Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga talakawa ™as™antu irin ta.

Sai kuma ta ji daWin abin da ta ce ranta ya yi fari ko banza ba za ta zauna agidan wannan mai kama da canis ba sai ya zo ya san yadda zai yi da ita,ai dama abin da ya shirya a yi mata kenan shi ya sa ya aure ta ya kawo ta kuma ita ta sai ma kanta don in da ™waWayi a kwai wula™anci!

Atine ta ji jikinta ya yi sanyi sosai har ta fara tunanin in da za ta samu kuWin A.m ta mayar masa don ya na ba ta ta kai ma mai kujeru akan bikin ´arta marainiya wanda mijinta ya mutu ya bar mata.

Sai ta ji kamar ta ce ai mijin ta ne ma ya bu™aci ta kawo ta,amma da ta yi tunanin ba ta san dalilin da ya sa ka shi ya bu™aci hakan ba sai ta kama bakinta ta guntse ta ce." Ai Hajiya Juwairiya a kwai aiki da tsafta sosai ta yi aiki da dama shi ya sa na kawo ta,kuma za ki ya ba sosai sai kin gode min,amma ki gwada ta in ba ta yi miki ba sai a kawo wata.Kin sai an gwada akan san na ™warai.

" In ko haka ne ta na bu™atar gyara don sai na canza mata tufafi ba za din ga mana girki da shi ba,ni ban san da™i™anci da rashin wayewa."

Ta ce ta na kallon Atine da ta yi hamdala a ranta jin ta amince da ita,sai kuma ta kalli Juwairiya ta na mata kallon tsaf irin na ciki da waje har mutum ya gano munin ka.

" Ina yini"

Juwairiya ta ce mata ganin ta na mata kallon ke ba kya gaisuwa ne.

Šauke idanunta ta yi ba tare da ta amsa gaisuwar ba duk da ta tabbata ta ji gaisuwar da ta yi mata.
Sai ta mi™e ta kalli Atine ta ce."Wash na gaji ba ri na shiga ciki."Har ta fara tafiya sai ta tsaya.
" Ina fatan Atine ta yi miki bayanin aikin da za ki din ga yi a gidan nan? Ina da da tsohuwa da take share-share da ´an abin da ba'a rasa ba.So ke aikin ki kula da Wakina da na mijina da wankin underwears Win mu da girki.Kasancewar ba zama nake ba don yanzu waje zan fara fita na baki amanar gidana, da mijina duk sanda ba na nan ki rin™a kula da abincin sa ruwan wankan shi kayan sawan shi da wanda ko ina nan ke zaki kula da wannan."

Ta Wan numfasa ta Wora da ce wa " Game da kayan sawar shi irin wanda yake so ina fatan ke ba da™i™iya ba ce kuma ba' a yi asaran tara ba na yi mishi time table a Wakin sa na kayan da yake saka wa sai ki din ga dubawa ki na cire masa."

Wani iri Juwairiya ta kanta ya yi mata take wani irin zafin kishin mijinta A.m ya taso ya mamaye zuciyarta,har ya hana ta jin abin da Zainab take ce wa sai kuma tausayin sa ya kamata matu™a jin irin ballagar mace da yake aure.

Ta ™ara rintse idanunta ta na jin kishin iya adadin masu aikin da Zainab ta yi waWan da suka gama kallon mata miji,kuma a haka yake i™irarin ya na sonta lallai ta yadda so halitta ce kuma makaho ne.

" Ki na ji na ina magana kin yi banza da ni!"

Zainab ta daka mata tsawa ganin ta tafi duniyar tunani.

" Yi ha™uri ina sauraren ki ne."

To ba na son shashanci in ina magana du™ar da kunnin ki saitina za ki yi kuma duk na yi magana ki Waga kanki."
Ta ce sannna ta ci gaba da tafiya ta na faWin." Atine ba ri na Wauko miki abu."

" Kut! Na shiga uku A.m ya san halin matar sa ya kawo ni cikin gidan nan."

Ta faWi ta na jinjina kanta tare da tunanin irin zaman da za su yi da ita .A jiyar zuciya ta saki mai ™arfi jin sakacin da Zainab ta yi da mijinta.

KuWi masu yawa ta mi™a ma Atine wacce ta sandare da jiranta,saboda har wanka ta yi ta saka kaya shara-shara wanda al'dar ta ce zama da irin wannan kayan a gida.

A lokacin Juwairiya ta gaji har ta fara gyangyaWi ga yunwa dake ta ™wa™wular cikinta.

" Kin ga na jima ban dawo ba ruwa na watsa ga shi ki yi ha™uri."

Ta ce da Atine sannan ta kalli Juwairiya ." Ke ki tashi ki fara aiki kuma na manta ban gaya miki ba! Ba na son raini da ™azanta."

Sai kuma ta ™wala ma Baba mai aikinta kira da gudu sai ga shi ta ™araso mari ta zabga mata.Banza da™i™iya ba na ce miki za'a yi sabuwar mai aiki ba? Da kika gan su sai ki fara nuna mata aikin gidan ko sun yi miki kama da irin ba™in da zan yi ne?"Ta tambayeta ta cikin zafin rai.

"Ki yi ha™uri Hajiya ai ba ki bani umurnin haka ba kuma..."

" Rufe min baki banza maza ki je ki nuna mata."

" Allah ya huci zuciyar ki."

Ta ce tare da kallon Juwairiya sannan ta ce ." Mu je na nuna miki aikin."

Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye ta dafe ™uncinta don gani take kamar ita ta mara.Zainab ciki ta koma tare da Waukar wayarta ta yi kiran rabin ranta.
Tsananin tashin hankali Juwairiya ta shige shi ji ta yi tamkar ba za ta iya rayuwa a cikin gidan ba,a tare suka share hawaye da Baba suka kuma kalli juna.

" Ki yi ha™uri Baba haka matar gidan take miki?Gaskiya ba ta da mutunci a matsayin ki na wanda kika haife ta.Wai mai masu da shi suka Wauki talaka shi ba mutum ba ne don kawai ya na nema a ™ar™ashin wani sai wula™anci."

Baba ta share hawayenta ta kama hannun Juwairiya ta ce " Humh ba zaki gane ba ne!Hajiya Zainab ta wuce tunanin ki ina tausaya miki wallahi Allah ya sa kin iya girki."

Ta Wan ™ara matsowa kamar ta na tunanin Zainab za ta yi musu laSe ta ce." Ina gaya miki wacce ta kora ta kawo ki da ta yi abinci juye mata ta yi a jikinta,ta rufe ta da duka wai mijinta ya ce ba ta iya girki ba.Ni fa ban taSa ganin mutum irin maigidan nan ba,ya tsane mu sai dai shi baya duka."

Duk da Juwairiya ta san matsayinta a gidan amma sai da gaban ta ya faWi ras!Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Da Juwairiya suka shiga kicin kusan ruWewa ta yi kamar za tai hauka,irin dukiyar da aka narka da kayan na'ura,duk da ta yi aikatau gidan masu kuWi ta san yadda ake sarrafa na'ura amma a ranar yar ™auye ta dawo.


Abinci mai rai da lafiya Juwairiya ta shirya sannan ta shiga Wakin da aka ba ta wanda Zainab ta yi mata umurnin duk ta yi girki ta yi wanka.

Juwairiya ta da fari kasa amfani da kayan bayin ta yi sai daga baya a hankali ta fara gane yadda ake amfani da shi bayam ta Sata lokaci ta na ™auyanci.


Juwairiya ta yi mamakin irin kayan da ta jibga mata da sunan ta dun ga amfani da shi,haka dai ta shirya ta na ta tunani barkatai a ranta yayin da kewar su Mama ya kamata, matu™a har ta ji hawaye na zuba a ™uncinta.

Juwairiya na zaune a Wakin da ya zama mallakinta bayan ta idar da salla sai kuma ta mi™e da sauri jin kamar Zainab na kiran ta.

Ta na ba™in ™ofar fita daga Wakin suka yi kicibis da ita za ta shigo." Ke kurma ne ina kira kin yi banza dani."

Ta faWa cikin Waga murya." Ki yi ha™uri ban ji ki ba ne."
Ta ce ta na kallonta amma kuma a tsorace take saboda kar ta kai mata mari.Tsaki ta yi." Maza ki je ki shirya dinning za mu ci abinci mijina yanzu zai shigo.Kuma ki cire wannan ™azamin hijabin na ki don na san ina ya gani ba zai iya cin abincin ba."

Juwairiya ta ji jikinta ya yi sanyi jin umurnin da ta ba ta domin ba za ta iya fita a haka ba,amma sai ba ta ce komai ba ta saSule hijabin ta koma ciki.

Hankalinta ya kwanta da ta tuna a kayanta a kwai hijabi wanda bai kai wancan tsawo ba,da sauri ta Wauko ta saka a jikinta bayan ta saka turare kamar yadda ta murceta.

Juwairiya na gyara dinning ta ji dirin mota alamun an shigo da mota,gaban ta ne ya faWi ras! Don jikinta ya ba ta masoyin ta ne ya dawo haka kawai sai ta ji gaban ta na faWi.


Da sauri take shirya dinnnig Win saboda ta gama ta kauce ma ganin sa,amma sai kafin ta gama ya riga ya shigo ya na takun sa da sarsarfa irin na ingarmar namiji mai jini a jika.

Shigowar sa ya yi daidai da fitowar Zainab daga cikin Wakinta cikin wata irin shiga ta alfarma,amma fa a gurin sa wanda kuma Juwairiya ta ga bai kamata ta fito da irin wannan shigar ba,sanin a kwai ta a cikin gidan don har tafi shigar Wazu rashin kyan tsari.

Da gudu ta faWa jikin sa ta na dariya cikin farin ciki.
Shigowar sa ya sa Juwairiya ta gane ashe tafiya ya yi saboda direban sa da yake janye da troley Win sa guda biyu kuma masu girma.

Duka suke dariya sannan suka faWa kan kujera suna bayyana iya kewar da sukai ma junan su.

A hankali A.m ya zura ma Juwairiya ido shi har ya manta sun yi da Atine yau za ta kawo ta.Ya Wauke idanun sa da sauri ganin Zainab ta bi in da yake kallo.

" Hubbina sabuwar mai aikin da Atine ta kawo mana ne,Allah ya sa ta yi maka sai dai na ganta kamar gidahuma ce ko ina yawo da hijabi,amma haka zamu yi ha™uri da ita don gaskiya na gaji da Waukar masu aiki."

A hankali Juwairiya ta Wago idanunta ta Wara su akan A.m duk da ba ta son hakan,amma ta na son ta ji mai zai ce mata.

Ga mamakinta sai ta ga ya taSe bakin sa ya kalle ta kamar ya ga kashi ya ce." Uhm na gan ta sai dai ki yi mata magana ta kiyaye sosai in kuma ta™i dole ki canza wata don kin san halina."Ya ce a ta™aice sai kuma ya canza maganar ya na kallon Zainab ya ce." Na yi missing Win ki babyna sati Waya da na yi kamar na yi shekara,yanzu haka ma ban gama abin da na ke yi ba na baro A.k a can na dawo na ga kyakykyawar fuskar ki."

Ya faWa kamar zai yi mata kuka yayin da idanunsa suka bayyana hakan ga Zainab da take kallon sa da wani irin murmushi ta na kashe masa ido.

" Allah ko zauji ka san ni da kai kamar hanta da jini ne Wazu ina ma wani operation, ka san Allah saura kaWan na yanka sa ba in da ya kamata ba kuma fa kai na ke tunani."

Dariya suka yi duka ya ri™e hannunta ya ce." Na san za ki yi fiye da hakan akai na amma ki kula rai ya wuce wasa."


" Ke banza wawiya!Ba ki da tarbiya ko?Ko baki ko ya a gida ba in ma'aurata suna magana ki ba su wuri maza wuce daga nan stupid kawai!"

Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye tun lokacin da A.m ya shige ta nemi hankalinta ta rasa ji take kamar ta ruga da gudu ta faWa jikinsa.
Gabaki Waya ta manta a wace duniyar take wasu irin zafafan hawaye ta ji ya wanke mata fuska, saboda tsananin son da take masa wani irin kishin sa ya tokare mata ma™ogaronta, har ta ji ta na son ta yi aman sa don ta na jin Wacin sa ya na hawowa bakinta.

Muryar Zainab da ta daka mata tsawa ya fargar da ita halin da take cikin da sauri ta ruga da gudu,ta shige Wakinta har ta na bugewa da bango ™um!Amma ba ta kula ba don tsoron Zainab take yi sosai a ranta.

Ta na shiga cikin Wakinta ta fasa kuka sai kuma ta toshe bakinta tuna ko a ina take daga ™arshe toleit ta shige, ta kulle ta ™ara sakin kuka ta na buga kanta a bango amma ba ta kula ba ko kaWan.

" Na shiga uku a haka zan rayu a gidan nan? Na tabbata zuciyata ta kusan kamuwa da hawan jini!Allah na ro™e ka ka yafe min laifin da na yi maka ka haWa ni da A.m wanda da ma burin sa ya kawo ni gidan sa kishin sa ya yi ajalina!"

TO FA JUWAIRIYA AN YA DAI? GARA DAI KI TSAYA A MATSAYIN KI KISAN KE FA AUREN GWANGILA CE AKAN KI AMMA BA MATAR SO BA.INA JIRAN COMMENT TSAKANIN FANS ŠIN ZAINAB DA JUWAIRIYA.







TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO


ŠUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ŠIN KU YA NA SAKA NI NISHAŠI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi noma sha shidda.Ga masu bu™atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ™ofa a buWe take na ™orafi gyara ko ™arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za™auran marubuciya,kuma ™awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ™ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.






*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 18*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM





Tun daga wannan ranar Juwairiya ba ta ™ara saka shi a idonta ba wanda hakan ya tabbatar mata da tafiya ya yi tafiya, ita ma kan ta mai gidan ba zama take ba tun safe in ta fita sai dare za ta dawo,ta kwashi abincin da Juwairiya ta dafa,wanda tun daga ranar farko ta yi amanna da abincinta mai shigen daWin tsiya,don ko A.m da ya ci ya yaba sosai ji ya yi abincinta ya yi kama da wanda yake ci a gidan iyayen sa.

Rashin zaman mutanen gidan haka ya ba Juwairiya damar sakewa a gidan kamar na ta ba ta da wani matsalar takura.

Juwairiya a Wan zaman da suka yi da Zainab ta gane ko ita wace ce mace mai son hutu da gata,ga shi ta tsani zaman gida ko da ace mijinta na nan ga ta da shegen son ™walama kullum ta na yawon siyo kayan daWi da ciye-ciye.


Juwairiya ta Wauki tsawon wata Waya a gidan a cikin wata Waya ta ™ara kyau da kuma irin mai da cimar da take yi,ita kanta in ta kalli kanta a madubi sai ta ™ara juyawa ta kalli kanta cikin jin daWin yadda ta sauya,wanda har take zolayar kanta da in ta je gida Mama ba za ta gane ta ba.

Juwairiya ba ta da son jiki ku san duk wani aikin gidan ta Wauke shi shi ya sa kullum gidan ya ke cikin tsananin tsafta da ™amshi, ita kan ta Zainab kullum yabawa take sai dai tsabar girman kanta ba ta taSa nunawa ba.

Aiki Waya da yake Sata ranta shi ne gyaran Wakin A.m wanda kullum ta shiga sai ta yi kuka sosai,musamman da Zainab komai ba ta Waukewa sai ita take gyarawa cikin kuka da zafin kishi.

Ganin yadda Juwairiya take da hankali da natsuwa ga shi mijinta ya yaba kuma har ya yi tafiya bai ce komai ba,sai Zainab ta Wan saki jiki da Juwairiya kaWan duk da ta san rabuwa za su yi saboda ta isa aure,don haka ta yanke shawarar za ta Wauko yarinya ta haWa ta da Juwairiya ta din ga koya mata girki da yadda take gyaran gidan,saboda ko ba™i ta yi sai sun ya ba gidanta.

Ta na tsaye a kicin ta na tunanin abin da za ta dafa sai ta ji Zainab ta ™wala mata kira,da sauri ta ruga kamar yadda ta bu™ata duk lokacin da ta yi kiran ta.

Ba tare da ta kalle ta ba ta na ri™e da jaka ta ci uwar gayu ta ce " Fi ta zan yi yau zauji ya na hanya don haka ina son ki shirya abinci masu daWi."Fita ta yi ba tare da ta ji mai ta ce ba.

Kwan biyu da dawowar shi da rana ta na shirya abinci a falon cikin sauri take son ta yi ta kammala kafin ya fito,wanda ta yanke shawarar haka ya dace ta din ga kauce mishi ™ila zuciyarta ta huta da raWaWin son da take mishi.

Ta na cikin shirya abinci kan dinning ta ji ™arar kiran waya ya shigo sai ta shiga dube-dube a tunanin ta wayar Zainab ce ta manta fa ita,don sam ba ta kula da A.m da yake bacci ta bayan ta akan doguwar kujera.

Sai dai jin ™arar wayar ya sa ta gane ba ta Zainab ba ce, wanda kuma haka ya ba ta damar fahimtar a kwai mutum a cikin falon.
Kiran wayar ya sa shi juyawa da nufin ya kashe wayar saboda a gajiye yake matu™a! Kwanan nan sam bai samu ya huta ba,ya laluba wayar sa da nufin ya janyo wayar ya kashe bai jita in da yake tsammani ba,tunawa ya yi da jifa da ita da ya yi lokacin da ya shigo cikin falon.

Sai ya buWe idanun sa a wahalce ya na waigen in da yake jin ™arar ta amma tsabar gajiya ya saka shi kasa motsa jikin sa ya Wauko wayar.

Ganin haka sai ta nufi in da wayar take ta na neman agaji ta Wauko masa tare da mi™a masa,yayin da idanunta suke cikin na sa kuma ta kasa Wauke ™wayar idanunta ga barin kallon sa.
Idanu suka zuba ma junan su na tsawon lokaci wanda hakan ya sa Juwairiya ta rasa natsuwarta,shi ya fara Wauke idanun sa ya lumshe su.

A hankali Juwairiya ta tako ta mi™a masa wayar da ta ™ara rurin neman agaji.

Idanun shi ya ™ara maida wa kanta ya na mata kallo ™asa-™asa ya na son ya gano halittarta,don shi zai iya rantsewa bai taSa yi mata kallon cikakke ya san ya take ba,shi dai ya san ya yaba da ita har ya ji zai iya aurenta matsayin matar da zai iya aure na kwangila ta haifa mishi yaro.

Wayar da ta mi™o masa ya kai hannun sa zai ™arSa ya haWa har da hannunta ya na ™are mata kallo tun daga sama har ™asa,da sauri Juwairiya ta janye hannun tare da fara tafiya a hankali da nufin tabar gurin don jin wani irin tsau da ta ji jikinta ya yi,yayin da take jin wani ™arin sa™o daga zuciyarsa ya na aika mata cikin zuciyarta.

" Juwairaah."

Ya kira sunanta ba tare da ya mi™e ba cak tsayawa ta yi ba tare da ta jiyo ba,haka shi ma ya na kwance ya na kallonta kusan tsawon minti biyu,sai ta jiyo gabanta ne ya buga ras!
Da sauri ta ruga zuwa Wakinta tare da faWawa kan gado ta saki gwauron numfashi idanunta ta rufe cikin wata irin murya ta ce."Allah na ro™e ka kasa na zama jaruma na gama kwangilata na bar gidan nan kamar yadda na saka ma raina."
Ta nisa tare da ™ara juyawa ta kuma ce wa." Haka kawai ka shigo cikin rayuwata ka hana zuciyata sukuni."

Idanunta ta buWe suka tsar™e a na A.m da yake tsaye a gefenta ya na jin abin da take faWi,ya kai hannu ya fi sau uku da nufin ya ri™e ta amma sai ya kai ma iska nushi don ya na ganin in ya taSa wata ´a mace bai yi wa Zainab halacci ba.

Ganin ta buWe ido sai ya ja baya ya haWe rai hakan sai ya Wan tsorata har sai da ta ja da baya ta na kallon shi don ba ta san ya shigo cikin Wakin ba.

" Ji nan Juwairaah! Ko kaWan kar ki saka a ranki zan iya rayuwa dake kin ga matata kuma iya Wan zaman ki a cikin gidan nan,kin ga irin tsananin son da nake mata don bai kamata sai na gaya miki zaki fahimta ba,don na faranta mata na aure ki don haka ki kiyaye duk wani abin da zai sa ki yaudari kan ki,don kin san haka ba mai yuwu wa ba ne sanin kan ki ne ruwa ba tsaran kwando ba ne?"

A hankali ta Waga mishi kai ganin ya tsare ta da ido ya na son ya ji amsar tambayar sa.
" Sannan kar ki Wauka ko na manta dalilin da ya saka na aure ki ne.".
Ya juyo ya na kallonta ya ce da ita." Wallahi na rasa yadda za' yi na fara Waukar ki a matsayin matata don ba mu dace ba,ni sai yanzu nake dana sanin da idona da ya rufe na yadda na aure ki,amma duk da hakan zan daure na aiwatar da shirina da zarar kin sami ciki na kai ki wani gurin ki haihu na karSi yarona mu shafe babin rayuwarmu."

Ya na kai nan ya fice ba tare da ya lura da kukan da take yi ba na ba™in cikin tsanar ta da ya yi,sai dai kuma daga ba ya ta dai na jin haushin kalaman da ya faWi saboda duk abin da ya faWa gaskiya ne,ita ma ta karSi auren sa ne saboda ta ta ceci ran mahaifiyarta da Wan'uwanta.

Washegari da safe Juwairiya na kwance hayaniyar masu gidan ya tashe su wanda ta kasa gane ko menene,amma ta tabbata ba lafiya ba jin yadda suke magana sama-sama musamman muryar Zainab wacce har kukanta ta ji.
Matu™ar tsoro ya kamata ji ta yi ta ™ara mugun tsoron A.m don ba ta san haka yake da tsiya ba.

Ta na zaune a Wakinta ta yi tsumu so take ta haWa abin karyawa amma ba zata iya fita ba jin yadda suke ta Waga murya kamar za su dambace.

Mamaki ya kama ta sosai wai masoya ne suke irin wannan faWar,ganin sun ™i yin shiru da sauri ta shige kicin ba tare da sun gan ta ba,ta fara Wora abinci jikinta na rawa gani take kamar a kanta faWan zai ™are.

Ta na shirya a binci a dinning ta ga A.m da ™atuwar troley Win sa ya na ja, ransa kamar an aiko masa da mala'kan mutuwa, ba tare da ya kalle ta ba ya fice daga gidan.

Ba'a jima ba sai ga Zainab da na ta jakar ta na waya bayan ta gama wayar ta kalli Juwairiya ta ce " Ke wai me sunan ki baki gaya min ba?Ko ki na jiran na tambayeki ™ila uwar ki zan ci da sunan."

A hankali Juwairiya ta furta." Juwairiya sunana."Yayin da hawaye suka fara turereniya a fuskarta.

Tsaki ta saki." ko ma mene ne ni tafiya zan yi kuma ™asar zan bari, ban ce kije ko ina ba kar a kwashi kayana akai gidan matsiyata,ki kula min da gidana duk abin da kike so ga waya ki kira ni in da matsala."

Jefa mata wayar ta yi a jikinta ta fice ba tare da ta yi tunanin za ta iya fashewa ba.

Tsananin mamaki ya kama Juwairiya yanzu ne ta gane musabbabin faWar

Please Login or Register in order to submit comment