Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amfanin ta a gidan?Ko ubanta yake neman ma na kuWin da za mu biya ta?"



SAUKAR MARIN YA SA NA FIRGITA AMMA NA CI GABA DA RUBUTU SAI DAI KUMA TAUSAYIN JUWAIRIYA YA HANANI ARASAWA,DON NA KASA GANE MAI NAKE RUBUTA AN YA ZAINAB KIN KYAUTA KUWA.
KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN BARI NA ARA TUNA MUKU DA SUNAN LINTAFIN
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO

TUNATARWA

DON ALLAH AN'UWANA MATA KADA KARATUN LINTAFI YA AUKE HANKULANMU MU MANTA DA BAUTAR UBANGIJI,KU TUNA ALLAH YA HALICCE MU DON MU BAUTA MASA NE.


GOBE JUMA'A KAR A MANTA KARATUN SURATUL KAHAFI ALLAH YA BA MU ALKAIRUN DA KE CIKINTA AMIN








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi noma sha shidda.Ga masu buatar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ofa a buWe take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaauran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.







*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 20*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM





A.m har ya buWe baki zai ara magana sai kuma ya fasa,ya Wauki wayar sa ya haye sama ba tare da ya ara kallon Waya daga cikin su ba.

Juwairiya ta dafe uncinta hawaye na zarya a fuskarta da ma ta san dole watarana Zainab za ta dake,ta tun da halinta ne sai dai yadda ta ji saukar marin ta ji sam ba za ta iya Wauka ba,domin da ya zo neman aurenta bai gaya mata har da duka a ciki ba.

Hawaye ta share ta juya ta nufi kicin saboda rashin arfin da take ji,tsayuwa ma wahala take mata don haka ba ta ara ce wa komai ba ta shige kicin Win.

Jingina ta yi da slinder na gas Win kicin ta saki kuka duk da ta na jin cewar,lokaci ya yi da za ta dai na asarar hawayen a banza akan su saboda ta fahimci bayan damuwar da suke saka mata,har da na auren su da suke faWa kamar kaji su hana wawalwarta sukuni.

Da yar ta samu ta kammala girkin da taimakon Baba da ta dameta da tambayar mai ke damunta,ganin ta i tanka mata sai ta kalle ta ta ce bayan ta gama kwashe abinci ta saka a kula.

"ar nan ya kama ta ki naimi maganin basir saboda shi yake damun ki,ji yadda kike cije baki ki na tafiya da yar."

Da takaicin maganar da ta yi mata Waki ta wuce ba tare da ta tanka mata ba.

Tun daga wannan ranar Juwairiya ta kame kanta ba ta barin ko haWuwa da shi su yi,saboda wani irin kunyar sa da take ji kamar ta nitse in ta gan shi,don ko gyaran muryar shi ta ji sai jikinta ya kama rawa kamar za ta ruga.

Kwana biyu Zainab ta takura kanta ta hana zuciyarta fita don ta faranta masa,saboda ta ga canji kwana biyu ya na wani shareta,da ta yi masa magana zai hayayyao mata kamar zai cinye ta.

Sai ta danne zuciyarta ta i fita ko ina daga aiki sai gida ta na ba shi kulawa,wanda da yar ta samu ya sauko suka koma rayuwar su kamar da.

Juwairiya kullum za ta yi musu abinci mai rai da lafiya su ci suna yabawa a zuci,don girkinta ya na matuar ayatar da su duk da babu wanda ya taSa yabawa,amma har Wan iba sai da suka ara kaWan.
Sai dai fa mai hali ba ya fasa halin sa Zainab a daddafe ta yi an kwanaki a gidan, wadda take jin kamar ta na gidan yari duk da irin kayan alatun dake gidan amma saboda ta saba fita sam komai ba ya burgeta.

Zaune take a Waki ta kulle kamar yadda ta saba duk lokacin da za ta yi rawa ta tura.
Tasha ado da wasu riga da wanda na an kanti masu kyau kalar pink,wandon bai kai asa ba.
Gyara gashinta ta yi ta fara rawa cike da warewa ta tura ta na murmushi don ta san yanzu za ta ga ruwan comment da like.

Ilai kuwa ta na turawa aka fara liking ta na kallo ta na murmushi,ta na shirin sauka wata numba da kullum take mata sallama a facebook,ta ara yi duk da ba amsa wa take ba amma ba ta gaji ba,ku san kullum sai ta yi mata sallama.

Tsaki ta yi ta sauka da ga online gabaki Waya ta na mamakin wannnan numba da take damunta,saboda ita in dai ba ta san mutum ba ba ta magana online,sanin cewar ita tauraruwa ce a yanar gizo so ba ta da lokacin da za ta tsaya ta na kula su,amma a ranta ta ji ta na son ta amsa sallamar don ta ji mai ke tafe da ita,saboda ta duba profile Winta ta ga ita ma ba aramar mace ba ce,don da Barrister Mardiyya take bearing.

Murmushi ta saki tare da ije wayar da sauri daidai lokacin da A.m ya murWa ofar ya shigo,sai ta kama hannunsa ta rie ta na dariya tare da kashe murya ta ce.
"Barka da dawowa yanzu na ji arar shigowar ka, ina wanka ne shi ya sa ban fito ba."

Dafe kan sa ya yi ya janye jikin sa ya zauna akan gefen gadon ya na kallonta tare da oarin rage kayan jikin shi.

"Babyna na gaji matua kamar kai na ciwo yake son ya yi,yunwa nake ji kawo min abinci in ci anan bacci nake son na yi."

Ya faWa tare da kwantawa ya miewa a kan gadon don jikin sa ko ina ciwo yake masa.

Zainab ta Wan canza fuska ta ce " Na Wauka za ka ci abincin a dinning ne fita nake son na yi,kuma Juwairiya ta riga ta shirya abinci meye sai ka wahalar da mutum gurin Waukowa."

Ta arashe maganar cikin yaui da yanga tare da Waukar wayarta,da take kusa da shi don ta tuna kamar ba ta sauka a online ba,sai dai kuma da ta tuna ba ta taSa ganin ya Wauki wayarta da sunan ya duba ba,ko kuma ya ce zai yi wani abu.

Gaban sa ya faWi da ta ambaci sunan Juwairiya ba zai ce ya manta da ita ba,amma sam ba ya son ya ji sunan sai ya ji haka kawai gaban sa ya faWi.

" Zainab ba na son rainin wayo ni da gidana da kuma matata ba ni da ikon na ce ga in da zan ci abinci?Kuma da kika ce wancan za ta kawo min,to ba ita nake so ba matata wacce nake da iko da ita nake son ta kawo min,kuma ki je ki dawo bacci nake son mu yi babu in da za ki."

A Wan kausashe ya faWa ya na harararta wanda ya zamar masa a'ida,kamar wani mace in dai aka gaya mishi ba daidai ba, sai ya yi harara.

Yarfe hannunta ta yi ta ije wayarta tare da fara orafi ta na ce wa." Haba Hubbi kai ma ka s 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~an na yi oari ban je ko ina ba,na baka lokacina na tsawon kwanaki.

Ta Wan matsa kusa da shi ta ce." Yau fa bikin anwar awar Anty Fati ake yi,ka ga ai ya zama dole na je ko?"Ta tambaye shi tare da tsare shi da ido.

Kallonta ya yi bai ce komai ba sai ya mie ya kunna tangamemen tibin da ke Wakin ya rie remote ya ce.

" Dole ki je mana gayyar soWi ni dai na gama magana ba in da zaki,ke ko kishina ba kya yi ki ta sa an aiki suna kawo min abinci,ko tunanin in canza miki ba kya yi."
Kusa da shi ta zauna ta na faWin." Yarda da kai ne Hubbi Allah in za a ban kur'ani zan iya rantse wa a kan ka,sam ba ni da haufi ko da ba ka yi min alawarin ba za ka yi min kishiya ba,hankalina ba zai tashi ba saboda ban taSa jin ka yaba wata mace ba."

Ta Wan kalle shi da murmushin yadda a fuskarta ta ci gaba da ce wa." Kuma duk abin da nake yi ai ba na zuwa da awayena waWanda ba su da aure gidana saboda tsaro."

Dariya ya yi jin abin da ta ce ya miar da ita ya na faWin." Ok Babyna ina godiya sosai da yardar da kika yi min,kuma ke Win zazzafa ce ta ko'ina ga kyau ga ilmi da da tarin baiwa kala-kala,ina gaya miki ba wata sai ke a nan."

Ya nuna mata irjin shi da da babbar yatsar shi dariya suka yi ta yi huggin Win sa,sannan ta ba manna masa kis ta ruga da sauri don ta Wauko masa abincin,duk da ranta bai so haka ba amma fitar ta ta rantse sai ta fita.

Don haka ko da ta dawo haka ta ci gaba da lallaSar sa har ya amince saboda ta dame shi,kuma bacci yake son ya yi da sauri ta Wauki Wan gyalen ta ta fice daga gidan.

Bayan ya ci abinci ya Wan mie tare da ba da tazara kafin ya kwanta,saboda abincin da ya ci sannan ya kwanta bacci.

Juwairiya ta warke sumul bayan Wan ciwon kwana biyu da ta yi ta zage ta na ta aikinta,cikin osawa a ranta ta na addu'ar Allah ya sa ta samu cikin ya Wauke ta daga gidan,ganin yadda Zainab ta mai da ita baiwa,shi kuwa daga ranar bai ara neman ta ba.

Ta na falo aiki take yi goge su tibi da abin da ya kama ta a goge a falon take yi.

Sosai ta mai da hankalinta a kan aikin da take yi ta na son ta gama ta Wora girkin abinci.

Ya fito daga Wakin sa ya na sanye cikin doguwar riga na jallabiya mai ruwan madara,wayar sa rie a hannun sa sam fuskar sa babu fara'a.

Juwairiya ta saki Wan aramin tawul Win da take goge tibin da shi za ta ruga ganin ya fito, amma sai ya yi maza ya rie mata hannu tare da kiran sunan ta.

Tsayawa kan dole ta yi tare da juya masa baya cikin tsananin kunyar sa.

Juyo da ita ya yi da murya mai sanyi ya fara magana.
" Ban san tunanin ki in da ya tafi ba tun daga ranar kin Wauke wuta kin mai da ni kamar wani dodo,bayan kin san wannan kamar sharan fage ne akan tsarinmu har zuwa randa zamu cimma haar mu,kowa ya huta da wahalar da kan sa mu samu maslaha a rayuwar mu."

Ta na son ta yi mishi magana irin ya faWa ta amsa mishi ko da maganar da ya yi mata babu daWi,amma kuma ta na matuar jin nauyin sa wanda ko haWa ido a bisa kuskure take yi.

Sai ta kauda fuskarta a ranta ta na faWin." Kai ne kake son ka cimma haar ka,amma ni ina son na kasance da kai har abada A.m ina sonka burina ka Wauke ni daga gidan ka nima ka sama min anci na rayu da kai duniya ta san mijina ne kai."

Amma a fili sai ta yi asa da kanta ta na kallon afafun sa suke da kyau da sha'awa.

" Ke ni fa ba na Waukar rainin wayo na yi ta miki magana kina sharewa,ki buWe baki ki yi min magana kuma ni ban ce ki yi min kuka ba."
Ya faWa ganin ta yi rau-rau idanunta sun kawo ruwa.

Kamar umurni ya ba ta sai ta yi oarin mayarwa ta na son kallon sa.

A.m ya saka hannun sa ya shammace ta kawai ya cire mata hijabin jikinta ya na faWin.

"Ni fa yanzu ban ga abin Soye-Soye a tsakaninmu ba bayan kin san ke Win matata ce,wanda aure ya ba ni damar mallakarki a gurin makwaWaicin anin mahaifinki."

Ta kauda kanta ba ta ce komai ba sai kuma ta saka kuka.
Dunule hijabin ya yi ya jefar ya ci gaba da faWin."Anyway yanzu dai ni maigida na ba da umurnin in dai daga ni sai ke ne a gidan,to amaryar wucin gadi ar ta ara saka hijabi ki bari sai in wanda kike jin kunya ta dawo sai ki saka abinki,amma ni da ke ai ba kunya tsakaninmu ko."

Ya gama maganar ya na tambayarta ya na wani irin murmushi mai kama da na mugunta ko ya na son shirya wani eta.

Juwairiya ta ji wani irin sanyi a ranta karan farko haWuwara da A.m yau ne rana ta farko da ya yi mata murmushi,duk da murmushin na sa da wata manufa ya yi amma hakan ya ba ta matuar citta a ranta.

Ta matsa daga kusa da shi ganin irin are ma jikinta kallo da yake ta fara tafiya a hankali.
"Juwairaah."
Ta tsaya cak daga tafiyar da take yi amma ba ta jiyo ba,shi ya taho har in da take ya matsa kuda da kunninta ya ce " Ina zaki matar wucin gadi ai ban gama magana ba,kin san ya kamata a Wora daga in da aka tsaya ko."

Banza da shi ta yi tana mamakin wai haka yake mai ya sa yau ya ara zuwa da salo ne?

" To shikenan tun da kin i magana da ma zan yi godiya ne na ranar nan gaskiya na ya ba sosai,wannan daren momerable and remarkable ne a gurina,Allah shi zai saka miki saboda ai ba ta ki da anin mahaifin ki ya yi."

Ya faWa ba tare da kunya ba kuma ya na kallon wayar idanunta.

Juwairiya ta Wago ta kalle shi ba tare da ta shirya ba ta ji ta sakar mishi wani lalausar murmushin,har dimple Winta suka losa ta ruga da gudu ta shige Waki tare da rufo ofar.

A.m ya saki dariya don kunyarta ta na matuar burge shi matuar gaske,saboda ya na son mace mai kunya juyawa ya yi zuwa waje jin shigowar motar Zainab,ya saki duk wani wulaanci da yake son yi mata da tsanar ta da yake ji zai more abin sa kafin zuwa ranar rabuwar su,saboda tsakani da Allah ya ji wani girmanta a ranshi tun ranar da ya mallake ta,tsananin talaucin da take ciki bai saka ta zubar da mutuncin kanta ba.
a an'uwana mata don Allah mu kama darajarmu domin shine mutuncinki, don Allah an mata ka da son abin duniya ko jinkirin aure ya sa ki zubar da mutunci,don ki na tunanin kin daWe ba ki yi aure ba ba zaki yi ba,ki tuna lokacin ki ne bai yi ba,kuma duk daren daWewa in da kina raye za ki yi,yayin da ki ka yi aure wulaanci shi ne abin da za ki girba har arshen rayuwarki.

Kuma ar'uwa da ki yi saurin aure ki fito gara ki daWe ba ki yi ba,ki daure har ki samu wanda zai kula da ke emotionally,phisically financially,and mentally.Shawara ce.

Juwairiya gado ta faWa tare da Waukar filo ta rufe fuskarta da shi.
" Mai ya sa yake min irin waWannan kalamai ne wai dama ba shi da kunya haka?Kai na rasa gane wa wallahi gabaki Waya ya canza dariya fa ya yi min."

Sai ta saki murmushi ta mirgina wani gefen ta na jin wani irin nishaWi a cikin zuciyarta.

" To ko ya fara sona ne?"

Da sauri ta kori wannan tunanin a cikin zuciyar ta amma kuma ta na fatan haka ta kasance,da sai ta ce tafi kowace mace sa'ar miji duniya,don A.m wuta ne gurin kyau da tsari.


Washegari Juwairiya ta na kicin abinci take haWawa hankalinta kwance cikin jin daWin abin da ya faru,jiya tsakaninta da shi jiya saboda kwana ta yi muryar sa na maimaita godiyar da ya yi mata.

A hankali ya shigo ba tare da ta sani ba don ta zage ta na haWa mishi abincin da zai ayatar da shi.

Ji ta yi an rungume ta ta baya ba tare da ta lura ya shigo ba.Wani irin ihu ta saki tare da matsawa gefe,sai kuma da ta lura shi ne ta Wan saki murmushi.

" Kai ki na da matsala Juwairaah!Yanzu da matar gidan na nan mai kike tunanin zai faru?Ke akan komai sai an ga gazawar ki?"

Ta yi shiru kawai ta na murmushi ba tare da ta ce komai ba,don ita ba ta san Zainab Win ta fita ba.

"Kawo min abinci yunwa nake ji."

Ya faWa tare da saka hannun shi a daidai gurin dimple Winta ya fita.

Bin sa da kallo ta yi har ya Sacewa ganinta ta yi ajiyar zuciya sannan ta shirya masa abinci.

Bayan ta ije masa abinci ya na zaune da remote a hannunsa ya ce ba tare da ya yi duba gareta ba."Amaryar wucin gadi zo mu yi hira tunda matar so ba ta nan,na lura kamar kina da ciwon rashin magana."

Sai ta tsaya ta na kallon shi da ya yi fuska kamar ba shi ya yi maganar ba.
" Ki zauna mana kika yi min tsaye haba sai kace wata soja."

Namma zama ta yi ba ta ce masa ala ba don ta lura so yake ta tanka.
A.m da ya kasa controling Win kan sa ya matsa kuda da ita ya na mata wasu irin abubuwa.

" Don Allah ina roon ka bu Waya.".
Ta ce yayin da idanunta suka fara zubar hawaye tsayawa ya yi ya na kallonta zuwa can ya nisa ya ce da ita."Ina jin ki Juwairaah."

A hankali ta yi oarin saita muryar ta ta fara magana cikin sanyi.
"Ka ce kar na saka soyayyar ka a zuciyata ni ma ina roon ka da ka dai na oarin kusanta kan ka da ni mu tsaya daga iya sharaWinmu,saboda ina tsoron kar zuciyata ta kamu da sonka duk da na san kai Win ba sa'ar soyayya da ni ba ne,kaddara ta haWa mu ina jin tsoron ranar da zan tsinci kai na cikin soyayyar ka don na san ka yi min nisa na har abada,amma soyayya ba arya ba ne kuma zuciya ba ta da ashi,A.m babu wata mace da za ta yi tozali da kai ba tare da ta faWa cikin kogin son ka ba.

Jikinsa ya yi sanyi matua ganin maganar da take yi daga cikin zuciyarta ta fito.

"Juwairaah kin taSa ganin an yi zaman aure ba tare da haka ba?Duk auren da kika ga ya ginu to hakan ya gina shi.Bani da nufin na cutar dake ki yadda da ni ki yi oarin yaar zuciyarki daga son jefa ki cikin wahala da take son ta yi,kafin na aureki sai da muka yi sharaWi babu so a cikin tsarinmu don ba zan taSa zama dake na har abada ba ,amatsayin matata.Kuma karki manta uban maudan kuWi na sa na auro ki".

Ya numfasa ya na kallonta ganin kukan da take yi hannunsa ya saka tare da tarar hawayen da yake zuba kamar an buWe famfo.

" Ki adana sauran hawayen ki a kwai ranar da zaki buace su kar fa su are,na tabbata ranar da kika haifa min baby in na baki abin da na yi ninya Juwairiya zaki nemi hawayen ki ki rasa bayan kin arar da su akan banza,don ni banga abin kuka a nan ba.Ki tuna mahaifiyarki na cikin kwanciyar hankali da jin daWi shin hakan bai saka ki saka ni a cikin farin ciki ba?"

Ya tambaye ta idanunsa a kanta hawaye suka ci gaba da zuba ganin tai magana sai sai ya mie ya fice daga gidan.

"Humh ba na tunanin a kwai abin da za ka ba ni na yi farin ciki fiye da ka sani a cikin zuciyarka.Am ka i ka gane abu ne na zuciya Allah ya jarabce ni da sonka tun kafin ka bijiro da manufar ka a kaina,na yi burin kar mu haWu tun ranar da na yi tozali da kai a kundin rayuwata."

Kuka take kamar wata zararriya ta na maganganu sosai daga baya miewa ta yi,bayan ta fahimci ya fice daga gidan ta ci gaba da aikinta.

A haka rayuwa take wucewa A.m ya na more amaryar wucin gadi duk da ya osa su rabu,amma ya na girmama lamarin Juwairiya a zuciyar sa.

Tun ta na Wari-Wari da shi har ta saki sosai da shi domin ya bada duk wata ofa da zai saka ta saba da shi,har ta kai ga A.m ya na waya da Juwairiya a Soye su sha hira ya na tambayarta ko ya jefa wallon a raga.
Duk sadda ya yi mata wannan maganar hankalinta ya kan tashi matua ita gani take irin abubuwan da yake mata son ta yake.

Juwairiya ta saba da A.m ta na jin sa a ran sa kullum sai sun haWu da juna ranar da Zainab take gida kuwa,dole sai ya kira ta a waya sun yi hira wannan ya ara saka ma Juwairiya son shi na mutuwa ta na jin duk ranar da ya rabu da ita mutuwa za ta yi.

Amma idan Zainab ta na nan ko kallon Juwairiya ba ya yi,har yau in zai yi maganar ta ko Zainab ta yi mishi nuna yake bai rie sunan ta ba,sai dai ya ce wancan ko wa ta ke da suna.
Tun Zainab na mata orafin ta rina cire hijabinta har ta gaji,ta dai na don ta fuskanci ko mai za ta yi mata ba za ta dai na ba,kuma ina ruwanta tun da ta fahimci Juwairiya a kwai tsafta da kula da kai.

Juwairiya ta goge ta waye ta ara wani irin kyau jikinta ya ciko ko ina,ita kanta mamakin yadda ta goge take yi,sai dai ko hoda ba ta saka wa bayan kwalli duk da Zainab ba ta hana ta ba.

To ina ma take da lokacin kanta daga aiki sai chert,don in dai ba ta gurin aiki ta na rie da wayarta,ko magana take hankalinta na kan wayarta.
Duk lokacin da Juwairiya ta samu tsarki sai ta samu lemun tsami da ruwan gishiri ta sha,ita burinta ko a matsayin mai aiki za ta zauna in dai ya na nuna mata irin wannan soyayyar za ta rayu da shi na har abada.

Kimanin tsawon wata bakwai A.m ya na jiran ya ji ta ce mishi ta na da ciki,amma shiru kake ji malam ya ci shirwa,har ya fara tunanin to ko shi ma baya haihuwa.

Hankalin sa ya fara tashi sosai gashi A.m har ya kasa daurewa ya tambayi Juwairiya shi fa ya osa,lallaSasa take yi ta na faWa mishi Allah ne bai kawo ba,amma a ranta ta san abin da take yi.

Ya na zaune a falo zuciyar sa na tafarfasa da ya tabbatar Zainab ta ara tafiya ba tare da ta sanar mishi ba,ya ji a ran shi tunna ya na da Juwairiya zai ci gaba da hauri har zuwa sadda za su rabu,amma duk da hakan dole ta Wauki mataki saboda ya kamata ta sanar mishi ko da bai amince ba,ba wai ta kashe wayarta tafi ba.


Wayar A.k ya katse masa tunanin da yake yi sai dai bai Wauka ba wayar ta katse ya bi,amma ba network sai a ka ce wayar a kashe.

Wani irin bugu ya ji ana yi mishi wanda ya tada hankalin sa da sauri ya fita don shi a zaton shi Sarayi ne suke so su shigo mishi,duk da ce wa arfe huWu da rabi ne na yamma.

Ya na isa get Win maigadi ya sheo da gudu ya na faWin." Ka yi hauri ina bayi na zaga.Wannan wa ne mahaukaci ne yake wanwasa ofa Allah ya sa lafiya."

A.m bai kalle

Please Login or Register in order to submit comment