Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau ki daina zuwa da yaran nan gurin shi idan zaki tafi don kinga abakin shi nake jin komai fa.
Nace cikin murmushi anty abinci yake son na bashi shiyasa muka tafi tare dashi ai.
Tace to daga yau dai ki bari yaran yanzu wayon tsiya ne dasu wallahi sun san komai don ba yara bane yadda kike zato.
Remoto na dauka ina kunna tv tace dani bazakici komai ba ke nan haka zaki ta zama da yunwa ko ?
Ina ma son nai mashi magana akai maki kayan abinci a part din ki don ki dinga dafa abinda ranki ke so idan kin tashi.
Don ba zai yuyu ace sai kinzo nan ba ko yaushe cin abinci shi kan shi ai wani lokaci zaiso ace kin mai wani abu idan yana bukata.
Nace anty ba sai nazo nan nayi ba ni hakan ma yayi min wallahi tace haka nake so ban son gardama fa.
Sallaman su mama Zulaine ya katse mata magana suka shigo nan aka fara gaisawa dasu.
Mama zulai ce ke fadin munzo ne muga yar aikin hindatu don Zulfa tace muna ita ta kawo mata zobo don tasan tana so tasha da rana.
Kin ga kuma ance kwayar zubar da ciki aka bata tasha don ta rantse muna ita bata sha komai ba daga bangaren ta banda wanan zobon data sha.
Ikon Allah inji anty ita hanne din ta kawo mata zobon tasha ke nan ko ?
Mama zulai tace ai har ita wanan din ta nunani tace, tace wani abu tasha shi ya jawo mata matsalan kuma haka shima likitan ya fada muna ai.
Yanzu muna son jin ta bakin ita hanne din ne kafin mu tabbatar da hakan garesu ko ?
Anty tace amma sai nake ganin kamar wanan matsalan ta cikin gida ne don haka abari mana maigidan ya dawo sai a sanar dashi kinga ai shi zai san yadda ya bullowa al, amarin ko ?
Hakane amma ai kin san wanan kishiyar taku da shegen wayon tsiya anya zai fahinci gaskiyan maganan kuwa don tun shekaran jiya muka fada mai komai amma banga ya dauki wani mataki ba akai.
Zai dauka anty tace don munyi shigen maganan haka dashi ina ganin dai bincike yake a hankali don ya gane gaskiyan maganan.
Mama tace to Allah yasa idan har yana bincike ai mu bamu da tacewa kuma sai mu kyakeshi muga gudun shi ko ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU IDAN KUMA KIN KARANTA DAKE DA ALLAH.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKN MU AKAN KI RASHIN KARANTAWA SHINE ALHERI AGAREKI IDAN BAKI BIYA BA DON GUJEWA DAUKAN ALHAKIN WANI A KAN KI, , ,
43

Na gama kwanaki na hudu da zan yi wanda daga wanan ranan zuwa turakar maigida ya hau kaina.
Anty ce ta karbi girki bayan ni inda duk wani aikin da za, ayi na maigida nice nake aiwatar mata dashi iyakan ta ta shiga dakin da dare.
Ni kuma zaun kwana tare da yara a part dina har jinior dashi muke kwana a tare da mu.
Idan nayi sallah zan zauna na roki ubangijina Allah nakan fara gode mai da irin rayuwan dana tsinci kaina a cikin dan shi ke da masanayan yin hakan a gurin shi .
Sai kuma na roke shi da yai min kariya da tsari akan duk wani abin ki ko shedan da zaitaba lafiyan jikina da rayuwana.
Na kan zauna sosai na tsayar da duk wani abinda ke a gabana gurin rokon ubangijina akan wanan rayuwan da na riski kaina a ciki na kasancewa da mijin matar da tafi ko wace mace daraja da kima a gare ni bayan mahaifiya na.
Yau gashi na kasance da mijin ta a matsayin nima matar aure a gareshi ya Allah kada ka nufe ni da cin amanan wanan boyar taka daidai da rana daya a rayuwana.
Satin Zulfa biyu aka sallamo ta daga asibiti nan ta dawo gida ta karasa jinyan ta tana zama da mama Luba kaunan mahaifiyar su maigidan ke nan.
Da kwana biyu ya kira mu gaba dayan mu a falon inda ya zaunar damu ya fara magana kamar haka.
Ba komai yasa na kiraku ba sai maganan abinda ya faru a cikin gidan nan kan abinda ya shafi zulfa gata nan.
Wanda ba don Allah ya gyara ba da anyi sanadin fitar cikin dake jikin ta yanzu.
Kuma wanan abin ya faru ne a cikin gidan nan inda aka bata magani tasha don cikin ya zube ba tare da sanin ta ba.
A iya bincken da nayi na gano inda matsalan ya dauko asali shine daga gurin mai aikin hindatu ce hanne.
Da sauri hindatu tace hanne fa yace kwarai sai dai nayi iya binciken da zan yi nagane cewa itama a cikin rashi sani ta aiwatar da hakan don ta rantse da abinda zai kashe ta bata san ta hada wanan abin da kayan hada zobon ta ba.
Shine dalilin da yasa zan dan ragwanta mata naso na kore ta ma gaba daya a gidan amma ance na kyale ta idan halin ta ne ai zata sake wani karo.
Magana yake amma gaba daya falon ba wai mun yarda bane dole dai akwai wani abu a kasa ai sai dai halin maza baka gane gabas din su kawai.
Nan hindatu ta haufadan karya wai kazafi akai ma hanne ita dai tasan inda ta sha maganin ta kawai.
Suka fara cacan baki a tsakanin su kowa na fadawa dan uwa bakar magana ni dai ina zaune na sada kaina a kasa ina sauraren su kawai.
Muryan anty ne ke fadin tashi mu tafi Rama muna da abinyi a part din mu tana gaba ina binta a baya muka barsu nan ba musan yaya suka karasa ba.
Sai da daddy ya shigo ne naji anty na mashi magana akan hukuncin da ya yanke yake cewa da ita,
Ki sa masu ido nasan abinda nakeyi kuma akwai abinda nake son na gano ayin hakan da nayi.
Ni dai kaina a duke yake don sam idan daddy yana tare da anty ina furin balain kunyan shi nake ji.
Shima sam baya sake min fuska sai ya nuna tankar bai ma san ina gurin ba lokacin.
Har na kanyi mamakin hakan amma daga baya sai naga ai hakan ma yafi sauki da ya sake min fuska kima ya ja muna matsala ai gara hakan kawai yafi sauki.
Har girki ya dawo kaina nayi shi a dadafe ba don naso hakan ba don sam ban son zancen girki a raina.
Yai tafiya haka yasa na sake jikina naci gaba da harkokina ina zuwa school sai dai cikin katon hijjab da daddy ya sawo min har guda biyar manya har kasa.
Na dan mai da jikina ko yaushe ina manne da anty na don babu canjin fuska akaina da tai min.
Bayan sati biyu ya dawo kowa na rawan kai suna futina mu dai part din mu ba wanda ya kula da haukan su don ni haushi da mamaki ma suke bani.
Akan namiji suke wanan haukan yanzu zaka ji su anjima kuma kaga sun shirya a tsakanin su.
Ni dai na fahinci cewa ina da rauni a gurin kasan cewa dana miji don hakan da nake ba wai rashin sabo bane ko wani kawai dai hallitane min hakan.
Tun da la, asar anty tace dani naje na gyara part din daddy don nasan nice da girki ranan.
Saida gabana ya fadi haka na dauki kayan gyara na shiga part din, yadda naga an hargitsa shi ba kamar yadda na gyara ba ranan da anty zatai girkin ta.
Komai a yamutse yake ban dakin ma bai shakuwa don da gani ba a wanke shi ba.
Ai gara zulfa ace tana bedrest ne sai dai ai a nan take kwana da mijin ta, amma ita hindatu mai yaci katfin ta da bazata gyara ba.
Nan na takarkare na gyara komai na darje makewanyin don nafi jin kyamkyamin shi sosai.
Gurin ya koma neat sai kamshi ke tashi yana kyali da dadin shaka komai nayi mai muhalinshi.
Ban dade da fita ba ya shigo part din tun a falo ya fara ganin sauyi don ya shaki kamshi maidadi.
Ya sauke ajiyan zuciya a fili yana fadin Allah yai wa wanda duk yai aikin nan albarka dama da safe da kyat ya iya yin wanka a bayi don kazantan shi.
Duk, lokacin da akace girki ya dawo kaina har kuka sai danayi a daki ni kadai ganin banda niyan zuwa gun daddy da dare anty ta matsa min da na shirya dole na tafi tun takwas na dare ta gargadani zuwa gurin shi.
Da kuka na na karasa falon ba laifi nayi kwalliya na cikin material mai ruwan milk da flower ja a jikin shi.
Na dora hijjab a sama nai mata sai da safe na wuce zanin da zan kwanta da rigar barcina duk da nasan ba tasiri rigan zaiyi ba acan amma dai na dauka na tafi dashi.
Nai sallama yana zaune idon shi akan tv sai wayan da yake yi jin sallama ya sashi ya dan dago kan shi yana kallona har na karaso kusa da inda yake zaune.
Durkusawa nayi ina mashi ina wuni daddy hannu ya mika min alaman inzo inda yake.
Ban musa ba na nufi inda yake ya kamo hannu na ya zaunar dani gaf dashi hakan naji wani nauyi da kunyan shi ya kamani.
Sai da ya gama wayan shi wanda na fahinci wani harka ne na business yake magana akai.
Ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin amarya duk ni keda wanan kwalliyan haka ?
Kaina na dukar kasa don nauyi da kunyan shi da nake ji ya rufe ni amma shi ko a jikin shi hakan.
Yace sai dai kinyi mantuwa don wanan hijjab din bai dace ace kinzo min nan dashi ba don baida amfani a falon nan.
Jiki a sanyayye na kwabe hijjabin a hankali, naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin may zai sa ki boye min wanan kyakkyawan suran naki Rahama ki daina min rowan jikin ki please.
Tashi ki sauko min da abinci na nan don ni nafi son naci a kasa na saba da hakan tun ina karami a gida haka mama laraba ta koya min kin san ni zance rabin rayuwana a gunta nayi shi.
Shiyasa kike ganin ina matukar mutunta mama don duk wani tarbiyan rayuwa itace tabani shi gashi kuma ina amfana da abina a yanzu.
Na aje abincin tare da zaunawa na fara zuba mai baiyi magana ba haka yasa na dago ina tambayan ko ya isa.
Yace duk yadda kika zuba min ai cinyewa zanyi tunda shi kike bukatan naci.
Mamaki nake a raina wai ashe daddy haka yake amma idan ka gan shi a waje zaka dauka ko da matan shi bai maganan uffan dasu.
Amma ashe ba haka abin yake ba a badini sakewa yake da matan shi sosai fiye da tsanmanin mutum.
Ya fara ci inq zaune a gefe ina wasa da yan yatsun hannuwa na naji yace dama ina son magana dake.
Haka yasa na dago kaina da sauri na dan kalleshi naga abincin shi yake ci hankalin shi a kwance.
Sai da yai kamar loma biyu ne yace dama ina son tambayan ki wani sana,a baba yake yi a kauyen nan ne ?
Sai da naji gabana ya fadi to ni may zance ne yanzu sai dai na fadi abinda na sani kawai akai.
Nace ni dai na taso naga yana zuwa cin kasuwan kauye ya na samun abinda zai ciyar da iyalin shi kullun.
Yace nasan da hakan wani sana, a ne yakeyi taka maimai kike gani yake wanda ke kawo mashi kudi ?
Nace yafi sayen dabbobi yana sayarwa sai kuma sanan kayan masarufi suma yana dan tabawa wani lokaci.
Yace na dabbobin yafi aminci ai don shi sanan irin kayan abinci hanya ce wani lokaci na halaka ga bawa mutane ne basu ganewa.
Sai na tuna da wa, azin wani malami da na saurara a wayan anty kan masu tauye maauni irin azaban da Allah ya tanadarwa yin hakan.
Har yagama cin abincin shi bai kara magana ba sai ruwan da ya kara tsiyayyawa ya kora na mike na kwashe kayan na mayar part dina na rufo.
Koda na dawo yana kallon national new a wani tasha na zauna nima ina kallon abinda yake kallo ba tare dana fahinci komai ba sai naji na sake hamma.
Baiyi minti daya ba naji ya dauki remote ya kashe tv ya nufi gurin Ac din falon ya kashe har wutan dauka na yayi cak a hannaye shi sai cikin master bed room din shi.
Yana ajeni ya shiga wanka nima ban kwanta ba na dan mike tsaye na kara gyara shiri na.
Na koma na kwanta yafito yana tsaye yana shafa turare nabi fadadar bayan shi da kallo.
Har ya gama yazo gareni tankar dai ranan ya fara sani na a ya mace don sai da na raina kaina matuka a gun daddy.
Allah Allah nake gari ya waye na bar dakin don bazan iya kare jurewa ba don na kasa sabawa da matsin irin nashi haka.
Nake mamaki ko hakan ke sa anty na da duk tai girki sai jikin ta ya dan motsa mata tayi ciwo ne ?
Washe gari bai barni na fito ba wajajen tara na safe na samu fitowa daga gurin shi.
Haka ya jawo min sabon tsana daga matan shi don har anty sai da naga dan sauyi a fuskan ta dana shiga gaishe ta.
Amma bata dade ba ta sake don dana dawo tambayan ko tana da abinda za, a ai mata kafin mu dora girki take ce min cikin wasa.
Ke aikin may zaki yi ku zauna ki kula da mijin ki kibar gajiye tai muna aiki kada kuma anjima kice ke bazaki iya ba.
Kunya naji na fice daga dakin naje na dama mata kunnun magani na kuma zauna saida na fifita mata shi don yai sanyi taji dadin sha.
Tana falo zaune na tunkaro ta da magani tana gani ta bata rai tana fadin Rama yanzu baki manta da dama maganin nan ba so kike muyi fada ko ?
Nace ai newa mama alkawari zan dinga dama maki shi duk lokacin dama shi yayi da kyat na samu tasha tana bata rai ina mata sannu har ta shanye na dauki cup din na fita dashi daga falon.
Na dawo na samu daddy ya shigo suna zaune tare nai mashi sannu da dawowa.
Yace yau ina son shiga da kaunar ki gurin su Alhaji mu gaisa tun kafin nai tafiya naso mu tafi ban samu lokaci ba.
Tace hakan na dakyau ai yace daga can har gurin Abba zan shiga da ita su gaisa tace amma ba don zaku biya ta gida ba da sai ince zan je naga Abba nima.
Yace may zai hana don zamu bi ta gida ne ba zaki ba ko may tace ba hakana bane kasan yaune zaka fara shiga da Rama gurin su shiyasa bazan biku ba kawai.
Inda nake ya juyo ba wani sakin fuska a tare dashi yake ce min ki shirya karfe hudu zamu fita.
Daga haka ya fice ina mamakin shi cikin raina kamar bashi bane da safe yai ta jagwalgwalani har tsawon wani lokaci.
Sai da ya jima da fita nake cewa da anty may za, awa Abba dashi da Alhaji ?
Tace kije kiyi abinda ya dace idan kin gama ai maci ko don nasan baki wasa da alamarin Abba ai Rama nace ba dole ba anty mahaifi ba wasa ba ai.
Tai murmushin jin dadi yadda nake mata kara da mahaifin ta na mike na shiga kitchen.
Cake kamar kullun na hada masu sai miyan dana shiryawa Hajiyan daddy kafin wani lokaci komai ya dauki kamshi na sa a kula na shirya komai yadda ya dace na kuma gasa kaji nai peppeying din su.
Na idar da sallah na shirya cikin wani lace light blue mai kyau da tsada na kawo after dress fari mai duwatsu na aza sama tare da rolling din dakwalin shi a saman kaina.
Na juyo zuwa falon anty sai kamshi ke tashi a jikina takalmi masu tsini na saka a kafana.
Ban dade da zama ba ya shigo dakin shigan kananan kaya yayi kayan sun matukar karban jikin shi sajen fuskan shi da ke kara mai kyau ya kwata lub lub a fuskana shi, fuskan shi yai matukar kyaun gani.
Ya dan duka yana wasa da jinior yana cewa yaron baba ka fa isa shiga school haka na.
Anty tace daya huta da gorin Rama kullun zasu fita sai tace dashi No school bye suna mashi sheri.
Ya dan dago yana kallon inda nake yana cewa kyaleta kaji mai suna kaima zaka fara fita kamar kowa wanan school din da aka bude sabo zan kai ka.
Ban san yaya akayi ba yau nai magana sai cewa nayi daddy amma har dasu Nasir za, a mayar can ko ?
Kafin ya bani amsa anty ce tace si dai zauna inda suke don kada akai min dana shi kadai zakice wai wani Nasir can .
Nace haba anty Nasir fa soja ne ba wasa gare shi don kar ya shigo da bindiga kiji tsoro wata rana.
Sai naga ta canza fuska tace kaiyya Rama da Allah zai gwada min haka danafi kowa farin cikin ganin haka ga rayuwa na sai dai Allah kawai.
Cikin bata rai naji yace da ita zaki fara ke nan ko may ya kawo wanan irin maganan ku ba zaki daina ba ko ?
Ya juya inda nake a fusace yana cewa dani ke kin shirya mu tafi ne ?
A sanyaye nace eh sai dai bazan iya fita na bar anty na cikin wanan yanayin ba gaskiya ya juya ya bar falon da sauri tace kira gajiye ta fita maki da kayan har lokacin magana take cikin sanyin murya.
Bayan na kira gajiye maimakon na fita tunda ana jirana a waje sai na dawo na zauna a hannun kujeran da take zaune akai na dan kwanto da kaina ga jikin ta sai naji ta rugumay ni.
Cikin hawaye nace anty ban san magana na zai soshi zuciyar ki ba a wanan lokacin da ban yi shi ba wallahi .
Itama dai hawayen takeyi tace dani Rama ai fatan alheri kikai mashi nice dai nake ganin da shawan son ganin hakan a gareni amma hakan da wuya gare ni.
Anty don Allah dai ki daina fadar hakana ciwo fa ba mutuwa bane yin haka kamar shigewa Allah gabane.
Tace babu komai Rama ai na bari ku gaida su hajiya idan kunje ina gaida Abba don Allah kinji.
Ina shirin tashi daddy ya dawo falon yana cewa yaya baki fito bane kallon yanayin mu yayi kowa na sharan kwalla a fuskan shi.
Ko da muka fito mun samu Hindatu suna shan iska ita da wata kawarta sai hanne mai aikin ta dake dauke da abu zata kawo masu inda suke.
Daddy yana gaba ina nin shi a baya sai dai mutum zai dauka ko jerowa mukayi gashi nai matukar kyau damu.
Kawar Hindatu ke cewa da ita kai kai kai kardai nace wanan ce armaryan taku hindatu ?
Ta tabe bakin ta cikon dan dago kai ta dan kalle mu sai kuma ta kawar da kanta gare mu tace itace fa kinganta nan sai wani rawan kafa yake akan ta.
Wanan ai ba bakauya nace ku kuna may kuka bari ya kwaso maku wanan zankadediyar yarinyar haka a gida.
Nifa na dauka irin yan kauyen nan ne da naji kina ta wai wata yar kauye gaja da ita ashe yarinya sunan muna kauye ne kaiwa wallahi.
Wanan idan har bakiyi da gaske ba wallahi tana kwace maki miji kina ji kina gani ke ni har sai da naji wani abu fa jita fa don Allah ji yadda suka dace dashi.
Don Allah kubura ki bar maganan nan don zafi nake ji a raina na tsani naji ana koda yarinyar nan wallahi.
Har muka shiga mota maganan mu sukeyi inda daddy ya bude min gefen mai zaman banza na shiga yadawo ya bude gefen shi ya shiga yaja muka fice gidan.
Sai da muka dan yi nisa da gida har lokacin rai na a cunkushe yake min sai naga ya ciro handkici a wani guri ya miko min yace ki share fuskan ki don bazan fita dake haka ba azaci ko dole nai maki kibiyoni.
Karba nayi na dan goge fuskana ba tare da ya kalloni ba fuskan shi na a titi yace kamata yayi ace kina kara mata kwarin gwiwa ba wai kina biye mata kuna karaya ba haka.
Nace daddy ban iya ganin anty tana irin haka na jure ganin ta ban san har yau may ke damun anty ba take irin wanan kalamin haka.
Bata da lafiya ne a jikin ta shine take ganin kamar zata iya rasa rayuwan ta ta wanan sanadin ta manta da Allah shine mai kashewa da rayawa a duk lokacin da yaso.
Rahama idan zaki taimake ni kan anty ki zan fi kowa farinciki da hakan duk da dama kina yi amma zan so ki kara taimaka min gurin kawar mata da mumunan akidar yarda da tayi da maganan likitoci gurin fadakar da ita cewa shi ciwo Allah na iya kawo saukin shi idan ya tashi yin ikon shi don ba ko wani magana ne likita zai fada ya zama gaskiya ba.
Nace insha Allahu daddy zan yi yadda kace dani yace nagode da hakan .
Mun isa gidan su mun samu Alhajin shi yana gida a lokacin dama ya kwatanci hakane don mu samay shi a gida.
Suna falo zaune da hajiya da Aisha da anty kubura yar wajen mama laraba da sun zo gaida su don atare suka taso kuma ko yanzu komai a tare suke abin su.
Anty Aisha ce ta hango mu tafe tun daga nesa, tace ga yaya nan kamar da amaryan shi.
Hajiya tace hauka yake da zai kwaso wanan yar matsiyata ya kawo muna gida shi dai da yaga yana iya hada jini da jinin matsaiyata sai yaje yai tayi ai.
Ko da ta gama maganan ta a cikin kunnawan mu munji komai don muna tsakiyan falon bamu kai ga zama ba.
Alhaji karami ina kuma zaka shigo min gida da wanan yar matsiyatar mai farar kafar tsiya daga shigan ta gida har an fara neman kashe matan gida ana zuba masu guba ga abunci.
Cak naja na tsaya guri daya naji kafana bai daguwa daga inda nake tsaye a bayan shi.
Duban uwar yayi da mamaki ya kara duban ta yace haba hajiya matata ce fa kikewa wanan kalamin haka ba dadi.
Cikin matsanacin bacin rai yake mata magana tace eh nagani matarka ce kuwa yar gidan

Please Login or Register in order to submit comment