Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi matuar burge Mama wani arin burgewa ta baje akan tabarma har ta na cire hijabin ta da Wankwalinta.

Hakan ya yi matuar ara burge Mama sai ta ara jin ta saki jiki da ita tace."Bam ma sanki ba yarinya,amma da na ganki da Mariya ar maocin mu na gane kece wacce aka yi maganar aiki da Juwairiya..."

"Ni ce Mama tabbas ni ce ina ta jiran ta ba ta zo ba,sai da ga ba ya Mariya ta zo tace min kin hana ta "Tace tare da atse Mama ba tare da ta kai aya ba.
"Haka ne gaskiya aikin nan ki nemi wata kawai."Mama tace ta Wan canza fuska kaWan,ganin haka sai jikin Anty Naja ya yi sanyi amma saboda ya ba hankalin da ta yi na Juwairiya ta kasa hauri tace."Don Allah Mama karki hana ta wallahi ba ni da matsala da ga ni har mijina,kuma in kina tunanin kwanan da za ta yi ne mijina ba zama yake ba wani lokacin ni kai na sai na yi bacci yake dawowa."

Ta matsa kusa da Mama tare da rie hannunta ta yi rau-rau tace."Don Allah Mama kar kice a'a ban Wauki Juwairiya a matsayin me aiki ba anwa ce a gareni,kuma duk ranar da kika ga wani abu ya faru mara daWi a tsakanin mu ki hana ta zuwa."

Ta yi shiru ko Mama za ta ce wani abu amma sai ta ga ta kauda kanta ta na tunanin wanda ba za ta iya cewa ta yanke ta barta ko a'a."Kin ji Mama ki amince don Allah!Na yi masu aiki da dama amma basa iya rie min amana,bayan haka sace-sace suke min."

Duk maganganun da take yi ba ta ce mata komai ba,aranta ta na tunanin karta amince a za a sami matsala da Baba Sani duk da shi ma ya na da laifi,in da ace ya na taimaka musu da ba za ta yi aiki ba.
'Ki na ji Mama da ban so na gaya miki wani sirrina ba,amma nuna amincewar ki ya zama dole na sanar miki domin ki taimakeni ki ceci aurena.Mai aikina mijina ya kama ta da yarana tana basu kirjinta suna tsotsa ita kuma ta na saka musu hannu a gabansu.Hankalinsa ya tashi warai ba yan ya mia ta ga hukuma ya kawo su asibitin da nake aiki,hankalina ya tashi warai na yi kuka kuma mun yi rikici da shi daga ba ya yace dole na bar aiki ko mu rabu.Ina son aikina saboda da shi nake taimaka iyayena,sannan ina son aurena na yi-na yi a dai na saka ni aikin kwana amma ba zai yiwu ba.

Mijina ya bani zaSin na bar aiki na kula mishi da yaransa ko ya rabu da ni,domin yai barin na ara Waukar me aiki.Mun yi rikici da shi sosai daga baya ya haura na samu mai aiki amma daga wannan ya kama ta da wani matsala zai rabu da ni."Tace cikin hawaye ta ja numfashi sannan ta Wora da cewa.

"Mariya ita ta ja ra'ayina akan Juwairiya saboda ta gaya min ta na da hankali,da yar na ami 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~nce da na ganta na yadda da maganar Mariya ki taimake ni Mama in har kika amince zan zama tamkar arki,zan taimaka ma rayuwar ku."

Jikin Mama ya yi sanyi sosai har ba ta san sanda ta amince ba jin aure na shirin mutuwa,duk da watarana ita ma aure za ta yi."Na amince Allah ya kyuata amma ar nan ya kamata ku din ga kiyaye wa,ni ma matsalar ba daga gareni ba ne a kwai anin mahaifinta ba lai-lai ba ne ya amince amma ta fara mu gani."

Sosai ta ji daWi ta buWe jakarta ta ciro dubu ishirin da biyar tace."Ga kuWin ta na wata biyu dubu ishirin sai ki fara koda sana'a ne,sannan dubu biyar na baki kyauta kuma gobe in Allah ya sa tazo za ta taho da tsao."

Mama ta ji daWin kuWin da ta bata ta na ta murna da saka mata albarka har ta yi mata sallama,ta kama hannun Juwairiya tace."Sis sai kin zo gobe ko?Don Allah ki zo da wuri anninki suna ta maganarki."Tace tare da shafa kanta.
"Gaskiya ta na da kirki sosai."Mama tace ta na juya kuWin da ta bata,sai kuma ta aje kuWin ta kalleta tace "Kin san me ba zan taSa kuWin nan ba sai mun ji me Baban ku Sani zai ce."Da sauri ta mie kawai ta na faWin."Ki ba ni naje na yo miki sare-sare ki fara sana'a ni fa ko me zai yi sana yi aikin nan,tunna shi ba taimakon mu yake yi ba don haka ba shi hurumin da zai hana mu."

Ta yi maza ta fice daga Wakin kafin Mama tace komai sam ba ta jin tsoron abin da zai ce in dai ba kasheta zai yi ba ta rantse sai ta yi aikin.

Kamar yadda ta gaya mata mijinta ba mazauni bane haka kuwa ta gani,don tun da ta fara aiki ba ta gan shi ba sai tanamemen hoton su da yake manne a falon wanda tun da taje ranar da Mariya ta kaita ta gan shi a hoto,wannan dalilin ya sa hankalin ta ya kwanta ko da ta ga Baba me aiki aikin ta take yi ta tafi ba ta kwana.

Ta na aikin ta cikin kwanciyar hankali ga abinci da take ci kullum taci mai kyau ta sha mai kyau,don Anty Naja ba ta da rowa ko nama taci sai ta rage mata saboda yadda Juwairiya take kula da yaranta ga ta da tsafta ko ina na gidanta tsaf ya na tashin amshi.

Kusan sati biyu ta na aiki cikin jin daWi kuma har zuwa wannan lokacin Baba Sani be dawo ba,kullum in dai za ta dawo Anty Naja na sawa a yi girki da su ta saka mata a kula kuma da yawa,don haka ba sa matsalar abinci ga Wanye da take badawa a kai ma Mama in dai za ta yi aikin kwana.

Ranar Juma'a da safe bayan ta gama aikin ta ta shirya musu abincin karyawa ta ibi nasu kamar yadda ta yi mata umurni,kasancewar ta gama aikin kwana za ta yi hutu har ta bawa Juwairiya hutun kwana biyu.

A hanya Juwariya ta na tafe ta na ta yi mata addu'a don tsakanin su Allah ne kawai zai biya ta,saboda irin kyautata mata da take yi fara aikin ta ta bata kaya masu kyau sosai da abin alheri ko hijabi kala biyar ta bata,sannan ko bai ta yi bata ce mata me aiki sai dai tace ar'uwanta ta na da matuar kirki sam bata nuna wani abu ko rashin mutunci.

A dai-dai ofar gidan su ta tsaya cikin firgici ganin Baba Sani ya Ware kan motar sa ya na rie da atuwar bulala,sai juya ta yake ya na zare ido ransa a Sace da ga ganin yadda ya Waure fuska alamun ba mutunci.



Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na bakwai.Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE)

Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA BAKWAI*



Tsananin mamaki ya kama shi ganin yadda Juwairiya ta gan shi amma sai ta yi tsaye ta na kallon shi, ba tare da nuna wani tashin hankali a fuskar ta ba ko tsoro.

Ya Wan are mata kallo cikin mugun nufin sa amma sai ya ga duk da ramar da ta yi,ta ara mishi kyau Wan tafiyar da ya yi.

Juwairiya da tsaya ko zai ce wani abu amma ganin ya yi shiru,ya sa ta nufi hanyar shiga ofar gida za ta shige.Da dauri ya sha gaban ta a ransa ya na mamakin dai na tsoron shi da ta yi,tun ranar da ya nemi haWa jiki da ita.
"Da ga gidan uban wa kike?"
Ya tambayeta da fuskar shanu y na zare mata idanunsa da suka kaWa suka yi ja,saboda tsabar fitina da ya saka ma kansa.Ta Wan ja ta tsaya tare da matsawa nesa da shi ganin yadda ya matso daf da ita.

"Ba na hanaki yawon maula ba,shi ne don kin ga ba na nan kika mai da shi sana'ar ki?"Ya tambayeta tamkar zai kai mata bugu.

"Ni ba maula naje yi ba,aikatau na samu nake yi domin na ciyar da kammu."Ta faWa mishi ba tare da jin tsoro ko shakku a ranta ba.

Wani irin azababben mari ya wanka mata wanda ya sa ta yi taga-taga za ta faWi,amma ta dake duk da azabar da ta ji kamar za tai fitsari a tsaye sai ba ta nuna mishi ba,don a shirye take ta shirya tsaf!Ko kasheta zai yi.

Matuar mamaki ya kama shi wai yaushe ya yi sake har ta raina shi haka,amma sai ya ara Waure fuska yace."Na ga kwana biyu kin raina ni Juwairiya saboda na nuna miki manufa ta a kanki,to wallahi har yanzu ina kan baka na saina cika muradina gara ma ki amince ki sami maslaha a rayuwarki."
A wannan lokacin ta ji wasu tagwayen hawaye sun cika mata fuska,zuciyarta ta amince da lai-lai shi ba mutum bane don ta yi tunanin rasuwar mahaifinta zai saka ya haura da udirin sa.

"Ka sani ko mutuwa zan yi ba zan lamunce ka biya buatar ka a kaina ba!Ina matuar kaico a rayuwata da ka fito a matsayin anin mahaifina.Ko mutuwa zan yi sai dai na mutu."Tace mishi ta na oarin shigewa gida.

Sororo ya yi lai-lai ya yi sake tunna har taga wallar shi ta na faWa mishi mugayen kalamai,masu tsauri a cikin idanunsa ba tare da shakku ko shakkar sa ba.

"Tun da kika ce haka mu zuba ni dake,bari na tuna miki akan ki zan iya komai tun da kika girma na Wora kwaWayina akanki Ki kuka da kanki zan iya komai don na cimma manufata."

Ta buWe baki za ta yi magana wani irin takaici ya toare mata maogaro,sai hawaye da suka fara turereniya a fuskarta da ta tuna anin mahaifinta yake mata wannnan halin,sai ta ruga a guje ta shige cikin gida ta na kuka.

Mama dake oarin hura wuta a murhun gawayi idanunta duk sun yi ja, suna zubar hawaye saboda wutar tai kamawa sai saka leda take yi.Sai ganin ta ta yi ta shigo da kuka ta shige cikin Waki ta buWe baki da nufin ta yi magana,duk da cewa ta san dalilin kukan saboda ta ji dirin motar sa sanda ya dawo sai kuma ga shi ya shigo.

"Saboda ba na nan shi yasa kika saka ta ta na yawon maula ta samo muku abinci ko?Na rasa wani hali kike so ki koya mata shi yasa na tsaneki saboda mugun halinki."
Ta yi shiru ba tace komai ba dama Wabi'ar ta kenan duk sanda zai yi mata rashin mutunci ba za ta tanka ba,haka ma yanzu mutuwar Yayan sa bai saka ta canza ba.
Har ya gama bambamin sa ya fice bata ce ala ba,amma ta na jin gara su haura kawai da tashin hankalin da zai jawo musu.Bayan ta gama kukan ta ta share kamar kullum don Mama ba za ta taSa lallashinta ba.

"Juwairiya ina ganin a haura da aikin nan kawai."Tace cikin unar zuciya ta na kallon ta."Gaskiya Mama sai dai kiyi hauri,amma ba zan haura tunna shi ba taimaka ma na yake ba."

"Amma kina ganin tijarar da yake mana ko?Kin san halin shi ba shi da kirki,ni fa bana son tashin hankali ya dinga jibgar ki a banza."
Juwairiya shiru kawai ta yi a ranta ta saka komai zai faru sai dai ya faru,amma aikin Anty Naja yanzu ta fara.Hankalin Mama ya tashi da safen ranar da ta gama hutun ta bayan Juwairiya ta yi sallah ta tafi aikin ta,ba ta kula da kiran da Mama take wala mata ba.

Da yamma da ta dawo Baba Sani ya shigo da bulalarsa ya yi mata duka,har bata iya tashi amma ba hana washegari ta koma aikin ta ba.Ganin irin dukan da yake mata Mama ta hana ta aikin,sai dai wannan karan ta bijire ma umurnin ta don ta rantse ko kashe ta zai yi ba za ta bar aikin ba.

Tsakanin ta da mijin Anty Naja ba ruwanta da shi tun da ta fara aikin so uku ta gan shi,duk sanda ya shigo ya ga yaran a kusa da ita sai ya fara musu faWa ya kora su cikin Waki ya na harararta ya na mazurai,a yadda yake mata ta lura ya matuar tsorata da halin masu aiki.

Ganin haka ta ara kame kanta ta na mamakin yaran duk da suna zuwa islamiya amma ba su wani iya karatu ba,don ko babban dake da shekaru tara ko alhamdu bai iya cikakka bare ya damu da sallah ba,sai kallon catoon da suke yi kullum ba auautawa,ganin haka ta dage da koya musu da saka su su yi salla,abin da ya ara saka Anty Naja son ta a cikin zuciyar ta.

Ganin an canjin da yaransa suke samu abin ya burge shi har yake amsa gaisuwar ta a sake,wani lokacin har kyauta yake mata na kuWi yace ta kaiwa mahaifiyarta don Anty Naja ta gaya mishi mahaifinta ya mutu.

Kusan kullum Juwairiya ta dawo sai taci na jaki a gurin Baba Sani jikin ta duk shatin duka ne,amma hakan bai saka ta karaya ba ta ci gaba da aiki don yanzu suna ci ga Mama dake sana'ar ta rayuwar su ta na tafiya cikin rufin asirin Allah sai dai takurawar da Baba Sani yake mata,wanda hakan ya na damin Mama ga shi tai ta dai na aikin.
A haka rayuwa take gara musu yau fari gobe tsumma,yayin da kullum burin Baba Sani ya cika burinsa amma Allah bai ba shi damar ida mugun nufin sa a kanta ba.Ganin haka sai ya Sullo mata da nuna mata kuWi ya na jan ra'ayin ta akan ta amince mishi ko sau Waya ne,amma tai duk ta gan shi sai ta nemi tsari da sharrin sa don ganin sa take kamar wani sheWani.

Ta Wauki tsawon shekaru biyu ta na aiki a gidan Anty Naja,a lokacin ta girma ta ara wayewa ga hankali da natsuwa kullum cikin hijabi take bata cirewa sai in mutanen gidan ba sa nan,ko ita Anty Naja ba za ta ce ga yanayin jikin ta ba,don tun kafin takai haka da Baba Sani ya saka mata ido ta yi tunanin ko jikinta yake ruWarsa,bare yaanzu da ta zama an mata ta cika ta batse ga Anty Naja da take ba ta kaya masu kyau kuma ta ba cin me kyau,har mai na shafawa da na wanke kai take siyar mata.
Maza da dama sun sha bayyana soyaryarsu gurin ta wasu kuma suje gurin Baba Sani,amma sai ya taarare yace Juwairiya ar mace ce sannan ba ta da kamun kai har kwana take a waje.Ya faWi mugun abu da ba ta mata suna ya gaya musu,wasu suna jin haka za su tafi wasu in suka nace ya yi musu korar kare don ya rantse,in har ba ta amince mishi ba to ita da aure sai dai ta ga ana yi ko kuma in ya mutu.

Juwariya yarinya mai kimanin shekaru sha tara.Ta na da haske amma ba can ba,fuskarta mai kyau irin zagayayen fuska gareta,da dogon hancin ta haoran ta masu kyau ga ar wushiryar ta a tsakiya,wanda in ta yi dariya yake ara ma kyau matua!Da dimful Winta.Bata da jiki amma a kwai shafe sannan doguwa ce ba can ba,amma ta na da tsawo wanda yake ara mata kyau.

irar jikinta me kyau ne ko ita ta na alfahari da hakan wato irin jikin nan ne mai Waukar hankali waWanda ko wane namiji yake burin samu mace mai irin sa.Wannan dalilin ya sa kullum take cikin hijabi do ko awayenta suka shigo suka gan ta ba hijabi,sai su yi ta zuzuta ta su na yaba kyawun jikinta.

A wata ranar litinin da safe bayan mutanen gidan sun gama karyawa suka wuce gun aiki,kasancewar da garin a kwai zafi sannan Anty Naja ta tura mata da tsako a cikin wayarta me botira da ta siyar mata,don ta din ga kiran ta ko kuma in ta tafi aiki da wuri ta gaya mata abin da za ayi,don yanzu girkin su ya dawo hannunta saboda Baban Abnaj yafi son girkinta.
Waina da miyan karas za'a yi da farfesun rago,ganin ta na da aiki ya sa ta zage damtse ta na yi tun ta na cikin hijabi har ta cire ta na ta aikin ta,ta kunna wayarta ta na sauraron karatun kur'ani cikin suratul ma'ida.Ta shafa'a ta na ta aikin ta sai anwar Abnaj mai suna Ibtihal ta danna remote ta Sata saitin tibin,Abnaj Wan shagwaba ya saka kuka ya zo ya na sanar da Juwairiya akan ta zo ta gyara musu.

Hannunsa ta kama suka nufi falon da nufin ta gyara mishi,ta na tsaye a gaban tibi ta na ta oarin yadda za ta gyara amma ta kasa gashi ita ba ta san yadda ake yi ba,sannan gashi har sun fara kuka akan a gyara musu.
A hankali ya buWe ofar ya shigo da sallama a bakinsa,Juwairiya da hankalin ta ke kan tibi ba ta san ya shigo ba,ko in ce dukan su sai bayan ya Wauki tsawon lokaci ya na kallonta cikin mamaki a ransa ya na mamakin dama a kwai wannan halittar a gidan sa?Don shi zai rantse bai taSa mata kallo ko na sakan bane ya san dai ta na da kyau a fuska.

"Oyoyo Daddy!"Abin da yaran suka ce kenan wanda ya Wauki hankalinta ta mie a razane ta yi diri-diri,tamkar za ta shige cikin asa yayin da wani irin kunya ya lulluSeta.
Ganin yadda ta diririce sai ya shige Wakin sa akan ya Wauko abin da ya saka shi ya dawo saboda mantuwa da ya yi,wato wasu fayal da ya ije da nufin ya tafi dasu sai gashi ya manta da su kuma ana buatar su.Ashe da rabon ya yi gam da katar!Don shi ya ga matar aure dama tuni ya yaba da hankalinta.

Ko da ya shiga cikin Wakin wani irin kasala ya ji y rufe shi ya faWa kan gadon shi ya na jin wani irin shauki na ta ya na zagaye ilahirin jikin shi.Ko da ya shiga Wakin faWa kan gadon sa ya daWe ya na jin wani girmar lamari har na tsawon lokaci,sannan daga bisani ya mie ya Wauki fayal Win ya fito.

Kawai sai ya tsinci kansa da bin hanyar kicin Win ya Wan tsaya nesa da kicin Win zuciyar sa na bugu da arfi,take yake jin lamura suna sauya mishi har ya fara dana sanin dawowar sa gida gashi komai na son ya canza musamman akan yarinyar da take ba shi girma

"Abnaj fito na gyara muku tibin ku barta ta yi aikin ta,kun dame ta da surutu."Yace da yaransa da suke kicin Win suna ta zuba da Anty Juwairiya kaza,ita kuma ta na ta yi musu dariya ba yan ta basu kwan da ta soya musu.

Yaran suka bi shi suna murnar zai gyara musu tibi,bayan tafiyar sa ziciyar Juwairiya ya buga dam!Da ta kalli wayar idanunsa cikin rashin sani ganin yadda ya kafa mata idanu lokaci guda,abin da ta hango ya matuar tsorata ta wanda bai yi kama da so ba sai tsantsar sha'a warta da ta hango.In ko haka ne abincin ta ya are a gidan.

Bayan fitar sa ta Waga labule ta na kallon farfajiyar harabar gidan,sai kawai ta ji hawaye ya na sauka a kan uncinta bai yi kama da mutumim banza ba saboda ya na da dattako.To me wayar idanunsa suke nuna mata?Ita kuma irin na ta jarrabawar kenan?




Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na takwai.Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA TAKWAS*


Tun daga wannan ranar Juwairiya ta ga canji a tattare da shi,ya sakin mata sosai kuma ya na matuar kyautata mata,ko hira yake da matar shi sai kiji ya tsoma ta ciki yace"Wai haka aka yi Juwairiya ita za ta faWi gaskiya."

Ranar da ya fara mata hakan ta yi matuar razana ta kalli Anty Naja ta ga ko me za tace amma sai taga sai dariya take ta na jin daWi har ta na ara tambayar Juwairiya,wani tsabar takaici kaWa kanta kawai ta yi ta shige kicin Win wanda dama shi ya wala mata kira don kawai ya tambaye ta.

Bayan sati Waya sai gashi ya dawo gidan da wuri da yake a ranar matar sa na gurin akin ta na night duty acan za ta kwana.Bayan ya yi sallar magariba ya kulle ko ina na gidan ya shigo,tun da taga ya dawo da motar sa ya wuce masallacin kofar gidan sa gabanta ya faWi hankalinta ya tashi,domin ita canjin da ta gani a gurin sa ya na tsorata.

Bai fito ba ya na karatun kur'ani har kiran sallar isha ya tafi masallaci,sannan bayan ya yi sallah ya dawo ya zauna a falo shi da yaransa suna kallo shi kuma ya na aiki a laptop Win sa.
"Abnaj je ka kira min Antyn ka Juwairiya kace ta zo ta bani abinci."Yace mishi ba tare da ya kalle shi ba,burin sa ya ganta ya san ta Soye kanta a Waki don kar ya ganta.

Yaron ya ruga da gudu zuwa can ya dawo yace."Ga ta nan zuwa."Ya ci gaba da kallon sa bata jima ba ta fito da dogon hijabin ta har asa.Ita sai yanzu dake matuar dana sanin gadin mijin wata da yaran ta da take,don a a kwai haramcin haka a cikin addini mace baliga da namiji ba muharramai ba dama na ukun su sheWan ne.

Nesa da shi ta tsaya kamar za ta yi mishi magana sai kuma ta juya ta shige kicin ta Wauko abincin shi ta ije mishi za ta juya."Ba kiji ba Juwairiya."Yace da ita ganin za ta shige Wakin da take kwana har ta na haWawa da gudu-dugu.

Tsayawa ta yi bata re da ta juyo ba ta na watsa da yatsun hannunta gani take kamar zai haie mata kamar yadda anin mahaifinta ya yi mata,amma sai ta ga ya araso ya tsaya Wan nesa da ita ya mia mata sabuwar waya mai kyau a kwali ya Wan daure fuska."Ga shi na ji Antynki tace Abnaj ya saka miki waya a ruwa ta lalace shine na hutar da kuWin ta,amma fa ki kiyaye ki dai na basu don nan gaba in kika bari suka lalata sai na haWa da bulala kafin na canza miki wata."Yace ya na kashe mata ido.
Zare ido ta yi ganin wayar da ya siya mata irin wanda take gani a hannun su masu kyau da tsada,ina ita ina wannan wayar ta na ar gidan Malam Shehu kuma me za ta ce ma Anty Naja."

Kamar ya san me take tunani sai ya kaWa kansa yace."Karki damu na san me

Please Login or Register in order to submit comment