Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gayu wai ace kawayena ne su.
Gashi duk wacce zata shigo da ledan ta na gift zatazo min duk wanan jigilan da nake bai hanani yawan zuwa duba lafiyan anty ba ina kuma shiga na bata magani idan time yayi.
Walima sosai mai gyara harka ta hada min inda aka gaiyyato malami yazo yaiwa mata wa,azi akan zamantakewan aure a wurin da hakkin iyayye da yayan su kuma.
Nan ma anci ansha anyi photuna aka kuma watse lafiya ranan yan garin mu suka so komawa amma yamma yayi nace su bari su kwana da safe akaisu kasuwa sai su tafi.
Sunyi amanna da shawara na haka suka baje akaci gaba da sha, ani dasu sai dare kawaye na kowa ya kama gaban shi nan aka shiga gyaran wurin dan a samu wurin kwanciya.
Ni dai har akaci aka sude banga ko mutum daya ba daga ban garen matan gida banyi wani dogon mamaki ba don nasan za, arina dama da hakan.
Muna daki ne zaune ni da su Rukkaiya da Suwaiba daddy ya shigo part din bayan ya gaisa da mutane a ya nufi dakina din.
Sun gaisa da yan uwa na kuma gabatar mai dasu tunda sunayen su yake ji sai yake tambayan su mazajen su ?
Sun fice sun bamu guri mu gana dashi nan yake tambayana muna dai lafiya ko ban tare da wani matsalar komai ko ?
Nace lafiya muke sai yake tambayana may za, abawa yan gatin mu idan zasu koma, ne yace wancan karon da anty ki mukai shawara, sai nace ko yanzu ma da ita zaka kara shawara daddy aita inda aka hau tanan ake sauka .
Yafice zuwa dakin anty ban san yaya sukayi ba sai yake cewa dani ta na fada mai kawai abinda ya dace nan na fahinci akwai matsala ke nan nace dashi yabasu turamay da dubu biyar din su ashirin da biyu ne dama sukazo har kanne na maza da akazo min dasu su biyu.
Washegari sai ga Anty Aisha da kyautan tukwaicin ta kawo masu nan aka shiga murna naba mama Laure da amaryan baba suwaiba da Rukaiyya zanuwa a boye kada sauran ran su ya baci.
Rukaiyya na dankawa duk wanda yagani yai magana sai tace kayan sako ne zatakaiwa wata don nasan idan ba ita na bawa ba wani zai iya bude ledan yace ya gani a hannunta.
Wuce wan su yasa naji wani irin kewan su ya kamani sun so tafiya dani gida amma daddy bai yarda ba yace ba al, adan gidan shi ne hakan ba sai dai duk wanda zaizo ya zauna dani yana iya zuwa.
Don hakane aka barmin Attu da mama Abu matar maigari su zauna dani a dakina kamar yadda ya umurta din.
Yan suna duk wanda yazo yaga yadda anty ta soye sai a koma gefe a dinga tsegumin hakan .
Tun washegarin suna ban zauna ba ina kokarin kula da anty duk da ba wani karfi jikina ke dashi ba sosai amma haka nake daurewa ina bata kulawa mama Altine ma bata koma ba tana gidan tare da ita.

********* ********* *********
Dan hutun sati biyu kawai na samu nafara fita makaranta don saura wata shidda in kammala karatuna.
Ban zuwa da yaron sai dai yanzu dole nakan dawo karfe biyu in bashi nono in koma don abin ya taru yai min yawa akaina.
Ba girki nake ba shiyasa na samu saukin fitinan matan gidan don ba ruwa da zancen kowan su sai dai mu hade wani lokaci a compound din gidan kowa ya wuce.
Ranan sai ga maigidan ya kira mu a falo don har anty saida ta halarci wurin nice na shigo a karshe ina dauke da baba a kafada na.
Ina shigowa duk suka mayar da kallon su akaina sallama nai masu na samu wuri zan zauna naji daddy yace miki min shi nan mu gaisa.
Yana karban shi yake cewa babana yaya naga kana ramaywa kuma kaida kafito da girman ka yanzu naga ya fada kuma ?
Humm, umm ikon Allah dai bai karewa a duniya muna dai ganin mamaki kan agidan nan yaya za, ayi dama yaro yai kiba ido yai mai yawa haka.
An haifi dan gwal sai wani faman tarairaya shi ake kamar shine farau din zuwa gidan nan kafin wasu hindatu uwar rashin mutunci ke maganan.
Daddy yai murmushi ya kaiwa yaron kiss a fuskan shi yace bashi bane farau sai dai ki sani wanan babana ne sai dai kuyi hakkuri don ba mai wasa da alamarin mahaifin shi.
Tanan kuma aka bullo muna ai magana ace tsohon gida ne ba mai bakin takanwa akan tsohon gida.
Ina jin su nai shiru ina duban wayana dake a hannu na sai naji daddy yace bana son abin jawo magana please.
Yace na kira kune don ina son kowa takawo min sunayen mutum uku da zasu sauke farali a ban nan isha Allahu in an hada ya tashi mutum goma sha nawa mutum biyar sun kama sha bakwai haka nai casting din plan dina.
Gaba daya falon kowa yai shiru baka jin motsin kowan mu sai can daddy ya soma wasa da yaron dake hannun shi.
Zulfa ce takawar da shirun da cewa amma yayana mutum uku dadai ka kara muna ko daya ne ko ?
Ni ba mashi ba yadda duk kan mu muna da bukata muma ai banji an anbace mu ba daga tafiyan ko ana nifin har mu ke nan wai ?
Baidai yi magana ba sai anty ne tace shin kowan mu kujera uku daidai komai sai lokacin yace Saade so kike na wata yafi na wata yawa ne komay ?
Ke kuma dake fadin gar kukuna da bukatan zuwa ai idan zaki koma ne sai ki shirya ki dauki kujera daya daga ciki ko.
Zulfa idan har baki gode da ukun dana baku ba kina bukatan kari zaki iya karawa da kudin ki ai zaki iya ko ?
Nan kowan su ke magana mikewa nayi don agajiye nake nace mun gode daddy Allah ya saka da alherisa yasa badi afi hakan .
Yace Amin Rama nagode na nufeshi zan karbi yaron yace barshi zan kawo shi idan nagama ganin shi.
Ina ruwan dan baka saba ba na kauye ya samu burodi toshine may son kin nuna ke wai ta kirki baki korafi ba akai tunda ba a saba ganin kyautan kujera ba.
Hindatu ce ke wanan maganan nace da ita cikin sakin fuska shiyasa ai nake godiya wanda ya saba ma naga ai ya karba bai mayar ba.
Aikin banza ke nan ashe da so kike nace ban so ki kara da naki kikaiwa mutanen kauye ko ?
Nace shi aikin Allah da tallaka da mai kudi duk daya suke a wurin ubangiji ko ba a bani kujaran ki na karaba nagode da wanda aka bani tunda ban saba gani ba gashi yau Allah yakaini ga gani da raina.
Ina fadin haka na barsu a falon kowa ranta bai mata dadi ba don kowa da abinda ke damun shi ina tafe ina mamakin haleya irin na wasu.
Ta yaya za ai ma alheri mai tarin yawa haka amma ace mutum wai bai gode ba har ya tsaya korafi haka ?
Jama, a duniya mai na kashewa matan daddy ne dukkan su uku suke hattara na haka ne don nasan kowan su zargin ta ya shafe ni.
Ni may zan masu a rayuna nayi fari a gun su yanzu ma ayi muna abin arziki nayi godiya yazama kuma laifi don har anty na bataji dadin kalman godiyan danai amfani dashi ba a gurin.
Bayan na dawo daki na kwanta sai kuma tunanen yanzu wa zan bawa wanan kujeran kuma na san dai Inna ta da Babana suna daga ciki insha Allahu to dayan kujeran fa kuma ?
Maigari a, a ina Attu dai ko mijin ta kakana namiji don ban ko kawo zancen wani ba a fanin mahaifina don ba damuwa sukayi ba damu a baya.
Dan dama yanzu da sukaga baba nada dan rufin asiri suna dan sha, ani dashi don bukatan abin hannushi.
Can kuma na koma tunane watau daddy yana da wadata hakane ashe da har zaiyi kyautan kujerun makka har haka da yawa.
Sam bai nuna yana da zarafi hakan don shi ba mutum bane mai son yawan karyan duniya mutumin da hayaniya ma aikine a gareshi bai da ko yawan abokai haka agari.
Idan harkaji yace wani abokina ne to tabbatar wani harkan business ne ya hadashi damai shi din.
A hankali na lumshe idanuwa na ina kwance rairai ina kallon sama banji shigowan shi ba sai kafana danaji anja min.
Na bude idanuwa na daddy ne a tsaye saman kaina rugumay da yaron yace tunanen may kikeyi haka a kwance ?
Murmushi nayi na yunkura zaune ya miko min yaron nakarbe shi ina gyara mai kwanciya don yaton barci yake yi daya shigo dashi.
Nace daddy mun fa gode yace da akai may kuma again ?
Nace makkan daka ba yan uwan mu mana yace godiyan bai isa ba ke nan har yanzu ina son mutum wanda idan an mai alheri ya sani ba wanda zakaiwa alheri yai maka korafi ba naji dadin godiyan ki Rahama don haka mutum hudu zaki bani daga bangaren ki.
Da sauri na dago kaina nace mutum hudu daddy yace haka nace Allah nagode ma na fadi a fili nace mahaifana da kakanin na nake son suje daddy.
Yace wasu daga ciki ke nan nai saurin cewa Attu da mijin ta mana ai banda wasu kakan nin da suka fi min su a duniya don ni dasu na bude idona.
Anya Rahama baki son kai ba anan don banji ki sa kowa daga bangaren mahaifin ki ba sannan kuma in ga kara aiki hada da maigari su tafi ko ?
Nasan maigari ya cancanci hakan agare ni amma kuma aida girma na ya gani ga wayanda sukai wahala dani kuma ma suke a cikin yi har yanzu din.
Daddy dai bai min magana ba yabar dakin washegari da safe bayan nai wanka na shirya naje part din anty don na gaida ita tun daga kofan shiga dakin ta nake jin muryan ta daga daki tana magana sama sama.
Akan may zakace komai daidai da Rama zaka dinga min idan da nasan wanan auren cin amana zai koma min tsakani da kai da ban hada shi ba wallahi.
Duk irin rawan kafan da kake akan yarinyar nan duk ina kau da kaina naga abin yanzu yana son ya wuce wuri kuma hakana .
Saade wai may yasa kika canza gaba daya ne hakana please halin da ban sanki dashi ba a baya yanzu shine kike kirkirowa kan ki.
Tace dole ne na nuna maka abinda ka dauko yi min abaya akan sauran matan ka nai magana ka daina shine yanzu ka dawo da yin shi akan Rama.
Ke Saade ya ishe ki haka na gane ke baki san ana tausaya maki ba baki tausayawa rayuwan ki balle na wani.
Na fahinci baki kaunan a zauna lafiya har may naiwa Rama wanda ke ko ku ban maku shi ba a gidan nan.
Ko ku daban kuke gare ta da zan mata abu a kasa da ku nagane abin naki akwai son kai sosai a cikin shi.
Kamar yadda kike da iyagiya uku akan ki nawa haka itama take daure dashi a kanta don haka bazan wullakanta kowa ba don wani yaji dadin rayuwan shi.
Abinda na bayar ke nan wa kowa don haka in zaki bani list din ki ki bani idan kuma bazaki bayar ba duk daya a waje na.
Ke yanzu ba abin kunya bane agare ki ace kina wanan bakin kishin akan yarinya karama da kika tayar da hannun ki duk kin bi kin sakawa kan ki fitina haka kan abu daya.
Maimakon in shiga sai kawai naja kafana na juya na fice daga gidan ba tare dana bari sun san naji maganan su ba.
Sai dai na tafi da tunane da mamakin anty a raina wai shin haka kishi yake yasa mutum ko yana cikin wani hali bai tunane bai tunanen makomar shi, sai yayi wanan halin .
Ko dana dawo gida haka kawai sai na fara jin nima dan tsanar ta a raina kamar yadda yanzu nasan kishi yasa bata kauna na ko kadan sai dai dariyan hakori kawai.
Zama nayi da Attu da mama na fada masu komai sai da suka gama jina suka ce dani dama tana da zazzafan kishi ne sosai rashin hada miji da itane yasa bazaki gane ba.
Ba wai bata son ki bane kishine kawai ke cin ta kada ki biyewa rudin shedan yataru ya ruda ku gaba daya har kukai ga abin kunya duniya a karshe ke zata zaga ace tai maki halarci yanzu kina son ki butulce mata kuma.
Ki bita da halinta sai a zauna lafiya yawan son mijin ta ne yake sata yin hakan ba komai ba sai dai mu bazamu ce kada kibi mijin ki ba don kada ranta ya baci.
Ai itama musulmace tasan abin da sharia ya tana da akan aure in ba so take ya karkata a kanta ita kadai ba ya tashi da shanyayyen bari gobe kiyama.
Na nisa ina cewa ni abinda yake damuna bayan wanan shine duk kan su da babu mai kaunata a cikin su.
Attu tace shine kishi ai yadda basu kaunar ki hakane ma basu kaunar junan su kowa kan shi ya sani a fagen kishi ai.
Nan dai sukai ta bani musalai ina zaune ina sauraren su daga karshe nai masu sallama na shige dakina na kwanta.
Waahegari ma kamar na wuce abina sai dai na daure na shiga muka gaisa da ita sunan mun shirya ne amma ba kamar da can baya ba muke da ita.
Don wani lokaci sai ta dinga daure min fuska wani sain kuma zata sake kamar ba ita bace muyi hiran mu lafiya.
Yau ma fuskanta a gimtse yake babu walwala don haka sai ban tsaya ko tambayan ta komai ba nima nasha toka nai mata sai na dawo nafice.
Bina tayi da kallo bayan na fita tana fadin mutum abin tsoro ne wallahi yanzu yariyar na tana ganin daidai muke da ita ke nan.
A, a ta fara gajiya ne da halin ki tunda ke baki daukan girman ki da Allah ya baki ai ba haka take ba idan ta shigo nan take zama sai ma kin korata wani lokaci.
Mama wai may yasa baki son ayi zancen gaskiya ne akan Rahama yarinyar nan baki san halinta bane sanin baya kikai mata.
Mama Altine tace ina ko zan sani tundake da yanzu kuka hada miji da ita kin fini sanin ko ita wa cece ai.
Yarinyar nan kina bani mamaki gaba daya yanzu halaiyar ki duk ya sake abinda bakiyi a bayane kika tsirowa rayuwan ki.
Wanda ke daki yana fama da kan shi ina shi ina wani tsiro tsirkin kishi kuma kwance a daki.
Au mama har ke ma gori zakiyi min ke nan ko ba mamaki ko shi wanda nake zaune agidan don shi ai abinda yake nufi ke nan dani banda moriya ya samu inda yake morewa yanzu.
Aiko kin kyauta tunda kin samo mai inda zaiji dadi sai dai kuma ga shedan nason hanaki cin riban abin .
Ki kawar da idon ki shiyafi maki ki koma fa Allah wanan abinda kika dauko bashi ne mafita ba a gare ki koda kina da lafiyan ma.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE KIN SANI, , , , , ,

66
Kamar yadda na furta sunayen daba bayar ke nan sai dai Inna tai min magana dole aka janye tafiyan ta maigidan ta maigari ya tafi don kara.
A bangaren anty abin zaiba mutum mamaki don babu dan gidan su ko daya data bayar sai kawayen ta na kut da kut tabada.
Acewan ta wai ai yan uwan ta sun tafi dakyat na katsalandan na rufe ido na ce mata amma gaskiya anty idan haki bada sunan mama Altine ba a tafiyan nan baki kyauta ba.
Wani kallo nake a suwa ta watso min amma nadake nace bawai nai maki karan bani bane anty ganin dacewan hakan nayi gareki .
Don idan baki hakan ba daga baya abin zaizo ya damay ki, nake gani, bude bakin ta sai cewa tayi aiko ke idan ga halarci zaki iya bayar wa a naki bangaren ai.
Nace idan nai maki haka ban kyauta ba na shiga hakkin zumuncin ku zan iya haddasa maku wani abu a tsakanin ku daba haka ba da zance wani nawa ya fasa ita ta tafi din.
Shiru tayi batai magana ba nima naci gaba da ba yaro nono ina kallon waya na, sai can naji ta nisa tana ce Rama na gode wallahi sam banyi tunanen yin hakan ba sai yanzu da kikai magana.
Nace nagode anty tace damay fa kuma nace da kikai amfani da shawara na duk da ban kai ba ban isa ba amma na tunar dake kuma kika dauka.
Tace kai Rama ke nan ni fa yanzu sai kinyi hakkuri dani don ban san may ke damuna ba wani lokacin.
Wani lokaci idan nai wani abin sai daga baya naga radhin dacewan shi yanzu badon kin bani wanan shawaran ba sam ban kawo mama ba ga zancen wallahi.
Na mike tsaye ina mika mata yaron da ya gama shan nono ina cewa je gun maman ka na huta nima.
Ta karbe shi tana cewa dani kai wanan baban fa karfi yake ji yanzu zakiga yana wani dan zabure zabure haka dashi.
Dariya nai masu na ce kai amma baba idan ka wujijiga min anty na yau sai na daki kan nan naka kana ganin bata da lafiya.
Tace aiko da yau kun hade da uban shi don ni da kaina zan buga mai waya na sheda mai kin dakar mai tsoho haka kawai.
A raina nace yau kan yan arzikin suna akan anty nake cewa wai ni anty wani shiri ake yine akan fitan yaran nan daga primary ne ?
Kai Rama har wani shiri kuma za ayi don zasu gama karatun pramary nace ai kin san haka ake yanzu wa yara ai masu buki na fadawa yan uwa don yaro yaji dadi ya kara hazaka.
Tace to ai shiri na hannun ki yanzu ke uwar su nina isa nace ga abinda za, ayi Nasir yace dani ban yi daidai ba naki yafi gareshi.
Nace haba anty shi Nasir din nawa za aiwa wanan shedan kuma anty tace aikin san shi hukuma ne sai lalashi.
Saura sati biyu fitan yaran a makaranta don haka kamar yadda uqar tace tabar min shiri a hannuna na nayi komai ban kara tuntuban taba sai aiwatar da komai nake a kaina a cikin jikina kuma.
Sai ana saura kwana biyu na dinga yawon kai gaiyyata gun yan uwa da abokan arziki wasu kuma ina kiran su a waya ina sheda masu zancen.
Na buga kalanda, books da robobi sai abinci dana ba Zarah ta bayar ai muna saida dare na shiga wurin anty na sanar da ita cewa gobene fa taton yayye yaran da za, ayi a makaran tar su.
Tace ai ita shaf ta manta da komai sai yanzu danazo mata da zancen ta tuna take tambaya na may zata taimaka muna dashi nace mun gode mun gama shirin mu ko.
Washe gari tunda safe mun shirya zuwa wuein taron, a bangaren Hindatu ma tayi shiri sai dai batai tunanen nima na shiryawa yaran irin haka ba.
Taro yakai taro muka iso wurin can muka samu wani rufa muka yada zango a cikin sa da mutanen mu suma hindatu runfar dake kallon inda muke take zaune da mutanen ta.
Kusan late Zulfa ta iso don duk mun gaiyyace ta zuwa taron duk da a cikin murane muke amma sai da kowan mu ta nuna wanin halin kishi a bainan jama,a.
Kulolin da Zarah ta iso muna dashi ne ya dauki hankalin kowa a wurin sai da aka gabatar da komai na kan yayye yaran inda munyi nasara yaran namu na cikin wa yanda suka samu kyauta sosai a ranan cikin dalibai sai dai babu yar wurin hindu a cikin kyauta ko daya na kokari da aka bata.
Nan aka shiga raba abubuwa sosai muka burge mutane muna raba kalanda da books mai dauke da hotunan yaran aa cikin sa.
Hankalin Hindatu yai matukar tashi sosai Zulfa ta baro rufan Hindatu bayan ta dan zauna tadawo rufar da muke a zaune a gurin.
Ina ga yan uwan Anty sun manta da zulfa na furin nan suka shiga zuga anty wai ta sake min ina mata gaba akan sha, anin yaranta yanzu Allah kadai yasan nawa na karba a gun mahaifin su naci riba dashi kan wanan sha, anin haka.
Nan ta hau ta zauna kan maganan su muna aha, anin mu dadi dadi sai naga ta fuske min tun a wurin na rasa gane kanta.
Photo ma da zamuyi da kyat tazo ta shiga akayi da ita ana gamawa tabar wurin ta ki zama a karasa komai da ita.
Bayan wucewan ta ne Zulfa tace dani Rahama zan so nai dan magana dake kafin a watse wurin nan ko kina da lokaci nace ina dashi anty.
Muka kebe da ita tace da fatan zaki fahince ni don ba gulma bane ko zuga zan fada maki shi abu in kanayi tsakani da Allah to kayi shi kai tsaye.
Yanzu ina zaune a bayana nake jin abinda ake fadi gamay dake kan wanan abinda kika shiryawa yaran nan duk da kinyi don Allah ne amma an zuga antyn ki ance kudi masu yawa awajan maigidan kinci riba dashi.
Baki ganin tabar wurin rai a bace don haka nasan akwai wata a kasa nan gaba kan wanan matsalan.
Nace wallahi wallahi anty Zulfa ban karbi ko kwandala agun daddy ba bai ma san da zancen ba sai daren jiya nake fada mai komai akan bukin da za, ayi din.
Tace ni dai na fada maki abinda naji kuma naga ta dauka ban san may yasa take daukan zancen mutane ba haka suna ruda ta.
Mun dawo gida a gajiye har a lokacin ba wani fuska a gin anty gareni nima sai na share ta kamar ban fahince ta ba.
Washegari ina falo zaune da dare wanda har lokacin ban karasa walwalewa daga gajiyan jiya sai ga wayan daddy yashigo min nazo falo yana nema na.
Ban je da baba ba nan na barshi wurin Aisha a goye suna kallo da Atika na fice part din.
Nai mamakin ganin kowa zaune a falon shiko yana zaune ya saka laptop din shi a gaban shi yana aiki a cikin sa hankalin sa a kwance.
Na gaida su na samu wuri na zauna saman kujera ni da ban damu da zama sama ba don girmama su sai gani yau na dane kujera na zauna daran.
Kusan minti shidda zuwa bakwai ya dago kai yace damu ummhum kin shigo Rahama dama

Please Login or Register in order to submit comment