Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ

Telegram : https://t.me/NovelsHQ

[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"To sun ce ba sa jin barci ki rabu da su."

Baffa ya shigar musu shi yasa ta ƙyale su, ta tafi ɗakin Baffa ta tafi da ruwan gora saboda yana shan ruwa da daddare.
Ta bar su a falonta suna dasa sabuwar hira har da Baffa shima komawa ya yi ya zauna.

Ammah ta sake dawowa ta gansu dirshan suna hira.

"Yau wai meke damun ku? Baffa mu je ka kwanta ka ƙyale yara nan."

Baffa ya amsa da to, Saddam ya kalli Abdurahim suka kalli juna suna kunshe dariya.

"Munafukai."

Ammah ta faɗa tana hararansu.
Suka kwashe da dariya Baffa na mirmishi.

"Ammah Baffa fa ba ya jin barci."

"Ya faɗa maka?

"To ga Baffan nan a tambaye shi? Baffa wai kana jin barci?

Saddam ya juya yana tambayan Baffa.

"To ko ban ji Saddam tunda Jamila ta ce ina jin barci ai haka ne gaskiyan magana."

"Baffa kai fa mijin ta ce ne na lura."

In ji Abdulrahim yana dariya.

"A'a ba mijin ta ce ba ne shi, mijin kan ta ce ne."

Saddam ya gyara masa, Ammah ta wurgesu da cussion ɗin kujera tana cewa su fitar mata a cikin ɗaki su kuma suna ta dariya.

"Ammah gaskiya fa muka faɗa. Duk abin da kika ce Baffa ba ya iya miki gaddama."

"Ku kuma kuna jin haushi.?

"Aa kawai dai shima Baffa ya dinga nuna ƙwanjinsa."

Baffa na ta dariya ita kanta Ammah dariyan take yi.
Saddam da Abdulrahim shaƙiyan yara ne haka suke tasa su da zolaya.

Baffa ne ke faɗa musu, su yi fatan samun mace irin Ammah dukkansu mijin kan ta ce za su zama.

"Tana da kyakyawan hali misalin mace ta gari ce Jamila."

"Awwww.."

Suka haɗa baki wajen faɗa ganin Ammah na ta mirmirshi jin Baffa na yabon ta.

"Su Baffa an iya kalamai."

Saddam ya faɗa yana tsintsira dariya.

"Ammah da kalaman nan ne Baffa ya sace zuciyarki?

Ta wurga masa harara tana mirmishi.
Baffa ne ba su labarin ai haɗa su aka yi kuma suna haɗuwa ganin farko suka aminta da juna.

"Love at first sight kenan."

Abdurrahim ya faɗa yana dariya.

"Ammah ta ga farin bafillace ina za ta yi sakaci."

"A'a itama ai fara ce, ni ne na yi sa'a."

Baffa kenan yana ta wasa Ammah kunya ta ji ta bar musu falon su kuma su Saddam suna ta dariya.
Da gaske yau hira suke ji domin har ɗaya saura na dare suna falon Ammah suna hira.
Saddam kawai ya sako wata maganar wai yanzu sai Baban Hanan ya zo ya ce Hanan ɗiyar shi ce?

"Haba ai da kunya. Shi da ya ce baya son cikin ?

"Irin su ba su da kunya ina nan da kai zai iya dawowa ya ce ina abin da Auta ta haifa."

"Ai ko da ya ci ubansa wallahi."

Abdulrahim ya faɗa da iya gaskiyan shi.
Baffa na gefe bai ce komai ba cigaba da magangansu suka yi Saddam na faɗin shi jiran ranar kawai yake yi ranar da Habib zai sako kafarsa a gidan nan sai ya tara matasa anguwa sun yi masa jina jina.
Abdulrahim ya ce daga karshe mu haɗasa da jami'an tsaro.

Ammah ta fito lokacin da suke auna irin iziyar da za su yi ma Habib duk ranar da tautsayi ya kawo shi gidan nan.

"Ni na manta da shi, koma yana ina yanzu na tabbata Auta ta fi shi samun rayuwa mai inganci. Ai ba za ka yi zalunci ka sha ba sai Ubangiji ya yi sakkayya tun a duniya."

"Ai Ammah yana can ma yana girban abin da ya shuƙa. Irin addu'o'in bala'in da na dinga auna ma wannan mutumin ai in dai Allah ya karɓi addu'o'i na to yana cikin iftila'i."

Ammah ta ce har Umra ta je ta yi addu'an Ubangiji ya yi ma Auta sakayya kuma da ikon Allah yana can yana gani.

"Kuma wai ko danginsa ba su sake neman ku ba Ammah.?

Abdulrahim ya tambaya.
Ammah tace ba wanda ya sake neman su, ai in shi Habib ya ce ba ya son cikin bai kamata su su juya baya ba tunda sun san jinin su ne.

Sai a lokacin Baffa ya yi magana da cewa shi ya yanke alaqar daga farko.

"A baya ɓacin rai da ganin halin da Auta ta shiga ya sa na ce na haramta ma Habibu da danginsa abin da Auta za ta haifa. Amma daga baya na fahimci na yi kuskure, Hannatu mace ce duk iya abin da za mu yi mata tana bukatar Uba da danginsa."

Kallon Baffa kawai suke yi mamaki ya hana su magana.

"Ko ba a ba shi y'arsa ba watarana ina da rai ko ba ni rai in har Habibu da danginsu suka waiwayi jininsu ku karɓesu ku kuma ba su dama"

"Dama kuma Baffa? Wani irin dama kuma?

Ammah ta tambaya cikin mamaki.
Received at 09:09Reactions: ❤ 9, 👍 1, 😱 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Damar ya nemi afuwarku sannan ku ba shi dama ya haɗu da jininsa."


"Cewa ya yi ya gane ya yi kuskure Baffa? Kuma cikin da ya ce ba ya so ne za ka ce a ba shi dama ya ga jininsa?

"Ban sani ba amma ina ji a jikina lokacin ya kusa. Ko da ina rai ko ba ni da rai wasiyya ce Jamila. Hannatu mace ce wata rana za ta yi aure tana bukatar mahaifi da dangin shi in har Habib ya gane kuskuren shi ku karɓe shi ku yafe masa muma mutane ne muna yin laifi Ubangiji na yafe mana to babu laifi in ya yi laifi kuma ya gane kuskuren shi ya tuba."

Da alamun maganganun Baffa sun sanyaya musu jiki har da Ammah ita kanta

"Baffa ni ban gane maganganun ka ba, ka haɗu da Habibun ne ko ya kira ka a waya ne?

"A'a ban sake ganin shi ba kuma da ya kira ni da na faɗa miki. Kawai tunasarwa ne domin na san ko a jima ko a daɗe Habibu zai dawo ya nemi Ummu Salma tare da bin kadin cikinta jikinta. Jininsa ne zai yi nadama ko kuma alhaki zai bibiye shi, alhakin ne kuma zai kawo shi nan kusa."

"In har ya zo kar ku yi masa rashin ɗa'a. Ku yi masa kara sannan ku ba shi dama. Muma damar Ubangiji ke ba mu da babu wata damar da duk rayuwarmu ba ta kawo yau cikin farinciki ba."

Shuru suka yi kowa na saƙa maganganun Baffa a zuciyarsa

Ammah dai cewa ta yi Baffa na jin barci ya zo su kwanta sai ya miƙe yana faɗin kanshi ke ɗan ciwo ta duba masa panadol.
Saddam da Abdulrahim suka miƙe suka fita tare da Baffa suna yi masa sallama.

"Allah ya tashe mu lafiya."

Suka amsa da Amin suka tafi bangaren su

Baffa kuma ya shiga ɗakinsa tiolet ya shiga ya kama ruwa ya zo ya sauya kaya zuwa jallabiya ya kwanta Ammah ta shigo da maganin ta tashe shi ta bashi ya sha ya kora da ruwa ya koma ya kwanta.

Ammah ta yi zuru tana kallon shi domin a cikin lokaci ƙalilan sai ta ga duk Baffa ya sauya ya yi wani sanyi da shi.
Da ta tambaye shi sai ya ce ciwon kan ne ya ɗan dame shi.

"Kuma shi ne tun ɗazu ba ka yi magana ba? Ko rashin barci ne Baffa?

"A'a yanzu nan ne ciwon kan ya fara amma na san zuwa safe zai bari.'

Ta yi masa Allah ya sauwaƙe
Ta rufa masa bargo a kafafunsa sannan ta yi shirin barci itama ta kwanta bayan ta je ta rage hasken falonta ta rufe falon.
Kofar turakan Baffan ma sakayawa ta yi, saboda ana sanyi ba ta kunna fanka ba.

Itama ta gaji shi yasa tana kwanciya sai barci.
Can cikin dare ta ji Baffa na kiran sunanta.

Ta tashi cikin barci ta ji yana cewa ta kunna masa fanka zafi yake ji.
Ta yaye bargon ta sauko daga kan gadon ta kunna hasken ɗakin

Sai ta ga Baffa na ta zufa abin mamaki sanyi fa ake yi.
Ba ta yi musu ba ta kunna masa fankar tana duba agogon bangon dake ɗakin Baffa uku saura na dare.
Gefen Baffa ta zauna tana miƙa hannu tana share masa gumin da ya taru a saman goshinsa.

"Baffa ciwon kan ne?

Sai ya ɗan buɗe idanuwansa yana kallonta.

"Na ga kana ta gumi ne! Ko akwai zazzaɓi a jikin ka ne?

Ta faɗa lokaci ɗaya tana dafa goshinsa.
Sai ta ji jikinsa ya ɗan yi ɗumi.

"Baffa ina jin zazzabi ne zai kama ka jikin ka ya yi ɗumi."

"Ba komai ki koma ki kwanta."

Baffa ya faɗa a sanyaye muryansa ta yi wani iri.
Ammah ta ji kawai gabanta na faɗuwa ko Baffa na ciwo bai saba yi mata magana da wannan muryan ba.
Sai hankalinta ya tashi ta fara cewa ko ta ƙaro masa maganin ne ya yi mirmishi ya ce ciwo kan ya sauka kawai zafi ne yake ji ta koma ta kwanta.
Ba ta yarda ba sai da ya rike hannunta duka biyu gam a cikin hannayensa.

"Ki koma ki kwanta na ji sauƙi zafi ne kawai na ke ji kuma da kika kunna fankar ba ki ga na daina gumin ba."

Ba ta kwanta ba zama ta yi da shi tana riƙe da hannayensa.
Abin da ya ƙara tsorata ta ganin ga iskar fanka amma shi yana ta gumi ita ke share masa gumin ma da hannunta.

Zuwa can kuma sai ya samu barci sai da ta ga yana mumfashi a hankali sannan ta koma ta kwanta a zuciyarta tana faɗin da sassafe za ta kira Baba ya zo su je asibiti da Baffa ba ta taɓa ganin ya yi irin haka ba.

Bini bini ta juya tana kallon Baffa tana taba shi ta ga dai yana ta barcinsa.
Itama barcin ne ɓarawo ya sake tafiya da ita.
Received at 09:09Reactions: ❤ 13, 👎 1, 🥰 1, 🤔 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai dai kamar a cikin barcin ta yi mafarkin Baffa na kiran sunanta ta farka a firgice.
Sai tarin shi ta ji daman ba ta kashe hasken ɗakin ba ta yi kanshi cikin firgicewa

Tari kawai Baffa yake yi har gadon da suke kwance yana jijjiga.
Ɗago shi ta yi ya jingina da filo tana shafa masa bayansa lokaci ɗaya tana yi masa sannu.

"Sannu Baffa me ya faru ne?

"Tari ne kawai ya sarƙe ni."

Ya amsa mata cikin rawam murya. Har a lokacin gumi yake yi ta sauko daga kan gadon ta fita tsakar gida zuwa kitchen ta kunna filitar kitchen ɗin ta dauko kofi ko da ta dawo tarin ya dawo ma Baffa jikinta ba in da ba ya rawa ta durƙusa ta tsiyaya masa ruwan a kofi ta zauna a gefen shi ta ɗago kan shi tana ba shi ruwa jikinta ya saki ne lokacin da ta ga ruwan da take ba ma Baffa yana dawowa ta gefen bakin shi sannsn tarin bai tsaya ba.

Har yana hawaye wasu suna zuba wasu na sake tunkuɗowa.
Ammah ta ruɗe hankali tashe take kiran sunan Baffa.
Amma ba ya iya amsawa tarin ya sarƙeshi kamar wanda ya ci wani abu ya sarƙe shi.

Idanuwansa sun yi jajir gwanin ban tsausayi.
Amma ya miƙe tana faɗin bari ta je ta taso su Saddam su zo su tafi asibiti amma sai Baffa ya riƙo hannunta ta dawo ta zauna tana yi masa sannu.

"Ka bari na je na taso su, ba ka da lafiya Baffa mu je asibitin tarin nan naka ya yi yawa."

Bai saki hannun na ta ba, kan shi ya fara girgiza mata tarin ya ɗan lafa masa.

"Ki yi haƙuri Jamila."

Baffa ya faɗa cikin dashewar murya.
Hawaye na zubo masa ta gefe da gefen kunnuwansa.

Kamar an kwarara ma Ammah ruwan sanyi haka ta ji, ta kasa magana kawai ta kafe Baffa da idanuwana.

"Ki yi haƙuri lokaci ya yi da za mu yi sallama da juna haka nan."

Ya faɗa tarin na sake kama shi, Ammah ta durƙushe a ƙasa a gaban shi zuciyanta ke bugawa hannunta da jikinta babu in da ba ya rawa

"Baffa me kake faɗa haka? Ina kuma za ka je?

Bakinta na sarkewa saboda tashin hankali.
Kuma ya riƙe hannunta gam yaƙi sakinta.
Cewa ya yi ta zo ta zauna dole ta mije ta zauna a gefen gadon ya janyo jikinsa da ya saki ya ɗora kan shi a samam cinyarta suna masu kallon juna.

"Ki yi haƙuri Jamila lokaci ya yi."

Sai ga hawaye, yaushe ne rana na ƙarshe da ta ga kukan Baffa? Duk da yana da raunin zuciya amma ba kuka irin wannan ba.

Ta san mutuwa tunda iyayenta sun rasu amma ba'a taɓa mata mutuwa ana ta zuru'an ba. Yadda Baffa ke yi kawai ya sa jikin Ammah ya saki gabaɗaya.
Baffa ya gama kwanakin da aka diɓo a duniya yau ko tana so ko ba ta so lokaci ya yi da Baffa zai tafi ya barta.

Yadda Baffa ke yi lokaci ne ya yi watakila ma mala'ikun ɗaukan rai suna cikin ɗakin. Tarin da yake yi na kiran ajali ne. Ba ta san a ina ta samun ƙwarin gwiwa ba amma jin bakinta kawai ta yi, tana maimaita ma Baffa kalmar shahada kuma sau ɗaya ta maimaita ya kama yana yi.

Baffa ya cika idanuwansa kamar suna kallonta amma ba ita yake kallo ba idanuwansa sun yi sama ya rufe kalmar shi ta ƙarshe da la'ila ha illallahu muhammdun rasulillah.'
A man cinyar Amma ya cika har a lokacin akwai danshi hawayensa a gefe da gefen kunnuwansa.

Ammah ta kasa gane a wani yanayi take ciki. Ta ɗago idanuwanta tana kallon agogo Uku da mintina arba'in na daren ranar Litini Baffa ya koma ga Allah.

Hannunta da ta ji ya sandare ta miƙa ta shafe idanuwan Baffa. Sannan ta yi jarumtar sauke kan shi a saman gado ita kuma ta sauko ƙasa ta durƙusa a gaban shi tana kallon shi.

Me take ji? Wani abu ne ƙullutu mai girma ya yi mata tsaye cak a wajen zuciyarta shi bai wuce ba shi kuma bai faɗa mata ba.

Baffa ne ya tafi ya barta? Ta kasa gasgasta abin da ya faru cikin mintina. Ga shi kwance kamar mai barci kamar ta kira shi ya amsa.
Wai ba ɗazu nan nan ba daɗewa suka gama hira tare da su Saddam ba lafiyan shi ƙalau fa, cewa kawai ya yi kan shi na ciwo ashe na ajali ne.

Hawaye ko kaɗan ba su kawo mata ba zuciyarta ta bushe, amma ta yi mata nauyi jikinta ya saki gabaɗaya.
Received at 09:09Reactions: ❤ 12, 😭 6, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta miƙe tana jin kamar ba ita ba. Tana jin ta kamar falle takarda saboda yadda take jin kanta. Gyara ma Baffa kwanciya ta yi akwai zanin ta a gefe ta jawo shi ta yaga shi da ƙarfin tsiya da kanta ta duka ta haɗa babban yatsun kafafun Baffa ta kulle su kar kafin safe su sandare. Sannan ta fita ta koma ɗakinta ta buɗe wardrope ta ɗau zaninta sabo ko taɓa sa shi ba ta yi ba ta zo ta rufe Baffa ruf daga kafafunsa har kansa.

Sannan ta shiga toilet ta ɗauro akwala ta zo ta shimfiɗa darduma ta fara sallla, ba ta san ko raka'a nawa ta yi ba ita kawai salla take yi da ta sallame ta sake miƙewa ga Baffa kwance a kan gado a matsayin gawa


Ta kasa zama ko na minti ɗaya ballatana ta yi wani tunani ji take yi kamar za ta haukace kamar ƙarya ne sai dai ba ƙarya ba ne ga Baffa nan kwance babu rai a tare da shi.

Ta yi salla har sai da kafafunta suka ga ji, har sai da ta ji an fara kiran sallar asuba a wasu masallatan da suke kusa da su. Sannan ta dakata ta zauna tana jan casbaha ta ƙura ma gawar Baffa idanuwanta amma ta kasa kuka ta rasa ma abin da take ji amma wani abu mai nauyi yana yi mata ɗaci ya tokare mata a maƙoshi ya kasa wucewa.
Tana nan zaune har lokacin salla ya yi ba ta iya tashi ba Hasbunallahi wani'imal wakeel kawai take maimaitawa bakinta na motsi kamar ba ta cikin hayyacinta

Daga tsakar gida ta ji muryan Saddam na kiran sunanta. Ƙofar dakin Baffa a buɗe take sannan akwai hasken wuta zumbur ta miƙe ba ta son ya shigo ya fahimci halin da ake ciki yanzu sai ta yi zaraf ta fito suka haɗu a tsakar gida.

"Ina kwana Ammah"

Bai fahimci yanayin ta ba ganin ta da hijabi bai kawo masa wani tunani ba.

"Ina Baffa? Har wasu masalatan fa sun tayar da salla?

"Ku je kawai, yau a gida Baffa zai yi salla ba ya jin daɗin jikinsa."

Ya ce Subhanallah me ke damun shi ta ce zazzaɓi ne.
Sai ya wuce yana faɗin to bari su je masallaci su dawo sai su shigo su duba shi ta amsa masa, bayan ficewarsa ta daɗe a tsaye

Baffa ke fara tashi, ya tashe ta ya yi alwala sannan ya fita ya tayar da su Saddam ya tada su domin su tafi masallaci.
Allahu akbar ga shi yau sun sun tashi amma Baffa bai tashi ba. Ɗakin ta koma ta tayar da salla.
Sai da ta idar da salla sannan ta zo gaban gawan Baffa ta buɗe shi tana kallon shi kamar ta kira shi ya amsa.

"Allah ya jiƙan ka da rahama Baffa. Allah ya haɗa ka da mala'ikun rahama Allah ya sa su yi murna da zuwanka. Ubangiji ya karɓi baƙunci ka."

Ta kasa ƙarisawa tana jin wani irin abu na ta so mata.

"Allah ya haɗamu a darussalam."
Sannan ta miƙe ta ja zanin ta sake rufe shi.
Fita ta yi zuwa falonta ta ɗauki wayarta sannan ta nemi gefen gado ta zauna ta kira wayar Abdulrahaman

Lokacin baya gida ya je masallaci Ummu Sulaim kuma ba ta ji kiran ba wayar tana chaji ne kuma a silent take. Ganin bai ɗaga kiran ba sai ta kira Abdullahi

Shi ta same shi, domin ya dawo daga masallaci kenan ya kwanta wayar ma tana hannun shi ne sai ga kiran Ammah gaban shi ya faɗi kiran waya wajen shidda na safe Allah ya sa lafiya.

Sai ya ɗaga wayar da sallama amma kirjinsa na duka.

"Baba."

Ta kira shi kamar yadda ta saba kiran shi.
Ya ji wani kaifi a muryanta da zai ce bai taɓa jin Amma ta kira shi da wannan muryan ba.

"Na'am Ammah lafiya kuwa?

"Lafiya ƙalau ka taho gida yanzu."

"Amma me ya faru?

Ya faɗa yana saukowa daga kan gado cikin ruɗewa jikinsa ya ba shi ba lafiya.

"Na kira Abdulrahaman bai ɗauka ba, ka kira shi, shima ya taho gida yanzu."
Ammah ta faɗa tana ƙokarin daidaita yanayinta.

"Ammah wani abu ne ya faru?

"Ku zo dai. Ku zo gida"

Da sauri ta kashe wayar tana numfarfashi lokaci ɗaya ta dafe kanta tana kiran sunan Allah.

Dai dai lokacin su Saddam suka dawo daga masallaci, hango Ammah suka yi a falonta ya sa suka shiga dakin suna gaisheta

Ta mike da sauri ba ta son su haɗa idanuwana.

"Ammah ya jikin Baffan? Mu je mu ga jikinsa na shi ko kuma kawai mu je asibiti ."

Abdulrahim ya faɗa Saddam ya ce shima dai haka ya gani.

"Yanzu haka maleria ce."

"Ba ta wuce ita ɗin ce."
Received
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ammah ta yi gaba suka bi bayanta har zuwa cikin ɗakin Baffa.
Ta tsaya a gaban gawan Baffa su kuma suna bayanta tunda suka shigo ɗakin kamar an zare musu lakkan jiki ganin Baffa kwance rufe da zani ya sa suka fara kallon juna.

"Ammah zazzaɓin ne ya yi zafi haka?

Saddam ya faɗa yana fatan Ammah ta amsa da cewa zazzaɓin ne ya yi zafi Baffa ya rufa har saman kanshi amma abin da bai gane ba akwai bargo me ya sa Baffa zai rufa da zani?

Abdulrahim ko ƙura ma Baffa idanuwana ya yi Baffa ba ya motsi, kirjinsa ya doka a rikice ya kalli Ammah.

"Ammah Baf..f"

Sai ya kasa ƙarisawa, domin da gudu Saddam ya durƙusa ya yaye zanin Baffa ga shi nan kwance idanuwansa a rufe daga sama har ƙasa suka sauke ganinsu a ƙafafunsa in da Ammah ta haɗa ta ɗaure.

A tare kirjinsu ya doka, Abdulrahim shima ya yi ƙasa ya durkushe yana ganin duruduru. Ammah suka kalla da ta koma ta jingina da bango tana maimaita salati a cikin zuciyarta.

"Baffa ya tafi ya bar mu, jiya ƙarfe uku na dare Ubangiji ya karɓi Baffa."

Ammah ta sanar da su cikin wani irin murya.
Saddam ya faɗa jikin Baffa kamar ba namjji ba ya wage murya yana kuka yana kiran sunan Baffa

Shi ko Abdulrahim bakin shi ya danne da hannu bibbiyu kuka na son ƙwace masa da rarrafe ya fita daga ɗakin ya koma ƙofar ɗakin Baffa yana hawaye, hawaye masu ɗaci da zafi.

Jiya fa har ɗaya saura na dare suna tare da Baffa suna hira ashe ciwon kan da ya ce yana ji na ajali ne.

"Innalillahi wa'inna inna ilaihirraju'un."

Haka Abdulrahim ya ke maimaita yana kuka mara sauti hawaye na zuba wasu na koran wasu
Saddam daga cikin ɗakin Baffa ana jiyo kukansa.

"Baffa "

Haka yake kiran sunan shi yana kuka har da shessheƙa.
Ammah ce ta yi ƙarfin halin daka masa tsawa.

"Meye haka? Kai da za ka yi masa addu'a shi ne za ka tasa shi kana yi masa kukan wofi?

"In kuka zaka yi, ka fita waje."

Ta faɗa tana buɗe murya.
Tashi ya yi da gudu ya fito waje, ya kusa ture Abdulrahim dake zaune dirshan a ƙofar ɗakin Baffa yana kuka.
A tsakar gida shima ya baje yana kuka da duka muryansa.

Hamma Abdullahi ya fara isowa gidan.
Sun yi waya da Abdulrahim ya faɗa masa Ammah ta ce su zo gida shima ya ce ya ga kiranta hankalinshi tashe ya ce wani abu mara daɗi na faruwa duka sun ji a jikinsu.

A waje Abdullahi ya yi parking ɗin motarsa
Da sauri ya shigo gidan sai dai kukan da ya ji ne ya sa ya faɗo gidan da gudu jallabiyan jikinsa ma a bai bai ya saka ta saboda sauri.

Ganin Saddam baje a tsakar gida yana kuka mai sauti ga Abdulrahim a ƙofar ɗakin Baffa yana hawaye tare da salati.

"Me ya faru?

Ya tambaya muryansa a buɗe.
Ganin sa ya sa Saddam ya sake rushewa dakuka.

"Hamma Baffa."

Ya faɗa shessheka na hanasa magana.

Abdullahi ya zaro idanuwana.

"Me ya faru da Baffan?

Zuciyarsa ne ta nemi tsayawa cak lokacin da Saddam cikin kuka yake faɗa masa Babu Baffa, Baffa ya tafi ya barsu.
Abdullahi ya yu wurgi da takalmin kafarsa ya rumtuma ɗakin Baffa yana fatan ya ga ba gaskiya ba ne yana fatan ya ga Baffa zaune.
Sai dai abin da Saddam ya faɗa masa gaskiya ne.
Ya iske Baffa na kwance babu rai a jikinsa ga Ammah zaune a gefe tana jan carbi ko bai tambaya ba yasan yau sun wayi gari cikin wata jarabawa.

Allahu akbar, duk cikin su yafi shaƙuwa da Baffa saboda tare suke kasuwanci daga shi sai Saddam da Abdulrahim tunda kodayaushe suna gida tare da shi.

Ya durƙushe a gaban Baffa ya dafe kanshi hawaye suna shatata masa.

A jere yake sauke numfashi na kukan zucci.

"Ku daina masa kuka Baba, Baffa addu'an mu yake buƙata a yanzu."

Ammah ta faɗa muryanta ta karye amma ta kasa kuka.
Abdullahi ya juya yana hawaye yana kallon Ammah.

"Ammah."

Ya kirata muryansa na rawa bakinsa na rawa duk a lokaci ɗaya.

"Baffa ne ya tafi ya bar mu?

Ya faɗa kuka na taso mata, ya kwantar da kanshi a kirjin Baffa yana rera kukan zucci yana sharɓe majina.

"Baffa Allah ya gafarta maka."

"Ubangiji ya sadaka da rahamarsa."

A lokacin Abdulrahaman ya shigo gidan shima ganin su Saddam a tsakar gida cikin wani yanayi, ga shi suna ta kuka kamar ba maza ba.
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Bai tsaya tambaya ba ya faɗa dakin Baffa shi ne kaɗai bai gani ba jikinsa ya ba shi wani abu ne ya faru da Baffa amma bai taɓa kawo ma Baffa mutuwa ba.

Ko bai tambaya ba, ya san amsar. Ga Abdullahi durƙushe a gaban Baffa yana kuka.
Ammah na gefe da Hijabi da casbaha ta sunkuyar da kanta.

Tabbas Baffa ya amsa kiran mahallicinsa ashe zaman hiran da suka yi jiya na bakwana ne Baffa lokaci ya yi. Shima gefen Abdullahi ya duka shima yana kallon Baffa amma shi bai yi kuka ba zuciya ce ke suya kawai.

Ya fara yi masa addu'a daga karshe ya ce" Allah ya gafarta maka Baffa"

Shi ya janyo zanin ya sake rufe shi sannan ya tashi ya zo gaban Ammah ya duka yana kallonta.

"Ammah ya haƙurin mu?

"Mun gode ma Allah Abdulrrahaman."

"Allah ya jiƙan Baffa, Ubangiji ya ba mu haƙurin rashin sa."

Ta amsa da Amin kallon ta

Please Login or Register in order to submit comment