Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ranar ta kammal aikin ta za ta tafi matar tace." Don Allah Juwairiya ki tsaya zamu je gidan biki ni da yarana,zuwa yamma zamu dawo sai ki tafi in kuma na yi dare zan kaiki a mota."

Duk a ranta ba ta so ba amma sai ta amsa da." To." Ta koma ta zauna yayin da ita kuma ta shirya da yaranta suka fita.

Tun da suka tafi har aka kira sallah ba ta dawo ba,ranta ya fara Saci don ba ta son ta yi dare kar Baba Sani ya dawo ya kuma ™ara mata wani sharrin.

Jin ™arar mota sai ta yi maza ta le™a ta windo ta na tunanin ita ce,sai dai cikin takaici ta koma ta zauna ganin mijinta ne ya dawo.
Ya shigo da sallama ya amsa ya na kallonta." Juwairiya har yanzu ba ki tafi ba?"Ya tambayeta ya na kallonta." Eh tunna ka dawo bari na tafi "
" No ki kira ta nima ™ara fita zan yi."
Don takaici ko amsa mishi ba ta yi ba to me ya dawo da shi koma wa ta yi ta zauna.

Ya shiga cikin Wakin sa mintina biyar ya fito sai kawai Juwairiya taga ya yi kanta gadan-gadan! Da sauri ta mi™e tare da saka salati dai-dai lokacin da ya fisgota ya haWa ta da jikin sa da ™arfi.

Kasancewar shi namiji me jiki da ™arfi ya yi nasarar kayar da ita ™asa tare da yi mata rumfa,yayin da dabbe ya kaure ko kaWan ba ta yi tsammanin ya na da wannan halin ba.Kuka ta saka ta na rokon shi,amma bai kula ta ba yaci gaba da ™o™arin ida nufin shi.

" Inna lillahi Faruk!Me zan gani dama amanata kuke ci?"Ta furta cikin ™araji! yayin da ta yo kan juwairiya ta hau ta da bugu.

Juwairiya ta yi kuka ta yi ihu ji take kamar numfashinta zai fita domin kanta ta hau ga ta da ™iba,da ™yar ya samu ya SamSare Juwairiya ta samu ta gudu.

Da ™yar ta samu ta isa gida ta na kuka a ranar ta rantse ba za ta ™ara yin aiki ba,ko da mutuwa za su yi yadda ta shigo Mama ta tsorata.

Bayan ta yi mata bayani tana kuka Mama sai da ta zubar mata da hawaye ganin halin da take ciki.A ™alla sai da ta yi sati ta na jinyar jikinta don har sai da ta kwanta ciwo.

Haka rayuwa take tafiya musu yau ba™i gobe tsummma ga ciwon Mama ya yi tsanani.Wani abin ™arin tashin hankali Ibrahim da dama can ba lafiyayye bane,saboda sikila ne shi jikin sa da ya yi sauki amma a cikin kwana biyun nan jikin ya tashi.

Ciwon shi sai yake son ya danne na Mama amma duk wanda ya ganta ya san ta na cikin tsananin ciwo.Ga kuma Baba Sani da ya sanar da Juwairiya ya yi mata miji wato Alhaji Tanimu.

A ranar da Baba Sani ya gaya mata sumewa ™au ta yi don ya tabbata Baba Sani ba ya ™aunarta,don ita da ya aura mata shi gara ta zauna ba aure ko ace mutuwa ta yi.

Waye a faWin garin be san Alhaji Tanimu ba wanda ya mai da mace tamkar rigar sawan shi.Mutum ne mara addini ga shi kamar wani hor.Kusan duk shekara yake sakin mace ya ™ara aure bayan ya tabbatar sun sami ciki,don baya son haihuwa a tunanin ta shi kan shi be san iya yawan yaran shi ba,duk da wasu ya na ba ma iyayensu mata kyauta wasu kuma ya kai su almajiranci.

Sannan an sha kama shi ´ara ™anana ya na musu ya lalata musu rayuwa irin mutumin da Baba Sani yake son ya zama mijinta kenan.Ai Juwairiya ™aramin hauka ta yi don gara yace ta shiga duniya.

Shiko Alhaji Tanimu se Winkirama Baba Sani kuWi yake yi hankalinsa kwance ganin zai mallaki wannnan zu™e™iyar,shi ya sa be damu ba ko sanda ya zo zance ta™i fitowa tallar ta fa aka kawo mishi har gida.

Rayuwa a wannan karan tafi yi wa su Juwairiya illah ga aba abinci sannan dukkanin su ba lafiya,ga Baba Sani da yake ta shirye-shiryen bikin ta don har an kawo kayan sa rana watan gobe biki.

Mama ta shiga tashin hankalin ciwonta ya ninku ga yunwa har takai sai su wuni ba su saka komai a bakin su ba.
Juwairiya ta tsara ma kanta ta gudu amma in ta ga halin da su Mama suke ciki sai ta ji kamar ta kashe kanta ta huta,ita kanta ba lafiya take da shi ba don ta na ganin har tafi su Mama jigatuwa saboda zuciyarta da take ji kamar za ta fashe.

Ganin yunwa zai kashe su sannan duk kuWin da Baba Sani yake karSa bai ta ba ba su koda na sabulu ba,ta je gurin Mariya ta ara mata naira dubu biyu ta fara jarin gyada.Da wannan suke samun abinci.

*******
Zaune yake cikin damuwa sai kuma ya mi™e don a yau jin sa yake duk shawarar da amininsa ya ba shi zai iya Wauka saboda halin da yake ciki.Makullin motar shi ya Wauka ya nufi gidan A.k.
Sai dai cikin rashin sa'a ba ya nan don haka bayan sun gaisa ya fice daga gidan ya samu wani guri mara hayaniya ya tsaya,tare da ciro waya ya kira A.k.

Ba'a fi minti goma ba sai ga A.k akan mashin ya sauka ya buWe gaban motar ya shiga ya na share zufa."Am sorry aboki motar da ka siya min na kai ta service ba'a gama ba kan dole na baro motar na hawo mashin.Are you under the weather?"Ya tambayi aminnin nasa ganin yanayin sa.

Yace ya na kallonsa bai tanka ba illa ajiyar zuciya da ya yi ya kauda kansa gefe guda,ganin yadda aminin na sa yake ya san yauma ba lafiya to ko dame yazo oho don ya san dai zancen.
Suka Wan yi shiru ba tare sun ce uffan ba na tsawon lokaci sannan A.k ya katse shirun da cewa." Lafiya na gan ka wani iri in ce ba mutuniyar bace ta haWa maka zafi."

"Akan maganar da na nemi shawarar ka yau ma na ™ara bijiro maka da ita.I really need your advise pleese help me out."A.k ya kalle shi yadda idanunsa suka kaWa suk yi ja ga mamakin sa sai ya ga hawaye ya na sauka da ga ™uncinsa.
Ya kama hannunsa ya haWa da nasa ya ri™e sosai ya na kallonsa ya ci ga ba da cewa."I know my wife she is a woman of raging jealousy.Bazan iya haWa ta da wata mace ba kuma ba yan haka na yi mata al™awari,amma ina jin zafin rashin yaro da ba ni da shi wanda hakan in ban Wauki mataki ba zai iya taSa lafiya ta,domin a yanzu ya kai matsayin da ba na iya bacci.

Tun da ya fara magana A.m ya yi shiru ya na kallon sa a ransa tunani yake to ko amininasa ya ci kai ne ko kuma rashin haihuwar ya taSa tunanin sa, kamar yadda yace shi dai ya san ta aure ake samun haihuwa ya ba, shi shawara ya™i bi saboda wani al™awari na shi na banza to amma bari ya ji me yake tafe da shi.

Ganin ya yi shiru ya dafa kafaWarsa ya na cewa."Try to be patient ka san zuriya kake bu™ata kuma dole a aure za ka same shi,ba zaka so ka sami Wanka ta zina ba wanda na san ba halinka bane,amma ni banga dalilin da zai sa ka™i ™ara aure ba bai ita ta Sata mahaifinta da kanta ba?"Ya Wan faWa da zafi kuma da tsigar tambaya.
" Haka ne." Ya ba shi amsa sannan ya ci gaba da cewa." Duk akai na ne ta samu wannan matsalar gaskiya i can't make up my mind ko zan iya cin amanarta."

˜arin takaici maganganunsa suka ™ara ba shi gani yake ba shi da tsayuwa a gidan sa,amma shi bai ga yadda matar shi zai ta da hankalin shi ba,don kawai zai ™ara aure kuma duk laifin tane.
Ya kaWa kafaWunsa yace."It is up to you ni dai na gama baka shawara."Yace amma sai kuma ya ga hankalin aminin nasa ba shi a gurinsa wata™ila ma be san me yace ba.

A hankali ya bi gurin da yake kallo shima Juwairiya ce da tiren gyaWa a kanta da ga ganinta ka san ta na cikin wani hali, kusan ma ta na tafe ta na share hawaye saboda har Alhaji Tanimu ya kawo kayan auren ta na jin gara ta ha™ura ta aure shi,wata™ila shi Allah ya tsara ya zamo mijinta ta san bawa ba ya wuce abin da Allah ya tsara mata,sai dai yanayin halin da Mama da Ibrahim suke ciki ya sa ta zagaya wa da gyaWar da yau ba ciniki ta haWa da kuWin da Mariya ta ba ta ta kai su asibiti.

A.m da ya zuba mata ido ya na kallonta bai taSa ganin mace me sanyi da wani irin shauki a tare da ita ba sau,haka kawai ya ji ta kwanta mishi a rai ba wai son ya na son ta ba irin zai iya magana da ita har ya ba ta lokaci su yi wasa da dariya,kuma ya nemi shawarar ta kuma zai iya yin komai don ta yi farin ciki,zai iya cewa yau ne rana ta farko da ya ga wata mace bayan Zainab har ya na jin zai iya mata magana.

Wato in ya fahimci zuciyar shi ™awa yake son ya mai da ita ko ™anwa." To amma duk tsanar talaka da na yi sai ace na yi ™awa da ´ar talaka kuma ™as™antacciya ´ar talla kai an ya da wuya.".
Yace a zuciyar a cikin zuciyarsa ya na me ™o™arin kauda idanun sa daga gareta don jin hakan bai dace ba ace duk matsayin shi.Sai-dai idanunsa sun kasa Wauke kan su daga kallonta ya na ™ara za™ulo kyawunta.

Ta na tafe cike da damuwa har tazo ta gaban su za ta wuce." Me gyaWa." Kalmar da bakinsa ya furta ba tare da ya ba shi umurni ko tunanin hakan ba.

Juwairiya ta ji wani irin sansanyar murya mai kama da sarewa ta kira ta ta na son ta juya amma sai ta da™ile kanta da juyawar,don ™ila in ta ga mamallakin wannan muryar ba ta san halin da za ta shiga ba sai kawai ta ci gaba da tafiya yayin da aranta take addu'ar Allah ya sa karya ™ara kiranta, don ta san in ya ™ara kiran ta ba za ta iya tursasa zuciyar ta da ™in juyawa ba.
A.m ransa ya matu™ar Saci ™azama da ita ta na talaka zai kira ta ta™i waigowa ya so yaje ya yi watsi da kayan tallar,ya ga uban wa take ta™ama da shi ta™i amsa kiransa amma da ya yi tunanin ko kurma ce sai ™ara kiran ta a karo na biyu.
Cak! ta tsaya amma ba ta wai go ba ta na addu'a a cikin ranta yayin da idanuwanta suka za™u da suga wannan mamallakin muryar.A hankali ta tako ta iso gun motar su ta tsaya ta kasa magana kuma ta kasa Waga ido ta kalle shi.
Kusan minti goma ta na tsaye ba tare da ya kalleta ba me ya gani oho ganin ita ma ba ta da ninyar ta yi mishi magana kuma ba ta tafi ba A.k dai ya na zaune ya na kallon ikon Allah.

A.m ya buWe motar da nufin ya yi mata wula™anci dai-dai lokacin da idanuwan su suka tsar™e da na juna.
Kyansa yanayin jikinsa idanuwansa da yadda yake kallonta suka ruWa ta ta yi kamar za ta faWi, amma sai ta dafa jikin motar sa ta na kallon shi cikin wani irin shauki,lokaci guda ta ji abu me kama da guduma ya sauka akanta! Yayin da wani irin shokin na soyaryarsa suka dinga Wana mata son shi a cikin ranta,har ta ji za ta iya mutuwa in ba ta same shi ba.

Idanun su da suka tsar™e da juna sai ya tsinci kansa da kasa mata rashin mutuncin da ya yi ninya a yatsine yace."Nawa-nawa gyaWar."
Ta zuba mishi idanunta sai kuma ta janye ta lumshe su tare da kauda ganin ta gare shi ahankali da sanyaryar murya tace.Hamsin gwagwani Waya."
Ya Wan ™ura mata ido haka kawai kyawunta da muryarta yake ruWan shi a kanta."Duka buhun nake so nawa."Yace tare da barin kallonta lokacin da ta Wora idanunta akan sa.
Zare ido ta yi " kwai yawa fa kusan na dubu uku da Wari biyar ne.Tace mishi hakan sai ya burge shi ya tsinci kansa da yin murmushi.
"Ok bari in ci Allah ya sa da daWi."Da sauri ta saka hannunta da baya rabo da lalli ta mi™a mishi ta na faWin." A kwai daWi kaci kaji."
Yabi hannunta da kallo ya karSi gyaWar ya Sare tare da taunawa,lumshe idanunsa ya yi yace da ita."Gaskiya a kwai daWi zuba min a leda sauran kiyi sadaka da shi."
Da sauri ta zuba mishi sannan ta kalli gefen A k da ya yi mutuwar zaune saboda tun tarihin rayuwarsa da A.m yau ce rana ta farko da ya siyi abu a gurin masu talla,sai ya yi lakato ya na kallon A.m da ke cin gyaWa har ya na faWin ta ™ara mishi ya yi daWi.
" Yayana kai fa ba ya cine."Ta kalle shi sai kuma ta mai da maganar da tsigar tambaya ta na kallon A.m,kaWa kafaWunsa ya yi ya na kallon shi ya ma manta da shi yace."Ba ya ci."
Juwairiya tace " Ka tambaye shi ne?"Sai kuma ta kalli A.k tace."Wai haka Yayana?"
"Yes Am ok."Yace da ita ya na kallonta.
Zuba gyaWar ta yi ta mi™a mishi ta na faWin."Kaci a kwai daWi."Ya ™arSa tare da faWin."Thanks sis."
A.m ya zaro kuWi da yawa ya mi™a mata. Gashi sis ki cire kuWin ki sauran ki ™ara jari."Zare kuWin ta ta yi tace."Siyan da ka yi na gode."
Hakan sa ya yi matu™ar birge shi ya na ta kallonta har ta yi nisa ya le™o ta cikin murfin motar yace." Manene sunan ki."
Ya Wan Waga muryarsa yadda za ta ji don ta yi nisa,waigowa ta yi ta kalle shi tare da sakar masa murmushi ta tabbata wannan kyakykywa gayen ya yi mata sata mafi girman abu a rayuwarta,wanda ta san ba zai dawo mata da shi ba kawai za ta ci gaba da renon giSin rashin abin da ya Wauke mata har iya tsawon rayuwarta!
" Sunana Juwairiya Ahmad."Tace tare da ™o™arin Sullewa a ranta ba ta son ta ™ara haWuwa da shi don ta san babban goro sai magogin ™arfe.
A hankali ya kwantar da kan shi akan jikin kujerar da ya saukar da kansa ya na murmushi ya furta.Juwairaaah! Da wata irin murya ya ja sunan ya yi mishi wasali sosai." Ta na da kyau haka kawai sai na ji ta burge ni."

Ba tare da wani shakku ba A m yace."Bayan kyau a kwai hankali da natsuwa .Rayuwarta a kwai tarin tausayi ka aureta kawai ta haifa maka yara.

Da sauri A.m ya buWe idonsa ya Wora akansa wani irin Sacin rai da takaici ta ya ya zai haWa shi da ita ´ar talaka me talla ita yake nufin ta haifa mi shi yara!Ina imposible wasa yake yi.

Ya buWe baki zai yi magana sai kuma ya figi motar tamkar zai zubar da su,A.k dai bai ce komai ba koma kashe su zai yi, ya yi amma iyakan shawarar da zai iya ba shi kenan kuma in dai bai Wauka ba to ba zai ™ara kula shi akan damuwar sa.

˜ofar gidansa ya ije shi ba tare da yace komai ba bayan ya fito daga motar ya le™a ta tagar motar yace.Allah ya bamu alkhairi ka yi tunani shawarar da aka yanke ina sauraranka."
Ba tare da ya tanka mishi ba ya ja motar a guje dariya ya saki tare da girgiza kan shi ya shige gidan sa.
A.m da ya koma gida sai yaji wani tashin hankali game da maganar da ya yi mishi,amma ya kasa amincewa wanka ya yi ya kwanta don baya so ya yi tunani akan maganar,sai dai bayan baccin ya kwashe shi sai ya yi mafarkin ga Juwairiya ta na kuka ta mi™o mishi yara guda biyu shi kuma ya na cikin ™aton rami ya fito da ninyar ya ™arSa sai ta Sace ta na wani irin ihu,ihun da ya fargar da shi ya mi™e a zabur! Ya na salati don har yanzu bai daina jin sautin kukan a cikin kunninsa ba.

" Ita za ta haifa min yara amafarkin da na gani kenan amma a kwai matsala.Tabbas matsala babba don ko ni auren ta zan yi cikin sirri ba tare da sanin kowa ba wato auren wucin gadi,na ´anta mata rayuwa na ba ta jin daWi amma mu yi aure na tsawon shekara Waya tazo a matsayin me aikin gidana bayan ta samu ciki, na Wauke ta na kai ta wani gurin in ta haihu na biyata na karbi yarona na kawoma matata masoyiya Zainab."

Tofa masu karatu kun ji A.m abin da yake so.
*Hakan zai yiwu?
*Ta ya ya A.k zai karSi lamarin shin zai bashi goyan baya kuwa?
*Wani irin aure yake son yi?
*Shin ya zai yi da Baba Sani da ba shi da buri sai dai rayuwar Juwairiya ta wula™anta,zai amince mutum me daraja da matsayi ya aureta?
*In ma ya amince taya za'ai Juwairiya ta yi rayuwa a gidansa a Soye a matsayin matarsa amma kuma azahiri ´ar aiki?
*Ta ya ya za ayi auren sirri ba tare da sanin Mama ba?
Ku dai biyo ni a shafi na gaba"SAKACINA KO HALIN MAZA"
NAGA RUWAN COMMENT IN ANA SO NA CI GABA.=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ=Ø Þ=Ø ÞTAKU JAMILA LAWAL ZANGO=Ø”Ü=Ø”Ü=Ø”Ü=Ø”Üd'd'




Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G0J8rS0cxTtCCC38iwA3B9
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA GOMA SHA BIYU*



Juwairiya ta na Sacewa ganin sa ta tsaya ta tsuguna tare da sakin wani gigitaccen kuka sosai wanda ba ta san dalilin yin hakan ba,sai bayan tasha kuka sosai zuciyarta ta fara jera mata tarin tambayoyi."

Me ya sa nake kuka ga mutumim da na san ba zan taSa samun shi a cikin rayuwata,na sa ni cewar dariya ba so ba ne.! Maganar da ya yi min ba ya nufin zai iya sona a cikin ransa,sannan na tabbata ya yi aure har ma da iyali saboda kamalar shi ta nuna na cikakken mutum me iyali."

Ta tallabe fuskarta da hannunta wani sashi na gefen zuciyarta,ya na ™ara jaddada mata da cewar ko da ya nuna ya na sonta Baba Sani ba zai taSa ba shi auren ta ba,mutane wanda ba su kai shi matsayi ba sun nemi auren ta amma ya hana bare shi da ga ganinsa kasan ya ji™u da nera,da duk wani ababen more rayuwa.

Sai ta share hawayenta tare da Waukar tiren jiri na jiri ya na iban ta ta na ji kamar ta haWiye zuciya ta mutu in ta tuna wannan tsohon ze mallaki jikinta.

Gizo-gizon hoton sa da murmushin da ya yi mata lokacin da ya tabbayi sunan ta idanuwanta suke hasko mata,ta rintse idanunta da ™arfi ta na son su da™ile mata ganin ta ga mutumim da take jin kamar ya saka ta a aljihun sa su yi ta yawo.

Bayan ta dawo gida ta na zaune jingine da bangon Wakin su idanunta a sama ta na aikin tunanin da ta Waura Wamara da shi tun lokacin da idanunta suka yi tozali da shi.

Mama dake tsaye ta na karantar yanayin ta tun da ta kawo mata kuWi tace wani mutum ya siye,ta zauna a gurin ta na kallon sama sai hakan ya tabbatar mata da a kwai lauje cikin naWi.

" Juwairiya lafiyar ki kuwa."Mama ta kalleta lokacin da ta dafa kafaWarta,amma ba ta ji ta ba har sai da ta maimaita sau biyar ba ta ji ba sai ta juyo da fuskarta.

Ga mamakin ta sai ta ga ta juyo tare da saka hannunta ta rungumeta ta fashe da kuka,hankalin Mama ya ™ara tashi dama tun safe take jin wani irin zafi-zafi a ™irjin tare da sauke wani irin ajiyar zuciya mai kama da zai tafi da rayuwarta.
Ya™e me kama da murmushi ta yi tace." Akan maganar auren ki ko Juwairiya ya za mu yi da ™addarar ubangiji,komai kika ga ya faru Allah ne ya ™addara."

Ta sauke irin wannan ajiyar zuciyar da ke barazanar Wauke numfashin ta sai kuma hawaye suka fara turereniya a kan ™uncinta.
Ta buWe baki da nufin ta yi magana amma ta kasa sai ta rufe bakin tare da sakin kuka wanda ya fi na Juwairiya sauti.

Hankalin Juawairiya ya tashi matu™a!Tun da lamarin ke faruwa Mama ita take kwantar mata da hankali amma yau ha™urin ta ya gaza.

" Don Allah ki de na kuka wallahi na ha™ura ba zan ™ara nuna damuwata ba,in dai akan auren nan ne kin san yanayin ciwon ki.

Ta faWa ta na share hawayen ta don ta na tsoron kar ciwon Mama ya tashi,ga shi aure za ta yi babu wanda zai kula da ita sai Ibrahim wanda ba cikakkiyar lafiya gare shi ba,don har Wingishi yake yi kafar sa Waya ba lafiya.

Mama ta mi™e ba tare da tace komai ba ta fice daga Wakin ta na jin matu™ar tausayin ta kasancewar ba ta sami bango abin jingina ba.Tanimu ba mutumim aure ba ne ita kuma mace ta na zama zinariya ce in har ta samu miji na gari,ta fauwala ma Allah lamuran sa saboda Allah na iya can za lamuran sa iya addu'ar da take yi wa Juwairiya rayuwar ta ba za ta taSe ba.

Buta ta Wauka ta shiga bayi ta tsarkake kanta ta fara kai kukan ta ga Allah Sarki gwani gagara misali!

Ganin haka Juwairiya ta mi™e tare da sakin kuka ta toshe bakin ta bayi ta shige ta saki bakinta ta na kuka mai tsuma zuciyar me sauraro." Me ya sa ka shigo rayuwata a lokacin da nake jin duniya ba ta da muradina a cikin ta gyambo biyu kake so na yi ta jinya a cikin rayuwata! Na rashin ka da auren mutumim da na tsana a rayuwata!"Kuka sosai ta yi sannan ta fito ta yi alwala tabi sahun Mama.

Wunin ranar ta yi shi ne a suku-suku tamkar wacce ba ta da lakka a jikinta,ta kasa cire shi a ranta.Da daddare ta na kwance sai mutsu-mutsu take ta na jin Mama na ajiyar zuciya ™ut!˜ut! Wanda hankalinta ya tashi kwarai ba ta rintsa ba sai kusan asuba ta ji Sarawo bacci ya kwashe ta.

Da asuba bayan ta yi sallah ta na karatunýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿ alkur'ani ta yi mamakin da Mama ba ta tashi ta yi sallah ba,sai ta mi™e dai-dai lokacin da Ibrahim ya shigo ya dawo daga masallacin dake kusa da su.

" Mama ki tashi ki yi sallah." Amma shiru ba ta amsa mata ba da sauri ta ™ara jijjigata sai dai ta ga Mama idanunta sun ™an™ance jikinta ya saki da ™yar take janyo numfashin dake barazanar kuSucewa gangar jikin ta.

" A'a Mama don Allah karki mutu ki bar mu kin ji Mama!"Kuka take sosai ta na girgiza Mama da ta ™asa buWe idanun ta saboda nauyin da sukai mata,a jikin ta ta na jin wani irin zafi me kama da rushi ya na zagaye ilahirin jikinta don har huci yake ya na fitar da tiriri me zafin gaske!

Jin ihun Juwairiya ya sa matar Baba Sani ta shigo wanda hankalinta ya tashi matu™a ta na tausayin su sosai,sai dai ta san halin tijararren mijinta zai iya shuka mata rashin mutunci koma ya sake ta bare yanzu da yake mata rashin mutunci zai ™ara aure.

KuWi ta mi™a ma Juwairiya ta saka yaron ta ya nemo me keke napep aka saka Mama a ciki zuwa asibiti.



*********
Bayan A.m ya fita gidan iyayen shi ya nufa don ya Wan kwana biyu be le™a su ba,ya na shiga ya ga ana ta murnar matar ™aninsa ta haifi ´an biyu gidan ya cika sai murna ake,saboda daga asibiti nan aka wuto da ita.

Jikinsa ya yi sanyi ya irga yaransa yanzu huWu kenan sai

Please Login or Register in order to submit comment