Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai Hamma Kabiru da Hamma Abdulrahaman suka haɗa hannuwa suka zura shi a cikin kabarin shi.
Allahu Akbar bawa ba a bakin komai yake ba, duk abin da ka mallaka in ka mutu daga kai sai farin likkafani za a zuraka a cikin ƙasa a toshe ko wata ƙafa. Ya illahi Ubangiji ka datar damu duniya da lahira.

Wajen toshe kabarin da kasa ne har da Mai martaba ya saka hannu, suna ji suna gani aka rufe Baffa ruf sannan duk in da aka hango iska sai an toshe shi bayan an gama jera itace an rufe ko'ina sannan aka rufe shi da ƙasa. Kafin a watse a maƙabarta liman sai da ya yi nasiha ya jawo hankalin mutane a game da mutuwa.

"Jama'a mu ji tsoron Allah a dukkan ayyukanmu mu dinga tunawa da cewa wata rana za mu mutu, mutuwa ba ta ƙwanƙwansa ƙofa ba ta neman izini kada mu shagala mu yi tunanin cewa ai muna da sauran lokaci ko mu yi tunanin tsoffafi ke mutuwa ni ina da ƙaruciya ba yanzu zan mutu ba ko mu dinga tunanin ina aikata zunubai amma kafin na mutu zan tuba to ya kamata mu farka mutuwa ba ta zaɓa da lokacin ka ya ƙare a duniya za ka tafi ko kana so ko ba ka so. Tana ɗaukan jariri ta bar uwa tana ɗaukan uwa ta bar jariri tana ɗaukan uba ta bar ɗa, tana ɗaukan uwa ta bar uba, tana ɗaukan tsoffi ta bar yara matasa sannan tana ɗaukan matasa ta bar tsoffin abin da zamu gane shi ne mutuwa tana tare damu aduk in da muke, wataƙila a cikin mu ɗin nan akwai wanda ba zai wayi gari ba, wani ma ba zai kai anjuma ba, duk wannan na Allah ne abin buƙata kawai mu dinga tuna mutuwa mu kuma ribanci kyakyawan ayyuka, ku duba wannan bawan Allah jiya har sallar isha'i tare da shi muka yi a masallaci yau da asuba da ɗan wajensa ya zo yana faɗa mini rasuwarsa kamar zan ce me ya sa me shi? Sai na tuna ajali ko ba ciwon in ya yi kira sai an tafi. Ƴaƴansa sun ba ni tabbacin har wajen sha biyun dare suna tare da shi suna hira sun koma gidajensu sun kwanta da asuba aka kira su, suna zuwa gida ba su same shi da rai ba. Abin lura anan jiya lafiyan shi lau a cikin iyalan shi bai san yau ba zai wayi gari ba Ajali ya yi kira Ubangiji ya yi ikonsa. Ina mai baku tabbacin Alhaji Hadi mutumin kirki ne salla akan lokaci ba ya wucesa tare da iyalansa. Sannan yana da daraja mutane da sannin haƙƙin zaman tare, Ubangiji Allah ya gafarta masa, tashi ta ƙare mu kaɗai ne yanzu muke da kaico, mun dai ga in da ake saka duk wanda ya rasu a cikin ƙasa daga kai sai halin ka, guzirin mu shi ne kyakyawan ayyuka da nisanta kanmu da aikata zunuban da Ubangiji ba ya so. Jama'a mu ji tsoron Allah mutuwa ta zame mana wa'azi."

Kowa a makabarta jikinsa ya yi sanyi.

"Mu tuba da wuri tun kafin lokaci ya kure mana. Ba mu san yaushe ne za mu mutu ba amma tabbas mutuwa tana tare damu, yau in ka raka abokinka watarana wasu ne za su rako ka, yau in ka raka babanka watarana wasu ne za su raka ka, haka rayuwar za ta tafi tun kana zuwa raka wasu kai ma watarana kai ne tun muna jin labarin mutuwar wasu muma watarana tamu mutuwar za a ji. Ubangiji ka sa mu yi kyakyawam ƙarshe."

Aka amsa da Amin jikin kowa a sanyaye
Nan ya ce za a yi addu'a.

Ya yi addu'a sosai daga karshe ya rufe da cewa

" Allah ya jiƙan Alhaji Hadi. Allah ya sada shi da mala'ikun rahama. Ubangiji ya haskaka kabarin shi ka ba shi ikon amsa tambayan kabari ka sanya shi cikin amimcinka. Allah ya yafe masa kurakuransa Allah ya ba mu sa'a gabaɗaya."

Aka sake amsa da Amin Amin gabaɗaya.
Received at 09:59Reactions: ❤ 4, 😭 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Kowa ka gani jiki a sanyaye wasu na kuka wasu na jimami a cikin masu jimanin har da Habib da yake can baya ya sunkuyar da kai har ƙwalla ya yi Ubangiji yana son shi da ya ba shi ikon tuba tun kafin ya mutu.
Ko bai sunkuyar da kai ba, ba ma lalle ba ne ahalin Ummu Salma su gane shi ba saboda wahalan rayuwa sannan a halin da iyalan Baffa ke ciki ba ta kan shi za su bi ba. Yana cikin tawagan mutanen da suka bar maƙabarta iyalan Baffa kaɗai aka bari sai Mai Martaba da wakilan fada dare da sauran dogarai.

Habib ya tafi yana waiwayan Lamiɗo, daga nesa ne kawai sai da ƙwarjininsa ya dake shi. Duka duka sau ɗaya ya taɓa ganin shi
Zahiri  tun kafin auren su da Ummu Salma amma yana ganin shi a hoto in Hamma Kabiru ya saka shi Ummu Salma kan nuna masa.

Duk da ya sauya kuɗi da mulki suna nuna kansu a ganin farko ma in ka yi masa. Ya tafi yana hawaye, hawayen nadama da tausayin kanshi, ruɗin duniya da sheɗan sun ruɗe shi ya rasa Ummu Salma rashi na har abada.

A wajen makabarta ya haɗu da Sani suka gaisa ya yi masa godiya. Domin ya taimakesa da ya kira shi ya faɗa masa rasuwar Baffa ko ba komai ya samu jana'izarsa amma yana cikin jimamin har Baffa ya koma ga Allah bai nemi gafaran shi ba domin ya san cewa tabbas ya kuntata masa bisa ga abubuwan da ya yi ma Ummu Salma.

Yana tafe a hanya yana istigafari da neman yafiyar Ubangiji.

A can maƙabarta kuwa dukkansu suna duƙe a gaban kabarin Baffa da Hamma Jibo ya ɗan saka wani alama na katako a wajen yadda ko da watarana ziyara ya kama su za su iya gane kabarin Baffa. Duk da ana mutuwa sosai a lokacin ma kaburbura wajen biyu aka haƙa a gefen na Baffa.
A rana ba wanda ya san adadin mutane nawa suke mutuwa.

Addu'o'i suke ta yi ma Baffa domin a lokacin da sahun ƙarshe ya ɗaga kafarsa mala'inkun tambaya za su sauka fatan su Allah ya ba shi ikon amsa dukkan tambayoyi.

Hamma Abdullahi ya kasa daina kuka hawayensa suna ɗiga a saman kabarin Baffa shi da Abdulrahim shi ko Saddam jiri ne ya ɗebe shi lokacin da ya miƙe sai da Hamma Abdulrahaman ya kama shi ya ce ya koma gefe tunda ba zai iya daurewa ba.
Hamma Jibo da Hamma Mustpha sun yi jarumta sosai idanuwansu ne dai suka kaɗa suka yi jajir amma ba su yi kuka ba haka ma Hamma Kabiru da Hamma Abdulrrahaman, Lamiɗo ma ba a gane yanayinsa duk sune masu dauriyan.

Baffa Umaru da Baffa Salihu  sun kasa daurewa suma hawayen suke yi haka ma Daddy sai da ya share hawayensa da wani farin hanky Mai martaba kuma ba a gane yanayinsa tunda yana cikin rawaninsa ne Saleem na gefe jikisa duk ya yi sanyi ga sauran yaran su Baffa Umaru maza da suka taho daga Mubi wasu na hawaye wasu na sharɓan kuka domin Baffa na kowa ne mai barkwanci ga zumunci da son ƴan'uwa.

Sai da za su bar maƙabarta sannan Hamma Jibo ya juya ya kalli kabarin Baffa sannan hawaye suka kawo masa bai share su ba ya barsu suna ta faman zuba kamar famfo.

"Allah ya jiƙan ka Baffa."

"Allah ya gafarta maka Hadi. Allah ya sadaka da amincinsa."

Baffa Umaru ya faɗa yana hawaye.

"Sai mun zo Hadi Ubangiji ya karɓi baƙuncin ka."

Baffa Salihu ya faɗa shima yana ɗauke hawayensa.
Kamar ba za su tafi ba, sai dai ya zama dole suna tafe suna waige, shike nan an yi an gama sun tafi sun bar Baffa a in da yake a halin yanzu nan ne gidansa na gaskiya gidan kowa ma na gaskiya.

Haka suke tafe tun daga maƙabatarta har gida ba wanda ya yi ma wani magana. Kowa na fama da raɗadin zucci.
Hamma Saddam sai da Abdulrahim ya riƙe shi ya ce jiri ma yake gani hawaye suke yi har suka dawo gida.
Cikin gida Hamma Jibo ya shiga yana maganar a ɗauko manya tabarmu da cafet saboda masu zaman gaisuwa a waje. Adda Suwaiba ce ta ɗauko manyan tabarmun Ammah guda biyu sai kuma cafet.

Suna da shi a gidajen su, sai Hamma Abdulrahim ya je gidan shi ya ɗauko na su tabarmun da cafet duk aka ba za a haraban gidan aka zazzauna ana karɓan gaisuwa.
Mata kuma in sun zo bayan sun yi gaisuwansu a waje cikin gida suke shiga su yi gaisuwan su.
Received at 09:59Reactions: ❤ 8, 😭 4, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
A ɗakin Ammah, Mami take zaune tare da Ammah da su Ummin ikki tare da su Umma Balki, sai ga Fulani zaune a gefen Mami tana ta ba ta baki da lallashi domin tun bayan da ta farfaɗo take gunjin kuka mai ban tausayi Fulani na tunsar da ita da cewa ta daina kuka ta yi masa addu'a.

Gimbiya Shahida kuma na gefen Ammah zaune tare da Ummin ikki sai Bilkisu. kowa mamakin Ammah yake yi ba ta kuka kuma duk wanda ya yi mata gaisuwa za ta amsa tana sanye da hijabi da casbaha a hannunta amma kallo ɗaya za ka yi mata ka jinjina ma raɗadin da ke ji a zuciyanta.

Ummu Salma kuma da su Baɗɗo suna ɗakin Baffa tare da su Adda Suwaiba.
Sauran mutanen Mubi kuma suna tsakar gida wasu daga cikin iyalan su Umma Balki da sai bayan an yi jana'iza suka iso suna cikin ɗakunan barcin Ammah da na Ummu Salma, wasu kuma suna cikin ɗakin tsakar gida.

Ana zazzaune ana ta amsa gaisuwa an yi jugum jugum, kowa ka gani fuska a koɗe gwanin ban tsausayi.

Baɗɗo na gefen Umma Salma ba ta barta ba, domin Gimbiya  Shahida ta ce a zauna tare da ita a kula da yanayinta.

Tun bayan da aka fita da gawan Baffa Ummu Salma ta ji kanta ya yi wani irin sarawa, ta ji kamar an ɗora mata wani ƙaton dutse a saman kanta sara mata yake yi irin sarawar da ba ta taba jin irin shi ba. Ita dai tana biye da duk wanda ya riketa ne duk in da aka bi da ita can take zuwa.

Tana zaune ne hawayenta sun ki tsayawa. Wani irin abu ne mai zafi da maƙaƙi ya tokare mata a zuciyarta da kirjinta ba ta taɓa jin abu mai zafi irin shi ba ko lokacin da Habib ya saketa ba ta ji irin haka ba wannan abun ya ninka abin da ta ji a wancan lokacin sau dubu

Tantama take yi tana shakkun cewa wai yau ba Baffa? Jiya fa sun yi magana da shi ashe ashe Allah ya yanke ganawarsu gani take yi kamar a mafarki gani take yi kamar a ce ta farka ta ga komai bai faru ba. Ta ga lokacin da aka tafi da gawan Baffa daga lokacin ta ji komai ya tsaya mata duniyar ta tsaya mata cak ba ta jin daɗin komai bakinta ya yi wani takaf ɗaci daci ma take ji jikinta ya yi mata nauyi, cikin jikinta ya dunƙule a waje ɗaya maranta ya ɗaure haƙoranta na karo da junansu tana jin kamar jikinta na kamewa a waje ɗaya Baffa zai dawo wasa ne bai mutu ba haka take gani amma in aka shigo yi musu gaisuwa ta ji ana cewa Allah ya jikansa sai ta ji kukanta ya ƙaru da gasken kenan babu Baffa yanzu shike nan ya tafi ya bar su.

Ta jima tana jin labarin irin raɗaɗin rashin wani na kusa dakai, ita da ta tashi uba ta rasa a lokacin da ba ta taɓa kawo masa mutuwa ba ko a mafarki ko a hasashe ta yi hasahen rasa Ammah ko Baffa sai zuciyarta ta ƙuntata ta ji labarin ɗacin mutuwa ita sai yau ta ɗanɗani wannan ɗacin ta sha jin waɗanda aka yi ma rashin irin ta uwa ko uba suna faɗin har abada ba za su taɓ mantawa ba yau itama wannan rashin ya risketa tana jin itama har ta koma ga Allah ba za ta daina kuka ba har abada ba za ta ƙara dariya ko wani farinciki ba tana ganin farincikinta ya ƙare tunda ta rasa Baffa.

Baƙi suna ta zuwa maza da mata, wasu daga can Mubi ne wasu iyalan su Baffa Umari ne da su Umma Balki mata da maza dake can wasu garuruwan suna aiki sai gida ya sake kacamewa da koke koke ba yadda za a yi domin Baffa ya rasu ba kuma zai taɓa dawowa ba.

Har bayan azahar ba wanda ya sha ko ruwa a cikin waɗanda mutuwa ta shafa sai dai wasu na can gefen da ba su damu da mutuwar ba, domin sun ma kafa dandalin hira ne ba ko nuna jimami ga waɗanda aka yi ma wannan rashib, wasu ma sun fara ƙorafin su yunwa suke ji wasu ma wayarsu suke dannawa. Shi gidan mutuwa kaɗan ne daga ciki ke cikin jimami da ka mutu an kai ka an binneka shike nan taka ta ƙare sai iyalanka ne za su jima suna kukan rashinka.

Sai da duk aka yi salla sannan Ammah ta yi magana da Adda Nauwara tunda ita ce Babba ta ce su dafa abinci ko saboda yara.
Su kansu sun san an yi mutuwa sun natsu a waje ɗaya.

Harira na tare da su Sabuwa yaran kuma duk suna tare da su.
Sultan da shi aka je makabarta tare da sauran yaran su Hamma Jibo suna can haraba tare da iyayensu wajen zaman gaisuwa.
Received at 09:59Reactions: ❤ 13, 😭 4
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Adda Nauwara ta fito ta yi ma Adda Suwaiba magana suka tattara kansu surukan gidan suka yi maganar ɗora abinci , duk da ma daga maƙota duk an fara kawo abincin wasu har sun fara wawaso, wato yanzu gidan mutuwa ya koma gidan da ake ci a sha, barin ma in a ka ga gidan akwai maiƙo.

Kayan abinci akwai su danƙam a store ɗin kitchen cefane ma akwai domin kwana uku da ya wuce Hamma Abdulrraham ya yi cefane.
Suka ɗibo kayan miya suka gyara babban tukunyar Ammah mai lamba talatin suka ɗora a wani babban murhun gawayinta a tsakar gida gawayin ma akwai shi tunda lokacin bayan lokacin Ammah na amfani da shi.
Wajen ukun rana suka gama abincin aka zuzzuba anan cikin gida sannan aka zuba aka fita da shi waje daman kuma an kawo katan katan na ruwan gora da lemu sama da katan hamsin a cikin gida bayan wanda aka sauke a waje an samu abin da ake so tuni gidan mutuwa ya koma gida cin abinci da kuma hira , ana ci ana hira ana korawa da lemun gora da ruwa. Yara dai duk an saka musu sun ci tunda su yara ne ba ma su san abin da ke faruwa ba.

Waɗanda mutuwar ta shafa ko ruwa sun kasa kaiwa baki. Ko su Fulani ma sun kasa cin abinci ruwa kawai suka sha.
Ammah ma ba ta ci ba, ba ma wanda ya yi mata magana ganin yanayinta Ummu Salma ce Baɗɗo ta matsa mata ta ci abinci sai dai kawai ta kalleta hawaye na kwaranyo mata.

"Ba zan iya cin abinci ba Baɗɗo. Abinci ba zai wuce ba, bayan na san Baffa na cab cikin kabarinsa a yau ba zan iya ba."

Ta sake fashewa da kuka, mutanen dake ɗakin suna ta ba ta baki amma ta kasa ci, wai ta ci saboda cikin jikinta ta ce ba za ta iya ba su ƙyaleta.
Kukanta ya dawo saboda tana yi tana shessheƙa.

Bayan la'asar Mai martaba za su koma tare da Fulani da Gimbiya Amratu za a bar Gimbiya Shahida da Saleem sai an yi addu'an uku za su koma Daura.
Har cikin gida Mai martaba ya shigo sake yi ma Ammah gaisuwa da yin sallama.

Hamma Jibo ne ya yi masa jagora. Mata suka dare sannan Mai martaba ya shigo tare da Waziri da shamaki dogarai suna dake a bakin ƙofar ɗakin Ammah ya shiga har ciki ya zauna a saman kujera.

Ammah na gefe kanta na kasa su Umma Balki sun bar falon sai Mami ne kawai tare da su Gimbiya Shahida sai Ummin ikki da su Bilkisu

Ya yi ma Ammah gaisuwa tare da ba ta haƙurin wannan rashin da suka yi gabaɗayansu tare da tausasan kalaman hakuri da cin wannan jarabawan

"Allah ya jiƙan shi, Allah ya ba ku haƙurin rashi."

"Amin ranka ya daɗe mun gode Ubangiji ya mayar daku gida lafiya."

"Ammah Mai martaba ya ba da kuɗi masu yawa ya ce a siya kayan abinci da duk abin da za a nema a wajen zaman makokin nan"

Hamma Jibo ya faɗa yana zaune daga gefen Ammah.

"Allah ya ba da lada. Mun gode ranka ya daɗe."

Bai amsa yana da cikin rawaninsa idanuwansa da wani farin gilashi ya kalli Mami da ta jingina da jikin kujera a rana ɗaya kawai ta wani faɗe kamar wacce wani cuta ya kamata. Kamar ma ba ta san abin da ke faruwa a falon ba hawayenta ne kawai ke zuba da motsin carbin hannunta.

"Batula ya haƙurin mu?

Mai martaba ya tambayeta yana mai kallonta ta cikin rawaninsa.
Tana ji ashe ba ta ɗago ba amma bakinta ya yi motsi alamun ta amsa.

"Allah ya jiƙan shi, Allah ya ba da haƙurin rashi."

Ta amsa da Amin tana mai rufe bakinta da tafin hannunta guda ɗaya wani kuka ne ke ƙwace mata kawai sai ta kifa kanta a jikin kujera tana faman rerewa kukan da ya kashe ma duk wanda ke ɗakin jiki barin ma Mai martaba da ba ya son jin kukan Batula kukanta na tuna masa da shekaru talatin baya
Ɗakin Ammah kawai suka shiga daganan suka fita ya ce sai ranar addu'an bakwai in ya samu dawowa in kuma bai dawo ba zai turo wakili shima nan da sati uku zai tafi ganin likita a ƙasar London.

Tawagan wakilan Gwmnan Jahar Adamawa ne suka kwashe su zuwa fadar gwammati daga can za su wuce filin jirgi su koma Daura.

Da gaske dai Baffa ya rasu, tun da ga shi har an yini an kwana Baffa ya yi kwanan kabari. Barci ko ɓarawo bai saci Ummu Salma ba haka Mami ma, kuka kawai take yi ba saurarawa.
Ammah kuma kwana ta yi salla domon nema ma Baffa rahama da gafara a wajen ubangijinsa.
Received at 09:59Reactions: ❤ 13, 😭 4
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk anan suka kwana har Bilkisu mazan kuma a can bangaren su Saddam da safen ne Hafiz da matarshi Salima suka iso ya ce a status ɗin Hamma Kabiru ya gani ashe ba rabon ganawarsu da Baffa a ranar ma mota biyu daga Mubi sun sake zuwa amma ba su kwana ba kama daga yan'uwan matan su Hamma Abdulrhaman tare da abokan ayyukansu duk sun taho gaisuwa gida ya sake cika danƙam
Sannan abokan aikin su Hamma Jibo daga Abuja, Gombe Taraba duk sun taho gaisuwa. Kuma suna shigo da su cikin gida domin su yi ma su Ammah gaisuwa.

Lamiɗo dai tun jiya bai sake shigowa ba gida cike da mata. Amma zuciyarsa da tunaninsa suna wajem Ummu Salma ne a daran ma ya kira Bilkisu a waya ya ce ta duba masa ita. Domin ya yi ta kiran wayarta ba a ɗauka ba ita ba ta nemi wayar ba tana cikin jakarta, jakar kuma Adda Suwaiba ta tusa mata a wadrope ɗin Ammah ta saka maƙulli ta rufe.

Bilkisu ta ce masa tana tare da ƙawarta lafiyanta ƙalau shi ya sa hankalinshi ya ɗan kwanta amma ya san tana cikin damuwa sosai, su kan su dauriya ce irin ta maza amma rashin Baffa wani babban rashi ne a gare su gabaɗaya.

A ranar ma su Gimbiya Maimuna da Gimbiya Hadiza tare da Hajiya Zainab suka zo gaisuwa daga Daura.
Ba su jima ba, iyakarasu awa biyu suka juya.

Mutane suna ta zuwa gaisuwa daga garuruwa dabam dabam. Wasu mota ne wasu kuma jirgi ne.
Abinci ga shi nan ana kawowa wanda ake dafawa ma a cikin gida mai rai da lafiya ne sannan ga ruwa ga lemu, girkin ma da nama ake yin shi, shi ya sa gidan yake cika da mutane maƙil.
A ranar ma Hajiya Falmata ta zo tare da wasu dangin Daddy daga zamfara su dai yan zamfara a ranar suka koma Hajiya Falmata ne ta ce sai an yi uku

A ranar dakyar Mami ta iya cin abincin ba domin tana so ba Ammah kuma sai kunu aka dama mata ta sha kaɗan Ummu Salma kuma ta kasa cin abinci daƙyar ta sha tea shima sai da Gimbiya Shahida ta matsa mata tana gama sha kuma sai amai sai ga ta kwance jikinta ba karfi da za ta faɗi irin yadda kanta ke ciwo da sun tausaya mata tana kwance akan gadon Baffa tana ta hawaye da kukan zucci

Har bayan mangariba ba ta saka komai a cikinta ba, kuma mai rai ba zai zauna bai ci wani abu ba. Sai Gimbiya Shahida ta kira Saleem a waya ta ce ya yi magana da Lamido ya shigo cikin gida ya lallashi Ummu Salma ko za ta ci abinci saboda yanayinta

Yana faɗa masa bai tsaya ba tare da Saleem ɗin suka shiga cikin gida falon Ammah ya fara tsayawa ya yi musu gaisuwa.
Ammah ya kalla a cikin kwana ɗaya duk ta zabge kamar ba ita ba.

"Ammah kin ci abinci?

Ya tambayeta lokaci ɗaya yana kallonta cikin tausayi da wani abu daga ƙasan zuciyarsa

"Ta dai sha kunu amma abincin ya kasa ciyuwa Lamiɗo."

Umma Balki ta amsa masa.
Sannan ta cigaba da faɗa masa Fatima dakyar ta yi cokula ta ce ta ƙoshi sun kasa cin abinci

"Kowa ya san an yi muku rashi amma hakuri za ku yi ku ci abinci saboda lafiyarku, ita Auta ma tea aka ce tasha ta amayar da shi tana can kwance tana kuka to gwara su sun samu sun yi kuka ita uwar taka ko hawaye ba ta yi ba. Na ce Jamila ki yi kuka in ba za ki a gaban mu ki kebe kanki ki koka domin abin kukan ne ya same ki , ta kasa yin kuka zuciyarta ne kawai ke cikin azaba ina tsoron kar zuciya ta kume mata itama wani abu ya same ta"

Hankalin shi ya tashi, ko daga ganin yanayin Ammah zafin dake cikin zuciyarta ya wuce tunanin mai tunani.
Gabanta ya sake matsowa ya durƙusa ya riƙo duka hannayenta ya sanya su a cikin na su ya ji sun yi ɗumi kuma suna ta rawa

Ya kalleta idanuwansa har sun sauya launi
Ba ya son ganin damuwarta, yanzu sai ya rikice

"Ammah."

Ya kira sunanta a cikin karaya domin shima ya karaya bai kuma san da wani kalamai zai yi amfani da shi wajen lallashinta ba. Rashi ne babba ya same su musamman ma ita, duk wanda ya zauna da Baffa da Ammah sai ya ji rayuwarsu ta birgeshi.

"Na'am Lamiɗo."

Ta amsa masa tana kallon shi.

"Kar ku damu da ni, lafiya ta ƙalau na san Allah ne ya ɗauki ran Baffa, ni musulma ce na san kaddara na kuma karɓeta."

Ta ɗan ja fasali kafin ta cigaba da faɗin

"Ku je ka samu Auta ka duba ta, an ce tun jiya ba ta ci komai ba tana ta kuka ga lalura a tare da ita."
Received at 09:59Reactions: ❤ 9, 😭 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta faɗa idanuwamta sun kawi ruwa amma ba ta barsu sun zubo ba.
Kowa a falon su kawai yake kallo.

"Ammah zan je, amma ke ma ki yi haƙuri."

"Na yi Lamiɗo."

"Baffanku ma maganarsa ta ƙarshe kafin kalmar shahada haƙurin ya ba ni."

"Ammah to ki yi kuka. In wani abu ya same ki ina za mu saka kanmu."

"Babu abin da zai same ni Lamiɗo. Baffa ya ce na yi haƙuri yana gangaran mutuwa sau uku yana ba ni haƙuri Lamiɗo me ya sa zan masa kuka. Aikina shi ne na dauwama ina yi masa addu'an rahama har nima ta Allah ta kasance a gare ni."

Bakinta ne ya fara rawa daman hannayenta dake cikin na shi sun daɗe da kama rawa, bai san lokacin da ya durƙushe a gabanta ya jawota a ƙirjinsa ya rumgume ta yana mai lumshe idanuwana kamar shima ya fashe da kukan zuciyarsa ta yi wani dum kamar ba shi ba.

Ammah jin ta a jikin Lamiɗo ya sa wasu hawaye masu zafi suka saukar mata wannan hawayen ji ta

Please Login or Register in order to submit comment