Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take sai hankalin A.k ya tashi musamman da ya ga ya maida kan shi a jikin kujera ya na kallon shi.Nan take ya fahimci amininna sa ya na cikin damuwa.

" Ya dai aboki a kwai matsala ko yanayin ka ya nuna a kwai abin da ke damun ka."
Ya kauda kansa gefe ya na faWin."Kai ma ka san matsalar a kan Zainab ce ta na ba ni ciwon kai lamarin ta a kwai gyara.Na rasa yadda zan Sullo mata ga kafiya da taurin kai."
A.k ya watsa hannun shi in akan wannan ne be wani dame shi ba yadda ka san auren dole a ka yi musu kullum cikin faWa."In dai akan wannan ne ba ni da matsala daku kai ba hauri ita kuma kafiya ni lamarin ki ya na bani mamaki.Kun fi kusa kun san yadda zaku sasanta kan ku."
Ya faWa ba tare da wata damuwa ba don ba yau ya saba kawo mishi arar ta ba,kuma ko yaje ba saurarsa take ba gashi shi baya iya hauri da fushin ta haka kawai su yi ta sa maka Sacin rai.
"Ko zamu keSe ina da wata magana da zan Wan tautauna a tsakanin mu kuma sirri ce."A.m yace da muryar raWa ya na kallon gefen matarsa don ya yadda da aminin na sa ba zai gaya mata ba.
"Ki kawo mana abincin falona."Yace sannan suka shge cikin aton falonsa da ya sha gyara ya na ta amshi.Bayan sun ci abinci sun natsa har sai da suka yi salar azahar sannan suka natsa tare da taSa hirar kasuwancin su.
A.m ya gyara zama ya na kallonsa cikin fuskar tausayi ya fara magana duk da wani gefe na zuciyarsa ta na masa gargaWin karya faWa masa amma ya fara magana da cewa.
" A kwai wani sirri da na Soye a raina na san zaka fahimce ni kuma ka ba ni shawara me kyai kamar yadda ka saba,ina ganin kamar na yi wa iyayena rashin adalci da na Soye musu cewar ni ne ba na haihuwa bayan ba haka lamarin yake ba.
"Na yi wa Zainab alawarin ba zan yi mata kishiya ba kuma ba zan taSa gaya ma iyayena cewar ba ta haihuwa ba,amma na yi tunanin za ta canza halayenta mu yi zaman lafiya amma kullum ara bijiro da abin da zai saka mu samu saSani,jiya duk ruwan da ake ta na waje wai sun je fati kamar ba matar aure ba,gabaki Waya ba ta damuwa da halin da zan shiga in ta Sata min."

Ya yi shiru ko zai ce wani abu amma be tsinka shi ba sai kallon shi da yake yi ganin haka sai ya Wora da cewa." Jiya ta kai fagen da na mareta wanda daga baya na yi dana sani.Ka ba ni shawara kar Zainab ta haukani."

A yanayin yadda ya yi maganar sai ya ba shi tausayi,sai dai ya na mamakin wai Zainab Win ce bata haihuwa kuma ya yi mata alawarin va ze gaya ma iyayen shi ba,sannan ba ya yi mata alawarin ba ze ara aure ba to wane irin shawara yake son ya ba shi don ya san be wuce yace ya ara aure ya samu matar da za ta ba shi yaro ba.
"Gaskiya ka yi wauta kana tunanin in kai ne ba ka haihuwa za ta yadda ta zauna da kai?Kuma ka cuci iyayenka kullum muka haWu da Daddy sai ya yi min orafin rashin haihuwar ka ya na tausaya maka,ga kuma masoyinka da yake Satar da kuWin shi gurin yi maka sadaka da neman maka magani."

Ya numfasa ya na kallon shi a tsanake yaci gaba da cewa."Wace shawara kake son na ba ka bayan ka yi mata alawarin ba zaka ara aure ba kasan dai zuriya ta hanyar aure ake samun su,don haka Baban soyayya kaje kuci gaba da soyewa kawai shine shawarar da zan baka."

Abin da A.k yace mishi kenan ya mie don ransa ya gama Saci.A.m shima miewa ya yi don ba shi da abin da ze ce kan shi ya Wau zafi,shi dai ya san koma mene ne ba zai karya alawarin da ya yi mata ba.

Bayan sun fito ya kalli matar A.k da take tattara gurin da yara suka ci abinci ya na dariya."To ni madan zan wuce."Dariya ita ma ta yi "Wato an gama gulmar mu ko ba komai nima ina nan zuwa gidana musha namu."
A.m ya ara dariya yana cewa."Baku da dama ne shi yasa musamman mutuniyar ki.A.k ya ja hannun shi ya na faWin.Muje ka ji in ka biye mata sai ta Sata maka lokaci da surutun ta suka fice.
******
Juwairiya ta ara samun aiki a gidan wata mata mai suna Hajiya Binta,matar ta na da kirki matuar gaske yaranta bakwai.Kusan dukkan aikin gidan Juwairiya take yi,saboda yawan yaranta take wahala a gidan sai dai amma babu laifi suna aruwa da ita.Matsalar ta Waya mafaWaciya ce sam ba ta da hauri kamar zawo take,duk yadda take taka tsan-tsan amma sai ta rori abin da za ta yi mata faWa.

Saboda ba ta saba da irin aikin ba sai yake ba ta wahala warai,in ta dawo aiki ba ta iya taSuka wani aikin watarana ma sai tasha maganin ciwon jiki.

Ganin irin wahalar da take sha Mama ta ba ta shawarar ta haura da aikin,amma ta nace sai ta yi musamman da ta ga kuWin aikin na ta da tsoka.

Yaran matar kwata-kwata basu da mutunci ga rashin kunya abu kaWan za su hauta da zagi suna ci mata mutunci,mahaifiyarsu kuma ba ta son ganin laifin Wanta hakan ya sa ba ta kula su.
Abin da ya ara tsorata ta ganin sun girme mata aramar cikin su ita ce take tunanin za su zo tsara da juna.

Hatta wankin su ita take yi musu don tsabar rashin mutunci harda pant da breziya suke ba ta wanki,amma ta yi hauri ta jure burinta ta samu abin da za su dinga ci.

Sai dai rashin mutuncin da suke mata da ta fahimci ba me arewa bane ta yi tsalle ta fara nuna musu sam ba za ta Wauka ba.
Hakan ya saka suka ara saka mata ahon zua,domin zuciyar su tsabar hassada ce suna yashin kyan da Allah ya yi mata musamman da suka ga sun Sata jikinsu da mayukan bilicin.

Abin da Hajiya Binta ta tsira ya sa Juwairiya ta ji aikin ya fita a ranta,saboda kullum ta zo sai ta tuhumeta da cewar ta yi mata sata.Hakan ya tinzira ta ta saka a ranta duk ranar da ta ara za ta bar mata aikin ta.

Haka kuwa aka yi tai zuwa aikin bayan kwana biyu da barin aikin sai ga motar an sanda da Hajiya Binta akan Juwairiya ta sace mata sarar gwal Win ta.
Juwairiya ta shiga cikin tsananin tashin hankali ganin yadda Wan sandan yake oarin tasa ta zuwa ofis Winsu,hankalinta ya tashi matua ya dinga kuka tana rantsuwar ba ta Wauka ba.Tsananin tashin hankalin da Mama ta shiga ba'a magana duk da ta san halinta,amma sai ta shiga ruWu ta din ga tamabayarta da in ta san inda yake ta fito mata da shi,hakan ya saka Juwairiya cikin tashin hankali ta dinga wani irin kuka gani take kamar Mama ba ta yadda da ita ba.

Baba Sani ya sami abin da yake so don haka ya ara zuga Hajiya Binta kan ta tafi da ita ofishin Wan sanda,burinsa ya cika dama tintuni yake addu'ar Allah ya sa haka ya faru.

Mama na gani aka tafi da Juwairiya ta na wani irin kuka gani take kamar dukan ta zasu ta yi har sai ta amsa laifin da ba ta aikata ba.Ganin an tafi da ita Mama ta nufi hanyar shiga cikin gida ranta na wani irin suya,hango halin da Juwairiya take ciki da yadda take kuka ta na kiran sunan ta,sai kawai gani akai ta yanke jiki ta faWi asa.

Hankalin Mariya ya tashi matua wacce take zaune a asa ta na kuka sosai,gani take kamar ita ta saka ta a cikin wannan hali saboda hanyar aikin da ta yi mata.

Ita da mahaifiyar ta suka kama Mama suka shigar da ita gida,sai dai daga baya kan dole suka kwasheta zuwa asibiti ganin numfashint 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~a na Waukewa gashi ta na aman jini!

Baba Sani ya yi matuar jin daWin faruwar lamarin duk da ba shi da shiri akan hakan sai dai ya na ganin yanzu ne burinsa zai cika akanta,don ya tabbata basu da wanda zai yi belin ta hakan zai ba shi damar Wora mata sharaWin zai yi belinta amma sai ta amince za ta yadda da buatarsa,don haka ma yai zuwa ogishin da nufin sai sun yi mata dukan kawo wua ta galabaita saboda ya san ta a kwai kafiya.

Juwairiya na zaune a cikin cell Win ta udundune kanta a cikin jikinta tun da suka kawota take kuka,tunanin halin da Mama take ciki yake damunta wani irin sauro da yake damunta da ihu da cizo,yasa take ta zubar jawaye ga yunwa dake waularta."Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin fair."Abin da bakinta yake faWi kenan cikin tsananin tashin hankali.

Tun da Hajiya Binta ta kawota ba ta ara zuwa ba sai washegari da safe lokacin ta matuar galabaita,bayan sun tuhumeta amma tai amsa laifinta dukan tsiya suka yi mata sannan aka maida ta.

Da rana sai ga Baba Sani ya shigo ofishin ya na zare ido,gurinta yazo ya na kallonta." Kin ga abin da kika jawo ma kanki kosaboda shegen taurin ranki.'Yace ya na kallonta duk da ita ba shi take kallo ba saboda tai ta kalleshi wani irin tsanar sa take ji matua.

" Har yanzu kina da dama zan iya fitar dake amma sai kin amince za ki yadda da buatata."Yace da ita ya na kashe murya.
Wani irin kallo ta watsa mishi " Allah ya yi min tsari da mugun nufin ka,da na amince gara na tabbata a gurin nan ko ya zamo shine ajalina."
"Ok haka kika ce ko?To ai shikenan kuWina ya huta tunna kin zaSi rayuwar zuwa gidan mutane kina sata."Yace tare da watsa mata harara ya fice daga ofishin,kuka ta saka tare da cigaba da addu'ar ta ta na roon Allah ya kawo mata mafita.

Kwanan ta uku a gurin ranar da Hajiya binta ta shigo ta buaci a saki Juwairiya taga sararta,duk da cewa azafi aka yi mata amma ko hauri basu bata ba.Ita dai da gudu ta dawo gida tasan yaran Hajiya Binta suka ulla mata wannan ullalliyar amma Allah ya fisu kuma addu'a takobin mumini.

arin tashin hankali da ta zo Mama ba ta a gida Ibrahim ne yake sanar da ita ciwon Mama,wani kukan ta saka ta fita zuwa gidan su Mariya domin Mariya bata gaya mata Mama ba lafiya ba.

Yadda ta ga Mama hankalinta ya tashi warai rungume Mama ta yi ta na kuka sosai.Mama ce ta buWe ido jin muryar Juwairiya hankalinta ya Wan kwanta ganin ta fito,don ba ta san halin da take ciki ba shi ya sa jikinta yake rikicewa.

Likita ne ya shigo ya mia ma Mariya takadda yace."Gashi ki siyo wannan maganin ya kamata ku din ga kwantar mata da hankali, domin ta na da hawan jini ga ciwon zuciya, matuar ana Sata mata rai to watarana zuciyar za ta buga!"
Wani arin tashin hankali Juwairiya ta shiga jin Mama na da waWannan ciwuka rungumeta ta yi tana kuka."Mama kema mutuwa za kiyi?Don Allah karki mutu ki barni!Rayuwata za ta shiga cikin garari.Allah na gode maka ka bani ikon cin jarrabawa,amma karka Wauke min mahaifiyata ka barni da azzalimi."

Mariya ta kama ta ta rungume ta na buga bayanta hawaye ya na kwaranya a fuskarta tsananin tausayi ya cika mata zuciya ganin halin da take ciki."Kin ga ni Mama za ta barni ko!Wai me ya sa rayuwata tazo a bain jadawali ne?Nake kurSar ruwan bakin ciki mafi zafi da una a zuciya."Tace cikin kuka." A'a Juwairiya karki faWi haka!Kada ki kasa cinye jarrabawarki kin san Allah ya na jarraba mutum dai-dai imaninsa.Kar zuciya ta sa ki yi saSo.Ina ji a jikina zaki ji daWi a rayuwarki.Allah zai ba Mama lafiya."Ta gaya mata ta na shafa bayanta.

Dayar Juwairiya ta daina kuka sai ajiyar zuciya hannun Mama ta kama ta rie ta na kallonta.Duk wani hidima na asibitin su Mariya da mahaifinta suka yi har kuka ta yi ta na gode musu domin Allah ne zai biya su.

Bayan Mama ta samu saui aka sallame su akan Mama za ta din ga zuwa ganin likita ta na karSar magani,hankalin Juwairiya ya tashi ta na tunanin ina za ta din ga samun kuWin da Mama za ta din ga zuwa ganin likita.

Kan dole ta ara saka Mariya ta nema mata wani aikin don sana'ar da suke yi sun cinye tsugune kawai suke,da fari Mama tai yadda ta ara yin wani aikin amma daga arshe dole ta haura ganin yunwa na so ta yi musu tabo.

Kwasam ta haWu da wani matashin saurayi mai suna Mas'ud Allah ya jarabci Juwairiya da son shi yaro Wan gata da sanyin rai ga kyautatawa.Shigowarsa rayuwarsu ya sa sun samu canji sosai,duk da ya ga ita yar talaka ce amma be saka yai sonta ba don da Allah yake sonta.Mas'ud ya na temaka musu sosai ya na aiki a Jami'ar Ahamdu Bello a library kuma Wan samaru ne iyayen sa sun rasu sun bar mishi dukiya sosai,sannan Wan kasuwa ne.

Juwairiya ba ta taSa jin ta na son mutum ba sai akan sa, gabaki Waya ta ji ta na son ta aure shi sai dai tasan hakan ba me yiyuwa bane,don babu yadda za'ai Baba Sani ya barta ta aure shi sai dai akan yadda take jin sonsa, za ta iya fito na fito a tsakanin su ko gidan me unguwa za ta iya kai shi.

Haba tunna ya ga ya na zuwa gurinta ya saka tashin hankali yayin da shi ma Mas'ud ya kafe,ganin shi ma Wan zamani ne sai yace bai tashi uren Juwairiya ba don bashi da kuWi,nan take yace mishi kar ya damu ya amince zai yi mata komai.

Ranar da Mas'ud ya kira Juwairiya ya gaya mata Baba Sani ya amince da auren su har ya ba shi izini ya turo magabatansa,kawai jin sa Juwairiya ta yi amma ba ta yadda da abin da yace mata ba.Ganin haka sai ya yaleta kawai in ta ga zahiri ta yadda.
Da misalin huWu da kwata Wan Baba Sani ya yi sallama ya shigo ya yi kiran Juwairiya taje shashin Baba Sani ya na kiranta a Wakin matarsa.

Gabanta ya faWi amma sai ta saka hijabinta ta nufi Wakin ganin a kwai bai ya sa ta ji a ranta a kwai abin da ke faruwa sai ta tsaya daga kofa ta na sallama."Yauwa Juwairiya shigo."

Baba Sani ya faWa da murya sanyaya a hankali ta yaye labulen ta shigo tare da tsaya daga nesa ta na kallon mutane jikinta ya bata dangin Mas'ud ne.

Mio mata alkur'ani ya yi tare da canza fuska kalar tausayi yace." Dangin yaron nan Mas'ud suka zo neman auren ki,amma ni bazan cuce su ba sun yi min tambayar kina da tarbiya nace gara suji a bakin ki, don nasan ke ar mace ce sannan kin yi yawon aiki gidajen masu kuWi,duk mazan gidan sun sanki a matsayin a mace ga abin kunya na satar da kika yi,har aka kulle amma ga kur'ani ki rantse musu hakan be faru ba "

TaS ji ta yi asa ta gaza Waukarta ta ji wani irin hajijiya ya kamata." Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un."











Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na goma sha Waya.Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G0J8rS0cxTtCCC38iwA3B9*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA GOMA SHA AYA*


Ganin tai karSar kur'anin hawaye ya na zuba uncinta ya yi murmushin mugunta,ya juyo ya na kallonsu sannan ya ara saka kuka har da hawaye share-share yace." Kun ga abin da na gaya muku ya zama gaskiya? A matsayina na anin mahaifinta babu yadda ban yi da ita ba akan ta zama macen warai, amma tai jin maganata!"

Juwairiya da take cikin wani yanayi na tashin hankali mara misaltuwa,ta rintse idanunta ta na jin wani irin aton abu ya taso daga irjinta ya tokare mata kirji ya kuma i wucewa.

Tana son ta ji saukar hawaye akan uncinta ko ya rage mata raWaWin da zuciyarta take ciki.Kunnuwanta ba za ta iya jure jin kalamai da yake yi ba,ya na aibanta ta ita da mahaifiyarta.

Ta muzanta iya muzanta da yar ta yi nasarar jan jikinta ta fita zuwa shashin su,ta bar shi da bayin Allah da suka yi zuru suna kallon shi,yanayin su bai nuna sun yadda da maganar da yake musu ko akasin haka.

Da gudu ta faWa Wakin tare da anamre Mama ta na wani irin kuka." Mama duniya ta min zafi! Ina jin wani irin bain ciki a cikin zuciyata,wallahi nafi buatar mutuwa fiye da rayuwata! Wai me na yi wa Baba Sani ya tsane ni haka!Gara ya kashe ni da Wacin da yake saka ma rayuwata."

Mama ta rungumeta ta na shafa bayan ta don gani take kamar hauka ta yi." Lafiyar ki Waya kuwa?Ki yi shiru ki yi min bayanin yadda zan fahimta."

Kusan minti goma ta na kuka ganin ta kasa magana sai ajiyar zuciya take,a ranta ta na jin bain cikin rabuwa da masoyinta,don ta san yadda ya aibata ta babu yadda za'ai su yadda Wan su ya aureta.

Da yar Mama ta samu ta daina kukan sannan ta yi mata bayani.Ran Mama ya Sace sosai ba ta san sanda ta ji jawaye ya na zuba a uncin ta ba." Na gaji da halin da yake min! Zuciyata ta fara gajiya amma ba komai Allah ya fi shi da ikon Allah sai ya yi nadama,akan halin da yake miki."

Sosai Juwairiya take kuka koda Mas'ud iyayensa suka koma gida suka sanar mishi a abin da ya faru,hankalinsa ya tashi matua duk oarinsa na ya fahimtar da su,amma sun i arshe wan mahaifinsa ya gyara zama yace." Ko da a ce yarinyar ba halinta bane,to anin mahaifinta ba ya son ya baka ita ka kyale musu yarinya ga an'uwan ka nan sai ka zaSa a cikin su."

Ransa ya Sace matua da ma ya ba shi izinin ya turo dangin sa saboda ya faWa musu haka.
Motarsa ya Wauka sallama ya yi bai ko tsaya Mama ta amsa ba ya faWa gidan,a yadda ta gan shi ta san ba shi cikin hayyacin sa.

Da sauri Juwairiya ta ruga da gudu don ta saka hijabi ganin ya shigo." Mama ya Baba Sani zai yi haka? Juwairiya ya aiba ta a gaban iyayena. Wai me kuka yi mi shi ya tsane ku?"Ya faWa yayin da idanunsa suka kawo ruwa.

Cikin jimamin lamarin Mama ta share hawaye ta kalli Mas'ud da ya haWa kansa da gwiya hawaye na zuba a fuskarsa,sai ya ba ta matuar tausayi ta san yadda yake son Juawairiya duk da iyayensa suna da shi amma a haka yake son ta.

Ka yi hauri ka san matar mutum kabarin sa Allah be nufi Juwairiya matar ka bace,ka bi zaSin iyayen ka ni na san duk korar mata masoya da yake in har lokacin ta ya yi bai isa ya hana ba."

" Gaskiya Mama ba zan iya jure rashin Juwairiya ba zan je na sami Baba Sani duk abin da za'a yi sai dai ayi haka kawai ya din ga cusgunawa rayuwarku.Ya katse ta da faWin hakan ransa a Sace tare da miewa.

" Zo Mas'ud don Allah karka je a yadda ranka yake a Sace za'ayi Satatta,ka san halin shi ba shi da hauri ni ce na haifi Juwairiya ina me baka hauri ka haura da ita,shi kaWai ne wanda take gani a matsayin na ta in har aka Sata mishi wa za ta rie?Ka yi hauri Allah be nufa za ka aure ta ba."

Kawai sai gani ta yi ya saka kuka ya na kallon Juwairiya da ita ma take kuka na tausayin halin da suke ciki." Juwairiya zuciyata za ta shiga cikin wani hali na rashin ki.Ki yi min addu'a Allah ya ba ni mace me irin halin ki,ni na san ke wace ce ko idanunki mutum ya kalla ya san kina da tarbiya da natsuwa.Ina sonki zan haura da auren ki saboda umurnin Mama."

Fita ya yi har da gudun sa ya na sharen hawaye Juwairiya ta mie da gudu ta shige Waki tare da saka kuka.Sam ita ba ta ga dalilin da Mama za ta hana shi ba,ba ta san me Baba Sani yake nufi da ita ba shi ya sa take girmama shi,abin da ya sa tai ga ya mata ta san duk ranar fa ta gaya mata udirin sa akan ta, ila zuciyarta za ta buga domin abin ya yi muni.

Tun daga wannan ranar ba ta ara gani Mas'ud ba ko wayar da ya siya mata Mama wacewa ta yi ta ije,don a yadda ta ga take-taken ta za ta iya kiran shi kuma shi ma haka.Tun ta na saka ran ze dawo har ta cire sai dai ta wahala kafin ta cire son shi a ran ta,sannan da ga baya taci gaba da al'amuranta.

Mariya ta sami miji za ta yi aure anan kusa da layin su za ta yi auren don haka su Juwairiya su ne an mata.Su Juwairiya an sha gayu da lalli an yi kyau sosa,ana ta hidimar biki don ba zama an saci Wan Sarawo.
Zaune suke ana hirar an mata Juwairiya ta kalli Mariya yadda ta sha kyau yace."Su amarsu kin ganki kuwa,dama komai munin amarya ranar bikinta sai ta haska."

Fari ta yi musu ta na dariya tace." Ku zauna kuna rungume filo ni dai Allah ya hutashshe ni na shige daga ciki,ku tsaya kuna ruwan ida kwayi kwantai."
Wani irin dundu Juwairiya ta duma mata ta nafaWin." Ji min ar bain fata wato fatan da kike mana kenan tunna kin shige daga ciki ko? To in sha Allah muna bayan ki."Sauran an matan suka taso mata ita dai Mariya dariya take musu,sannan tace." Ai ke Juwairiya Baba Sani ya hana ki aure da tuni kin haihu ma.Amma ba komai Allah ya na tare dake lokacin ki ne kawai ba yi ba."
Shiru ta yi sai hawaye yayin da mutanen Wakin suke ta ba ta baki.
A haka suka sha bikin Mariya aka kaita Wakin ganin Juwairiya za ta tafi ta kama ta tare da saka kuka.Sai kuma ta ba Juwairiya tausayi ta rungumeta ta na share mata hawaye.

Mariya ta share hawaye tace." Maganar da mukai dake akan aikin nan kije Allah za kiji daWi kin ga ni na yi aiki da su."Juwairiya tace." Ke ni raba ni da aikin nan don na yisu amma ban ji da daWi ba."
" Allah ki gwada wannan kin ga yanayin halin da kuke ciki,ga shan maganin Mama dole kina buatar kuWi."
" To zan shawarci Mama duk abin da tace sai na je."Da wannan Juwairiya ta tafi gida cike da kewar awarta wacce ta temaka mata.

Koda ta yi ma Mama magana shiru ta yi zuwa can tace." An ya zan barki kiyi aikin nan nifa tsoro nake yi kina ganin rashin mutuncin da Hajiya Binta ta yi miki,amma tuna kin ce Mariya tace ta na da mutunci sai ki je Allah ya tsare ki."

Numfashi ta saki tace." To bari na gwada mu gani."

Juwairiya ta fara aikin cikin jin daWi ga karatu da take samu ake yi wa yaran lesson da islamiya matar ma ba ruwanta.

Watan ta biyu a gidan

Please Login or Register in order to submit comment