Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tabbata gobe in ta yi ido biyu da ita,zarginta zai zama gaskiya don ta wuce a kalle ta ace mata ´ar aiki.

" Wash Allah na!Haba A.m na gaji fa wallahi kaina ciwo yake yi,komai za ka gaya min ba zan fahimta ba, ka bari zuwa gobe sai ka gaya mini duka fa yanzu na dawo."

Ta ce mishi cikin ™orafi saboda ta san bai wuce ™orafin abin da ya faru a tsa™anin su zai yi mata magana ba.

Mi™ewa ya yi ya koma Wakinsa ya san tun da ta ambaci sunan sa ba za ta saurare shi ba,dama in dai ta kira sunan shi yayin da suke sa'in sa ba,ba za ta yi abin da yake so ba.

Washegari da safe A.m tun da ya yi sallah bai dawo ba,sakamakon ™anin sa da aka kira shi bashi da lafiya ya na asibiti.

Zainab ba ta tashi ba sai kusan ™arfe da rabi saura minti biyu,wanka ta yi sannan ta yi salla,saboda duk tashin da A.m ya yi mata ba ta tashi ba,gajiya ce sosai a jikinta har zuwa sadda ta tashi ba ta daina jin bacci ba.

Wani irin yunwa take ji a daddafe ta yi sallah,sannan ta zira doguwar riga ko hoda ba ta shafa ba ta fito don ta karya,ta san cewa zuwa wannan lokacin Lantana ta kammala abinci.

Da ga wanka ta fito bayan ta Wauki tsawon lokaci ta na dirje jikinta, da yake wani irin haske tamkar zara cikin wata,ita kanta mamakin hasken da ta yi take yi ta san cewa ta na da haske,amma ita ba fara ba ce sai dai yanzu wani irin haske ta ™ara har kusan kashe ido take yi.

Duk da ta Sata lokaci gurin yin kwalliya amma fa ba wata kwalliya ta yi ba,kasancewar ta ba mai irin sha'awar kwalliya irin waWan da ´an mata suke yi,su zama tamkar aljanu.

Wata doguwar riga ta saka kalar milk amma jikinta an yi mata ado da farin duwatsu,masu kyau don yanayin rigar ya fi kama da na indiyawa.

Turaren da ta Wauka wanda A.m yake shafawa tun da shi ta feshe jikinta da shi,ta na son ™amshin sa sosai saboda in ta sha™i ™amshin sa ji take kamar A.m na kusa da ita,amma wanda ya siyo sam ™amshin sa bai yi mata ba,har cikin zuciyar ta ta tsani turaren, amma shi gani yake kamar watsa take masa.

Juwairiya a yadda ta tsara ma kanta hak za ta fita Zainab ta ganta,don ta na ji a ranta kuma ta rantse ba za taci gaba da Soye kanta ga a gurin ba,za ta bayyana na komai kuma duk ta shirya da abin da zai faru.

Sai dai kuma yadda ta ga surarta ya fito ba za ta iya fita a haka ba,kasancewar ta mai alkunya da yakana.

˜aramin hijabi ta Wauka ta rufe jikinta da shi sannan ta Wauki sabuwar wayar da A.m ya canza mata mai kyau da tsada,bayan ya gargaWe ta da kar ta bari kowa ya ga wayar saboda tsadar ta.

A lokacin da ta kama murfin ™ofar fita Wakin sai abin ya mata mamaki,domin ita kanta mamakin kanta take na yadda ta shirya hakan,duk da ta san dala za ta Wauko ma kanta babu gammo.

"Sannu da shigowa Hajiya Zainab barka da dawowa Allah ya ja zamanin ki a gidan A.m."

Lantana ta ce mata kamar ta na mata gatsali kamar kirari,amma a zuciyarta dariyar ™eta take yi don ta san za'a kwashi ´an kallo.

"Lantana ya kai ban ga abinci a dinnig ba ke wace irin shashasha ce,kin san na dawio ko dama haka kike barin mijina da yunwa?"

" Allah ya huci zuciyarki Hajiya!Amma ba ni nake girki a gidan nan ba tun da kika tafi"Ta ce cikin sauri saboda ita ta ™osa ayi ta ta ™are.
" Ban gane ba shi yake yi ko fita yake ya siyo bayan son na ki."Ta tambaye ta da mamaki duk da ta san A.m ya tsani abincinta kamar yadda yake mata ™orafi.

" Ba' a waje yake siyo ba Juwairiya ce take girkawa,amma yau ban san mai ya hana ta fitowa ta girka ba."Tsabar gulma da yake cinta har saurin baki da take yi ta faWa in ina ta fara.

" Juwairiya?"

Ta faWa cikin zare ido don ita ko kaWan ba ta tunanin ta na gidan ba.
" Wayyo Allah na! Uban me yar iskan yarinyar nan take min a gida?Da ma ta na gidan nan ba ta bar gidan ba."

Lantana ta matsa daga gefe tare da kare wuyanta ganin ta nufe ta,a ranta addu'a take yi.

BuWe kofar kicin Win ta yi ba tare da ta nuna ko War a ranta ba,duk da ta ji hargoguwar Zainab sai dai hakan bai razanata ba.


Lokaci guda Zainab ta yi shiru lokacin da ta yi ido biyu da ita.

Gabanta ne ya yanke ya faWi dam!Ganin ta canza mata kamar ba ita ba.

Wani irn tashin hankali ya ziyarce ta ba tare da wani tunani ba ,sha™eta ta yi tare da sakin wani irin kuka.

"Ke dan ubanki mai kike yi a gidana?"

Juwairiya ta fisge gabar rigarta da ta ri™e ba tare da ta ce mata komai ba, ta nufi gurin gas za ta Wora abinci,da ba tare da ta ji tsoron ta ba.

Lantana kuwa tsalle ta yi gefe jikinta har rawa yake ganin yadda hankalin Zainab ya tashi,duk ta ™osa a fara ta ga yadda za'a ™are, a zuciyarta ta so ace munafukin ya na nan,sai ta ga ™arya da nuna isa ya na faWa mata matarsa ce.

Sha™eta ta yi sosai kamar za ta kaita lahira ta na faWin." Wallahi yau sai kin raina wayon ki saina nuna miki kuskuren shiga gonata da kika yi,duk cin mutuncin da kika yi mini ashe ki na nan a gidan kuna cin amanata bari ya dawo haWaku zan yi na ™ona."

A.m dake tafe a mota da sauri har baya ganin gaban sa ya so ace ya na gida uwar haka,sai dai ciwon ya tashi sosai don aiki a ka shiga da shi afendis ke damun sa.

Ya na tu™i amma hannun shi rawa yake yi saboda ya san a wannan lokacin,Zainab ta farka kuma komai zai iya faruwa.

Ko da ya iso gida bai yi parking ba ya ije motar tare da rugawa zuwa cikin gidan.

Zargin sa ya tabbata daidai saboda tun kafin ya shigo cikin falon,yake jin ™arar Zainab da hargowa.

" Zainab ki bar abin da kike yi ki tsaya zan yi miki bayani."Ya ce da ita don yau ta faru ta ™are.

Wani irin banzan kallo ta yi mishi tare da sakin ™ara." Uban me take mini a gida kalle ta fa A.m sam ba ta yi kama da mai aiki ba,duk tunani na tabar gidan na..."


"Wannan dalilin ya sa nake ta son ki ba ni dama na yi miki bayani "Ya katseta ya na faWin haka.

" Bayanin me za ka yi mini bu™ata ta kawai ta bar gidan nan."

Janye rigarta ta yi da ™arfi ta ture Zainab daga jikinta cikin tsawa.

" Ya ishe ku gabaki Wayan ku na gaji kuma kar ki ™ara ri™e ni ki na tuhuma ta,saboda matsa..."

Wani irin saukar mari ta ji ™uncinta mai zafi wanda ya saka ta ji jiri ya kwashe ta,ta yi taga-taga za ta faWi amma ta ri™e drower na kicin Win.

" Ki iya bakinki kuma ki tsaya a matsayin ki."A.m ya faWa bayan ya kwasa mata mari.

" Ka ™yale ta ta faWi abin da za ta faWa yau sai na wula™anta rayuwarki."

Juwairiya da ta ji saukar marin har ™wa™walwarta ta rintse idanunta cikin kuka sosai,don yau ta tabbatar A.m ba ya sonta! Munafiki ne mayaudari ne kawai ya na more jikinta ne da mugayan kalamansa da yake yaudarar ta.

Ta buWe baki za ta yi magana sai ™amshin turaren A.m da ya canza ya daki hancinta,wani irin amai ya taso mata duk yadda ta so ta mai da shi ina ta makara!

Da sauri ta ruga zuwa bayi amma tun kafin ta kai ta fara amai tamkar za ta amayar da ´an hanjinta.

Sai Zainab ta din ga kallon A.m da ya tsaya tamkar gunki ta buWe baki za ta yi magana,ta kasa sai ta ji kamar babu harshen ta a cikin bakinta,yayin da kanta ya Waure iya Waurewa kuma ya yi mata nauyi,jin kanta take ya yi nauyi, tamkar an yi mata gammo an Waura mata duniya da abin da ke cikinta.

Matsawa ta yi gurin A.m sai kuma kamar an tsikare ta,ta ruga da gudu cikin Wakin Juwairiya da take ta she™a amai tamkar ba za ta yi rai ba.

Allah sarki tsayawa ta yi ta kasa komai kamar jira take ta gama ta fito ta yi mata sannun a yadda ta nuna,amma iya tashin hankali da take ciki ya sa ta yi mutuwar tsaye,har ta kasa banbance wace rayuwa take ciki tsa™anin ta duniya da lahira.

A.m da ya ™araso da sauri don bai fahimci wainar da ake toya wa ba,ya yi tunanin ko Zainab ta biyo ta ne da dake ta.

Abin tausayi amai take yi tamkar ba za ta daina ba,kuma A.m ya yi mamaki har ta gama amai ta fito bayan ta wanke bakinta,Zainab ba ta tanka ba,sakamakon suman tsaye da ta yi.

Wani irin ajiyar zuciya ta saki tare da firgita kamar wacce ta dawo daga doguwar suma.

Duk da cewa ita ba likitar mata ba ce,amma a iya zaman ta cikin asibiti ta san yadda ake gane mace mai ciki.

Hannu Juwairiya ta kama tare da duba tsakiyar hannun,sannan ta Waga ™wayar idanunta.

Gabanta ya buga da sauri sabo da fahimci abin da Zainab take dubawa,lokacin da ta je asibiti ita da Hauwa abin da likitan ya duba kenan ya ce mata ta na da ciki.

Sam ba ta yi tunanin ciki ne da ita ba saboda wancan ba ta yi amai ba sai kwaWayi.

" Na shiga uku ya Allah karka saka mafarkin da nake yi ya zama gaskiya!Ka sa na buWe idanuna tun kafin na aikata abin da duniya za ta yi tur da ni a cikin mafarkin.
Juwairiya take da ciki wa ya yi mata?"

Ta faWa cikin ™araji tamkar wata zararriya ta na ihu gabaki Waya kamanninta ya canza

Juwairiya da A.m har ma da Lantana da ta yi laSe a bakin ™ofa ta na jin mai ke faruwa!Suka haWa baki gurin faWin

" Cikiiii."

Sai kawai na ga Lantana ta hantsila ta yi waje cikin tashin hankali,ba tare da na yi wani tunani ba na bita a guje,saboda ba zan iya ganin wannan bada™alar ba.



KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu™atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ™ofa a buWe take na ™orafi gyara ko ™arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za™auran marubuciya,kuma ™awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ™ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 30*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM



Zainab ji ta yi ™asa ba za ta iya Waukar ta ba,ta yi kukan kura sai ta faWa kan Juwairiya ta ™ara sha™e mata ma™ogaro.
" Uban wa ya yi miki ciki da ma ke ´ar iska ce."

A.m da sauri ya yi kanta tare da ™o™arin Waga ta kanta ganin ta na son ta yi mishi illa."Ba ki da hankali ´ar mutane za ki kashe?"Ya ce lokacin da ya Waga ta daga jikinta.

" Barni da ita wallahi in a kwai abin da yafi kisa zan yi mata! Ta ya ya za ayi tayo ciki ta shigo mini da shi gida."

Sai kuma ta ce." A.m don Allah karka sa na haukace ahalin yanzu ji nake kamar numfashi na zai Wauke!Ka da zargina ya zama gaskiya ka barni na koreta a gidan ta je can ta nemi uban cikinta."

" Zainab ki tsaya ki fahimce ni na yi miki bayan..."

"Wai mai za ka gaya mini?In dai ba ka na son ka faWa mini yau ne ranar da fitan numfashina zai yi bankwana da gangar jikina"!To na ro™e ka don Allah ka ™yale ni.Juwairiya ta fita daga gidan nan shine kawai zai saka na fitar da zargi a cikin zuciyata."Ta ce tana kuka sosai.

" Sam ba za ta bar gidan nan ba samun sau™in ki shine ki fahimci abin da zan gaya miki,domin ba ni da nufin na cutar da ke duk abin da yake faruwa na yi ne don ke."

Ja da baya ta fara yi tana mishi wani irin kallo,sai ta kalli ta ta kuma ™ara kallon sa kawai sai ta sha™e shi.

" Na shiga ukuna ni Zainab zuciyata ,za ta buga A.m zai kashe ni,ka da son yara da kake yi don kawai ba na haihuwa ya sa ka naimi Juwairiya ka haihu ta zina! Tur mai za ka yi da Wan zina kuma ya fito ta jinin matsiyata."
Sai kuma ta sake shi ta nufi kanta tana faWin."Wallahi saina kashe ku iyaye sun dan™aramin dukiya,shine za ku din ga zina akan gadona har ku samu ciki h."

" Ya ishe ki Zainab! Kar ki ™ara ai banta min yaro,kin san halina ba zan taSa aikata zina."

Ya buWe baki zai gaya mata matsayinta sai ya kasa ya sunkuyar da kan shi ™asa,yayin da tsananin tausayi ya kamasa ganin yadda ta koma kalar tausayi tana kallonsa.

" Ki fahimce ni Zey ke san ba zan taSa haWa ki da..."
" Ba na son ji! Ba na son ji!! Mayaudari munafiki mai al™awarin banza.Tur da na aureka na yi nadamar ranar da na ce ina sonka,kar ka matso kusa da ni in ba haka ba kashe ka zan yi!"
Ta faWa tana girgiza kanta tare da toshe kunninta ganin ya nufi ta zai ri™e ta.

" Wannan dalilin ya sa na yi duk iyakan ™o™arina na fahimtar dake."

Ya ce da ™arfi ya na kallonta sannan ya ci gaba da cewa." To tun da ba ki bani dama ba,bari na gaya miki gaskiya..."

Katse shi ta yi da ™arfi tare da ™ara cakume shi ta ce." Mai za ku gaya mini mai kake son kace?Abu Waya na sani cewar mijina A.m ya na kwana tare da ´ar aikina,wallahi kaf duniya sai sun ji don a jarida zan buga,A.m ya yi ma ´ar aikina ciki za su haifi Wan shege Wan zin."

Wani irin sha™a ya kaima wa da ya sa ta ji numfashinta zai Wauke.
" Kar ki ™ara aibata min ciki Wan dake cikinta halastacce ne kuma ta aure muka same shi,don ban san ta ba a matsayin ´a mace ba,sai da aka karSar min aurenta."
Ya zaro idanun sa ganin ba ta fahimci abin da ya faWa ba." A ta™aice Juwairiya matata ce ta sunna wanda Daddy ya karSar min aurenta! Don haka karki ™ara aibanta min yaro don wallahi sai kin gane baki da wayo."

Kawai gani ya yi ta sulale a ™asa ta faWi sumammiya.Da sauri ya yi kanta ya na kiran sunan ta.

Gabaki Waya ya ruWe ya rasa ta in da zai fara rungumeta ya yi cikin tashin hankali sunanta kawai yake kira.

Da gudu Juwairiya ta shiga kicin ta ibo ruwa ta watsa mata,amma sam ba ta farfaWo ba jikinta ya yi Wip kamar babu rai a jikin.

" Zainab don Allah kar ki mutu ki barni ba zan iya rayuwa ba,in har babu ke a cikin duniyar nan,ki tashi na yi miki bayanin na aure ta ne don ke,don Allah ki buWe ido.



A.m yake faWi ya na jijjigata cikin tashin hankali." Ya kamata a kaita asibiti fa kar ta mutu."

In ji Lantana da take kallon tashin hankali wanda ba' a saka mishi rana.


A.m ya mi™e daidai lokacin da Lantana ta ruga kiran direba,don ya kasa komai sai zare idanu da yake yi.

Zubbur ya ga ta mi™e tare da sakin wani irin ™ara wanda sai da gidan ta girgiza,kawai sai ta saki dariya kamar sabon kamu.
Wani ihun ta saki da ™arfi ta yi kansa ta na faWin." ˜arya kake yi wallahi ni kaWai na tashi a gidanmu na rayu ni kaWai ban taSa sharing Win wani abu ba,sai kai abin da nafi so fiye da komai a rayuwa.Ina hakan ba zai taSa faruwa ba!"

Ta ™ara ri™e shi ™am ta ci gaba da cewa.˜ila mafarkinmu duniyar mahaukata ya kawo mu,don na lura kai kanka ba ka san mai kake faWa ba,don wata™ila baka cikin hayyacin ka."

Mari ta kawo mishi cikin zafin nama ya kauce tare da ri™e hannunta,ya zare idanun sa ya ce."Tabbas bari na ™ara gaya miki ita Win matata ce,gaskiya kunninki yake gaya miki,kamar yadda igiyar aurena uku yake a kanki,haka ita ma amma ki tsaya ki sauraare ni,kin san ina sonki ba zan yi abin da zai cutar dake ba. na aureta ne don na..."

"Kai."

Ta daka mishi tsawa da idanunta da suka rine sukai jajur!Saboda tashin hankali.

" Karka gaya min maganar banza ka rabu da ni macuci ha™i™a ka cuce ni,ka kuma yaudareni.Ka manta ka yi min al™awarin ba za ka taSa min kishiya ba,balle ka sanar da ni ce ba na haihuwa shi ne yau ka auri wata mace ban sani ba,kuma saboda cin mutunci ka kawo ta gidana ka na kwana da ita a gadon da iyayena suka siyar mini,wallahi mafi girmar kuskuren da ka yi ka kawo ta gidana,ka maida ni banza shashasha sauna! Ashe in bana nan sakewarka kake da ita?Har kana mini munafucin baka ri™e sunann ta ba.


Wayyo Allah na! A.m ya maida ni banza ya kawo matarsa gidana a matsayin mai aiki!Wace irin banza ne ni har na kasa gane tsakanin su?

Wallahi sai kun yi nadamar abin da kuka yi mini,zan nuna maka cewar da gaske ba a yi ma family Winmu kishiya,take yanzu zan kasheka in kashe kaina haka kuma in kasheta!Mutuwar kasko za mu yi daku,ban taSa sharing ko da wani abu ba balle na haWa jiki dakai ™azami kawai."

Da gudu ta ruga kicin kafin ya farga har ta Wauko wu™a ta yi kansu ta na faWin." A yanzu za ayi ta ta™are yanzu zamu yi mutuwar kasko,hisabi akan abin da kuka yi mini zan yi muku tun kafin aje lahira ku haWu da ubangiji,munafuki mai karya al™awari."

" Zainab ki ki natsu karki aikata dana sani! Look Zainab kar ki aikata abin da kike son yi,sheWan ne yake so ya kaiki ya baro,don Allah ki natsu zan yi miki bayani,ina da dalilin da ya sa na Soye miki auran."

Kallon mahaukaci take mishi ta tsaita wu™ar daidai gurin Juwairiya tana matsawa kusa da ita.
" Saina nuna miki kuskuren da kika yi mijina za ki aura,kin yi babban kuskure ni kaWai nake rayuwa a gidan mahaifina,haka dangimmu kaf babu wata mace da aka yi wa kishiya sai ni?Wallahi ba ku isa ba,sai na nuna muku kuskurenku."

Gadan-gadan ta yi kanta data tsorata ganin ta nufo ta da wu™ar,Soyewa ta yi a bayan A.m da hankalin sa ya tashi matu™a,saboda yadda Zainab ta koma za ta iya yin komai.


" Zainab kar ki kashe musu ´a za ki yi dana sani fa shari'a ba za ta ™yale ki ba kema kashe ki za'a y."

"Don na kashe ´ar matsiyata uban wa zai taSa ni na san ko an kulle ni Daddy zai fito dani."Ta bashi amsa idanunta a bushe.

" To ni in kika kashe min Wa wallahi saina kulle duk yan gidanku ba ke ba,saboda ko ba komai zan ga Wana a duniya na rungume shi iyayena su yi alfahari da hakan."Ya ce mata cikin zafi da Waga murya.

Kukan kura ta yi taho kan kanta da gudu jin abin da ya faWa,yayin da idanunta suka rufe ba ta ji ba ta gani.

" Yadda ba na haihuwa kai ma ba za ka taSa ganin Wanka ba,saboda kai na lalata mahaifata,don na faranta maka shine za ka auri wata,wallahi baka isa ba."

Da sauri ya cakume ta ya ri™e ™am iya ™arfinsa ganin abin da take shirin yi.

Juwairiya ta sada™ar mutuwa za ta yi lokacin da ta yi kanta da wu™ar.Ta rintse idanunta tana salati.

FuWuwa suka yi a ™asa ita da shi ya fara kiciniyar karSe wu™ar.
Sai kawai ta kai mishi wukar jikin shi Allah ya ba shi sa'a ya kauce,wu™ar ta yanki hannun sa sosai.

Ba Juwairiya kawai ba hatta wanda ta yi yankan sai da ta Wan firgita ganin irin jini da ya fara tsartuwa a hannun sa.

A.m ya kira sunan Allah da ™arfi ya ji wani irin raWaWin azaba yana ziyartar sa,jikin shi ne ya kama rawa ganin duk da yankar da ta yi masa,jini na zuba amma ba ta razana ba,sai ta nufi Juwairiya da ta yi kan sa ta kama hannun sa tana kuka,mai haWe da salati matu™ar tsoro ya shige ta ganin abin da ta yi.

" Ai na gaya muku wallahi sai kun gane kuskuren ku na cuta ta da kuka yi!"Ta faWa lokacin da ta yi kanta.

Da sauri A.m ya mi™e ya saka ™afafun sa ya taWiyeta ta faWi yarab!Amma da ™arfin hali duk da buguwar da ta yi,sai da ta ™ara nufo ta da wu™ar.

˜ara hankaWe ta ya yi za ta faWi ya tare ta bayan wu™ar ya faWi gefe.

Ta saki ihu tana zage-zage kamar wata mahaukaci.

Da ™arfin tuwo ya ri™e ta tare da yin dubara ya sakata a cikin Waki,sannan ya jawo ™ofar ya kulle.

Wayar sa ya Wauka ya kira Mominta don ita kaWai yake tunanin za ta shawo kanta.

Zuciyar sa a fusace ya ja hannunta suka fita,a cikin mota ya saka ta sannan ya shiga ya ja.

A.m dake tu™i gabaki Waya hankalin sa ya tashi ™warai,ko a mafarki bai taSa tunanin abin da Zainab za ta yi mishi ba,duk da daman ya san zai sha fama da ita.

Ya juyo yana tu™i da bai san in da za shi ba ya kalle ta,sai ya ga ta dun™ule jikinta hawaye yake turereniya a fuskarta,kamar rawar sanyi take yi ganin yadda ta takure lokaci guda.

Ya sani cewa ya tono ma kan musamman in iyayen sa suka ji abin da ke faruwa,don ya san Zainab sai ta fallasa komai.

Guri ya samu ya samu ya yi parking ba tare da sanin abin da zai yi ba,ya kwantar da kan sa a jikin sitiyarin Win.

Karo na farko yau ta ga karaya a fuskar shi tun iya rayuwar da suka yi ba ta taSa ganin abu ya saka jikin shi ya yi sanyi ba,ko da kuwa Baba ne Sani da ta lura ya na matu™ar tsoron shi,amma yana Soyewa,sai ya ba ta tausayi sosai.

Ta kalli hannunsa da yake tu™i jini duk ya Sata in da ya ri™e kuma ya na ta zuba,kawai sai ta saka kuka tare da cire Waukwalin da ta Waura,ta kama hannun za ta Waure.

" Asirina ya tonu ko kaWan ban taSa tsammanin

Please Login or Register in order to submit comment