Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rikeni riko na tsakani da Allah ba kissa ba cutarwa tsakanina da ita amma yau ga shi wai mijinta mijin sunnan tane mijina nima.
Tace to daure kije kiji kiran da hajiya take maki yanzu kinji yi hakkuri don Allah kibar kuka.
Na mike da kyat tare da gyara hijjabin dake a jikina na nufi falon idanuwa da suka sha kuka sunyi zurun zurun dasu don kukan da nasha.
Ina shiga falin daddy na fara tozali dashi ya shigo gaida mama da zuwa magana suke da mama da anty da ganin shi abuga na miji hankalin shi a kwance yake abin shi .
Yana saye cikin shadda ghalila mai ruwan danyen kore sai maiko takeyi a jikin shi yana sheki.
Sai naga ta kara min kwarjini a idanuwa na yau fiye da yadda na san shi a baya sajen fuskan shi ta kwanta lub lub a fuskan shi zakace baima taba aje mace ba a gidan shi don kurciyar shi daya fito fili.
Wani irin shock naji har cikin kaina da sauri na dukar da kaina kasa kamar na bude kasa na shige don kunya.
Da kyat na karasa gaban su tare da rusunnawa a gaban anty kamar kullun ina fadi cikin dassashiyar murya gani anty.
Tace dani bakiga mijin ki bane banji kin gaida shi ba da kwana mana ko kin gan shine yau da gari ya waye ?
Hmm naji mama tace tare da fadin ikon Allah wai in baka mutu ba baka gama ganin ikon Allah ba aduniya.
Jin abin da mama tace yasa daddy ya kai hannu a fuskan shi cikin dan furzo da iska daga bakin shi yana shafan sajen fuskan shi a hankali da hannu daya tare da dauke kan shi daga kallon mu.
Umurnin anty na bi cikin dassashiyar murya nace a hankali daddy ina kwana.
Dan gajeren murmushi yayi tare da mikewa yana fadin shi zai fita yana ganin zai isa a wudil akwai wanda yake son gani a can.
Anty tai mashi a dawo lafiya yafice daga falon ba tare da ya tsaya amsa mata ba ita ma.
Anty take cewa dani bayan fitan shi Rama kina son kijawa kan ki ciwo ne haka ko kije kiyi wanka ki gyara jikin ki don Allah ki daina wanan kukan haka mana may ye amfanin kuka hakane wai ?
Ikon Allah lalai Saade kin dauko wa kanki ruwan dafa kanki da hannun ki yanzu kamar Rahama yarinya son kowa kin wanda ya rasa kike kokarin cuna ta haka ga mijin auren ki.
Yarinya ta zauna a cikin tsofin mata tayi kishi dasu ba wani hayani shine wai har kike gwada mata yadda zatayi da mijin auren ki.
Haba dai mama mijin ta ne fa itama yanzu yadda nake da iko dashi haka itama take da iko dashi a gidan nan.
Yaya zanga abinda zai iya halakata ban lurar da ita ba hanya madaidaiciya.
Mama tace eh lalaine kuwa naga alaman hakan lalai kinyi nisa bakuajin kira yanzu kan dole sai na mike nasan abin yi akai.
Don Allah mama kada kice zakiyi wani abin kaucewa Allah anan da hankalina wallahi.
To inko da hankalinki kina bukatan addua gaskiya don abin naki bana kai sake bane an dai kaiki an baro kawai anga gurin ci.
Na hade yawu masu daci ikon Allah yau ni mama Altine ke aibantawa haka har da zargi akaina wai nakai anty gurin boka da malamai na kwace mata mijin ta.
Maimakon na shiga wanka na koma bakin gado na zauna sai sake sake nake a cikin raina ina maijin kunan rai a tare dani.
Zuwa tsawon wani lokaci na daina jin maganan su a falo haka yasa na fahinci sun shiga daga ciki ko daya ya tashi yabar daya a gurin.
Na mike na fito don na gaskanta hakan kamar zan dauki wani abu a gurin babu kowa a falon har gajiye ina gani tana ciki tana aiki a lokacin.
A hankali na nufi kofan fita daga part din na bude shi cikin sanda na fice daga part din na nufi hanyan fita get.
Gefen filawa nabi ina tsoron kada na hadu da wata daga cikin matan gidan don ina tsoron haduwa dasu yanzu saboda na zama mara gaskiya a cikin su.
Ina kaiwa bakin get maigadi na hangoni yafara washe baki yana cewa cikin jin dadi hajiya Rahama ashe wani abin arziki ne ta samay mu haka kuma ?
Sai da safen nan ai nake samun labari gurin mutanen gidan nan ban tsaya sauraren karshen maganan shi ba na bude get na fice daga gidan.
Nai saa wani mai Napep ya kawo wasu mata uguwar na tsayar dashi na dauki shata sai uguwar su Zarah na nufa.
Nayi saa zarah na gida a lokacin bata fitaba tana gani yamutse dani na hargitse takw cewa dani Rahama lafiya kike kuwa kika koma haka lokaci daya ?
Ban tsaya bata amsa ba na fada saman fogon kujeran dake falonta na shiga kuka ba kakautawa hankalin Zarah yai matukar tashi sosai tai tambayan duniyan nan a kaina babu amsa gare ni.
Sai itama ta shiga kuka don tasan akwai mugun labarin da zan fada mata wanan irin kukan haka danakeyi balafiya ba dai kan.
Sai da mukayi mai isar mu takoma tana lalashi na kuma cikin tsigar lalami da ban ki har na dan tsagaita kukan nawa.
Nace zarah na shiga uku na lalace a rayuwana na zama babban yar cin amana yau zarah ina zan sa kaina yau zarah na shiga uku zarah.
Tace don Allah don kaunarki da Annabi ki fada min may ke faruwa dake wai Rahama don Allah daina kukan nan ki fada min.
Na dago jajayen idanuwa na sauke su ga nata nace cikin kuka Zarah aure aka daura min jiya.
Tace aure aure Rahama aure dawa kuma shine kike wanan kukan kamar mutuwa wallahi na dauka wani abu ne ya samu antyn ki ko wani naki.
Nace zara dole inyi kuka zarah wanda aka daura min aure dashi ne abin kuka da tashin hankali.
Wa aka daura maki aure dashi Rahama ta fada cikin son jin mutimin da aka aura min.
Na dukar da kaina kasa tare da girgiza kaina cikin takaici na kamo hannun ta na jimke cikin nawa da karfi na sako wasu hawaye daga kwayan idona nace.
Zara Daddy Zarah daddy mijin anty na shi aka cuce ni zara aka mayar dani yar cin amana ga idon duniya yau.
Salati ta saka tace cikin dafe kirjin ta Rahama wai da gaske kikeyi wanan mijin yar naki kuma kika aura don Allah.
Na tabe baki nace wai haka sukace niko ko kashe ni za, ayi sai na kashe wanan bakin auren da akai min .
Hannuna takara matsewa cikin nata tare da girgiza kanta a hankali tana fadin Allah kadirin Allamanyashau .
Rahama Yisuf Rano ne mijin ki yau kuma Allah abin godiya amma yaya hakan ya kasance ne wai ?
Nan dai na koro mata dan abinda na sani tace yanzu ma ashe da yardan anty ki akai wanan hadin shine kike tayar da hankalin ki haka ?
Maimakon ki godewa Allah da yabaki miji malakin iri Yusuf Rano da duk wata mace ke mafalkin samun irin shi a duniya .
Yau ke Allah ya baki shi a cikin sauki shine bazaki godewa Allah ba akan wanan kyautan da yai maki na bazata.
May kike so Rahama illimi addini na boko arziki kyawo da kuma zati duk ubangiji ya hore ma Yusuf shi.
Don haka kamata yayi ki godewa Allah akan wanan baiwan da yai maki haka a lokaci daya.
Kallon ta nake galala cikin mamaki don lafazin ta jin shi nake kamar tana watsa min ruwa zafine a jikina bazan iya sauraren ta ba don haka namike tare da daukan jakkana tabini da kallo tana fadin ina kuma zaki haka muna magana ?
Gyara hijjab dina nayi na goge hawayen dake fito min nace nina tafi Zarah na dauka zaki bani shawaran da zan samu mafita ne a cikin sa ashe ke ba haka zuciyar ki yake ba kina cikin masu biyewa son zuciyar su kan abin duniya.
Nan na barta tsaye tana mamakina na fice daga gidan tafiya nake ban san inda nake saka kafana ba da kyat na iya tare mai adaidaita sahu na shiga tasha ya kaini inda zan samu mota.

********* ********* *********
Karfe biyu suna kofan mai gari sun zo suji inda shawara ya tsaya akan dan su don su samu a tsayar da matsaya akan zancen.
Don suna son nunawa Yusuf Rano bai isa ta hana su abinda suka gani suna so ba gari.
Don ma sunyi bincike a kan shi an fada matsu irin matakin daya kai zuwa yanzu yana cikin jerin matasa uku da ake ji dasu a gari.
Don akwai su da taimako al, umman garin da na kasa dasu gasu da kokari gurin taimakawa matasa samun aikin yi agari.
Wanan halin ne ya kara ja masu farin jini ga mutanen gari da daukaka duk inda aka ambaci sunan su zakaga ana girmama su sosai.
Haka yasa sukai shakkun taka shi yadda suka saba taka duk wani mara karfi daya shiga tsabgan su a gari don ba mutunci ne da su ba.
Cikin girmamawa aka karbe su tare da duk yi masu abinda aka saba taron bako dashi.
Sai bayan sun natsune maigari ya fara dayi masu sannu da zuwa nan mai magana yace da maigari sunzo ne su ji inda magana ya tsaya don a shirye suke tafe da komai daya dace.
Maigari ya dan murmusa yake cewa a gaskiya bayan tafiyan ku an samu akasi ga hakan don yanzu haka maganan nan da mukeyi daku wanan yarinyar ta zama mallakin wani a jiyan nan.
Don an daura mata aure ta zama matar wani ko yanzu sai dai muce ayi hakkuri da wanan kaddaran haka Allah ya nufa ba zata zama surukar ku ba sai wasu.
Alhaji haruna ya dago kai cikin mamaki yace aure fa kace an daurawa wanan yarinyar kuma ?
Eh hakane Alhaji Allah yayi ikon shi jiyan nan iyayyen yaron nan da take can gurin shi a birni sukazo da yake dama da sanaya Allah kuma yayi shine mijin sai aka daura atake dashi.
Kana nufin Y Rano ta aura ko may ban fahince ka ba maigari ?
Wanan dai yaron marikin ta can a birni shine Allah ya nufa ya zama mijin ta a jiya jiyan nan.
Amma maigari bakuyi muna adalci ba wallahi ta yaya zakuyi muna haka a gaskiya bakuyi muna adalci ba anan.
Mikewa yayi fuuu ya fita daga zauren ana kiran shi amma bai tsaya ba makarraban shi suka bi bayan shi suma suka fada motar su a fusace suka bar garin.
Can kusan hawa titin da za a sauka a fada hanyan kauyen mu da babu kwalta nan na hadu da motocin su har biyu biye da juna nabisu da kallo ina tambayan kaina ko motar su waye haka kuma suka fito kauyen mu.
Muka fada hanyar kauyen mu gwaram gwaram mota shake da kaya da dabbobi a cikin sa muka isa garin bayan sallah la, asar ke nan.
Daga bayan gari na sauka naja hijjab dina na rufe samar fuska yadda babu wanda zai gane nice a lokacin don yan gulma.
Gidan kakan nina na nufa don can yafi min siri sai zuwa dare na karasa duk inda zan nufa walau gidan mu ko gidan Inna ta.
Sun tare ni da ba, a sai dai da mamaki fal a fuskan su don basu tsamanin ganina ba cikin wanan lokacin haka jiya jiya fa aka daura min aure.
Nasamu suyi gurasa shi na zauna naci sai da na koshi na sha ruwa na mike nai sallolin da ake bina nan na zauna ina ci gaba da zubar da hawaye.
Kakata mace ce ta shigo dakin ta samay ni zaune ina hawaye ta samu guri ta zauna tana kallona cikin tausayawa.
Tace dani Rahama may yakawo haka ne wai ko bakyason mijin naki ne kike wanan hawayen haka.
Kaina na girgiza tare da gyara zamana kafafuwana dake mike na mayar na lan kwashe su tare da dukar da kaina nace.
Attu bazaki gane ba ban san may nayi ba ko wani nawa yayi a duniya wanan irin kaddaran ke samuna ?
Dafarko auren garbati an min shi nai biyayya akazo kan Jatau da akaso lakaka min Allah ya kareni daga hakan .
Yanzu kuma Attu a rasa mijin da za, a aura min sai mijin anty na uwar dakina matar data dauke ni kamar yar data haifa a cikin ta.
Attu a wayi gari kuma yau ace wai mijinta aka daura min aure dashi may nayiwa su baba suke min haka a rayuwana?
Idan da can an min haka ina karama ni yanzu ai naci a tabayi ra, ayina akan hakan .
Murmushi tayi tace yo in banda abinki Rahama har nawa kike in ba lalacewan duniya ba da zakice sai an tambayi ra, ayinki kan zabbin dakike so ga auren ki.
Baki na turo ko ina dai ba dadi ke nan bakin su daya ke nan kowa na goyon bayan a binda bai dace ba su a ganin su wai hakan ya dace ke nan a gurin su?
Nace amma Attu ana barin hasal kodan kunya kuma ko ?
Tace kaiyya shike damuwa al, aumma abinda Allah bai haramta amayar dashi haramu don al, ada kawai amma in bashi ba ai ita boyar Allah nan ko banza ba wani hadin jini a tsakanin ki da ita sai so da kauna da yarda ya hada ku.
Dayake ita ta Allah ce tana da zuciya irin na addini ta san ya kamata kuma ta bukata aka aiwatar mata da bukatan ta.
Allah kadai yasan dalilin yin haka a gurin shi don don shiyasa boyayyen alamarin da ya boye a hakan da akayi.
Ni wanan matar bamu da abince mata a duniya sai mu bita da addua ita da zurian ta na alheri.
Yanzun dai ki tashi ga ruwa can mai zafi kiyi wanka ko zaki dan ji dadin jikin ki, kici abincin dare sai ki kwanta.
Ban ki ba don ina bukatan wanka dama namike na je na iske har takai min ruwa ban daki na shiga na watsa nafito na debi maclean nai brush ko zanji dadin bakina tare da dauro alwala nazo na jira lokacin sallah.
Kafin na gama shiri naji har an fara kiran sallah na tayar da sallah ina gamawa wani sanyi da zazzabi suka rufe ni a lokaci guda nan na dunkule dadafe na iya sallah isha, i na kara dunkulewa a gurin babu natun fita ke nan gare ni.
Zazzabi ne mai karfi ya rufe, ni lokaci daya Attu tashigo dakin ta samay ni ina rawan sanyi cikin hijjabina tace lafiya dai Rahama nace da ita Attu zazzabi ne ya kamani.
Subbahanallahi yanzu kuma kinzo lafiya ciwo kuma haka a gagauce ya rufe ki cikin rawan murya nace idan kina da bargo ki kara rufa min don Allah Attu ?
Inajin mijin ta ya dawo take fada mai nazo amma banda lafiya yashigo yadda ya ganin a rufe yasa shi rudewa yafita ya samo min yan hadiya ban ko tsaya dubawa ba na hadiye don wahalan da nake ji.
Hakana kwana dasu ina ta faman yi masu sambatu har garin Allah ya waye suna kaina sai sannu suke min.
Washegari tunda safe inajin Attu nace wa mijin ta kodai yarinyar nan tana da aljannu ne a kan ta ba asani ba jifa yadda ta kwana tana sambatu kamar mai shafan jinnu.
Yace bari dai nai sakkon samun iyayyen ta na fada masu halinda ake ciki kar muzo mu aje yar mutane a gida haka.

********* ********* *********
Gajiye wai may Rama keyi a daki tun da rana banga fitowan ta ba falon nan Ramako na da hankali ta kama kunshe kanta a daki kamar wata bakuwa can.
Cikin mamaki Gajiye tace hajiya ai na dauka tana dakin kine kwance tun dazu don dai bata dakin su.
A razane Anty tace ina ta shige kara duba min ita don Allah suka kewaye gidan kaf bani cikin part din anty tace duba min key din dayan part din nan da babu kowa a ciki ko can ta koma ta zauna.
Mama dake bantalan goro zataci tace may zaikaita can aiko data isa rasa kunya beran tankwa ke nan don samun guri.
Gajiye tafito daga dakin da key a hannunta tana fadin hajin kin ga ga key din nan bata can ke nan don guri a rufe yake yadda yake ko yaushe ai.
Nan dai hankalin anty ya tashi ta kira wayana not rechable ake fada mata, ta mike ta fice daga part din zuwa bakin get ta tambayi maigadi ko yaga fitana yace lalai yaga na fita amma baiga dawowa na ba gaskiya.
Da sauri ta koma dakin mu ta bude wardrobe din kayana kayana suna ciki a jere yadda suke tabi kan mirro da kallo taga babu brush dina da man shafina a gurin.
Daga tsaye takai zaune saman gado tana fadin haba haba Rama may nai maki mara kyau da zakiyi min haka ?
Ban dauka alheri zai zama maki fitina ba a rayuwana cancantaki ahaka yasa nai maki wanan alherin na sadaukar da kaunana a gare ki.
Gajiye dake tsaye tace hajiya a daibi sannu babu inda zata inda ya wuce gida ai sai a buga aji idan ta na can gida din.
Anty tace wanan ai abin kunya ne aji cewa wai gudu tayi don Allah gajiye ina rokon ki kibar wanan magana iya ni dakw ko mama bana son tasan cewa gudu tayi don kalaman mama suna bata min rai wallahi.
Yanzu abinda za, ayi shine dauko min wayana falo naji ko tana can gida kinga mun san inda take ai bana son na kira waya a gaban mama ne.
Takira layin da muke kiran Inna ta bai shiga ba sai takira lawali mai waya yaje ya tambayo inna ko nazo.
Ya tafi gidan maigari wurin inna bayan yai masu bayani Inna tafito da kanta tai magana da anty kamar haka.
Hajiya mun wuni lafiya tace Alhamdullahi Inna yaya yaran suna lafiya ko ?
Duk lafiya lau muke,
Inna ko Rahama ta karaso gurin ku ne don bata nan ?
Cikin raza inna tace bata man hajiya ina tashiga kuma don dai wallahi batazo nan ba.
Anty tace don Allah a tambaya gidan sauran yan uwa ko tana can don Allah amma Rahama bata kyata min ba data wuto bada sanina ba yanzu ma dai asan inda take shine ai matsalan.
Inna tace hajiya sai mukaji labari ba dadin ji amma don Allah hajiya yaya akai haka ?
Wallahi wanan abin har ga Allah bai min dadi ba ace yarinyar tarasa mijin da zata aura a rayuwan ta hajiya sai mijinki uban diyan ki ?
Kai haba Inna wanan ra, ayina ne hakan wallahi Rahama bata ma san anyi ba sai bayan anyi na fada mata shine nan ta tayar da hankalinta haka .
Gaskiya hajiya abin ne babu dadin ji wallahi dole ne ta zargi kan ta ai don tasan bata kyauta ba wallahi.
Ni dai don Allah idan har wani abu ke faruwa zamata da ku don Allah ki fada min hajiya kada ki boye min don Allah ?
Wallahi inna iyakar gaskiyar ke nan ma fada maki yanzun dai ki bari sai na shigo zakiji komai ai inna ki kwantar da hankalin ki a duba muna ita zan kara bugowa anjima ta wayan ki.
Sukai sallama Inna sai faman hakkuri take ba anty ita ko sai fadi take wallahi babu komai da yardan ta akai komai asalima ita Rahama bata san komai ba ga hakan.
Bayan wani lokaci takara kira Inna ta kara fada mata ta aika duk inda ake tsanmani zan tafi bana can .
Haka yasa hankalin anty ya kara tashi ta tayar da Gajiye da hamza driver suka tafi gida zarah ko ina can.
Tace da Gajiye nazo amma ban jima ba na bargidan don ta fada min gaskiya.
Hankalin anty ya tashi ta shirya lokacin da tasan mijin ta yana gida ta nufi falon shi.
Yana zaune kasa saman kafet da remote a hannun shi yana ganin ta ya bita da kallon tausayi.
Ta samu guri ta zauna tare da gaidashi da dawo ya amsa mata a kasalance sai tai shiru ya mayar da fuskan shi ga kallon news din da akeyi a tv.
Can tace besty akwai matsala fa a gidan nan ya juyo da sauri yace matsala kuma ;amay ?
Tace wallahi tunda rana mun nemi Rama a gida nan mun rasata kuma na buga waya can kauyen su bata can.
Yace shine matsala na dauka wani abin ne kuma ya faru baya na har kin tayar min da hankalina haka ?
Tace wanan ba matsala band nata da hankali besty yarinyar nan fa a hannun mu take kuma ace ta bata?
Yace Rahama yarinya ce da zaace wai ta bace ta san dai inda ta tafi don haka banga abin tayar da hankali ba anan.
Kallon mamaki take mai kafin wanin su yayi maga Nasir ne ya shigo falon yana fadin Mummy ina little mum dina ta tafi ban gan taba tunda na dawo school ?
Nasir Rama ta tafi unguwa tana nan dawowa wani irin ba dadi yaji don tambayan da yaron yai min.
Nasir ta kara cewa mummy bazan ci abinci ba sai anty ta dawo muci tare bari naje nai game har ta dawo ?
Kiran yaron yayi yace zo nan muci tare da kai ko baka ci da daddy Nasir ?
Yaron yace zaka bani a baki yadda anty ke min daddy ?
Kallon matar shi yayi ta kada mai kai alaman bagashi nan ba ka fara gani.
Sai ga Amira ta shigo tace mummy ina little mun tazo ta samin kayan barci tai min addua zan kwanta ne barci nake ji.
Nan ya jawo yarinyar yake cewa zo nan nai maki addua sai kije ki kwanta kinji uwata.
No daddy na anty nake so ita har a kafa take muna addua idan zamu kwanta tace shedan bai zuwa gurin batcin mutum.
Ikon Allah yace a fili Saade yaya akayi haka kika bari komai sai yarinyar nan kewa yaran nan idan da wani guri tai auren yaya zakiyi da yaran nan haka.
Tace tafini kusanci dadune yanzu shiya kawo haka kadai san matsalata aiko.
Don haka hakkuri zakayi gobe mu shirya mubita tun kowa baiji asan abin yi akai.
Ya kallo ta wani iri yace wa ni badai ni ba nina aike ta komay kedai da kika ce kinji kin gani dabara ya rage naki yanzu ai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA, A YAFE MAKI BA DABARA YA SAURA GA MAI TSORON ALLAH ANAN, , ,


IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA

Please Login or Register in order to submit comment