Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ji ko me Mama za ta ce amma sai ta ga ta tsaya ta harWe hannunta a irjinta ta na sauraren wannan tatsuniyar ita tunanin ta to meye haWin ta da wannan dogon labarin wanda take ganin ina ruwan ta da labarin sa.

Juwairiya ta rasa in da za ta kama ta ci gaba da zancen a wannan lokacin ji take kamar ta Wora hannu ta yi ta kuka ganin yadda Mama ta kafe ta da ido.

" To saboda wannan ne ya na son a koya mata abubuwa da girki yake son ya s..."Juwairiya da ta ci gaba da magana sai kuma ta tsaya tare da sakin kuka wanda hakan ya ta da hankalin Mama, amma sai ta yi shiru ta na kallonta yadda take kuka mai sauti.

" Shi ne yake son mace wacce za ta zauna a gidan shi na shekara Waya ta koya ma matarsa girki da yadda ake kula da gida,na tsawon shekara Waya kuma duk wacce ta amince za ta yi zai tallafa ma rayuwar su,ban san tsinannen da ya gaya masa halin da kuke ciki ba har ya zaSi Juwairiya a matsayin wacce za ta yi,don wallahi da na sani ba zan bari ba ai gara na saka ata."Muryar Baba Sani suka ji ya na magana a bakin ofa.

Mama ta ji wani irin juwa ya kamata murna za ta yi ko farin ciki amma kuma Juwairiya ta din ga yawon aikatau kenan?Juwairiya a yanzu ya kama ta ace ta na Wakinta,sai dai kuma mutumim ya yi hidima ga rayuwar su wanda wani Wan'uwan ka ba zai iya haka ba.


Ta buWe baki da nufin ta nuna rashin amincewarta amma sai ta kasa saboda ya yi musu halacci haka kawai sai ta ji ba za ta iya musawa ba,amma ranta ta saka dole in Juwairiya ta gama aikin ta za ta yi aure da irin mijin da take so ko da hakan zai saka ta karya alawarin da ta yi ma marigayin mijinta ne don za su raba abin faWi ila kutu za ta raba su,saboda haurin abin da yake mata wanda sakamakon hakan ya sa zuciyarta ta buga.

Juwairiya ta shiga tsananin mamaki gani Mama ba ta ara ce mata komai ba ta takure gefe zuciyarta cike da tashin hankali,wani irin zazzaSi ya rufe ta sai makyarkyata take hawaye ya na zuba a uncin ta.

Mama ta yi jim da kofi a hannunta bayan ta ba ta magani tasha." Ni fa hankalina ya tashi Juwairiya ke ma kin yi gangancin karSar wannan kwangilar duk da hakan ya tseratar da ke da ga auren wannan tsohon,amma kin manta irin wulaancin da dukan da kika sha a dalilin aikatau."

Juwairiya ba ta ce komai ba sai hawaye da suke shatata fuskarta.
Mama tace ta rasa wani irin tunani za ta yi akan maganar aikin Juwairiyar da za ta yi,kuma da ta nemi sanin waye hatta ita Juwairiyar ba ta gaya mata ba sai wani lulluSin biri suke yi wa kare an ya? Akwa lauje cikin naWi!Ta faWi a zuciyarta cike da shakku.
Ta zauna a gefen gadon da take kwance tare da janyo mata bargo." Allah ya baki lafiya."Ta ce tare da zabga tagumi.

Wa su irin zafafan hawaye suka wanke mata fuska sai ta canza kwanciyarta saboda ta juya ma Mama baya." Ki yafe min Mama na san ban yi miki adalci ba,amma na yi hakan ne saboda na ceci rayuwar ku duk da hakan ni zai kai ni kushewata saboda ara kusanci da na yi da shi,shi zai jagoranci ruhina zuwa mutuwa.Allah na roe ka ka cire min son sa a cikin zuciyata."

*****


A.m zaune a tanamemen falon sa da remote a hannun sa gefe kuma Zainab ce take aiki da computa da ta Wora a cinyarta,saboda gwanancewa da aiki da ita da ta yi ba tare da ta kalle abin da take daddannawa ba take aikin ta,yayin da hankalinta ya na kan A.m da yake ta jan tsaki ya na juyi a kujerar.

Talatu mai aiki wacce take sabuwar ar aikin da Mominta ta kawo mata saboda halinta sam ba ta daWewa da me aiki.Ita ce ta yi sallama ta shigo idanunta akan A.m saura iris ta yi Sari amma sai ta ije ta ci gaba da kallon shi.

A.m wanda da ma hanya yake jira miewa ya yi ya kwasa mata mari ya ce." Wai ke wace irin mayyar yarinya ce ba na hanaki kallona ba!Banza atuwa da ke maza fice min daga falo! Kuma yau zaki bar gidan nan."

Da sauri ta ruga ta na shafa gurin da ya mare ta don ta ji zafi sosai jikinta har rawa yake saboda ita duk ta gan shi,sai ta ji ta na son ya kula ta duk da ta san shi ba san ta bane amma ya na da kyan da duk mace za ta yi mafarkin samun shi.
Zainab kuwa tsaki ta yi a ranta ta ce." Haka kawai duk ka tsani an aiki kullum cikin canza masu aiki muke wannan karan sai dai ka yi hauri amma ba zan canza ba."
Juya wa ya yi ya kalli Zey da ta daina aikin da take yi ta na kallon shi ya ce." Allah na tsani yarinyar nan ke duk masu aikin ki dangin mayu kike Wauko wa,gaskiya ki sallame ta ni sam ma abincin ta ba ya min daWi."

"To ni ya kake son na yi ko ni kake son na dun ga yi maka girkin?"Ta Wan saki dariya ta ci gaba da magana ta na ce wa." In haka kake tunani gara ma ka cire har na yi aure ban taSa shiga kicin da nufin na yi girki kai ko ruwan zafi ban iya dafawa ba,ka ga ya zama dole ka ci na ta in ba so kake ka Wauko kuku namiji ba wanda da ma kafiyarka na tsiya da bain kishi ya hana ka,amma ni ban ga dalilin da ya sa ka za ka i Waukar kuku namiji ba a gidammu su suke girki ni kai na na gaji da cin abincin masu aiki."


Wani kallo ya watsa mata ya ce." Zainab ki kiyaye ni da maganar kuku a haka yadda kike zama kusan naked ne zan Wauko kuku,matan ma da suke kallon ki ni na san bain cikin halin da nake shiga sai dai na lura shashasha ce ke kin Wauki rayuwar yahudu da nasara ba ki san darajar kan ki ba."

"To aiko ka na ruwa wallahi tunna duk yawon duniya da ka yi baka waye ba ni ban ga dalilin da zai saka kasa na din ga Soye kai na ba kamar wata onannniya."
Ta ba shi amsa cike da gatsali ta na girgiza afa.

" aryar iskanci kike tunna kin nuna ba za ki canza ta ba sai dai ki zaSa ko aikin ko ki zauna ki rina dafa min abincin da kanki,tun da na tashi na ga iyayena suna girki a gidammu amma ke saboda sakarci ki ce ba ki iya ba.Ki na ganin annina duk sun iya girki ke na rasa wani irin tarbiya kika samu. "
Ta katse ta hanyar Waga masa hannu ta ce."Ka dakata kar abin ya zama cin fuska kuma da kake wannan maganar ai ka san wacce kake aure da matsayin ubana."

"Dallah rufe min baki ke ma kin san sai dai ki yi min gori na mahaifin ki ya rie muami,amma ba wai ko kun fi mu kuWi ba iya tarbiya ne kawai da muka hora su da shi, saboda arzikin da muke da shi bai saka ya sa mun yi watsi da al'adarmu ta yi ma miji girki."

Tsaki ta saki ta ci gaba da aikinta ta na faWin." Ai sai ka yi ba ka da aiki ne ni ina da abin yi kamar yadda ka gani."Ta Wan ara sakin aramin tsai a hankali ta ce." Jarababbe kawai."

Ya kalle ta ya na bain cikin halin ta don shi bai yi tunanin halinta haka yake ba."Mu zuba da ni dake tunna baki da mutunci kuma da ga yau in kika ara zuwa wani guri bayan akin ki Allah y...."

Da sauri ta tashi ta waurgar da ar mini system Win dake hannunta tare da faWawa jikin shi ta rufe bakin shi jin zai kafa mata dokar fita,in ta bari hakan ya faru ita kuwa ya za ta yi da zuwa pati da yawaon da suke da awayen ta.

" Haba mai sanyina don Allah ka yi hauri karka faWi haka kai ma ka san wallahi ban saba zaman gida ba,in ka hanani fita ya zan yi kuma ka san kai ma zaka saka Allah ya yi fushi da ni ne,amma na riga na saba da yawo ba zan iya zama guri Waya ba ko da ka rantse."

Ya kalleta da mamakin abin da ta ce ba yan Allah ya jarabce shi da sonta ya riga ya rufe mishi ido da sai ya ce bai yi dacen macen warai ba,amma so makoho har zuciyarsa ta sauko ya kalleta da shauki ya haWa hannunta duka ya na murxawa da hannunsa don ya na ganin damar sa ne yanzu ya ce.

" Na lura don kin ga ina son ki shi ya sa kike wahalar da zuciyata Zey amma ba komai ina fatan Allah ya saka miki irin son, da nake miki a zuciyarki nawa zaki gane halin da na ke ciki."Ya faWa ga mamakin ta sai ta ga yana hawaye.
Hankalinta ya tashi ta ara maalalewa a jikinsa ta na share masa hawaye saboda jikinta ya mutu murus da son sa.


" Ni ma fa ina sonka hubby kai Win ne ka cika faWa ba ka min uzuri duk da oorina da nake kuma ka san yanayin aikina.

Janye hannunta ya yi akan fuskarsa aran sa ya na faWin." Na sani amma kuma hakan bai hana ki fita ba."

A fili kuwa sai ya saki Wan murmushi kamar ba shi ya gama hawayen bain cikin Juwairiya za ta shigo duniyar auren su ba wanda ya Wora laifin duk akan Zainab amma sai ya ce.
" To ki canza me aiki ni bana son wancan yarinyar k..."

Ta atse shi ta na faWin ."Na ji zan canza amma kuma Momi ta ce in dai muka kori wannan ba za ta ara ne mo mana mai aiki ba tunna ba ni da hauri."

" Kar ki damu dama tuntuni nake son na tambaye ki na yi ma Atine mai aikin gidammu ta kawo mana macce matashiya wacce ta iya girki sosai,in kin bani dama sai na gaya mata ta nemo mana kuma ba za'a daWe ba, za ki ga ta kawo mana tunnna ita ma ta na irin kawo su kusan family mu ita take kawo musu masu aiki."

Ya ce tare da rungumeta ya na goga fuskar shi a na ta."Ok ba komai sai ta kawo mana amma ba za mu kore ta ba sai an kawo mana wata."

A.m hamkalinsa ya kwanta ganin bai sha wahalar samun haWin kanta ba miewa ya yi ya shige Wakin sa,ya gallah wanka ya fice kai tsaye gidan su ya wuce ya sami Atine mai aiki ya ce." Ina son in kika tashi zamu fita da ke zuwa wata unguwa amma ya zama sirri a tsakanimmu in kika yi min hakan zaki samu alkhairi."

"Ka faWi ko mene ne in sha Allahu zan yi maka."

Ta ce cikin mamakin in da za su kuWi ya zaro masu yawa ya ba ta.Atine jikinta na rawa ta karSa ta na kallon shi." Wata yarinya nake son na nuna miki ki kaiwa Zainab a matsayin ar aiki.Shikenan buata ta kuma ba na son kowa ya sani kawai ki bar shi a matsayin ke kika kawota."

Duk da mamakin maganar da ta yi amma tunanin ta bai kai ko ina ba,ta amince masa akan sai ya zo daga arshe watsar da tunanin ta yi don ta san ya wuce arfin ya kula ar aiki ,kasancewar yadda ta ga ya na hantarar su bare ma ta yi tunanin wani abin.


********

A ranar da Juwairiya za ta tafi hankalinta ya tashi matua wanda da Mama ta so tai kan ta din ga kwana duk da a kwai nisa sosai ta so Juwairiyar ta din ga zuwa ta na kwana har shekara Wayan ta yi,amma sai Baba Sani ya kafe dole sai dai ta din ga kwana tunna kuWi ya biya.

TO MASU KARATU GA DAI AMARYA JUWAIRIYA ZA TA TAFI GIDAN ANGONTA KO YA ZAMAN SU ZAI KAYA ?SAI KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN SAKACI KO HALIN MAZA.

TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO


UBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT IN KU YA NA SAKA NI NISHAI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi noma sha shidda.Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.




*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 17*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM



Juwairiya ta yi tsuru da jakarta ta na kallon Mama da ke tsaye a gefen ta rie da hijabin ta a hannu ta na oarin saka wa a kanta sai ta ji hawaye sun ara wanke mata fuska,ta share da sauri domin Mama tun Wazu take mata orafin kuka yanzu ma da taga ta na hawaye sai ta yi tsaki ta ce." Gaskiya kukan nan na ki ya fara sie ni Juwairiya na ga ke da Baba Sani kuka shirya hakan,amma kin bi kin dame ni da kuka in da kin san ba za ki iya ba uban wa ya ce ki amince."


Sai ta rungume Mama ta ara fashewa da kuka ta na jin wani irin bain ciki da fargaba ga gabanta da yake faWuwa a kai akai don ji take kamar ta ce a ta fasa.
"Mama akan ki sami lafiya na amince amma ki yafe min in na Sata miki na ga kamar ran ki ba ya son na tafi."Ta ce da ita cikin hawaye fuskarta ta tura shi a jikinta.

" Ki na ganin in da bai yi wa rayuwarmu halacci ba wallahi Baba Sani bai isa ya saka ki ara wani aikatau ba,don kullum na yi sallah sai na roi Allah ya raba ki da shi saboda irin cin mutuncin da kika fuskan ta."
Share hawayenta ta yi ba ta ce komai ba ta shafa kan Ibrahim tare da rie hannun sa suka fito tare.

" Mama ji nake kamar kar na tafi sai kun tare a sabon gida."Ta faWa tare da fuska.
Mama ta kalle ta ta ce " Gara ki tafi Juwairiya saboda yau aka yi zaki tafi kuma kin ga mutumim nan ya yi ma rayuwarmu hallaci wanda dalilin haka ina matuar girmama shi."

" Humh." Ta ce a cikin zuciyarta sannan ta Wora da ce aranta jin abin da Mama ta ce." Da kin san abin da ya ulla da ba ki girmama shi ba,shi Win macuci ne sosai ya fiye son kan sa da rayuwar matar sa da kin san dalilin da ya sa ya yi mana wannan abubuwan da kin tsane shi har iya arshen rayuwar ki."

A lokacin da suka yi nisa mama ta kama hannunta ta rie sai hawaye ta ce." Juwairiya ki rie mutuncin kan ki a duk in da kike kuma, duk abin da ki kai kin san Allah ya na kallon ki mutunci na a mace shi ne zai zama ado a rayuwarki,ba wai ina zargin ki ba ne a' a ina miki nasiha a matsayina na uwa wacce arta za ta yi nesa da ita,sannan ya zama dole na saki a hanyar daidai don kar ki ga mutum zai aikata abu a Soye,ya na tunanin ya kauce idon mutane bayan ya manta mahaliccin sa ya na ganin duk abin da ke"

Jikin Juwairiya ya ara sanyi kamar anara haka kawai sai ta ji ta fara tsarguwa yadda Mama take ta mata wasu irin maganganu, wanda take shan jinin jikinta don in ta yi mata irin waWannan maganganun ko kallonta ba ta iya wa.
Yanzu haka ta kasance ta yi asa da idanunta ta ce."Mama an ya ba zan."
Katse mata hanzari ta yi tare da taran Wan mashin ta karSi jakarta da ta rie da ta yi tsumu ta Wora a kan mashin Win sannan ta kalle ta ta ce." Ma za ki tafi Allah ya tsare da kin sami lokaci ki leo."

Juwairiya ta haye mashin jikinta babu karsashi hawayen fuskarta sun ci gaba da kwaranya yayin da Wan mashin Win ya fara tafiya a kan titi.
Wani arin abin da ya ara zubar hawayenta cikin unar rai da ta tuna yau gidan mijinta za ta akan mashin da ullin kaya a jaka, ba tare da an kawo mota kamar yadda ko wace mace mai gata wacce mijinta yake son ta ake mata,duk lokacin da ta tuna wannan sai ta ara sakin kuka har Wan mashin Win ya juyo ya kalle ta ya na faWin."
Lafiya Hajiya?"

Amma ba ta kula shi ba kuka sosai take har suka isa gidan Atine,a lokacin da ta isa ba ta nan sai da ta jira ta sannan ta dawo sallah ta yi suka kama hanya.

Wani irin faWuwar gaba take yi har sai da ta dafe irjinta.Kasancewar a kwai tazara sosai da gidan Atine sai da suka hau nafe.

A lokacin da suka iso ofar gidan da Juwairiya ta saka a ranta na A.m ne hankalinta ya yi matuar tashi matua gaya.Kawai sai ta ji asa ba za ta iya Waukar ta ba ta sani A.m suna da kuWi amma ko kaWan ba ta taSa tunanin haka gidan sa yake ba.

" Dole ka ce baka sona kuma ba zaka taSa sona ba saboda ba mu dace ba ni kai na sheda ne."

Ta furta cikin karayar zuci don ta san ya fi arfinta na har abada.Gaskiya fasalta gidan sa abu ne da zai Wau lokaci saboda gida ne mai matuar girma, da tsari ga shukoki masu kyau waWanda suka ara awata gidan,don haka mai karatu na bar maka aikin tsara fasalta iya tsaruwan gidan,A.m a hannun ka don in na ce zan yi zan Wauki lokaci ni dai na yi wa gidan suna da aljarnar duniya.

Lokacin da suka shiga cikin falon Juwairiya ku san neman numfashinta ta yi ta rasa, don barazanar shiWewa yake yi saboda tsaruwar falon da ke Wauke da ku san set huWu na kujeru mabambanta.

Duk lokacin da ta ara taku a cikin falon zuciyarta karaya take da son A.m da ya shige zuciyarta saboda ta haiance ma kanta da yaudarar kanta take yi A.m babu abin da zai yi da ita.

A asar kafet Win dake zagaye a tayas Win da ya sha guga ya na ta yalli da Waukar ido ta zauna tare da rintse idanunta,hakan ta ji ba ta son idanuwarta su yi tozali da matar A.m don ta san zuciyarta za ta buga.

Atine ta zaro wayar ta ta yi kiranta sai dai cikin takaici ta ije wayar ta kalli Juwairiya ta ce." Ba ta dawo aiki ba amma ta ce mi jira ta za ta duba patient ta dawo."

Sai Juwairiya ta sauke idanunta daga kallon Atine saboda kiran sunan ta da ta yi,ta ci gaba da kallon asa yayin da zuciyarta yake bugawa tamkar za ta fito.

Kusan waya biyu suka shafe suna zaune a falon sai kowa shiru jefi-jefi Atine take sakin tsaki,amma Juwairiya iya tsawon lokacin ko tari ba ta yi ba sai sautin bugun zuciyarta da yake ta ara tsanantuwa.

was!was!!was!!! Suka ji sautin takalmi wanda Juwairiya ta sadaar da matar gidan ce ta dawo,bayan iya tsawon lokacin da ta Wauka ta shanya su zaman jiran ta kamar wasu dussa.

Bugun takalmin Zainab ya na tafiya tare da bugun zuciyar Juwairiya da take jin tamkar za ta fito,ta rintse idanunta ta na burin a ce ba Zainab Win ba ne take oarin shigowa,domin tsoro ya bayyana a fuskarta sai take ganin kamar za ta gane dalilin shigowar ta gidan.

Koda ta shigo waya take yi zama ta yi ba tare da ta ce musu komai ba ta ci gaba da wayar ta.

Juwairiya ta kasa Wago idanunta ta ga matar mijinta na wucin gadi wanda take cikin zuciyar sa yake fifita ta fiye da komai har ya zaSi ya cutar da rayuwarta duk akan ya farnta mata.

Amma idanuwanta sun kasa haWa ido da ita hasalima ko Wagowa ba ta yi ba, duk da ta fahimci ta gama wayar da take yi bayan ta Wauki rabin awa.

" Am Atine na Sata miki lokaci ko?"

Tambayar da ta yi mata kenan ta na kallon matar da ta kusa jika da ita a yatsine.
" Ba komai Hajiya dama me aikin ne da muka yi magana da megidan ki na kawo miki."Ta ce mata ta na kallonta.
" Ok."

Abin da tace kenan ta janyo wayarta ta kunna data yayin da tsawanni suke ta shigowa ta na duba wayar har na tsawon lokaci,daga bisani ta kashe ta kalle su duka daidai lokacin da Juwairiya ta yi sa'ar yaar idanunta, na tsoron haWa ido da ita da suke ta kalle ta, don ta ga wannan mace mai ji da kanta da wulaan ta mutane.

Karab ida 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~nun su duka suka haWu da juna Juwairiya da yar ta yi nasarar daile gangar jikinta da yake shirin tashi da zura da gudu ganin kalar matar da A.m yake aure.
" An ya ar Nigeriya ce?"

Ta tambayi kanta cikin tsananin mamaki domin yanayin ta da kyanta surar ta gabaki Waya ya tsorata ta,saboda hasken ta har wani kashe ido yake yi sosai da ta yi duba ga kalar fatar jikinta sai ta ga ta yi baa wuluk kamar gawayi,duk da ya ba kyan fatarta da awayenta suke yi.

Zainab kuwa wani irin tsanar ta ya shiga ranta haka kawai sai ta ji ba ta kwanta mata ba,ba wai kuma kyan da ta gani ba ne ya tsorata ta a'a ita sheda ne akan A.m ko an mata larabawa za ta kawo mishi ba zai yi dubi garesu ba, duba ga yadda ta sha wahala kafin ya amince da ita sannan tun da su kai aure ba ta taSa jin ya yi maganar wata ko wata ta kira shi ba.

Amma sam Juwairiya ba ta yi mata ba saboda daga ganin ta za ta yi munafunci ganin yadda take duar da kanta asa-asa.
" Atine an ya wannan arinyar kina ganin ta yi?Kin san A.m a kwai shi da yanyani ji yanayin shigar ta da wani zumbulelen hijabi kin san ya na da tsafta, kar ta zo ta na ma na girki ya na shiga sannan wallahi zubin ta bai yi min ba don ni na daina Waukar an aiki gidahumai auyawa,bai gaya miki Wakin sa da komai na shi ita za ta din ga gyarawa ba?A can zo wata kawai."

Juwairiya ta yi asa da kanta jin abin da ta faWa duk da ranta ya Sace,amma ta yi tunanin fiye da hakan a gurin ta saboda ta karance ta tsaf mace ce mai Wagawa da nuna ta isa,musamman

Please Login or Register in order to submit comment