Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka fahinci halinci halin mutum.
Babu wani dadin aure dayafi yi bari na bari kaso abinda taje so fiye dashi yan uwan shi su zamo tankar naki da zuciya daya.
Abokan zaman ki kada ki bisu da sheri bar mugu yaita mugunta shi idan baka rama ba kaine a kan sa duk abinda yayi sai ya koma mai.
Attu tace amma malam ya dace abata tsari wanda zaibi jikin ta don ni ina tsoron matan birni wallahi ba imani ne dasu ba akan kishiya.
Malam yai murmushi yace Attu ai shi wanan matsala bawai matan birni ne kawai ba har na kauyen idan Allah ya hada ka da maiyi hakane ke faruwa.
Ita hankalinta ba a kwance ba kaima naka da kake tare da ita ba akwance yake ba.
Bawani abu zan ma jikan ki ba sai tsari da zan bata tasha shi yanzu anan Allah ya tsare mu baki daya mu dasu.
Ya fara binciken wani abu a cikin kayan shi muna kallo yajawo ruwa cikin wani gora ya karkada ya mikowa Attu yace tabani na sha tamika min take na sha da bissimillah a gurin namiko mata dan roban da nasha yace Allah ya tsare ya kare.
Muka ansa da amin yace kiyi biyayya ga magabatan ki sai a zauna lafiya dakowa banga wani matsala mai yawa ba ga al, amarin ki sai yawan tarin alherin hakan idan Allah ya yarda.
Can ya dauko wani abu yace dani karbi wanan na sa hannu na karba yace murzashi da hannun ki biyu sai ki shafe fuskan ki da shi har zuwa kirjinki.
Nadaga hijjabina nayi yadda yace nayi yace Allah yabada zaman lafiya ya bada zuria masu albarka mukace amin.
Har zamu mike yace da Attu idan an kai ta kada ta shiga gidan sai ta karanta fatiha da kulhuwallahu falaki da nas kin gasu nan ba karamin abu bane faidar su yafi jin su da mukeyi amma muna sakaci gurin amfani dasu.
Mukai mai sallama na dawo gida gurin dana shafa wanan maganin ga kamshi gashi kuma inajin yana shiga jikina kamar wani abu na min yado a jikina lokacin.
Haka dai na daure har yazo na daina jin hakan da nake ji.
Nai mamaki ganin zarah tazo tare da wasu yan mata course mate din mu da muke dan shiri dasu nasan aikin anty ne hakan.
Taro sosai akai masu da yamma sai ga mama Altine tazo tana ra yan kamay kamay bata daiga canjin fuska ga kowa ba don an tare da mutunci yadda aka saba.
Can daki inda muke Zarah ce ke faman bamu dariya wai tana min lacture din yadda zan dinga yi na sace zuciyan miji ga sauran kishiyoyi na.
Dariya ma take bani take cewa oh dariya ma kike min wallahi ko kishiya daya zaki sama dole ne fa sai kin zage damtsem ki gurin zama karuwan gida karuwan dakin ki.
Don Allah ki daure ki fitae da kunya ga idon ki Rahama ki rage wanan halin rashin magana a gavan mijin ki don zai iya cutar dake yin hakan.
Samu kayan da kika san na jan ra, ayime ki dinga saka mai idan kuna ku biyu kai bama ku biyu ba nuna masu fa ke kece kawai a wuce gurin.
Nafisa tace aiko akwai wasu kaya english wear da suka fito masu kyau na mata su ya dace ki saya da mun isa sai ki basa na sayo maki su wallahi zaki shana sosai a cikin su ga jikin ki zai dauki kaya wallahi.
Ba wani buki bane akayi andai yi walima wanda yan uwana su Rukaiyya sunzo kuma sun nuna su nawa ne a gurin kuma an shirya dasu za, a tafi birni gurin kaini idan za, a tafi kaini din .
Babu abin da mama lauratu ta harta amna duk abinda akaci akasha sai da muka aika mata dashi.
Ba laifi iyayyena sun min gata duk da maigidan yace kada akawo ni da komai mata ya bukata mata kawai za, a kai mai.
Amma sai da maigari yaba da kudi akai dubula nakiya da alkaki da sauran abubuwan da ya dace aiwa amare.
Su mama laraba da ya uwata biyu sai Aisha da Fatima da wasu mata uku daga dangin su suka zo tare da kayan lefen su.
Nan guri ya cika da yan kallo ina daki na shirya cikin jan lafaya da anty taba Zarah tazo dashi cewan ta wai shi zan saka ajikina.
Kalar shi kamar ja ko purple gashi nan dai mai kyau da shi da tai makon Zarah na shirya jikina tsab.
Basu dade ba sukace a fito masu da amarya zasu tafi don kada yamma ya soma lokacin sai da akaini gidan mu nai masu sallama babana yai min nasiha sosai ma ratsa jiki tare da samin albarka ga aurena.
Muka fito muka nufi gurin maigari shida mutanen shi da matan shi suma saka saka min albarka ina kuka aka kama hanya dani zuwa sabon rayuwa agidan da na tsawon rayuwa a cikin shi.
Sai fanan tunane nakeyi yadda zamana zai kasance cikin wa yan nan mutanen masu wuyan fahinta.
Kaina naduke muna a motar dani da Attu da mama laraba dake zaune a gaba tare da driver da suka zo dashi.
Attu ta duko a hankali take ce min na fara adduan da malam ya fada min a raina hakan na soma jero adduoi a cikin zuciya na harda ma wanda malam baice ba duk na dinga yi a raina.
Nai mamakin jin cewa wai mun iso garin nan na ci gaba da jero addua gaba na sai faduwa yake faf faf faf duk na rude na rikice.
Muna shiga gidan naji daya daga cikin matan ta rangada guda irin mai sunan ruda kishiya.
Aiko haka din ne ban yi tsanmani zanga mutane ba cike a gidan sai dana gama addua na fito ne naga ko ina makil da mutane yan uwa da abokan arzikin su sun zo.
A hankali ina rike a hannun Attu da mama Altine muka fara tafiya zuwa cikin gidan.
Anty tasha kwalliya sosai tafito tare da mutanen ta sai ji nayi ta rungumay ni cikin murna da jin dadi muka kara har ciki da yake idona yana a rufe na dauka a part din anty muke.
Dakatawa mukayi daga kofan anty na fadin adakata tayi addua ta shiga da kafar dama.
Nagama ta duko a hankali ta rada min Allah ba da hassan da hussaini Nasir ya samu yan uwa.
Kuka na saka a hankali tana rike dani har zuwa uwar dakin da yake mallakina ta zaunar dani a bakin gado na zauna da bisimillah a bakina.
Gaba sai faman faduwa yakeyi abinda ban sani ba shine ashe tunda aka gyara part din sai wanan lokacin ta shigo gyaran da akaiwa part din yafi duk sauran part din dake gidan kyau tsab an kashe kudi sosai a gurin.
Take taji wani kishin hakan ya tokare ta yaya akayi besty ta farawa da iyawa yai masu haka akaina wanan ai kamar rashin adalci ne take gani.
Nan dai aka gabatar da abinci ga baki da sukai min rakiya daga kauyen inda yan uwana ne sai yan uwan mahaifina dana Innata su goma sha biyu akazo dasu.
Mamaki suke wai yau ni Rahama dake cikin su Allah ya kawo cikin wanan daulan duniya hakan.
Aka tsiyaye aka barni da yan uwana da kawaye na duk da haka fuskana yana rufe ban bude ba har lokacin.
Naji an fado min a jikina tare da rugumay ni naji yace little mum kika tafi ki kika barni why ?
Nasir ne jin muryan shi yasa na bude fuskana a hankali tare da rugumo shi a jikina.
Sai ga Amira da gudunta tafada min ajiki tana murna da farin cikin ganina rake cewa mummy tace bazaki kara wuce wa ki barmu ba wai kema yanzu kin zama matar daddy mu.
Murmushi nayi na jawota a jikina ina tambayan su kunci abinci Amira tace dani Nasir baya cin komai sai dai yasha drinks har da dukan shi mummy tayi.
Nacewa Nafisa ta debo min abinci na basu mama Altine na gefe tana kallon mu nan nafara ba yaron abinci ya ko soma ci a hankali.
Ina cikin bashi anty ta shigo dakin da kawayen ta sunzo su gannin suka samu yaran na a jikina ina basu abinci da hannuna a hankali.
Wata kecewa ji yaran nan da akayi dasu suci abinci amma sukaki yanzu gasu suna ci a nan.
Suka dan yi min nasiha suka fice daga dakin aka barni dasu Attu da mama suma nasiha dai suke min anan zasu kwana sai washe gari zasu tafi.
Bayan na bude idone nabi dakin da kallo sai lokacin na fahinci ba part din anty muke ba ke nan nima an bani nawa part din ke nan a gidan ikon Allah yau ni Rahama keda part a wanan mamakeken gidan na Daddy ke nan.
Bayan Sallah magariba sai ga mama Laraba ta shigo take cewa na shirya zamu falon maigidan dukkan mu.
Bata dade da fita ba sai ga Anty na tashigo take cewa oyya mike maza ki shirya zamu hadu a part din maigidan za, a muna magana a can.
Ita da kanta ta shiryani tsab cikin wani lafaya mai launin purple colour ta dauko turare kala kala duk ta feshe min jikina da.
Duk wanda ya ji yasan cewa ni amarya ce ga zanen lallen da akaimin ya kara haskani ga kitso da aka yarba min kanana akaina.
Bakishiya ba ko natare da kishiya ta ganni sai taji wani abu ya soke ta a ran ta balle kishiya.
Gaba daya matan gidan har maigidan duk suna falon shi a zaune tare da su mama Laraba da yan uwan ta da sukaje dauko ni kauyen mu tare zuwan mu kawai ake jira sai gamu mu mun shigo anty tana rike da hannuna fuskana yana a rufe lif kamshin turarena sai daya razana duk wani wanda ke falin lokaci sa kishiya fargaba ke nan.
Anty na kokarin zaunar dani saman kujera amma saina zamo kasa saman kafet na zauna.
Kowan su kishi ya turniketa sai kada kafa sukeyi cikin takaici da jin haushi nikan duk nasha jinin jikina a lokacin.
Ina jin mama ce ta bude taron da addua tare da soma kiran sunan maigidan sai na Saade zulfa sai hindu a karshe.
Tace to yau ga Rahama Allah ya kawo ta cikin ku a irin matsayin da kuke kuma a gidan nan watau na matar gidan itama.
Don haka kai Alhaji dakai zan soma don Allah don Allah kayi kokari ka kwatan ta adalci a tsakanin iyalin ka haka shine zai kawo maka kwanciyar hankali ga iyalin ka.
Kowan su anan zaman ka yau sukeyi babu banbanci a tsakanin su sai har idan kaine ka soma hakan .
Don haka kowa ya tsaya a matsayin shi babba ya rike girman shi karami yarike girman shi na karanta kada wata ta shiga hakkin wata a cikin ku.
Idan kunyi hakan gidan ku zai zama abin sha, awa gakowa kuma gurin zuwa ga ya uwa.
Amma idan har ba zaman lafiya kamar kullun babu wanda zaku gani yana zuwa gurin ku.
Don haka kuda yau tazo ta sama a gidan ina mai kara baku hakkuri da ku kara yin hannkuri ga yadda auren yazo a bazata gareku haka Allah ya kaddara akwai aure a tsakanin su dama haka abin yake ga Allah.
Da fatan za, a zauna lafiya cikin kwanciyan hankali batare da wani fitina ba duk amana kuke a gurin shi.
Hindatu tace Allah yasa haka mama amma ina da magana sai lokacin daddy dake zaune a falon kamar baya ciki yai magana yake cewa ki bari tagama maganan ta mana may ye na gagawa.
Tace ai ba zancen gagawa bane sai gaskiya don wallahi bazan lamunci yarinya taimin rashin kunya ba don tana takaman ita wai matar gida ne don ba kunyane fa Rahama sai in wa yarinya dukan tsiya wallahi.
Yace tunda ga yarki an kawo maki ko?
Zulfa tace kinji ko mama tun baki tashi ba dama nasan indai yaya ne ba wani adalcin da zai shuka anan tunda tun farko yana son Rahama dama.
Sai lokacin anty tai magana tace wanan kuma zargine irin naku amma babu soyayya tsakanin su a baya gaskiya kuma kun sani.
Don Allah malama ki rufe muna bakin ki munafuka kawai ai duk bakin ku daya badake aka hada baki akai muna hakan ba hallan don a tozarta mu.
May ye na tozarci a cikin kara aure ba, a kara aure ku aka auro ku kuka shigo inji anty kowa dai tashi tafisheshi kawai.
Nan fitina ya fara kowa na fadawa dan uwa bakaken magana a tsakanin su.
Hawaye ne ke zubomin daga cikin mayagin da nake rufe har kaina tun ina yi a boye har yafito fili na kasa boye kukana a gaban su ba kowa yajamin wanan zargin ba sai anty na.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, DON BA A YAFE MAKI BA , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA DON ALLAH YANA GANIN, ,
40

Duk yadda anty tayi dani wai na koma part dina na kwana ki nayi nan muka kwana nida su Nasir a dakin da muka saba kwana don sai da na bari anty ta shige na fito na dawo dakin na kwanta.
Sai washegari ta gan ni kwance a dakin ko shi cikin kargin hali ta taso gabanin asuba don ta duba lafiyan yaran ta sai kawai ta samay mu kwace tare da yaran duk sun haye min jiki muna barcin mu hankali a kwance dasu.
Muryan ta naji da asuba tana tayar dani dan sallah nai mamaki yadda yau nai barci haka har sai da aka tasheni wai kamar nai wani aiki.
Na mike zubur ina salati nace anty mun makara yau ko gashi ban hadawa babeis dina abincin makaranta ba.
Tace yanzu Rama saida kika kwanta da yaran nan don Allah ban tsaya saurarenta ba na fada ban daki kada na kara makara da sallah.
Nafito na fara gabatar da Nafila nakawo asuba nayi na dan dauki lokaci ina addua na mike na nufi kitchen.
Ranan faten doya nai masu yaji kayan lanbu sosai da drinks na zuba masu a gorunan su.
Na hadawa kowa basket din shi nai masu wanka na shirya su da sauri har na dauko hijjab zan kai su wurin mota sai nayi wani tunane naja na tsaya a sanyaye nace Gajiye don Allah zoki kai su bakin mota.
Sai bayan ta tafi ne na soma gyaran dakin naiwa dakin tsab na koma falo na gyara shi tare da saka kamshi dakin anty na shiga na fara gyara har nayi nisa ga gyara motsina ya tayar da ita.
Tace Rama may kuma kikeyi nace anty ina gyaran daki ne tace haba mana Rama kinga haka zai yuyu kuma ace kin saura gyara min daki yanzu.
Don Allah daga yau ki bari ki je ki shirya Hamza idan ya dawo kai yara zai saukeki makaranta maigidan yace bai yarda ki fita ke kadai ba don wanan mahaukancin sojan bai fita zancen ba har yanzu.
Ni kaina saida tsoro ya kamani don na tuna yadda mutanen shi suka dinga farautana a baya.
Karasa aikin nayi na wuce dakina na part din anty nai wanka na saka wasu zannuwa da riga na kawo katon hijjab dina na dora sama ban yi wani kwalliya ba irin yadda na saba yi idan zan fita.
Na dauki takarduna na nufi dakin anty nan jinior ya lake min wai zai bini da kyat anty tai mai wayo na samu na fice ina mata sai na dawo.
Ina fitowa na samu hamza ya na jira na a waje sai muka hade da hindatu ta fito a cikin shirin ta zata fita daga gidan tana ganina ta bini da harara.
Na kawar da kaina kamar ban ganta ba har ta doshi motar ta ko may ya faru kuma naji ta kwalawa Hamza driver kira ya je da saurin shi gareta cikin girmamawa.
Tace wai so take ya kaita uguwa yanzu yace cikin dan girmawa hajiya don Allah kiyi hakkuri tun jiya da dare Alhaji ya bugo min waya na kai amarya school.
Kam kazan uban nan hamza ni zance ka kaini guri kace wai Alhaji yace ka kai mai wata can wani guri ?
Ka ko san abinda kake fada min kuwa da bakin ka zakace min wai zaka kai wanan mara mutuncin wani guri ?
May kake nufi ko shi Alhajin may yake nufi ko kana nufin ta kaini matsayi ne a gidan ko ta fini ?
Ba hakana bane hajiya Alhaji ne ya bani umurnin yin hakan yanzu zan aje ta na dawo don yanzu ya kirani yana min fada wai ban kaita ba tun dazun kada ta makara.
To bazaka kai taba sai na gama lalura na ai ya saya mata mota tun tana kwartuwan shi ko ?
Hamza dai ya dukar da kai don maganan ya soma fin karfin shi don shi namiji ne ba ruwan shi da zancen kishin matan gida.
Yace hajiya sai dai kiyi hakkuri don bazan iya ketare umurnin Alhaji ba na gyara maki naki.
Ya juyo ya barta tsaye ta rusawa kowan mu zagi na fitan arziki ni dai na shiga mota yajani muka fice daga gidan.
Muna kaiwa naiwa hamza godiya na fada mai six zai dawo ya daukeni daga school din yaja mota bayan yaga shiga na aji don haka aka umurce shi dama dayi sai yaga na shiga aji ya tafi.
Na samu har an shiga aji Allah ya taimakeni ba mai tsanani bane lecturar dana samu ya barni na shiga.
Bamu samu kan mu ba sai karfe biyu muka fito don yin break da sallah lokacin ne yan course mate dina suka fara yi min murna wai ashe na yi aure shine ban gaiyace su ba ?
Murmushi mai kama da yake ne kawai nai masu muka fita da Zarah zuwa inda muka saba zama muyi breakfast da sallah.
Min dauki lokaci muna magana wanda ya shafi karatun mu tana min bayani na kuma fahinta sosai da bauanin da taimin ta miko min nawa handout din da ta saya muna da bana nan.
Bayan mun fito daga masallaci muka koma class don mu dan kara taba karatu don kada a barni baya.

********* *********
*********
Hamza na hanya yana sauri kiran maigidan ya riske shi tambayan shi yayi ya sauke ni yace eh yace babu wani matsalan komai ko ?
Yace babu shi sir sai dai an samu matsala a gida don mun fito zamu tafi hajiya Hindatu tace sai na fara kaita inda zata na fada mata zan kai amarya school amma ta dinga zagina har tana cewa sai tayi sanadin da na bar gidan nan tunda ta gane ni munafuki ne .
Don Allah sir a fada mata kaine ka sani yin hakan ba laifina bane don ina gudun kada ta jamin matsala kuma .
Hamza dani da Hindatu wake biyan ka albashi ka dani da ita, bayan kayi abinda ya dace kayi kuma zaka bata zancen.
Ina sauraren sherin da zata kullama akan hakan idan ta isa ita uwar sheri ce a gidan.
Nan ma a gida bayan mun fita hargowan Hindatu ya jawo hankalin mutanen gida Gajiye ce tafita taji abinda ke faruwa shine tq dawo tana fadawa Anty a falon ta.
Anty tace waiko matan nan suna da hankakali kuwa wanan ai sallon neman fitina ne tun ba, aje ko ina ba.
Nadawo gida a gajiye ban tsaya ko neman abinci ba na shiga na gaida anty tana min sannu da dawo wa.
Na juya zan fita tace dani dazu nake jin yadda kukayi da Hindatu da safe da zaki fita.
Nace anty ni dai idan hakan zai zama matsala ne na dinga hawa Napep na tafi ko idan za, a sauke yaran sai na shirya mu fita tare.
Tace saboda may ai ba tsoron ta aka ji ba ko wanan kuma dokane da umurni daga maigidan ai don haka ki fita batun ta ki kama harkan gaban ki don ba zaman lafiya suke so ba su idan kin biye masu kullun za, a jiku a gidan nan ne.
Tace koma side din ki ki gyara ki dan zauna don ki fara sabawa da hakan don in kina zama nan anan kike son maigidan ya dinga samun ki ?
Na turo bakina ina dan buga kafana a kasa nace haba anty wani maigida kuma zai dinga samuna kuma ?
Tace ke to may kike nufi dama wallahi ki shirya da ya dawo kasan nan amarci zaki fara cur wallahi.
Ke zo nan ma ai na manta wallahi barin kina Dr mai gyaran harka tazo ta gyara mashi ke kikoma dalleliya dake kamar ba, a taba shigsn ki ba.
Na dago kai da sauri nace wayyo ni anty don Allah dai ki bari please ni wallahi ba wanda ya taba shiga na Allah ko .
Ji wanan ko kina mantawa da Garbatin ki ne wai kina manta kin taba aure ko don kin raina da zama da tsohon ko ?
Ban son irin maganan na kwasa da sauri nafice daga dakin key na karba hannun gajiye na bude part din kafin magariba na dan share na goge ana kira na fada bandaki nai wanka nafito na tayar da sallah.
Na idar sai gasu Nasir suma wanka nai masu don suji dadin barci saboda ana zafi saboda yanayin dama da ya fara a lokacin.
Daya daga cikin kayan da Nafisa ta sayo min na saka ajiki muka fita zuwa part din anty bayan na rufo kofana.
Muna shiga muka samu anty tana zaune falo jinior yayo kaina wai na dauke shi daukan shi nayi naje nai mashi wanka.
Nashirya su tsab na debo abinci tare dasu muka zauna muka ci abinci a tare da su mukai ta shiriritan mu suna kallon mu ita da gajiye.
Kayan dake jikina take kallo ya fitar min da suran jikina tsab wani abu taji a ranta da sauri ta nemi tsarivga Allah kada ya nufeta da kishina haka.
Amma dai tasan akwai aki a kanta na dan lokaci tunda har ta fara jin yanayin kishi a kaina haka.
Mace ce Rama da duk namijin da ya samay ta zai more don akwai abubuwan more rayuwan namiji a tare da yarinyar nan wanda kaf din su babu mai ko kwatankwacin hakan daga cikin su.
Ta sani sarai idan besty ta ya gane hakan a kaina ba ita gaba dayan su sun kade wallahi don wanda ke da kamar wanan yaushe zai nemi wani abu gurin wata mace can kuma yana da wanan garshi.
Jinior ke ta kokarin wai sai yaban abinci ga baki ina ki nace anty kiwa danki magana fa zan make shi.
Sai naji shiru da sauri

Please Login or Register in order to submit comment