Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don mugun halinki don baki da kunya shine yanzu har zaki wagale baki kina fadin magana son ran ki idan fitsari banza ne kaza tayi mugani.
Banda marasa tarbiya da rashin mutunci da kika tara min a gida suna jawo min magana da abin kunya a gida dagari may kika tsinana min.
Sai naji amarya ta cabe da cewa ai dama duk wanda yace ruwan wani bai tafasa shiko nashi ai ko dumi baiyi haka abin yake.
Nace don Allah dai kuyi hakkuri kubar wanan zancen don Allah yanzu girma yazo ya kamata ku daina hakan.
Haka dazun kuka tara mutane a kofan gidan nan abin ba dadin gani don Allah don Allah na roke ku ku daina yin haka a rayuwan ku.
Daga kofan ta da take zaune tace ke kama kanki ke har yaushe kike da zaki wani tsaya wai kina muna nasiha inda bamu san asalin kolo bane da sai yace muna daga masar yake.
Baba yace Rahama kyale wanan mara mutunci don shedan ya auri zuciyar ta ba yau ba na kusa yadda kwallon magwaro na huta da biyan kuda.
Baba kayi hakkuri ka daina biyewa irin wanan maganganun na mata don ba girman ku bane hakan.
Ke kama min bakin ki ke har yaushe kika gama da naki matsalan don kin iya cin amana daga taimako kuka san asirin da kukaiwa mata kika aure mata mijin ta wallahu tir da halin yan cin amana irin ku a duniya.
Shiru nayi sai babane yace kaiyya ace halin mutim jarin sa ke kina ganin abinda kikeyi ko shi kowa keyi ne a duniya wai.
Don ba yarki bace ai da yarki ce ko ni mahaifinta baki bari taiwa alheri balle har makwabta su ma su samu.
Ganin nayi shiru ne yasa baba ya fahinci raina ya baci don haka shima sai yaja bakin shi yai shiru.
Mun dan zauna jugun sai nake cewa baba dare ya soma zamu tafi gida don akwai duhu yau a garin yace hakane Rahama Allah yai maki albarka ya tsare muna ku daga duk wani abin ki a duniya.
Nace amin baba mun gode namike mun tsayar da magana dashi da safe za, azo a samay shi ya nuna yadda yake son tsarin.
Nai masu saida safe sai ga yaran amarya sun shigo gidan tace yauwa hajiya ga yaran nan kin gasu tace kuyiwa anty ku godiya ko .
Nace au sune nan sannu ku ko kuna lafiya na dan shafa kanun su suka rusunna suna gaidani.
Uwar tace ai gobe in Allah ya kaimu zasu shigo su gaida ke can gidan.
Mukai masu sallama na fito inajin mama na fadin munafuncin banza da wofi kawai mutum bai iya da gidan shi ba yace zaizo gyaran gidan wasu ai duk zaman da mutum keyi a can muna da labarin shi a nan.
Ban da boyi boyi may aka gane a can din anzo za, a cimu da burgan aiki wai anga yan kauye ko ?
Naje gida ina fadawa innata yadda mukayi tace Allah ya kyauta ai ta riga tai nisa batajin kira tana fadin hakane don ta hanaki aikin ki na alheri ga mutane kin san shu,uma ce ta gaske ai.
Washe gari ma bayan mun tashi ina da gurin zuwa wuni gidan kakan nina daga can na biya gidan mama altine don ban sha, awan shiga gidan namu ko kadan.
Ado magini yazo muka fito ni da maigari ya fada muna nawa za, a kashe nai mamaki kwarai nace garin dadi na kauye gaskiya komai nasu da albarka yake. By
Na shiga na kawo mai kudi yace a ranan zasu fara saka foundation din gina nagani idan yayi kyau.
Sun tafi sun samu baba ya shiga dasu ciki don a auna yadda ginan zai kasance sai mama ke cewa ita kada a taba mata dakin ta abarta da abinta hakana.
Baba yace baki isa ba tunda ba gidan ki bane kuma bada kudin ki na gina abina ba dashi kika ganni kika shigo yadda nake so haka za, ai min.
Sai da takai har baba ya shiga ya linkida mata duka da farar safiya sannan ta natsu.
Aiki ya fara gadan gadan tanaji tana gani ga kuma jiki yai mata tsami ga banza.
Gidan kakanin na na nufa bayan yaran amarya sunzo mun gaisa suka tafi muka kama hanya.
Muna shiga Attu ke cewa dani tayi fushi sai da nagama ganin iyayyena da yan uwana nazo ganin su .
Nai dariya nace haba Attu ke fa ta daban ce bari nayi nazo mu sha hira a tsanake daku.
Nace ina tsohon mijin ki tace mijin ki yafishi yarinta ne balle ki kira min miji da tsoho.
Nan muka zauna aka shiga hiran yaushe rabo a tsakanin mu daga ni sai Atika mukazo don Fatima tana can ta shiga gurin yan uwan mahaifiyar ta.
Hira sosai mukayi da Attu take tambayana yaya baiwar Allah nan mai mutunci da karamci yaya jikin nata kuma ?
Nan dai na fada mata komai don wanda baici ka boyewa magana ba najikin ka dole ka fada mai wani abin.
Tace ki dai daure aita hakkuri ai tayi kokari wallahi ko a zamanin da can baya da wuya a samu macen da zata sadaukar da rayuwanta da komai nata ta zabawa mijin ta macen da zai zauna da ita don samun farin cikin shi tana kallo.
Da ace mata zamu kawar da kishi a rayuwan mu muna sadaukar da ran mu ga abinda zai amfane ne mu duniya da lahira da babu sauran macen da zata shiga wuta a lahira.
Gsshi kuma mutunci da kimarta zai karu sosai a gurin miji don dole nauyi da kunyanta ya hanashi wani abin koda yayi niyar yin hakan idan ya tuna da kawaicin da akai mashi shima.
Nace Attu Allah dai ya gyara amma ai maza yanzu ba sanin hakan sukeyi ba don suma yanzu mazan ne sai a hankali dole sai mace ta kai ranta nisa akan su.
Nace waiko Attu mai zogala na nan kuwa tace tana nan wallahi nace bari dai yau na shiga na leko ta.
Na hada tsaraba sai gidan makwabciyar Attu duk da suna da dan jayawa kadan tsakanin su da su Attu din.
Da sallaman mu tana ganin mu tace ikon Allah wa nake gani haka yau a gidan nan ko dai ido na ke min gizau ne wai.
Sai naga kamar Rahaman Attu nake gani a gidan nan nace cikin dariya nice din dai Nana mai zogala tace wallahi kama kawai na kurciyan ki ne nagani nai amfani dashi.
Tabarma ta shimfida muna muka zauna nan muka shiga gaisawa tana ta murna da jin dadin ganin mu.
Tace yaya kuke na dawo wani lokaci nake tambaya najiki shiru ake cewa wai ai kina birni kin yi aure a can.
Tace ke kadai ne ko kina da abokan zama ne nai dariya nace Nana abokan zama har uku nice ta hudu Nana.
Tace wai, tau Allah ya kyauta sai a hada aita hakkuri nace in sha Allahu Nana na mika mata ledan da muka shigo dashi ta karba tana cewa zan baki wani shawara.
Na gyara ina sauraren ta sai ta dakata ta na bude ledan da na bata take cewa ikon Allah harda tsaraba na samu haka Rahama wanan ya da alheri kike tun kina karamar ki.
Taita godiya can ta gyara zama tace kada ki yarda ki sabawa ubangijin ki akan dan wanan rayuwan da bai kai ko cikon cokali ba .
Kedai ki saka Allah a gaban komai sai kiga da farko za, a fara gwajin Imanin ki da abubuwa da dama.
Sai kin saka imani a ranki sai kiga da sannu ubangiji na walwale maki al,amuranki sannu a hankali.
Kin san Assma,ullahil, husna idan da zaki tsaya ki fake a garesu sai kiga da sannu ubangiji na maki falala a rayuwan auren ki.
Zaki iya karanta Ya Allahu yahu, 1000 zaki kuma iya nafila raka, a biyu, sai salatin Annabi da hailala saiki karabta Allahu yahu, kafa 66 shima wannan anayin sa don neman bukata a gurin Allah.
Ya Azeez minazeen 41 bayan duk sallah farillah na asubahi har tsawon kwana 40 akwai fa,ida sosai a cikin wanan kalman.
Idan kuma kina da matsala da mijin ki ko kishiya ta sakaki gaba zaki iya yin wanan zikirin Al Khaaliq kafa 5000 insha Allahu zaki sha mamaki sosai ga matsalarki.
Don samun tsari ga duk wani sheri ko kaidin da za, ai maki zaki iya karanta Al Mutakabbir sau goma safe da yamma.
Zaki kuma iya karanta subbahanallahi walhamdullahi Allahu Akbar ko yaushe ba adadi don samun farin cikin zama da mijin ki.
Naji wani irin dadi sosai ta kuma fara jero min irin hikimomin zama tsakanin kishiyoyi irin dubarun su na baya naji dadi sosai shiga na wurin Nana mai zogala don na karu sosai da ita.
Nai mata sallama na dawo gidan Attu ban bar gidan ba sai da yamma yayi na dawo gida a gajiye dan tafiyan da nake a kasa kwana biyu gabobina kamar nai wani aikin wahala dasu.
Gashi tun da nazo ban samu kiran maigidan ba shima banji ya kirani ba sai dana idar da sallah ishai ina gurin zaune na jawo wayana sai naga ashe ma a kashe wayan yake ban kuna ba.
Na kunna wayan sai naga ina da dan sauran caji aciki maganan da mukayi da Nana mai zagale ya fado min a rai data girman kai da son jan aji ga matan zamani shine ke kawo yawan fitina a tsakanin ma aurata a wanan zamanin.
Bayan mace tasan cewa a karkashin iko da mulkin mijin ta take amma sai wayewa da boko yasa mace ganin ai daidai take danamiji bazata iya kwantar da kanta ba ta samu aljannan ta dan boko da take takama ya ratsata ko wayewa.
Dil na danna kira a layin daddy kira daya biyu gana uku naji ya daga wayan tare da fadin Assalamu Alaikum.
Na karba mai sallaman nashi cikin girmamawa yace yau an ga daman jin motsin mu ke nan ?
Nace ba hakana bane ba mu da sevices ne daddy inda nake yace ok su baba maigari suna dashi a gidan su da nake samun shi mu gaisa ke nan.
Shiru nayi yace kin dai ga daman kiran layin mu ke nan yanzu kowa na lafiya ko nace lafiya muke daddy.
Nace naga sako gun Hamza an gode Allah ya kara arziki yace ai ba sakkon ki bane da fatan anyi yadda nace dai nace a sanyaye anyi daddy kuma sun gode.
Sai shiru nace sai anjima yace Allah bamu alheri na kashe wayan sai na kira layin anty tana dauka tace dani.
Kai haba haba dai Rama yanzu fissabilillahi kin kyauta ke nan Rama ki kashe waya gani da yara muna son jin lafiyan ki shike nan tunda kika samu gida da yan uwanki kin manta da kowa nan.
Nai dariya nace afuwan anty services ne babu shiyasa tace shine ko wurin kira na kudi baki zuwa ki kira kiji lafiyar mu Rama ?
Ga yara sun hanani shakat da tambayan yaushe mummy zata dawo sun damu na kiraki suji muryan ki amma ke kin tafi kin share mutane can.
Nace ai min afuwan anty abani su mu gaisa tace ai gasu tsaye sun min cirko cirko sunji ina kiran sunan ki a waya.
Nan ta basu muka shiga gaisawa Nasir yace na karbo mai ragon shi a wurin maigari ita kuma Amira tace na karbo mata lalle a wurin inna ta da kuli wurin mama Altine.
Mun gama wayan na lumshe idanuwa na daga inda nake kwance rigingine sai tunanen su da kewar su yazo min a raina .
A gaskiya ban kyauta ba ko ga Anty na da yaran ban masu adalci ba don nasan zasuji kewa na dama.
Gaskiya zama da manya ko zitartan su mutum zai dan samu wasu hikima a gun su gashi yanzu dan hikimar da Nana ta bani yai mun amfani yanzu yanzu.
Da ace sai na koma ne zan gan su da banji dadi ba sai nauyi da kunya zai biyo min baya.
Amma dan kiran da nai dabara yanzu nayi zai dan rage min wani nauyi a kaina ke nan.
Bayan na kwanta naji dadi a raina ko ba komai dai nazo gida naga yan uwa da abokan arziki na kuma godewa Allah da baiwar da yai min na zama abin kwatance a idon yan uwa da abokan arziki.
Zama mukayi mai ma, ana ni da maigari inda ya bani shawar warin zaman duniya tare da fada min wasu sirikan da ban sani ba a rayuwa naji dadi sosai da wanan taimako.
Nan na fara shirin komawa gida cike da farin ciki da jin dadi a rayuwana don wanan tafitan ba karamin dadi da karuwa na samu a cikin sa ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA BA, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YA SAKA MUNA AKAN KI DON KIN SAN ONLINE NOVEL NE WANAN, , ,
55

Da dare ina zaune tare da maigari a kofar turakan shi bayan ya idar da sallah yaci abinci ke zaune yana ta sakatan hakoran shi yake cewa dani bayan ja zo na zauna.
Gobe ne tafiyan ku idan Allah ya kaimu lafiya nasan da safe zamu iya ganin driver din ku yazo daukan kan ku don haka nake son mu kara tataunawa dake.
Nace a ladabce da to baba yace shi lamari na duniya yakan zowa bawane ta fanin da bai zata ba a rayuwan shi.
Wanda yansan Allah ne ya kawo mai jerabawa hakkika ya godewa Allah da hakan don yana daga cikin imanin bawa yadda da kaddara mai kyau ko mara kyau.
Don haka daga yau ina son ki cire wani tunane a ranki nacewa ko zaton wani zai iya maki wani sheri a duniya.
Rahama ina son don Allah ko da yaushe ki dinga sawa a ranki cewa kin fa shigo ne kin samu mutumin nan da matan shi a tare.
Ma wuyacin abu ne mutum yace ya samu yadda yake so kai tsaye a rayuwan shi sai ua hada da hakkuri tare da addua na neman tsari daga shedan da makiran mutane.
Don haka bana son naji kin kasance daga cikin matan da suke da son kansu fiye dana dan iwan su.
Ace kece aka sama a gidan a matsayin matan shi shin yaya zakiji a ranki, ?
Wani mataki kuma ke zaki iya dauka akan wacce tazo ta samay ki da mijin ki a gidan kuna zaman ku na lafiya.
Nissawa nayi tare da sauke ajiyan zuciya nace afili ba dadi baba yace to haka ne suma a yanzu suke ji a kan ki.
Ita wanan boyar Allah matar shi abar zanceen ta don sai ince ashe har yanzu akwai sauran salihan mata a duniyan nan basu kare ba.
Don ta sadaukar da rayuwan ta saboda farin cikin ku keda mijin ta da "ya"yanta don samun farin cikin ku a duniya.
Don haka don Allah Rahama ki sawa zuciyar kii hakkuri akan duk wani abinda kike ganin suna maki na musgunawa wanda a shirye suke sai inda karfin su ya kare a kan ki.
Amma idan hakkuri yana gaban al, amuran ki baki biyewa shedan ya rinjayi zuciyar ki ba zakiga abubuwan suna zo maki a cikin sauki yadda ma baki taba zato ba a rayuwan ki.
Abinda nake so yanzu yazama dole ki kwanta ki bisu a hankali kiga gudun kowa a kanki.
Don yanzu a shirye suke da suga ko ta halin kaka ssun kawar da ke daga shiga rayuwan mijin ku wanda hakan haline naku na mata.
Ko wacce bata kaunan taga kishiyarta ta darata dako digon allura ne a gurin mijin ku.
Amma sai naga kamar ya ta kin kasa ga irin hakkurin da na sanki dashi kin fara biyewa rudin shedan har kina son yin sakaci da daman da ubangiji yai maki na samun miji mai nagarta da mutuncii abin alfahari ga kko wace mace data ssamay shi a rayuwan ta.
Rahama mijin ku ba mutum bane da za ai sakaci da samun irin shi don haka don Allah kiyi haakkuri ki kara akan wanda kike dashi a baya.
Don gaskiya Rahama na faahinci kin fada son mijin ki yanzu ga yadda mahaifiyar ki tai min bayanin komai.
Amma kuma sai gashi kina son yin sakkaci da daman da Allah yai maki a kan shi ai da kika ga cewa waccan dayar matar nashi kamar ta fara rinjayan ku a tsakanin ku .
Ai kamata yayi ki kwantar da hankalin ki har kiga iya gudun su shifa asiri baya taba tasiri iyakar shi kwana arbain ne a duniya.
Daga yau ina son ki sa, a ranki cewa babu wani asiri da zai sake tasiri a kanki sai dda amincewan ki don da kin fahinci da akwai matsala to kada ki kara bari har wani ya fahinci hakan yai tasiri a kanki ki yaki zuciyar ki gurin kyautatawa mijin naki a lokacin koda kuwa yana muzanta ki a gaban kowa gada ki damu da hakan don mijin ki ne ba wani ba can ki kaiwa ai kinyi ne don samun lada a gare ki.
Karbi wanan ya miko min wani abu a kofin dake gefen shi na karba nayi yadda yace dani din naa shanye na shafa sauran a fuska na.
Yace da yardan ubangiji babu abinda zai samu rayuwan ki sai abinda yafito daga Allah dai.
Rahama ki godewa Allah don a dan binciken da akai min a kanki kina tare da tsarin ubangiji sun sani su ma babu abinda zasu iya maki yai tasiri don ke hasken mata ne a rayuwa wanda ba ko wace mace ke dace da hakan ba, sai
wacce Allah ya halitta da hakan.
Allah ya baku zaman lafiya a tsakanin ku ya kawar da ahedan a tare da ku ko yaushe ki ta hakkuri ya ta don Allah don shi hakkuri makami ne ga bawa maiyin shi.
Nai mashi godiya namike zuwa dakin inna ta a can ma dai maganar dai duk nasiha ne mai kama da jan kune da daurewa da hakkuri.
Na kai kallona ga tarin kayan da aka aje muna na tsaraba wanda duk yan uwa ne da abokan arziki suka kawo muna shi da kuma maigari daya kashe zarahin shi sosai a kaina haka kakannina suma sunyi nasu kokarin sosai a kaina.
Da safe mun shirya sai ga Atika ta samay ni da kukanta wai dole da ita zan tafi na rasa yadda zanyi don yarinyar ta bani tausayi sosai dabara nai mata nace ta bari idan zan akawo min kaya sai azo min da ita.
Amma ina taki yarda sai kuka take tana turjiya a kasa haka yasa ta ban tausayi nace zan tafi da ita idan ta kwana biyu sai a dawo da ita.
Uwar taji dadi sosai itama yarta zata birni ta ga gari tasan bazata dawo haka ba babu karuwa a garesu.
Sha biyu da yan mintina Hamza na kofan gidan maigari nan aka fara fitowa da kaayan mu ana jerawa a motan da yazo dashi katon rago maigari ya bayar wai akaiwa abokin shi Nasir.
Naji dadi sosai a raina nake cewa baba duk wanan ragon na Nasir ne haka ?
Yace to bai samu doki ba ai sai ya samu rago ko nai godiya sosai muna nan bamu kai ga fitowa ba sai ga amaryan babana ta shigo gidan da kaya niki niki wai da ita da baba suka hada min tsaraba.
Sosai naji dadin hakan yau ni Rahama ne babana yaiwa wanan gatan haka a duniya aiko na san komai ya canza ke nan a gidan mu.
Can muka kebe da ita dakin inna ta taciro wani leda daga jikin ta tace cikin kashe murya hajiya kin min abinda ban taba zaton zan samu ba ga rayuwan aure na a gidan ku.
Don haka nima yadda kika soni kuma kika so jini na babuu nuna banbanci a garesu naga ya dace na taimaka maki da dan nawa siriin namu na mata dake taimakon mu zaman aure.
Tsakani da Allah na baki kamar yadda bakki dauke ni da zuciya biyu baa haka nima wallahi ban dauke ki da hakan ba wallahi.
Don Allah kada ki dauki wanan abinda dana baki a shirmay na bata lokaci sosai wurin hada maki shgi tun shekaran jiya don Allah da kinje na rokeki kiyi amfani dashi.
Nai dariya nace mama Amarya kefa uwatace don may zan yi zargin zaki cuta min wallahi ni a uwa na dauke ki harga Allah.
Tace nako ji dadin haka wallahi kuma na gode da hakan da kikai min niko insha Allahu sai inda karfina ya kare wurin yi maki duk abinda ya dace uwa taiwa yarta nai mata godiya muka fito.
Sai ga jama, an gidan Garbati danaje naiwa abin arziki niki niki sai da nai kuka don murna da tunna baya.
Har sabuwa sai da naje na gaida ita a gidan ta don rayuwa ya juya mata baya fitina ya hanata kwantar da hankalin ta tabari tai zumunci da yan uwan yaran ta har yanzu.
Yan uwa da abokan arziki suna tsaye muka fito nabi duk wanda yazo muna Allah sauke lafiya da dubu daya Rukaiyya da Suwaiba ne naba dubu biyar biyar su kara don kudi yaa saura a jakkana.
Muka kama hanya zuciyana cike da damuwa da rabuwan da zanyi da yan uwa na in kkoma can cikin bare da ba su san darajana ba gashi nan sai haba haba akeyi dani.

********* ********* *********
Karfe uku da yan mintina muka shiga get din gidan mu bakina yana dauke da wallahu galibun alla amrihi, kamar yarda Nana ta koya min.
Zulfa muka fara cin karo da ita ga mamakina sai naji tace a, a mutanen kauye ne sannun ku da dawowa ashe kuna hanya ?
Nace anty mun samay ku lafiya yaya su baby suke tace Alhamdullahi yaya mutanen gida anbarsu lafiya ko ?
Nace duk suna gaida ku nagode ta shige motar ta ina ganin unguwa zata tafi don tayi shiga na alfarma sosai.
Sai ga yaran su fito daga part din mu da gudun su suka fada a jikina da murnan su na rugumay su ina jin dadi raina.
An fito da ragon da yasha wahala sai Nasir ya nufi gurin nace Nasir ga ragin ka nan inji baba maigari akawo ma.
Haba murna tsalle da ihu yaran suka shiga yi gashi kuma suna tsoron ragon nace kaji nakine Amira ke da Jinior inji inna tace akawo maku.
Nan na barsu sun kewaye dabbobin suna kallo suna ta magana a kan su don sun zama masu abin kallo saboda sai dai a kawo masu shi a yanke suka saba gani.
Ragon ya shiga kuka don ganin shi a bakon wuri sai ga anty tafito da murnan ta da gudu na nufe ta na fada ajikin ta ina jin dadi.
Muna cikin murna mukaji muryan hindatu na fada

Please Login or Register in order to submit comment