Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ikon Allah kenan duk da ta cire rai sai gashi Allah ya saka ta na da rabon yi.Abin da iyayen gidan ta suka zaSa mata ya sa ta ™ara yadda da cewar nufin su rayuwarta ba ta da wani amfani sai dai don ta yi musu hidima saboda girki suka zaSa mata,ita ta na ganin wani kalar girki ne ba ta iya ba,amma kuma da ta fara karatu sai ta raina kanta don gani ta yi kamar da can ba ta iya komai ba.

Ganin hakan sai ya dage damtse burinta ta iya girki ta yadda za ta siye zuciyar A.m,da take jin kamar ana mata wahayin son shi.

Duk da cewa makarantar sau uku take fita a sati amma ta na jin daWin karatun,sosai fiye da komai ba kamar da da ita kaWai take rayuwarta in dai matar gidan ta na nan.

Juwairiya ta yi ™awa Waya a makaranta wacce suka sha™u sosai duk da ba su daWe ba,sai dai ita matar aure ce har da yaranta biyu.

Suna matu™ar shiri sosai komai ma su tare suke yi ga halin su ya zo Waya ba ruwan su da hayaniya,musamman ita da take kullum cikin bege da ™aunar masoyin ta.

Kimanini wata uku da fara karatun Juwairiya wanda Zainab ta Wauko ´an aiki har guda uku sai A.m ya yi tsalle ya kawo ™auli da ba'adi.

Ganin haka sai ta kori Baba in da aka kawo mata mai jini a jika ta na koya mata girkin amma ba ta kwana don ta na da miji sai dai tun safe in ta zo sai magariba take komawa gida.

Ranar wata Juma'a Juwairiya ta tashi da ciwon kai mai zafi da zazzaSi ko tashi ta yi sallah ta kasa ga wani irin sanyi da yake shiga cikin ™ashin jikinta ya na nu™ur™usanta.

Abin takaici gashi suna da test don ana gabda yi masu jarrabawa.

Ganin ba zata iya zuwa ba gashi matar gidan ba ta nan kuma yau A.m zai dawo daga tafiyar da ya yi,wayarta ta Wauka tare da duba numbar ta kiran numbar Hauwa Tukur amma wayar ba ta shiga ba sai ta yi tsaki ta jefar da wayar ta kwanta.

Ta na kwance jikinta na ™ara zafi sosai kamar wuta misalin tara sai ga kiran Hauwa Tukur ya shigo,da ™yar ta janyo wayar da ke kusa da ita ta kanga a kunninta ta na nishi a wahalce.
"Hello Juwairiya ba za ki zo makaranta ba ne lafiya kin san muna da test ga shi Malam D.d ba shi da mutunci."Hauwa Tukur ta faWa a ranta ta na tunanin mai ya hanata zuwa,kasancewar ba ta wasa da karatu.

" Wallahi ba na jin daWi ne kin san sai da lafiya ake komai.Don Allah ki yi min test Win in zai yi wu."Ta ba ta amsa ta na kyarmar jiki.

Bayan ta yi mata sallama tare da mata al™awarin in dai ya yadda za ta yi mata ta kashe wayar ta koma ta kwanta.

Sai misalin shidda na yamma A.m ya shigo babu abin da ta yi masa na abinci.
Ganin halin da take ciki ya ruWe sosai kamar zai yi hauka a tunanin sa ciki ta samu,don haka jiki na rawa ya Waga waya ya kira likita ya zo ya duba ta.

Juwairiya ta ji hankalinta ya yi ™ololuwar tashi jin ya kira likita ita yadda take jin ciwon gani take kamar ciki ne.

Kawai sai ta ji hawaye ya fara sauka a ™uncinta don ta san lokacin rabuwar su ya yi daga ranar za su fara irga kwanaki.

Bayan likita ya zo ya yi mata gwaje-gwaje ya sa ta yi fitsari ta kawo masa.

A.m da ya yi zugum duk ya ™osa ya ji abin da likitar zai faWa,ya na ta addu'ar Allah ya sa likita ya yi mishi kyakykywan albishir.
"Ga wannan maganin za ka siyo maleria ce ke damunta in sha Allahu tasha magani za ta warke."

Hankalin sa ne ya tashi matu™a kawai sai ya ji hawaye na son ya zubo a ™uncin sa yayin da zuciyar sa ta karye da tunanin zai samu Wa.

Jikin sa a sanyaye ya karSi takaddar ya fice tare da likitan don ya siyo magani ko kallon ta da take zaune bai yi ba.

Wani wawan ajiyar zuciya ta saki wani irin sanyi ya ziyarce ta jin ba ciki ta samu ba.

A ™alla sai da ta yi kwana uku sannan ta warke sarai ta shirya ta tafi makaranta.

Suna zaune da Hauwa Tukur ba yan sun fito daga lakca Hauwa Tukur da hankalinta yake kan danna wayarta ta kalle ta da ta zuba uban tagumi ta yi nisa gurin karanta wasi™ar jaki.

"Yawan tunani ba shi da amfani ga lafiya kuma ban ga dalilin da zai saka ki zo makaranta ki zuba uban tagumi,ba yan kin baro gwarzon ki a gida nifa da kika ce baki da lafiya na Wauka ciki ne da ke."

Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta ta zare idanunta ta na kallonta.
"Subuhanallahi ciki kuma ni fa ba matar aure ba ce."

Ta faWa tare da gwalalo idanu jin abin da ta faWa yayin da take mamakin mai ya saka ta faWi haka.

Sakin dariya mai sauti ta yi ta Wauki lemun robar da Juwairiya ke sha ta zu™a tare da kwashewa da dariya.

"To don Allah meye na tsorata haka sai ka ce na ce kin yi kisa."

Ta faWa ta na mamakin yadda ta razana haka saboda ta ha™i™ance ma kanta ita matar aure ce,sai dai in ba ta son ta ga ya mata amma ko wa ya kalle ta ya san ta na da aure.

"Haba Juwairiya ko wane mutum ya kalle ki ya san kina da aure kin san a kwai matan da dole a gane matan aure,duba ga yanayin jikinta ki kalle kanki kema kin san bakya son ki gaya mini ne,to ki mai da wu™ar ni ban ce zan gan shi ba bare ki yi tunanin ko zan bashi ™anwata ne."

Ta ce da tsigar wasa saboda ta na son ta kwantar da hankalinta ganin yadda ta birkice lokaci guda.

Jin abin da ta faWa sai hankalinta ya tashi sosai duk da gargaWin da zuciyarta take mata na kar ta faWa mata halin da take ciki,amma ta na jin lokaci ya yi da za ta daina shanye damuwarta ita kaWai ta sanar da ita ko don ta samu shawarar yadda za ta cire son maso wani a ranta.

Kama hannunta ta yi ta haWe da na ta ta kalli ta cikin muryar son kuka ta ce."Tabbas tunanin ki haka ne amma ina bu™atar mu samu in da babu mutane ina da damuwa ina son ki ba ni shawara."

Ganin ta fara kuka sai ta ri™e hannunta suka koma in da babu mutane.
"Tabbas tunanin ki gaskiya ne ina da aure amma auren sirri na yi da mijina na shekara Waya."

Sai ta din ga kallonta irin kin zare kenan ko kuma baki san mai kike faWa ba ta kasa magana sai kallonta take yi.
Ganin ta kasa yadda da abin da ta faWa mata sai ta ™ara fashewa da kuka ta na jin wani irin zafi a zuciyara ta.


Hauwa Tukur da ta yi shiru ta na jinjina wannan lamarin mai kama da shirin fim ko hikaya a gare ta!A ranta ta na mamakin ta ya ya za'ai wannan aure ba tare da sanin mahaifiyarta ba!Ita ko wani irin so take mishi?An ya ta yi tunani kuwa mai ya kai ta namiji ba Wan goyo ba ne Wan masara ne ana goyon shi ya na kayan gemu."

Maganar zuci take amma ba ta san maganar zuci ya fito fili ba.
Ta ri™e hannunta ta na kuka sosai ta ce ba yan ta yi murmushi mai ciwo."
Dole ki jero min waWannan tarin tambayoin ni ma na san na yi kuskure,kullum cikin dana sani da kukan zuci nake yi."

Ta saki hannunta ta mi™e tare da juya mata baya ta ™ara ce wa da ita."Allah ya jarabce ni da tsananin son shi sosai,amma A.m ya tsane ni baya sona ni ce mace ta farko da ya tsana saboda a koda yaushe cutarwa ce a tsakanin mu ya na ™ara saka min son shi a raina.

Na san ce wa ban yi ma mahaifiyata adalci ba amma babu yadda zan yi ne Baba Sani ya™i taimakonmu,gashi ba na son na rasa ta,kuma ko banza auren sa ya ceci rayuwata daga auren Alhaji Tanimu,amma kuma yanzu ina tsoron ranar da A.m zai rabu da ni na san ranar ita ce ranar da fitar numfashina zai yi bankwana da gangar jikina."

Hauwa Tukur da take jin tashin hankali ita mamaki take ba ta da har ta yadda za ta iya saida Wanta,amma sai ta danganta shi da don ba ta san son da yake tsananin uwa da Wanta ba ne shi ya sa ta aikata wannan aiki,da kuma zafin talaucin da take ciki uwa uba Baba Sani da ya ke mugu azzalimi.

Ta nisa sannan ta fara magana cikin mamakin mugun hali irin na Baba Sani.

"Gaskiya na ga wauta da ™uruciyar ki duk da kin yi hakan ne saboda ki taimaki rayuwarku,amma a kwai kuskure a ciki haba ta ya ya zan amince na auri mutum kuma na zauna a matsayin mai aikin matarsa har na iya wanke mata ™azantarta wallahi hakan ba zai yi wu ba,na tabbata da kin ™i amincewa in dai idon A.m a rufe yake ya na son yaro dole ya naimi wata hanyar k..."

"Don Allah ki fahimce ni na san na yi kuskure amma kuma abin da ya faru ya riga ya faru!Ki ba ni shawarar yadda zan saka soyayyata a cikin zuciyar sa,yadda dake ya sa na bayyana miki damuwata saboda friend in need is a friend indeed."

Ta katseta jin ta na ta maimaita maganar da wautar da ta yi bayan ta san hannun agogo ba zai taSa dawowa baya ba.
"Wane shawara zan baki ni fa ina son naga ranar da wannan lamari zai fasu har na za™u da na ga kin yi ciki don a kwai turka-turka kina ganin Zainab za ta yadda ta karSi yaron ne?shi kan sa bai yi tunani ba domin ya ibo ruwan dafa kan sa ala'mura canzawa za su yi saboda man propose but Allah dispose. Sannan babban kuskuren da ya yi na kawo ki gidan sa Zainab ta sanki ina tausaya masa lokacin da maganar ciki za ta fito fili,don Zainab ba ™aramin hauka za ta yi masa ba.

Ni yanzu shawarar da zan ba ki shi ne ki ™o™arta a ki samu ciki za ki ga yadda komai zai canza."

Saka kuka ta yi ta ce."Shawarar da za ki ba ni kenan?ba ki san waye A.m ba kuma ba ki san Zainab ba shi ya sa kike ganin kamar inna samu ciki zai soni wayar ta ta ciro ta nuna mata hoton A.m da Zainab wanda ta Wauke shi na falon su da suka manna..

A duk lokacin da ciwon son shi ya kamata sai ta ciro hoton ta na gani saboda zuciyarta ta sare da soyayyar A.m ganin irin zu™e™iyar matar da yake aure,amma haka ba ya canza komai ta na ganin son shi kamar wahayi ake mata.

"Duk da wahalar da shi da Zainab take mata har ™asashe take fita kasuwancinta amma kullum ya na gaya min ita ce matar so ni matar wucin gadi ne,amma abin takaicina sai ya zo ya din ga more ni ya na gaya min irin baiwar da Allah ya yi min bai taSa kuskuren faWin ya na sona ba."

Hauwa Tukur ta yi matu™ar tsorata da ganin su kamar wasu larabawa yanzu ta gane dole jikinta ya canza saboda irin daular da take ciki.
Hannunta ta ™ara ri™ewa ta ce."A.m ya haWu irin mazan nan ne masu wayo da dubara sam ba za ki taSa gane in da ya dosa ba,amma na yi mamakin in da kika samo wannan gayen saboda ma™ura ne gurin kyau."

Murmush mai kama da kuka ta saki."Don Allah ki ba ni shawara yadda zan jawo hankalin sa."

Numfashi mai ™arfi ta."Ikon Allah ita Zainab wata irin banzar mace ce ina tausaya mata ranar nadamarta saboda na ga sakacinta sosai mace sai kace mahaukaciya abubuwan da take yi sam babu tsari aciki kuma ni na fi ganin laifin A.m da ya barta take mishi wannan iskanci.Gaskiya ba na goyon bayanki da kike kare kanki daga Waukar ciki, wanda ko ba a faWa ba na san irin kuskuren da matar sa ta yi kenan kuma na tabbata ta na nadama.Ga kuma in da son duniya ya kaita haba ai ya raina mata wayo ya kawo matar sa cikin gidan ta ya na more abar sa ya maida ita shashasha.

Duk da ita ta na tunanin ba zai taSa duba gareki ba saboda ba ku dace da juna ba tunaninta bazai kawo mata zai iya Waga ido ya kalle ki ba duba ga matsayin sa,ba ta san namiji ba haka yake ba abin da kake ganin yafi ™arfin sa sai kiga ya mutu akan abin."
Sai ta kwashe da dariya ta duk da ganin halin da take amma rainin wayon ya yi yawa gani take kamar ya na raina musu wayo ne daga ita har Zainab Win.

" Matsalar ka bayyana damuwarka ga mutumin da ka yadda da shi kenan na yi tunanin za ki ba ni shawara,amma ba ki duba halin da nake ciki ba kin tsaya ki na min dariya."

Ta faWa a zuciye tare da Waukar wayarta za ta tafi.

Da sauri ta Wauki jakarta ita ma ta kama hannunta."Afuwa lamarin ne a kwai rikitarwa ni dai ina baki shawarar ki kasance a shirye, saboda duk ranar da Zainab ta san abin da ke tsakanin ku Allah kaWai zai raba ku lafiya yanzu ki Waga waya ki kira A.m ki sanar mishi da kina son shi mijinki ne fa,wanda yake dawowa ba yan ki ya kwanta mai zai hana ki sanar da shi."

Ta ce mata ta na kallonta a ranta jinjina lamarin take yi."Ba zan iya gaya masa ba kuma ba zai bani damar haka ba haba ya kamata ya ce ya gane irin son da nake masa ko ™wayar idanuna ya kalla ya kamata ya gane."

"Ai ko dole ki sanar masa meye amfanin dakon son mutumin da bai sani ba kuma ko banza,daga ranar da kika gaya masa irin son da kike masa wallahi ko baya sonki ya kalle ki a matsayin kina son sa zai din ga kallon ki kuma ko banza masoyinka yafi ma™iyin™a sannan a tunanina a haka wani abu mai girma zai shiga tsakani ba tare da ya sani ba."

Juwairiya jikinta ya yi sanyi matu™ar gaske zuciyarta ta halasto mata irin tarin son da take dakon sa ta ji ya na tasowa nan take ta faWa kogin zuma har ta ji za ta iya kiran sa ya zo ta sanar mata da damuwar zuciyarta duk da kafin su yi aure sai da suka yi sharaWin babu wannan wayarta ta zaro domin ta kira shi.


WANI IRIN FIRGITA NA YI SABODA BUGUN ZUCIYAR JUWAIRIYA DA NAKE JI YA SA CIKINA YA MURŠA NA TASHI DA NUFIN NA JE BAYI,AMMA KODA NA DAWO TSABAR TASHIN HANKALI BAI SA NA GANE MAI KE FARUWA BA SABODA SAUKAR BUGUN ZUCIYARTA JI NAKE KAMAR ANA BUGAMIN GUDUMA.
TOFA KO YA ZA TA KAYA A M ZAI AMINCE DA SOYAYYARTA?

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu™atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ™ofa a buWe take na ™orafi gyara ko ™arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za™auran marubuciya,kuma ™awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ™ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.





COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.






*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 24*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A tare zuciyarta take bugawa da ringing Win da wayar take yi.Ta kira sau biyu bai Wauka ba sai jikinta ya yi sanyi ta ije wayar,ta kalli Hauwa da ta kafe ta da ido.
" Na kira shi amma bai Wauki ba ina tunanin wayar ba ta kusa da shi."Ta faWa cikin karayar zuci.

Zama sukai suna jiran kiran wayar ko wannen su zuciyarsa na buguwa tamkar za ta fito.

Sun jima a gurin suna jiran kiran sa har suka gaji.Ita ta fara mi™ewa ta kalle ta ta ce." Mai zai hana ki fara nuna masa so misali ki din ga nuna mishi kin yi kewar shi ,da kalamai masu zafi kuma ki din ga tura masa,ai shi ba yaro ba ne dole ya fahimta wata™ila ya san za ki kamu da son sa shi ya sa ya ce kar maganar so ya shiga tsakanin ku."

"Ki na ganin haka shine mafita na riga na Waukar wa kaina in har bai ce ya na sona ba ba zan taSa yadda na bar ciki ya fito a jikina ba."Ta gaya mata cikin sassanyar murya.

" Allah kawai ya san me ya Soye a gaba amma ki dage da addu'a kuma ki din ga nuna masa irin yadda kike son sa a aikace ke fa matar sa ce,kuma tun da ya har ya iya haWa jiki da ke ban ga abin da zai hana ya soki ba,amma ni fa nafi son ki bari ki sami ciki naga irin haukar da zan yi.

Maganar ya gundireta fara tafiya ta yi ba tare da ta ce mata komai ba, a ranta sam ba za ta amince da shawarar ta ba, ta yi al™awari ba za ta dai na zubar da ciki matu™ar ba zai zauna da ita na har abada ba.

Kamar yadda suka shirya sai ta fara Wan sakin layi ta na yi masa wasu irin abubuwa saSanin hankalinsa saboda har mamakin ta yake wai dama haka take!

Duk wani abin da take mishi ya biye mata har ma ya na mata fiye da haka.

Ranar da suka shirya za ta gaya mishi amma a waya don ba za ta iya taran idanun shi ta furta mishi ba.
Da fari text ta ce za ta rubuta mishi sai Hauwa ta ba ta shawarar ta kira shi.

Cikin sa'a ringin Waya ya Wauka ta na sanar mishi da ta na son ta yi magana da shi kuma maganar is verry important sannan kuma comfidential.

"Ok ba ki da damuwa tun da kina cikin makaranta ki bani Wan lokaci,ina gidan A.k na je gaida matarsa ni da Zainab bari na shigo cikin makarantar,ba sai kin gaya min a waya ba."

Duk yadda ta so ta hana shi zuwa don tafi son su yi a waya amma ya kafe ga shi nan zuwa,daga bisani kashe wayar ya yi ganin za ta yi masa gaddama.

"Ya ce ga shi nan zuwa ya™i yadda na gaya masa a waya."

Ta faWa yayin da zuciyarta take bugawa."Gaskiya ya na girmama lamarinki bari na Soye yau ina son na ga A.m, a zahirin gaskiya da ya sace zuciyar rabin raina ya hana ma ™awata sukuni."

Dariya ta yi ta kauda kanta ba ta ce komai ba saboda ™irjinta yake bugawa.

A lokacin da motarsa ta shigo sai Hauwa ta mi™e da sauri ta laSe,ta yadda za ta din ga kallon duk abin da ke faruwa ba tare da ya ganta ba.

Har kusan in da take ya ™araso da motar sa sannan ya yi parking ya fito ya taho in da take.

Kallonta ya yi lokacin da ya zauna akan Waya daga cikin kujerun, da suke a gurin tare da sakin wani wawan ajiyar zuciya.

"Kin tsorata ni fa wallahi na Wauka ko babu lafiya,amma tun da na gan ki lafiya lau faWa min matsalar ki."

Ya faWa ya na kallonta tare da ri™e mata hannu suna kallon juna ido cikin ido.
Sun Wauki tsawon lokaci suna kallon junan su ba tare da sun ™ifta ba.
Da sauri A.m ya mi™e tare da juya mata baya domin ko ba ta faWi abin da take son faWi ba,idanunta sun bayyana tsa™on su dama ba tun yau ba yake ganin ta na sakin layi,wanda yake biye mata don ya faranta mata.

In ko ta na son ta faWa masa son shi take, kamar yadda ya gani a ™wayar idanunta, ya kamata ya yi maza ya dakatar da ita, don ba zai taSa son wata mace ba bayan Zainab Win sa.


Juyo wa ya yi ya kalleta ta da take ta in da inda ta in da za ta fara."Juwairaah kar ki ce ki na sona don ni ba na sonki."

A zabure ta tsaya gaban sa ta fara hawaye kamar an buWe famfo.

A hankali ta nuna kanta da yatsa ta ce."Ba ka sona A.m da gaske ba ka sona kake yi min abubuwa irin na wacce ake so?"
˜ara masowa ya yi kusa da ita."Yes ni fa ban taSa jin ina son ki ba,kawai ina girmama lamarin ki kamar yadda na sha gaya miki.Saunawa kike son na gaya miki ba na sonki ko kafin na aure ki na faWa miki,Zainab ita ce macen da nake so kuma na aure ki da sanin ki akan ki haifa min yaro na bata.Wai mai ya sa kike dawo da hannun agogo baya ne?"

Ya faWa cikin Waga murya duk da babu mutane sosai a gurin sai Waya biyu,amma har an fara taruwa ganin ya na magana da ™arfi.
"Ina sonka ba zan fasa sonka ba!Na fara sonka tun kafin ka bijiro mini da aurenka, kuma na san kai ma ka na sona sau nawa kasha faWa mini ka na son surar jikina da halina,mai ya sa ba za ka so zuciyata ba?"

Ta faWa cikin muryar da tafi nasa amo don ji take kamar za ta yi hauka.
"Ni fa ban taSa ce wa ina sonki ba sai surar jikinki,kuma ta ya ya zan yi na saka son macen da na san ban ba mu dace ba.Ki tuna mahaifinki har ya mutu bai bar muku komai ba,sanin kan ki ne mahaifina ya yi fice a duniya."

A.m ya faWa ran sa na suya ganin ta na son ta tara mutane, wannan kamar cin mutunci ne mai ya sa ba ta gaya masa a gida ba.

Cikin jin zafin ta ya fara tafiya zuwa motar shi, da gudu ta bishi ta dur™usa a gaban sa ta na hawaye."Tabbas haka ne ka faWi gaskiya mahaifina bai bar mana komai ba sai talauci,amma ka sani ba kuWi ba ne kawai Allah yake sawa a so mutum shi ya sa har yanzu na kasa gasganta son Zainab kake yi.
Saboda ka na sonta ne don kawai ita ajin ka ce na san watarana za ka fahinci gaskiya, za ka gane a kwai baiwar da Allah ya kan yi ma bayin sa aso su ba wai sai dukiya ba.

Ni na san watarana za ka soni kuma sai ka yi nadamar abin da ka gaya mini ko ina raye ko ba ni raye."
Ta numfasa ta na jan numfashi ganin ya yi shiru ya na kallonta sai ta Wora da ce wa."Ina sonka ba zan fasa sonka ba sai ranar da numfashina ya yi bankwana da gangar jikina."

Tafiya ya fara yi bai ce mata komai ba.Kamar wata zararriiya ta mi™e ta juya ta na kallon shi ta kira sunan shi.

"Ina sonka! Ina sonka!! Ina

Please Login or Register in order to submit comment