Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya barta da tunane ita kadai a dakin ta na fito cikin shirina zani makaran ta nazo na sallamay ta dakin ta.
Nan na samay hankali a tashe tace anya Rama fitan nan naki kuwa yau zai yuyu .
Da sauri na juyu nace anty lafiya dai ko ?
Tace ina fa lafiya Rama wanan mahaukacin da ya like maki yazo ya samu daddy ku da hauka yace koda karfin tsiya sai ya aure ki.
Duk da naji tsoro a raina amma a fili cewa nayi Allah ya fishi mugu azzalumi kawai.
Nace mata sai na dawo tace fitan zakiyi ke nan Rama ?
Nace anty saboda shi na zauna gida karatuna ya tsaya kuma ?
Tace to Allah ya tsare nace amin anty sai na dawo ke nan tace Allah yasa nafice.
Tun barin layin uguwar mu na lura da wata bakar mota dake bina a baya a guje na kwasa Allah dai ya tsare ni na isa school lafiya.
Yinin ranan a firgice na wuni har Zarah ta fahinci hakan a gareni take tambayana ko lafiya nake haka yau ?
Ban boye mata ba tace badai boy kike nufi ba dan gidan haruna daura nace kamar haka naji sunan shi fa.
Tace aiko kin shiga uku wallahi wanan dan iskan mara mutunci may zakiyi dashi ke ?
Tace abu daya zan muyi shine idan mun tashi sai ki shiga motana ni na tafi da naki gida na ko yaya kika gani ?
Nace hakan yayi ba matsala ai yadsa muka tsara haka mukayi na samu na isa gida lafiya a firgice itakuma ashe sun bita sai da sukaga ta nufi gidan ta har can suke tafito sukaga bani bace sai suka juya.
Washe gari tsohuwar motar anty na shiga basu gane ba sai da naje school suka fahinci nice a cikin motar.
Aiko suka darkakeni saida na shige wani guri na samu na isa gida lafiya haka yasa na fadawa anty halin da nake ciki.
Tace na zauna babu inda zan kara zuwa sai komai ya lafa zan fita nayi hakkuri da karatun kwana biyu.
Shiryawa tayi sai gidan mama laraba tasamu babu kowa a gidan suka gaisa da ita take cewa lafiya dai ko Saade.
Nan anty take cewa mama magana nazo muyi dake da fatan zaki saurareni ki fahinci abinda nazo maki dashi.
Nasan baban su Amira a duniyan nan babu shawaran da zaki bashi bai dauka ba kuma ya zamo mai alheri a karshe.
Tace matsala kuka samu ne dashi tace mama ba matsala bane sai dai kuma matsalar ce.
Nan dai ta kwashe abinda ke tafe da ita na neman shawara akan auren da take son yakara ya bijera mata.
Mama laraba ra dubeta da kyau tace yanzu ke Saade da kanki koke son mijin ki ya karo maki kishiya bayan wa yan nan ma da kike dasu ba wani zaman dadi kukeyi dasu ba.
Nikan Saade da zaki bi shawara na da sai nace hakan ma da kuke ya isa don kishiya fa ba dadi gareta ba.
Mama nasan da hakan amma ina sin ki fahinci manufata a hakan don samun saukin mu nan gaba dani dashi da yaran baki daya.
Mama kinga da yaje gaba a kasa rike mai diyan diyan shi yace zai dauko wata don nasan halin shi akan yaran shi.
Gara ya dauko wacce na sani kuma na yarda da ita da ya dauki fitsarariya wace zata zo ta ganawa yara mugun hali.
Umm, umm Saade dadai ki kara tunane matan yanzun ko ince mutum yanzu ba dan goyo bane wallahi.
Mama garafa da wanan din nasan ta yasan ta musan halinta kin ga yafi komai sauki a gare mu.
To ke saade dakike wanan magana Allah fa shi yai ciwo yai magani ai ciwo ba mutuwa bane don sai mai lafiya ma ya tafi yabar maiciwon a duniya.
Tace hakanane mama nidai don Allah a duba min bukatana ko za, a dace ga hakan tunda ni yaki jin magana na.
Mama tace kin ga idan har wacce kike son ya aura din batai mashu ba ko kuma ita din butulu ce fa kinga kin zalunce shi ta zalunce ki ke kuma.
Jikin anty yai sanyi a lokaci guda hankalinta ya dan tashi take kuma wani natsuwa yazo mata tace cikin kuka mama ba wata bace can daban nake son ya aura sai Rahama dake gurina.
Kin dai gane ta kinga ko nasan halinta yasan nata ai banyi tsan manin irin hakan ba daga gareta.
Salati mama Laraba ta saka tare da tafa hannunuwan ta alaman mamaki ya kashe ta lokaci guda.
Tace Rahama dai Rahama dai Sa,ade dana sani ta gurin ki anya kuwa kanki daya Saade da zakice mijin ki ya auri yar uwar ki.
Mama Rahama yar uwata ce amma bata jini ba sai girma da arzikin daya hada mu ya koma yan uwan taka a tsakanin mu yanzu.
Jikin mama laraba yai sanyi yadda taga anty na zubar da hawaye tasan irin haka ita kadai tasan abinda take ji a zuciyar ta ai banza baikai zomo kasuwa.
Idan ya duba ga maganan ta gaskiya ne don dan nata ai yana son kulla amma Allah bai hada shi da matan arziki ba ita waban mai hankali lalura ya hana ta bashi lokacin ta.
Mama Laraba ta nisa tace yanzu tunda ke da bakin ki kika bukaci hakan ai Alhamdullahi da shine yazo da maganan kinga sai muce yayi rashin hankali duk da aure ya hallata a tsakanin shi da ita.
Don haka ki barni dashi insha Allahu zamu zauna dashi kan maganan kuma da yardan Allah zai fahince ni don ban taba bukatan wani abu dashi ba bai min ba don haka wanan din ma ai bazaki ba idan na fahintar dashi.
Anty tace nagode mama da kika fahince ni haka da wuri ba kowane zai gane hakan ba sai ma ai min daukan banda hankali ban san ciwon kaina ba.
Ai maganan aure babban magana ne Saade ba ko wace mace zata iya wanan sadaukar da ran da kikayi ba haka shiyasa za, a dauka ko baki da hankaline.
Tsananin son mijin ki da yaran ki yasa har kike masu gwadayin fatan alheri a rayuwa nan gaba.
Anty tace ni har ga Allah ina ma mijina kwadayin kasancewa da wanan yarinyar koda kuwa ina da raina na ne nidai bukatana naga ya samu kwanciyan hankalin aure kaman ko wani magidan ci a gidan shi.
Naji na kuma gane manufan ki don haka banda abinda zance sai nace Allah yai maki albarka a rayuwan ki yasa a gama da duniyan nan lafiya.
Tace amin a sanya tasan takawo maganan inda za ai mata maganin shi indai mama ce don Allah ya bata sa, an dan yar uwar ta sosai.
Tace yanzu mama ba sai na sake mai magana ba ke nan ko?
Ba sai kin shiga ba Saade ki barni dashi kawai zamu zauna da shi insha Allahu.
Tai sallama da mama Laraba ta barta tana mamakin ta da tausaya mata don tana gani don kawai rashin lafiyan dake damunta ne ya kawo mata wanan danyen yanke hukuncin da taiwa kan ta.

********* ********* *********
Ance labarin gari a tambayi dan gari ashe komai nawa dadin hira yaja Gajiye har sunyi hiran da Farida.
Wanan labarin ne da sunan kauyen mu da sunan iyayyena yadda za, a samay su idan sunje garin mu kaf Farida ta fadawa soja komai.
Haka yasa yafita batun daddy a nan birni suka zagaya shi da iyayyen suka tafi har kauyen mu gurin iyayyena.
Kan sunzo nemawa dan su aure na Allah ne ya taimaka babana da maigari yakira shi kan zancen basira yazo mai yace.
A gaskiya sunan na haifi Rahama ne kawai yanzu amma uwar rikon ta da maigidan ta sunfi ni iko da ita don ko a gurin su take kun ga idan nace nai masu haka ba kyautawa zama tare ba.
Basu so jin haka ba sai cewa Alhaji haruna yayi amma kai ka haifi abinka kana da iko da ita har yanzu .
Kayi tunane akai ko nawa kada kaji komai zan zube maku shi yanzu anan basai mun tashi ba.
Babana yace adaiyi hakkuri don Allah Alhaji a bari zan ga shi marikin nata don idan nai masu haka kamar naci amanan zamane.
Don dai a rayuwa banda abinda zancewa wa yan nan mutane sai godiya ga irin alherin da suke min.
Basu so haka ba sai da maigari ya basu hakkuri akan su dawo nan da sati mai zuwa suji shawaran da aka yanke akai.
Da haka sukai sallama suka kawo alheri mai yawa na ban mamki suka babana da dama duk wani wanda ke fadan maigari a wannan lokacin.
Suka tafi sukan mutane sai gani suke ana dace nayi saa da wanan babban kamu da nayi a rayuwana.
Kafin wani lokaci bari ya karade garin ko cewa wasu masu kudi sunzo neman aure na daga birni ai.
Bayan tafiyan sune maigari yake cewa baba yadda yayi yana da kyau gara da bai biyewa abin duniya sai an tsaya anyi bincike akai.
Don irin haka karshe sai anyi abin yazo ya ya koma ciki kuma don duk auren da aka gwada mai dukiya haka baya karko.
Don gaskiya kalaman dattijon nan yasa na zargi wani abu a kasa ko.

Babana da kanshi ya tafi gurin mama altine da wanan labarin tace ikon Allah amma may zai sa su zagaye ta bayan shi Alhaji yusuf sozo nan bayan a tare suke can a gari guda.
Ai idan ma da sanin shi to tare ya kamata suzo nan ko kuma azo tare da wakilin shi nan din.
Koma may ye zan kira ita yar uwar nata da take gurinta naji na bakin ta baba yace haka yafi dai.
Ya tafi ya barta tana mamare bayan ya dan bata wani abu daga cikin abinda aka bashi yakai saura ya boye bai bari mama lauratu tasan da maganan kudin ba.
Don da zaran ta sani sunan su sorry sai taga bayan su kaf hankalinta zai kwanta da su.
Inna da ta samu labari take cewa maigidan ta ita gaskiya mutanen sun bata tsoro don hankalinta bai kwanta ba sam da wanan magana maigari yace zai sayo mata kati sai ta kirani taji may ke gudana ne wai nasan da zuwan bakin ko kuwa ?

Sakon kiran da mama laraba kewa daddy ya samay shi don da wayan ta tai amfani ta kirashi.
Amma sai aka samu akasi baya gari yake cewa mama injin dai lafiya ko tace babu komai sai alheri wani dan magana ne nake son muyi da kai kawai.
Yace ta dakance shi zai dawo nan zuwa jibi don yaji may ke gudana a gurin ta sam bai kawo wanan zancen a ran shi ba don daga shi sai Sadatun shi ke wanan rikicin dama a tsakanin su don ko ni da akeyi a kaina banda labarin hakan.
Mama Labara taje gun mahaifin daddy ba tare da sanin yar uwarta ba takai mashi shawaran da Saade ta kawo mashi.
Dama shi Abba ya dade da bada goyon bayan hakan don haka bata samu wani matsala ba gurin fahinta.
Yake cewa tunda har matar shi da kansa ta bude baki ta bukaci hakan to ya kamata aje agana da iyayyena don su san da zancen suma.
Da dare daddy ya dawo don haka bai samu zuwa gurin mama ba sai da safe bayan ya karya yatafi ansa kiran uwar goyon shi kaunar mahaifiyar shi.
A falon ta suka zauna kamar ta sani Faridan ta ta canza yanzu tace dashi su fita daga waje magana ne wanda daga shi sai ita sai Allah take son suyi shi don kada abin yazo baiyi ba abatawa saadatu sunan ta ga banza.
Suna barin gurin ya bude mota motar shi suka shiga don ya fahinci magana ce mai muhinmanci ta siri kuma da alama bata son a ji koma may ye din..
Sunan shi ta kira a hankali take cewa da fatan abinda zan fada maka bazai zazzafa ma zuciya ba zaka tausasa zuciyar ka ka fahince ni da kunnen basira.
Yace insha Allahu mama nai maki alkawari koma may ne indai bai sabawa sharia ba zan yi nazari ko na rugumi ko may ye da zuciya daya da hannu bibiyu.
Tace masha Allahu nakuma gode Allah yai maka albarka da fatan samunbalheri ga abinda zamu tatauna din yace amin.
Tace Yusufa ina son na rokeka da farko da kayi hakkuri kuma ka kara hakkuri da iyalin ka kowa da irin rayuwan da Allah ya kaddaro mai dashi.
Yusufa ina son in roke ka ba don nakai ba ko na isa ba sai don hangen alherin da abin zaizo ya haifar daga baya.
Kayi hakkuri bukatar da matar ka ke binka dashi na auren yar uwarta ka yarda ka cika mata burin ta a kan hakan.
Don ni gaskiya Saadatu duk ta sare min gwiwa na da wanan zancen don haka zancen abune na a tsaya a duba bisa ga hujjojin da takawo din.
Kaga Saadatu dai mace baza, ace bata kishin ka bane tanayi kaima ka sani abinda manufan ta ya hango ne sai an daure za a hango shi din.
Sannan kuma aure ne take kokarin kullawa aure kuma kowa yasani sunnan ma, aikine sallalahu Alaihim wassalam.
Bai kamata ki daukan shawaran ta ba tunda itace da kanta ta bukaci da ai haka din baiwa kaine ka bijiro mata da zancen ba.
Balle tace anyi mata butulci ko wani abin cin fuska da zarafi, tazo ta mutu din da take ikirari kazo kana da ka sanin rashin cika mata burin ta tun tana raye.
Ka ga idan abin yai dadi ko bayan ta zata sha addua ga wanan hadin da tayi tsakanin ka da yarinyar nan.
Idan ma bata mutum ba dai itace ta bukaci yin hakan da kanta da bakin ta ba wai wani ya tilasta mata yin hakan ba ita ta nema da kan ta.
Tazo din ta mutu yaranta dakai da take ganin zasu iya fadawa wani hali kazo kana kukan rashin yin haka daga baya.
Jikin shi ne yai sanyi don bai taba tsanmanin wanan magana bane mama Laraba ke neman shi ba dayi.
Saadatu ta bashi mamaki matuka da ta nace akan wanan magana haka har yakai tun sunayi su biyu a tsakanin su gashi yanzu takawo maganan ga magabatan shi.
Yanzu shi yaya zai iyacewa mama hakan bazai yuyu ba bayan kwararan hujjujin da ta kawo mashi yanzu a gaban shi wanda ita da Sa,adatu ke gani hujjane a garesu.
Shi fa bai taba jin son Rahama da aure ba a rayuwan shi ba asali ma dai mamakin mazan da ke ta hauka akanta yakeyi don baiga abin burgewa gareta ba gaskiya sai dai idan farar fatan ta tane ke rudin su.
Shi bayan Saadatun shi fa baitaba tsayawa kallon wata mace bata bashi sha, awa haka na ba.
Ko su wa yan nan dake gidan shi aure daine mukkadari kawai a tsakanin shi da su har yake zaune dasu don biyayya kawai.
Amma bawai don yasan wani dadin zama da mace ba may mace zata iya maka wanda zai iya saka natsuwa ko shagalta a kan ta duk shi bai san wanan abin ba.
Can dai ya nisa bayan ya fahinci mama tagama fadar abinda zata fada mai shi take saurare yanzu.
Yace mama nagode da wanan shawaran naki tunda haka take bukata da kan ta insha Allahu zan yi kokari naga na cika mata gurin ta akan hakan.
Sai dai kuma bazan so jin daga baya tadawo tana wani korafi ba da bakin ta akan yin hakan kuma don mama kin san halin mata akan kishi kuma.
Ita Saade na rasa may nene ke damun rayuwa ta data yankewa kanta wanan danyen hukuncin haka ba ?
Mama tace yanzu ai koma maye dai itace ta bukaci ganin hakan a rayuwan ta ko naka yanzu shine kayi kokari kaga ka kwatanta adalci a tsakanin matayen naka.
Don tserewa hushin ubangijin ka a gobe kiyama Allah kuma yai maka albarka ya daukaka zurianka.
Yakare muna ku daga sherin makiya da mahassada nagida da na waje sai ka jajirce sosai gurin kwantata adalci akan iyalin ka don nauyi ne mai girma ya kara hawa kan ka yanzu kuma.
Na kuma ji dadi kwarai na rokeka alfarma irin haka kuma kai min shi a take babu bata lokaci don haka yanzu abinda nake son ka dashi shine.
Kabar wanan zancen a ranka itama Saade sai dai ka shirya yanda neman auren naka zai kasance idan har Allah yayi sai dai aji kawai anyi auren.
Don baiyyana shi zai iya kawo muhawara mai karfi har takai karshe azo a samu akasi a hakan.
Yace hakane mama insha Allah zan bi al, amarin a tsanake yadda abin zaizo a cikin sauki ba tare da rayuka sun baci ba akai.
Tace hakan na da kyau Allah yai maka albarka tagi ka huta abin baka dama aanan shine maganan kawai .
Yai mata godiya tare da sallama tana ta saka mai albarka tafita yaja motan shi yana tafe yanajin wani irin abu a zuciyar shi.
Shi yanzu ma ta ina zai fara ne wai takan Saade ko ta kan wanan yarinyar da akalaka mai akai ko kuma da maganan jama, a zaiji.
Mahaifin shi dana Saade ne suka fado mashi arai dole ta kan su ne zai fara bai tafi gida ba sai da yaje kasuwa ya samu Abba suka gana dashi akan maganan.
Abba yai murna kwarai da jin wanan labarin yake cewa yai matukar farin ciki da jin haka aiko ba komai Saadatu tayi jahadi babba anan, don aure ta hada don farin cikin ka.
Yasan Alhajin shi na gona a wanan lokacin don haka ya juya akalar motar shi zuwa gida inda ya nufo gidan cike da natsuwa da karin imani a zuciyar shi.
Don maganan da mahaifin Saade yai mashi a yanzu ya kara sa jikin shi yin sanyi ga ala, marin kowa na fada mashi cewa aure ne yayi kawai.
Yana shigowa gida ya nufi part din shi duk da sanyin Ac daya kunna a falon bai hana shi jin zafi ba a jikin shi.
Zama yayi tare da mike kafafuwan shi saman dan table din dake a tsakiyan falon.
Ya dafe kan shi da hannun shi daya yana jin kan nashi na matukar sara mashi a lokacin.
Shidai Allah ya gani wanan auren yafi ko wani zo mashi da rikici a rayuwan shi yanzu shi dawani ido zai kalli Saade ko dawani ido zai kalli Rahama wai a matsayin matar auren shi da zasu raya sunna a tare zaman aure fa ba zaman wasa bane anya kuwa Saaden shi tayi la, akari da wanan abin kuwa a yadda yasan mata da kishin tsiya.
Yanzu dai zaiga Saadatun don yaji ta ina zasu fara bullowa zancen don komai yanzu yana hannun ta ita da ta kawo maganan.
Zai danka mata komai ta gudanar yadda take bukata shi nashi idone kawai yaga iya gudun ta.
Yana zancen zuci Zulfa ta shigo falon da ganin yanayinta kasan bata da lafiya a lokacin .
Jin an shigo falon ne yasa shi bude idanuwan shi dake a lumshe ya sauke a kan ta.
Yace da ita lafiya yau kike kuwa ta samu guri ta zauna daga gefen shi tana cewa yau tunda safe a kwance nake na rasa gane kan jikin nan nawa duk kwanakin nan.
Yake cewa ki shirya muje asibiti yanzu adan kara dubaki muji may likitan zaice akai.
Ta mike da kyat tana fadi bari naje na dan kimtsa kafin ka gama sai na fito.
Tana barin gurin yake cewa a ranshi bari ya shiga gun Saade ya ganta tunda hakkanta ya cin ma ruwa ta kai ga yadda take son ganin su.
Fitina kawai take son kirkiro mashi yana fama da fitinan wasu takara saka shi ga wani sabo.
Yamike zuwa part din na anty muna zaune sai kwasan dariya muke Jinior ne ke bin mu yana cizo wai hakoran shi na kaikayi inji anty.
Ganin daddy ya shigo falon muka shiga gaidashi tare da kokarin mikewa mu bar falon don su gana inda nake zaune nake gaida sai baima tsaya falon ba ya nufi bedroom din ta yana fadin ke may ya hanaki zuwa school yau ko ba a karatu ne yau din.
Ta bi yan shi tana fadin ina zata fita mahaukacin soja ya saka security's dinshi akan ta ko ina tabi binta sukeyi yi
Yace binta kuma garin yaya haka ya faru ban sani ba kuma ke baki sanar dani abinda ake ciki ba tace yanzu haka kai nake jira ka shigo nai maka maganan ai.
Don ashe wai har can kauyen su ya tafi gurin iyayyenta ya nuna masu kudi nan dai tana zama take labarta mai abinda ke faruwa take cewa dashi yanzu haka ita duk a rude take ta rasa yaya za, a bullowa zancen don ta fahinci wanan sojan ba karamin tantiri bane gaskiya kamar aure dole ne ga mata a gari ko ina amma ya nace wa mace daya haka ?
Yace yanzu ma zancen ta ya kawo ni gurin ki ai bukatan ki ya biya tunda har kina son hadani da mamana fada.
Yace daga gurin mama furin Abba na nufa na fada mashi kina akan bukatan ki sai dai ki sani ba korafi ko wani magana akan hakan daga baya.
Don bani na bukaci yin hakan ba kece da hujjan ki mara tushe kin samu mama kin mata dadin baki ta hau ta zauna nai magana tace ban yi mata biyayya ba kuma don haka yanzu dabara ya saura gareku.
Sai ki san yadda zaki tsara tunda kece kika hada abinki da kan ki ba wani ya hada maki ba.
Tace Alhamdullahi Allah nagode ma dajin wanan labarin farin cikin hakika Rahama alheri ce a gare mu besty ba zaka gane manufana ba sai bayan anyi abin idan Allah ya tabbatar insha Allahu.
Idan har kana tunanen zan tsaya kishi da Rama a rayuwana kayi kuskure ni don ka nai wanan hadin amma ka kasa fahintana cikin saukin kai.
Kaima kasan abinda mata kewa bakin kishi ai abu daya ne ko toni ina iya hadawa danawa da nata duk ta kwashe na bar mata ita kadai in wanan ne?
In dai har zakai muna wanan alfarman ni da ita don ni may yarage gare ni banda bautan Allah kuma yanzu.
Wani kallo yai mata yace kada ki soma wanan maganan idan ba haka ba wallahi yanzu nace na fasa tace rufa min asiri idan ka kara botse min kuma wa na san zai taro min kai kuma ?
Ban ni dai yanzu nasan yadda zan bullowa wannan yar butsar din tawa don nasan akwai rikici babba tsakani na da Rama nan gaba.
Baki ya tabe yace wanan matsalar kune ni dama ban dauka aka ba balle ku tsanmani zan saka maku baki ga zancen

Please Login or Register in order to submit comment