Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar ni don Allah na tafi."

Kallon ta ta yi tana dariya ta ara cewa." To mara aji matar mahaukaci, ya ce na tura masa da adireshin gidan, sai ki kwantar da hankali don na fiki murnar tafiyar ki ko banza yau zan yi bacci lafiya, ba tare da na yi rarrashin kukan da ake min duk dare ba.In kun so sai ku kashe kanku munafukai kawai."Wani irin daWi ya lulluSe jin zai zo duk da tana tsoron haWuwar su amma idanuwanta suna aiayin son ganin sa.Yana isowa hon ya shiga yi ba aautawa.

Da gudu ta ruga har tana bige afa da ofa amma bata kula ba,ko sallama ba ta yi mata ba sai hannun da ta Waga mata.

Duk da bugun da zuciyarta take mata amma gaka nan ta yi shahada ta shiga suka zuba ma junan su ido.
A.m da yazo da fushi duk sai ya nemi fushin ya rasa musamman da ya ga ta rame kamar wacce ta yi ciwon shekara.

Kau da kan sa ya yi ga barin kallon ta ya Wauki biro ya saka a tsakanin yan yatsun ta ya matse da arfi har sai da ta yi ar ara saboda zaba.

" Kin san irin girman laifin da kima yi mini?Kin Sata mini rai warai kuma saina miki horo mai tsanani,na rantse kika ara gigin ara zubar min da ciki saina illata ki sannan jikina ba zai yi wahala ba sai kin mayar da abinnda kika zubar.
aryar iskanci kike ba ki san waye ni ba muje gidan za ki ga abin da zai faru dake."

Tsananin tsoro ya cika mata zuciya ganin irin muguntar da ya yi masa,sai ta ji tsoron kar yazo ba kowa a gidan ya kashe ta a banza,saboda har yau tana tuna irin shaar da ya yi mata.

Ganin fuskar sa babu fara'a hankalinta ya ara tashi.
" Ka yi hauri na gane kuskure na insha Allahu ba zan ara ba kuma na yi hakan ne..."

" Ban tambaye ki dogon surutu ba in har kina son na yi hauri to ki oarta ki mayar da abin da kika yi mini asarar shi a yau."

Ya faWa ba tare da ya kalle ta ba hankalin sa na kan tuin da yake yi.

Yanayin yadda ya ya nuna mata hankalinta ya Wan kwanta,domin ta yi tunanin fuskantar haka daga gare sa,ta Wauka dukan mutuwa zai yi mata kuma ya kore ta.

Tun da ya faWi wannan maganar bai ara cewa uffan fa har suka iso gida lokacin a na kiran sallar isha'i,don haka parking kawai ya yi ya fice masallaci.
Ajiyar zuciya ta saki mai arfi tana are ma gidan kallo wanda rabon ta da wata biyu kenan

Da ta tuna Zainab sai da gabanta ya faWi ras! Duk da ta san ba ta gidan shi ya sa ya je ya Wauko ta,a ranta take tunanin ko ta yi tafiya zuwa waje.

Bayan ya shigo tana zaune a falon gidan sai are wa falon kallo take saboda ganin ya canza,kallonta ya yi sai kuma ya Wauke kan sa zai haye sama.

Da sauri ta rie hannun shi." Don Allah ka yi hauri ka yafe min wallahi na tuba kuma na yi nadama."

Hararar ta ya yi tare da galla mata tsaki ya janye hannun sa sai kawai ta faWa jikinsa tana kuka sosai.

" Ke fa matsala ce ta ko ina bayan asarar da kika yi min kukan banza za ki rarrashe ni da shi ko?Kawai zan haura ne in har kin yi alawarin yau za ki mayar min da asarar da kika yi min."Ya faWa cikin wata irin murya.

ago kanta ta yi tana share hawaye ta kalle shi sai kuma kunyar abin da ya faWi ya sa ta sunne kanta tana murmushi.

" Yunwa nake ji warai kin korar min matar so,sai ki maye makwafin ta kafin ta gama hutun ta dawo,sai ki yi oarin mai da asarar da kika yi mini don ba zan wahalar da kaina ba.

Da sauri ta tashi ta walalo masa ido tana dariya sai kuma ta nufi kicin,wanda dama kafin ta yi alwala sai da ta Wora masa abu mai saui wanda zai ci,don ita yau murna ba zai barta ta ci komai ba.

Mamaki ta yi da ta ga ya biyota kicin Win duk da orafin abin da ta yi masa yake yi,da kuma yi mata gargaWin kar ta ara sai ta ji sanyi sosai a ranta ,saboda yana da saurin fushi zai kuma iya yanke komai ba tare da tunani ba,amma kuma yana da saurin sauka.

Ba aramin mamaki ta yi ba da ya nuna mata shifa da gaske ita za ta mai da asarar da ta yi masa

Hakan ya sa ta dage sosai don ta faranta masa saboda ya manta komai.Daga arshe da kan sa ya karSi jagoranci komai,saboda bai san ya yi missing Winta alot haka,a haka bacci ya yi ya kasheta da aunar sa da take sakata hauka a kan sa,sai ya fake da duk a cikin horo yake mata wanda so yake ya maida asarar da ta yi masa.

Sai da suka makara sallar asuba ita ce ta farka ta zare jikinta sannan ta tashe ki,kan dole a gida ya yi sallah,ya kuma sawa suka koma bacci.

Ba su tashi ba sai misalin sha biyu na rana kiran wayar da A.k yake yi ya tashe shi.

Tsaki ya saki zai kashe wayar sai dai da sauri ya mie ganin kira rututu a wayarsa,da ya kalli agogo salati ya fara yana Wan buga bayanta ganin sha biyu har ta gota.

Mie wa ta yi ita dama tuni ta farka ba ta so ta farkar da shi ne,ya sa ta ci gaba da kwanciya amma yunwa take ji matua.

" Hello hala yau mutuwa ka yi ne ana ta kiran waya ka san muna da bai sai ka zo ka buWe mini falon ka ina waje bai na ta jira.

Da sauri A.m ya sauka asa shaf ya manta da client din sa da za su zo yau yana faWin." Ki sauko ki bani abinci mai saui fita zan yi."

A.k ya dogare a bakin ofa yana kallon sa ganin sa da kayan bacci." Wai hala rashin matan na ka ya sa ka fara shaye-shaye ne? Haba bacci har sha biyu da an mintina sai ka ce wanda ya yi sabon aure.

Shafa kansa ya yi ya ce." Kai fa banza ne bari na watsa ruwa mu tafi."

Yana oarin hawa Juwairiya ta fito da nufin ta shiga kicin ta Wora girki kanta a sunkuye ta gaishe da A.k da ya yi tsaye yana kallon Am da yake shafa kansa.

" Kai amma ka ci uwar Wan rainin wayo ka bar ni ina can ina ta neman ta,Baba Sani ya tasa ni a gaba ashe kana nan ka na cin amarci har da makara."
Tsaki ya yi ya harare shi daidai lokacin da ta shige kicin ya sausauta murya ya ce."Nima ganinta na yi ta dawo."

Ya na taSe baki ya yi maganar ya Wauki remote ya kunna tv bari na yi sauri na watsa ruwa ka rage zama.
" Allah ya yi munafuki anan ka yi sauri ka fito kai ka sani da gulmarka."
Dariya ya yi ya bugi bayansa." Da babu ai gara ba daWi."Ya ce tare da haye wa sama.

Kusan sati biyu tun da Zainab ta tafi Lantana ba ta zoba,sakamakon yarta da take aure ta haihu an yi mata aiki ta tafi jinya.Hakan ya ba su damar sakewa suna jutawar su.
Kullum ranar duniya sai A.m ya kira Zainab amma ba za ta Waga ba, kuma yana ta biko gurin iyayenta,sai wulaanci suke masa daga arshe mahaifinta da kan sa ya kira Daddy A.m a kan ya daina zuwa gidan shi Zainab sai ta huta za ta dawo.Da zarar ta dawo za ta dawo Wakinta don haka ya daina damunsa.

A.m ya yi fushi sosai sai ya yi zuciya ya yaleta musamman da ga matar wucin gadi,ta dage tana faranta masa ko ba komai zai yi maleji kafin ta dawo.

Juwairiya ta yi amfani da wannan damar ta saka rayuwarta a cikin ta A.m duk da irin gwasaleta da yake yi, yana yabon Zainab amma da ya fita zai kira ta yana gaya mata ya yi missing hawayenta na banza don Allah ta yi mishi kukan zai siya.

In ya faWi haka dariya take mishi ta ce ashe kukan banza ya ara matsayi tun da har siye ake son ayi.Haka dai suke zaman su cikin girmama juna da kulawa.

Washegari Zain 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ab ta kira lantana aka ta je ta gyara mata gidan ta,saboda tun da ta tafi kewar sa ya dame ta ko bacci kasa yi take yi,duk kiran da yake mata rungume wayar take yi tana kuka,amma shegen girman kai ya hana ta Waukar wayar in ta tuna kuma da abin da ya yi mata sai ta ji duniyar ya yi mata zafi.Ita tunanin ta A.m zai biyo ta asar ne.


Sai dai tana tunanin yadda za ta iya danne zuciyarta,ta zauna da Juwairiya bayan ta gane amanarta suke ci,duk da A.m ya yi mata rantsuwar yana shan magani ne saboda ita, amma kuma bai aryata numbarsa a wayar Juwairiya ba,sai dai ya nuna sam bai san zancen ba wataila son sa take don kwanaki ana kiran sa da bauwar numba,bai dai taSa Wagawa ba ne shi yasa bai fahimci komai ba.

Zainab ta gane sam ba za ta iya rayuwa babu shi ba,amma dole ta canza zaman su domin sai ya gane kuran sa,ita kuwa Juwairiya Momi ta ce ta bar lamarinta a hannunta don sai ta yaba wa aya zainta.

Lantana ta shigo gidan da mamakin ofar a buWe duk da ta ga motar A.m a gidan,amma ta san ba' abarin ofar falon a buWe.

Tura ofar ta yi ta shigo tana arema gidan kallo yadda yake tashi da amshi da gyara komai tsaf,jikinta ya bata a kwai mace a gidan.

Tsaye ta yi tana Wan tunani sai kawai taga Juwairiya ta rugo da gudu daga sama tana dariya,jikinta daga ita sai yar bes fara da wando fari tirikwata wa da A.m ya siyo mata da suka fita,saboda shi yana koyi da hadisin ma'aiki wanda yake mana koyi da saka fararen kaya.

Da gudu take saukowa tana dariya shi kuma ya biyo ta cakulkuli yake mata wai kan dole sai ta yi mishi kuka yaga hawayen banza.

Kamar yadda Lantana ta yi tsuman tsaye tana kallon su haka suma suka zuba mata ido cikin firgici.


TO FA NIMA IDANU NA ZUBA MUSU TARE DA BASU LOKACI DOMIN NA GA REACTION IN SU



KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 29*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Juwairiya kunya ta kama ta matuar gaske ji ta yi kamar ta nutse a asa,juwaya ta yi za ta koma ciki,amma sai A.m ya janyo ta tare da haWa ta da irjin shi.

" Ke! Wace irin mahaukaciya ce da za ki shigo gidan ma'aurata kai tsaye sai ka ce Wakin gidan ku."

"Lantana jikinta ya kama rawa kamar mazari saboda tsawar da ya daka mata,ta yi mugun firgita ba ta gane abin da ya ce ba.

" Ka yi hauri yallaSai wallahi ban san ka na ciki ba,kuma Hajiya Zainab ta ce na zo na gyara gidan za ta dawo."

Ta faWa jikinta na rawa kanta na asa ta na mamakin abin da ta gani don ta firgita.

A.m ya yi farin ciki sosai jin abin da ta ce sai ya Wan ture ta daga jikinsa,ya kalli Lantana da har yanzu idanunta a asa suke,ba ta son ta ara ganin abin da ta gani,domin ila arya suke mata.

" Ok sai ki je ki yi aikin ki munafuka na sha mamaki da Zainab ta tunume ni akan ina tare da Juwairiya,a she ke ce munafukar da take son raba aure.
Wallahi kin ji na rantse miki in har kika yi gigin faWa mata abin da idanun ki suka gani,kaf an gidan ku ni ne ajalin su don bom zan siya na tashi gidan."

Ware idanunta ta yi tsananin tsoron sa ya kamata saboda idanun sa sun tabbatar mata da zai yi fiye da haka.

" Ba ke kin iya munafunci ba to bari na ara miki da abin da zai kashe ki,don ba za ki iya faWa mata ba duk munafuncin ki saboda in ban kashe ki ba,to ita za ta yi ajalin ki kin ga gulma ta yi riba kenan."


Ya ce da ita ya na zare mata ido domin haushi take ba shi,tun da ya ji ita ta faWa mata komai,ga shi yanzu ta korar masa da matar so.

"Juwairiya matata ce wanda na aura a bisa wasu dalilai da ba zan gaya miki ba,saboda bai shafe ki ba."

Ya ara matse ta sosai a jikin sa kiss ya sakin mata a kumatunta,ya na mata wani irin kallo da ya saka ta kauda idanunta saboda kunyar Lantana.

" Kin ga in ta dawo sai ki gaya ba mata yau in ara gani ba kuma iyakan runguma ba,ki sanar mata duk abin da kika gani kar ki rage."

Lantana da sauri ta shige kicin tare da rufe ofar.

" Innalillahi na shiga uku!"

Ta sauke ajiyar zuciya mai arfi yayin da kanta ya kulle ta rasa in da za ta fara tunani.

" Wallahi wannan mutumin ya rikita ni na rasa mai zan fara tunanin,a halin yanzu zuciyata ba za ta iya fahimtar komai ba,domin ya saka ni a cikin ruWu."Ta ce yayin da ta Wora hannu akanta.

" Da gaske ya ke faWin matar sa ce ita?A 'a lamarin nan a kwai rikitarwa! Ji fa yadda ta koma tamkar wata gilas,saboda tsabar kyau kai Zainab shashashar mace ce,wai ta je hutu ai kuwa ki dawo za ki ga sakamakon hutu."

" Wa ni ai komai na ga kuna yi ba zan iya gigin gaya mata ba,haka kawai ku da holewa ni da shan bugu.Kai amma fa A.m arshe ne gurin rashin mutunci don ko kaWan Zainab ba ta yi tunanin ta na gidan ba."

Irin maganar da take yi a zuciyarta kenan ta buWe ofar a hankali ta na leen su,sai ta ga sun ara rugawa da gudu sun yi ciki.

" Allah ya kai mu ki dawo gidan nan za mu
sha kallo!Allah ya sa kar ki yi shigowar dare in ba ma idanuna abinci,sai ki gane sakaci kika yi ko halin maza A.m yake nuna miki."Ta faWa sannan ta kama aikinta zuciyarta cinkushe da tunani kala-kala.

Bini-bini za ta lea ta na kallon sama amma sai ta ji shuru kamar bacci suka yi.

" Ha ina tausayin ki yarinya ba ri Zainab ta dawo."Ta ce ta na aiki cikin mamakin lamari da al'ajabi.

" Humh namiji bunun aya."

Abin da take ta nanatawa kenan a cikin zuciyarta.


A.m ya rungume hannun shi ya na kallonta da ta kwanta akan cinyar shi,ta Wora filo a irjinta idanunta lumshe kamar ta na bacci,sai dai a zahirin gaskiya ba bacci take yi ba.

Zuciyarta cinkushe da kishi da tunani jin Zainab za ta dawo,domin a yadda take jin son sa da kishin ta ba za ta iya Soye kanta ba,kamar yadda ta yi a farko ta na jin ko sama da asa za su haWe za ta nuna kanta a wannan karon.

Kamar yadda take tunani shi ma haka zuciyar sa take cinkushe da tunani,ga shi ya gagara samo mafita.

Duk da cewa zuciya da gangar jiki sun yi kewar Zainab,amma in ya tuna za ta dawo gaban sa yake wani irin yankewa ya faWi.

Ya sani a yanzu babu wanda zai kalle ta yabce ita yar aiki ce,duba ga yadda ta koma tamkar wata tarwaWa.

Ya na ta tunanin ko ya Wauke ta daga gidan sai dai ya na jin ba zai iya jure rashin abincinta ba,saboda har yanzu ya kasa iya cin abincin Lantana.

Wayarsa ya zaro ya gwada wayar Zainab da ya daina kira,saboda in Wauka da take yi.

Sai dai ringing Waya ya ji ta amsa tare da sakin kuka.
" Ka daina sona A.m ban taSa tunanin a kwai ranar da zan yi fushi da kai ka yale ni ba."

Ta amsa daga Sangarenta ta na wani irin kuka da yake tafarfasa masa zuciya.

Tsam Juwairiya tamie daga jikin sa ta fice daga Wakin ba tare da ta kalle shi ba,yayin da zuciyarta ke mata luguden bugu na kishin sa.

Binta da kallo ya yi ganin ta canza kalar fuskarta kamar ba wacce ya sani ba.

Sai da ta fice daga Wakin ya saukar da nauyayyar ajiyar zuciya.

" Ya kike son na yi kin mai da ni kamar wani wallo don kawai kin ga Allah ya jarabce ni da son ki?Kawai na ba ki dama kije duk abin da kika yi ninya ki yi,ni dai har yanzu ba zan fasa gaya miki ina sonki ba."

Ya ce da ita ya na jin tsananin haushinta da kuma fargabar abin da zai faru,domin ya na ji a jikin sa kamar lokaci ya yi da zai gaya mata zaman Juwairiya a gidan su,don su daina samun saSani,duk da ya san zai sha wahala kafin ta amince.

" In har ka na sona da gaske A.m ka daina kawo rigima a cikin aurenmu,sannan ka tuna da alawarin da ka yi min don Allah karka canza."

Shiru ya yi bai ce komai ba ya rufe bakin sa da hannun sa ya na jin saukar kukan da take yi.

" Ka yi shiru ba ka ce min komai."Ta faWa cikin muryar kuka.

" Mai kike son na ce miki Zainab wane irin halacci ne ban yi miki ba! Ki dawo a kwai wata magana mahimmanciya wace za mu tautauna,kuma in kika fahimce ni in sha Allahu ba za mu ara samun tarnai a aurenmu b."

" A.m a kwai matsala ne don Allah ka faWa min?"

Ta tambaye shi da zauwa jin muryar sa ta canza." Babu kuma kar maganar da na ce miki za mu yi ya Waga hankalinki domin alkhairi ce."
" Ok to shikenan baby ba matsala,amma fa ka canza gabaki Waya,domin da ace babu wata matsala cewa za ka yi in jira ka mu taho tare."Ta ce da shi da wata kalar murya.

" Wataila da izinana kika tafi?"

Ya ce da ita a ufule kawai sai ta ji ya datse wayar, a lokacin da take faWin.

" Tun da ba za ka zo ba sai arshen za mu dawo,saboda zamu tsaya mu yi siyayya."

Miewa akan gadon ya yi tare da shafa gemun sa da ya awata masa fuska.

Wani irin damuwa ya ji ya lulluSe shi sosai.

" Gaskiya na canza shawara ina ganin kawai zan Soye Juwairiya duk san da ta samu ciki,sai na saka Zainab ta yi cikin arya a zuwan ita take da ciki in ta haihu Wan ya zama Zainab a zuwan ita ce ta haihu."

Take ya amince da shawarar sai ya mie da sauri ya saka takalmin sa ya fice zuwa Wakinta.

Ta na tsaye a gaban mirrow ta juya bayanta tare da Wan jingina kanta da gefen mirrow,a ranta ita kaWai ta san mai take tunani,domin iya tsananin damuwar dake kan fuskarta na hango.Ba tare da ta san ya shigo ba ya fara magana.
Kallon sa take yi da wani irin canji a fuskarta har ya gama mata bayani,ba ta tanka ba illa kallon sa da take kamar bao a gare ta.

Ganin ba ta da ninyar magana sai ya saki tsaki ya juya ya na faWin." Ina fatan kin ji mai na ce."

Ko kaWan A.m bai canza mata ba wai don Zainab za ta dawo,haushin da take ba shi duk ya yi mata maganar abin da ya tsara sai ta yi shiru ta zamar masa kamar wata kurma.

Zaune suke a falo sun dawo daga siyayya A.m ya ce ta raka shi a kwai turaren da yake son ya siya.

Sun zaune a falon asa sun baje kayan ciye-ciye suna ci

Turaren da ya siyo ya na son ya yi haWa da wanda yake shafawa,saboda turaren ya tafi da imanin sa gashi ba zai iya canza wanda yake fesawa ba.

A hannunta ya kama ya fesa mata a hannun ya ce." Matar shige ki ji amshin sa ya yi daWi ko?"

Juwairiya har ga Allah amshin bai yi mata ba,kallon sa ta yi ta Sata fuska tare da toshe hanci." Humh ni ban ji wani amshin daWi ba don ni warin almiski ya yi mini,kuma ni ba na son almiski."

" Allah ko ka ji gulma wannan turaren ko shugwaban asa ya shai amshin sa ba zai kushe ba,balle ke ni na san gulma ce irin ta ki don ko wanda na ke shafawa ba ki taSa cewa ya na daWi ba."

Dariya ta yi lokacin da ta toshe baki ganin haka sai ya ji haushi sosai ya biyota ya na faWin." Allah sai na fesa shi a jikin ki duka."
Zagaye falon suke yi har ya kamata zai fara fesa mata turaren,yayin da take roonsa don har ga Allah bai yi mara ba.

Wayar sa da take aljihun wandon sa ta fara ara da sauri ya ciro,jin kiWan da ya saka ma Zainab ce.

" Hello gani a airport ka zo ka Wauke ni."

Ya kalli Juwairiya da ta ji abin da Zainab Win ta ce saboda ta na jikin sa ya Waga wayar.

Da ido ya yi mata magana sannan ya Wauki key Win motar sa ya fice.

Ta na ganin sa ta faWa jikin sa tare da sakin kuka sosai." I miss you honey."
Da so ya yi ya ture ta ganin irin shigar da ta yi duk da cewar a da in ta yi shiga wani lokacin ya na orafi,amma yau ganin ta da gyale ta yi roling Win sa,sai ran sa ya Sace sosai,domin shi da za ta fara shigar Juwairiya ya na so,saboda ya gane hijabi wani sirri ne da Allah ya bawa mata duba ga jikin Juwairiya da yake mamakin irar sa.

Ga mamakin ta sai ta ga ya yi shiru, bai cika magana ba sai kallon hanya da yake yi,hakan bai saka ta damu ba saboda ta yi tunanin ko har yanzu fushi yake yi da ita,duk da cewa ita ya kamata ta i masa magana,amma sanin hali sai ta kama bakinta ta yi shiru.

Wayarta ta Wauko ta yi kiran Momy ta gaya mata jirgin su ya sauka lafiya.

Ko da suka isa gida wanka ta shige saboda ta gaji matuar gaske,kanta har wani sarawa yake yi saboda ciwo,in da Allah ya taimake ta ta ci abinci a jirgi,so babu abin da za ta nema illa ta yi sallah ta bi lafiyar gado.

Ya shigo da dubuwar farar rigar bacci wanda ya Waure igiyar ta bayansa,ganin ta kashe fitilar Wakin ya kunna fitila mara haske.

"Zainab ki tashi magana za mu yi kuma mai mahimmanci."

Ya ce da ita don yau yake son ya gaya mata komai,gudun kar ta ganta a gidan lamari ya jagule,saboda

Please Login or Register in order to submit comment