Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kike tunani zan yi mata bayani.Kuma ba ni da nufin na cutar dake alkhairi ne zuciyata,don Allah ki karSa kin san babu kyau mai da hannun kyauta baya."Yace da ita ya na wani marairaice fuska sai kace maraya.

"Gaskiya ka bar shi bana so ina gani a matsayina na ar aiki bai kama ta na rie irin wayar nan ba,don daga ganin ta na san za ta yi tsada kuma in Anty Naja ta gani me zan ce mata?"Sai ta tsinci kanta da furta hakan yayin da takai aya ta tsare shi da ido ta na tambayarsa.

Shi ma ya Wan razana jin tambayar da ta yi mishi kansa ya Wan sosa ya kafe ta da idanunsa yace."Haba Juwairiya kina abu kamar ba mace ba,kice mata saurayin ki ya baki mana."

"Ka yi hauri don Allah ba na son kyakykyawar alaar mu da matarka ya Sace,kai sheda ne mace ce na warai kuma ta yi min halacci."Tace dashi da murya raunanniya yayin da hawaye suka fara turereniya a fuskarta.
Ganin haka sai jikinsa ya yi sanyi ya Wan yi shiru ya na nazarin maganar ta zuwa can ya ja numfashi yace."Laifi ne don nace ina sonki ni fa bani da nufin na cutar dake,kawai ina son ki zamo uwar aana ne."Tsananin tsoron da ta nuna ta na me gwalo ido sai abin ya ba shi dariya.

Tafe take cikin sauri bayan ta tashi daga aikin zuciyarta tunanin sabon halin da mijin madan Win ta ya fito dashi,yake damun ta har ta fara tunanin ko ta aje aikin ila in Anty Naja ta gane ba lalle-lalle ne ta fahimce ta ba.Kallon tsadaddiyar wayar dake rie a hannunta da ya bata take kallo wanda ya rantse ya maya in har ba ta Wauka ba to zai ba wa Antynna ta da take tsoron sani ta bata da kanta.

Abin mamaki dai-dai za ta shiga gida ta ji an dameta da hon,kamar ba za ta juya ba sai kuma ta juya in da ta ga mijin Anty Naja a cikin mota ya na Waga mata hannu,wato biyo ta ya yi ba tare da sanin ta ba ya ga gidan su.Tsabar takaici ba ta kula shi ba ta shige cikin gida.

Koda ta gaya ma Mama abin da ke faruwa hankalin Mama ya tashi warai ta yi shuru kawai ta na jinjina abin a ranta,ta Wauki tsawon lokaci ba tare da tace komai ba zuwa can ta nisa tace."Ina ga ko haura da aikin nan tunna mun sami jari Juwairiya,ni nafi son kiyi aure shine mutuncin ki.Kin san maza basu da ta ido zai iya furtawa hakan ya jawo miki matsala gara mu yi rabuwar mutunci,in ban da shi ma ina ke ina kishi da Anty Naja mace me mutunci."
"Nima haka na gani Mama hankalina ya tashi warai."Tace da ita ta na juya wayar da ya ba ta."Kinga gobe ki mayar mishi da wayar shi,kice ni na ce ki mayar masa na tabbata ya tsorata ki ne amma ba zai yi gigin bata wayar ta baki ba,in dai ba ya na so ya kira ma kansa ruwa bane."
"To Mama in sha Allahu zan mayar masa,ni ma bana son na rie irin wayar nan don Allah kaWai ya san abin da Baba Sani zai faWawa jama'a."
"Haka ne Allah ya fishi."Ta bata amsa tare da miewa don Wauro alwalar kiran sallar magariba da ke ta kwaWawa masallacin kusa dasu.
Washegari da ta je gidan bayan fitar matarsa ya dawo kamar yadda an kwanakin yake mata,ta na ganin shi ta ara tamke fuska kamar ba ta ganshi ba ta ji gaba da aikin ta.
Ta yi tunanin zai yi mata magana amma sai ta ji shiru na tsawon lokaci,da sauri ta waigo sai ta ga ita yake kallo kamar bai taSa ganin ta ba.Mia masa wayar ta yi tace."Mahaifiyata tace na dawo dashi,kuma don Allah ka yi min rai ka fita sabgata domin ba za ta amince aci amanar Anty Naja ba."
"Ni kuma sai na shiga wani hali ko?Wannan dalilin ya sa kika i Waukar wayata jiya da daddare sai ma kika kashe wayar.Dama masoyi ya na zama maiyi Juwairiya?"Ya arashe maganar da sigan tambaya,a yadda ya furta maganar sai ta ji ranta babu daWi,ganin namiji mai natsuwa ya na mata magiya akan ta so shi.

Wani irin abu ta ji a ranta in da ace matarsa ba ta shiga tsakani ba,babu yadda za'ai tai auren shi sai dai ba za ta zama butulu ba.Ganin tai kallon sa bare ya saka ran za ta yi magana,sai ma hawaye da ta soma ganin haka ya Wauki wayar da ta ije mishi ya fice ya san ta na sonshi,amma tsoro ne ya cika mata zuciya in ko haka ne zai je har gida ya nemi aurenta.

Kwana biyu haka suke wasar ar Suya ganin haka sai ya dena shiga sabgar ta ko dawowa gida ya dai na,ya na shirye-shiryen zuwa gidan su ya nemi auren ta.
Ranar wata yammacin talata ta tashi daga aiki kasancewar an yi rana sosa,da yake lokaci ne na damina garin ya fara haWa hadari.Juwairiya sauri take ta isa gida saboda ta kauce ma bain hadarin da yake tasowa ya na canza garin da yake duhu sosai.
Hon ta ji an danna mata ta waiga sai ta ga Daddyn Abnaj ne ya na mata murmushi yace."Maza shigo na kaiki gida kar ruwa ya zane min masoyiyata."Ta yi kamar ba za ta shiga ba amma ganin har an fara iskar hadari ya sa ta buWe gidan baya ta shige,tare da haWe girar sama da asa don karya tambayeta dalili

Hakan sai ya ba shi dariya sosai bai ce komai ba suka fara tafiya, sai ya sai ta madubin motarsa dai-dai in da take zaune."Wato na zama direban ki ko."Ya jefa mata tambaya dai-dai lokacin da ya fara tafiya.
"Ina wuni."Tace ba tare da ta amsa mishi tambayar ba.
"Ba zan amsa ba ina fushi."Yace ya na kallonta ta gilashin motar.
Ba tace mishi komai ganin hakan ya sa ya fara magana da murya mai taushi."Matsalar an mata kenan da kun ga namiji ya na aunarku,shikenan kun samu zaren ja amma babu komai nima lokacina ya na nan zuwa,don na fara hango sona a cikin wayar idanunki."
Ta Wan saki ranta saboda ta fara sabawa da shi ya wan janta da Wawainiya da yake musu ta ja numfashi ta sauke ta fara magana da cewa."Ku kuma maza ba amana ka san kusancin dake tsaanina da matar ka,amma ka bijiro da wannan lamari haba kai ma ka auna ka gani bai dace ba."

"Kija min aya da ya hana hakan ko hadisi."Ya faWa a raunane kuma a taaice.Babu amma Bahaushe ya na girmama al'adarsa hakan ya saSa ma al'adar Bahaushe."Sitiyarin motar ya buga da arfi yace "Kin ji ko in da karatun naki ya tafi ina miki zan can addini kina yi min wata magana can,kawai na gane bakya sona ki ce na haura kina da wani hakan zai sa na bawa zuciyata hauri duk da na san za ta shiga wani hali."

Yanayin da ya yi maganar sai ya bata tausayi amma ta san abin da yake so ba mai yiwuwa ba ne.Murfin motar ta Salle za ta fita ganin sun araso gida ya yi parking,sunan ta ya ira da wata irin murya.Ta waigo ba tare da tace ala ba,sai asa da kanta da ta yi wato alamun ta na sauraren sa.
"Ki yi tunani zuwa arshen sati nan nake so na turo magabata na,ina ganin za ki dakata da akin nan kafin kizo a matsayin anwa kin ga sai ki Wora daga in da kika tsaya ki na samun lada rututu!

alle motar ta yi ta fice dai-dai lokacin da ya mia mata an rafar Wari biyar kusan kimanin dubu ishirin ba tare da ta karSa ba ta fice,musamman da ta ga Baba Sani tsaye a ofar gida shi da wani mutum ya zura mata ido.

Ganin jikinta ya soma rawa ya kalli in da take kallo,sai hakan ya yi mishi daWi domin faWuwa tazo dai-dai da zama,ya buWe murfin motar ya fito ya nufi su Baba Sani dake kallon Juwairiya kamar ya shae ta.

Da sauri ta matsa za ta bi ta bayansa ta shige cikin gidan da ya bake ofar,amma sai ya daka mata tsawa tare da jan hijabinta."Ina zaki ar iska maza dawo,iskancin naki ya kai har a kawo ki gida a mota.Kawai sai ya saka salati da arfin sa ya ci gaba da cewa."Inna lillahi gara da ka mutu Yaya Ahmed in da ka na raye Juwairiya ita za ta ashe ka.Karuwa kika zama fa ke ko kunya duniya ba za ki jiba tunna baki ji na Allah ba."
"Ashsha!Subuhanallahi haba Malam ya za ka dinga jifan ta da waWannan muggan kalamai?Iya sani na Juwairiya yarinyar kirki ne ta WaWe ta na tare damu ta na mana aiki.Yanzu haka mun daidaita ne nake son ka bani auren ta,ma'ana na yaba da hankalinta ina sonta."

Wayyo Allah faWin haka da ya yi wato ya na son Juwairiya ji Baba Sani ya yi kamar ya watsa mishi fetur ya kyasta ashana domin bain cikin sa biyu ne a kan maganar.Na farko ta ya ya za 'ai mutum me hannu da shuni yace ya na sonta,sannan kuma bain kishinta ya taso ya lulluSe mishi zuciyarsa kawai sai ya ara kuka ya na faWin ma abokin da suke hira cewar."Kaji ko wai na ba shi aurenta bayan ya gama iskanci da ita ni nasan ya na naWe tabarmar kunya ne.Amma ta ya ya zai auri mazinaciya!Ba Juwairiya dake tsaye ta na kuka ba har ta Daddyn Abnaj sai da yaji wani irin abu ya soke shi ya rintse idanunsa ya na jin kamar ya shao wuyar Baba Sani,take ya fahimci wani abu wato na zaman unci da suke yi iya zaman su da ita bata taSa basu labari ba,duk da ya san cewa ba lai-lai bane ta gaya musu kasancewar ta na da zurfin ciki.

Ya kalli Juwairiya da ta ara sautin kukan ta ganin mutane sun fara taruwa Baba Sani yaci gaba da magana da arfi ya na nanatawa,sai ta ruga da gudu dai-dai lokacin da Baba Sani ya kai mata bugu a bayanta.

Ba ta san ya suka are ba ya dai shigo gida ya na ta faWa tare da ja mata jifa'i kala-kala, Juwairiya ta so ta tanka saboda abin da ya yi mata a gaban mutumim da yake girmama lamarin ta,amma Mama ta hana duk san da ya gaya mata baa ta buWe baki za ta yi magana Mama za ta hana ta,har ya gaji da rashin mutuncinsa ya fice.

A ranar Juwairiya ta ci kuka sosai ta ji ta ara mugun tsanar shi a ranta.
Washegari ganin tai shiryawa taje aiki Mama ta shigo Wakin ta tsaya ta na kallonta tace."Juwairiya ba zaki je aiki bane naga rana ta yi."
"Na haura da aikin Mama gara na zauna a gida dama kin san mun yanke shawarar na daina zuwa,sai ga abin da Baba Sani ya yi min a gaban shi Allah kunya nake ji matua.Karuwa ya kira ni."Sai kawai ta saka kuka ta na jin zafin kalmar da ya danganta ta da ita."
Mama a ranta har tafi Juwairiya damuwa amma sai ta Wan gyara murya tace."Ki yi hauri komai lokaci ne watarana sai ya yi dana sani,amma da kin daure kije kila ma ya shafa miki lafiya don na tabbata ba zai ara miki maganar soyayya ba,ganin yadda ya tozar taki."
"To Mama shikenan a haka rayuwata za ta are duk wanda ya fito neman aurena sai Baba Sani ya Sata lamarin gaskiya na gaji."Tace cikin hawaye yayin da ta tuna katoSarar da ta yi na faWin hakan,kamar ta nuna ta na son auren kenan sai ta zari hijabinta da sauri ta fice zuwa aiki.

Ko da ta isa bata sami Anty Naja ba duk da ta san dama abu ne me wuya ta same ta,abin mamaki ta yi sallama ta shiga fuskarta babu walwala,sai ta same shi zaune akan one siter ya zuba tagumi ya na kallon hanya,ganin ta ya saka shi sakin ajiyar zuciya mai arfin gaske.
"Shigo mana Juwairiya hankalina ya tashi matua na yi zaton wannan mara kirkin Baban nan naki ya hanaki zuwa "Yace da ita ganin ta dogare a bakin ofa,ta Wan tsaya ta na kallon shi sai kuma ta ara haWe fuska haushin sa take ji don shi ya yi shishshigi a lamarinta,har ya saka Bab Sani ya yi mata wannan tozarcin.

"Gaskiya ban ji daWin abin da ya faru ba!Haba sai kace ba anin mahaifinki ba.Lamarinsa ya tsoratani bain cikina yadda yai yadda da maganata akan ina sonki da aure.Kawai ki gaya min dangin ku naje can na nemi aurenki."

Yace da ita ya na kare mata kallo don ya fahimci a wani hali take,takaici ya kamata jin abin da ya faWa sai ta mie hanyar kicin ba tare da tace mishi komai ba.

Gabanta ya sha tare da rie mata hijabi yace."Na fa fara osawa da halin ko in kula da kike min haba waike dutse ne a irjin ki ba zuciya ba!Ki ji tausayina ko don halin da kike ciki ki zaSe ni a matsayin mijin ki hatta mahaifiyarki ba za ta zauna a wannan gida ba.

Takai hannu da nufin ta wace hijabinta sai ya rie hannun cikin kalar tausayi ya na jin kamar ya yi mata kuka,ganin sam ba ta da rangwame akan soyayya.Baki ta buWe da nufin ta yi magana sai suka ji sallamar Anty Naja ta shigo da sauri da alamun gajiya tare da ita.

Da sauri ya saki hannunta ya matsa gefe ya na zare ido,ita ma cikin tashin hankali ta tsaya ta kasa haWa ido da ita ta na jiran tashi n hankalin da za ta fuskanta.
Amma sai dukansu ta basu mamaki ta faWa kan kujera ta na lumshe ido "Wash Allah! Na gaji matua Juwairiya bani ruwa don Allah."Tace cikin sakin fuska ba tare da ta fahimci komai ba."
Da sauri Juwairiya ta shige kicin ta na mamakin sokanci irin nata haba ta ya ya za'ai tace bata fahimci komai ba.Bayan ta kawo mata ruwan ta haWo har da abin motsa baki,ta shige kicin ta ci gaba da aiyukan ta can sai ga shi ya shigo yace."Ina jiranki in kin gama zaki tafi ina hanyar da nake tsayawa sai mu arashe tautaunawar.

Ganin ba zai saduda ba Mama tace ta haura da aikin in ta bata kuWin aikin ta na wata haka kuwa aka yi,bayan ta yi mata albashi ta ara mata harda zannuwa masu kyau biyu nata sai Waya Mama ta Winka,kasancewar suna da biki a family Win su kuma tare da Juwairiya za su tafi garin Kano.

Hankalin Anty Naja ya tashi matua ganin ba ta zo aiki ba,ta shiga ruWani ta din ga tunanin ko ta yi mata wani abu amma bata gano ba.Shi ma hankalinsa ya tashi sosai duk da yaso sai sun gama daidaitawa a tsakanin su sai tabar aikin,amma ta yi sauri gashi ya na son yaje gidan ya na tsoron tijararren anin mahaifinta

Sai ya azalzala ma Anty Naja ta shirya ya kaita har ya na mata barazana da ya na nan akan bakan sa in dai ba Juwairiya ba sai dai ta bar aikin,ai kuwa ba shiri ta shirya suka taho ya ijeta a kofar gidan ta shiga ciki ya zauna da yaransa ya na jiran ta fito,burin sa ya ga Juwairiya.

Juwairiya na tsakar ta na girki Mama ta na zaune ta na jan carbi ta yi sallama ta shigo,da sauri Juwairiya ta saka hannu ta rufe fuskarta ta na dariya.
Anty Naja ta harareta ta na kallon Mama tace."Da ma Mama haka Juwairiya take bata da kirki? Kawai ta guje mu ba tare da mun yi mata wani abu ba,hankalina ya tashi warai Mama gaskiya ba ta kyauta ba."

Ta arashe maganar ta na kallon Juwairiya sannan ta Wora da cewa "Ko mun yi miki wani abu ne?Ai gaya mana ya kamata ki yi ba ki Wauke kafafunki ba.Ni da yara da Daddyn su Abnaj duk hankalin mu ya tashi."

Mama ita ba tace komai ba tace komai ba sai dariyar yae take mata,bayan sun shiga Waki suka yi gaisuwa a tsakanin su sanann shiru ya biyo baya.Sannan Anty Naja ta katse shirun tace."Me ya faru Mama kwana biyu bata zo aiki ba na yi tunanin ko wani ba lafiya,amma da nazo naga kowa lafiya.Ko na yi laifi ne Mama."

Matuar kunya sai ya lulluSe Mam ta ji kamar ta nitse ta rasa yadda za ta fara mata bayani,har Juwairiya ta yi sallama ta shigo,ganin Mama ta kasa mata bayani ta kalli Juwairiya tace."To ko auren ne ya zo,in kuma wannan ne Mama ai ni ce me haWo kayan Waki ko?"Ta arashe maganar ta na me tsigar tambaya.
I ta dai Juwairiya ba tace komai ba ta na ta wasa da yatsunta,Mama ta daure tace."Ba shi bane ban san dai yadda zaki Wauki zancen bane shi yasa na kasa sanar miki,amma ranar wanka ba'a Soyan ciji."

Gaban Anty Naja ya faWi daram!Sai ta ji zuciyar ta ta raya mata lai-lai a kwai abin da suke Soye mata,duk da bata san ko menene ba amma taji ta firgita Allah ya sa ba wani lamari me girma ya faru ba.
Ganin ta yi shiru ba tace komai ba jikinta ya yi sanyi Mama dai ta daure tace."Dama mijinki ya bijiro da wata magana ya na son auren Juwairiya har ya shigo da maganar gida,mu kuma muka ga rashin dacewar haka saboda irin halaccin da kika yi mana shi yasa nace ta dakata da aikin kawai ki nemi wani."Tace ta na karantar fuskarta.







Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na Tara.Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakauran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA TARA*

Abin mamaki da yake macece wayayyiya sai bata nuna komai ba duk da irin tarin luguden da zuciyar ta take mata,ta na jin kamar ta fita ta shao shi munafiki kawai haba ya kamata a ce ta Wago tuntuni saboda yadda yake yabon ta da kalamai magana Waya biyu ya sako sunanta,amma da yake ba ta da wayo sai ba ta Wago ba ta danganta kular da yake bata a dalilin ta na kular mishi da yara,sam ba ta yi tunanin zai ce ya na sonta ba ganin basu da komai ar Malam Shehu.
Wayancewa ta yi ta na dariyar yae tace."Haba Mama ni na yi tunanin wani lamari ne me girma yasa kika hana ta,amma akan wannan Wan aramin abin zaki hana ta,in dai a kan wannan ne karku damu ai gara ya auro wacce na sani da ya Wauko min wata.Kuma karku manta shi fa mijin mata huWu ne,don Allah karku ce zaku hana mishi aurenta."


Yanayin yadda take maganar ya nuna da arfin hali kawai take yi,amma ta na oarin aalo dariya.
"Haba ar nan ai ana barin halas don kunya kawai ya nemi wata,amma Juwairiya ba tsarar auren sa bane."
Anty Naja ta dage ta rie kishinta ta na ba ma Mama baki akan ta haura ta yadda ayi auren,sannan ta Wora da ko ba zasu bashi ba don Allah Juwairiya ta dawo aiki.

Daga arshe ta yi ma Mama sallama ta fita har ta na tonon Juwairiya ta fito tare suke da angon ta yazo biko,ita dai ba tace komai ba a ranta take mamakin wani irin hali take dashi.Bayan ta jaddadawa Juwairiya tazo aiki ta yi musu sallama ta fita.

Bayan ta fita ta buWe murfin mota ta shige tare da haWe girar sama da asa a ranta ta na mamakin raina mata wayo da ya yi wato ya turo ta ta yi mishi bikon budurwar shi,bayan ta sheda Juwairiya yarinyar kirki ne sai tace amanarta suke ci.
A yadda ya ga yadda ta fito sai hankalinsa ya tashi don bai yi tunanin za su gaya mata abin da ke tsakanin sa da ita ba,sai ya yi dana sani da tuntuni ya tare ta da maganar.
Bayan sun fara tafiya ya kalleta yadda ta ara cin magani fuskarta ba rahama yace cikin arfin hali ya yi mata tambayar."Ya take ko ba ta jin daWi ne?"

Haba kamar jira take ya yi tambayar lokacin da take kallon waje ta fara bala'i in da take shiga ba nan take fita ba tace."Munafiki da zamu taho ai da ka gaya min biko zan je na yi maka.Da ma amanata kuke ci kai da ita da ta amince ila sai dai in ji ta tare a gidana ko."

Nan ta Salle ta na gaya mishi kalamai zafafa mara sa daWin ji,in da take shiga ba ta nan take fita ba a hanya ta zage shi tatas! Ta yi mishi wankin babban bargo.Shi dai shiru ya yi mata don ya san ya ibo ruwan dafa kansa kuskuren shi Waya da bai sanar mata ba,kuma bai Wauka su Juwairiya za su yi suSul da baka su gaya mata ba.
A haka suka kwana sam ba ta barshi ya rintsa ba,shi kan shi bai san ta iya rikici ba,sai ayau ya san ta na da zafi mata da kishi humh ba'a magana.
Washegari Juwairiya ta na zaune ba ta da ninyar zuwa aiki amma Mama ta matsa mata akan taje.Sai dai yadda ta ga gidan ta san ba su kwana lafiya ba.

Tun daga falon take kallon yadda ya hargitse ko ina an birkita shi sai gabanta ya fara faWi ta san cewa a kwai wani girman lamari da ya faru.
"Munafuka kema me ya kawo ki gida!Maza fita matsiyaciya me kwacen miji kawai,in banda ke jahila kina ar talaka za kiyi tunannin mijina zai aureki."Anty Naja take magana cikin zafi sannan ta Wora da cewa."Fita kar na ara ganin ki a gidana,sai abi wani sarkin amma mijina yafi arfin ki.

Ko da ta dawo ta sanar ma Mama tace."To shikenan Allah ya sa haka yafi alkhairi.Hankalin Baba Sani ya kwanta ganin Juwairiya ta bar aiki kullum ta na gida,hakan sai ya yi masa daWi musamman da yake tunanin yanzu komai zai kwaSe musu.
Juwairiya ta yi tunanin Baban Abnaj zai biyo bayan ta,amma shiru kake ji Malam yaci shurwa wato matarsa taci arfinsa.Ganin haka sai suka kama sana'a sosai da kuWin da Baban Abnaj yake basu,yanzu har abincin siyarwa suke yi Ibrahim ya na kai wa ofar gida.Kuma suna samu ba laifi don da shi suke cin abinci.


*********

Kimanin shekaru huWu da auren su suna zama cikin so da aunar juna,sai an saSanin da ba'a rasa ba a tsakanin ma'aurata.Kullum A.m ya yi kasae ya ji Zainab tace mishi ta na da ciki amma hankalinta ba shi a gurin tunna ba ta taSa yi mishi maganar baby ba.


Lamarin sai ya fara damunsa musamaman da annin shi da sa'annin shi suna da yara,amma shi matarsa ko Satan wata ba ta taSa yi ba.

Sai kuma Allah ya Wauki son ara ya Wora mishi in ya gan su kamar ze zare.Ya na matuar son yara kullum ya na hanyar gidan an'uwan shi ya na manne da yaransa.Daddy Win shi ya fara orafi ya na tsoron kar A.m ya Wauko rashin haihuwa sai ya fara mishi orafi sosai kullum ya na kiran waya akan suje likita ya duba su.

Ganin yadda ya Wauki son yara ya Wora ma kansa sai Zainab ta yi gum da bakinta ba ta taSa suSutar baki

Please Login or Register in order to submit comment