Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babbane akwai dakuna uku da katon falo sai haraban gida da sauran abubuwan rayuwa.
Zaune nake da yaran gaba dayan mu a falon mun dawo ke nan daga wurin shan icce cream tare dasu mukaji ana nocking din kofan gidan namu.
Nasir yake amsawa da ana zuwa yayi tsawo ya girma ya zama saurayi yana bude kofan gidan sukai tozali dashi mahaifin nashi ne a gaba.
Yace daddy you are wellcome cikin harshen turanci tare da cewa sauran da hausan shi daya dan sauya dan yawan turanci a can.
Sannun ku da zuwa sai ya dan riko hannun daddy nasu yana fadin daddy we miss you, ya rungumo yaron tare da riko hannun shi yana tambayan shi mummy ku na ciki ko ?
Yaron yace tana nan ciki gata can zaune a falo ma a lokacin ina zaune a kasa namike kafuwa na Abdul ya hau kan kafafuwan nawa yana shan icce cream sai jinior dake zaune saman kujera dana kara jikina gap da kaina yana shan ice cream din shi a roba mai dan fadi duk sun zagaye ni muna hira.
Sai ganin shi nayi yana shigowa rike da hannun Nasir a nashi ga mutane a bayan shi.
Na dago kai naga mutanen da yake tare dasu da sauri na mike ina gyara zamana tare da fadin sannun ku da zuwa baba.
Sai dai daga cikin su babu wanda ya amsa min gaisuwan nawa haka yasa na san anzo dani arai sosai don duk sun dauki zafi sosai dani


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,

89
Duk na daburce na rasa may zanyi don ganin su da nayi a gidan nawa na dauke yaron dake jikina ina masu sannu da zuwa.
Wuri suka samu suka kai zaune take Aisha ta shiga kawo masu abin sha a gaban su suna ta bin mu da kallo.
Nasan ba komai bane sai ganin irin yadda dagani har yaran gaba daya duk mun sauya ma ganin su.
Don munyi fresh mun kara girma da kyau nayi jiki da fari don canjin yanayi dana samu a can din.
Nan na fara gaida su tare da masu sannu da zuwa sai dai basu wani karba min a cikun farin ciki da gani na din.
Sai baba maigari ne ke fadin Rahama a she kun dawo nace eh baba wallahi mun dawo yace yaya karatun ya jama, a can da kuma yaran nace dashi Alhamdullahi.
Yace sai dai kuma yaya na gan ku a nan ba a gidan mijin ki ba kuma don can naga ya kamata ace kun sauka aiko.
Nace eh baba akasi aka samu sai dai kune baku sani ba amma gaskiya a halin yanzu bamu tare da shi don tun ina can muka samu matsala dashi gaskiya baba ba ni da auren daddy a kaina don mun dade da rabuwa dashi akan wasu dalilai.
Magana nai masu ditect ba wani farga ba komai a zuciya na sai sune ma naga sun shiga rudani wanan ya kalin wancan suka fara a tsakanin su.
Sai shi maigari ne yai karfin halin fadin Alhaji Yusuf wai abinda take fadi gaskiya ne ko may don bamu fahinta ba mu ?
Daddy yai dan murmushi tare da girgiza kan shi yace ba gaskiya bane baba asalima ban san inda wanan maganan ya fito mata ba ni.
Na dai san mun dan samu matsala da ita tana can tun wanan lokacin kuma bamu sake haduwa ba da ita har yaran sai yau din nan baba ni ba irin mutanen nan bane masu saurin sakin mace akan da matsala kadan.
Maigari yace dani Rahama ban taba tsanmanin wanan halin daga gare ki ba kada ki kasancce a cikin irin matan nan da abin duniya oan yi saurin badewa idanuwan su.
Nace baba kada kuyi min wanan zaton don bani daga cikin masu wanan irin halaiyan ko kadan.
Haba Rahama koma may ya faru a tsakanin ku ai ya kamata ace mun sani ba wai ki bugun gaban kan ki ba ki tare a wani wurin da bamu da masaniyan shi a rayuwan ki.
Nai murmushi nace baba ku kwantar da hankalin ku kun san wa kuka haifa ai bazan yi wani abin assha wanda zai taba mutuncin ku a duniya ga idon mutane.
Sai lokacin babana yai magana yace na sani Rahama kuma ina shedan ki ga hakan amma ki sani gidan mijin ki yafi maki daraja ga komai.
Nasani baba amma kuyi hakkuri fa wanan hukuncin da har kukaga na dauka a kaina don shi abu mafi sauki ga rayuwa na daya dace inyi.
Baba ni ke zama da daddy yanzun kuma nace bana yi don Allah kada ku tsaurara min matakan da zuciyana baya iya jure daukan shi ga yin hakan danayi.
Baba na roke ku da kuyi hakkuri ku barni na samu natsuwa a rayuwa kan abin da zai fitar dani daga wanan rayuwan da bawan Allah nan yake son jefani a ciki.
Amma Rahama daga ke har shi din kun barmu a cikin duhu kan maganan din mu bamu fahinci may kuke fadi ba gar yanzu bamu san may ye matsalan ba.
Maimakon nai magana sai hawaye suka fara zubo min shar shar sai duk hankalin su ya tashi wanan abokin na mahaifina da suka zo tare ne yai magana.
Yace ni ina ganin da mun bawa wanan yarinyar dan lokaci har ta samu natsuwa sai a san mafita akan zancen don tunda muka ga Rahama har ta bude baki taimuna wanan magana haka yau ya kamata mu bita a sannu.
Sai duk sukayi shiru can baba maigari yace gaskiyane nima tunanen da nake ke nan yanzu a raina don haka kai malam Yusuf kayi hakkuri don Allah harta samu natsuwa.
Da haka aka bar maganan sukai min sallama ko abinci basu tsaya sunci ba acan ma bayan sun fita basu tsaya ba don a ranan zasu koma gida acewan su.
Sun tafi suna cike da mamaki da fargaban abinda ya faru yau din a tsakanin mu don abin ya daure masu kai sosai.
A motane suke magana shi wanan mutumin yace ya kamata abi zancen a hankali kamatayi suji ta bakina tunda har na jajirce masu akan hakan don da alama shi mijin baida gaskiya bayan musaawan da yayi bai kawo wani kwararen hujjaba akan maganan ai.
Nima dai abinda ya daure min kai ke haka iji maigari yace dole akwai wani matsala tunda tun auren su bata taba kawo muna wani kara ba makamancin haka din.
Ni dai tun tafiyan su haka na wuni a hargitse dani don nasha alwashin daukan wa kaina fansa akan abinda daddy ke min din.
Daga baya na ba kaina shawara na fitar da zancen a raina na rugunmi yara na na bar zancen wani daddy can.
Bayan kamar yan kwanaki na gama hutawa na ina batun fara aiki muka samu waya Abban anty ba lafiya sosai.
Ban tsaya ba washe gari na kwashi yaran sai kano muka dira a gidan mama laraba nai muna masauki don bamu je gidan daddy ba.
Wurin mama ne nake samun labarin wai an gyarawa amaryan daddy part din anty da ke kusa da nawa din a nan garin yanzu a ciki take zaune.
Ban damu ba don batun shi ni ya fice min akai ko mun tafi da dare asibiti mun duba jikin tsoho ba lafiya ko kadan yana jin ance mune cikin karfin hali ya bude idanuwan shi yana dan murmushi ya mikawa Nasir hannu yazo inda yake.
Yaje sun gaisa haka yaiwa sauran yaran abin gwanin ban tausayi yace cikin murmushi Rahama naso na zauna dake na taya ki duba yaran nan amma ban tsanmanin hakan ba don ciwon nan da wuya yabarni.
Don Allah kici gaba da kokarin da kikeyi a kan su kece da dadin hakan wata rana kin yi kankanta da daukan wanan nauyin a kanki amma kuma gashi cikin ikon Allah kin rike wanan amanan da aka bar maki da kyau ina maki fatan alheri dake da yaran nan a rayuwan ku nan gaba.
Kuka na fara haka yasa na bar dakin mun dan jima asibitin sai godiya yan uwan su ke tamin ganin yadda yaran suka koma a lokaci guda bakacewa suna da maraicin uwa a tare dasu don na zamay masu uwa ko a garesu yadda ya dace.
Sai dare muka koma gida tun da safe labarin rasuwan Abba ya samay mu ba mu tsaya ba muka garzaya gidan gaba dayan mu.
Damu akai komai aka kai daddy masaukin shi daddy bai san da zuwan mu ba sai da yazo yaga Nasir a waje yai matukar mamaki sosai.
Bayan sun kebe ne yake tambayan yaron da yaushe suka zo yake fada mai ai da aka bugowa mummy waya shine jiya muka taso har yake labarta mai yadda mukayi da tsohon a daren jiya da muka zo ganin shi.
A ran shi yace wanan yarinyar akwaita da bakin wayo sai dai ban san Rahama da riko irin haka ba ai dole ne na sauke girmana nabi yarinyar nan a sannu a zauna lafiya tunda nagane yanzu bani gaban ta .
Sun shiga ciki ina waje zaune da wata sister din anty da muke shiri tun banyi aure ba muna hiran mahaifin su ya shigo ciki gaisuwa.
Damu ya fara cin karo zaune saman farar kujera mun mai gaisuwa shima kamar babu komai a tsakanin mu ya shiga ciki yai ma sauran yan uwa ta, aziya yafito tun wanan lokacin ban san yaya ya karata ba kuma.
Sai dai na nemi yaran ban gansu ba ake ce min sun fita da daddy su ai shiya tafi dasu da zai wuce.
Naso sa damuwa amma na danne don ina tsoron mutane su fahinci abin da ke a tsakanin mu dashi a wurin.
Tsora kada ya rike yaran ya biyo min ta nan yaci galaba na sai dai yadda nake ji a raina koda zai karbe yaran shi ne zan iya hakkuri dasu din in har ya biyo min ta nan.
Mun dawo gidan mama har nai shirin kwanciya bai dawo da yaran ba gida hankalina yana atashe sai mamane ke tambayana wai ko zai dawo dayaran nan kuwa yau.
Nace a sanyaye ban sanu ba mama tace barin kirashi naji ina ya tsaya dasu ga dare yayi tana kiran shi ya dauki wayan.
Tace kana ina da yara ga dare ya soma baka dawo mata dasu ba har yanzu yace da ita suna nan gida tare dani.
Mama tace dawo mata da yaranta hakana su kwanta dare yayi zaiyi magana tace dashi Alhaji karami kada ka soma kace zaka tsoma yara a cikin zancen ku.
Kanemi shiri yadda ta dace a gun matarka yafi wanan hanyan dakake son dauka.
Yai dariya yace mama ba rike su zanyi ba nima ina son ganin su ne tunda hardasu ta hana min ganin yara na.
Tace na fada ma dawo mata dasu yanzu batai magana ba amma nasan abin zai damay ta a rai.
Yace gamu tafe mama aishi Abdul din ma da bai sanni ba sosai tundazun fitina yake min shiko takwarana sau fada yake wai wata ta shiga dakin maman su bazan iya rigimar yaran ba gani tafe dasu mama.
Tace cikin dariya aika dandana kaima kaji abinda take ji yau dasu ku dai maza nakan rasa ina tunanen ku yakan shiga idan kun tashi tsula tsiyan ku.
Tunda mama tace ga shi tafe da yaran na shige ciki abina don bani kaunan ganin shi ma idan na tuna yadda ya rufe ido yazo tsula min tsiya a baya.
Dana bita son miji da yanzu bankai wanan matsayin da Allah yakaini gareshi ba da akaso ai min bakin ciki akan shi.
Ina cikin wanan tunanen ne naji muryan su sun dawo suna nema na nan Nasir ya shigo dakin dauke da kanin shi a kafadan shi yayi barci ko.
Yana shimfideshi sau ga uban a bayan shi dauke da Haidar shima yayi barci a jikin shi sai daya aje shi yace da yaron dake tsaye ya fita.
Yaron na fita nai kamar ban ganshi ba adakin sai wani irin kallo yake bina dashi kamar ranan ya fara gani na, naji yace Rahama wai may kike nufi ne damu haka ?
Da har zaki zo garin nan kiki sauka a dakin ki kizo nan gidan mamana ki sauka ban fahunci har yanzu inda kika dosa ba fa da auren mu.
Najuyo nace dashi abinda kai niyar yi a can kasan da kaje har kake ikirari a akaina nake jiran ka dashi har yanzu.
Yace ni banje don yin wani abuba da ina da niyar yin wani abu aida a lokacin nayi ko tunda ba wanda zai hanayi idan natashi yi.
Nace ko yanzu ai sai ka tashi don shi nake jira a gare ka kasani kuma ba zan zauna da mutumin da bai son cigabana ba har abada.
Yai murmushi tare da cewa nine yau kuma bani kaunan cin gaban ki kike iya fadin haka da bakin ki Rahama ?
Kada fa idon ki ya rufe don kinga kin kaiga bukatan ki yau kice ni zaki watsa ma kasa a idona.
Nai murmushi nace aika dade da goranta min ko kan hakan koka manta ne na tuna maka yau ne ?
Na manta sai kin tuna min kila zan tuna don ni ban iya kawo komai a yanzu.
Malam ka ba kan ka lafiya gidan kane dai bazan koma cikin shi ba nagaji da zama da mutanen dake son ganin baya na akoda yaushe.
Suwaye ke son ganin bayan naki nace wanda suka zugoka daddy kazo idon ka a rufe kana son ci min mutunci don an zuga ka.
Ni ban damu da kowacen su ba duk su uku din amma su duk abinda zasuci min dun duniya ta shine gurin su a kullun.
Gida dai ne na bar maku abinku sai a barni na zauna lafiya please ba kare bin damo kuma.
Yau nine karan kuma, Rahama ko wa ?
Ni ba zan taba muzantaka ba don nasan darajan ka a gare ni kuma ko banza uban diya na kake yanzu don haka kada Allah ya kawo ranan da zan aibanta ka a gaban wani hausace ta kumshi haka nai maka.
Yai shiru yana kallo na amma sai nai kamar ban ma san yana tsaye a wurin ba yaja kafan shi ya fita daga dakin ba tare da yai magana ba ko may yasa oho ?
Acan falo naji muryan shi suna magana da mama ya dan dauki lokaci a wurinta kafin ya tafi

********* ********* *********
Nasan zai iya dawowa washe gari don haka tunda safe na shirya muka bar garin zuwa kauyen mu ni da yaran.
Mama na fadin tun yau zaku tafi nazaci ai sai anyi uku zaku wuce can din nace bari na tafi yau mama don wurin aiki sun fara nema na.
Tace to Rahama duk dai abinda zakiyi ki sa tsoron Allah a gaba ki sani auren ki yafi maki komai mutunci a duniya.
Ni dai ban ga wani abin assha a agareki ba ko wanan karramawan dz kikayi na zuwa gurina ki sauka da yaran duk yawan fadin garin nan yai min dadi sosai wallahi .
Yanzu ni abinda nake so dake shine ki janye wanan fushin da kikeyi ki koma dakin ki ki zauna yafi daraja da kima.
Murmushi nayi kawai nace mama da adaiyi hakkuri don hakan shine sauki a gare mu ni dashi mama yaya zan zauna da mutumin da kullun baida ra, ayin kasa sai wanda aka sashi yaiwa mutum may nai wa daddy wanda zai dinga juyani haka akan matan shi.
Tace ya fada min komai amma din Allah kiyi hakkuri ki koma dakin ki nace mama ko zan koma da daddy ba zan zauna a gidan nan ba idan har inda muke bai mai ba yana iya canza muna wuri amma ba nan din ba kan na gama zama da Hindatu kuma.
Tace umm, umm Rahama hakkuri baibar komai ba a duniya kiyi hakkuri dai a sasanta a tsakanin ku nai dariya na gyara gyalen jikina mukai mata sallama na tafi.
Ana sallah muka shiga gida don bamu fito da wuri ba banzo da niyar komawa ba a ranan dama shiyasa Nasir bai biyo mu ba.
Bayan tafiyan mu daddy yazo gidan da Bashir sai samu yayi mun tafi yai mamaki duk da ranshi ya baci amma sai mama ke fada mai yadda mukayi da ita kafin na tafi.
Bashir ne ya iya magana yace wanan kuma sabon zance ne ita kanta ta sani kamar itace idon gidan nan yanzu kuma tace bazata dawo ciki ba ke nan sun zama masu gida daban daban ke nan.
Gaskiya barin Rahama a main house matsala ne don yanzu haka dan barin da tayi din nan mutum bai zuwa ya sha ruwa a gidan nan.
Shi dai daddy bai iya magana ba don shiru yayi kawai abin shi abin ya daure may kai ya rasa may nake nufi ne dashi.
Sun dauki lokaci da ita suna magana sai fada yake kwasa akan ba zai amince da hakan dana zo dashi ba din.
A can gida ma bayan na huta ne maigari ya shigo muka kebe dashi da Inna ta yake min gaisuwan Abba din da kuma tambayana halin da muke ciki ya kuma roke ni da karna baye masu komai don a san mafita ga zancen.
Ban boye masu ba duk yadda mukayi na fada masu komai har abubuwan da ake min a baya ina shanyewa duk na labarta masu komai.
Yace yanzu shu hakkuri zai kara bani amma za, a dakanci zuwan daddy din aji may ya yanke akan bukata na din.
Matan daddy sun samu labarin dawowa na kasan nan itama hindatu ta shiga nata kalar haukan ba hinduba har da Raliya tayi irin nata take cewa dashi.
Ashe yar gwal ta shigo kasan shiyasa naga ka wani birkicewa mutane dan kwana biyun nan haka yai mata wani kallon shekeke yace wace yar gwal kuma ?
Tace matarka mana Rahama tunda ita gani take tafi kowa a wurin ka yace ashe ke baki sani ba tafi kowa din gani kike kamar ita ke ganin hakan ni nasan tafi kowa din ai shiyasa kikaga na birkice ai din.
Nan ta shiga surfa bala,i inda take shiga ba nan take fita ba yai shiru ya kyale ta yagama shirin sa ya fita baiko tsaya karyawa ba shine suka fita zuwa gidan mama da bashir din.
Kwanana biyu a gida ina shirin wucewa ne daddy ya yazo garin nan suka samu wuri da maigari aka kira mahaifina yazo kan zancen namu.
Duk abindana fadi maigari bai rage mashi komai ba sai ya dukar dakai yace a yi hakkuri amma kowa yasan matsalan mata indan sun fi daya a gida sai hakkuri.
Ita Rahama ne bata ganewa nifa nasan abinda nakeyi ba wai ban sani bane komai da nakeyi ina yi ne don zaman lafiyan ta hakan ma da nake duk gani suke ai bayan ta nake ko yaushe.
Sannan maganan canza gida ba zan sake mata gida ba anan dai zata zauna inda muke illa iyaka dan gyaran da za, ai mata kawai shine .
Yanzu ai tunda tana gari bari a kirata taji da kunnuwan ta sai ayita a kare anan ta koma dakin ta idan kun shirya din tsakanin ku.
Ina saye da dogon hijjab dina na shigo da sallama a zauren na samu wuri na zauna tare da gaida mahaifina da kwana.
Yace Rahama ai ina gida ina jiran zuwan ki sai ga sako kuma maigari ya turo nazo mijin ki yazo mun zauna dashi babanki maigari ya mashi bayanin komai kamar yadda kukai magana dashi.
Sai dai gaskiya akan canza wurin zama yace bai amince da hakan ba yanzu dole inda kike din zaki koma sai dan gyaran da za ai maki.
Nai murmushi nace baba nifa dama don ku ne zan koma gidan daddy amma ba don wani abu ba can don nasan in na koma ma halin ba dainawa za, ayi ba mai laifi daban wanda akewa fada daban.
Rahama yace yana gyara zaman shi ban so kimun wanan kaken ba haka don kina da wani manufa a ranki dani.
Nace ni banda manufar komai a kan ka zama dai ne idan ba za a canza min wuri ba sai a hakkura kawai.
Yace wanan kuma dama shine gurin ki kadai ki yunanen don na rabu dake ko bazan iya rayuwa ba ko wani abu
Nace ni awa da zan hanaka rayuwa dama ai ba tare dani kake ba da kake rayuwan ka don haka ko yanzu kuma da bamu tare ba wanda ya hana wani jin dadin duniya sai ma ni da aka tauye kawai.
Kai haba ya isa haka mana sulhu fa muka zo ba batawa ba bashir yace Rahama don Allah kiyi hakkuri abi wanan maganan a tsanake.
Yanzu dai kinji yace bai aminta da zancen raba gida ba don haka ina son kiyi hakkuri da wanan maganan.
Nace Bashir ita wacce ya raba damu din ai bata fimu ba ban damay shi bane da da nima ya yarda danawa bukatan
Ita da ta damay shi ai ya fifita mata gida ta zauna ita kadai babu tsangwaman yara ko namu gare ta.
Yai dan murmyshin yake don jin abinda nace nace aidole kai min dariya tunda na zama abin dariya gareka yanzu don banda wani sauran moriya a gun ka.
To bazan iya ba ni ma don babu wacce ta fini balle a dai rabu kowq ya huta shi ke nan ba mai matsawa wani kuma a zauna lafiya yara dai ne zaka iya wucewa da abinka idan ka so hakan.
Rahama wai kanki daya kuwa kike wanan magana haka a gaban mu inji mahaifina.
Nace Abba ni wallahi mudin ba hada mu za, ayi ba guri daya ba zan ta ba komawa ba gidan nan na kwanmace na zauna ni kadai har bayan raina.
Subbahallahi may yasa kikai saurin rantsuwa ne wai inji Bashir nace wallahi iyakar gaskiya na na fada maku in har yace ba zai canza min gida ba to sai dai ya hade mu guri daya duk mu hudun a zauna tare ko kuma ya sauwaka min kawai .
Kai ban si ki rantse ba dai adai bi zancen a sannu ko nace ni banda wani magana bayan wanan shike da igiyar aure a kan shi zabi ya rage nashi yanzu.
Duk shiru sukayi yadda na zare ban jin kunya kamar ba Rahaman da suka sani ba a baya can shiru shiru dani yanzu girma yazo min na kuma kara wayewa idona ya bude.
Shiko daddy haushin iyayyena yake ji a ran shi don yaso ne su fatatake ni na koma kai tsaye bai san na wuce wanan bz agun su ina da daraja da kima sosai sa kwarjini ga idanuwan su kuma dole su duba min abinda zai fitar dani.
Nace ni tunda bai yarda ba abari na wuce don gobe zan koma Abuja zan

Please Login or Register in order to submit comment