Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsigar tambayar kansa saboda ganin da ya yi kan maganar auren ta kawai ya bata da aminin na sa wanda suka zama kamar an'uwa.


Miewa ya yi ya tsaya a windon dake ofishinsa ya na kallon waje ganin Daddy ne da aninsa yake tua shi,ya yi maza ya fice daga ofishin tare da shigewa cikin wani ofis wanda ya san ba za su neme shi acan ba ya kulle kansa.


" Wayyo Allah na! Ya zan yi na san Daddy ya biyo ni ne ganin na i Waukar wayarsa ga shi kwana biyu A.k bai zo ba abubuwa duk sun caSe.


Sai ya yi shahadar kiran wayarsa duk da ya san ba dole ba ne ya Wauka saboda ya yi fushi tunna mai tsanani da shi.


ilai kuwa wayar ba ta shiga wanda ya tabbatar mishi da ya yi blocking Win layin ne,Waga wayar ya yi zai yi jifa da ita sai ya fasa ganin kira ya shigo a ransa ya na addu'ar Allah ya saka shi ne,duk da ya san abu ne mai wuya ya kira shi

Ganin kiran Daddy sai hankalinsa ya tashi ya kai hannu zai kashe bai san sadda hannunsa saboda ruWewa ya danna masa amsa kira ba har kuma ya saka a amsa kuwa.

"Son lafiyar ka kuwa wai me ke faruwa ne?Rejecting Win wayana kake yi are you alright kuwa? Ina A.k wayarsa ba ta shiga lafiya yake mai ya faru tsakanin ku mutane suna ta kirana suna complaining tun shekaranjiya na Wauka ko bai jin daWi.Gashi gobe ne tafiyar ku chaina.


Daddy ya fara magana ya na jero mishi tambayoyi cikin tsananin damuwa wanda ya ara ta da hankalinsa to mai zai cewa Daddy shi kam ya yi nadama sosai ya san ya na da saurin fushi amma nan da nan yake sauka.


"A.k ya yi fushi sosai dama haka yake da Waukar abu gaskiya na shiga ruWani kawai na haura da auren bani da rabon haihuwa ne don ba zan iya karya alawarin da na yi ma Zainab ba,ba zan iya rabuwa da ita ba don ina son ta na tabbata duk ranar da na kawo wata mace Zainab za ta yi kisa in kuma ba ta yi ba za ta kashe kanta ko ta rabu da ni,ni kuma ina sonki bazan iya rabuwa dake ba."


Sai kawai ya rintse idanunsa ya na jin wani gululun bain ciki ya tokare shi a maogaron sa ya duka asa don jin shi yake zai faWi."Hello ka na ji na a kwai abin da kake Soyewa son ban yarda yadda yake girmamani,zai daina zuwa aiki ba maza ka shirya muje gidan sa duk in da kake ka dawo ina jiranka ga shi nazo ofis Win ka baka nan."


Muryar Daddy ya katse mishi tunanin sa ya firgita lokacin da ya faWi haka dama ya san babu wanda zai yi gigin gaya masa sun samu saSani ne in ba so suke su rasa aikin suba.


" Um um Daddy ba ni kusa na fita a mashin zan karSo tsako bari na dawo sai muje."

" Ok duk ma in da kake yanzu ka yi maza ka dawo."

Daddy ya ba shi umurni tare da katse wayar sa ya bi wayar da kallo ya san dai a kwai abin da ya haWa su,amma haka kawai A.k ba zai i zuwa gurin aiki ba sanin sa mai wazo da kiyaye halalin sa.

Kamar an ce Waga labule sai ya hangi A.m ya zura da gudu ya na sanWa ya fice daga kampanin kamar wani Sarawo,kamar yadda mutane suka tsaya suna mamakin haka tare da tunanin lafiyarsa kuwa Daddy sai abin ya ba shi dariya ya kira Mudassir ya nuna mishi shi,dai-dai lokacin da ya fice da gudu har ya na buge kai da get.


Dariya suka ara kwashewa da shi." Wai me ke damun son ne ya canza kwana biyu."Daddy yace ya na kallon Mudassir shiru ya yi kawai don ba za'a ji mutuwar Sarki bakin shi ba.

Yafi kusan rabin awa in yakai hannu zai wawasa gidan sai ya janye ya kai ma iska naushi ya na jin tsananin nadamar abin da ya yi masa.

" A'a yallaSai kai ne a tsaye."



Megadin gidan da ya fito da ninyar ya siyo abu a shago ya gansa tsaye.Jikinsa ya hau rawa don shi bai ji ya wanwasa kofar ba ya san zai sha faWa." Don Allah ka yi hauri wallahi ban ji ja ba kuma ba bacci nake ba."


Ganin ya gigice sai ya buWe baki a wahalce yace." Karka damu yanzu na zo."A taaice ya haWa kalmomin don baya son magana.

" To shigo zan Wan siyo a bu a shago ne."
Yace ya na waigen in da yabar motarsa amma ganin bai gan ta ba ya wuce abin sa.


A hankali yake taku zuwa cikin gidan ya na isa kofar shiga falo ya ga an buWe oda tun kafin ya wanwasa,matar A.k ne ta na dariya." Hangoka na yi na Zey."Tace masa da masa.

" Uhumh kawai yace ya ara sa ciki ya zauna."Ina mijin ki na yi mishi laifi don Allah ki ba shi hauri tun kafin ya fito duk da na san ba dole ba ne ya fito."Yace mata cikin damuwa.

" Oh wannan tsakanin ku ne ya dai kama ta ku din ga hauri kun girma fa shi ma tun da lamarin ya faru yake ta huci na ba shi hauri amma yai."


Tace sannan ta mie ta nufi Wakinsa ba ta jima ba ta dawo fuskarta babu walwala na in zuwa da ya yi duk irin haWa shi da Allah da ta yi kan ya gane kuran sa.Bayan fitar ta ne A.k ya rintse idanun sa ya na jin Wacin abin da ya faru tsakaninsu shi da Allah yake son shi ba wai don kuWin sa ba,amma haka A.m ya rufe idanunsa ya na gaya masa baaen maganganu kuma sab ba zai goya mishi baya akan abin da yake so ba.


A.m ya canza fuska tun da ta gaya mishi bai ce da ita komai ba idanunsa a rintse ya mie tamkar wanda wai ya fashe mawa a ciki ya fice ba tare da yace komai ba,abin da ya sa ya zo tsoro yake kar A.k ya gaya ma Daddy abin da ke faruwa kawai ya haura,amma tun da yai fitowa bari ya Wauko Daddy koma me zai faru ya faru.

Da ya koma hankalin Daddy ya tashi ganin yadda ya Wan faWa tsakanin kwana biyu,dafa kafaWarsa ya yi." Ka na cikin damuwa lafiya wai me faruwa ne?Ina A.k Win?"


Ya jera masa tarin tambayoyi a tare ya shai numfashi ya fesar sai kawai ya kwanta akan kafaWar Daddy cikin muryar kuka ya na hawaye yace." Daddy A.k ya yi fushi da ni mun Wan sami saSani ne saboda wata ar matsala kuma na je gidan sa na ba shi hauri,ni na janye wannan maganar amma yai saurarata har ya ije aiki.Daddy shi ne ya Sata min rai na kasa rie kaina na faWa mishi baaen maganganu, amma na yi nadama sai dai ya datse layina layika na ba ya son magana da ni."


Sai ya sa kuka kawai hankalin Daddy ya ara tashi yau shagwabar ta tashi kenan.

Miewa ya yi." Oya tashi muje gidan na sa amma ba ka kyauta ba duk da tsaanin harshe da haori ana saSawa,nan gaba ka kiyayye ba'a Sata ma wanda yake kusanci da kai sosai in ma hakan ta faru oari ake a rie fushi don dole zaku ne mi juna."

Daddy yace ya na shafa bayan sa." Gaskiya ne Daddy na ba shi hauri fa kuma na yi nadama.


A lokacin da suka isa gidan da matar shi ta shiga da nufin ta gaya masa,har ya ji muryar Daddy a falo da sauri ya zo ya durkusa ya na faWin." Da kan ka Daddy ai da ka sanar min ni zan zo."

" Ta ina zan sanar maka bayan ka kashe wayarka.Son ya yi laifi a yafe mishi don kawai kun samu saSani za ka dai na zuwa aiki, in ka ara hakan zan hukuntaka ta hanyar turaka asar waje ka yi wata biyu ba tare da ka dawo gurin iyalin ka ba,saboda ka Sata min rai kuma na yi fushi da kai."

Jin abin da ya faWa da sauri maman Najwa ta mie tare da ficewa ko gaisuwar da ta tsaya ta yi ma Daddy ba ta yi ba,don ya ba ta kunya duk da ta san in ya yi hakan ya cutar da rayuwar masoya.

" Ka yi hauri Daddy na yi nadama hakan ba zai ara faruwa ba! Da ma A.m Win ne ya...."


" Daddy ya yi hauri kawai ya koma aikin sa ni nama haura akan maganar da muka yi na fasa na janye."



Yace da sauri ya na kallon A.k don ya tsorata ya Wauka gaya ma Daddy zai yi.Daddy ya kalle su duka kamar a kwai abin da suke Soye mishi wanda shi ne ya kawo musabbabin faWan.

" To wai me ya kawo rikicin?"


Ai kafin ya rufe bakinsa A.m yace."Daddy ba komai ai mun shirya ya wuce."


A.k dai bai ce komai ba Daddy ya kama hannunsa ya haWa." Kar na ara jin kun yi faWa ku yi min alawari."


"Hakan ba zai ara faruwa ba Daddy komai ya wuce."Kamar sun haWa baki don a tare suka faWa. " Ok ka shirya ka taho aiki dama ina son na ara maka girma."


A ranar dai ba wata magana na amininai da ya shiga tsakanin su,amma tare suka fita zuwa aikin sai dai A.k ko zuwa su tafi cin abinci kamar yadda suka saba bai yi ba,don har yanzu ya na jin haushin abin da ya yi mishi hakan ya sa yake yin azumi don ya rage mishi fushinsa tunna ko Allah muna mishi laifi kuma ya yafe,amma shi mutum ne wanda ya san mahimmancin kansa.

in zuwa su je suci abinci hakan ya tabbatar ma A.m bai huce ba sai da ya daidaici ya gama tarin aiyukansa da ya jibga ma kansa,ya shiga ya na zaune a kan kujerar ofishin ya rintse idanun shi wataila bacci yake.


Shigar shi ya farkar da shi ya tashi ya zauna." Don Allah ka yi hauri haba na san ina da fushi,amma ba ni da rio na lura kafi son Juwairiya da ni na haura da haihuwar don ni ba zan aure ta ba don na rayu da ita har abada,amma tunna ba ka so mu manta da zancen.


Ga mamakinsa sai A.k ya bugi bayan sa ya na dariya yace." Haba na manta da wannan kuma akan maganar Juwariya na yadda ka aure ta Allah zan ba ka gudummuwa in har Daddy zai amince ya nema maka auren ta a sirri."


Ya Wan kalle shi ko ya yi tunanin wasa yake masa amma bai ga alamun haka ba sai ya rungume shi ya na faWin." Na ji daWin amincewar ka yamzu mu tafi gurin anin mahaifin ta."














Tofa masu karatu kun dai jin yadda ta kaya game da waWannan aminan juna,Baba Sani zai yadda ya basu auren ta.Ku ci gaba da bibiyata na gode da yaba lintafina da kuke.

UBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT IN KU YA NA SAKA NI NISHAI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi noma sha huWu.Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.




*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 14*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Sakamakon aiki da ya yi musu yawa sai hakan ya hana su zuwa kamar yadda suka shirya a ranar,saboda ba su tashi daga gurin aiki ba sai bayan sun yi sallar magariba daga nan kowa ya nufi gidan sa.


A.m ya ji daWi sosai ranar kasa bacci ya yi gani yake kamar ya auri Juwairah ya gama musamman da aminin sa ya amince,duk da a cikin zuciyar sa har yanzu ya na tunanin mai ya saka A.k ya sauko har ya amince duk da dokin nai da ya hau daga farko.


A haka dai ya yi ta sae-saen shi amma ya rasa gano komai daga arshe ya janyo bargon da Zainab ta rufe jikinta da shi ta na bacci,ya rufa da shi tare da juyawa dai-dai fuskarta ya rungumeta ya na shaar daddaWar amshi daga gareta,yayin da hankalin sa yake kwance kamar ya yi bao ya mutu a ransa duk ya osa gari ya waye su ji yadda za su kaya da anin mahaifin Juwairah.


A.k kuwa ko da ya koma gida hankalinsa a tashe gani yake kamar ya aikata zunubi me girma akan amince masa da ya yi,amma da ya auna a mizanin hankali sai ya ga da ta auri wannan tsohon rayuwar ta ta shiga garari gara A.m da ko ba komai za su samu ci gaba a rayuwa,duk kuma abin da zai faru wannan kuma ya bar ma Allah lamuran sa shi yake da iko akan komai,kawai abin da zai yi shi ne ya gaya ma Juwairiya kar ta yadda zuciyarta ta fara son A.m.


Ya daWe sosai ya na shawara kafin ya furta ya amince da auren musamman da ya ji mahaifiyarta ba da lafiya,a taaice dai tsotsan tsamiya suke yi a rayuwar su tare da alhini.


Washegari da safe A.m ya yi mishi dirar mikiya ko karyawa a gidan sa ya yi,wanda Maman Najwa ta yi  
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~mamakin sammakon sa amma sai ta yi tunanin ko ya na son A.k ya manta komai.


Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Juwairiya.


Baba Sani ya na oarin fita gurin aiki da ar auran motarsa da yake rie da makullin ta a hannun sa ya na karkaWawa.

Ganin su a kofar gidan sai ya yi turus ya na tunanin mai ya kawo waWannan larabawan kofar gidan ko sun yi makuwa ne,saboda ya na da Wagawa sai ya Wauke kansa zai shige cikin motar sa ba tare da ya kalli in da suke ba,duk da tunani ya cika ran shi ganin sun tunkaro sa.


"Assalamu alaika Malam barka gurin ka muka zo,don Allah ko zaka ba mu lokacin ka duk da ba ka san da zuwanmu ba,amma in ka bamu an mintuna zamu tafi musammam in ka yi ma abin da ke tafe damu kyakykyawar fahimta."



Yace da shi da murya mai sanyi duk oarin sa ya tabbatar masa da bain sa ne saboda fuskar sa ta nuna kokwanton ko sun yi makuwa ne,duk da ya san ya na da an mata amma ko kaWan bai yi tunanin za su zo neman Waya da ga cikin su.


Ya kalli A.m da ya Waure fuskar sa kuma bai ce komai ba ya lura wamda ya yi mishi magana ya fi shi sakin fuska,sai ya mai da hankalinsa ga A.m yace a cike da shakku don shi har yanzu bai yadda gurin sa suka zo ba.


" An ya gurina kuka zo ko kuma kun yi makuwa ne wataila tambaya ce da ku."


" Ka na shakkun mun zo gurin ka ne mu ba mutane ba ne? Ko aljanu ka gani." A.m ya ce mishi ba tare da ya kalle shi ba hankalin sa na gurin wayar sa dake hannun sa ya na daddannawa.


Baba Sani nan take ya ji ran shi ya Sace ya kalle sa a ran sa ya na faWin." Ba ka sanni ba kenan amma bari na ji da wanne kuka zo."


" Gashi kuma sauri nake zan tafi aiki sai fai ku dawo wani lokacin." Ya ce fuskar sa a Waure ganin A.m ya zo da rainin wayo.Am ya buWe baki zai yi magana sai A.k ya watsa mishi kallo kuma aka ci sa'a ya yi shiru ya ci gaba da kallon wayar sa.

" Don Allah ka yi hauri ka bamu an mintina kamar yadda na buata da farko ka saurari abin da yake tafe da mu."


A.k ya ce cikin marairaicewar fuska ya kuma haWa hannun sa biyu ya na roon sa.A.m kuwa kofar gidan ya din ga bi da kallo ya na jin wani tsigar jikin shi na tashi,wai shi zai haWa jini da ar wannan wulaantaccen gidan mai kama da bola,duk da Baba Sani ya na oarin gyarawa amma abincin wani gubar wani.



" Ok to muje in har zaku taaita maganar da ta kawo ku a cikin lokacin da kuka iba."

" In sha Allahu."

A.k ya bashi amsa a lokacin da suka shiga cikin gidan zuwa Wakin Baba Sani A.m ya na ta wulita ido ko zai ga Juwairah don shi yanzu ma ya manta da kamannin ta.

"Maza ku gaya min mai yake tafe daku da farko ina fatan ba laifi na yi ba kuka zo kama ni."Ya faWa kamar kuma ya ji tsoro a fuskar sa.

Hakan ya sa A.k ya murmusa shi ko A.m ko kallon sa bai yi ba.A.k ya gyara zama ya kalli Baba Sani ya ma rasa yadda zai fara ya na son ya ce A.m ya faWi buatar da ta kawo su,amma ya san dunula maganar zai yi ta yadda ma ba zai fahimce shi ba ya lalata abin,bayan dai in ina da ya yi,ya kuma shiga umbiya-umbiya daga arshe ya faWi abin da ya kawo su don barin kashi a ciki baya maganin yunwa.


Alokacin da Baba Sani ya ji maganar da A.k ya faWa sai ya ji kamar bai fahimci maganar ba kuma har ga Allah a cikin zuciyar sa ya gasgata hakan da bai ji ba.


" Ikon Allah bayin Allah don Allah ka ara maganar wallahi ban ji me ka ce ba yadda ka san ciwon kurumta ya kamani,a lokacin da ka yi maganar sake faWi kamar yadda ka faWa kuma da Hausa don Allah ba turanci ba.


A.k ya so ya yi dariya jin ya ce ya yi magana da Hausa ila in ya ara maganar da larabci zai ce ya yi mishi,A.m ya mai da wayar sa a aljihun rigar sa shi bai ga dalilin da A.k zai tsaya ya na Wan waken zagaye ba,ya san a ran shi irin abin da suka zo mishi da shi bai isa ya hana auren Juwairah ba



" Auren Juwairiya kuka zo nema!" Ya maimaita hakan ya fi sau ba adadi daga bisani ya mie zubbur ya na faWin." Haba dama na yi tunanin a lokacin da na ganku irin yaran manya ne da suke shaye-shaye su yi Satan kai su dami mutane,kun ga tunanina ya zama gaskiya ga ku kamar mutanen kirki ta waje amma ta ciki ba hali."


Ya numfasa sannan ya ci gaba da cewa ba tare da ya ba su ikon koda jan numfashi ba." Wallahi na Wauka wani abin ya kawo ku ko ba sa rana akan Juwairiya a bazan taSa yadda ta auri wani daga cikin ku ba,bare na ba da Juwairiya yanzu haka bikinta saura sati Waya don haka ku wuce ki bani guri an waya kawai."


A.m ya harzuo ya na faWin." Wa kake ce ma an waya kai ne mugun Wan waya da ka kasa gane mutanen kirki da na banza,ba giya muke sha ko kuma kamfanin wayar muke haWiya."



"A.m ya kamata ka saukar da fushin ka kasan me muka zo nema."


A.k ya ce mishi tare da kama shi ya zaunar ya na dafa kirjin sa.
" A'a ka barshi ya yi min rashin kunya ya biyo ni har gida zai gaya min magana,a Wakina fa kake.To bari kaji ko mutuwa za kai sai dai ka mutu, kai ko maka mutu ne aka fito da kai a abari,a ka ce na baka auren Juwairiya numfashin ka zai dawo wallahi sai dai a turbuWaka a cikin asa ta rufe maka ido."
" Wai tsaya kun ma san me kuka zo min da shi?Juwairiya da na tsana a rayuwata shi ne zaka kazo ka na da kuWi ka aura taS wallahi ina."


Da aka kai wannan gabar sai A.m bai ce komai ba ya rintse idanun shi kawai don aikin A.k ne.Amma sai ya ji A k ya yi shiru ya na kallon Baba Sani da yake faWin iri-iri ba ya son ar wansa ta aru,kai wannan wane irin mutum ne an ya a kwai zumunci a duniya saboda son duniya ko ya ce son kai,mutane sun manta zumunci bayan Allah ya gaya mana zamu tsallaka siraWi mara zumunci ba zai sha ba.


A.m ya buWe baki zai yi magana ganin A.k yai magana dai-dai lokacin da Baba Sani ya sausauta murya ko me tuna ya sa ya yi sanyi ya ce." To kai in ban da ku me za ku yi da mace irin Juwairiya yarinyar da ta gama zagaye duniya ta na yawon aikatau kuma duk mazan gidan sun san ta,sam ba ta da hali mahaifiyarta ta koya mata bin maza har sata take yi ka tambaya har kulle ta a ka yi a prison."

Ya ara sausauta murya ya matsa kusa da A.k don ya fi A.m saui ya fara magana kamar zai yi mishi raWa amma A.m ya na jin me yake faWi." Ina da yara sun yi karatu na boko in kuma so Juwairiya ba ta san komai ba har talla yi take yi,ai da ka aure ta gara na yi maka fatan ka mutu ba aure.

" Juwairah nake so kuma zan aureta ko da ace duk mazan duniya sun san ta a matsayin a mace."A.m ya ce ransa a Sace.


" To ba zan ba da ba kuma kamar maganar ta ita matar wani ne na rantse,a yau zan Waura mata aure ba sai an jima ba don ina zargin ku za ku iya sace ta.To ni sai in ce kamar an yi maka baki kamar ka mai zai saka ka auri Juwairiya uban ta har ya mutu faskare yake yi, a gurin faskaren ya sara ma kansa ya mutu shi ne za ka ce ka na sonta.


" Nima ba son ta nake ba ban taSa jin ina son wata a mace bayan matata ba,kai ma in ka furta ina sonta ka yaudari kan ka don duk faWin unguwarku ban ga macen da zan ji ina son ta ba."


Kawai sai ya yi galala ya na kallon shi a ransa tunani yake to uban me zai yi da ita,koma dai mene ne ba za ba shi ba in ma ya na son ya yaudare shi ne ya ba shi aurenta,yadda ya rantse Juwariya ba ta ba jin daWi a duniya tun da ta kange kwaWinsa a kan ta gara ya ba ma wannan tsohon ya wulaanta rayuwar ta.

" Ku faWi ko me za ku ce ni ba yaro ba ne kuma ba zan baku auren ta ba yanzu ma zan Waura mata aure don haka ku cire wanann tunanin."

A.k ya karkace ya zaro makullin mota ya ije masa a gaban sa sannan ya janyo cek da ga aljihun sa ya ije na kimanin miliyan biyar.


Wayyo Allah zo ka ga ido sai ya zare ido can kuma ya fara mitsinan kansa ya gane ko mafarki yake." Ka bar cutar da kanka ta hanyar mintsnin kanka ba mafarki ba ne a zahirin gaskiya lamarin ke faruwa,in har ka bamu haWin kai har gida zan canza maka rayuwar ka ta dawo sabuwa in har zaka ba ni auren ta."

A.m ya ce da shi ya na kallon sa yadda ya ruWe kamar zai zare." Ikon Allah don Allah in mafarki nake ku dake ni sai na farka wai ni ne

Please Login or Register in order to submit comment