Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

******

Zaune take a dan dakin da aka gyara mata dakin tsoho ne baida fadi sosai rufin shi duk ya tsofe sosai .
Tana gefe daya a takure cikin damuwa abinda tsohon nan yai mata a daren jiya tana ganin shi kamar baida karfi amma yafita karfi sosai yadda ya makureta ya nuna mata karfin maza duk ihu da shure shuren da takeyi sai da ya kai gareta.
Ga gari ya waye sai wani dan guntu kunu mai sanyj aka kawo mata duk kasari a cikin sa babu ko dadin ganin shi.
Ga yunwa yanzu yana damun ta ga wanan abin da take tunane da ya tsaya mata a rai idanuwan ta na kallon kofan dakin.
A inda take a zaune taga an bankado kofan dakin da karfi wata dattijuwa tagani a tsaye a kanta tana mata kallon banza tace da ita.
Ke may kike nufi da bazaki fito ki yi ko shara ba ko kin samu wurin mike kafa ne sai dare yayi ki cika mutane da ihu irin najiya kamar kanki aka fara aure.
Ban masan ihun dakikeyiwa mutane ba kamar sabon abu a gareki bayan kin gama ba yan kwararo kanki a garka.
An dai ji kunya wallahi wai budurwa a haka nakashe babu abin kai gida anan duk bakin tallan da ku kai wa uwar ku ta kasa sai maki ko yar katifan kada kizo dashi.
Ta karewa dakin kallo tana cewa ni ban maga wani abin kishi ba anan don dake da yar sadaka mai gindin banza duk daya kuke a gidan nan.
Kai koma sadaka aka bashi ke ai yafi nan kishi da wanan abin kunyan haka.
Indai da kwadai da wullakanci maza ki fito ga sharan gida nan idan kin gama ki wanke kwanukan da aka bata jiya.
Daga inda lawisa take zaune ta watso mata kallo tace ni ba zama nazo yi da tsohon mijin ku ba balle ki ce kin samu yar aiki don haka ki nemi mai maki wanan aiki.
Har ta kai kofa ta dawo baya tace towoo mara kunya dama nasan da halinki ba yau ba to ki sani kin samu tsohuwar zamani don zamuyu daidai dake ne a gidan nan.
Lawisa tace ai bana tsoron muyi daidai din ko kashe ni zakuyi keda mijin naku sai dai ku kashe ni amma bazan taba ko kara ba a gidan nan .
Muzuba dake ai jiki magayi wallahi ni dake a gidan nan kafin su ci gaba sukaji muryan su Rukaiyya ga maigidan a bayan su tafe cikin hasala shima.
Tana ganin yan uwan ta ta mike tsaye Rukaiyya tace maza tazo su tafi gida yau wanan bakin auren ya mutu ke nan.
Kofan Jatau ya tsaya yace sai yaga inda zasu fita da ita a gidan shi don babu shegen da zai fitar mai da matar shi.
Kudin shi yasa ya auro ta don haka basu isa su fitar da ita gidan nan ba nan suka shiga zagi suzaga ya zaga.
Rukaiya na ganin zai bata masu lokaci ta bangaje shi suka kwasa a guje yan gidan suka biyo su suna atare atare suka samu suka fice daga gidan.
Da kyat Jatau ya mike sai sannu yara da mata ke mashi don har ya gurje a gwiwan hannun shi.
Gidan maigari ya nufa a hasale yana zuwa ya labarta masu abinda ke faruwa a gidan shi.
Nan aka saka salati maigari ya tura aje azo da baba da mama lokacin yaran na mayar mata da yadda sukayi da Jatau a gidan sa da mutanen gidan.
Sukaji sallaman yaron maigari Rukaiyya ce ta fita don ganin mai sallama Lawisa sai kuka take wiwi tana Allah ya isa ga iyayyen ta da suka cuce ta suka kaita gidan wanan bakin tsohon kazami.
Rukaiyya ta dawo take fada masu ai yaron maigari ne yazo gidan yake neman mahaifin su.
Mama tace yafita ya tafi kasuwan kauye akace ance azo da mama nan mama tace babu inda zata sai mijin ta ya dawo.
Dole yaron maigari ya koma ya fadi sakon ta akace tana da gaskiya Jatau yayi hakkuri har lokacin da baba ya dawo sai a zauna.
Nan suka wuni mama da yaranta suna kulla abinda zasu yi idan sun je gurin maigari don sun san baba ba zai dauki wani matakin da ya dace ba ita ko ta sha alwashin sai ta debi wani abu gun Jatau da zata gyara dakin diyan ta dashi ta fitar da ita kunyan daki.
Sai yamma lis baba ya dawo gidan kamar kullun bai ko kai zama cin abinci ba yaron maigari ya sallama mashi yafita gurin shi.
Can ya dawo yana kwadawa mama kira tun a kofan gida tasan da maganan tafito cikin shirin ta tana cewa lafiya yake mata wanan kiran haka ?
Yace may Lawisa ta dawo yi gidan nan bayan an kaita gidan mijin ta don yanzu yaron maigari yazo yana sanar dashi halin da ake ciki.
Mama tace eh tana gida ita ta tura a dauko mata yar ta tunda yazo wa mutane da rashin mutunci har gida saboda yaji dafin ta bashi yarta ai dama kudin bazawara ya bayar bana auren budurwa ba.
Yanzu ko bata mayar mai da yarta sai ya zube mata kudin auren budurwa zata bari lawisa ta koma gidan nan nan.
Baba yace wai lauratu may kike so ne a duniyan nan wanan abin fa duk kece kika jawo shi ba wani ba don da baki karbi kudin shi ba ba zai saka mu a gaba ba hakan nan.
Wanan ma ai rufin asirin ki ne da yar ki don in bashi din ba da ya aure ta ya rufa mata asiri wayazo ya taya ta a gidan da sunan aure.
Tace dama ai bazaka ga laifin yarka da ta tsale ke ra gudu zuwa birni ba ita da aka biya kudin kan ta.
Don Rahama da uwarta sunfi karfin ka shine zaka ce dani haka ita Rahaman har wani farin jini ne da ita da tsufi ke zuwa neman ta gidan nan da zakaiwa diya na gorin aure.
Ko dai tsufi ne ke zuwa ta daifi wa yanda ke zaune gida suna aikata abinda bai dace ba aiko.
Don may bazai yi magana ba yaga abinda bai yi mai dede ba a rayuwan shi tace ai yanzu sai kaje kabashi wanda yai mai daidai amma babu inda Lawisa zata sai ya zube mata kudin auren budurwa.
Washe gari tun da safe suka amsa kiran maigari da yai masu sun samu har Jatau ya hallara a kofan gidan maigari.
Suna zuwa aka fara magana kansu maigari yana tambayan baasin da yasa mama ta tura a dauko mata yarta daga gidan mijin ta bayan an gama magana.
Mama ta kwashe cin mutuncin da Jatau yazo har gida yai masu tun dasafe tace wanan dalilin yasa ta rike yarta sama ai kudin bazawara ya biya bana budurwa ba.
Maigari yace malam Jatau may yasa ka aikata hakan ya gyara zaman shi yace wa maigari an samu kuskure a nan amma ayi hakkuri don shi gaskiya yana son matar shi don haka adaiyi hakkuri.
Nan mama ta kafe kan yarta bazara koma ba sai ya zube kudin da ake zubewa budurwa da kayan aure ko ya sakar mata yarta.
Jatau dai ya fahinci idan yai wasa wanan matar tafishi balai zai tashi a tutar babu.
Nan dai ya shiga kamay kamay yana bada hakkuri akan a dai yi hakkuri a bashi matar shi.
Amma mana ta kafe kan sai ya biya su kudin auren budurwa har aka watse a gurin ba akai ga matsayan zancen ba.
Sula dawo gida kowa na cicika gashi shi Jatau yaji dadin dan kwanan da yai da Lawisa duk da yadda yake ikirarin ya samay ta din amma son ta ya shiga ran shi lokaci daya.
Haka ya koma kamar karamin mahaukaci ranan har takai iyalin shi sun fahinci ya fada tarkon karamar yarinya da ya jajibo masu a gida lokacin.
Nan suka fara sake mai habaici irin na tsufin mata da suka san kan mata shiko bai bi ta kan su ba don ba batun su yake yi ba yana batun yarinyar dan ya sharaf.
Da yamma ya shirya yazo gurin mama don su sulhuta dashi amma babu magana mai dadi mama tana a kan bakan ta na sai ya biya sauran kudin auren budurwa zata yarda yarta ta koma gidan shi.
Tabarshi nan tsugunne takaicin ta duk ya rufeta badon yana son yarta ba don ya samu gurin sauke manyan ta shi da ba abin da zai hana yai mata rashin mutum ci amma babu yadda ya iya dole yabi ta yadda take so ya samu matar shi ta koma dakin ta.
Ita ko mama tana ganin ya fara saukowa ta sa a ranta sai tai mai mugun yaga sun kwashi rabon su sai ta lalashi lawisa ta koma don ko banza hakan yafi mata zama gida ai.
Da dabara mama ta fara koyawa Lawisa irin hikimar ta na kwatan abu a gurin miji da sauran dabaran zaman da zatayi a gidan Jatau ta zauna lafiya.
Mutanen gari sun saka mama a gaba da tsegumi amma ita ko a jikin ta hakan bai taba damun ta ba kanta kawai ta sani.
Har yaran nata suka fara fahintar halin uwarsu don sun fahinci kudine kawai a gaban ta lokacin ba damuwan su ba nan suka fara mata tijara ta kasa gane masu baki dayan su don sun hada kansu gareta.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA HAKKIN AMANA YA NA KANKI YAR UWA, ,
21

Sai misalin karfe biyu na rana anty ta falka daga nauyayen barcin da take yi lokacin.
A hankali ta bude idanuwanta da sukai mata nauyi muryanta a kasalance ta motsa bakinta da kyat tana fadin tare da bin mu ida muke zaune jugun jungun dakin ni da ma.
Rama sannun ku ko jikin har yakai an kwantar dani ko wallahi bana jin dadin jikin nawa kwata kwata.
Da sauri na mike daga inda nake zaune na kura mata ido ban ko kwakwaran motsi a lokacin.
Nake cewa sannu anty yaya jikin naki mama ma ta mike da sauri ta karaso inda muke tana mata sannu da jiki.
A hankali ta daga idonta ta kalli ledan drip din da ake kara mata tace har ruwa aka saka min ashe.
Nace yaya jikin karo na biyu ta daure ta kakaro murmushi wanda ya zama mata dabia hakan.
Tace Alhamdullahi Rama sannu da kokari kinji tajuya gurin mama tace mama sannu na hanaki hutawa ko ?
Mama tace Allah dai ya baki lafiya kin ji nace mama bari na kira likitan yace idan ta tashi a kira shi na mike ina kai kofan dakin aka turo kofan.
Mijin tane yashigo dakin da wasu leda a hannun shi na magani da fruits na karbi ledan mama tana mashi sannu da zuwa yake cewa ashe ta falka.
Heart beat yaya jikin naki tai mashi murmushi tace Alhamdullahi dear ashe kana kusa bakin gadon ya karasa ya zauna.
Tare da dan tausa muryan shi gareta suna magana yanayin shi a cikin damuwa yake sosai a lokacin na juya da sauri nafice zuwa fadawa likita ta tashi.
Bai tsaya likitan tare muka shigo dashi dakin nan ya samu suna magana yakarasa kusa da ita yana tambayan ta yadda take ji yanzu.
Bayan an rubutun da yayi na dan lokaci ya mikawa mijin nata takardan yace aje a sayo wanan magani a gwada mata a gani.
Likita yace za, a cire drip sai a bata abinci ta ci kafin a kawo wanan maganin da ya rubuta mata.
Tare suka fita sai ga wata nurse ta shigo dakin ta gaida mu nan ta fara cire mata ruwan dake jikinta tabar canular a hannunta tana mata sannu.
Ruwa na bata ta wanke baki tare da dan gyara zama nake tambayan ta azuba abinci ko na hada mata shayi ta sha ne ?
Tace tea zata sha kadan ko hanjinta zai dan warware mata don bata jin dadin komai a lokacin yadda tace haka ne mata tea mai zafi da kauri na hada mata.
Sai gashi ta dan fara zufa tace na bare mata lemo tasha sosai ta zauna tasha lemon da nake barewa ina bata sanka sanka tana sha a hankali.
Ranan dai haka muka wuni faman laluran asibiti don tace akai yaran daga school gidan sister din ta, sai a lokacin nake tunane ashe anty nada yan uwa a garin.
Ni dan zamana da ita ban ji tana magana akan yan uwanta ba ko da na rana daya ne amma sai gashi naji tana cewa akai mata yaran ta can gurin yar uwarta.
Haka dai na bar wanan mamaren a cikin zuciyana ni kadai naci gaba da abinda ke gabana lokacin.
Haka mukai ta fama da ita don taji jiki sosai abin tausayawa idan mutum ya ga halinda take ciki a lokacin.
Kwanan ta uku aka bamu sallama muka dawo gida don yanzu ba fever ba kuma dizzynes a tare da ita.
A hankali take lalaba rayuwanta inda duk wani motsin da zatayi idanuwan mu yana a kan alamarinta don likita yace tana bukatan hutu da kulawa sosai.
Wanan dalilin yasa muka mayar da hankalin mu akan komai da zatayi in ba wanka da kewaya ba babu abinda muke bari tayi a rayuwan ta.
Sai gashi cikin yan kwanaki ta gyagije sosai baka cewa itace tai ciwo haka a yan kwanakin da ya shige.
Har ta kwata asibiti ta dawo gida ni dai banga daya daga cikin abokan zaman ta ta leko taba da sunan sannu.
Abin ya bani mamaki matuka don ashe kishi harda ciwo anayi akai ashe kishi yana birni kauye hauka suke yi da sunan kishi.
Ranan da dare ta kirani take sheda min gobe monday zan fara fita zuwa training din data fada min.
Nace anty baza, a bari idan kin kara jin sauki ba sai na fara tace a, a haba aiko yanzu Alhamdullahi ai na samu lafiya sosai ni ko wanan adduan da kullun kike min ne waya sani.
Don ko da yaushe itace may cewa dani Rama ai min adduan nan mana na sha da sauri zan mike naje na samo ruwa nai mata tasha tana lumshe idanuwanta.

****** ********* ******
Tun da safe na shirya don tare da yara da zasu makaranta zamu tafi saida nayi duk wani aikin daya dace ace nayi a part din kafin na fita na shigo dakin anty cikin shirina .
Ta bani wani takarda da zan kai furin mukai sallama dasu na fita gabana sai faduwa yake don ban san may zan je na sama ba a gurin.
Makarantar yaran muka fara sauke su sai ya wuce dani zuwa inda zamu tafi mun dan taba tafiya mai dan nisa bayan mun sauke su sai gamu a wani bakin get an rubuta NANA TRAINING CENTER da manyan haruffa.
Nan ya saukeni tare da yin min sallama sai shidda zai dawo na yamma ya dauke ni kamar yadda anty ta umurce shi.
A hankali nake tafe sai mata nake gani manya da yara nau,i nau,i, kowa tana harkan gaban ta a gurin.
Wata yarinya nagani tafe da saurinta har ta dan wuce ni nai mata sallama nace don Allah office din shuga nake nema.
Da hannu ta nuna min ta wuce da saurin ta gurin na nufa amma office din a rufe yake lokacin.
Nakoma gefe na rakube a guri daya ina aukin raraba idanuwana gurin kallon masu shige da fice a gurin kowa sai harkan gaban ta takeyi.
Can naga wata mota tashigo har kofan office din da nake tsaye sai ga wata yar matashiyar mata tafito daga cikin motar rike da handbag din ta tana kokarin gyara gyalen ta.
Sai da tazo gap dani zata shige nai mata ina kwana ta juyo tana kallon na tare da amsa min har ta juya zata shige sai kuma ta waigo ta dan tsaya tace amma ke newa ce a gurin nan ko nace mata eh.
Dan kallona tayi sama da kasa tace ok ra sa kai tashige office din kai tsaye.
Sai bayan yan mintina wata ta leko tace ance ki shigo ina shiga ba laifi don gurin ya hadu sosai tace kece daga gurin anty Sa, ade ko ?
Nace nice hajiya take cewa yanzu ta bugo min waya amma na dauka ai ko wata babbace ke ashe karama ce.
Idan son samune da zaki iya sai mu jefa ki guri biyu kiyi training din mugani ko ?
Nace zan iya insha Allahu wanan matar dake tsaye ta kalla bayan ta gama dan rubutu a wani file tare da kallon takardun dana mika mata dana shigo.
Tace ki bita zatai maki bayanin komai idan kun fita nace nagode tace ba matsala muka fice muka barta aciki tana rubuce rubucen ta.
Matar da aka hada mu bayan mun fita tace kingane may ye sunan ki nace Rahama Aliyu tace zan fara kaiki ajin koyon zaman gida da sauran aiyuka idan mun gama sai mu koma fannin kwalliya da ado ko yaya kika gani ?
Nace nagode anty tare muka shiga na samu mata a zaune wasu harda cikin su wasu kuma dai gasunan.
Ta nuna min guri na zauna tai indroducing dina ga sauran mata ba bata lokaci aka fara normal activities din da suke yi gurin.
Sannu a hankali na fara fahintar abinda ake nuna muna na na kuma fahinci anty ta kawo ni ne don na fahinci duniya sosai kafin na shigeta.
Zama da iyali ne akai darasi a ranan kowa taba da hankali tana sauraren bayanin da akeyi a gurin.
Ana gamawa wasu suka fice wasu kuma suka tsaya aka fara darasin ado da kwalliya na jiki dana gida.
Haka muka wuni ana fahintar damu abubuwan karuwan duniya a gurin dan har tafiya da nau,in magana sai da na fahinta akwai sallon yin shi.
Sai biyar saura aka fito nan naga wasu masu training na shigowa matar tace na shiga tunda ba, azo daukana ba.
Fanin girke girke ne nan kuma aka shiga sabin darasi har shugaban gurin tana shigowa yin bayani abin gwanin ban sha,awa dashi.
Fitowan mu yayi daidai da zuwa Hamza driver na shige muka nufi gida da murna na.
Irin sallaman da aka koya muna yau da shi na shigo gidan cikin tausa murya harda dan tafiyan da aka nuna muna ya dace mace ta dinga yi.
Suna ganin haka suka saka min dariya anty dake zaune a kasa tace da kyau kaunata aiki ya fara ke nan.
Nai dariya na gaidasu da tambayan lafiyan jikin ta ban zauna ba na shiga na kwabe na dora muna girkin dare.
Sai bayan magariba nagama nashiga nai wanka tare da dauro alwala nai sallah.
Tun wanan ranan sai ya kasance banda lokaci kai ko kadan don busy nake koda yaushe haka ya rage min duk wani sauran kunci da tunanen gida dake cikin raina.
Sosai na mayar da hankalina ga training din dake bamu sai gashi tun ba aje ko ina ba na fahin rayuwa zan iya yin komai in a gentle maner.
Hakan yasa anty taji matukar dadi a ranta ko yaushe tana min kallon sha, awa sosai don jina take kamar blood sister din ta har cikin ranta.
Banda matsalan komai tare dani don komai nake so yanzu zata saya min shi ba bata lokaci haka yasa ma ko ina son abu ban nunawa a gabanta.
Ko abin yan mata tagani yanzu zatace wanan abin ya dace da Rama na bari na saya mata shi.
Mama Altine kance Rahama zaki ko iya shan ruwan garin mu idan munje.
Nace kai haba mama a ina natashi da bazan sha ruwan kauyen mu ba ni wacece mama?
Kwana biyu bana ganin mijin su kila don bani zama ne yasa bamu haduwa ban sani ba.
Na koma wata saliha dani don ko matan gidan na iya shegen su bana kula tsabgan ko kadan sai na mayar dasu wasu binan can.
An yi bukin yaye mu na course din wats biyu danayi a Nana traning center anty bata samu zuwa ba sai mama da yara ta tura sukazo min.
Alhamdullahi abinda akaje nema an samu don na sake gaba daya na koma Rahama ta ta birni komai nawa ya sake gashi makerin kyawona ya gama kera min hallitana na cika na zama budurwa a lokaci daya ko don sauyin abincin dana samu ne yanzu ba irin wanda muke ci a kauye ba nai saurin wanan girman haka ?
Sati daya da gama training dina addimition dina ya fito na jorna da BUK nan na fara zuwa makaranta ban samu wani wahala ba don yanzu kan mage ya ya waye sosai.
Ranan na dawo da yamna lis a gajiye nake banga anty a falon ta ba yadda na saba samun ta tana dan zama ana hira.
Sai da na shiga gurin mu na aje kayana nafito zuwa dakin ta a kwance na samay ta nace anty lafiya dai ko ?
Tace da sauki yau ina dan jin jikin ne Rama amma ba wai wani can ba da yamman nan ne ai na, dan ji ba daidai ba.
Na dan tsaya tsaye ina nazarinta a gurin sai dai ban fahinci komai ba na juya na fita zuwa kitchen.
Abinci na hada muna don baci akeyi ba sai nayi dan kadan nagama na shige dakina wanka nayi na fito zuwa gurin anty na samu ta tashi tayi sallah tana zaune a gurin ta ishishire kafata tana ganin na shigo ta mayar da hankalinta gare ni tana fadin har kin kammala ne Rama ?
Eh anty na bata amsa ina nufin gadon dakin dake yamutse a lokacin na fara gyarawa tace ai dama kin barshi har da safe ki gyara nace bari dai a gyara kiji dadin kwanci ai.
Fira muke ina dan kawar da kayan da nagani barbaje a dakin take cewa dani ya kamata fa idan kunyi hutu ki dan leko gida hakana.
Kada muyu rashin hankali yau fa kin kai wata biyar a garin nan babu wani labarin gida kada ace ko an sace ki ne ai.
Dariya nayi nace haba dai ina zasu zaci haka tunda sun san da mama muke nan din ai bazata bar dukiyanta can ba ta gudu.
Innan ki nake tunane wallahi nakan so a dan aika mata da dan wani abu sai dai gurin nakune da wuyan zuwa wallahi sai in mutum zan tayar yatafi can din.
Anty ai zan tafi da zaran anyi hutu na dubo su nima hankalina yana gurin inna wallahi ga rayuwa yanzu kowa kan shi ya sani.
Amira ce ta shigo dakin tana kwala min kira wai nazo ga Nasir zai bata min waya na ya dauka yana game dashi.
Amira bari ya gama sai na baki ke ma kiyi game din dashi a, a Rama jeki karbi wayan ki bana so ana ba yaro waya ni.
Ba wasa a fuskanta don haka na bar

Please Login or Register in order to submit comment