Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta nuna mishi ita ce ba ta son ta haihu take shan ™wayoyi ba.
Sun Wan fara samun saSani yadda yake kwaso yaran ´an'uwan shi ya kawo gidan ya siyo musu kayan wasa.Ranta Saci yake sosai ta na ganin hakan kamar takuratawa rayuwarta ne,duk yaran da ze kwaso ba ta musu komai sai masu aiki.Gaskiya Allah ya jarabce shi da son yara sosai.

Wataranar Alhamis Zainab ta tashi da ciwon ciki kamar za ta mutu,hankalin A.m ya tashi matu™a ganin a sume ya Wauke ta ya saka a mota suka nufi asibiti.
Bayan an karSe ta aka yi mata ´an gwaje-gwaje tare da turata Wakin hoto,duk abin da ake ta na kwance kamar gawa ba ta san in da kanta yake ba.Likita ya gano mahaifarta ce ta samu matsala sakamakon tarin ™wayoyi da ta din ga Winkira ma kanta masu ™arfi na hana haihuwa.Wanda sakamakon haka mahaifar na gabda ruSewa in da likitan ya ba A.m shawarar ayi mata aiki a cire mahaifar.
Tsananin tashin hankali A.m ya shige shi ya din ga kallon likitan kamar ™arya ya yi mishi."Me yasa Zainab za ta aikata hakan?Hakan na nufin ba ta son shi ne har take shan maganin hana Waukar ciki don kar ta haihu?"
Irin tarin tambayoyin da yake yi ma kansa kenan amma ba shi da amsarta,daga bisani ™e™eshe zuciyarsa ya yi kan ™aryata likitan ya san Zainab ba za ta aikata hakan ba,musamman yadda ta ga Daddyn shi ya mutu akan ya ga ya haihu,sannan yadda yake nuna mata ya na son ta haifa mishi baby ta na nuna masa Allaha ne be kawo ba.To hakan na nufin yaudararsa take.

Sai ya yi zuru ya na kallonta da take saukar da numfashi cikin rashin haiyaci ta na bacci,sakamakon allurar baccin da likita ya yi mata.Sai ya shafi fuskarta ya na me tausaya mata halin da ta shiga.

"Gaskiya ban yadda da maganar likita ba ina ta ya ya zan rayu ba tare da na ga Wan cikina ba,duk da na san Allah ya ba jarabtar bayinsa amma gara wata jarrabawar ba wannan ba.Ya na ganin halin da Daddy Win shi yake shiga saboda rashin Wa duk dukiyar da ya tara ya tafi a banza.In in haka ne ya zan yi da shares Win da na saka ma yarana tun kafin su zo duniya a ™asashen waje.

Nan take zuciyarsa ta™i amincewa da abin da likitan ya faWa duk da ya san asibitin su ™wararru ne.
Kusan awa Waya ta na baccin wahala sannan ta buWe idanunta.Da sauri ya ri™e mata hannu ya na shafar kanta."Kin tashi babyna sannu. Yace ya na ™o™arin temaka mata tashi ta zauna.

Bayan ya haWa mata tea ya ba ta tasha ta lumshe idanunta ta na ji har yanzu wani abu ya na karta mata a cikinta,ita kaWai ta san irin tarin azaba da raWaWin da take kwankwaWa.

"Ya jikin sannu kin ji abin da likita yace game da ciwon ki?"Ya tambayeta da murya mai sanyi ya na gyara mata Waurin Wankwalin ta da yake son ya warware.Ba tare da tunanin komai ba tace."A'a hubbina."A ta™aice ta ba shi amsar don ba ta son dogon surutu.

Ya Wan ja numfashi ya fesar ya jinjina girman lamarin baya so ya gaya mata,bai san yadda za ta karSi lamarin ba cewar ba ta haihuwa mahaifarta ya fara ruSewa wanda dole sai an yi mata aiki.To amma ya na son ya gane shin da gaske ita tasha maganin hana Waukar ciki har ta illanta musu kanta,ba yan haka da ya bari sai ta warke.

"Likita yace ba zaki taSa haihuwa ba yanzu ma mahaifarki za'a yi miki aiki a cire."Yace da ita ya na son yaga yadda za ta ™arSi lamarin.
"Inna lillahi.Tace tare da bayyano wani tashin hankali a fuskarta nan take fuskarta ta sauya sai hawaye,ta yi ™asa da kanta ta na son ta yi magana amma ta kasa sai hawaye dake ta gasar sauka a fuskarta.A zuciyar ta kuwa illa tarin nadama da faWin"Na cuci kaina!"
"Ina son na sani da gaske ke kika illan ta mahaifar ki Zeey sabosa bakya son ki haihu da ni,ko dama ba kya sona ne ko a kwai wani ™udiri a ranki."Yace bayan ya yi ™asa da kan shi dai-dai da kunninta saboda baya son aji me yake faWi.

Ta dago ta kalle shi fuskarta cike da hawaye ganin yadda fuskarsa ya bayyana da tashin hankali,don in ba ta yi ™arya ba har hawaye ta gani a fuskarta.
"Na shiga uku yanzu in yace ya na son ya haihu ga shi ni bana haihuwa ya zan yi?Kuma wallahi ba zan taSa iya lamun ce na gan shi da wata mace ba.Gara ma ace na ga ranar mutuwata!Tace a zuciyarta ta na kukan nadama.

"Ka yi ha™uri hubbi ka yafe min na san na yi wa rayuwata illa ba zan taSa haihuwa ba!Girman lamarin ya yi wa zuciyata girma.Duk akan sonka ne ina son karka juya min baya inna fara haihuwa na saki sanann jikina ya canza,kuma na sha jin kana faWin baka son jikina ya canza kafi son na kasance yadda nake.Kuma a wannan lokacin ban shirya haihuwa ba gani nake yara kamar takurane a gareni duba ga irin yanayin aikina."Sai ta fashe da kuka ta na ™arawa taci gaba da cewa."Wallahi ba zan iya buWe idanuna na ga wata mace a matsayin muharramar ka!In kuwa ranar ta kasance to kasa a ranka zan kashe kai na na kasheta sannan na kasheka.In ta™aice maka mutuwar kasko za muyi,don ina sonka ba zan juri wata a kusa dakai ba."
Tsananin tashin hankali ya shige shi tare da nadamar furta mata waWannan kalamai da yake na baya son yanayin ta ya canza,duk da be yi tunanin za su yi tasiri a gareta ba har ta aikata wannan abu su yi dana sani.

Ya zura hannun sa a aljihun wandon sa ya na kallon yadda fuskarta ya canza zuwa tsabar tashin hankali,ita kanta ya san ta yi nadama amma kuma mara amfani.
Ganin be ce mata komai ba ya na tunanin wanda shi kansa be san tunanin da yake ba,sai ta ci gaba da cewa."ko ma me ya faru duk akan sonka ne A.m ina kishin ka zan iya komai a kanka,son da nake maka ya sa na lalata mahaifata."
Ta kalle shi idanunta ya na zubar hawaye ta kama hannunsa ta haWa da nasa tare da kai bakinta dai-dai saitin kunninsa."Don Allah ka yi min wani al™awari,ka amince za ka yi min sannan gaya maka."
Ya dam™e hannunta ™a™am ya na hawaye matu™ar tausayinta ya kama shi ganin duk akan son shi ta shiga cikin wannan halin domin ta burge shi.
"Na yi miki al™awari amma wa ya gaya miki in mace ta haihu mijinta ya na tsanar ta ni fa ina yaba miki kyawun halittar ki amma ba wai ba na son ki haihu ba.Yanzu ya zan yi da iyayena da suka Wora idanunsu akaina suna son suga jikar su?"
a tambayeta ya na ganin tsananin wautar ta da ta aikata hakan,ita ma da ma wannan kan gabar take so yazo sai ta ™ara dam™e hannunsa tace." Ka yi min al™awari ba zaka taSa juya min baya ba kuma wannan ya zama sirri tsakanin mu cewar nice ba na haihuwa,sannan ka gaya ma dangin ka cewar matsalar da ga gareka take.Bayan haka ba za ka taSa yi min kishiya ba,in kuma ka yi to lai-lai nice ajalinmu baki Waya."
Ta faWa da farko da son ya Wauki al™awarin muryarta a sha™e ta na murza hannunsa,amma daga ™arshen maganarta sai ta ™arashe da murya kamar wacce take ba shi umurni ko tsoratarwa.

Rungumeta ya yi ya na jin matu™ar tausayin ta duk da girman lamarin amma sai be ga wata illa a ciki ba,musamman da ya ga duk akan sa lamarin ya faru don haka zai amince ya gaya wa iyayensa da hakan, dama shi a duniya be ga wata mace wacce za ta haWa kanta da Zey Win sa ba ita kaWai ya ji ta burge shi kuma zai ci gaba da son ta ba tare da ya haWa ta da wata ´a mace ba don babu ita a duniya.

"In dai akan wannan ne karki damu na miki al™awari,zan shirya mana viza zuwa ™asar indiya a duba min ke don ban yadda cewar ba zaki taSa haihuwa ba.˜ara ru™un™ume shi ta yi ta na faWin."I love you nureel ™albi.!"

Loakacin da suka ji Zainab ba lafiya hankalin su ya tashi take a ka cika asibitin domin sun Wauka ko ciki ta samu.Mahaifinta da ba shi ™asar ya na jin ta na asibiti ya biyo jirgi ya dawo,ya na ta addu'ar Allah ya sa ta samu juna biyu,saboda ya na tsoron kar ita ma ba ta haihuwa kamar Mominta,duk da ya so ya ™ara aure ta yi ruwa ta yi tsa™i ta hana.

Wani irin gata suke nuna mata sosai musamman gidan su A.m duk tunanin su ya sami Wa ne,saboda tunanin su ya sa suke yi mata abinci irin na masu ciki suna kawo mata.
Hakan sai ya sa jikin A.m ya yi sanyi ya na tausayin su don haka ya shirya musu biza suka wuce Indiya domin a duba lafiyarta.
Kwanan su biyu suka huta sannan suka fara ganin likita,sai dai gwajin farko da suka yi mata aikin gaggawa suka sa aka shigar da ita tiyata,saboda mahaifar ta fara ruSewa ta na narkewa a jikinta wanda hakan zai iya kawo mata matsala.A.m ya shiga tsananin tashin hankali duk yadda yake cikin tashin hankali sai ya kwantar da na sa ya na lallashinta ganin ta na son ta yi ™aramin hauka.

Be baro ™asar ba sai da ya tabbatar ta warke garau babu wanda ze ce an yi mata aiki.Sannan suka wuce zuwa yawon sha™atawa don ya kwantar mata da hankali.
Zainab ta yi kuka har ta ba uku lada daga ™arshe suka tattaro suka dawo cike da alhini.
A lokacin da A.m ya sanar ma family Win sa sun shiga cikin tsananin tashin hankali barim ma Daddy da har sai da ya yi kuka,ya rungume A.m ya na shafa bayan sa da tsabar tausayi da ya cika mishi zuciya." Yanzu son kai ma ba zaka ga ™wanka a duniya ba.Allah Sarki ni da kai ne kawai ba mu da rabon haihuwa."Sai ya ci gaba da sharara hawaye.

Mahaifin shi ya jinjina lamarin tsananin tausayin Wan na sa ya kama shi."Ni yanzu nafi tunanin matarsa an ya anyi mata adalci ina ga ka bata zaSi kawai,domin na tabbata da ita ne ke da matsalar aure zaka ™ara in kuma ta amince za ta zauna dakai kaga ba'a shiga ha™™in ta ba."Yace ya ba kallon Wan nasa cikin tausaya wa.

A.m ya ji matu™ar tausayin iyayen nasa ganin yadda suka tashi hankalin su,suna jimami da alhini anya ya kyuata musu kuwa.Sun ba shi tausayi matu™a wanda ya sanyaya jikinsa amma ko ma menene ya riga ya yi mata al™awari.
"Haka ne Baba nima na bata zaSi,amma tace ba za ta iya rayuwa ba ni ba."Ya ba shi amsa kansa du™e." To shikenan Allah ya kyauta ai faWan likita ba na Allah ba ne,sai kaga Allah ya canza lamuransa "Sun yi matu™ar jimami suka fauwala ma Allah lamuran sa ´an'uwan shi suna ta yi mishi tayin ya karSi yara daga cikin ´a´an su,duk da ya na son hakan sai dai ya san Zey Win shi ba za ta yarda ba.

Zaman nasu sai ya™i jituwa tun daga lokacin sai suke samun saSani da ya fara mata faWa, sai ta saka kuka tana faWa masa don ya ga ba ta haihuwa ne.
Tun ya na ha™uri har ya fara kai su gaban iyaye mahaifin shi kullum ha™uri yake ba shi ya na nuna mishi halin mata,dama tunna baya haihuwa ya shirya karSan fiye da haka a gurinta.

Rashin zaman ta a gidan shi yake ™ara damun sa kullum ya dawo aiki ba ze sameta a gida ba sai tarin ™azaman ´an aiki masu kama da mayu a gurin kallo.Shi ya manta rabon da yaci abinci me daWi in dai ba gida yaje ba ko,gidan amininshi A.k.Kullum ba ta da gurin zuwa sai ™awa ta gayyace ta bikin ™awarta ana birthday Win ´ar ™awarta aikin ta ne kullum yadda ka san ana tsikarin ta in ta zauna a gida mace kamar me aljanun fita yawo.

Ya dawo da misalin karfe huWu da rabi rabi na yamma yanayin garin hadari yake haWawa ya canza iskar garin ta na bada wani iska mai sanyi-sanyi babu abin da yake so ya sha ruwan tea me ™amshi ya shige cikin bargo ya yi bacci shi da ´ar matar shi.

Sai dai abin takaici ya na shigo da motarsa ya ga ba nata motar tsaki yaja ya yi parking Win motar a kasale ya fito be kula sannu da ma'aikan gidan suke mishi ba ya shige Waki.

Sharab!Ya zauna a falon sa ya na jin wani irin ™unci ya saka yatsu biyu ya tallabe gemunsa ya lumshe ido da takaici,burinsa ya buWe idanunsa ya sauke su akan kyakykyawar matar shi amma sai ya yi tozali da mero me aiki da tiren abinci ta kawo mishi tsaye ta na kallonsa.
"Ke!Uban wa kike kallo."Ya daka mata tsawar da yasa ta watsar da tiren abincin za ta ruga,sai kuma ta dawo da sauri ta tsaya ta na ™o™arin gyara gurin ganin iri n aika-aikar da ta yi.
" Anty ce tace na kawo maka abinci in ka dawo."Tace da shi bakinta na rawa ta na ci gaba da kallonsa.Ji ya yi tamkar ya sha™eta ya mi™e kamar ze kai mata duka da gudu ta ruga..
"Zainab kina bani tarin matsala na gaji da kwashe-kwashe da kike min gaskiya."Ya faWa idanunsa suka ™ara rinewa saboda tarin damuwar da yake ciki.

Bata dawo gidan ba sai zuwa ™arfe tara na dare ta shigo da gudu saboda ruwan da ake yi tamkar da bakin ™warya,a lokacin A.m na zaune akan kujera two seater ya matsu ta shigo yau sai ta gane kuranta.
Ba ta kula da shi da yake zaune da waya a hannunsa ya na dubawa ba,ta tsaya a falon ta na ™o™arin cire kayanta da ruwa ya soma ji™ata saboda tafiyar da ta yi zuwa cikin gidan.
Gyaran murya ya yi wanda yasa ta fahimci ya na falon gaban ta ya Wan faWi,amma ta dake bata ce komai ba sai ™o™arin ta na cire doguwar rigar da ya matseta kamar za ta yi amai,ta na ™wala ma Mero kira.

Wani ™arin haushi ya turni™e shi ita sam ba ta kishin jikinta ganin shigar da ta yi,sannan ta na cire kayanta amma take kiran me aiki tazo kai Zainab lamarinta a kwai gyara.
Bayan ta cire rigar ta umurci Mero ta Wauko mata wani wani kayan ta saka,sannan ta nufi gurin sa da yake zaune saboda tsaban takaici be kalleta ba bare ya tanka mata,sai kallon agogon hannunsa yake.
Ba tare da nuna damuwa ba taja tiren abincin da ya saka Mero ta kwashe wan can ta kawo mishi,saboda tsabar yunwa da yake ji amma ya kasa cin abincin sam babu tes jira yake a gama ruwan ya ya yi take away.

Fara ci ta yi ta kalle shi tace."Habibi ba ka ci abinci ba lafiya."Banza ya yi da ita yaci gaba da kallon wayarsa ya na danne-danne a cikinta.

Kai hannu ta yi ta taSa wuyan shi ko ta ji da zafi a tunaninta ba shi da lafiya,amma sai ta ji jikinsa normal.TaSe bakinta ta yi ta ci gaba da cin abincin a ranta ta na faWin."Miskilancinne ya motsa bari na kama kaina."

Kusan minti talatin ya na kwance be tanka mata ba har ta gaji da zama ya™i kunna kallo ta san ta na kunnawa, ze taso mata tunna dama a yadda ta gan shi jira yake ta taSo mishi,sai ta mi™e sif za ta shige Wakinta ta hau charting.
Idanunsa a lumshe ba tare da ya buWe ba yace."Da ga ina kike?"Yace a cikin wata irin murya me kama da da baya son maganar.
Dawowa ta yi ta zauna ta duburbuce ta fara in ina.Ya ™ara jeho mata wasu tambayoyin da cewa."Sai yanzu kika dawo ba na hana ki dawo min gida da daddare ba?Me yasa baki wuce gidan kuba.Kuma da izinin uban wa kika fita?"

Gabaki Waya ta tsorata ta kuma ruWe ganin yadda yake jeho mata tambayoyin da ta kasa amsa koda Waya ne.
Mi™ewa ya yi ya matso kusa da ita ya na kallon kayan da tasa ya Wauka ya na kallonta a wula™ance."Ba na hanaki saka irin kayan nan ba wai ke me yasa bakya kishin kanki yanzu fa a gaban ´ar aiki kika canza kaya,sam bakya kishin sirrina Zainab hauka kike son na yi a kanki na fara gajiya da halinki."

Duk cikin maganganunsa ba wanda ta ji haushi sai tambayar ta daga ina take da Wan yi jim ta kuma dake ta ba shi amsa da cewa."Ina tunanin mun gama magana akan fita ba sai na tambaye ka ba saboda gaskiya ban ga a na wannan takurar a gidan mu ba.Kuma fa gidan ™awar Anty Usaina muka je yau ake birthday Win Wanta."Ta ™arashe maganar ta na son ta ja hankalin shi ya sausauta fushin da ya Wauka.
Ya ™ara jan tsaki me ™arfi dama ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ™o™i.
Tsawa ya daka mata yace "Malama karki raina min wayo na gaji da waWannan banzan bidi'oin da kika saka a ranki.Kin raina ni matu™a Zainab baki Wauke ni da daraja ba a matsayina na mijinki,watakila haka kika ga ana yi a aure a matsayinki na matar aure ba zaki shigo gidana ba sai tara da mintina."
KaWa kansa ya yi ya mi™e yaci gaba da cewa."Kin san nace miki in har kika fita ba da izinina ba,ban yafe miki ba kuma mala'ikun rahama suna tsine miki harki dawo sai ki kiyaye."
Hararan shi ta yi tace cikin gunaguni."TaS ni ai na gaya maka ba zan amince a takurawa rayuwata ba.Haka kawai to meye amfanin ilmina na lura so kake ka mai dani irin gidahuman matan nan marasa ilmi,waWanda suke bari namiji na raina su wai duk in da zani saina tambayeka Allah ya kyauta."
Da takaicin yadda ta raina shi bata shakkar shi yace."Ba ma fita ba na hanaki driving sai dai duk in da zaki a yi driving Win ki."Ya na faWin haka ya fara taka matakalan bene ze haye.
A sukwane ta jawo rigar shi ta baya cikin fushi tace."Wallahi ba za ta saSu ba wai bindiga a ruwa Ka mata ni zan yadda wani shashashan direba ya tu™a ni,karka manta kusan motocina daga gidanmu na zo da shi bare ka yi min iko,in ma akan wace ka siya min ne ba zan ™ara hawa ba amma ba wanda ya isa ya kafa min dokoki."

Nu na ta da yatsa ya yi ya na cewa."Ba na hana ki kuma na yi miki warning akan ri™e min riga da kike yi ba,to wannan ya zama na ™arshe da zaki ™ara wannan gangancin.Kuma kika kuskura kika zage ni sai kin raina kanki,don jikin ki ze gaya miki."

Dariya ta yi me sauti ta ba shi amsa da faWin."A lai-lai da ka tabbata Wan ™waya kamar ni zaka buga aiko ruwan sama se inna so bare wani gardi can.Duk mutanen gidan ku kuwa sai an koya musu hankali ai ban yi kalar matar duka ba.Ko ka manta matsayin uba na."Ta numfasa sanann ta Wora ta na kallon shi da tsananin Sacin rai ya sa shi tsaye ya na kallonta.

" Kuma da kake faWin karna zage ka inna zage ka me za ka yi?"Tace mishi cikin zallar rashin kunya ta na karkaWa ™ugunta.A.m ya yi ™uta yace.
" To ki kwatanta ki gani fitsararriya kawai."
Baki ta turo mishi tare da murguWawa." Ni ba fitsararriya ba ce banza mara m....".

Wani irin mari ya gaura mata wanda yasa ta Wauke lokaci guda ta yi taga-taga za ta faWi amma ta dake tare da kwarma wani uban ihu,abin ka da farar fata lokaci guda fuskarta ta sunduma domin marin ya gigitata sosai.
Amma saboda taurin zuciyarta ta cakume shi ta na ihu ta na zagin sa shi kansa ya yi mamakin kafiyarta,ture ta ya yi ya shige Wakinsa tare da bugo ™ofar kai tsaye bayi ya wuce ya sakar ma kan shi ruwa,domin ta haWa mishi zafi kwanyar shi har wani tafasa take yi.





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na goma.Ga masu bu™atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ™ofa a buWe take na ™orafi gyara ko ™arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za™auran marubuciya,kuma ™awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ™ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA GOMA*

Bayan ya fito da ga wankan ya na jin yadda sautin kukanta yake tashi ya na mishi kuwwa a kunninsa,sai ya ji be kyauta ba da ya mari rabin ransa take ya zira doguwar riga ya fita don ya rarrasheta.

Šakin ta ya shiga ya ganta ta na ta kuka ta na haWa kayanta tare da ™o™arin kira a wayarta,sai dai da alamu ba ta samu wanda take kira ba.Wayar ya fisge tare da rungumeta cikin tsigar rarrashi.
Dukan sa ta fara a ™irjinsa ta na ™o™arin raba jikinta da na sa,da kyar ya samu ta sausauta kukan ta Wan yi shiru ta na sheshshe™ar kuka cike da shagwaSa.

Da ™yar ta ya samu ta yi shiru amma ta rantse mishi duk ranar da ya ™ara kai hannunsa jikinta sai ta haWa shi da Daddy Win ta,shi dai aikin lallashi yake ya na gaya mata maganganu masu daWi har da kama kunninsa ya na faWin ya tuba.

Bayan sun shirya suka kwanta cikin ™aunar junan su kamar babu abin da ya shiga tsakanin su.Yanayin garin sai ya basu damar yin bacci cikin shauki suna ma™ale da junan su.
Washegari suka tashi kamar babu wani abin da ya shiga tsakanin su na saSani.Bayan ya yi wanka ya fice gidan amininsa ita ma ta gallah wanka ta fice aiki.
Parking Win motarsa ya fito ya caSe Anwar Wan gidan A.k da ake goyo don yanzu ya iya tafiya.
Juya shi ya yi ya na dariya tare da Wauko tsarabar sa ya ba shi wanda duk ze zo sai ya kawo musu,sannan suka shiga cikin gidan sai ga ´ayarsa ita ma ta rugo da gudu ya Wauketa haka dai ya shiririce ya na musu wasa har ya Wauki tsawon lokaci.
" Yau kai ne a gari in ji ma™i ba™o ka ga angon Zainab to sannu da zuwa."Matar A.k tace ta na dariya bayan ta kawo mishi ruwa.
Shafa kansa ya yi ya na dariya yace."Gaskiya kince wani abu irin wannan kirari haka,kin san ™awar taki bata da dama ba ta bari na naje ko ina gaskiya kin cancanci tukwici."
Dariya ta yi tace."Gaskiya makka da madina nake so a kai ni."Tace da shi."Duk kin je sai sai in kina bu™atar zuwa sai na saka sunan ki a cikin jerin masu zuwa."Dariya suka yi duka.
Sannan ta wuce ta na gyara dinning domin cin abincin rana.Bayan A.k ya fito daga Wakin baccin sa ya ba shi hannu suka tafa tare da tsokanar junan su A.k yace."Ina madam Zey."Ya shafa gemun sa ya Wan canza murya yace ´ar rigima za ka ce min na san yanzu ta wuce gurin aiki."
Dariya ya yi shima ya na kallon shi."Ai hali ne ya zo Waya an haWu ne da an dace."Su kai dariya tare da ™ara tafawa."Madam ta gama shirya abinci ka zo muci."A.k yace da shi yamutsa fuskarsa ya yi ya na kallon shi, nan

Please Login or Register in order to submit comment