diya matan sai a kaisu a bola a yar mu gani.
Bai kulata ba ja yaran shi suka fice don kada su makara basu samu sallah idin ba a ranan.
Dun kai awa biyu a waje ashe saida ya biya dasu gidan mahaifanshi da wasu yan uwa yai masu barka da sallah ya dawo gida.
Part din anty ya fara shiga yai mata barka da sallah tana ganin haidar a kafadan shi yai barci tace a, a babana daga massalacin kuma kai barci ta mika hannu ya miko matashi ta shinfide shi a wurinta.
Ya dan jima ya fito ya shiga wurin Zulfa da hindatu nice ta karshen zuwa ya dubani nai mai barka da sallah ina tambayan yaran yace haidar yayi barci suna gurin uwar su ta shimfide shi can.
Naji dadin jin haka don alama ya nuna ba karamin saukowa anty tayi ba sosai ya dan zauna kamar yadda ya zauna suka gausa da kowa ya fito.
Haka akaita aikin sallah ban sha wahala ba don ga gajiye da Aisha da helen da Atika su ne karfin aiki sai fama da wayan mutane nakeyi masuyi min barka da sallah.
Sai wani lokaci aka kawo min yaran Amira tai masu wanka wai sun bata jikin su da maikon nama.
Muna cikin magana naji hayaniya ya kaure wai ashe kan girki ne hindatu tace ita zatai girki ranan zulfa tace bata isa ba ai can suke zaune da miji don haka ba ruwanta da girkin kano.
Sun jima suna fitina shiya shiga tsakanin su ya raba fitinan yace baza tayi ba dani da ita ba maigirki a garin nan sai idan mun koma can don haka bai son wani fitina kuma.
Tai masifa babu kunya gajiye na mayar min nace babu gwani ke nan a garesu don basu bar kan su ba ma balle wani shetin daine aka kullawa a tare.
Dare yayi na shiga gun anty na gaida ita sai na samu ta kwanta naga wata yar dattijuwa tazo wai gwagon ta ne muka gaisa da ita na karasa gun anty nace anty yaya dai tace dan nama biyu fa naci shine jikin nawa ya koma min ba dadi wallahi.
Nai mata sannu na dan dade a wurin ta nai mata Allah ya sauwaka na tafi don yara saboda na bar haidar baiyi barci ba a lokacin.
Washe gari sai dana karya naje gaida ta tana zaune a kasa ga cup din tea a gaban ta bata sha ba sai sanyi yakeyi .
Nace anty kisha mana kada yai sanyi tace bari Rama bana jin dadin komai jikin nan nawa sam ba dadi wallahi da kyat na samu tasha tasha magani.
Na jima na barta don ta dan huta na wuce wurin daddy na gaidashi suna tare da Zulfa na gaidasu a tare ya amsa min itama dai ba laifi ta dan amsa a dakile.
Yake cewa dani yana son mu shiga gurin su baba kafin mu koma sai dai bai san lokaci ba amma mu zauna a shiri dai.
Naji dadin jin hakan nai mai sallama na fita daga wurin su din na zagaya inda su Aisha ke aiki a gurin gajiye na dan zauna tare dasu.
Yinin ranan dai haka naji bana jin farin ciki a tare dani haka dai nake daurewa ban yi magana ba da kowa.
Zarah ta shigo mun dade muna hira shiya mantar dani komai da nake ciki a gidan mun sha hira ta tafi.
Da dare na leka anty ban dade ba na dawo don kaina yana min ciwo a lokacin na kwanta sai barci ya dauke ni har suka gama suma suka shigo suka kwanta.
Can cikin dare naji ana dukan kofana da karfi na falka kusan tare muka fito falon da Aisha dake barci a dakin su.
Nace waye yace bude Rahama nine na bude da sauri don jin muryan daddy da nayi ina budewa nace daddy lafiya dai ko a wanan lokacin.
Yace Saade ce jikin ya tsananta mata sosai ina son muje asibiti yanzu da sauri na koma na dauko hijjab dina don dan rigar barci ne a jikina dama.
Na bi bayan shi da sauri muka nufi dakin tun a kofa kanajin kugin ta tana nishi ina shiga naga halin da take ciki take jikina ya mutu don abin ba kyau .
Nai mata sannu ta dago kai da kyat tace dani Rahama kin tashi kinga jikin ya tashi kuma again tun da safe haka nake yanzu ne ya zama worst haka kuma.
Nai mata sannu ta karba tace dani Rahama don Allah ki ta hakkuri da diyan ki gasu nan zan bar maki amana a hannunki da fatan zaki yafe min.
Hawaye suka zubo min nace haba dai anty don Allah ki bar wanan magana duk zafin ciwo ne daddy yace ku kamata muje gun mota da sauri.
Dagota da zamuyi sai ta rike min hannuwa na gam tana son yin magana ba baki kuma gareta bayan maganan da tayi din.
Innalillahi kawai nake kira nace daddy kama muna ita don Allah daddy ka yafe ma anty don tana cikin wani stage yanzu mawuyaci ya juyo da sauri yana kallon mu ya karaso ya rike ta kafin wani lokaci tafara dan shakuwa tana murmushi ga magana abakinta amma baya fita batafi minti biyu ba Allah ya karbi abinshi.
Salatin da na saka ne yasa shi kara razana ya ruvumay ta ajikin shi yana fadin Saade na yafe maki na dan taba hannun tanaji ina ba motsi rai yai halinshi a saukake ta cika a dakin ta.
Wani iri kuka ne yazo min da ban san na iya irin shi ba ma nace yau nawa ya samay ni anty kin tafi kin barni da babban nauyi a kaina haka ni Rahama na shiga ukku.


Please Login or Register in order to submit comment