Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na kowa ne.
Yace yanzu dai komai ya wuce ai Allah ya wanke ki banga abin tsayawa bata rai ba anan tunda zancen ya wuce.
Nace ai kaine duk wani sanadin fitina na dasu ina son in tabbatar ma daddy zan jure ko wani irin hali da zan shiga dasu akan ka nakuma jure hakan na zama jaruma a wurin su, don na tabbatar masu da kai kan ka cewa ni zama nake da kowan ku tsakani da Allah.
Insha Allahu daddy bazaka taba danasanin aure na da kayi ba indai ta wurina matsala zai fito har mu saba maka.
A hankali ya karasa takowa inda nake yakai zaune tare da min kiss a goshina yace nagode da kika kara tabbatar min da hakan da bakin ki Rahama.
Na dade da sanin kina gujewa bacin zuciyan wasu ki hade shi a ran ki ni kaina nazo nayi nadaman yadda nai maki gama yadda Allah yai saurin nuna min kuskuren abinda nayi da wuri.
Wani sanyi naji ya lulubeni a lokaci daya atake kuma hawayen nadama suka soma zubo min don nasan nayi kuskuren daukan zafin da nayi da kowa bayan Allah ya wanke ni ga maganan ko.
Yace ina son daga yau ki saki ranki da kowa ki koma normal batare da su mama sun fahinci akwai matsala a tsakanin mu ba.
Nace in sha Allahu ya wuce zanyi yadda kace tunda haka kake so amma ni kawai dama dan hutawa nake kafin na koma bakin aikina.
Yace ai ban ki hutun ba nima ina son hakan amma a rika dan kula mutane aba kowa hakkin shi don Allah.
Ya fice daga dakin bayan mun samu fahintar junan mu nace a raina dama ance matan yanzu a dakin su suke yaji ba sai wani yaji ba.
Gashi mun samu matsala kuma mun shirya a tsakanin mu batare da tsofin dake gidan sun fahince mu ba.
Tun washe gari na dan fara shiga mutane in dan zauna sai dai ban jin dadi sosai saboda dana zauna zan fara barci a gurin.
Har sai nake tunanen ko dai wani ciwo ne ya shigeni haka na barci na san dai dana haihu duk wani treatment din daya dace aimin a asibiti Faiza tai min shi a gida.
Ashe ba haka bane gajiya ne kawai yake sani barcin bayan kwana biyu sai na murmure har na fara zuwa gun aikina yadda ya dace don saura wata daya da kwanaki mu gama bautar kasan namu ko .
Haka yasa na dage sosai ga aiyukana na gidan mijina dana wurin bauta ma kasa don kada na samu matsala a ko wani ban gare.
Daddy yakan yi kwana goma zuwa sha daya ko sha biyu sai ya leka kano yai kusan kwanakin da yayi muna ya dawo.
Har nai arbain wanda yazo daidai kuma da gama bautan kasa na a asibitin da nakewa aiki din.
Sun karbi takatdun mu mu hudu sunce zasu iya neman mu anty time idan bukatan hakan ya taso garesu.
An bamu kyaututuka na yabo kamar kada a rabu muka barsu suna jin kewar mu sai kuma gida gasu mama na shirin komawa gida don yanzu hankalin su ya koma gida sosai sun gaji da zama wuri daya.
Daddy yaban kudi masu yawa mukaje dasu sukai sayayya saura kwana uku su tafi sai shirin tafiyan su akeyi don shi zai mayar dasu gida da kan shi.
Naso zuwa amma daddy ya hana yace na bari idan sallah yazo sai mu tafi can muyi sallah tunda ya gabato su ma don azumi suke son komawa dakunan su.
Ranan da zasu tafi kusan duk mun nuna damuwan mu don bamu son su tafi saboda suna da dadin zama sosai.
Bayan tafiyan su sai gidan ya koma muna shiru kamar ba kowa dama ance bako Rahama ne ga wuri.
Shirun da gidan yayi yasa muna shirin kwanciya ranan saiga Ihisan cikin kayan barcin ta take cewa wai ita bazata iya kwana dakin ta ba tsoro take ji.
Nace a, a Ihisan in banda abinki ai ba yau kika fara kwana dakin ba kuma kefa kika matsa da abaki wanan dakin ke shi kike so.
Don haka kiyi hakkuri ki koma dakin ki ki kwanta kiyi addua Allah zai tsare ki tace itafa atabau sai dai in Atika zata zo su dinga kwana a tare.
Atika tace wa ni wallahi bazan tafi ba keda kike fada a school din mu cewa ba baban mu daya mu yan aikin gidan ku ne anty mu ta karbewa mamakin miji shine mukewa mutane sallon banza kika sa akai min dariya.
Wani iri naji ba dadi a raina amma na daure nace haba Atika don kawai tace ki tayata kwana shine zaki mata sheri haka ?
Tace wallahi anty ba sheri bane ai mama Laraba ce tai muna sharia da muka dawo gida tace kuma nayi hakkuri kada na fada maki.
To ai yanzu gashi duk da anbaki hakkuri kin fada naji tace ai haushi naji wallahi ni ba zan tafi ba na juya inda Ihisan take da alama dai tsoro take ji din nakoma lalashin Atika din tace muje amma kinci arzikin anty wallahi nace nagode.
Na juya wurin Ihisan nace da ita haba ihisan ai ba sai kin tozarta dan uwan ki ba zakiji dadi kowa ma ai yasan cin arziki mukazo gidan ku shi mutum rana gare shi da kike ganin shi don akwai ranan da zai taimaka maka.
Tace Iam sorry mummy bazan sake ba ai mamanace tace dama idan sun min tsiya na fada masu hakana amma na bari tun ranan da grandma tai min fadan hakan.
Nace good girl haka ake son yaro ya dauki fadan manya dama ki bari kinji a zauna lafiya da mai kudi da tallaka ai duk Allah yayi shi ko.
Suka wuce zuwa dakin nace kada a manta ayi addua dai idan za a kwanta suka insha Allahu.
Bayan tafiyan su mamakine fal a zuciyana yadda mace zata zaunar da karamar yarinya haka tana koya mata kissa da kisisina Allah kadai yasan irin hudubar da taiwa yarinya da zatazo ko idan sunyi waya.
Don haka zan bi yarinyar sannu a hankali na fahinci komai da take kullawa agidan don idan nai sakaci zata iya min wani kulli da ba zan iya fitar da kaina a ciki ba wata rana.
Sai da na samu kebewa da Atika nai mata fada mai kama da jan kunne akan ta sani ba daya suke ba da Ihisan don kada wata rana taga tayi abu tace ita ma zatayi sosai naja mata kunne Alhamdullahi kuma yarinyar ta fahinci maface ni sosai.

********* ********* *********
Bayan daddy ya isa gida ya kai su mama Laraba gidan ta inda anan Attu zata kwana sai washegari yasa akaita gida.
Ya isa gidan shi ya samu iyalin shi lafiya anty ce da girki bayan sun gaisa ne take tambayan shi su mama yace da ita ai tare suka dawo ya sauke su gida ne.
Tace a a na dauka ai tare da Rahaman zasu dawo gaba daya tunda ta gama abinda ya kaita can din ko ?
Yace cikin mamaki ta dawo ina kuma tace ban gane ta dawo ina ba, ba anan take ba dama ko a can zatai ta zama kuma ?
Yace dama kunyi da ita cewa idan ta gama zata dawo nan ne ?
Tace da kai dai mukayi haka da zata tafi yace to a can zata zauna don aiki zata fara badadewa ba da zaran danta yayi kwari.
Nan ta bishi da kallon mamaki tace au Rahaman aiki zatayi ita ke nan yace eh ba shine burinta ba ko haka zatai tsawon shekaru bakwai ya tafi a banza bata more mai ba wa alumma ?
Abin mamaki baya karewa kullun a gidan nan tace daga karshe yayi ashe nike wautana anan ina murnan zasu dawo gida.
Yace ai da nan da can duk daya ne a garesu ko may ake a can wanda ba ayi anan din waya ne kullun kuna gaisawa idan kun ga dama to sai may kuma ?
Bata iya magana ba don mamakin daya bata yawani zare a lokaci daya kamar bashi kamar wani bako ya koma mata sam yanzu ba kamar wanda ta sani ba a baya.
Mai dubaiyya da son jin bukatunta amma yanzu shi da kan shi ma ke kirkiro mata matsala.
Don tunda ya tafi da yara karatu can ta fara kawo wutan gane cewa akwai magana gaba don haka ta mike tsam ta bar falon ta barshi yana cin abinci.
Ya bita da kallo sai dai yana jiran ta tunda duk itace ta jawo mai yin haka ai ta dauko fitina ta saka a ranta bata zaman lafiya dashi kwata kwata yanzu haka ma abokan zamar ta kamar wacce asiri ke aiki a kanta har yanzu.
Shiru shiru yana jiran ta sake maganan ya bata amsa daidai da maganan ta amma sai yaji shiru bata kara yin maganan ba again.
Abinda bai sani ba ranan ta kwana tana tunane kan maganan sai daga karshe ne ta dai yanke shawaran ta hakkura tasawa kanta saida kawai akan zancen Rahama.
Don dai koma may ye dai ai itace silarshi tana ta bada kai ana mata dariya a tsakanin su ga yaranta can har biyu gunta amma bata ji wani korafi ko kadan ba daga yaran har yanzu ko sunyi waya dasu lafiya lau take jin su.
Hakkuri da nadaman abubuwa yazo mata a rai a lokaci daya ta mike ta roki Allah da ya sanyaya mata zafin Rama da take yawan ji a zuciyar ta koda yaushe.
Tasan yarinyar bazata iya cewa ga wani abinda ta taba mata ba na cutar wa amma yakai yanzu saboda halin da take gwada mata har ta fara mayar mata da amsan magana mai zafi.
Shine dalilin da taja bakinta tai shiru ta dai san halin mijin su fiye da kowa hutsune bai jin mutunci idan idon shi ya rufe.
Kowa kuma haka yakewa don may karamar yarinyar da ta raina zata fita sanin maganin zama da mijin su lafiya aiko wacce mace na kishin mijinta ta san kuma Rama na da kishin ita ma tunda mace ce amma ta iya dannewa ta boye sai itace bazata iya boye nata ba.

Aike da kira ya ishe shi a gidan su Hindatu har takai ranan an datse a gidan mahaifan shi nan Alhaji shi ya sa baki yace sai yaje ya duba matar nashi tunda yanzu ta gane kuren ta.
Baiso ba haka ya daure ya tafi da yamma shi da Bashir daya dauka don ya raka shi gidan ya ganta amma ran shi baiso haka ba.
Sun isa gidan suka aika a sanar da zuwan su hindatu naji ta fada daki tafara dauko kwallin da aka bata ta shafa tare da wani powder da turare duk tayi yadda aka umurce tayi ta yafa taiwa uwarta sallama ta fita uwar nacewa kinyi yadda akace kiyi ko kin dai san irin kudin da muka kashe a gurin nan.
Tace kada ki damu mama nayi komai yin fatan dai mu dace kawai idan ya ganni din.
A lokacin saura wata daya ta gama idda da takeyi tana fita ta samay su zaune a falo ta gaidasu a cikin wani irin ladabin shagu.
Ya dago kai da kyat yana amsa mata yana kallonta yaji wani irin shock a ilahirin jikin shi gaba daya yaga ta sauya mashi ta koma kamar wata hawai niya mai rikida ako wani lokaci.
Tai mashi kyau ta koma kamar wata yar shila a ganin shi, wani irin sonta da kaunarta yana fisgan shi.
Cikin washe baki yace da ita idon ki ke nan daga magana kadan sai ki fushi ki dawo gida.
Take ta gane cewa tarkon ta ya kama kurciyar da take hako nan ta shiga juya shi yadda take so har sukai mata sallama suka tafi Bashir dai yana kallon ikon Allah.
Sai da suka kama hanya yaji daddy ya sauke ajiyan zuciya da karfi yace yaya akayi ne mutumina ?
Yace kaina ne naji yai min wani irin sarawa wallahi muna barin wurin nan kamar kar hindatu tafito gaba daya sai na nemi natsuwana na rasa.
Yanzu kuma mun bar wurin naji kaina yana sara min ba dadi wallahi nan dai Bashir ya nisa yace dashi nifa kada nai magana nayi laifi kuma ?
Yace kamar ya kayi laifi kawai kafadi maganan ka mana kai tsaye ?
Yace abinda zan fada ne da nauyi akwai kuma kamshin gaskiya a cikin sa yace kafadi maganan ka mana kai tsaye ka tsaya kana wani kwanaye kwanaye haka dakai ?
Bashir ya nisa yace anya Hindatu bata gama da kaiba yadda naga ka zabura daka gantaka kuma sukurkuce a lokaci daya ga wani kamshi wani irin mugun turaren gargajita danaji tanayi.
Daddy yace kai amma akwai ka da wani magana yanzu nine hindatu zataiwa magani kake gani ya kamani ?
Bashir yace kai kafi karfin sherin mace ne ko may wallahi ka fada tarkon mata kace nace da kai wata rana bai yi magana ba sai murmushin da yayi yace kai akwai da wani zance wallahi hindatu fa matatace ka sani.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,

77
Idan daddy ya tafi baya wuce kwanakin da na fada a baya sai gashi wanan tafiya har ya gwauta kwana ashirin da biyu a kano.
Baya kiran mu kamar yadda ya saba kiran mu a baya idan yana can sai jefi jefi zai dan kira sama sama yaji lafiyan mu.
Sai dai abinda na dan kula dashi shine yawan kiran Ihisan da takanyi musanman ma da dare naso na dan gane wani abu amma sai kuma nai tunanen kila rashin uwar ta a gidan yanzu yasa yake yawan kula ta din.
Ranan sai gashi ya dawo sai dai ya fada ya dan yi baki kadan mun tare shi da murnan ganin shi sai dai ba wani walwala sosai a tare dashi sai na dauka duk gajiya ne hakan kawai ya kama shi.
Sai da yai wanka ya huta bai dade ba yafito ya fita daga gidan ina mai tayin abinci yace dani barshi kawai bana jin cin abinci yanzu.
Ga watan Azumi saura yan kwanaki a lokacin sai kuma ba hankalin maigidan wuri daya don da gani akwai abinda yasa a gaban shi.
Ni dai ban tsananta wa kaina sai nasan may yake ciki ba ina dai kokarin wurin ganin na sauke duk wani nauyin da ya dace ai mashi.
Wani abinda na lura dashi kuma shine duk dare sai mun kwanta za, a kira shi da waya zai dauki lokaci yana waya.
Lokacin ne na fara shan jinin jikina da gane cewa da mace yake waya sai na nemi walwala a tare dani na rasa amma duk da hakan bani nuna komai a fili na bar abin a raina kawai.
Ana azumi saura kwana ukku lokaci duk kwanan shi shidda da dawowa yace zai koma kano a gobe banyi mamaki ba ko zaton wani abu tunda nasan cewa gida ne can kuma akwai iyali.
Sai da ya shirya yafito yana waya naga shirin wucewa yakeyi nace daddy sai ya juyo yana kallo na naji yace da wanda yake wayan minti biyu ya kashe ya kara juyowa inda nakke yace dani umm,humm ?
Na dan kwantar da murya nace daddy dama naga kafin ka dawo za a tashi da azumi shine nace baka sai muna abin taron azumin ba.
Yace ban fahince ki ba may kike nufi da hakan nace wai da nace kayan shan ruwa kodon yaran nan ko ?
Yace Rahama yaushe kika fara wanan halin har ni zakice wai ban sayo maku wani abu ba ko may kike nufi da wanan maganan naki ?
Ko kin taba min magana akan na sayo maku abu a gidan nan bani ke sayowa ba in naga dacewan hakan ?
A sanyaye nace don Allah daddy kayi hakkuri nayii kuskure dama don naga wancan karon ka dan jiima baka dawo bane yasa nai magana yanzu din.
Yace o,wo yai min wani irin kallon sama da kasa kamar wanda ke hake dani dama yana jirace na tanka mai.
Nace Allah ya tsare aje lafiya adawo lafiya yace amin kamar a hasale ya juya ya wuce abin shi batare da ko juyowa ba again.
Mamaki ya kamani nakai zaune a kujeran dake kusa dani ban san abinda yasa daddy yanzu magana ba magana ba sai ya hauni da masifa sosai.
Aisha ce takawo min Haidar da ke kuka na karbe shi sai ga baba ya biyo su ya kwanta a jikina nan na sauke ajiyan zuciya na gyara ina fitar da nono nabawa yaron.
Ina shayar da yaeon ina tunane ga baba da ke tsaye rabin jikin shi kwance a jikina ya damay ni da tabe tabe a fuskana.
Nace a sanyaye don haushi nakeji a raina bari mana baba yaton bai bari ba nakai mai duka akai abinda bana yi duka sai dai inwa yaro fada.
Take yaton ya fara kuka sai kuma yabani tausayi bashi ya bata min rai ba na fashe haushin uban shi a kan shi.
Na jawo shi da hannu daya ina lalashin shi har na samu yai shiru Aisha taji kukan shi ta fito tana tambayan may ya samay shi kuma ?
Nace baijin magana ne na dan duke shi shine kikaji ya bare baki haka yana damun mutane da kukan banzan shi.
Nan dai taja yaron suka fice suka barni ina tune a zaune sai naga ni may ma yakaini yi mai magana bayan nasan yadda muke a yanzu dashi.
Sai zuwa sha biyu har lokacin banajin dadin yadda muka rabu ya tafi dani a hasale sai na yanke shawaran kiran shi na bashi hakkuri.
Kira daya biyu ga hudu ya daga yace cikin muryan shi mai nuna har yanzu baya jin dadin ranshi da fadin.
Yaya akayi kuma na dake nace ba komai sannu da hanya kawai dama zan maka sai kuma na baka hakkuri bisa ga saba makan danayi da zu a yafe min don Allah nayi kuskure na sani.
Yace is ok sai anjima ssi ya kashe wayan kit bin wayan nayi da kallon mamaki may naiwa daddy ne haka nake tambayan kaina ?
Abinda ban sani ba ashe bani kadai ke fuskantar wanan halin ba kowan mu ya rasa gane kan shi tun zuwan shi gidan su hindatu abubuwa suka jagule baki daya a kan shi.
Wanan zuwan da yayi yazo a tsayar da maganan komawan ta gidan shi har ya iso gida baida walwala ba isa gidan shi ba sai da yaje gidan su hindatu ya zube tsaraban da ya sawo masu a hanya.
Ya samu iyayyen shi da zance sai dai hajiya ta nuna bata yarda ba taso abar hindatu a hakkura hakana a hakkura kawai.
Amma yadda daddy ya dage sai hankalin su ya tashi Alhaji yai gyaran muryan yace kinga ayi hakkuri tunda shike da abin shi don haka barshi ya gyara auren shi a zauna lafiya.
Dole hajiyan ta hakkura sai dai bataso hakan ba Alhaji ya tura manya aje a gyara zancen sai ga masu zuwa sun dawo da sabuwar magana kuma.
Wai iyayyen hindatu da ita kanta sunce in har zai amincr idan ta koma ya maida ita Abuja da zama ita ma ta amince da zata dawo.
Nan hajiya ta hau fada tace sam ba zai yuyu ba anan ma gaban kowa yaya aka kare da ita balle ta bisu can inda babu idon kowa sai su yasu yasun su.
Amma daddy na zuwa yace may zai hana ya amince da nan da can ai duk gidan shine shike da iko akan komai don haka ai wanan ba matsala bane ai.
Hajiya tace yanzu da hankalinka Alhaji karami kake wanan magan kafa san halin yarinyar nan sarai bawai ta canza bane .
Yace kai hajiya ita hindatu wani haline da ita kawai ni keda gidana ai zan san yadda zanyi indon wanan ne ai ba wani matsala akan shi.
Tace a, a fa yar mutane dake can zaune kalau cikin rufin asirinta kada taje ta tayarwa yar mutane da hankali kuma ?
Hajiya ita da Rahama din ai duk ni aje su ko may zai kawo wani fitina kuma yanzu tunda kowa yasan kowa dama .
Hajiya bata dai gane komai ba don ya dage daya amince da atafi din shi ba matsalar komai ga yin hakan tace to shike nan ai may daki shiyasan inda ruwa ke mai yoyo.
An mayar da aure ko su anty dake garin basu da labari sai ji da sukayi ga bakin shi yake fada masu batace dashi kalla ba don ta fahinci irin rawan kafan da yake duk aanan lokaci ta san kuma ruwa baya tsami banza ai.
Bayan kwana biyar sai gashi ya dawo lokacin Azumi nada kwana biyu da dauka bai nuna min komai ba mun tare shi cikin mutunci.
Sai bayan an sha ruwa yana zaune da yaran suna hira na shigo falon bayan na idar da sallah nai mashi sannu da shan ruwa na juya zan wuce yace dani gobe ina son duk wani kayan daki a fitar sai za a saka sabo ne .
Na juyo da mamaki don naga kayan ai basu komai ba amma kuma sai na share don kada na daukowa kaina magana nace Allah ya kaimu kawai.
Sun gama ya sallami yaran yai shirin kwanci sai dana fahinci cewa yadan dade da shigewa na shirya naje dakin.
Na mulke jikina da ture masu kamshi don kawar da karnin nonon da nake shayarwa a lokacin.
Har na shiga na kwanta yana waya bai gama ba har barci ya dauke ni ya gama bai tayardani ba sai da muka tashi don yin sahur.
Washegari tin safe muka tashi da aikin kwashe kayan da ya umurce mu dayi bamu jima da kwashewa baaka fara shigo da wasu iri dirka dirkan kujeru masu kyau da girma.
Ma aikata suka gyara komai sai dai dakina da dayan dakin dake facin din na ihisan komai nashi iri daya ne da nawa kala ne kawai aka banbanta masu sai biyu zuwa uku suka gama lokacin ina kitchen mun fara hada abin buda baki ko.
Munyi mamakin ganin hakan amma naja bakina nai shiru ban tsaya magana ba don jin ko yaya hakan din.
Sai dare sosai ya dawo har yaran sun shige ko dakun nan su don azumi ne kowa ya gaji ba wani dogon hira.
Ko ni har na shige na kashe wutan falon ya dawo gidan jin motsin dawiwan shi yasa na fito ya na zaune yana cin abincin da ya samu an jera mai na buda baki.
Nai mai sannu da zuwa ina kokarin juyawa naji ya kira sunana na dakatar da tafiyan dana fara yi tare da juyowa gare shi.
Yace zoki samu wuri ki zauna ina son nayi magana dake ne samun wuri nayi na zauna sai dai ba gaf dashi ba.
Yace Rahama ina son yin wani magana dake ne sai dai ina fatan zaki fahince duk da nasan ba wani bakon abu

Please Login or Register in order to submit comment