Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da kyau ya jawoni ya matse ni gam a jikin shi yace haka ba kyau sai may ke da kyau akace.
Rama iam in need of you ina bukatan ki ina son shan wanan abin sosai a jikin ki ina jin dadin hakan kina da matukar dadin al, amari Rama.
Ganin yana kokarin kauce hanya yasa na saurin dan dukawa na zille daga jikin shi nai kasa ya dan kalle ni a kasalance yace rowan su zaki yi min nace inda kake ma yau akwai irin shi a can daddy kada kasa muyi sabon Allah please.
Ajiyan zucita ya sauke tare da kada kanshi yace banzaci zaki hanani abinda zuciya na ke muradi ba.
Saboda ke na kasa tafiya aikina ina jiran dawowan girki na dana na wuce abinda ka fisheni Rama.
Nace daddy kaji ranan ai ba yawa yafi mu fada ga sabon Allah haka ba kyau ai kasani.
Baiyi magana ba sai gyara kwalar rigan shi yayi yadan kalleni ya juya ya fice daga dakin nawa kawai.
Nabishi da kallo ina jin wani abu a raina shin dadin abinda yai min ne ko tausayin halinda yake cikine a lokacin bandai sani ba..
Daga haka na mike na shiga ban daki na dauro alwala har nai sallah ban daga ba ina wurin a zaunr kunya da nauyin yadda zan fuskanci anty nake ji lokacin.
Babu yadda zanyi dole na mike ina saye da hijjabi mai hannu a jikina na nufi part din yara na samu sin dawo.
Na shiga suna ganina sukayo kaina kallo daya naiwa jinior na fahinci baijin dadi da sauri na karasa gun su na dan riko shi ina tambayan shi may ke damun shi ne ?
Sai ga uwar tafito daga daki itama bata kwabe bijjab din jikin ta ba da tai sallah take cewa ni koro shi ina sallah yazo yana damuna.
Nace anty jinior fa baida lafiya ne, tace lafiyan shi lau kalau yake fushi yake na koro shi kawai.
Najawo yaton zuwa jikina inda nake tsugune nace ga jikin shi da zafi sosai tana kokarin gardama nace maike damun ka jinior yace goshi na ke ciwo nace da ina kuma ?
Ya bude baki zai min magana sai amai yazo mai shar ya amaye min duk jikina da amai ban damu ba duk na rude na da sauri itama ta karaso tana cewa ikon Allah.
Har ina gardama ashe ko baijin dadin jikin shi ne haka banyi ta kaina ba sai da na tube yaron na goge mai jikin shi nace gajiye don Allah dauko min rigan shi da sauri daki.
Ta fice ta dauko rigan na saka mai na kwantar dashi namike na cire hijjab dina daya baci da aman yaron.
Dagani sai dan karamin riga daidai cibina sai dogon wandon dake jikina surar jikina ya fito gwanin ban sha,awa dashi.
Na dan duka gurin yaron dake kwance ya dunkule a guri daya ina dan tausa mai cikin shi a hankali.
Daddy ne kaman an jefoshi falon a lokacin ya shigo yadda ya samay mu mu uku akan yaron ne yake tambaya tun bai karaso ba mai ke faruwa ne kuma.
Juta mukayi inda yake tsaye yanan shigan shi ya nuna ya dawo ke nan ba zai fita ba kuma indai kagan shi a cikin jallabiya a jikin shi.
Anty ce take cewa baida lafiya ne sai amai yake ta faman kwararawa tun dazun.
Ya nufo inda yaron yake ya dan duka gareshi tare da kura mai ido kamar yana nazarin shi.
Inda nake ya jiwo yana may ya samay shi yanzu yanzun fa na dauko su daga islamiya lafiyan shi lau.
Fever ne ya kama shi ina ganin sanyin da akayine ya dake shi hakanan.
Yace sai da nai magana da na ganshi da dan riga karami haka a jikin shi wanan wani haline irin sanyin da akayi yau za, a sawa yaro wanan dan riga haka ?
Yanzu gashi anja mai ciwon haka ga banza saboda rashin sanin zafin kai don may baza, a kula da yaro ba irin wanan ?
Gajiye dake daga gefe itace ta saka mai kayan a jiki da zai fita tace cikin sanyin murya wallahi shi ya matsa sai su yake so.
Yace don ya matsa shine dole sai su za, a saka mai baida wasu masu nauyi ne da za, a biye mai son ran shi haka ?
Ranan munga fadan daddy cikin bacin rai yace a shirya shi su kai shi asibiti a gani .
Ni dai ina gefe na makure guri daya don ya bani tsoro yadda yake faman fada haka ido rufe kamar yaron ne kawai dan shi kwaya daya a rayuwan shi.
Tare da anty suka fita sai bayan fitan su na sauke ajiyan zuciya.
Sai wani lokaci suka dawo gidan yaron ma yayi barci yasha allura da magani.
Naso na kwana gurin shi amma anty ta hana tace naje na huta ba ga gajiye nan ba gobe akwai makaranta kada na wahala.
Washegari tunda safe na shigo duba yaron yana barci har lokacin na dan dade tsaye anty tace kada fa ki makara Rama.
Koda naje school sai da na bugo wa anty waya ina tambayan ta ko ya tashi yaci abinci tace gsshima zaune yana shan tea zamu koma dashi asibiti idan baban su ya fito.
Haka yasa hankalina ya dan kwanta naci gaba da karatuna don Allah ya gani har cikin raina ina matukar jin yaran anty a raina.
Ba dole na so su ba so kuma na tsakani da Allah ni da uwarsu taiwa hanyan alheri a duniya iri iri wani ma ban iya tuna shi.
Sai shidda saura na shigo get din gidan na kai motana inda ake aje mota na aje na fito tare da dan tsayawa ina kwaso takardun dana dawo dasu daga school din.
Sam ban kula da suna gurin ba sai dariyan su da naji a lokacin yasa na dan dago kaina su biyu ne a tsaye da gani rakiya tayowa kawar ta wacce na sha ganin ta tana zuwa gidan gurin ta sosai.
Daga inda nake ina iya jiyo hiran su bawai a, asirce suke magana ba yadda zanji suke maganan.
Kai maza ho shi wai farin fatan ne yaha shi a nan ko may wai ?
Hindatu tace kin san yan kauye kamar dabbobi suke basu san makwancin da ya dace da su ba ko ina sai su dauka matsayin su yakai su shiga.
Wani za ai wa bRkado kila haka taga anayi a gidan ubanta zama da cin amana don rainin wayo ni da girki ki sa min miji gaba ki fice dashi wai ita karamar yar iska.
Wallahi jira nake ta kara gigin fita dashi taga yadda zan mata a gidan nan sai ta raina kan ta yar jakar uba kawai.
Ni duk iskancin da rawan kan da yake a kanta kar nake kallon su bawai na kyale bane a banza shiri nake kafin na fara aiwatar da nufi na yar abu kazan uba.
Zuciya ne yazo min na karasa fitowa daga cikin motan kawar nata tace ashe ba matar so bace tunda ya barta tana shiga wanan motar da ya sha jiki.
A zuciye na karasa fitowa na aje takarduna a cikin mota tare da gyara saitin hijjab dina na ce hindu kike ne ko wa ?
Idan baki aiwatar da nufinki a kaina ba ashe ba Adamu kwangila ya haife ki ba.
Yar kauye nake kuma Allah yai min zaben makwanci daidai dani don ban raina da kyautan Allah ba akaina.
Ni kika zaga lalai yau akwai balai gidan nan nace bala,i a kan ki keda kika kirashi mahaukayiciyar banza da wofi ke wakika fi kishi da hauka.
Shiru shiru ba tsoro bane wallahi ke kuma tsohuwar kilakiya na fahinci aure ta gagare ki sai yawon bin gidaje kina kashe aure mota kika ce ba, a canza min ba ko may ?
Nace na baki sati biyu ki dawo zaki sha mamaki a gidan nan don kin sara a kan gaba ko .
Nace dibeku don Allah idan ni farine ya rude shi a kaina ke may ya rudeshi a kanki shafafen baya ko shafafen gaba mace haka kamar an daurawa kara zani dake.
In ba halin aure ba ko auren ma na cinne ai ko a kafa daddy ba zai jaki ba nai tsuki na kwashe su na watsar na juya zan shige naji motsinta tanufoni a zuciye .
Shiryawa nayi da nufin tana zuwa tasha mamaki yau amma sai naji muryan Anty tana cewa daga nesa ke Rama shigo ciki hakana ya isa.
Tace ke kuma ki kama girman ki ga yarinyar nan wanan ai zubar da kaine shifa kishin nan kowa na dashi amma ya danne nasa don a zauna lafiya.
Tace ko zaki shigar matane don dama kece kika tura wa mutane alkakai ai anty tace banda lokacin hauka ni yanzu ma kirana akayi nazo.
Muna shiga falo gurin jinior dake kwance na nufa ina kokarin dago shi daga kwance ina cewa yaya jikin jinior da sauki dai ko ?
Anty tace yaji sauki ai mun koma dashi yau ma an mai allura na fever din.
Tace waiko hindatu na da hankali maigadi ne ma fa ya kira gajiye yake fada mata ta fada min babu lafiya a waje na fito.
Nan nake fadawa anty yadda abin ya soma tace kyale ta ai baki yasan abin fadi bai san ansan da za, a mayar mai ba.
Na jima zaune ina lalashi jinior na mike zuwa part dina don nayi sallah sai da nai wanka na fito hira.
Ban dade da zama ba sai ga daddy ya shigo falon fuskan shi babu annuri a cikin sa.
Gurin jinior dake zaune ya nufa ya dan yi hira dashi can ya dago kai yace Saade may ya faru tsakanin Hindatu da Rahama a gidan nan har ta zagi ubanta ?
Shiru falon yayi ba wanda yai magana yace ba tambaya nakeyi ba kun kyale ni nan ba babu amsa kowa shiru yayi.
Yace gaskiya bazan dauki kishin da zagin iyayye ba a gidan nan har yaushe Rahama ta shigo da zata dinga zagin iyayyen na gaba da ita haka cikin rashin sanin darajan su.
Tacs dakata besty itama Rama ai matarka ce ita da ta fara zagin iyayyen ta nata sunfi nata daraja ne ko may ?
Idan da ta rike girman ta ai da bai kai ga haka ba mata ke nan kullun bata son a zauna lafiya ita ?
To itama Rama ta gaji da cin mutuncin da ake mata yau ta tsaya ta rama .
Yaya zata zagi iyayyenta don ta rama ace kuma ya zama laifi wanan ai zalunci ne don uba baifi uba ba ai.
Idan bata son a zage ta ta daina zagin iyayyen wasu ba kowa ne za, a zaga ya kyale ba haka har da tanayi kawar ta nayi don tana matar so a gidan sai a kyale ta ta taka kowa yadda take so komay ?
Yace koma may tai mata bata jira na dawo ta fada min shine zata tsaya harda zagi irin haka bazan dauki wanan shashancin ba gaskiya.
Tace aiko da sake wallahi don ko ba zan hanata daukan mataki akan hai,inci ba.
Naga alaman da sanin ki ake komai haka don gashi kin nuna min zahiri nagani na kuma gane komai ?
Nan suka fara mayar wa juna da magana a tsakanin su a raina nace lalai yau na tabbatar kuwa hindu yar so ne kamar yadda ake fadi a gidan daddy.
Nace anty don Allah kiyi hakkuri ba zan so ganin wanan ranan ba a tsakanin ku haka.
Don haka anty indai don nice ya kwana gidan sauki dama ban sauke ba balle a tayani azawa gara na bargidan nan ku zauna lafiya yafi tunda don ni ake wanan fitinan haka ?
Na dire karshen magana na ina mikewa tare da kama hanyan fita part din raina a bace.
Ina fadin ai talaucin da take min gori ko yaushe a kan shi ba fin mu tayi ga Allah ba ya bata.
Daga haka na fice na barsu ina fita anty tace nasan za, a rina don mai hakkuri bai iya fada ba.
Yanzu kai daga kaji zancen ta shine zaka zo ka hau mutane da masifa in ace kullun abinda ake ana fada maka ne ai ba, a zaman lafiya gidan nan.
Tsuki yaja ya fice daga part din ina shiga part dina kuka yazo min yanzu shi ke nan don ya kasance anmin dole sai kuma aita musguna min ban ramawa ko may ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, DON HAKA CIN AMANA NE YAR UWA , , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA BARKI GA ALLAH YABI MIN HAKKINA AKAN KI NA CIN AMANAN , ,
46
Tun wanan ranan na kama kaina ban shiga tsabgan kowa agidan tun safe nake ficewa sai shidda zan dawo gida.
Na dan shiga gurin anty na gaida ita daga haka kuma sai gobe ko zaman hira banayi idan tai magana sai nace karatun exam na keyi shiyasa.
Ido ra samin wani lokaci gajiye kan shigo mu dan yi hira ta dan min magana mai kama da nasiha ta wuce.
Gaiwan da nakeyi wa matan gidan yanzu na daina sai dai su wuce in wuce idan mun hadu su bini da harara.
Yaran ne kan shigo duk dare mu dan bata lokaci dasu wataran inda sunyi barci tare zamu kwana dasu.
Yau Na dawo da yamma lis duk da agajiye nake kuma yamma yayi sosai ban wuce ba na shiga na gaida anty tace min ya karatu nace Alhamdullahi.
Daga haka na wuce ciki nai wanka nafito da alwala na tayar da sallah na dade zaune a gurin bayan na gama adduoina na shiga tunanen duniya.
Sallaman anty ne naji ta shigo har bedroom dina ina ganin ta namike zaune ina cewa anty ina wuni.
Bata amsa min ba ta samu guri ta zauna tare da kura min ido na tsawon wani lokaci gyara zama na nayi da kyau don nasan tunda naganta magana ne yakawota guna.
Tsawon dan lokaci mu haka da ita ccan tace dani Rama haka zamuyi dake yanzu ?
Na dago kai a hankali na dan kalleta sai kuma na dukar da kaina a kasa tace ban taba zaton tun yanzu zaki iya watsa min kasa a ido ba haka ?
Nace anty ni kuma tace ke mana Rama dan maganan da akayi ya wuce kin rike shi a ranki kina ta fushi da kowa a gidan.
Kina ganin matakin da kika dauke shine mafita a gare ki ko may ?
Nace anty gara na bar masu mijin su kowa ya huta tunda nice matsalar su agidan.
Dana zauna ina jawo maki matsala keda mijin ki akan gaskiyana fa ya rufe ido a gaban mu yai maki rashin mutunci.
Bazan tsaya don ina yar kauye diyar tallkawa ba adinga ci min mutunci da mahaifana da basuji basu gani ba.
Shine matsalan ki ke aiko in kishiya ne har fiya da haka zakiji a gareta tunda burin kishiya shine kullun taga bacin ran kishiyar ta a fili kinga sunyi nasara akan mu ke nan.
Amma kina haka basu ba koshi may gidan dariya zai min yace aigashi abindana shuka tun ba aje ko ina ba ga abinda aka girba akai.
Tausayi ta bani tunda ita har yanzu gani take a ranta itace ta sa daddy ya aure ni bawai yana so bane yayi.
Namiji fa mai mata fiye da daya dama haka yake idan halinsu ya motsa basu tsaya bincike sai dai su yanke hukuncin da suke gani shine daidai a garesu.
Haka halin maza yake kin sani ra, ayin kan su suke bi bawai abinda sharia ya kidanya ba.
Nace anty ni kan ba zan tsaya kullun ana zagiki da iyayyena ba kuma ace mutum wai kada ya rana dan ta fada min na fada mata shine kuma zai zama laifi anty ?
Ki daina wanan maganan Rama abinda ta fada mashine yai amfani dashi amma nasan ai zaizo ya gane gaskiya wata rana da kan shi.
Nace ai ba sai ankai wata rana ba mijin su daine na bar masu abinsu ba shi ke nan ba dama don kine na daure nake wanan rayuwa yanzu ko anty don Allah a hakkura dai hakana.
Ke yanzu matakin da ki ka ga yafi maki ke nan Rama watau ban isa ba dake ke nan yadda nake tunane a baya ?
Nace anty kin isa ke ma kin sani da ba don ke ba wa ya isa yai min haka a zauna lafiya sanin kankine duk abinda nake akan ki nake yin shi a duniya.
Tace to naji na kuma gode don nasan kina min bawai ban sani bane Rama ?
Yanzu fada min matakin da kika son a dauka nan gaba nace wani mataki zan dauka anty banda na bar maku mijin ku na koma gaban iyayyena ko kasa suke ci su kwaba su bani yafi min darajan akan wanan irin balain haka.
Fitinan safe daban na rana daban kullun cikin tunane da zulmi gari ke wayewa mutum don bai san da wacce za, a tare shi ba duk kuma baka tsira ba kaine mai laifi dai.
Tace ashe Rama da sauran ki ina cewa kin kai ashe baki kai ba dama hakan ai shine kishin .
Idan zaki jawo mijin ki ku zauna lafiya yafi maki inkuma kince ba zaki tausasa zuciyar ki ba akan kishiya kinaji kina gani ki koma yar kallo da reno a gida.
Don hakan da kikeyi ba zai kaki ga komai ba akarshe sai tarin nadama da dana sani nan gaba.
Nace idan na zauna ganin kwam ke nan a cikin ku anty exam nake jira na gama next week na kama gaba na don ban zama a na wullakantani har abin kema ya shafe ki.
Lalai ma Rama wai kina hauka ne ko may da kike fadin wai ke zaki tafi zaki tafi ina wai ?
Har kina ikirarin kin bar muna mijin mu kishiyace zakiyi fushin zuciya kice kin barwa miji Rama aiko in haka zakiyi wataran za, ayi bake wallahi.
Nace ni yafi min anty nagaji wallahi bazan iya ba ai tawa mutum cin mutunci har iyayyen shi in kuma kai magana ka rama ace ka taba matan gida a sauke ma balai.
Ni dama nasan Allah ne ya jefoni cikin ku ba wai son raina bane don bazan iya wanan bakin fitinan ba haka.
Gara na bar gidan kowa ma ya huta in dai don nice ban ko sauke ba balle ince a tayani azawa akai.
Wai ko Rama kin ko san aure kuwa auren ma kuma na mai mata da zaka zauna da kishiya ?
Nace ai in ban sani ba yanzu na sani tunda zahiri nan na gani akan gaskiya na akaci maki mutunci.
Badai ke akaciwa bani akaciwa ko kuma ni din dakike jiwa na sake kece bazaki sake ba ke nan.
Ashe hasashen da nake a kan ki na zaki iya ashe abin ba haka yake ba ke nan tun yanzu gashi kina son watsa wa mutane kasa a idanu.
Na dauka ko a bayana zaki rike min alkawari ashe ni ke haukana agurinki abin ba haka yake ba.
Kina ganin idan kinyi haka kin kyautawa iyayyen ki damu ke nan Rama.
Anyi magana kice ke zaki wuce zaki wuce zuwa ina don dan wanan magana kawai.
Nace anty da na zauna ana min sheri ace kuma ban magana don ana takama da an fini asali ko wani abu gara na bar gurin tun ana sheda juna da ido biyu.
Na dukar da kaina wasu irin hawaye suka fara zubo min a lokaci guda ina fadin ni ban iyawa anty gaskiya mijin su daine yasa suke min haka ko to na bar masu abinsu azauna lafiya.
Kuri tai min da ido tana kallon yadda nake kuka cikin tausaya min don tasan cewa itace tasani cikin wanan rayuwan haka da nake ciki.
Ga dukkan alamu magana na ya shigeta sosai don tasan nikeda gaskiya ga maganan babu dai yadda zatayi ne kawai akai.
Sai dai duk irin yadda nake ji bazata bari na tafi ko ina ba don tasan bacin raine yake damuwa na haka irin namaza da suke kunsawa mace.
Don ko ita da farko ta dau abinda zafi amma yadda taga na dauka sai take gani idan batayi saurin kawo iyakar abin ba zai iya jawo matsala fa kowa ma.
Naji tace yanzu dai kin nuna min ke nan ni bban isa dake ba Rama kin daina jin maganata ko ?
Cikin kuka nadago nace anty ba hakana bane don Allah kiyi hakkuri ki barni na tafi gidan mu ki raba wanan auren da babu komai a cikin shi sai bakin rigima da rashin kwanciyar hankali komai nayi a gidan nan ba fita zanyi ba .
Don ni nazo na samy su da mijin su kinga kuwa idan nace na nace sai na zauna nan gaba abinda za, ayi min sai yafi wanan ma .
Don Allah anty ki barni in tafi ki huta su huta ba sai ina nan ba za ai fitinan dani.
Kiroka min a sallamay ni na bar maku gidan ku ku zauna lafiya dakowa shine mafita.
Na karshe maganan ina mai fidda sautin kuka cikin ban tausayi ita dai ido ta kura min kawai tama rasa may zatace dani a lokacin.
Idan anki sakin fa ?
Muryan daddy ne da bamu san yana tsaye daga kofa ba yake magana tare da karasa shigowa dakin kai tsaye hanayen shi zube cikin aljihun shi.
Dagani har ita muka daga kai muna kallon shi don ba wanda ya tsanmanci zuwan shi a wanan lokacin.
Nace aiko ba saki zan tafi don shine sauki a gareni dana zauna inda matsayina baikai ba ana zagina da iyayyena idan nai magana ace naiwa matan gida rashin mutunci haka.
Ban saba sakin mace ba ni a rayuwana don haka in ma shine gurin ki a ranki kiyi gagawan kawar da wanan shawaran don baki da nasara anan.
Laifi kikayi kuma nai magana kewaye da baza, a maki magana ba kan abinda bai dace ba kice ke baza, a gyara maki ba ?
Nace ai wanan ba adalci bane daga jin maganan mutum daya sai azo a samu sauran da fada da cin mutunci ni gaskiya wallahi bazan iya ba.
Don ana takama anfini anfi iyayyena sai na zauna a na takani yadda akeso har da baren gida kuma ace kada na rama.
Wanan yanzu matsalarki ce wanan nidai ba zan yarda ana min rashin tarbiya ba agida na kyale ko ma waye ?
Nace ni duk wanda ya sanni bai cewa banda tarbiya a cuce ni kuma nai magana karo na farko ace banda tarbiya ai Allah na gani yasan mai gaskiya.
Yace hmmm haka kuke

Please Login or Register in order to submit comment