Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baza ta iya fada min bane don haka gara kawai dana daure na tafi ai.
Yace ai yanzu gaki kina mukurkusa ke kadsi a daki, nace ai nz huta har barci saida nayi da muka iso ban wani wahala sosai ba ai.
Nace ga mama nan munzo da ita ta dan huta kwana biyu tare da mu ta dabe muna kewa.
Yace aiko kin kyauta wallahi dama tana cikin raina sosai don bai kamata mu kyale ta ba haka a can sai taga don yarta bata raye ne muka fita batun ta.
Don Allah nasan ba sai na fadi ba ma abata kula yadda ya dace kada taga don yarta bata nan taga banbanci koda yake kema ai uwar ki ce ita din.
Nace daddy indon wanan ne kada kaji komai a ran ka don mama banda abinda zan saka masu dashi a duniya nan don sune sillan zamana haka a rayuwana.
Murmushi yayi ya juya ya fice daga dakin na kwalawa Aisha kira tazo ta bani wani abu don tashi aikine gare ni wasan dadi.

********* ********* *********
Washegari da kaina na shiga kitchen ina shiryawa su hajiya da mama abinci don nasan idan na barwa yaran bai wuce su yi tea da irish da kwai kawai su tashi.
Miya nake hadawa don har na gama dafa abinci hankalina yana gun abinda nakeyi don haka banji shigowan shi ba sai muryan shi da naji daga bayana yana fadin.
Wai may kike yi haka a kitchen da kan ki na dan juyo gare shi cikin dan murmushi ina fadin barka da fitowa ina kwana daddy.
Ya karaso yana fadin yaya gajiyan tafiya koda yake naga alaman baki gaji ai tunda ga ki a kitchen da safen nan.
Nace wai abinci nake kokarin hadawa su hajiya mai dan nauyi don nasan yaran nan idan na barsu shirmay zasu yi min kawai.
Ban san cewa ya karaso har inda nake tsaye ba sai jin shi nayi ya rungumoni ta bayana tare da sauke hannayen shi a saman cikina yana dan tabawa a hankali.
Ajiyan zuciya na sauke a hankali nace daddy baka gudun wani ya shigo ya samay mu a hakan nan yanzu.
Yace and so what, ?
Idan wani ya shigo din wata na rike ba matana ba, ban rike ki ne kike a haka murmushi na karayi na ce kai daddy dai.
Hannun shi ya kara saukewa a saman wuyana ban san lokacin da na sauke wani irin ajiyan zuciya ba a hankali.
Nace daddy kada fa wata daga cikin matan ka su shigo nan kasan bani ce dakai ba yau gaahi kuma kazo kana rike ni haka ?
Yace matsalan ku ke nan wallahi kishi to na sake ki matsoraciya kawai na dan sake murmushi nace yafi min sauki ai.
Ya dan ja baya daga inda nake ina rage gudun gas din da nake amfani dashi din sai jaji yana cewa yaya zamuyi ne da zancen hajiya don bamu samu ganin wani babban likita ba.
Don ganin su yayi muna wuya andai bata magani shi take amfani dashi har ta danji dama sai kuma gashi daren jiya kuma abin ya dawo mata.
Nace yaya take jine wai ?
Yace tace wani abu ke tsaya mata a ciki kamar da yana mata ciwo wani lokaci kuma har yakan ma hana ta tafiya.
Murmushi nayi nace at this age da take take jin wanan gaskiya ina fa sai an mata aikin shi zaifi don ko tasha magani ya bari watarana zai iya dawo mata da karfi yai barazana a gare ta.
Yace wai Rahama may zai hana ki dubata a nan gida ki gani ko zaki fahinci abinda kyau ?
Nace da sauri wa ni daddy?
Kana ganin ma hajiya zata yarda da aikina har ta bari na dubata gara kawai kuje asibitin a dubata a can nima zaifi min sauki wallahi.
May zai hana ta bari a dubata yadda take fama da jiki haka kawai ki gama zanzo mu shiga gunta sai ki dan fara dubata don Allah.
Daddy banki ba amma dubawa a gida kamar sabawa doka ne kaga ba wani abin gwaji da zai nuna ga ainihin abinda ke damun ta din.
Yace nace ki dai duba min ita bashi ke nan ba ban son mu tsaya muna gardama haka don Allah nace shike nan bari na gama zuba abinci nazo.
Daga wurina wurin hajiyan nashi ya koma yake sanar da ita cewa zan shigo na dubats yanzu idan na gama aiki don haka ta shirya.
Da sauri ta dago daga kwance tace wa ni nice Rahama zata zo duba har wacce Rahama din yau she ta zama wata likita can da tai ilimin gane ciwo na.
Raliya dake hada mata tea tace ai shine gara dai aje aga babban likita zai fi yadda take ji din nan.
Fada mashi dai ke yar albarka amma haka kawai ka dauko min wata matar ka can kace wai ta dubani yo Allah na tuba kai da ka dauke ta wata tsiya sai kaje ta dubaka yadda ta saba amma bani hauwa ba kan.
Sai Raliya ta sake fadin ga dai likitoci manya da suka san aiki ko bayani kai masu sai sun fada ma matsalarka.
Ke rufa min bakin ki banson raini noses kawai ke kin san abinda ta sani ne ko aikin ki ne hakan kada na sake jin bakin ki a cikin maganan nan.
Tace Allah ya baka hakkuri daga fadar gaskiya sai a lake min kuma, yace rike gaskiyar taki na fada maki.
Ke yi shiru gaskiya ne bai son a fadi ranan littani ki shirya ki kaini asibitin kin ji tunda shi ya nuna ya gaji da zuwa.
Yace haba hajiya akan may za gaji da alamarin ki tace baga shiba kuwa kazo min da wani zance watau ni gani gidahuma ko na zauna matar ka tai min shirmay ta kashe ni.
Yace haba hajiya aikin nan fa aikin ta ne kin sani sai dai idan wani manufa ne zai hanaki bari ta duba ki din don dai nasan Rahama har case din da yafi naki ta na dubawa don yanzu haka ma har naji ta fadi maysalan ki ko da komai.
Taceina ruwan gobe da nisa ta zama yar magori ke nan ashe tun ba a ga mai ciwo ba har an san matsalan shi.
Bai yi magana ba ya mike ya bar dskin tabishi da harara tace ka zauna yarinya karama tana juya ka yadda taso har ta kawo gare ni don raini.
Sai lokacin Farida tai magana tace wai ma hajiya har wata Rahama ne can zata tsaya dubaki wai yaushe har tai wani karatun kwarai banda galihun da yai mata.
Raliya tace ashe kema kin gane ni fa nasan komai kallon su kar nake kawai ana muna barazana wai ga likita a gida.
Ko aikin ma ai sai anga daman fita ake fita yin shi likitan kwarai ne zai ta zama a gida ba shiga gun aiki to ire iren su sunyi yawa a wirin yan galihu.
Amira ce ta shigo da sallama tana cewa a, a hajiya ashe dai sauki yazo ga shayi naga zaki tausa da bread.
To ga abin karyawa inji mummy mu tace na kawo maki saura ki lashe kwanon tace cikin tabe baki har wani abincin zan lashe kwanon akai abincin naku da maggi da mai ke yawa cikin sa.
Sai su Farida da Raliya suka kwashe da dariya kyeta hajiyan tace may kuka dafa ne wai nasa bai wuce shayi da kwai dai shine cimar naku ai.
Amira tace wa ai mummy mu tafi da nan bude kigani mana nasan sai kin ci ko may ye ma tace ja,ira nice zan bude bude dai naga shirmay naku.
Ta fara bude kulan tueon semo sai kular shinkafa da miya da kaya ganishing a cikin sa sai kular miyan yauki da wani na cow leg sai kulan miyan kaji naman yanka manya manya.
Tace ja,ira ashe kin san may kukayi kike min shakiyanci dama kamar kun san shayin nan ya ishe ni wallahi tace mummy mu cefa tai maki shi da kanta keda hajiyan maman mu.
Tace shine tai barnan nama haka daga inda Raliya take zaune tace ai kin san nama a gidan nan ba matsala bane da yakare kawo masu wani za, ayi .
Sai hajiyan tace dole ma tunda baida aiki sai na zuba masu dadi suna ci Amira tace cikin tsiwa kowa ma ai yana zuba mai tunda ba fridge din gidan nan da babu nama irin namu a cikin sa don tare ake sayowa kowa lokaci daya tana fadin haka ta mike tabar su tace cikin daga hannu bye bye aci lafiya ko.
Ni dai banga yazo ba ni kuma banyi magana ba sai dana gama komai na shirya na shiga gaida ita ban dade ba na fito don na samu tana cin nama Farida kuma yadda naga ta daure fuska ban ko bi ta kan ta ba ma gaisawa mukayi sama sama na fito abina.

********* ********* *********
Ranan monday ban samu fita ba ina gida Raliya ta kwashe ta zuwa asibitin bayan daddy ya basu kudin komai yadda zai ishe su don ya tafi lagos aiki.
Sun tafi sun ga likita bayan tayi bayanin komai ne sai likitan ke cewa zan tura ku wurin doctor Rahama Abdullahi ta duba ku don wanan fannin ta ne kuma itace zata tsaya tai maku yadda ya dace da kyau.
Ya kira massinger shi ya kai min file din su office dina yace ku bishi zuwa office din ta suna zuwa ake cewa dasu yau bata fito ba wai bata jin dadi suka koma gun mutumin da sukafito.
Yace da zakuyi hakkuri har tazo da zaifi akwai masu iya duba ku ba wai babu ba amma ita tana da experices kan wanan matsala na mahaifa so sai don a germany tai karatun shi.
Kallon juna sukayi da yai maganan sai kuma sukaji yana cewa ina ga matsalan cikine don tana da tsohon ciki idan ba zaku gaji ba zaku iya dawowa zuwa gobe nasan zatafito don tana da aiki da zatayi gobe.
Sai dai ku fito da wuri don ku ganta kafin ta shiga aiki gani ta yai maku wuya.
Likita yanzu kana nufin ba wani da zamu gani bayan ita din tunda bata nan ya da bugi table yace akwaisu da yawa ma sosai kuwa.
Bari na tura ku wurin wata ita naga tashigo dazun sai dai zaifi kyau kuga ita wanan likita din dana fada maku ne.
Ya tura su wurin doctor Lami tana tare da wata take cewa at dis age wannan case a gare ta da dai suga doctor Rahama Abdullahi naga zaifi kyau.
Kara kallon juna sukayi sai ita doctor din da sukazo gunta tace mama matsalan ki fa aiki za ai maki don samun lafiyan ki.
Aiko ta mike tashiga fada ta cewa Raliya su tafi don tana ganin kamsr basu san aikin su ba ma a nan.
Tun a hanya daddy ya kira Raliya yana tambayan ta sun tafi asibitin ne take cewa eh gamu hanya ma dawowa gida yake cewa da ita kun ga likitan ko sai tai shiru can kuma tace dashi eh mun gan shi .
To may sukace daku ne akan ciwon nata tace gadai hajiya din sai ta mikawa Hajiyan nashi wayan ta kara a kunnen ta.
Ya gaisa da ita tare da tambayanta yaya jikin jata take cewa dashi da sauki yace may likita yace daku ?
Tace wa yan nan mashiririta may suka sani asibiti kamar wanan wai ace muga Rahama itake da masaniyan irin matsala na fiye da kowa.
Yace ban gane ba hajiya tace ba zaka ko gane ba kaidai don wata yar banzan yarinya ma cewa tayi wai aiki zasuyi min.
Nan yace dama ko Rahama ta fada min haka na tace sai sunyi maki aiki don samun lafiyan ki.
Tace bakaji ba dama ai nasan bakin su daya hadin baki sukayi da ita wai ace dole sai na gan ta don ta nuna min ita din takai ta isa.
Yace hajiya yanzun dai zan dawo yau sai a san abin yi tunda abin na matsa maki haka zan zo muje aji ko may ye hakana.
Allah ya dawo dakai lafiya tace dashi sukai sallama ya kashe wayan shi yana mamakin wanan wani irin kiyayyane haka har da lafiyan mutum zai hada ?
May ya hada Rahama da hajiyane haka wai wanan abin yai yawa Raliya yace a ranshi don ba Raliyan ba kowa yanzu bata gani in ba Rahama din ba.
Sai dai kuma ko ita Raliyan ai bata tsira ba tunda tace tana barin ta da yunwa ta fita ko kuma a bata abinci ba dadi.
Yace kai hajiya ho Allah dai ta bar min ke naita ganin ki ko yaushe muna kwasan wanan draman naki.
Ya dawo da yamma rana daya suka dawo da zulfa sai dai ta riga shi isowa garin ita don har ta manta tayi tafiya ko.
Muna zaune da ita ya shigo falon mu muka shiga gaida shi yace da zulfa din ke kinga daman dawowa ai na dauka can zaki zauna kuma.
Tace kai kaji yaya in zauna gadin gida ko may ka kwaso mata ka gaba daya da yara ni zaman may zanyi can yace wa sanan maki nace ai dole daddy yai fushi anty daga zuwa kin samu wuri kin zauna in ya bude ido ba uwar gida ran gida a gidan.
Tace kaji Rahama dai da wani zance can muna dai uwargida ko ga amaren gida wake ta wata uwargida can kuma.
Mu dai raka ko a hakan mu samu dai a laba mu muci arzikin ku kawai tace su mama na gaida ku yace kin barsu lafiya dai ko tace eh.
Ashe hajiya suna nan har yanzu jikin ya kiya kuma sai jiya dana shiga ne Alhaji ke cewa dani ta samu wuri tai zaman ta nan nasan ba su dawo ba ashe.
Yace kai Alhaji koni ai ya kirani yana fada wai nazo na rike mai mata naki turota ta dawo an barshi daga shi sai yara a gida.
Nace ba a ga likitan bane har yanzu wai Alhaji ai yana da gaskiyan shi tunda ya tsufa dole yana son mai taimaka mashi kusa dashi ai.
Ya dan ja tsuki yace wani likita ba sun tafi dazun ba ance su ganki wanan algunguman Raliya nasan ita ce ke zugata ai.
Zulfa tace ashe suna ta ke nan kaima ka fara sani halin makirci na ta ke nan dai.
Ta maka mata harara yace dani ke taso ki hada min ruwa na watsa ko zanji dadi don nice da girki a ranan da ya dawo.
Sai da ya dan jima da fita na mike nabi bayan shi don hada mai ruwan wankan ca ya rike ni ban fito ba sai da nazo cewa yara su rufe kofa na koma.
Da safe na tafi wurin aiki ina office zaune ina tsaka ga aiki file din hajiya yazo table dina sam ban kawo cewa ita bace don ban san zananen sunan ta ba ma ni.
Nace su shigo sai gasu da Farida don tare suka zo dashi amma shi ya tsaya waya lokacin yace su shigo gashi tafe don dare jiya abin ya matsa mata sosai.
Kaina a duke yake lokacin ina rubutu sai da naji tace to babban likita gamu mun shigo sai a duba mu na dago da sauri na kalle su tare da mikewa tsaye.
Nace hajiya kune ashe dama ba a ga likitan bane ko may da aka turo file din ki nan wurina ban san kece mai sunan ba dana ce ki bari na dubaki ma a gida ai.
Sai ga daddy ya shigo office din yace ok sun shigo may aka ciki sai nai shiru can na dago kai nace hajiya yaya kike jin jikin naki ne ?
Yace ki fada mata komai don kinga na shi na karshe cikin mutum ukun da aka tura mu mu gani.
Na jawo takarda ta na fara rubutu akai sai farida ne ke min bayani cikin rashin fahinta amma ni na fahinci komai.
Na shiga jefo mata tambaya tana bani amsan abinda nake son ji na rubuta komai na dago na cire glass din dake idona nace gaskiya daddu sai mun cire mata mahaifa don idan ba haka sai na dan sasauta murya na kasa nace zai haifar mata da zuban jini da zai iya sanadin ta.
Tace a hasale tare da min dakuwa Rahama karbi nan tun baki isa saka dan kanfaiba rabona da jinin al,ada kinji.
Abin ya bani dariya amma sai na daure nace hajiya shi wanan din ba jinin al, ada bane jini ne na ciwo zai haifar maki ya koma cancer na mahaifa don haka don Allah hajiya ki daure ai maki aikin na tun kan matsala ta shigo.
Sai jikin ta yai sanyi tace na shiga uku ni hauwa,u yanzu ba wani maganin da zan sha ba sai an taba ni ba yar nan.
Nace hajiya haka shine sauki ba wai sai yaran mata kanana ke samun wanan matsakan ba harda tsofin da wanan matsalan ya sama ta faruwa dasu haka.
Nace hajiya kada ki ji komai wa yanda za suyi maki aikin kwararun likitoci ne don sun san aikin su cikin yan kwanakin da baikai sati ba zaki mike insha Allahu.
Jikin ta yai sanyi sosai ta juya gun shi tace yanzu yaya za, ayi yace hajiya aikinji abinda ta fada kiyi hakkuri a rabaki da wanan abin don Allah.
Nace hajiya taso ki hau gadon can mu gani ta mike da kyat jiki ba karfi ta hau gadon na sake labule na dauko abin awo ina dan duba maran ta daga kasa kadsn har nakai inda ciwon yake mata nace na ne yake tokare maki ko tace na ne kedai.
Nace idan ya gama zaiyi ruwa shine zai jawo maki wanan zuba jinin nan gaba kadan tun da har ya fara yi maki hakan.
Na kamata ta sauko muka dawo inda suke nace dashi daddy aiki zamuyu mata insha Allahu abin zaizo da sauki don haka zan bari har a aje magana sai a saka ranan da za ai mata aikin ko ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , ,
98
Ba don hajiya taso ba aka tsayar da ranan da za ai mata aiki don gaskiya ya fara son sako mata jini ya koma servicer cancer mata.
Take hankali ya tashi don har ta koma Kano sai gata an kwaso ta ragai ragai an dawo da ita ba dadi ba bata lokaci nai setting din yi mata aiki a take.
Da safe zamu shiga da ita don haka da daren nan muka bata gado a asibitin mu inda za ai aikin.
Fatima da Aisha sun zo tare da ita don Farida dama tana nan wurin Raliya ta tsaya bata koma ba tana taya ta kishi.
A taya kishi mana don ko ga maciji batayi da mu ko wani nawa sai kule kule da makircin da suke yi ko yaushe a gidan.
Don ni har ya kai nai mata kashedi a kan dukan min diya da takeyi da zaran yaro ya fita yanzu zai dawo da kuka yace gwago Farida ce kamar yadda muka koya masu kiran ta.
Ranan ta daki Abdul har bakin shi ya fashe ga shedan mari da taiwa yaron yai kukan wahala har yai barci don wahala.
Koda na dawo na samay shi a falo yana barci jikin shi yayi zafi nake tambayan may ya samay shi ne ?
Sai Amira tai shiru na sake tambayan su ina a tsaye nace ba tambayan ku nake yi bane kun kyale ni haka ?
Sai Aisha ce tace dani wallahi gwagon shi ce ta dake shi har da mari sai da ya fadi bakin shi kuma ya fashe takuma hana yin shi kuka.
Take naji raina ya baci na juya zuwa part din nasu tana zaune ta tsefewa yar wurin Raliya kai na shiga da sallama na.
Suka amsa min ciki ciki na ce cikin rashin damuwa yau kuma Farida may ya hada ki da dan ki haka kikai mai wanan irin dokan haka ?
Tace a tsiwace ko kinzo ki rama mashi ne don naga kamar kinzo a fusace ko banda hurumin duka dan kine kike nufi don suna diyan gwal ko ?
Nace wani irin magana kike min haka dukan ne dai irin haka bai min dadi ba kawai tace to na dake shi ba kuma zan fada maki dalili ba sai naji shaka da makura.
Nace to ki sani kiyi na farko kiyi na karshe tunda abin naki da niyya ne kika yi mai wanan irin dukan haka har may Abdul ya sani da zaki dakan min shi haka ?
Tace dama bamu san asalin kolo bane da sai yace muna ai shi daga masar yafito har kewa da zakiyi min iyakan dukan dan dan uwa na.
Nace da ita dan uwa dan uwa fa kikace sai dai ni bana jin lissafin ki daga cikin yan uwan nashi kinga kuwa ban sani ba ke nan ashe ?
Kaji banza waike kina ganin kin zama wata tsiya yanzu ko kada ki manta ni Farida na san yadda kika shigo gidan nan da yan tsumakaran ki kina rabe rabe kafin kiyi wayau ki cin amana ki kwacewa mata miji.
Nace wanan kuma karya ne ki tambaya kiji ni Rahama ban da ragga balle tsunma a tare dani ko da nazo gidan nan don ni ba mai kashin tsiya bace kin kuma gani kin sani.
In ma har cin amana nayi aure na da daddy ai kafin nayi kece kika so yi keda har yau son auren shi kikeyi keda ke zuwa wurin mata tai maki goma na arziki.
Don ki aure shi kika kashe auren ki gaki nan har yau kin ki aure kina zaman jiran tsanmani don hauka duk da kuwa yar uwarki na cikin gidan amma kin rufe ido don kwadayin abin duniya sai shi.
Tace ke akwai wanda yakai ki kwadai ne daga ganin sarkin fawa sai miya yai zaki ina sai faman haihuwa kike ke a dole ki cika gida da shegun yayan ki masu kama da diyan kwara.
Wama yasani ko wanan farin ba surki kikaiwa mutane ba kina labawa da wasu diyan kwara can a gefe.
Nace ban da wani shakka a nan don dani dake ansan wacce ta rike darajan ta har gidan mijin ta diya kuma yanzu na fara haifosu a gidan nan sai nai dozen.
Mara mutunci kawai wacce bata san ciwon kan ta ba sai kwadayi da makirci don son abin duniya da kika sakawa kan ki ke da daddy kuma sai a lahira idan ana aure in kina da rabo ya aure ki can din

Please Login or Register in order to submit comment