Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi amsa don tasan ya hanata zuwa gidan dan nata saboda wanan halin da take zuwa tayi.
Kwata kwata bata kaunan zaman Sa,ade da danta don acewan ta kullun wai ta girmay wa mijin nata shi yasa take masu wayo.
Ta manta cewa itama tana da diya mata dake aure a wanu gidan har su uku bata tunanen cewa abinda take wa yar mutane zai iya faruwa akan diyan ta.
Mata bamu tunanen cewa mu uwaye ne masu diya duk abinda ka shuka shine kake girma a rayuwan ka.
Muryan mijin nata ne ke fada mata cewa tazo gida ga Aisha, yar su ta dawo gida da matsala.
Wanan maganan da taji ne yasa ta dafe kirjin ta tana cewa zata tafi amma zata dawo don bata karasa maganan da ya kawo ta ba.

****** ********* ******
******
Tun da farar safiya muryan Jatau ne ya tayar da mutanen gidan da balain da yazo masu.
Yake cewa mama tafito bazai yarda ba tasan yarta honko ne ta dauka takai mashi gidan shi don an raina shi.
Shi za, aiwa wullakanci ko may da za, a dauko honkon akawo maigida don an mai dashi tsoho.
Gaban mama ne yai mugun faduwa haka ta daure tafito zani na faduwa mata gashi har mutane sun fara taruwa don gulma.
Tace a ranta bari ta rufe ido tai mai na mahaukaci kawai a wuce gurin gaba daya.
Ta na lekowa take cewa kai Jatau kada ka dauka ko tsoron ka ake ji duk haukan da kakeyi kyaleka na keyi.
Mata kace kana so mata kuma na baka banga dalilin da zaka taso tsofai tsofai dakai ba kazo muna kana wanan magana abin kunya.
Tace ankai maka honko din sai ka turo min yata yau din nan na fasa auren bazata zauna ba a gidan ka.
Da Jatau yaga mama ta fishi iskanci da hauka dole ya kwantar da nashi haukan yace baki da hurimin daukan min mata, don mata zamana take yanzu.
Matar ka da kace honko ce ai daga yau ta gama zama dakai a gidan ka don dama kudin bazawara ka biya bana budurwa ba.
Yace a shekeke yo ina budurwan take anan kin kai min hinkon diyar ki aiko sai ga su Rukaiyya sun fito daga cikin gida.
Mama ta juya garesu tana cewa maza kuje kuzo min da Lawisa gidan nan yanzun nan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANI NA BARKI DA NAUYIN AMANA A KAN KI YAR UWA

18
Anty na barin falon ta dawo part din ta samay mu zaune inda ta bar mu ganin yanayin mu kawai zai sa kagane rayukan mu a bace yake dagani har mama Altine a lokacin.
A kasa nake zaune kusa da dima diman kujerun dake a falon ta samu kujeran dake daf dani ta zauna .
Sai bayan ta zaunane ta dafa ni a hankali tare da ambatan sunana ta riko min hannuwa na ta hade da nata guri daya.
Jin ta ambaci sunana da irin rikon da taimin yasa na mayar da hankalina gare ta tare da kura mata ido ina sauraren ta.
Rama ina son ki kwantar da hankalinki ki dinga nazarin kowa na gidan da idon basira.
Kamar yadda kiia san duk wani gida mai iyali akwai irin kalubalin da gidan ke fuskan ta hakane ma ko a wanan gidan namu.
Don gaba daya matan gidan da iyayyen gidan kalubalin su akaina yake wanda ba komai ne yakawo haka ba sai ganin Allah ya dorani kan mijina da kuma su baki daya a gidan.
Wanda ba komai ya kawo min shi ba sai hakkurina da kuma halaiyana na gari yasa na cin ma wanan falalan haka.
Rama ina so daga yau ki kasance mai hakkuri ga al, amarin gidan nan don zaki ji ko kiga abubuwa da dama na cin fuska a gamay dani amma dole sai kin daure ki kawar da kan ki ga hakan.
Babu inda zaki muna nan tare da ke har lokacin da Allah zai nufa ki kara yin wani aure idan Allah ya yarda.
Don haka kada ki jefa kanki cikin fitina da rigigimun gidan nan a kaina.
Nasan dazu ranki ya baci yadda hajiya bata ji nauyi idon ku ba a matsayin ku na yan uwana tana tozarta ni a gaban ku yadda taso ta saba da yi min hakan ne tun farkon aurena da danta.
Amma duk wanan ni bai taba damuna don dai nasan Allah kadai yakai ya rabani da heart beat ba wai wani mahaluki ba.
Nan dai taita min nasiha mai tsuma zuciya akan rayuwa har naji gaba daya ma zaman duniya ba dadi a cikin sa.
Washe gari kafin wani lokaci na gama gyaran ko ina inda ya dace a gyara sai na dora girki guri ya kaure da kamshi.
Ina gamawa na shiga nai wanka na saka daya daga cikin dogayen rigunan da aka sayo min na gyara na fito tsab dani.
Na dade a gaban mirro ina kallon yadda halintan jikina ya nuna min sura na a wanan lokacin.
Gaba daya dan lokaci guda na sauya nayi matukar kyawo na zama wata young fresh dani .
Dakin Anty na nufa don na tambaye ta ko zata ci abinci dana gama dafawa a lokacin.
Zaune na samay ta a saman sallaya da alama ta idar da sallah ne a lokacin .
Jin shigowana da yasa ta dan mayar da hankalinta ga kofan ido ta tsura min har na karaso inda take zaune durkusawa nayi daidai inda take zaune ina gaida da ita.
A daidai lokacin da ta shafa ta dago kai tana min murmushi take cewa dani dama yanzu nake son kiranki don zamu dan fita zuwa unguwa sai dai ba mai nisa bane .
Na sharada zamu tafi gidan sister din maigidan ta haihu yau kwana hudu ke nan.
Sai da na tabbatar da ta gama magana nake cewa Allah ya raya tare da cewa dama nazo na fada maki na gama abinci ko zakici yanzu ?
Tace da hakan nayi zaifi min don ina dan jin yunwa dama kin ga sai na fita da nauyi.
Dama fitan nawa kamar fitan dole zanyi shi kin san alamarin dangin miji yadda yake rashin zuwa zai iya jawo min matsala.
Kallon ta nayi ta bani tausayi ga cikin ta ya girma kwarai a lokacin gashi tana matukar karfin hali sosai a lokacin.
Abincin na kawo mata ta zauna nan inda take zaune a kasa taci sai dai ba sosai ba don yanayin ta ba dadi gare ta.
Na tace mu fasa fita sai zuwa gobe idan ta dan kara jin sauki amma sai gashi ina idar da Sallah ta shigo inda muke tana ce min na zo mu tafi mu samu mu dawo in time.
Da sauri na mike tare da dan gyara fuskana na saka hijjab a jikina sai naga anty taja ta tsaya tana kallona wani irin.
Nima dai din kallonn ta nake don ban san wanan kallon da take min ba sai na ga tayi murmushi ta nufo ni tare da daukan gyalen rigan dake jikina tana mika min take cewa haba ko dai ni macen aure ai kinga shigan dake jikina ko.
Dole ba don naso ba na cire hijjab din na yafa gyalen kayan a kaina na fito kamar wata yar birni dani don ni kaina nasan na canza sosai.
Tana gaba ina biye da ita a bayan ta rike da hand bag din ta muna fitowa haraban gidan ne mukai kicibis da maigidan wanda da alama dawowan shi ke nan daga wani guri a lokacin.
Yana ganin ta ya dan ja ya yatsaya tare da jingina jikin shi a jikin motar daya fito daga ciki.
Jikin shi na saye da wani yadin maza mai laushe da daukan ido fari kal zaka iya gano yar farar singlet din ke ta cikin jikin shi
Da sauri na basu guri zuwa gurin motan da nake tunane itace motar ta da muka taba fita da ita.
Volvo ce yafito daga ciki ban san yaya akayi ina can tsaye dan nesa kadan dasu na kurawa kasa ido ina faman tunanen yadda in mota tashigo kauyen mu zamu dinga binta har zuwa kofan gidan da mai shi zai tsaya.
Sai muryan tane ya katse na dago da sauri ina kallon inda suke tsaye gaba dayan su shi da ita sun tsura min ido inda nake tsaye ina tunane.
Tace zo a wanan zamu tafi , zaifi muna saukin tafiya ai da sauri na dago na nufo inda suke tsaye yana kokarin jayewa ya bata guri ta shiga motan ne nake cewa cikin yar murya ina wuni.
Kamar baijini ba don bai amsa min ba sai kokari yake yaga matar shi ta zauna da kyau a cikin motan yana fadin don Alkah ki ja sannu ban son gudu ko sauri tace ina naga lafiyan gudu yanzu heart beat.
Tace zagayo ki zauna mu tafi da sauri na kara na shiga motan da ta bude min dayan gefen na shiga.
Ina jin tana mashi horn a inda yake tsaye hannayen shi harde cikin dan uwa yana kallon yadda take jan motan.
Daga inda nake na dan saci kallon su naga yadda suke nunawa juna tsatsan kauna zalla tsakanin su.
Wani kamshi da sayin ne suka ziyarci hanci na da jikina a lokaci guda wanda ban san lokacin da na sake sanyayan ajiyan zuciya ba don yanayin da naji.
Tace yaya dai Rama na naga tun dazu sai faman tunane kike yi may ke faruwa ne wai ?
Idanuwa na lunshe tare da sake dan murmushi nake cewa anty sauyin rayuwa ne kawai nake tunane da ina kauye yaushe zan taba wanan sabon rayuwan da nake ciki.
Murmushi tayi tare dayiwa wata mota da naji tai mata horn ita ta mayar masu da horm din tana cewa ya dauka ko maigidan ne da kan sa a ciki .
Yanzu ke har kin ganki a wani rayuwa ke nan Rama naji ta tambaye ni ta sake wancan maganan da take na motar da ta wuce gaban mu.
Nace anty idan da nayi auren gidan Jatau ai da ko jaki sai nayi shekara ban gani don ba fita ake a gidan shi ba.
Dariya anty tasa tace kai ai da jin sunan shi kasan mutanen dauri ne ba na yanzu ba wai Jatau.
Wani gida ta tsaya tana horn aka bude mata gidan ta danna kan motar ta zuwa cikin gidan.
Kishiryata zulfa ce tsaye da wata suka kuro muna idon su har muka kawo inda suke basu daina kallin mu ba suna son ganin ko maigidan ne a motar.
Can ta fito daga ciki sai naga sun kawar da kan su ga kallon su basu dade ba naga Zulfa ta juya tana kokarin shiga motar ta.
Muna kawowa wace suke tare tsaye bata da niyya muna magana naji Anty na cewa Samira yaya yau ?
A, a uwargida yau kece da kanki a motar oga wani kaya sai amali ke nan ?
Murmushi anty tayi mata muka sa kai zuwa cikin gidan gidan ya kaure da hayani zaka fahinci akwai mutane a gidan.
Wani daki muka nufa inda nake zaton nan ne dakin matar gidan da muka zo gayarwa din.
Da sallama muka sa kai a dakin yayin da matan dake dakin suka kuro muna ido su.
Matar suna da matukar kama da mijin anty sosai dagani basai anfada ma ba don jini yana aiki sosai.
Tun ba su gaisa ba take cewa a, a matar mulki an samu fitowa ke nan dai ai na dauka mulkin ba zai barki zuwa ganin baby ba ai.
Tace ai kin san ko don nazo naga dana zan zo ai na duba ku ko ?
Tace nasani ai ba don ni kika zo gidan nan ba don yaushe rabon da kizo gidan nan Sa, ade ?
Zama anty tayi daga gefen gadon da kyat ta zauna tare da maida numfashin ta.
Nan ta fara gaisawa da matan dake dakin ina tsaye daga gefe kofan ina kare ma matan birni kallo.
Can ta hangoni tsaye take cewa Rama zo nan mana ki zauna sai lokacin na karasa kusa da ita maijegon ke cewa zo nan ki zauna ga guri kinji donnke kawai zan tara.
Anty tace ai duk daya idan kin tari kaunana akai dariya suna kokarin mika mata baby dake nade a cikin showel fari tas dashi.
Bata jima rike dashi ba ta miko min shi gani da son yara nan na karbe shi na rugumay ina karewa taron kallo cikin sha,awa.
Sai fira suke kwasa tsakanin su inajin suna mata ba,a wai ashe ta tsofe ne haka ?
Maijegon nace masu ai kunsan ta da wayo taki bari kannen ta su samu sai ita ce mai daukewa.
Anty tace wanan kuma a tambaye ku don kune masu sawa ai bani ba inma rowa ne kukai masu rowa abin.
Aka kwashe da dariya maijegon ke cewa yanzu ko kishiyar ki ta bar nan har da gulman ki mukayi ai.
Anty tai dariya tace shine aikin ku ai dangin miji yanzu nazo shine nima zakuyi nata dani ko ?
Kai ai Zulfa yar uwa tace tace ni kuma yar uwar mijin ki ba kinga ma falo zan koma nasamu Nura muyi zumuncin mu.
Sai lokacin na fahinci mijin mai haihuwan dan uwan anty ne ke nan ita kuma matar yar uwan mijin ta.
Maijegon take cewa ai dama kuna zumuncin ne sai na damu dake dashi duk abu daya ne ba zumuncin.
Waya fada maki lokacin da muke zumutan mu a waya fada maki zaiyi ne ?
Saade baki da dama fa yanzu sabon gidan da kowa ke murnan shiga shine kika karbe masu part din da yafi kyau.
Kai ni saade na shiga uku wata sabuwa kuma ke nan yanzu wai mayye banbancin wanan part din da nasu Aisha ?
Su shi suke so ai, anty tace nikuma shi mijina ya zaba min na zauna ciki sai yaya kw nan.
Sai lokacin wata daga cikin mata ukun da muka samu tai magana tace kaji gaskiya haka nake son namijin da yasan kan shi a samu tare a mutu tare.
Anty tace kin san su matan yanzu su samay ka da mijinka suce sun fika iyawa ne in bashi ba gidan dai ai duk gidan ne ko ?
Maijegon tace barsu kawai indai bros ne karamin aikin shine ya mayar dasu tsihon gidan idan sun matsa ai na fada masu gaskiya, don kowan su sai cika take tana batsewa .
Ji min fa don Allah ijin matar dake zaune tace wai da may suke nufi don kina ta ffarko su amare sai ya fifita su ke nan ko?
Aini yaya yai min daidai wallahi don bai daukan raini ga kan shi da matar shi ba don haka na da wa yan nan da kike gani ko mu yan uwan shi sai munyi da gaske mu shiga gidan shi.
Yanzu dai kuka fada ai da bakin ku inji anty saade tana dariya
Maijego tace ni hajiya na rasa may yasa take son saka kanta cikin irin wanan magana ranan naje gida baba ya kirata ina jin suna case din dashi akan maganan.
Anty ce ta kawar da zancen dacewa yauwa fatima dama ina son ganin ki wallahi don wanan kaunan tawa nake son tayi joining din school din ku.
Matar da ta kira da fatima tai saurin kallona tace har ta gama secondry ne wanan din ?
Tagama almost two years ke nan yanzu masha Allahu inji matar tace karama da ita haka ?
Tace yanzu zan mata kokari tasamu matric ta jona sai tayi jam idan lokaci yayi mugani.
Nan dai sukai ta magana yadda za, ayi kan karatuna ina sauraren su duk dadi ya kamani cikin raina tace wa matar zata turo da komai nawa a kawo mata insha Allahu.
Bamu jima ba mukai masu sallama anty ta ciro kudi mai yawa ta dora saman gefen showel din da baby ke ciki tace asaya mai pant dashi.
Muna tafe ba wanda yai magana sai zuwa can take cewa zan tura ki da hamza gobe ai browsing din takardan ki mu gani sai ai amfani dashi.
Wani shago ta tsayar da mota muka shiga abubuwan amfanin mu da babu a gida ta saya masu yawa ina kallon yadda ake komai har biya muka dawo gida .
A falo muka zube mun samu yara sun dawo daga schools lokacin nan muka shiririce dasu don sunyo kaina muna hira na cire masu uniform din su na saka masu kayan gida na basu abincin su .
Shi Nasir nasan halin shi don haka na koma kusa dashi ina da yake na zauna yana ci muna dan hira har na samu ya dan ci abincin nasa.
Duk abinda mukeyi anty tana kallon mu a fakaice tana yabawa da irin hikimar da nake wa yaran wanda ko ita uwar su bata da lokacin masu hakan da nake masu.
Suna gamawa muka fara shirmayn karatun mu ina biye masu kafin lesson teacher din yazo.
Sai ga hanifa yar gurin Zulfa ta shigo inda muke ko uniform ba a cire mata ba lokacin ta zauna tare da mu ana ta wasa da karatu a lokaci daya.
Bata fi minti ko goma da shigowa ba sai ga wata mata badai tsohuwa bace can ta shigo da sallama tana ganin mu hankalin ta yana kan hanifa dake wasa da Amira take cewa hajiya barka da hutawa .
Anty ta karba mata tace hanifa wai kizo inji maman ki sai yarinyar tace bazata je ba nan matar ta shiga lalashin yarinyar amma fir taki bin matar.
Nace ki tafi ki barta mana tunda tace bata zuwa matar ta marairaice tace idan na tafi bada ita ba fada hajiya zatayi min .
Da kyat na lalashi yarinyar nace yanzu zamu hadu a gurin lesson da ita ta tafi kawai amma yarinyar taki binta.
Matar ta juya ta fita sai lokacin anty dake kishingide tana kallon mu tai magana tace ai yanzu dawowa zatayi don bazasu barta nan ba.
Suna ganin idan sun barta cuta mata za, ayi ne don haka ki lalashe ta ta tafi don Allah Rama rarashe ta tafi please.
Kafin anty takai aya ga maganan ta sai ga matan da dawo falon fuskan ta ba dadin gani da gani an mata fada ne sosai tana zuwa ta sukkuci yarinyar a kafadan ta tana ihu tana kuka ta fita da ita daga falon namu.
Anty tace may na fada maki ai basu bari yarinyar ta zauna a nan zuwan ki ne ma har take shigowa inda muke dan zaman da kukayi da ita ta dan saba da nan din.
Baifi minti uku ba Nasir na saman kaina wai yana min fakin ina zaune na ishishire kafana zaune saman ties .
Maigidan ne ya shigo rike da hannun yarinyar dake kuka suna shigowa ta sake hannun ta da rikon uban tayo kaina tana dariya da cewa itama zatai min kitso ne.
Anty na ganin su take cewa kadawo da ita ne kuma yace a hannun wanan bakuwar matar na ganta tana kuka wai ance ta dauko ta da karfi ta maida ita part din su.
Nikan ina ganin ya shigo ina kokatin tashi nabar falon kamar hadin baki yaran duk suka haye min jiki wai kitso zasuyi min dukkan su sai kokuwa suke kowa nason ya rike min kai na.
Kallon mu iyayyen keyi anty tace kaga shirmay da take so don Rama na biye masu suna yadda suke so da ita.
Yace ai yaro haka yake so dama shi ko yaushe yana inda yake ganin fuska ne shi amma su basu ganewa don kishin tsiya.
Muryan Zulfane a falon a fusace take cewa oya Hanifa come to mummy what are you doing here.
Yarinyar ta bata rai tare makewa a jiki na tana cewa mummy ki barni gurin anty please.
Zulfa get out kafin raina ya baci idan ba haka ba yanzu ranki zai baci ga hukuncin da zan yake a kan ki.
Wani kallo tai mashi sai dai yadda taga fuskan shi yasa takasa fadin abinda take da niyar fadi a lokacin.
Ta juya har takai kofa take cewa wanan ai rashin adalci ne yaya za aiwa mutum dole kan dan shi kowa ai yana da nasa yarinke abinsa mana.
Idan kai an mai dakai mijin tace ai ba zaka mayar damu muma sai yadda akayi damu ba da diyan mu a gidan kafin ta ci gaba da magana.
Ya kara fadi a hasale ba ita da akaiwa ba har mu dake falon sai da muka kadu idon shi ya kade yai ja yace get out i said
Da sauri tabar part din ranta a bace shima yabi bayan ta ba tare da yai magana ba.
Gaba dayan mu hankalin mu ya koma kansu kaina na sadda a kasa don sun bani tsoro gaba dayan su.
Mama tace ikon Allah zamanin nan ina zaki damu ne wai haka ni na taba ganin irin haka gida daya ace yaro ba zaiyi yadda yake so ba.
Anty tai murmushi tace gani suke yadda zukatan su yake akaina hakan ne nima zan aikatawa nasu diyan .
Niko yaro koba dan mijina bane ina son shi balle dan da mijina ya haifa yan uwan haihuwa diyana.
Allah dai ya kara haushe ki kan su kawai za, ace don sunyi nisa sai addua ai kishi ba hauka bane.
Murmushi anty tayi ta mayar da hankalin ta inda muke zaune muna sha, anin mu hankalin a kwance ba abinda ya damay mu.
Shaawan mu ne yakamata yadda taga na kwantar da hankalina kamar ba abinda ya taba faruwa dani a baya.
Gashi yanzu na kwantar da hankalina a gurin ta na gyagije kamar ba wani damuwa a tare dani.
Lesson teacher ne yazo muka fita zuwa lesson gaba dayan mu, nan muka hade da yar gurin hindatu itama a kusa dani tazo ta zauna tana ta zuba min surutu.
Uban daga inda yake mu bamu ganin shi yana kallon yadda yaran ke ta shige min a jikina.
Mamaki yakeyi yadda yaran sukai saurin sabawa dani haka sosai har Nasir da ke da tsauri a cikin su amma yana yarda dani haka.
Yana matukar tausayawa anty saade amma yanzu ya fahinci amun wanan yarinyar a kusa da ita ya sa ta dan samu sakewa sosai.
Don ko yawan tashi da jikin ta keyi yanzu ta daina yin haka sosai gashi mahaifiyar shi ta matsa kan sai yasa saade ta sallami wanan yarinyar don yaki yarda da hankan ne yasa sauran matan nashi dauko wasu suma su zauna dasu abinda bayaso a gidan shi amma babu yadda ya iya don samun lafiyan matar tashi ya yarde da hakan badon yaso ba.
Yanzu gashi a dalilin haka yaran shi na zama guri daya suyi wasan su da dariya wanda hakan zai kawo masu shakuwa a tsakanin su.

****** *********

Please Login or Register in order to submit comment