Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa Juwairiya na sona sai dai ba ta san irin namijin da ya kamata ta so ba,duba ga ni ba ajin aurenta ba ne kuma babban goro ai sai magogin ™arfe!Don haka ina kan baka na."

A.k ya ja motar sa ya fice ba tare da ya ™ara ce masa komai ba.

Zainab zaune a Waki ita da ™awarta Nabila suna hira,wacce ta yi takakkiya ta taho Zariya tun daga Abuja,saboda kiranta da ta yi tana kuka ta gaya mata abin da ya faru.

Nabila da ta gaji ta Wauko gajiyar hanya tana zaune akan gadon Zainab abinci take ci.

Wayar Zainab ta yi ™ara kusan sau goma na kiran ta,amma sai ta™i Waga wayar daga ™arshe kashe wayar ta yi ta wurgata can gefe a fili ta furta.
" Maye kawai mazinaci."

Ko da ba ta gaya mata ba ta san wanda yake kiranta.

" Yanzu kin tabbata abin da na ke gaya miki ko kin yadda namiji buhun ™aya ne? Wai ki gaya min ta ya akai kika gane suna cin amanarki?"

Zainab ta saki tsaki ta kalle ta da Sacin rai ta ce." Ni ba wannan ba ina acid Win da nace ki taho min da shi?"

" Karki damu tsa™on ki yana ije a jakata amma don Allah ki gaya mini,ya akai kika gane bayan duk kin Wana musu tarko sun tsallake?"

"Wani magani na tsinta a cikin drower ta A.m ya na sha na Waukar ciki da wuri."

Ta ce cikin damuwa yayin da idanunta suka kawo ruwa.

" In yana shan maganin haihuwa to meye hujjarki ko kina tunanin,A.m zai so ya haifi Wansa ta zina bayan ga matar sa ta sunna?Sannan ni ban ga abin da kika faWa a matsayin shedar suna cin amanar ki ba."

Ta faWa da tana kallon Zainab da ta yi tsuru-tsuru ta manta cewar,ba ta taSa gaya ma kowa ba cewar ita ce ba ta haihuwa,sai ta shiga in da in da daga ™arshe hannunta ta kama tare da fashewa da kuka cikin kuka ta ce

" Yau zan gaya miki wani sirri amma don Allah ko sauran ™awayen, ba na son ki gaya musu cewar na gaya miki ni ce bana haihuwa ba A.m ba,domin ya yi min al™awarin ba zai faWa wa kowa ba kuma ba zai ™ara aure ba."

Gwalalo idanu ta yi cikin mamaki jin abin da ta faWi da gaske ita ce ba ta haihuwa ba A.m ba.

Sai tsananin mamaki ya kamata ta shiga kaWa kai kamar wata ™adangaruwa zuwa can ta nisa ta ce." Har yanzu wannan ba hujja ba ce Zainab saboda wata™ila A.m ya na shan ™wayoyin ne don yana tunanin ™ila ™wayoyin Zai taimaka miki."

"Haba akan me za ki ce haka bayan na gaya miki cewar mahaifata aka yi min aiki aka cire.Kuma idan haka ne mai yasa ka bai gaya min ba"Ta faWa cikin ™osawa jin bin da ta ce.

" Wannan ma ba hujja ba ce har yanzu ba ki da hujja Zainab.Kina abu kamar ba likita ba bayan kin manta mahaifa takan ti™o a jikin mace ko da an cire ta,mata nawa ne suka haihu bayan a n cire musu mahaifa?.Musamman ke da baki taSa haihuwa ba."

" Wayyo Allah kin sani a ruWu in kin ce duk wannan ba hujja ba ce,to numbar A.m da na gani a wayarta shi kuma mene ne?"Ta ce da ita tana kuka sosai.
" Ba zan Sata bakina gurin faWa miki irin son da nake masa ba.Na ro™e ki kamar yadda kika yi min al™awarin za ki watsa mata acid ki taimake ni ki yi yadda muka shirya,ga bayanin in da take gidan kawunta wanda na samu labarin mahaifiyarta ta Sata."

"Ok tun da haka kike so zan yi amma na so a ce mun Wan ™ara lokaci,mu samu ™wararan sheda, yau Win nan zan cika aikin ki na koma Abuja bari na gama cin abincin.Ni™abi zan saka na watsa ma shegiya ki huta.

BARI NA YI NAN DON YAU BANI DA TACE WA LAMARIN YAFI ˜ARFINA.


KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu™atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ™ofa a buWe take na ™orafi gyara ko ™arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za™auran marubuciya,kuma ™awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ™ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 28*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Zainab dake shatatan hawaye ta karSi acid Win da ta mi™a mata,tana jin wani irin tsanar Juwairiya a ranta kamar ta je ta watsa mata da kanta.

Ganin Momy suka yi ta shigo tana murmushi a fuskarata ta zauna a gefen su.

" Humh ta yaro kyau take yi ba ta ™arko."


Ta ce tare da dafa kafaWar Zainab da har yanzu take Wigar hawaye,saboda gani take kamar a mafarki yake faruwa,ba ta taSa tunanin fuskantar haka da ga gare shi ba.

Ajiyar zuciya mai ™arfi ta saka tare da rungume Momy sai ta ™ara fashewa da kuka.

" Momy har yau na kasa yadda cewa A.m zai iya kula wata mace bayan ni,mace mara aji wanda ba ta da daraja a duniya duk cewar zargi nake yi amma in na tuna,sai na ji kamar na sha™e kaina na mutu."

Cikin kuka ta faWa da shagwaba gaba ki Waya ta haye jikin Momy tana shagwaba,sannan ta Wora da cewa.
" Ke sheda ce irin wahalar da na sha kafin ya amince da soyayyata! Yanzu sai wata aba wacce ban Wauke ta da ™ima ba ta shiga tsakanimu.Abin da ya yi min na ji na ha™ura da shi amma fa babu macen da za ta raSe shi,face na zama ajalin ta."

"Na sani ba sai kin Sata bakinki ba amm ni bana goyon baya akan acid Win da zaku watsa mata,saboda in har da gaske yake son ta zai iya yin komai don ta samu lafiya daga ™arshe kin ga ke kika rasa,amma da za ki bar komai a hannuna da sannu za ta gane kuskuren shigowa rayuwarki da ta yi sa..."

" Momy yanzu kina nufin na fasa watsa mata acid Win?"
Ta katse ta da tambaya tana magana da muryar kuka.

" Abin da nake so kenan in har zai yiwu kar ki manta ke ce ´ata Waya tilo da na mallaka, ta ya ya za ai na bar rayuwarki ta ™untata ki bar min komai a hannuna,mijinki kuwa sai ya gane bashi da hankali don wahalar da shi za muyi ki ™yale shi,zai gane ba irin ki ake wula™anta wa ba."

" Ai ni da nace ba zan kona gidan sa ba kawai ya sakeni na ha™ura da shi."Ta ce cikin shagwaba tare da ri™e hannunta.

" Ba ki da hankali mijinki za ki bar ma wata banza ´ar aiki? Ashe kishinki na banza ne tun da har za ki hau dokin zuciya ki kyale ma wata mijinki."


" Wannan karon Nabila ce ta karSe maganar da cewa." Momy ya kamata ta fahimci waye mijinta sannan kin san Zainab da ba™in kishi,ni har yanzu na kasa gane gaskiyar lamarin dake faruwa,amma ya kamata ta gwara A.m ta nisan ta kanta da shi har sai ya gane kuransa.

Zainab cikin zumSura baki ta ce." Ki bar shi da ni yake yi ba Anty Safna za ta tafi ingila ita da mijinta ba,bin ta zan yi na huta acan ba zan dawo ba sai na huta."

Nabila da mamaki ta kalle ta ta ce." Ki bar shi da ´ar aikin na ki Zey?"

" A''a na san cewa tun ranar da abin ya faru zai kore ta, so nake na gwara shi kin san yana masifar sona dole hankalin sa ya tashi."

Dariya ta yi ta ce." Haka ne ai bai kyauta ba amma yanzu Momy zuwana bai da amfani an fasa watsa mata acid Win?"

" ˜warai kuwa Nabila ku bar min komai a hannuna ita Zainab ta fita waje ta huta kafin muga abin da zai faru."

Haka kuwa aka yi washegari Nabila ta koma Abuja.

A ranar da su A.m suka yi nasara Zainab ta fito musu sun ga rashin mutunci,don tun A k na saka baki yana ba ta ha™uri ta dawo,har ya gaji ya koma gefe yana kallon A.m da ya yi kalar tausayi,kamar zai yi kuka yana ro™onta.

Cikin muryar sanyi ya ce." Ki fahimce ni tun lokacin da muka je ™asar waje aka yi miki aiki,na tambayi likita ya ba ni wannan maganin tunanina ko za ki iya haihuwa."

Kallon mayaudari ta yi masa ba tare da ta tanka masa ba,domin gani take ya ci uwar rainin wayo.

" Allah ki yadda da ni don Allah ki dawo Wakina zuciya da gangar jiki sun yi kewarki."
Ya faWa a raunane kamar zai yi kuka tare da kama hannunta.

Fisge hannunta ta yi ta harare shi tare da yatsina fuska." Ai ka gama tsarani wallahi gara ma ka fita harkata,domin zuwa gobe in sha Allahu na bar ™asar nan ba zan dawo ba saina huta iya son raina."Ta ce da shi tana kallon sa a yatsine

Wannan karon murya a Wage ya fara magana." Kar ki sake ki fita wata ™asa don ba da izinina ba,kuma in kika sake kika je Allah saina Sata miki rai"

" Ai kin banza kawai a suwa ai ni yanzu duk abin da ka zaSa a aurenmu daidai ne in ba rabuwa za mu yi na fi son haka,da na zauna da fasi™i wanda ba shi da aji ya rasa macen da zai kula sai ´ar aiki.."

" Ya ishe ki Zainab sau nawa zan gaya miki babu wani abu da ya shiga tsa™aninmu da ita kin ™i bani dama na yi miki bayani,ban taSa kallonta da nufin wani abu ba don ni ban ga abin da zan nema ajikinta ba,kar ki manta yawo take a cikin hijabi kamar wata ™onanniya.Yarinyar da ba ta da waye wa mai zan yi da ita...."

Zainab tsaki ta yi ta wuce kawai gani zai tsarata ya bita kamar zai shige cikin Wakin ya na faWin." Na gaya miki kar ki bar ™asar nan ba tare da izinina ba."

Garam ta kulle ™ofar saura kaWan ta haWa da hannun shi da ya kai da nufin ya kamo ta ganin za ta shige.

Bango ya kaima duka tare da kama kan sa ya ri™e.
A.k da ke zaune hankalin sa na kan waya amma a zahirin gaskiya yana jin bada™alar da suke yi ne,mamakin aminin na sa yake yi saboda ya saki da yawa Zainab ta raina shi sama ba ta ganin darajar shi balle ta girmama auren su.

Ganin ya nufi hanyar fita ya mi™e cikin ™osawa shi kansa ya gaji da zuwa biko,yana ji a ran sa ba zai ™ara rako shi ba don ya gaji da ruwan rashin mutuncin da yake kwankwaWa daga gurin Zainab da iyayenta.

A mota suna tafiya shiru A.m ya yi ™uta ya kalli A.k da hankalin sa ya na kan tu™i ya ce." Ka na jin wannan yar rainin wayon ko,wai wata ™asa za ta!Zainab ta raina ni matu™a ban san yadda zan yi da ita ba,amma in dai ta yi gigin fita waje Allah sai na hukuntata."

Shiru A.k ya yi ba tare da ya tanka mishi ba yana tu™in sa a ran sa cewa ya yi." Kamar da gaske zai iya."

˜aramin tsaki ya yi ganin haka sai A.m ya kama bakin sa ya yi shiru bai ™ara cewa komai ba,don maganar da yake masa kame-kame ne lamarin Zainab yana ba shi haushi sosai.

" Har yanzu ban ji kayi maganar Juwairiya ba."A.k ya faWa ba tare da ya kalle shi ba.

" Shiru ya yi ba tare da ya tanka ba duk da ya Wan daina jin zafin ta amma har yanzu yana jin haushin asarar da ta yi mishi.

" Ka rabu da ni da wannan shiriritacciyar ina maganar matar so wake ta matar shige,sai ka bari na gama da wanda zuciyata take muradi ba wata can ba."

Tuki A.k ya ci gaba da yi ba tare da ya tanka a bin da ya ce ba a ran sa shika Wai ya san me yake tunani.

Juwairiya ri™e da waya a hannunta suna kokuwa da Hauwa da ta rantse ba za ta kira shi ba.

" Hauwa ki taimake ni don Allah kada ki sa zuciyata ta fashe! Na san har yanzu A.m yana fushi da ni ne ha™urin zan ba shi."

Wani mugun kallo ta sakin mata ta ce." Wai ke ba ki da aji ne? Shi ya sa ya raina ki ya ke wula™antaki,Allah ya halicci mace da daraja mai girma a gurin Wa namiji in kika ba shi lokaci da kan sa zai kira ki,don haka ba zan ba da wayata ba."

" Wayata tana gidan sa babu ta in da zai kira shi kuma na san cewa ba zai taSa kirana ba,ko sau Waya ki bani na kira shi don Allah."

Ta faWa tare da marairaice fuska hawaye a kan ™uncinta.
" Bari na tura masa da tsa™on ha™uri daga gareki in har yana bu™atar ya kira ki zai neme ki,amma ba zan bari ki kira shi ba nuna son da kike masa ya yi yawa shi yasa yake gasa miki gyaWa a hannu.

Sai ta koma ta zauna ta zabga tagumi da kalar tausayi har hanzu hawaye na turereniya a fuskarata.

Yanayin da ta yi sai ya ba Hauwa dariya da takaici.

Wayar ta Wauka ganin ta™i cin abincin da ta ije musu ta faWa kogon tunani.

Tsa™on ha™uri ta tura masa da basu wuce kalmomi biyar ba ta ije wayar.

A.m dake kwance a kan makeken gadon sa da yake jin faWin sa ya kai faWin duniya.Filo ya jawo ya rungume da tare da jan tsaki.

Tsananin Sacin rai yake Wauke da shi saboda ya ya je gidan su Zainab ta bar ™asar.

Da ™yar ya iya dawowa gida ya kwanta yana jin wani irin zafi a ran sa.Tun ranar da tsa™on ban ha™uri ya shigo daga Juwairiya wanda yau kwana biyar da shigowa, bai ko karanta da kyau ba balle ya tura reply wani irin haushinta yake ji da yanzu ya fara irga ranakun da zai zama Daddy.


Wayar sa ta yi ringing har sau uku sai a na huWun ya Wauka a kasalance ba tare da ya tanka ba.
" Ban yi tunanin za ka amsa kirana ba balle ka Wauka."Muryar Baba Sani ta daki kunnin sa.
Da hargowa ya ja tsaki da takaicin ™in duba wayar da bai yi ba ya Wauka,wanda hakan ya kasance ne saboda baya son ya kalli wayar lokacin da kiran ya shigo.

" Ban san kai ba ne da babu abin da zai saka na amsa wayar,mara mutunci mai ya sa ka kira wayata?"

" Na kan yi mamaki in ka yi min wannan tambayar Juwairiya da take gidan ka irin mangwaro ce ka samo ka shuka ta fito,da kake tambaya ta dalilin kiran ka."

Shiru A m ya yi masa a yanayin da yake baya bu™atar tashin hankalin Baba Sani don yana shakkun shi sosai.
" Na so na zo da kaina amma dana tuna baka da mutunci,kuma ka yi min gargaWi sai na dana tsufana,gudun kar na mutu da ™afa Waya sanin baka da mutunci,kuma sam baka girmama na gaba da kai.

"Fine gara da ka yi ma kanka ™iyamullaini ™a™i zuwa in da nake da sai ka raina kan ka wallahi."A.m ya ce ran shi a Sace.
" ³ar Wan'uwana na biyo naji ba'asi A k ya zo nemanta jiya."Gabansa ne ya faWi ya yi shiru bai tanka ba,amma tsoro fal a zuciyar sa ya manta Mama ba ta gari,kwata-kwata bai yi tunanin in da za ta je ba,saboda haushin da ta ba shi ko tunanin halin da take ciki bai yi ba.

" Na ji ka yi shiru ne ko ka Satar mini da ita ka san fa ita Win dukiya ta ce,so ka kiyaye don wallahi zan iya shuka rashin mutuncin da baka taSa tunanin in da shi ba."

" Har a kwai wani rashin mutuncin da za ka yi min da zai firgita ni bayan san baka da mutunci gabaki Waya rayuwarka,a tsiya za ka ™are don baka gaji arzikiba garyar matsiyata."

Dariya Baba Sani ya saki jin abin da ya faWa sai ya ba shi amsa da.

" Ashe masu arziki zasu zama matsiyata don in ka yi gigin Satar da ita saina zaman maka ™adangaren ba™in tulu,don haka ka kula ba ni da mutunci kai ma sheda ne."

A.m da ran shi ya ™ara Saci matuka kaWa kan sa ya yi sannan ya ba shi amsa" Kama ta ya yi na zo na kamaka in ji dalilin da ya sa take zubar min da ciki,don na san wata™ila kai kake saka ta kuma wallahi in har na gane da saka hannun ka sai na saka kaf zuriyarku an Waure ku."Ya ce da shi ciin Waga murya .

" To shikenan Wan ˜aruna ina jiran ka amma ™ila ni zan fara Waure ka,matu™ar ka salwantar min da ´ar Wan'uwa kuma jarina,wai yaushe kuWin da ka ba ni zai gama aiki?"Ya canza maganar da sigar tambaya.

Da takaici ya kama shi jifa fa wayar ya yi ba tare da ya kashe ba,yana jin dariyar Baba Sani can kuma ya kashe wayar.

" Ina ga Juwairiya da tsinannen Babanta Sani su za su yi ajalina."

Ko me ya tuna da sauri ya Wauko wayar da ya yi jifa da ita.

Numbar da ta turo masa da tsa™on ha™uri ya fara bincika duk da bai wani karanta tsa™on sosai ba.

Wayar na ringing tana ™ara tayar masa da zafin dake cikin zuciyar sa.

Sau uku ya kira amma ba'a Waga ba har ya yanke shawarar ba zai ™ara kira ba,sai kuma ya ji muryar wata mace ta yi sallama.

" Ina Juwairiya take."

Ya faWa a gundure da takaicin kiran da ya yi." Ban sani ba kuma in ga wrong number ka yi saboda ban san mai wannan sunnan ba "

Ta faWa da Wan daga murya dama abin da ta yi ninyar ta yi masa kenan,saboda yanzu matu™ar haushi yake ba ta yana can yana wahalar da kan shi,ga in da ake masa son mutuwa.

" Ko da ban san ke wace ce ba kar ki raina min wayo kin san dai abin da ke tsakaninmu ,ba kiran ta na yi don ina so ba,a'a saboda ta Sata mini kuma sai na nuna mata kuren ta."Ya ce da Hauwa ran sa a Sace.

" Ok kai da ka santa kake wannan maganar amma na yi maka bayanin ban san ta ba balle na sa abin da ya haWa ku."

Hauwa haushi yake ba ta ji take kamar ta kama shi ta yi masa shegen duka saboda irin mutanen nan masu gatsali.

Ta buWe baki za ta yi magana ji ta yi an fisge wayar Juwairiya ce daga bayan ta wacce ta shiga bayi a she ba ta san ta fito ba.

Jikinta har rawa yake lokacin da ta kanga wayar a kunninta tare da fashewa da kuka.

" Hello don Allah ka yi ha™uri ka yafe min wallahi ba zan ™ara ba zuciyata za ta fashe na rashin ka a kusa da ita k..."Wata uwar tsawa ya daka mata.

" Ban kira ki don ki gaya min tsoki buruku ba kin ji na rantse kar ki bari mu haWe dake don sai kin raina kanki.Gidan uban wa kike Baba Sani ya kira ni ya ce min ba ki a gidan sa?Da auren kike gantali ni dama na san ´an iskan ™awaye kika yi da su suke zuga ki,to makarantar ma na da™ile tun da baki san mutunci ba kuma na rantse miki za ki fuskanci fushina mai tsanani."

" Don Allah ka yi ha™uri ka yafe min na yi kuskure ba zan ™ara ba."

Hauwa ce ta fara kiciniyar fisge wayar da ta yi mata kyakykyawar ri™o.
"Dole A.m ya din ga wula™anta ki haba kamar ba mace ba duk kin zubar da ajin ki ya raina ki an faWa miki so hauka ne haka ake nuna ma masoyi ?"

Duk yadda ta so ta karSe wayar ta ™i bata,har du™awa ta yi tana ba shi ha™uri yayin da idanunta ke zubar da hawaye.


" Gidan ™awata Hauwa Tukur."

Ta bashi amsa har tana in ina garin saurin ta faWa masa." Minti goma na baki ki dawo gida in ba haka ba za ki fuskanci hushina."

A wannan lokacin Hauwa ta ™arSe wayar."A.m duk abin da kake yi Allah yana kallon ka,don Allah ya jarabce ka da ™aunarka sai ka din ga wahalar da ita?Ina jiye maka ranar da Allah zai kama ka a kanta...."

" Ke karki kawo min maganar banza matata ce fa kin san irin ma™udan kuWin da na saka na aure ta?In har na gane ke kike zugata saina Waure ki igiya tai rara.Maza ta dawo cikin mitinan da na bata."

" Juwairiya ba za ta dawo ba saboda ba ta da lafiya sosai in har ka matsu da ta dawo to ka zo ka Wauke ta."

Šif ta kashe wayar cikin Sacin rai saboda tunanin da take mishi ya wuce wannan.

" Haba Hauwa kina gani har sallar dare nake yi don ya kira ni shine za ki ce ba zan koma ba,kin san wannan batsa kika yi don tafiya zan yi."Ta ce cikin murna.

"Ki ce dabbe za'a yi a gidan nan na ga wanda zai kada wani ko da ganina kin san ba za ki ibi komai a jikina.Wallahi mugun haushin sa nake ji ya faye son kan da da yawa na, yi ba™in cikin Wauke Mama da ya yi ita ce kawai za ta iya ™watar miki ´ancin ki,don ke baki maida kanki mace ba shi yasa yake gara ki ya na amfani da son da kike masa.


A.m da yake jin haushin kiran da ya yi mata yana ta zagaye kamar mai Wawafi.

Ya fi kusan minti talatin yana jiran ta dawo ko ba komai ya rage damuwar abinci da kullum yake fama da yunwa,don ko gidan su ya je babu wanda yake masa tayin abinci,ya san ana yin hakan ne don a hora shi.

Wayarsa ya Wauka yana tsaki ya tura tsa™o kamar haka.

" Turo min da adireshin gidan."

A lokacin da tsa™on ya shigo Hauwa na tsaye ta ri™e Juwairiya ™am da take son ta fice daga gidan.

" Ina tausaya miki Juwairiya ko wani namijin kika aura ba A.m ba za ki sha wahala sosai,na lura baki iya Soye so ba in dai kina son mutum su maza ba'a musu haka yayin da suka fahimci mace ma son su wula™anci yake biyo wa baya."

Hawaye ta share ta kalle ta ta ce." Wata™ila ba ki taSa soyayya ba ne shi ya sa kike daWin haka amma son da nake ma A.m irin na in ban same shi ba sai rijiya."
" Ina na taSa so ai kin san auren ™iyayya na yi da mijina.Ta yi mata gatse sannan ta Wora da cewa "Ai ko kina ruwa wallahi don ina tausaya miki."

Kama hannun Hauwa ta yi ta ri™e sai hawaye shar!"Ki

Please Login or Register in order to submit comment