Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali ga karatunki ko ki samu ki dan diba kafin ku dawo nace da ita eh anty .
Tace don Allah ki ta hakkuri da mijin ki maza sai hakkuri balle maa yanzu da kike can ke kadai dole sai kin hada da hakkurin wani abin.
Bayan mun gama wayane na zauna ina tunanen may ke damun anty ne wai nidai in ba ciwon tane ya taso ba take boyewa ?
Fatima na kira nake tambayan ta tace lafiyan ta kalau kila dai rigimar da akayi akan yara ne nace shine har zai damay ta haka take cewa .
Mama ihisan ce ta daki Nasir wai don suyi fada da ihisan a school da suka dawo shine takama yaron ta mamare shi kuma tasa ihisan tai ta dukan shi nan dai ta labarta min irin halin da ake ciki a gidan.
Raina ya baci har nai sallah na idar raina bai daina baci ba ina zaune na kunna tv wanda kusan kallon dai kawai nake bani fahintar abinda ake a tv .
Har ya shigo banji zuwan shi yazo ta bayana tare da dan rufo min idanuwa a hankali na sauke ajiyan zuciya tare da kamo hannayen nashi ina mashi sannu da dawowa.
Nan ya zube saman kujera yana fadin wassh Allah nagaji wallahi mikewa nayi na dauko mai goran ruwa da cup na kawo mashi tare da balle marfin goran na zuba mai namika mashi ya shanye na kara mai wani ya sake shanyewa again.
Bayan naje cup din daya sha ruwan , ya mayar da kanshi bayan kujera tare da mike kafafuwan shi na duka a hankali nafara cire mai takalman kafan shi tare da cire mai safan dake saye a kafan nashi
Yace Rama idanun shi still a rufe na amsa da na,am daddy, yacce may kike tunane haka har nashigo da sallama bakijini ba ?
Kamar nace dashi gida sai dai na dake a fili nace naga yau tun safe daka fita ko waya bamuyi bane dakai.
Yace nasan zaki damu da hakan amma ba wanan bane tunanen ki fada min may kike tunane ne wai ?
Daddy babu komai na bashi amsa tare da mikewa na kwashe takalman da nufin mayarwa inda yake aje takalman shi a falon.
Ban yi aune ba naji ya jawo hannuna na fada a jikin shi ya mayar da hannayen ya rufe dani yai min zobe da hannuwan nashi.
Ya kura min ido na dan wani lokaci yace dani Rama ki fada min may ke damun ki nace ?
Maimakon nayi magana sai idona ya kawo kwalla kawai gida kike son komawa ?.
Kai na girgiza mai ban dai yi magana ba dashi yace kin gaji da nine ko nai saurin dago kai tare da kallon shi na girgiza mai kai kawai.
Yace idan ba kin gaji da zama nan dani ba akan may zaki sawa ranki damu ki shirya sai na sakaki jirgi kii koma gida .
Don ni ban gama abinda ya kawoni ba nan din, cikin daurewa nace dashi ba hakana bane wallahi wai hindatu ce ta mari Nasir akan ihisan har sai da ya kwanta ciwo.
Yace a zafafe what ?
Mari fa kika ce Rahama marin karamin yaro may ye mata haka har haka ya faru.
Nace cikin kuka wai sunyi fada da Ihisan a mota ta yaga mai note book din shi shine uwar ta mare shi har uku takuma rike shi ihisan din ta rama bugun ta son ranta.
Ita uwarshi fa tana may hakan ya faru dabata dauki mataki ba kuma bata fada min ba.
Nace daddy may kake tunanen anty zata iya yi akan hakan koda lafiya gareta balle halin da take ciki na rashin lafiya.
Nan dai na fada mai komai ranshi yai balain baci sai maimaitawa yake yana fadin mari fa abin da mamaki gaskiya.
Amma kyale su dukkan su zan dauki mataki ne a kan su ya daga waya ya kira waya bayan sun gaisa ne yake cewa da anty din yace ta bashi Amira aka mika mata wayan ta karba suka gaisa da uban yace abawa Nasir din.
Amira tace daddy Nasir baida lafiya yau two days ke nan sai aka karbe wayan a hannun ta yace da uwar mika mata waya muna magana zaki karbe wayan a hannunta?
Yaro baida lafiya baki fada min ba ta na fada min kuma ki karbe wayan gurin ta mika mata muyi magana da ita.
Zatai magana yace ba Amira wayan yanaji ana cewa yarinyar kada ki fadi wa daddy abinda ya samay shi.
Yarinyar ta karba tace daddy yace Amira na may ya samu Nasir ne baida lafiya tace maman Ihisan ce ta do sai kuma tai shiru.
Yace maman ihisan tayi mai may Amira tace daddy baida lafiya ne yace Amira bakya son na sayo maki katon teddy dakikace kina so ne tace ina so daddy.
Yace to fada min may taiwa Nasir din tace dukan shi tayi daddy ita da ihisan har bakin shi ya fashe idon shi ya kwantar da jini.
Kuma ta shure shi a ciki ya runtse idon shi yana jin zafin maganan a ran shi bai bari anty tai magana ba ya kashe wayan.
Yana mamaki ita Saade wai wani irin sanyin raine da ita haka wai da har za ai wanan aika aikan taki fada mai kuma ta hana a fada mai.
Daga haka yamike ya shige daki wanka yayi ya canza kayan jikin shi ya fito na gabatar mai da abincin shi.
Ci yake kamar bai son ci haka yasa na dan matso kusa dashi na karbi spoon din a hannun shi ina diba a hankali ina bashi har na samu ya danci sosai.
Na kwashe kayan zuwa kitchen dasu ya zauna wurin yai shiru naga ya dan shiga damu na dan daure na kawar da nawa damuwar nace dashi.
Daddy kada wanan zancen ya damay ka haka duk abinda mutum yayi don kan shi idan ta cuta mashi yau ai gobe bazata cuta mai ba.
Shi yaro an haife shi ne ba, asan mai cin amfanin shi ba watarana zata ji kunyan abinda tai mai da yardan Allah.
Ya numfasa yace ita ai bata san hakan ba da batayi ba ni bani daukan hindatu cikin masu hankali da amfani da ilimin su shi kishi haukane Rahama ?
So take tasa kiyayya a tsakanin yara na komay abinda yai Nasir shi yai ihisan ai nace hakane daddy shi zai sa ka kyale ta idan halinta ne ai zata kara.
Ya limshe idanuwan shi tare da mikewa saman kujera na karaso tare da saka kafafuwana na zauna a saman jikin shi yadda kirjina zai iya gogan jikin shi.
Ajiyan zuciya ya sauke nacs hakkuri za, ayi don kowa da halin shi ake zama dashi amma bata kyauta ba gaskiya.
Kamo hannaye na yayi yana wasa dasu guri daya yace hindatu bata san don iyayye da dubaiyya nake zaune da ita ba har yanzu.
Dadin may naji ga auren ta ba kwanciyan hankali a kaina babu ga abokan zama.
Babu gwani a gurin hindatu kanta kawai ita tasani sai yarta bata damu da damuwar kowa ba a duniya.
Ta manta da yadda aka sakani a gaba kan auren ta na daure nayi shi badon naso ba don ni a lokacin Saade ta isheni rayuwa nake gani.
Ban taba tunanen zai zo nan gaba na ci karo da wa yan nan abubuwan ba a raayuwana ya nuna kirjina da hannun shi.
Na kara manna maisu nace kafin kai gamo da wa yan nan ai kayi gamo da wasu ya jawoni jikin shi da kyau yace ummumm hakane kuma sai dai su wa yan nan na daban ne ko ?
Nan wasan ya canza sallon anan falon muka murji junan mu sai da na matar dashi komai a ranan na samu natsuwa.
Hasken safiya ya hake min idona na bude su a hankali na sauke kan daddy daya dunkule a jikina mun rufu acikin fadin zanin rufa duk jikin shi yana a kaina.
A hankali na zare jikina daga nashi na fada ban daki nai wanka saida na fito nazo na tayar dashi yai sallah ruwan dake a jikina ne.
Yasa shi bude idanuwan shi ya sauke su akaina sai kuma ya dan zabura yace what Rahama makara nayi haka yau ko nafila ban samu ba ?
Ya mike da sauri ya fada bathroom sai da ya karya ne ya shirya tsab dashi yace yau ba zan dade ba zan dawo mu shiga gari kiga gari don ki samu bakin bada labarin kasar chaina da kyau.
Yadda yace hakan yayi ya dawo muka fita tare zuwa wani unguwa mai nisa can cikin garin gidan wani abokin business din shi muka je.
Da alama su a garin ma suke zaune don har iyalinshi na garin sai dai wai mutanen kasar ghana ne su mun dan jima gidan da zamu dawo matar da mijin ta sukai min kyata na bajinta.
Ba karamin alheri na samu ba ga abokan arzikin daddy ga abinda akaje nema Allah ya bashi saa sosai an yi signing din contrac din su wanda ba karamin kudi zasu samu ba ga hakan idan sun shigo dashi Africa.
Shi da bakin shi naji suna hira da abokin shi suna cewa basu taba saan tafiya ba irin wanan karon don komai yazo masu yadda suke so don basu taba zaton hakan ba garesu.
Shirin da naga yanayi yasa nasan mun kusa dawowa gida lokacin don haka nima na dinga sayen abin bukatan da nake so acan komai zan sayo dani da anty nake sayo muna shi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANCE BATA BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH DON CIN AMANAN ZAMA TARE DAKIKAYI, , , ,
51

Abubuwan sun daure mai kai tunda yake zuwa tafiya da mace bai taba irin wanan tafiyan ba da wata irin hakan .
Zai ci ya sha yadda yake so zai samu kwanciyan hankali yadda ya dace ko ranshi ya baci da ya dawo gida zan san yadda nayi na sashi ya sake.
Haka kuma yana mamaki yadda nake sayayyan kaya haka da kudaden da nake samu a gurin abokan shi da kanzo ko mu mutafi inda suke idan zasu tafi su kan min kyauta mai matukar daraja.
Ni kuma sai nake dabaran sayen kaya ina jefa a cikin kaayan shi da ake shigo masu dashi a gida Nigeria.
Babu wani wanda ke a cikin damuwa daga cikin mu munyi kyau sosai farina ya matukar karuwa don har da dan kiba nayi .
Shima mI gidan yayi haske sosai ya kara kiba jikin shi da gashin jikin shi yai mashi lub lub lub dasu gwanin ban sha, awa.
Ashe idan yai tafiya da mace ba karamin karuwa suke samu ba ga tafiyan shi yasa suke fadan zuwa tafiya idan ba da su za, ai tafiyan ba, don ba karamin alheri suke samowa ba idan antafi dasu a hakan.
Bai kara mamakina ba sai da yabani irin kudin da yake bawa mace in zasu dawo gida nata dana sauran yan uwa tai masu tsaraban irin kayan kasan da suka tafi.
Bayan na sayi wa kowa abinda ya dace na kuma yo nawa sayayyan da yaga yawan su sai da yai mamaki sosai don babu macen da yazo da ita take sayayya haka kuma kudin suna samu amma bai sanin inda suke kai kudin su agidan.
Ba karamin sayayya nayi ba da kudin daya ban don na saro bedshet na kasan chaina masu kyau pure cotton na saro takalma da bags masu kyau da sauran kayan amfanin mata nima ina son na soma yar sana,a idan na koma gida.
Kamar yadda muka bar garin da dare haka ma mukai wa garin saukan asuba da zamu dawo.
Hamza da Bashir ne suka dauko mu dare ne kowa na barci da kyat na samu layin gajiye ta fito ta bude min kofan part din mu.
Na fito saye cikin dogon riga purple, yaddin rigan mai mugun taushi da santsi, silk ne kayan sun matukar karban jikina sosai.
A hankali nake takawa na fito daga motan bashir din ina tare dashi ya riko dayan hannu na ina rataye da handbag dina mai kyau da tsada a kafada na.
Kowa yasan da dawowan mu ranan don haka suna jin motsin bude get suka fito don taron maigidan.
Idanuwan su kar a kaina babu wacce bata razana ba da gani na gaba daya na canza masu lokaci guda.
Na koma gefe daya duk da bai saki hannu na ba a lokacin yana rike da ni still ko wace tazo ta rugumay shi.
Balaifi shima yai masu murnan ganin su nan guri yadan rude da surutu duk da dare ne Bashir yai mashi sallama ya juya zuwa gidan shi bayan ya sauke kayan da muka shigo dasu wanda kusan duk nawa ne don shi bai tafiya da kaya haka masu yawa.
Yace dasu kowa yaje ya kwanta kafin gari ya karasa wayewa don karfe hudu saura a lokacin yace zamu dan kwanta mu huta don a gajiye muke.
Basu so hakan ba sai dai babu yadda zasuyi dole suka fice suka bar mu don yaki sake ni na koma part din mu don ita antyna bata fito ba.
Basu bar juna ba sai da sukai gulma na tare hindatu tace Zulfa kinga yadda wanan yar kauyen ta koma kodai ciki ne da ita ?
Zulfa tace nima mamakin da nake ke nan gaba daya ta juye wata iri kamar yar wani da wata ?
Sukace ba dole ba Allah kadai yasan abinda sukayi haka acan hindatu tace kin san namiji muna fuki ne ai.
Bamu tashi ba sai sha dayan rana daddy ya baru na fito part din ko shi sai da naita hada shi da Allah ya bari naje naga anty don yace sai two zan fito wai ina da gajiya kafana duk sunyi wani suntum don zaman jirgi da nasha.
Nashigo part din Anty dake zaune sai ganina tayi kamar a mafalki tace wai da gaske dama kun dawo ne Rama na rugumay anty da sai kallona take cikin mamaki don gaba daya na canzawa idon ta baki daya zaka rantse da Allah kace injin aka sakani na koma haka a lokaci guda yadda na goge na waye nayi kyau sosai kamar wata yar gidan wasu masu fada aji.
Nace miss you anty na ina cewa ina yaran tace sun tafi school ai tunda safe Gajiye ke fada masu dawowan ku sukai ta ihu suna neman ki.
Na zauna ina cewa kin san daddy da son rigima ko yanzu sai da nayi da kyat yabari nazo na ganki tace shi wanan yanzu wake batun shi ai duk ya burge ne gaba daya baijin has.
Nai murmushi don na gane nufinta Fatima tazo da murnan ta muka rugumay juna cikin farin ciki.
Itama ta yi kyau da ita fes kauyancin ta duk ya goge ta zama wata babba a idona.
Na tambaye ta lafiyan jikin ta take cewa dani da sauki nan muka zauna mukai hira sosai da ita tace bari taje dakin maigida su gaisa nima na mike zuwa nawa part din don na huta.
Tana shiga falon shi taci karo da kayyan dana muka dawo dasu a falon tabi kayan da kallon mamaki haka don tasan shi ba gwanin tafiya da kaya bane amma yau gashi yazo da kayya haka duniya juyin juyi ke nan.
Yana kwance barci yake ya dunkule a guri daya kamar maijin sanyi ta dan dade tsaye a kan shi tana kallon shi ta juya zata bar dakin tunda barci yakeyi.
Taji yace Saade karaso mana na gaji da yawa ne wallahi, tai murmushi ta karasa bakin gadon da yake kwance ta samu wuri ta zauna tana fadin an dawo lafiya yace Alhamdullahi.
Yace yaya kuke da yaran ya jikin naki ya juyo yana fuskantar ta da kyau tace duk muna lafiya.
Tace ban dauka zaka dawo yanzu ba ai ko da kace a satin nan zaku shigo yai murmushi yace ba dole na dawo maki da kauna ba hankalin ta nagareki da yara sai karatun ta da ta bari.
Tace Rama ba dai rigima ba kan gashi kuma daga kai har ita tafiyan yai maku kyau sosai wallahi doon kunyi wani fresh da ku kamar ba aiki kaje yi ba ?
Yai murmushi yace kuma ga tafiya anyi nasara sosai fiye da tsanmanin mai tsanmani wallahi don bantaba samun nasara ba irin wanan.
Masha Allahu abu ko yayi kyau wallahi haka muke son ji ko yaushe Rama tai tafiya a sa,a ke nan yace gaskiya kan don ni abin ya ban mamaki wallahi.
Nan dai yai mata bayani kan irin nasaran da ya samu ga tafiyan itama tayi mamaki kwarai kuma tai murna ta mike tana cewa bari ta barshi ya huta kada ta damay shi da yawa.
Ta mike take tambayan shi abinci fa yake cewa da ita zai tashi yai wanka sai yaci.
Tana fita hindatu ta shigo itama sun gaisa take cewa ta hada mai breakfast fa.
Yace saboda may zaki hada min bayan kin san da wacce nai tafiya sai yamma zata fita girki mai dauka ya dauka.
Bataso jin haka ba don ta shirya sosai tana son ya soma cin abubuwan da ta aiwatar akan shi lokacin.
Tace ai ba don wani abu nayi ba don kawai na taimaka mata ne tunda ta dawo da gajiya ba wani abu zata iya yi ba nagani.
Yace No ki barshi ai zasu kawo min daga part din ya mike zai shiga bathroom tabishi da kallon mamaki ina mukaje muka koma hakan harshi ga shi yai wani haske da kiba ya murje yayi kyau ke nan babu abinda yaje yi sai hutawa kawai da wanan shegiyar yarinyar ai zata gane kuren ta yar iska kawai.
Idan tayi tayi idan bata yi bata yi ba don in maggi ya hau kan mage sai tarihi bar yar iska zanyi maganin ta sai dai hange ita dashi a gidan nan.
Ya fito wanka ya shirya cikin kananan kaya ai matukar kyau dashi ya samu an kawo mai abin karyawa daga wurin anty ya zauna yana ci Zulfa ta shigo dauke da yar ta a kafadan ta.
Ya mika hannu ya karbi yarinyar yana cikin mata wasa ta samu guri ta zauna tana tambayan shi yaya hanya yace Alhamdullahi.
Shigowan hindatu ne ya katse masu maganan su itakuma zulfa ta daure fuskan ta don bataso hakan ba.
Itama wuri ta samu ta zauna tana cewa tafiyan wanan karon harda tsaraba haka muka samu ya dan dago yana kai cibin ferfesu abakin shi saida ya hade yace.
Tsaraba kuma yana ina tace gasu ko dauri dauri mun gani aje can yace kayan Rahama ne ni ban ma san may ta sayo ba ciki.
Duk wanan kayan na Rahama ne haka lalai ita ina ta samu kudin sayen kaya haka kuma ?
Yace sai ki tambaye ta ai tana gidan ya mike dauke da yarinyar yana kokarin bin kofan shiga gurin mu yace da su ina zuwa.
Ina zaka da ita kuma miko min ita har ka dawo inji uwar yarinyar tace dashi yace hakan.
Yace doka zaki saka min ni da ya ta ko may Zulfa tacee ba doka bane ina dai kafakafa da abina ne ita nake gani naji dadi a raina.
Bai bata amsa ba ya fice da yarinyar ran uwar ya baci don ita dai tunda ta haifi yarta bata taba shiga da ita wani part na gidan ba sai yau zai daukan mata yarinya zuwa waani gun kuma ?
Wurin anty ya fara shiga tana falon ta zaune tana waya ta kashe wayan tana cewa yau yae rowa ce aka shigo muna da ita nan ?
Yace gata nan yau nazo da ita ashe ko rowan ake muna don ko ni yanzu saida akai min korafi ina zan tafi da ita kuma danayo nan ?
Tace mayar mata da yar ta don Allah kada kuma ace anzo da ita nai mata wani mugun abu.
Humm yace yana tambayan ina yaran basu dawo ba ke nan tace basu dawo ba ai basu san mummy su ta dawo ba ma.
Ya zauna sun danyi hira da ita yana wa yarinyar dan wasa duk da ta nuna tagaji tana son uwarta da ta saba da ita.
Ya mike yana cewa bari na leka wanan nasan tana can tana barcin gajiya tace Allah ya sa indai Rama ne kila dai wani abin take naji ta shiru.
Ya shigo muuna zaune da Fatima kallo take ita niko ina duban waya na nan Fatima ta gaida shi da dawowa ta mike ta fice falon.
Nace a, a baby kece kika girma haka namika hannuna sai ko yarinyar tazo guna na karbeta ina mata wasa.
Yace taso muje ki bani magani Rahama har yanzu jikina yaki walwale min ya juya na mike nabi bayan shi dauke da yarinyar.
Muna shiga falon uwar na ciki zaune ita da hindatu yadda ya barsu tana ganin yar ga hannuna take cewa miko min ita don Allah abinda nake gudu ke nan kabawa wata ya ta wallahi.
Ya juyo cikin mamaki yace waye watan Rahama data dauke ta ko may ni dai na mika mata yarta data lafe a jikina tace ni dai nace abani ya ta don haihuwa wuya gare shi.
Kowa ma ya haifi nashi ya dauka ban hana ba ni nawa na sani don ni na san wuyan da nasha akan abina.
Tana katban yar ta wwuce a hasale tana kallon jikin yarinyar kamar may son ganin wani abu ajikin yar nata.
Murmushi nayi ban tsaya ba nashige don na dauko maimaganin inda na aje mashi su na barshi da hindatu falon.
Na dauko ruwa a fridge na kawo mai tare da maganin batai min magana ba nima ban mata ba.
Ban fita ba don tana ciki na samu dogon kujera na zauna yake cewa kisa a kwashe kayan nan a shiga maki dasu ciki kafin a fara shigowa .
Munyi waya da Tahir yace zai sa a turo maki da sauran kayan zuwa gobe humm naji Hindatu tace cikin mamaki.
Nace wanan kayan kan ai daukan shi sai su Lawali mai wanki don yafi karfin daukan mace.
Mikewa hindatu tayi tana fadin anga banza ba dole ai cin amana a kwaso kaya haka kamar hauka ba.
Da kike kwaso naki banza ba wanda ya hanaki ai don haka dole ki bar kowa da nashi.
Ke Rahama bana son magana har yaushe kika dawo da zaki tsaya wani fitina haka ku baku raina magana.
Hindatu tace idan kin min rashin kunya ni yanzu zaki jini wallahi don ni ban daukan rashin mutunci yarinya.
In ba samun guri ba wa yaa taba tafiya dashi ya dawo da kaya haka sai kece kikafi kowa da zaki ce ba za ai maki magana ba ko may ?
Wanan kuma ai matsalar kice keda abin ya dama a rai, mace baki da aiki sai hassada da bakin ciki a rayuwan ki da kike naki sha, anin waya saka maki ido balle ke ki saka min ido haka ?


Please Login or Register in order to submit comment