Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai ya ji zuciyar sa na bugawa,bai ™ara shiga cikin tashin hankali ba sai da aka Wora masa yaran masu kama da larabawa a kan cinyarsa.

Gidan gabaki Waya sun ruWe suna ta Waukar yaran waya kamar zasu ™arar da jikin su saboda Waukar hoton,har sai da ya tsawatar da su bari sannan suka dena suna ta kallon yaran.

Hawaye yaji suna bin ™uncinsa ya kasa Waukar yaran ya na kallon su gunun sha'awa kamar ya kwace yace ™wansa ne shine ya haife su.

Ganin ya na hawaye sai dukannin su jikin su ya yi sanyi suka koma suna rarrashin sa,amma ya kasa tsaida hawayen da ke kwaranya kamar an buWe famfo.
" Zainab an ya kin yi wa rayuta adalci kuwa?"
Ya tamabayi kansa dai-dai lokacin da mahaifiyar sa ta dafa kafaWun sa ta na rarrashin sa.Bayan ya sawa yaran albarka ya fice daga gidan kai tsaye kampanin su ya wuce tare da jiran A k su haWu da shi farfajiyar kamfanin.

A.k ya sanar mishi ya na kampanin in ya iso ya kira shi kawai,amma sai A.m ya nuna ya fito kawai ya jira shi saboda yanayin da yake ba zai iya ™ara kiran waya ba.

Ya na isowa ya same shi tsaye da waya a hannun sa da alama waya yake sai kuma ganin shi ya sa ya kashe wayar,tare da maida ta cikin gabar rigar sa ya ™arasa gurin da A.m ya yi parking Win motar sa.

Ina ga muje farfajiyar da Daddy yake hutawa abin zai fi ko a bisa mu yi magana don nima ina da maganar da nake son mu tautauna akai."A.k yace da shi bayan ya nufi hanyar gurin ba tare da ya ji amsar da ya ba shi ba.

Ganin haka sai shi ma ya bi bayan sa ba tare da yace komai ba.Bayan sun zauna shirun na su na ´an mintoci ya biyo baya wanda sai da nabi dindigi na gano dalilin shirun na su a duk lokacin da suka haWu kafin su fara maganar da ta kawo su,wanda suna yi ne don su sami natsuwa tare da nazarin maganar da zasu tautauna a tsakanin su.

A.k ya buWe baki da nufin zai fara magana amma sai A.m ya hana shi ta hanyar taran numfashin sa tare da gyara zama yace."Abokina ka fara bani dama na yi magana domin na samo mafita a kan damuwata,na yi tunani sosai kan maganar da muka yi da kai na Juwairaah.Tabbas yarinyar ta kwanta min a rai kuma na yaba da hankalin ta amma saboda al™awarin da na yi wa Zainab,kuma ita kaWai nake son takasance matata zan auri Juwairaah mu yi auren
kwangila da ita shekara Waya,kamar yadda ka bani labarin ™anin mahaifinta ni kuma zan siya shi da ruwan kuWi ya fasa auren da zai yi mata da wannan tsohon."

Ya numfasa ya na kallon sa ko zai fahimci yadda ya karSi zancen,amma sa ya ga ya na mishi kallo kamar irin amma ka zare ko!

Bai damu ba ya ™aWa kansa yaci gaba da cewa."Tunna ka gaya min ta yawon aikatau sai mu Wauketa akan za ta koya wa matata girki da kula na tsawon shekara guda,kaga a wannan lakacin in ta samu ciki zan Wauke ta daga gidan na kai ta wani guri,na san yadda zan tsara Zainab ta amince ta karSi Wan burina na ga Wana kafin na mutu.

"Amma baka da hankali ko na Wauka alkhairi ya sa ka kira ni nan,ashe ka je ka bugu ne ka zo ka Sata min lokaci."A.k yace tare da mi™ewa yayin kamar zai fice daga gurin bayan ya mi™e sai ya dawo ya ™ara zama ya na kallon sa yace." Aikin banza kawai na Wauka auren ta za ka yi na Sata lokaci na gurin sanin tarihin rayuwarta! Abin takaici sai ga shi kazo ka na min maganar banza. Shin baka da zuciya ne a ™irjinka har ka kasa tausayawa rayuwarta na halin ™uncin rayuwar da take ciki? Ko ™yamar talaka da kake yi ne ya sa kake son ka cutar da zuciyar ta.

Ya ™ara mi™ewa don ji yake kamar ze rufe shi da duka ya na jin zai iya gaya mishi duk maganar da ta zo bakinsa,saboda tun jiya da ya ji halin da take ciki Allah ya saka mata tsananin tausayinta a ranta.

A.m hannun sa ya kama shi ma sai hawaye ya na faWin." A tsakanina da ita waye yafi kusanci da kai ina cikin wani hali bani da nufin na cutar da Juwairaah wallahi tsananin son ganin Wana ya sa nake jin zan iya komai.In har ka amince ka bani goyan baya mukai auren sirri da ita na yi maka al™awari rayuwar Juwairaah sai ya canza daga talauci zuwa mafi ™ololuwar jin daWi na rayuwa.Kuma ko banza aurena zai zamo katanga a tsakanin da tsohon mutumim nan,™anin mahaifinta da yake takurawa rayuwarta duk haWuwana da ita zai saka ya dena saka mata ™ahon zu™a."


" Rufe min baki nace! Shashasha!Kawai ka san yadda zuciyar mace take da rauni kan soyayya.Kai fa namiji ne da ko wace mace za ta yi mafarkin samu,ka na tunanin in ka auri Juwairiya za ta iya ha™uri da rashin ka ne,a kan maganar soyayya kuWi ba ya tasiri mace za ta iya baka rayuwarta kuma ta sadaukar da rayuwarta duka gabaki Waya in har ta na sonka,ba za ta taSa damuwa da halin rashi ko ba™in cikin da za ka saka taSa."


Ya saukar da zazzafan huci ya ja numfashi sannan ya kalle shi da idanunsa da suka kaWa suka yi jajur." Ina tunanin yaudarar Zainab kake da kake faWin ka na sonta don da ka san yadda soyayya take tasiri da baka bu™aci auren Juwairiya na wucin gadi ba, don na tabbata kafin ku rabu sai Juwairiya ta faWa kogin son ka koda yankan namar jikinta kake yi Wanye,bare kuma za ka raba ta da abu mafi girma a rayuwarta kawai za ka rabu da gangar jikinta ne amma zuciyar da da ruhinta duk za ka raba ta da shi.Ba ka san yadda uwa take zama akan yaron ta ba,saboda ba ka haihu ba shi ya sa baka san soyayyar da Allah ya saka tsakanin Wa da mahaifi b..."

"Ya ishe ka! Rufe min baki nace banza mara mutunci! Har ni za ka yi ma gorin haihuwa na rantse tunna ka yi min gori sai na aureta kuma na raba ta da yaran na kai ma matata,na yi al™awarin sai kaga ™waina a duniya."

Ya matso tare da taSa ™irjin shi da Wan yatsa yace." Saboda nace zan aure ta ka wani tada jijiyar wuya'duk na gane kauce-kaucen ka don ta na talaka ba ka son na aureta.To siyan ta zan yi da kuWina kai ma ka san in ka yi tunanin zan aure ta na yi rayuwar har abada ka yaudari kan ka, me zan yi da ´ar talaka wanda basu da komai sai tsiya,kuma ka sani ko ban aure ta ba ina da kuWin da inna ce zan auri ´an mata waWanda suka fi ta kyawu da Waukaka zan iya auren goma in ana yi."


"To kaje ka auri ´an matan duniya duka in kana son Wan ™aruna amma ba zan haWa hannu da kai na saka rayuwar ta a cikin matsala."

Ya faWa tare da ™o™arin barin gurin rigar sa ya jawo ya juyo da shi gaban sa ." Ko ka sa min hannu ko ka ™i sai na aure ta ita kaWai ce na ji zan iya rayuwar aure da ita ba yan masoyiyata Zainab,don haka in dai kuWi na aiki ka ba ni sati biyu za ka gan ta a gidana kuma a matsayin me aikin matata za ta shigo gidan."

Ran sa ya ™ara Saci da ya tuna ya sha zuwa gidan ya ga Zainab ta daki me aiki,hakan ya na nufin in ranta ya Sace za ta dake ta kenan aiko in dai haka ne a kwai zalinci.

" Ai kin banza kawai sai dai in zaka Wauki numfashina ma'ana ba ni a raye,amma ni da kai na zan tona asirin ka kuma na ga uban da zai karSar maka auren tunna ba ´ar tsana ba ce,sai da waliyin ka za'a baka.Yace a fusace.

" Ok haka kace ko zan nuna maka true color Wina dama duk abin da aka haWa da jaki sai ya ci kara,ka haWa hulWa da talaka matsiyaci da be da komai sai tsiya na yi dana sanin tarayyata da kai don bi amfana min komai ba,duk halaccin dana yi maka ni da dangina muka ´anta rayuwarka shi ne zaka saka min da haka!"


To fa ran A.k ya Sace matu™a kawai sai hawaye ya kalli A.m da yake ta ga ya mishi maganganu mara sa daWi da ba™an ta rai,don shi in dai ran shi ya Sace bai iya magana ba."

" A she haka kake dama na daWe ina tunanin wannan ranar za ta zo,saboda a gaba na kasha wula™anta talawa irin na na gode in sha Allahu daga yau ba ni bakai,ba zan ™ara hulWa da kai ba kuma na bar muku aikin ku ka sana ni ba jahili ba ne ko yau na yanke ala™a da ku sai kun yi jimamin rashina."Yace ya na me tabbatar da hakan a ran sa.


Kai Win me kai Win banza me kake da shi kaje a kwai waWanda suka fika ilmi da zasu bu™aci gurbin ka.".
Lamarin fa ya yi tsamari gabaki Wayan su kowa ya hau dokin zuciya duk da zo mu saSa zo mu zauna,amma ba su taSa samun saSani irin na yau ba.

Ko da A.k ya nufi hanyar fita A.m jawo kwalar rigar sa ya yi tare da dawo da shi ya hau shi,da dambe don gani yake ya ma rai na mishi wayo ya na karkashin sa,sai ya manta abokantakar su ya dawo kan matsayi.

Aiko A.k a zuciye ya kai mishi mari ya kauce shi ma ya kai mishi suka rikice da dambe kici-kici.Me ba ma fulawa ruwa ya zo ya gan su da gudu ya ruga ya yi kiran mutane,su raba don ba zai yi gigin shiga tsakiyar su ba su bar shi da jinya yadda suke ji da karfi.

Da ™yar mutane suka raba su sai huci suke tamkar wasu zakuna.Faruwar lamarin sai ya yi matu™ar bawa mutane mamaki,tuna yadda suka sha™u kamar wasu ´an'uwa suna ta jimamin lamarin me ya haWu ko ma dai mene ne lamarin me girma ne,amma da suka tuna tsakanin harshe da ha™ori ana saSawa sai suka ba su ha™uri tare da Wauko musu ruwan sanyi,domin ya sanyaya zu™atan su saboda sheWan da ya yi nasara haddasa fitina a tsakani aminnan ko nace ´an'uwa.


A.k da ran sa ya Sace ko jiran wanda ya nufi zuwa cikin kampanin ya Wauko musu ruwa bai yi ba ya fice ya na jin a ran sa ya tafi na har abada.

Ko da a ka Salle murfin gorar ruwa aka zuba mishi ruwan wurgi ya yi da kofin tangaras Win ya nufi motar sa,ya shige tare da figar ta kamar zai tashi sama.


Ko da ya iso kofar gidan ya shiga sakin hon ba ™au™autawa.Allah Sarki Audi direba dake cikin bayi da cikin sa ya murWa ya shiga kenan ya ji hon wanda ya tabbata matar gidan ne me shegen yawon tsiya,amma da ya tuna ya ga ta fito Wazu sai ya yi maza ya fito ba tare da ya gama abin da yake ba sai dai hon Win da ake saki na rashin hankali.

Ya na wangale get Win sai yaga megidan sa ne yake ta zuba wannan hon,hankalin sa ya tashi kwarai don a tunanin sa ba lafiya ba.

Ya na shiga ko parking bai yi ba ya fito ya ™arasa gurin Audi direba dake mishi sannu ya na son ya kulle get Win ya ruga bayi,don har lokacin cikin sa bai dai na murWawa ba.

Mari ya zabga mishi." Kai wane irin banza ne matsiyaci kawai gidan ubanka ne da zan Wauki lokaci ina hon baka amsa min ba? Ko kuWin da nake biyan ka da shi ha™o su nake!"


"Allah ya baka ha™uri ina bayi ne cikina ya lalace."


Bai saurare shi ba ya shige cikin gidan falo ya shiga gibbiyar ta na kwance a doguwar kujera me cin mutum uku da remote a hannunta ta na kallo.


Ba tare da kallon in da take ba ya shige cikin Wakinsa ruwa me sanyi ya dinga kwankwaWa har sai da ya cika cikin sa,amma bai ji zuciyar sa ta dai na tafarfasa ba don ji yake kamar za ta fito.


Ya yi cilli da robar ruwan dai-dai lokacin da ta shigo ta na mishi kallon ko ya taSu ne? Tsaki ta yi kawai ta fice ta san in ta tambaye shi zai iya gaya mata ba™a ita kuma sai ta rama,don haka ba ta tanka mishi ba ta Wauki wayar ta dake kan gado ta fice a ran ta ta na faWin." To wa kuma ya taSo wannan kububuwan?Ba zan yi mishi magana ba ya ™are a kaina bari na bari ya huce."Ta koma ta yi kwanciyar ta ta na kallo.


Tofa masu karatu kun dai jin yadda ta kaya game da waWannan aminan juna.Ku ci gaba da bibiyata na gode da yaba lintafina da kuke.

ŠUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ŠIN KU YA NA SAKA NI NISHAŠI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi noma sha uku.Ga masu bu™atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ™ofa a buWe take na ™orafi gyara ko ™arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za™auran marubuciya,kuma ™awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ™ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 13*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


A.k ya na tuki ya na jin zuciyar sa na wani irin tafasa sai dukan sitiyarin yake ya na tsaki ji yake kamar ya je ya sha™e shi,ya na ji a ran sa ba zai ™ara hulWa da shi ba don ya tabbata ba shi da mutunci kuma yau zai mayar mishi da motar da ya siya musu a tare da suka je Dubai.


Da sauri ya taka burki ganin ya na son ya buge wani yaro dake sai da rake a tire,ya yi ™o™arin janyo natsuwa don ya samu ya isa gida lafiya saboda da ™yar yake gani.

Matarsa na zaune ita da yaranta suna assigment sai ganin sa ta yi ya shigo kamar an jeho shi,bai amsa sannu da zuwa da suke mishi ba ya shige Wakinsa wanda ya Waga hankalin ta ta mi™e ba shiri ta bi bayan sa.


Ganin yadda ya haWe kai da gwiwa ta Wauka rasuwa a kai don haka jikinta a mace ta ™arasa gun sa tare da dafa shi.

" Lafiya Baban Najwa in ce ba wani abu mummuna ya faru ba?"


Ta faWa cikin tsoro ganin yadda idanun sa suka canza sannan ta ™ara cewa." Ka yi ha™uri dama haka duniya take ni dai fatana ba mutuwa akai ba,ko wani mummunan lamari ya faru! Don Allah ka yi magana."
Bai amsa mata ko Waya ba ya Wauki ruwa ya na sha.Ganin haka sai ta janyo jikinta bayan ta ™ara A.c Wakin ta janyo mishi kofa a ran ta ta na addu'ar Allah ya sa lafiya.


Kimanin rabin awa ya Wauka a cikin Wakin sannan ya yi wanka ya fito da duguwar farar jallabiya a jikin sa,gefen ta ya samu guri ya zauna ya na kallon ta da Wan murmushi a fuskarsa.

Sai hakan ya sanyaya zuciyarta da take ta bugawa ta na tunanin ko wani abu me girma ne ya faru.

Ido ya zura mata bai ce mata komai ba hannunsa ta kama tare da Wora kanta a kafaWan sa." Zuciyata ta ku san bugawa da na ga ka shigo a cikin wannan halin."

Shafa gashin kan ta ya yi yace a hankali da muryar da har yanzu a kwai Wan Sacin rai a cikin ta." Mun yi faWa ne da A.m kuma me zafi don har na bar mishi aikin sa,zan kuma mayar mishi da duk wani abu da ya mallaka min."

Ya faWa ya na furzar da wani irin huci mai zafin gaske.

Kallon sa take da irin ba za ku taSa canzawa ba duk cewar ta san suna faWa amma wannan karan da alamar faWan ya yi tsamari ganin yadda ransa ya Sace.

" Me kuma ya ™ara haWa ku?"

Mi™ewa ya yi ya Wauki wayar sa zai koma Waki jin tambayar da ta yi mishi wanda ya Waukar ma kan sa wargaza shirin,amma kuma bai gaya mata ba sai yace." Wanann kuma sirri ne a tsakaninmu."

Ya ™arashe shigewa bayan ya ri™e hannun Farha dake ta nacin ya Wauke ta tun da ya fito daga Waki,ya bar ta a tsaye ta na jinjina wane irin rikicine ya faru a tsakanin su har ya yanke barin aikin.

" Ko ma mene ne su suka sani haba! Suna girma suna cin ™asa." Tace cike da takaicin halin su sai kuma ta yanke shawarar ta kira Zainab ta tambaye ta sai da wayar ta yi ringin sau ku,sannan ta Wauka tare da sakin wawan ajiyar zuciya.

" Hello sahiba ki yi ha™uri ina falo na bar wayar a cikin na manta da ita,sai da Atine me aiki ta kawo min.Ina yarana?"

Ajiyar zuciya ta yi tace " Ba komai wallahi suna lafiya dama na kira ki na tambaye ki ko A.m ya na nan,na ga aminin na sa ya shigo kamar sun sami saSani hankalina a tashe yake."


Tsaki ta yi ta taSe baki." Humh ke kika kula shi ni nawa da ya shigo ko kallon sa ban yi ba,na kyale shi don ba na son ya haWa min zafi saboda ni ma a cike na ke da wata da ta yi min rashin mutunci a tiktok."Ta ba ta amsa ta yamutsa fuska.


"Zainab!Wai ke ba zaki dai na yin rawa a tiktok ba! A da baki aure amma yanzu ke matar aure ce hakan bai dace dake ba,kin ci sa'a shi A.m sam ba ya yin tiktok amma in Allah ya so ya kama ki sai kiga wani ya tura mishi kuma ba zai ji daWi ba."

" Umh ke ni kyale ni lokacina ne kin san iya yawan adadin mutanen da suke bibiyata,so kike na yi asaran mutanen da suke zuzuta kyawuna?Ai in kika ga na dai na ™ila na mutu ne."


" To Allah ya shirye ki da masu hali irin naki a matsayin ki na matar aure ji je kina bayyana surar ki Wora wa™a ki nabi don kawai ki yi suna ko burge mutane,ba yan kin san haramun ne a addini kuma bayan haka malamin ahalari yace.Wal mar'atu kulliha aurati ma adal wajha wal kaffaini.Wato ita mace dukkannin ta al'aura ce sai dai fuska da tafukan hannaye. Gaskiya ya..."


" Wash Allah na! Wallahi Maman Najwa kin cika cika mutum wannan dalilin ya sa ban cika zuwa gidan ki ba.Ke kullum sai kin yi ma mutum wa'azi,ke da uztazi kika aura sai kin addabi mutum da wa'azi ina ga ko sallah mutum ya yi zaki ce ba dai-dai bane." Ta Wan numfasa ko za ta ce wani abu sai ta Wora da cewa jin ta yi shiru ajiyar zuciya ta sauke.

"In kin kira ni ne ki yi min wa'azi ba ni da bu™ata matar liman sai kije masallaci ko in da ake bu™ata.Ni ya maganar mu na fara yin sana'ar zuwa waje kin yi mishi bayani."Ta canza maganar don ta gundire ta ita ba ta da wani aki sai na yin wa'azi ita kam ba za ta iya ba,ita dai da ta ga za ta iya kashe rayuwar ta da kuruciyar ta sai ta yi Allah ya ba ta sa'a.


Dariya ta yi jin ta canza maganar tace." Na gaya miki tun ranar ni ba zai barni na fita zuwa wata ™asa saro kaya ba,gara mu dinga basu kuWin ko mu yi oder kin san yanzu komai a sau™a™e yake."

"TaS kin yi makaranta amma kamar baki waye ba ok da ma kina jira ya amince miki ne? Dama ba sana'ar kike so ki fara ba,ai koni da kika ji nace zan yi ba zan gaya mishi ba,sai ya ji na fara ke ranar da na Wan sako mishi maganar Yayyina suna zuwa waje yin business,bai kalle ni ba yace ai da yake mazan na su mahaukata ne basu san mahimancin iyali ba.Shiru na yi bance komai ba ai sai dai ya ga na Waware inna dawo koma me zai faru ya faru Am ready for the conseqeuncy."


A ranta ta na girmama irin halin Zainab wacce sab ba ta tsoron miji ga shi Allah ya yi mijinta da son girma,sai dai bai samu macen da za ta ba shi wannan girma ba aiko za'a sha daru don shi ma ba daga baya ba.

" To shike nan Allah ya sa ki gane ni dai ba zan baki kuWina ba kar mijin ki ya ji na baki,ni ina daraja aurena ke na lalata miki na ki gara na ba shi ya yi min oder hankalina kwance,sannan ki je ki rarrashe shi ki ji abin da ya haWa su ko ma bai gaya miki ba don Allah ki ba shi kula kina sakaci da mijinki fa kar wata ta yi miki kwace."



Ta faWa da tsigar tsokana duk da ta san Zainab yanzu za ta harzu™o mata da shegen ba™in kishinta amma ta kasa kula da shi.


" Kinga ni ko zamu fara Allah babu wata matsiyaciyar mace da za ta shigo min gida,na kuma riga na gaya miki in ta yi wannan kuskuren to ta tabbata ni ce ajalin ta.Kuma hankalina kwance yake ya yi min al™awari,wace mace za ta aure shi baya haihuwa ko ni ha™uri nake."



FaWin likita ba Allah bane Zainab in Allah ya so sai ya haihu domin ubangiji yudabbirul amri ne ya na jujjuya lamaruran sa,don haka ban ji daWin abin da kika faWi haka kuma kinga ya na iyakan ™o™arin sa.


Zainab sai ta ji wani iri a ranta ta na fatan hakan don yanzu yadda A.m yake son ya haihu har yake zubar da hawaye ta na son ko Waya ne ta haifa mishi ita fa ba ta son tara yara.
" Ina fatan haka Allah ya amshi addu'armu sannan da kike cewa na je na rarrashe shi Allah ya sauwa™e haka kawai kema kin faWa min don ki tsokane ni ne ko?A kan maganar fita waje ai dama ban miki dole ba.Ni na gaji da wayar nan don takaici kike ™ara min zan shigo gidan ki kawai mu tautauna ki gashe min da yara."


Ta maza ta datse wayar ta na ba™in cikin halin da ™awarta ta Waukar ma kanta saboda ta yi aure sai ta hana ci gaba a rayuwar ta?Tsaki ta yi ta Wauki wayarta ta ta shige Waki zuwa can ta fito ta ci ado kamar wacce za ta gasar kyau,ta Wauki key Win motarta da wayarta ta fice ta na ba za ™amshi mai sanyaya zuciyar duk wanda ya yi katarin sha™ar shi.

A.m ri™e da waya a hannunsa a cikin haWaWWen ofishin sa sai ya duba numbar A.k da nufin ya kira sai kuma ya yi cilli da wayar a kan duguwar kujerar da ke cikin ofishin.


Ya yi haka yafi sau a ™irga gabaki Waya abubuwa sun rikice mishi a kampanin wanda har Daddy ya fara ™orafi,ya sani A k wani jigo ne a cikin kampanin amma ransa ya Sace ya je ya gaya mishi maganganu mara sa daWi ga shi tun ba'a je ko ina ba ya fara dana sani.


" An ya Juwairaah auren ki alkhairi ne?"Ya faWa da

Please Login or Register in order to submit comment