Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sonka!!!"

Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya na jin kukan ta na yi mishi zafi sai ya ara sauri ya shige motar sa ya fice daga harabar makarantar a guje.

Durushewa ta yi a gurin tare da saka razanannen kuka.

Da sauri Hauwa ta fito ganin motar sa ta Sace tare da kama ta ta na son ta miar da ita.

FaWawa jikinta cikin muryar kuka da sheshshea.
" Ki taimake ni A.m ba ya sona ya tsane ni na tabbata son shi zai kashe ni domin na fi buatar na mutu fiye da ina kallon ya na fifita wata a kaina.Wayyo Allah na!Ina ma a ce mutuwa na yi ban haWu da shi a cikin rayuwata ba."

Hauwa ta ruWe ganin kukan da take ba na wasa ba duk da guy Win ya cancanki a so shi,amma ita a ganin ta bai kamata ta so shi haka ba ganin za ta cutar da rayuwarta a banza.

Da yar ta ja ta suka bar gurin domin su kaucewa mutanen da suka fara taruwa.
Ruwa ta mia mata wanda ta karSa tare da Salle murfin,ba ta ije gorar ba sai da ta shanye duka.

"Ki yi hauri ban baki shawarar ki faWa masa ba don ya wulaanta ki,da ace na san abin da zai faru kenan da ban ce ki gaya masa ba.Kici gaba da addu'a babu abin da ya gagari Allah.Amma da kin bari ki samu ciki wataila ta nan kawai za mu ci galaba a kan sa."
"In har A.m bai amince da soyayyata ba ni kuma ba zan yadda na samu ciki da shi ba, na gwammace na yi ta rayuwa da shi a haka da na haihu da shi ya gujeni."
Abin da ta faWi kenan cikin murya kaukausa ta Wauki jakarta ta tafi.

Tun daga ranar A.m ya Wauke mata fuska wanda sai da ta yi mishi kuka,sannan ta ba shi hauri ta janye maganar so a tsakanin su sannan suka shirya.
*****
Zainab ta yi kuWi na ban mamaki mace ce mai aji wadda take son ta zama babbar mace a kan komai.

Ta na da kuWi da aji da ilmi ta na jin ta a cikin manyan mata masu amsa sunan su.

Ita kanta ba za ta iya irga iya dukiyar da take da shi ba.A yanzu sam ba ta yawan zuwa aiki domin ta zamo babba, a asibitin da take aiki ba ta wani zuwa sai dai in za ayi aiki tazo ta farWe ta Winke.

Zainab ta na da matuar oari a gurin aikin ta shi ya sa kullum take ara samun Waukaka ta ko ina.

Irin kuWin da take samu ta zama babbar mace yar lukuta duk da ba ta son ta yi iba, aikuwa saboda kuWi ya zauna ta cika ta batse tamkar za ta fashe,ta yi wani irin kyau sosai abin ka da farar mace alkyarbar mata.

Duk yadda A.m ya so ya kafa mata doka dole ya watsar da makaman sa ya Wauki addarar sa,bayan ya fahimci matar sa mai aji ce kuma mafi Waukaka a cikin matan duniya saboda tarin ilmin da Allah ya yi mata.

Saboda arin girmar da ta samu haka ya rage zuwa aiki da take yi,sai dai in yawon ta ya tashi ta fice, sai hakan ya i ba A.m damar kasancewa da amaryar wucin gadi kullum su na tare da Zainab, in dai ba fita ta yi ba wanda kwana biyu ta rage yawo.

Rashin fitar ta sai ya takura su duka musaman A.m da kwana biyu ba su haWuwa sai a waya.

Saboda warewar Zainab mahaifinta ya yi mata alawarin gina mata asibiti na ta mallaki wanda har an fara aikin gini.

Wata tafiyar ta kama A.m a kan kampani da suke oarin buWewa na sarrafa fata,Daddy ya Wora A.m akan kayan da za ayi amfani da su.

A.m ya shirya viza tare da Juwairiya domin ya yi matuar kewarta,ba tare da ta sa ni ba sannan ya na son a duba lafiyarta don ya matsu da ta samu ciki su rabu.

Zuciyar sa ta kan buga daram! A duk lokacin da ya tuna zai rabu da ita,saboda ya shau da ita sosai sai dai ya san dole watarana za su rabu.

A.m da yake ta tunanin hanyar da zai bi ya samu ya tafi da ita,amma ya rasa ko da ya yi musu viza bai sanar da ita ba.

Ranar talata ya kirata bayan ya gaya mata za su tafi sai hankalinta ya tashi matua,don ita ba aryar da ya ce ta yi ba ne yake tada mata da hankali.

Tunanin ta yadda za ta bayyana masa abin da ke faruwa ne,saboda ta san muddin ta gaya masa sai ya kaita kushewarta,ganin yadda A.m yake nuna mata tsantsar damuwar sa akan rashin samun cikin ta.

Kamar yadda A.m ya gaya mata akan ta yi aryar Mama ba lafiya, ta yadda zasu samu su tafi,haka kuwa aka yi bayan ta shirya kayan ta akan za ta je ta yi sati biyu saboda ta yi jinyar Mama.

A jirgi hankalinta ya yashi warai ta aname shi cikin tsananin tsoro ta na jin kamar numfashinta zai Wauke,kasancewar ta na tsoron hawa jirgi sosai ko lokacin da ta raka Mama haka ta din ga auyanci.

A.m kuwa sai dariya yake mata ya ciro wayarsa ya na musu bidiyo, ganin yadda ta tsorata ta na auyanci,sam bai damu da kallon su da ake yi ba.

Juwairiya ta shiga cikin sabuwar duniya ta din ga zuba ido ta na auyanci,yayin da zuciyarta take yabawa da asar.

Bayan sun sha baccin gajiya ita kuwa sai da ta yi Wan zazzaSi, shi ya riga ta tashi ya na oarin cire kayan jikin sa ya shiga bayi don ya watsa ruwa.

Kallonta ya yi ganin ta tashi suka zuba ma junan su ido,na tsawon lokaci can kuma sai suka kwashe da dariya.

Hannu ya mia mata ya na faWin."Matar wucin gadi zo mu je ki taya ni wanka."
Dariya ta yi tare da noe kafaWarta ta mie za ta fita daga Wakin, ganin ya taho zai kamata kan dole sai ta taya shi wankan.

" Don Allah ka cika ni kunya nake ji."

Ta faWa ta na Soye fuskarta da murya na son jan hankalinsa,shi kan sa bai yi tunanin ta na da irin wannan muryar ba,saboda cikin salo da jan hankali ta furta har da Wan yi mishi fari.

" Kin san Allah dole yau sai kin taya ni wanka ko da kuwa muryar ar baby za ki yi don na gaji matua."
Hannunta ya kama ya na son ya ja ta zuwa bayi amma ta i cikin salo take magana da muryar kuka akan ya yaleta.

Ganin za ta Sata mishi lokaci cak ya Wauke ta bai direta ko ina ba,sai cikin bayin ya tsunduma cikin ruwan da ta ji sanyin shi matua.

Saboda tsaSar shagwaba kuka ta saka mishi da gaske,wanda hakan ya bashi dariya ya watsa mata ruwa a fuskarta.
"Sarkin kuka dama mai hali baya fasa halin sa na manta fa matar wucin gadi ar auye ce sam ba ta san soyayyar turawa.Allah sarki Zainab sai na tuna lokacin da muka zo cin amarcinmu mun yi soyayya sosai saboda ita mai aji ce."

Wani irin hajijiya na kishin abin da ya faWa ya kamata,amma ba ta son ran sa ya Sace ko ta Sata na ta,sai ta kalle shi ta yi dariya har da kashe mishi ido ta ce." Allah ko duk da ni matar shige ce ba matar so ba amma ka rubuta ka ije,zan nuna maka soyayya wanda ba zai taSa gogewa zuciyar kaba ko da kuwa mutuwa na yi ba rabuwa mu kai ba."

Ta bashi amsar abin da ya faWa duk da ranta bai yi mata daWi ba.

" Allah ya sa ni dai na san tsabar shagwaSarki ba zai baki damar haka ba, matar wucin gadi domin ke ma buata kike a lallashe mai hawayen banza.

Jin abin da ya ce sai ta saka kuka sosai ta na arawa har da diddire afafunta a cikin ruwan.
"Na rantse ka rubuta ka ije watarana wannan hawayen da kake kira na banza,sai sun zama abu mafi daraja a gurin ka wanda zubar su zai zama guba a cikin zuciyarka kuma da hawayen ka za ka rarrashe su."

Lakuce mata hanci ya yi tare da shiga cikin abin wanka ya ara dannata cikin ruwa ya ce." A kwai kuwa tabbas ranar da kika haifa min yarona kina kukan rabuwa da shi,ni ma zan zubar da nawa saboda tausayin ki da na Wana wanda ba zan taSa gaya masa ya na da wata uwar bayan Zainab."

Da sauri ta duar da kanta cikin abin wankan lokacin da ya saka hannun sa ya na oarin yi mata wanka,hawayen dake zubo wa a fuskarta suka haWe da ruwan suka gauraye ba tare da sanin ta yi kuka ba.

Wata irin kula A.m yake ba ta sosai sun sha yawo kusan babu ai da bai kai ta ba,ya yi yawo da ita ko ina tare da yi mata siyayya har ya na tonon ta da kayan lefe ya yi mata tunna bai yi ma matar wucin gadi ba.

Irin rayuwar da A.m ya nuna mata a asar ta haiance ma kanta tabbas ya na sonta,kuma kafin su bar asar za ta ara gaya masa ta na sonsa a karo na biyu,don har yanzu ba ta yadda ba ya son ta ba.

Bayan sun dawo daga yawo Juwairiya ta na kicin girki take yi,wanda A.m ya takura mata sai ta yi mishi tuwon ta mai daWi na shinkafa da miyar taushe.

Tare suka je suka yo cefane ko da ta shiga kicin Win bin ta ya yi da wayar sa,ya saita ta na girki ya na mata video,hakan sai ya yi matuar burgeta ta na ara son A.m,saboda namiji ne wanda ya iya kula da mace ko da baya sonta,amma yanayin kular da yake mata ya isa ya nuna mata cewar ya na sonta.

Ko da ta gama abincin a ranar cewa ya yi shi zai ba ta a baki saSanin da da ita take ba shi.

Haka ta zauna ya din ga ciyar da ita ya na Waukar ta hoto.

Da suka zo gun kwanciya A.m ya rungumota ko mai ya tuna,sai ya mie ya tsaya a bakin windo tare da zuge labule ya na kallon waje.

Hakan da ya yi sai ta gane a kwai magana a bakin sa, ba ta mie ba amma ta tattara dukkan hankalinta ta na kallonsa.

"Juwairaah gobe za mu je akan maganar dashen ciki da za'a ayi mik, likita ya ce za ayi miki gwaje-gwaje kafin ayi."

Gabanta ne ya faWi jin abin da ya ce ba ta ce masa ala ba,amma ta ji sanyi matua da ta ji ya ce sai an yi gwaje-gwaje kafin a farke ta,ta san likitan ba zai yi mata in ya gwada ya ga lafiyarta alau.

Dawowa ya yi kan gadon ya kama hannunta ya rie cikin murya mai sanyi ya fara magana.Na san ce wa ban kyauta miki ba don ba mu yi da yi miki aiki ba,amma ki taimake ni wannan ne kawai damata na yi miki alawarin ba ki duk wani jin daWin duniya, in har za ki yadda a yi miki dashe ki haihu ."

Wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska wato har yanzu ya na kan bakan sa,abin da yake yi mata ya na yi ne don ta yarda a farke ta ba soyayya ba ne.

Jikinta ya yi matuar yin sanyi kamar ruwa ya cinye ta ayau ta yi ninyar ta gaya masa ta na son sa,amma ta cire ran A.m zai so ta a rayuwa ta na son a karo na biyu,kawai sai ta yanke shawarar gara su je Allah ya saka likitan ya ce ba ta haihuwa ya yi mata aikin,fatan ta a ce shi zai zama sanadin numfashinta ta huta da tarin bain cikin da take fuskanta.

"Na amince in dai hakan zai saka ka farin ciki saboda burina kenan,na saka ka a cikin sa ko da ace ni zan fuskanci akasin haka."

Hannunta ya rie kam sai ya rungumeta." Na san cewa duk ranar da muka rabu zan yi kewar mace,mai hauri da hali na gari ina miki fatan Allah ya baki rayuwa ingantacciya,kuma na miki alawari zan bawa Wanki kulawa."

Komawa ta yi ta kwanta ba tare da ta amsa ba ta na zubar hawaye.

Washegari A.m da kan sa ya shirya ta suka tafi asibitin.Bayan gwaje-gwaje da likitan ya yi musu har da ita,ya tabbatar masa da lafiyar ta alau ba sa buatar wani dashi.Magani ya ba su wanda duk lokacin da zai yi tarayya da ita ya yi amfani da shi.

Duk da cewar bai ji daWi ba ya so ayi komai a wuce gurin,amma haka ya baro asibitin cikin jimami,ran sa duk babu daWi bayan ya karSi maganin.

A.m da gaske yake nufi da ya ce mata kafin su koma gida sai ya ba ta tsaraba,ita dai dariya ta ke masa suna gudanar da rayuwa a asar mai wuyar mantawa.

A ranar da zasu dawo ta na kwance ta na tunanin in da za ta kai abubuwan da ya siya mata,saboda ya yi mata siyayya ya kashe mata kuWi na ban mamaki ta san ko hauka ta yi ba za ta kai ma Mama kayan nan ba,haka kuma ba za ta kai gidan sa ta na amfani da shi ba amatsayin ta na ar aiki,mamakin sa take da ko tunani bai yi ba ya yi mata irin waWannan siyayya.

Ta yanke shawarar kai ma Mariya ta ije mata kuWin kuma sai ta din ga sakawa a banki.

Kamar yadda suka tsara jirgin su na sauka ta wuce gida kan sai ta ara sati,in ya so sai ta ce jikin Mama ne ya tsananta.

Juwairiya ta tsorata lokacin da ta yi sallama Mama ta amsa mata ta na udundune da bargo,sai hankalinta ya tashi ganin ta yi wa Zainab aryar Mama ba ta da lafiya gashi ta same ta ba lafiyar,shi ya sa aryar ciwo babu kyau don ita gani take kamar aryar da ta yi ne ya kama Mama.

"Mama dama baki da lafiya shine baki kirani kin gaya min ba."Ta faWa cikin tashin hankali ganin ta na jin jiki.

"Na so na kira ki ita ta hana gani take kamar jikin ba zai yi zafi haka ba."

Ibrahim ya ba ta amsa don ta kasa magana sai hawaye dake gangarowa,saboda tsananin zafin ciwo kuma duka kwana biyu ta fara ciwo.

Asibiti ta samo mai adaidaita ya kai su bayan an yi mata allura aka ba ta magani,suka dawo gida ta shiga jinyar Mama.

Rashin lafiyar Mama sai ya hanata komawa gidan ta na jinyar Mama da yanzu ta fara jin saui.

"Juwairiya ya kamata ki koma aiki kin san yau saura kwana goma sha biyar shekara Waya ya cika,kuma kin san na gaya miki ko duk duniya mutumin nan zai baki ba zan lamunta ki ara ko da kwana Waya ba."

Mama ta ce mata cikin murya mai Wan zafi duk da jikinta babu arfin da za ta Waga murya.
Gabanta ne ya faWi ta Wago ta kalli Mama sai jikinta ya yi sanyi ta ce."Na sani Mama kuma da zarar lokaci ya cika ni kaina gida zan dawo na yi aure kamar yadda kike buata,amma ki kwantar da hankalin ki kin ga yanzu ba kya jin daWi."

Ta mia mata kofin kunu tsamin da ta sa ta dama mata saboda tafi son abu mai ruwa-ruwa.

"Ai ina tuna miki ne don ranar da shekara Waya ya cika in har baki dawo ba sai dai ki ji na kai Baba Sani kotu."
Ta karSi kofin kunun da ta mia mata ta fara sha.Jikinta ne ya yi sanyi ta mie ta fice daga Wakin domin ba ta aunar ta ji Mama ta irgo mata kwanakin rabuwar su duk sai ta ji hankalin ta ya tashi.

A yau take son ta je ta gyara layinta da kampani m t n suka kulle mata tun washegarin da ta dawo saboda ciwon Mama ta kasa zuwa ta gyara,amma yau ta ga jikinta ya yi sauki ya sa ta shirya don ta san A.m zai neme ta har ma da Zainab saboda ta ara kwanaki akan sati biyu.

Kasancewar da yamma ne sai ta yanke shawarar ta tafi a asa tun da babu wani nisa.

Tafiya take a hankali kamar ba za ta taka asa ba ji ta yi wata mota ta sharo ta na shirin tureta.

Da sauri ta matsa gefe cikin tashin hankali ta na tunanin waye wannan mahaukacin da zai kasheta.

"Ke amaryar wucin gadi ina za ki je ba tare da izini mijinki ba?"
Muryar A.m ya daki kunninta lokacin da yake saukar da gilas Win motar sa.
Mamakin ganinsa da tsorata ta da ya yi ya sa ta Sata fuska amma da murmushi Wauke a fuskarta.
"Allah ka ba ni tsoro na yi mamakin ganin ka"Ta ce mishi lokacin da ta tsaya a gefen shi.

A.m ya kashe mota ya fito ya tsaya kusa da ita ya ce."Ina ta nemar wayarki ba ta shiga na kira wannan kwaWayayen Baba Sani amma kin san me ya ce."Wai sai na biya shi zai haWa ni dake hankalina ya tashi hakan nan na daure na zan zo gidan ku sai gashi mun haWe kin yi satar fita."

Dariya ta yi jin abin da ya ce."Ni ba satar fita na yi ba layina aka rufe zan je na buWe ne."Ta bashi amsa ta na kallon shi.

"Lafiya ba ki dawo ba gidan babu daWi kwana biyu na yi missing Winki ga tubbina da ya yi rashin daddaWar abincin.Gaskiya gangar jikina da tubbina sun yi rashin har na kasa haura ."

Zuba mishi ido ta yi jin abin da ya faWa kamar da gaske.
"Ai ko ya kamata ka fara sabawa ko ka manta saura kwanaki mu rabu.Kuma meye abin damuwa bayan ka na da matar so a gida ban ga dalilin da zai saka ka damu da matar wucin gadi ba."
Ta faWa cike da tsantsar kishin Zainab da ya bayyana arara a fuskarta.
Kallonta ya yi tare da matsowa daf da ita ta yadda har suna jin numfashin juna ya kama hannunta ya ce.

"Kishi ko?"

Ya saki hannunta ya juya mata baya sannan ya ci gaba da magana.
"Bai kamata ki saka kishin matata a zuciyarki ba kin san cewa ita ce matar so.Kin sa dalilin aurenmu am sorry to say da Zainab ta na haihuwa babu abin da zai saka na aure ki.Kawai ni na san in muka rabu zan yi kewarki da kishin mijinki don ki na da baiwar da ba kowa ce mace take dashi ba."

Ta na son ta yi magana kuka ya wace mata amma hakan na ta daure ta ce."Mai yasa ka shigo da ni cikin rayuwarka ka san ba gurbina a cikin zuciyarka?"

"Saboda ki haifi yaro na bawa Zainab saboda ina son na ga waina ya sa na aure ki."Ya faWa muryar sa a Wage.

"To mai ya sa kake gaya min maganganun da suke yaudarar zuciyata?Ka tsaya iya kan abin da kake buata a gareni."

Cikin kuka take mishi maganar sai ta juya za ta ruga da gudu da sauri ya janyo ta zai rungume ko mai ya tuna ya sake ta ta ruga da gudu ta na kuka.

Cikin motar shi ya faWa ya na wani irin huci kamar mesa ya daWe a gurin sannan ya figi motar a guje kamar zai tashi sama.

Lantana mai aikin Zainab da take laSe a bayan kango ta na kallon A.m da ya yi shirin rungume Juwairiya ta fito cikin tsananin mamaki ta na kallon in da motar shi tabi.

Zaro idanunta ta yi cikin tashin hankali ta na mamakin da ma cin amanar ta suke shi da ita?Allah Sarki baiwar Allah ta na can ta damu da ita gashi wayarta ba ta shiga,ashe ita ta na can suna cin amanarta.Haba!Biri ya yi kama da mutum ai ko yau dole Zainab ta ji abin da suke yi ita ta na can sai tsabar son kuWi ta Wauko mace zueiya ta ije ma mijinta.

TO FA WAYYO ALLAH BA RI NA YI NAN DON GASKIYA BAN SHIRYA GANIN WANNAN TASHIN HANKALI BA.






KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.








*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 25*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM




Hajiya Zainab tana zaune a aton katafaren falonta ita da awarta mai suna Nabila wacce suka taso tun yarinta,amma ita tana aure a Abuja ta zo ganin gidane da kuma ta ya Zainab murnar asibitin da ta buWe.

Lantana ce ta shigo saboda tsabar gulma jikinta har kyarma yake yi.

Duk da ganin tana tare da bauwa amma sai ta kasa hauri har bauwar ta tafi, matsawa kusa da ita ta yi ta fara magana don tsabar gulma da yake cinta.

"Hajiya don Allah in ba za ki damu ba ina son na yi magana da ke kuma mai mahimmanci."

Zainab ta kalle ta sheee tare da jan tsaki ta na tauna jingam a bakinta.
"Ni fa Lantana na fara gajiya da halinki yadda kika san ke kika kawo babu duniya,na san yau ma bai wuce ki ce na baki kuWin aiki kafin wata ya are ba,kuma na rantse ko me za ki ce ba zan bayar ba."

Ta faWa hankalinta na kan waya ta na hira da matar da ta addabeta take ta tura mata da sallama kullum,ba ta daina ba har sai da ta yi nasara ta fara magana da ita suna gaisawa.

Lantana ta kalleta a ranta ta ce."Banza mara mutunci kawai ai wallahi don kawai iskanci suke yi da ita da na so ma ya aureta na ga aryar iya shege."

Amma a fili sai ta ce." Ba wannan ya kawo ni ba idanuwana sun yi mummunan gani kuma in kika ji,wallahi hankalinki zai tashi matua ba na son abin da zai cutar da ke ne kasancewar ki na taimaka min.

" Ke dakata karki dame ni da shegen surutunki."

Ta ce bayan ta ije wayarta sannan ta kalleta ta ci gaba da cewa." Za ki iya magana ba ni da matsala awata ce tun na yarinta."

Lantana ba haka ta so ba amma tun da ta faWi haka gashi gulma na iban ta sai ta kwashe abin da ta gani,harma da ara magi da gishiri don ya yi zai cakwai ta fara gaya mata.


Ba ta kai ga arshen labarin ba in da take tunanin zai fi Waga hankalinta.

Zainab ta mie kamar wata mahaukaciya ta kai mata raruma.
Wani irin shaa ta kai mata cikin ihu ta zare idanunta kamar mahaukaciya.

" Ke baki da hankali mijina kike maganar kin gan shi da wata in ma da wata kika gan shi,bai kamata ki haWa shi da wata azamiya kucaka yar matsiyata ba."

Sai kawai ta rufeta da duka da mari take kai

Please Login or Register in order to submit comment