Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya faWo mata a rai kenan ta saki wani irin ara,da sauri ta sauko har tana faWi ta mulmulo amma ba ta kula ba.

Wayam babu ita sai wayarta dake yashe a kan gado.Da sauri ta Wauki wayar duk da ta san a halin da take ciki ba za ta iya karanta komai ba.

TO FA ARA! ARA!! ARA !!!





KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.








*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 27*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Ta na rie da wayar cikin tsananin tashin hankali yayin da jiri yake iban ta da yar take iya buWe wayar idanunta.

Sai dai duk iya iyakan oarinta don ta gano pattern Win da ta saka wayar,amma ta kasa har ta haura za ta kwaWa wayar da asa sai kuma ta fasa,ta ara kwatantawa sau biyu cikin ikon Allah a na biyun wayar ta buWe.

Bincike ta fara yi a wayar wanda iya yinta ba ta ga wani abu da zai dasa mata zargi ba,saboda Juwairiya ta adana duk wani abin da ya shafi A.m a cikin wayar ta Soye shi.

Ta yi nufin ta ije wayar sai kuma wata dubara ta faWo mata ta danna numbobin A.m.

Tana fara danna numbobin sai ga numbar A.m ta fito Saro-Saro an yi saving Winta da rubutun larabci,wanda iya wawanta ta yi ta gane mai sunan yake nufi,amma ta kasa saboda rubutun babu wasulla,ga shi karatun arabin na ta an yi Wan cikin cokali.

Durushewa ta yi a gurin tare da saka wani gigitaccen ara,kamar wata mahaukaciya ta fara rotsa,duk wani kayan awa dake cikin gidan tana unduma ashar.

"Wallahi ku dawo gidan nan nice ajalin ku sai na kashe ku duka mundin na gane cin amanata kuke."

Gurin mai gadi ta nufa kasancewa yau Lantana ta na hutun arshen mako da take yi.

"Kai ina A.m ya yi bayan gida a buWe sannan Juwairiya ita ma ba ta nan?"


Jikin sa ya kama rawa dama tun da yaga Am ya fito da Juwairiya a hannun sa,ya sha mamaki ganin tana matsayin mai aiki ya Wauko ta.

Sai ya ara kallonta ya ga yadda ta birkice kamar wacce aka kwanto daga turu, tana zare ido ai ba za a ji mutuwar Sarki a bakin sa ba.

" Hajiya ban sani ba da yake na zaga bayi yau na tashi da motsawar ciki."Wani wawan mari ta sakin mishi.

" Banza wawa kawai banga amfanin aikin ka ba."

Ta juya saboda ba ta cikin yanayin da za ta iya wani dogon magana.

******
A.m da ya shae ta tamkar zai kaita lahira yana jin zai iya kashe ta,saboda tsabar tashin hankalin da yake ciki.Ga baki Waya idanun shi sun yi jajur tamkar garwashi wuta,ya canza kalar da ba ta taSa sanin yana komawa ba.


Da yar take kakari saboda wahalar da ta sha,ga kuma A.m yana shirin kaita lahira ba tare da kwananta sun are ba.

" Uban me na yi miki da za ki kashe min yaro?Da kuWina na siye rayuwarki a she ke kike hana ciki ya shiga jikinki? Na rantse yadda kika salwantar min da yaro sai na kashe ki."

Juwairiya da take jan numfashi da yar idanunta sun yi gulu-gulu,domin A.m ya yi mata shaa ba na wasa ba.

Likitan dake tsaye yana kallon A.m da ya zama mahaukacin arfi da yaji,tsoro yake ya matsa kusa da shi kar ya illata shi,amma da ya ga yana shirin kisa,sai ya matsa tare da rie shi da arfi ya ce."Ma za ki tashi ki fita don ki ceci rayuwarki."
Duk da ba ta jin arfi a jikinta amma haka nan ta ruga,daidai lokacin da A.m ya ture likitan ya faWi asa ya bugu da bango,ya Wauki wani arfe dake gefe ya Waga zai maka mata.


Da sauri ta fice daga Wakin cikin tashin hankali, tana jin kamar ta sume jikinta babu daWi,amma ya zama dole ta ceci rayuwarta,don yau ta ara tsoron A.m sosai a ranta.

A.m da haushi ya ishe shi ganin Juwairiya ta gudu,ya san ko ya duba ta ba zai gan ta ba,saboda asibitin bene ne ga lungunan dake cikin asibitin,arfen da ya yi ninyar maka mata shi ya buga ma likitan,tare da ficewa da sauri yana neman ta.

Sai dai ya nemeta sama da asa bai ganta ba ara ya saki cikin araji, ya rantse yau da ya ganta sai ya raba ta da numfashinta,sannan kuma sai ta gaya masa dalilin ta na zubar masa da ciki.

Ya kai ma iska naushi cikin takaici yana dunule hannun sa,ji yake kamar ita yake duka.Allah ne kawai ya taimake ta da ta gudu da yau sai dai wata ba ita ba.


" Wayyo Allah dama ina haihuwa da gaske zan iya haihuwa?"

Ya daWe a gurin yana ganin kamar za ta fito daga arshe ya shiga motar sa,wanda Allah ne kawai ya sa ya iso gida.

Sai dai yana shiga cikin gidan ya tsaya cikin tsoro ganin an yi ma gidan kaca-kaca,komai na gidan an fasa hatta tv dake manne plasma duk ta yi raga-raga da su.

Ko da ya shiga cikin Wakin sa sai ya gwammace gara Sarnar falo da ta yi akan na cikin Wakin,saboda duk wani takaddu na shi na amfani sai da ta yaga su ta yi mi shi Sarna sosai.

Tsayawa ya yi da mamaki yana kallon ta tsoro ma ta ba shi,ganin yadda ta wargaza gashin kanta ta zama kamar wata mahaukaciya.


Tashin hankalin da yake ciki yasa ya kasa tambayarta abin da yake faruwa,duk da zargi da yake yi akan ta gane komai.

Zainab ta araso gurin sa cikin tashin hankali,ta shae shi idanunta sun canza kala,tsabar kishi cike a idanunta ji take kamar ta kashe shi,kawai ta huta domin ya cuce ta.

" Munafuki azzalimi mayaudari yau Allah ya tona asirin ka,dama amanata kuke ci kamar yadda Lantana ta faWa min ka arya ta?
A.m Wanka kake son ya fito ta zina ?Ba na haihuwa mai ya haWa ka da maganin Waukar ciki da wuri."

Duk da cewar ya ji maganar ta dake shi amma sai ya sauke ajiyar zuciya da ya tsaya iya nan ta sani.
" Zainab ki fahimce ni wallahi ba na zina kuma ba zan taSa yi..."

"Rufe min baki mazinaci kawai? Yau Allah ya tona asirin ka na gama yadda da kai.Ni da ba haihuwa nake ba,in fact ba ni da mahaifar da zan Wau ciki kake shan wayoyin Waukar ciki da wuri."

Ta ja numfashi da sauke nauyayyar a jiyar zuciya,tana gumurzun kuka gaba ki Waya ta fita hankalin ta.

A.m da ya rasa abin yi arasawa kusa da ita ya yi yakai hannu zai taSa ta,da sauri ta janye jikinta tana mishi wani wulaantaccen kallo.

" Ni Allah ya tsare ni na ara barin ka taSa ni da hannun zina ai..."

" Zainab!"

Ya katseta cikin araji sannan ya nuna ta da Wan yatsa." Kar ki ara kirana da mazinaci in ba haka ba jikinki ne zai gaya miki."Ya ce cikin Sacin rai.

" To meye kai in ba mazinaci ba ko fasii kake son na ce maka,wallahi na tsane ka ba na son ko kallon mayaudariyar fuskar ka,dole ka sake ni ba zan zauna da mazinaci ba."

Ta ce tare da ara cikwikwiye shi sannan ta Wora da cewa." A.m yar aikina fa kake nema!Na shiga uku Juwairiya ar matsiyata mai take da shi wanda ba ni dashi?"
Girgiza hannunta yake yi akan ta sake shi,ya fara magana da muryar sa da yake sace mata zuciya,amma sai ta Waga mishi hannu dare da daka mishi tsawa,kamar wani aramin yaro tana masa wani mugun kallo.

"Sake ni na ce ka bani takadda ta kuma na rantse maka,sai na maida Juwairiya kalar da duk wani Wa namiji ya ganta ba zai yi sha'awar ta ba.Ai ni ka gama tsara ni da kalamanka na yaudara matsiyaci kawai."
wace jikin shi ya yi yana hararar ta ji yake kamar ya kai mata bugu,ganin ta ara masa tashin hankali.

" Ki san maganar da za ki gaya mini mijinki ne, ni in har kika ara zagina zan miki hukunci,yanzu jikinki zai gaya miki ba tare da na yi nadama ba."

ara cakumo shi ta yi ta kama gaban rigar sa ido cikin ido ta ce."Na faWa kuma abin da ya fi haka zan faWa banza mai zan yi dakai sake ni na ara faWi mazinaci azami!"
Mari ya kai mata amma sai ta goce da sauri tare da fisgo rigar shi,ganin ya na son ya fita a Wakin ta kama ta sai da dire ta har asa.

Duka ya kawo ma hannunta da arfi ta saki jikin shi tare da sakin ara,amma kuma sai ta yi kukan kura ta kama shi da dambe.

A.m da yake jin zuciyar shi a wuya ba tare da tunani ba,ya shiga jibgar ta kamar ya samu jaka don iya arfin sa yake dukan ta.

Da fari ta biye mishi tana kokuwa da shi,amma da ta ji kasheta zai yi,da gudu ta ruga Waki ta Wauko gyale sai gida.

A.m ya durushe a gurin cikin nadama tare da kai ma bango naushi." Tabbas na gasganta cewa ke Win ba alkhairi ba ne a rayuwata!Juwairiya na tsane ki kuma wallahi sai kin yi nadama sosai,don sai na illata rayuwar ki yadda kika sa na doki matata mafi soyuwa a gare ni."


Juwairiya da take jin rashin arfin a jikinta,amma haka take gudu don ta tseratar da rayuwar ta,saboda yau ta ara gasgantawa A.m ba shi da imani kashe ta zai yi.
Hawaye yana zuba a fuskarta da ta tuna irin tashin hankalin da A.m ya shiga,saboda jin ta zubda ciki nan take tsananin nadama ya shige ta sosai.
Tsayawa ta yi cikin tashin hankali ta rasa in da za je,gidan Hauwa ya faWo mata a rai sai ta tari Wan mashin.

Tana shiga ta rungume Hauwa da ta fito daga cikin Waki jin muryarta tana kuka.

" Juwairiya lafiya mai ya faru?"Ta tambaye ta cikin tashin hankali.
" A.m ya yi fushi da ni na shiga uku! Wallahi ya tsane ni baya sona!"Ta ce tare da sakin wani irin kuka.

" Don Allah ki daina kuka ki yi mini bayani mai ya faru."
Ganin ta kasa magana sai kuka take na fitar hankali.

Zaunar da ita ta yi sannan ta ba ta ruwa tasha sosai ta kama hannunta ta rie." Don Allah ki gaya min mai ya faru."

Zubbur ta mie tare da Waukar hijabinta.Hauwa ta rie mata hannu ta ce." Wai mai ke faruwa ina A.m ki sanar da ni."

" Gurin A.m za ni ya yi fushi da ni ya gane na zubda ciki,don Allah ki zo mu je mu bashi hauri,wallahi ba zan iya rabuwa babu shi ba,don ina son sa."

Da takaici ya ishi Hauwa tsaki ta yi ta kamata tare da zaunar da ita akan kujera." Ba na son shashanci kin san ba kya son ki rabu da shi,kika zubda cikin da yake so?Babu yadda ban yi da ke ba,amma da yake kunnin ashi ne dake kika ji i.Na rasa yadda zan yi ba kya jin magana haba ya kamata ki fahimci mai kike yi."

Share hawayenta ta yi ta ce." Zan je na ba shi hauri ba zan ara zubda cikin ba,in dai haka zai saka shi farin ciki,amma ki je ki ba shi hauri don Allah."

Hauwa ta yi shiru ta na jinjina lamarin domin sam bai yi mata daWi ba,ta san da ma in dai A.m ya sani gakan zai faru,gara da ya sani ya Wauki mataki.

" Hankalina ya tashi sosai baki ga irin fushin da ya yi ba ,na san cewa ba zai taSa nema na ba,gashi garin neman gira na rasa rasa ido.Na san ayanzu ya tsane ni ba ya son ganin fuskata.

" Rashin Waukar shawara irin na ki shi ya ja miki,Juwairiya ya kamata ki gane gaskiya.Ni dai yanzu shawarata kar ki ce zaki koma gurin sa saboda ya yi fushi dake mai tsanani."

Ta ce tana kallonta da takaicin abin da ta jawo ma kanta,sannan ta ci gaba da cewa."Yanzu kin ga ba ki da lafiya ki ci abinci kisha magani,ni na san da zarar A.m ya huce zai neme ki don lamarin ku sai ku."

Ta faWa tare da miewa ta nufi kicin bayan ta rufe ofarta da key,saboda a take-taken ta za ta iya fita ta je gurinsa.

A.m ya daWe a Wakin yana zaune tamkar mutum-mutumi,gaba ki Waya ran sa ya Sace da abin da ya faru,duk sai ya Wauki laifin komai ya Wora akan Juwairiya.

Wayar sa ya fara dubawa don ba zai ce ga in da take ba.Sai dai ya gwammace dama faWuwa ta yi kan yadda ya ga Zainab ta mai da wayar.Sai ya Wauki key Win mota ya fice gidan A.k.

A.k na kwance a falonsa yana ya Wora yaron sa a kan ruwan cikinsa yana mishi wasa.

A birkice ya shigo fuskar sa babu walwala ji yake kamar ya Wora hannu aka ya yi ta ihu.

Zama ya yi ba tare da ya tanka ma Matar A.k da ke tsokanar shi ba,ganin haka sai ta ja bakinta ta tsuke.

A.k ya matso kusa da shi tare da dafa kafaWun sa." Lafiya mai ya faru."Shiru ya yi zuciyarsa kamar za ta one sai tafarfasa.

"Mu je cikin falonka ina cikin matsala A.k wallahi na rantse da zan ga Juwairiya ni ne a jalinta."Ya faWa da arfi cikin Sacin rai.

Da sauri ya ja shi suka shige falonsa har da saka key.

A.k da ya yi shiru kamar ruwa ya cinye shi cikin tsananin mamaki yake kallon sa,domin lamarin ya girgiza shi.

" Yanzu kana nufin Juwairiya ba ta gidan,ina ta tafi na san dai ba za ta je gidan Baba Sani ba,sannan Zainab ta yi yaji yanzu lamari ya Sace."

A.m ya yi uta ya ce." Ina zan san in da take wallahi yarinyar nan ta Sata min lissafi komai ya rikice,ban san wace hanya zan bi na shawo kan Zey,don ta yi fushi sosai,in da Allah ya taimake ni ba ta gane ta yi Sari ba,saboda ba ta tuhume ni akan haka ba.Ina ji ina gani ta yi min asarar babyna abin da na daWe ina nema."

Sai ga hawaye shar a fuskar sa ya na jin tsananin bain cikin asarar da tayi masa.
Wayar A.k ya fara ringing da sauri A.k ya kalle shi ya ce." Daddy ne yake kira kuma ina ga kai yake nema tun da kace Zainab ta fasa wayar ka."

Gaban A.m ya faWi da ido ya nuna masa da ya Waga wayar.

A.k ya danna wurin amsawa tare da saka sifikar wayar.
" Ina abokin ka yake dama ya fara hauka ne?ar mutane zai daka kamar ya samu jaka,maza ka taho da shi zaku gane baku da wayo tun da kai ba za ka iya ba shi shawara na gari ba."

if Daddy ya kashe wayar ba tare da ya ji mai A.k zai ce ba,don ya san suna tare da A.m.

Shiru suka yi kamar ruwa ya cinye su ko tari babu wanda ya iya yi.
A.k ya kalle sa da takaici yana gani duk shi ya janyo komai,haba ka auri mace ka ije wa matar ka,amatsayin ar aiki abin ya yi muni kuma babu tausayi a ciki.

" Lamarin mata hauri ake yi sai haur in ka ce dukan mace zaka din ga yi,to ya zaka yi duk ranar da ka haWa mata uku ko huWu?"

" Allah ya kyauta ya kuma tsare ni da tara mata uku,ko ita Juwairiya rabuwa da ita zan yi,zuciyata ba ta son wata a mace sai Zainab."Dariya A.m ya yi suka fice.

Daddy ya yi faWa kamar zai ari baki yana ta huci ji yake kamar ya rufe shi da duka.
"Saboda baka da hankali sai ka kama mace da duka goto-goto da kai.To wallahi maza ka je ka dawo da Zainab in ba haka ba za ka fuskanci fushina mai tsanani.Kuma duk ranar da ka ara dukan musu ar mutane wallahi sai na Sata maka rai."

A.m ya yi shiru yanzu yake tsananin dana sani da ya duke ta.
Ko da ya shiga shashin mahaifiyar sa ranta ya Sace matua ta yi mishi tatas!Akan ya je ya dawo da Zainab.A.k yake ta bada hauri.

Daddy ya yi mishi faWa sosai ya ara masa da hadisan monzon Allah da nasiha,sannan ya ba shi umurnin ya je ya dawo da ita.

Miewa suka yi kai tsaye gidan su Zainab suka nufa.A.m gabansa na ta faWuwa don ya san ba za su kwashe ta daidai ba.

Jefi-jefi yana kallon hanya yana jin matsanancin Sacin rai,in ya tuna da Juwairiya sai ya ja tsaki da arfi ya kauda kan sa,daga arshe ya Wauki laifin komai ya Wora akan Zainab don ita ta bada ofa har ta shigo rayuwar su.

Maigadi ya wangale ofa da alamun wani zai fita daga cikin gidan don ko hon ba su yi ba,Daddy Zainab ya fito da shiri makullin mota rie a hannun sa zai fita,ganin su ya sa ya tsaya yana musu wani irin wulaantaccen kallo.

Ya rantse da ace A.m ba Wan amininsa ba ne yau kotu za ta raba su da shi,tun da har ya iya dukan masa a guda tsoka Waya a miya.

" Mara mutunci uban mai ya kawo ka gidana ko ka zo ka ara dukanta a gabana ne? Ashe dama ba ka da mutunci na Wauki abu mafi soyuwa na ba ka?"

Masifa yake musu bai bari sun shiga daga ciki ba ya shiga zagin su har da A.k da ya yi rakiyan,sai da ya samu na shi kason saboda mahaifin Zainab ya yi fushi,bakinsa har kumfa yake saboda an bugi shalele.

A.k hauri yake badawa har da duawa ya kuma janyo hannun A.m,don ya dua da ya yi ikam ya na tsaye,zuciyar sa na tafarfasa jin rashin mutuncin da yake musu,a gaban an aikin gidan.

Da yar ya basu izinin shiga cikin falon bai suka zauna kusan awa babu wanda ya bi ta kan su.

Tsalam mahaifiyar Zainab ta shigo cikin falon tana kallon A.m a wulaance.

" Sannu isashshe da za ka kama min ata da duka,an ce maka jaka na aura maka? Na rantse Zainab ba za ta dawo gidan ka ba,tun da ba ka da mutunci.
Mai take amfana da shi da auren ka sai tsiya da hauri na rashin haihuwa da ba ka yi,shine saboda kai mara mutunci ne za ka kama min ita da duka akan wata banza ar aiki,to wallahi ba ka isa ba don ba za ta dawo gidan ka ba.
Shekarar ku nawa da aure ko Satan wata ba ta taSa yi ba,dole ka sakin mini ata ko kutu ta raba mu."Ta faWi tana harare-harare.

Duk irin rarrashin da A.k ya yi musu amma sun kafe kan ba za ta koma gidan sa ba,sai nanata maganar haurin da take yi saboda rashi haihuwar da baya yi.

Cikin fushi A.m ya mie yayin da idanun sa suka kaWa suka yi jajur.
Ya buWe baki zai yi magana da sauri A.m ya kama shi suka fice waje.Hannun sa ya ja zuwa mota ba tare da ya ce komai ba,ya shiga motar suka fara tafiya.Ganin yadda yake huci sai ya kunna ira'ar alkur'ani.

Suna tafe babu wanda ya yi magana sai zuwa can A.k ya kalli A.m ya ci gaba da tui.Jingina kan shi da kujera tare da lumshe idanun sa.

A lokacin da A.k ya shigo cikin falon A.m rie baki ya yi cikin tashin hankali yana kallon yadda falon ya hargitse babu mamora a falon

" TaS sai ka tanadar mata wasu ka ije saboda duk ranar da ta san da igiyar auren ka da Juwairiya,wallahi in babu kayan da za ta fasa sai dai wani Abdurrahman ba kai ba,lallai Zainab na da zafin kishi."Ya faWa cikin tsigar mamaki da tsokana.

A.m da ran sa a Sace ya kalle sa da takaici ya ce." Fata ma kake min ko so kake na rasa wani shashin na jikina,ni kaina yau na ara tsorata da lamarin ta,dole na Wauki mataki kafin ta san da wannan zancan in dai ba so kake na koma tafiya da afa Waya ba."

Dariya A.k ya yi sosai ya ce." Wannan ya rage naka ni dai babu ruwana tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka,kuma wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho."

A.m ya matsa kusa da shi ya gallah masa harara."Ni ba wannan ba yanzu ya zamu yi da waWannan marasa mutuncin gaskiya bazan iya zama ni kaWai a cikin gidan nan ba,ni da nake da zua zuan an mata biyu yanzu na koma babu ko Waya.Gashi yaunwa make ji wunin yau ko ruwa ban saka a bakina,saboda matsalar da damuwata ta saka ni."

" Ya rage naka sai ka san in da zaka je kaci abinci amma ba'a gidana ba,don matata ba kukun ka ba ne,ko da ka ga ada ina baka abinci saboda babu wanda zai baka ne,amma yanzu tun da a kwai Juwairiya sai ka je ka yi biko."Tsaki ya saki take fuskar sa ta canza.

" Na rantse har yanzu ina kan bakana sai na hukunta ta za ta san da wane irin namiji take zama,da na je na kirata gara na kwana banci abinci ba."Ya ce da A.k da ya Wauki makullin motar sa.

" Ok fine ya rage naka da na yi tunanin za ka yi bikon matar wucin gadi,ka huta kafin matar so ta dawo,saboda iyayenta sun yi fushi sosai kuma dole sai ka danne zuciyar ka akan duk abin da iyayenta za su yi maka,ar su kake aure kuma kai ka dakar musu a."

" Na ji don Alkah ka tafi babu abin da kake yi sai ara tafarfasa min zuciya,da na so na gaya ma mahaifiyarta magana amma kuma na gode da ka hana ni da na yi katoSara."

" Ok bari na tafi tun da ba za ka dawo da matar wucin gadi ba,sai ka ci gaba da cin abincin Lantana,sannan kar ka yi gigin zuwan min gida mai mata biyu ya zama gwauro."

Ya ce yayin da A.m ya fito don ya raka shi ba tare da ya bashi amsar shaiyancin da yake mishi ba.

Ya shiga cikin mota ya zauna tare da rie sitiyarin ya kalli A.m da yake rie da murfin motar yana jiran ya shiga,ya rufe mishi ofar motan.

" Ya kamata ka yi tunani A.m lokaci yana wucewa lamura canzawa,suke yi ka sanar da iyayen Zainab komai ka bayyana Juwairiya a matsayin matar k,tun kafin lamura su kwaSe maka.Na tabbata da kai ne ba ka haihuwa Zainab ba za ta zauna da kai ba."

Rufe mishi motar ya yi ganin ya shigar da afafunsa ciki,saboda fahimta da ya yi maganar da yake masa ba ta tasiri a zuciyar sa.

" Na riga na yi wa Zainab alawari ina sonta ba zan iya haWata da wata a mace ba.Na san

Please Login or Register in order to submit comment