Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

arba da shi ne ya sa gudun zuciyarta tsayawa na wani lokaci.
Kasala da wani irin sanyi ya lulluɓeta a lokaci ɗaya nauyin jikinta sai ya ƙaru.

Ya shigo falon sannan ya saka hannu rufe ƙofar falon
Lokacin da ya fara takowa a tsakiyar falon ƙirjinta ya fara bugawa fat! Fat!
Ta kafe shi da idanuwana ba kiftawa shima ita yake kallo da yanayin kallon nan na shi mai sanyata kasala.




*Janafty*
Received at 07:54Reactions: ❤ 19, 🥰 1, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk takun zai yi domin matsowa zuwa gareta, tare yake da tsinkewar zuciyarta. Ita ta fara ɗauke idanuwanta a kan shi domin ba za ta iya juran kallon shi ba tana jin wani iri kaifaffun idanuwansa da kuma ƙwarjinsa sun cika falon ga ƙofofin hancinta na shaƙo mata sanyayyan ƙamshin shi wanda a baya yake sanyata cikin shauƙi da soyayya amma yau zuciyarta ne ta fara tsinkewa tana jin kamar za ta yi amai tunda ya shigo falon ƙamshin gabaɗaya ya gauraye falon.

Kanta na ƙasa tana wasa da zoben azurfan da Mai martaba ya yi mata kyautar shi tana jin a jikinta da zuciyanta Hamma Lamiɗo bai daina kallonta ba sannan yana ƙara kusantowa zuwa gare ta ne.

Jikinta har rawa ya fara saboda fargaba, duk da ta daɗe tana shirya maganganun da za ta kare kanta duk ranar da Hamma ya waiwayota amma kuma ganin shi a gabanta bagatatan ya wargaje duka shirinta, ta kasa ko iya kallon shi ta kasa miƙewa saboda yadda jikinta ya yi mata nauyi.


"Ummu Salama."

Ta ji ya kira sunanta a hankali da wannan muryan na shi cikin amo.

Sai idanuwanta suka cika da ƙwalla ta yi kewar kiran sunanta da yake yi shi kaɗai ne ke kiranta da Ummu Salama. Ta ɗago suka sake haɗa idanuwana wannan karon har ya ƙariso gabda yana tsaye hannunsa guda ɗaya a cikin aljihun bakin yadin dake jikinsa ɗinkin riga da wando har da babban riga. Amma babban rigan tana hannun shi na dama, kafafuna sanye da budaɗɗen takalmi na fata baƙi kansa kuma ya saka baƙar hula gashin sa ya fito ta gefe da gefen hulan sannan fuskarsa ta yi fayau tunda ya rage gashin gemu sa da sajensa gabaɗaya.

Kallon shi take yi tana ji kamar ba Hamma Lamiɗon da ta sani a shekara ɗaya da wani abu baya ba. Kamar Hamma Lamiɗo da ta sani dai a shekarun baya ne. Ta kasa iya motsi ballatana ta iya amsa kiran sunanta da ya yi ko ta yi masa sannu da zuwa ba komai ya ƙwace mata kanta ta mayar ƙasa tana jin tafin kafafunta na ɗaukan ɗumi sosai. Wattani biyu ta yi ba ta gan shi ba amma ji take yi kamar shekara ce.


Shi ko kallonta yake yi da dukkan zuciyarsa. Me ya same ta? Ya ga ta rame wuyanta sun faɗa idanuwanta sun ƙanƙance komai na ta ya sauya ba kamar yadda ya tafi ya barta ba.

Wani abu ne ya faru da ita ne?

"What wrong with you?

"Are you sick?

Tambayoyin duk a tare ya jera mata su, ita kuma lokacin zuciyarta ne ke cigaba da tsinkewa tana jin kamar za ta yi amai shi ya sa ta miƙe dakyar tana jin kamar jikinta ya yi ma kafafunta nauyi.

"Sannu da zuwa."

Ta faɗa cikin sanyin murya amma ta ki bari su sake haɗa ido.
Ya amsa da yauwa a iya fatar bakinsa.

"Na ce ba ki da lafiya ne?

Ya sake tambaya yana mai ƙureta da idanuwansa.
Yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa? Me ya sa ba a faɗa masa ba? Kuma dalilin da ya sa ya ke turo Abdullahi kenan amma sai ya ba shi tabbacin lafiyanta lau, me ya sa ta rame? Gabaɗaya ta sauya masa ta yi baƙi kamar ba Ummu Salama ba.

"I'm asking you. Ba ki da lafiya ne?

Ya sake maimata tambayar wannan karon muryansa ta ɗan buɗe.
Ba ta so hawayen da suka kawo mata su zubo, hancinta kuma ya gaji da shaƙar iskar ƙamshin turarensa zuciyanta na yunƙurin amai kawai sai ta juya baya daidai lokacin da hawayen suka taho mata.

"Lafiya ta ƙalau Hamma."

Ta amsa shi da raunin murya kafin ta kwashi sauri tana mai rufe baki zuwa ɗakinta amai ne ya taho mata take saurin isa tiolet kafin ta sake shi anan shi kuma tunanin shi ko ta gudu ne sai ya taka ya bi bayanta. Yau ba gudu ba duk wani rashin fahimta dake tsakaninsu za su warware shi.

Yana shiga ɗakinta ya ji ƙakarin amai a tiolet da sauri ya ajiye rigar hannun shi a saman gado ya buɗe ƙofar tiolet ya shiga tana durjushe a tiolet ɗin tana ta kwarara amai duk tuwon da ta ci ne shi ne take amayarwa daman ya sani ba ta da lafiya yana ganinta ya fahimci haka kamar ba jini a jikinta.

Bai damu da kar ta ɓata shi ba, bai damu da warin amai ba, haka ya shiga tiolet ɗin ya riƙeta lokaci ɗaya yana rankwafawa yana yi mata sannu.
Received at 17:28
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta ba shi tausayi yadda take amai, kamar hanjin cikinta zai zazzage daga ƙarshe ma sai ruwa kawai ke fitowa, shi bai san shi ne ciwon ta ba ƙamshin jikinsa da take shaƙa shi ke ƙara saka mata hararwa ta rasa kuma yadda za ta yi masa bayani ya fahimta.

Jikinta sai rawa yake yi, tana mayar da numfashi sama sama in ta yunƙura ta yi aman ba ya zuwa sai wahala take sha, shi kuma yana ta faman yi mata sannu.

Ta jingina da bango tana mayar da numfashi.

"Sannu."

Ya faɗa yanan mikewa tsaye.

"Ki tashi ki wanke jikin ki, mu je asibiti."

Ta kalleshi hawaye suka kece mata a saman fuskarta.

"Hamma."

Ta kira shi cikin raunin murya.

"Na'am."

Ya amsa yana kiran nata na ratsa duka jikinsa da zuciyarsa

"Ciwo na yanzu ba shi da magani."

Ta faɗa tana yi masa mirmishi. Ji take yi kamar za ta yi amai amma ba komai a cikinta ba ta son ƙamshin nan tana so ta ce ya fita ta kasa.

"What? Akwai ciwon da ba shi da magani ne?

"Akwai."

Sai kawai ya zura mata idanuwana yana kallonta kirjinsa na duka, ta ga fargaba da tsoro a kallon da yake yi mata.

"Hamma."

Ta sauke numfashi.

"Ka je waje, zan yi wanka ne."

Ta gama faɗa tana yunƙurawa kamar wani aman zai fito amma kuma babu komai.
Ya kalleta sai ta gyaɗa masa kai shi kuma sai ya fara nannaɗe hannun rigan shi wai zai taimaka mata ta gyara jikinta.

"Aa."

"Zan iya da kaina."

Ganin kamar ba ta so sai ya ƙyaleta ya fito ya janyo mata kofa, yana fita ta rarrafa ta yi floshing ɗin aman da ta yi ya wuce rigar jikinta ma duk ta ɓaci da amai cire kayan da ta yi ta watsa ma jikinta ruwan sanyi.

Ta fito ɗaure da towel har lokacin yana ɗakin zaune bakin gado yana jiranta. Bedroom din na ta ma ya gauraye da ƙamshin sa

Da hanzari ya taso ya nufe ta, sai ta yi baya da sauri tana toshe hanci wallahi kamar za ta mutu haka take ji shi kuma mamaki ya sa kawai ya tsaya yana kallonta ya kasa magana.

Dube-dube take yi ina ta baro ƙasanta shi kawai za ta shaka ta zauna lafiya. Sai ta tuna yana falo da gudu ta fita shima sai ya bi bayanta yana tunanin ko bayan baya nan aljanu sun shafeta ne

Ya tsaya kawai yana kallonta ganin ta ɗauko gwangwanin madara ta buɗe ta kafa kai tana shaƙa har wani lumshe idanuwa take yi. Ya ɗauka ma madaran ne a ciki take so ta sha har hankalinsa ya kwanta amma sai ya lura koma mene shaƙan shi take yi ba sha za ta yi ba

Ita ba ma ta shi take yi ba shakan ƙamshin ƙasan take yi kamar da zuciyarta. Har wani daɗi daɗi take ji.
Harira ce ta fito daga kitchen sai ta yi kiciɓis da Yarima ta yi ƙasa da sauri tana yi masa sannu da zuwa

Ya juya ya kalleta sau ɗaya ya amsa.
Ya koma ya kalli Ummu Salama ya fara tunanin akwai abin da ke faruwa da ita wanda shi bai sani ba.

Kamar zai tambayi Harira sai kuma ya fasa itama ta tashi ta koma kitchen ƙarisawa ya yi kusa da Ummu Salma ba ta ma sani sai ganin kan shi kawai ta yi ya leka gwangwanin hannun ta.

"Ƙasa.?

Ya faɗa a saman leɓen shi cikin mamaki. Ita kuma matsowan shi kusa da ita yasa ta yi tsalle ta koma gefe har towel ɗin jikinta na neman faɗuwa ta tare shi da hannu ɗaya.

"Hamma."

"Ka tsaya anan"

Idanuwansa a kanta innalillahi tabbas wani abu ya same ta wanda bai sani ba. Me ta ke yi da ƙasa kuma? Ko Depression ne ya kamata ko wani cuta a ƙwakwalwarta amma in ba haka ba me ya sa za ta yi ta shinshinar ƙasa sannan ta hana shi ya matso kusa da ita.

Tausayin ta ya lulluɓeta koma mene ne ya faru duk shi ne sila da ace tana tare da shi da ba ta samu wannan laluran ba.
Ya yi tsaye kawai yana ganin ta tana ta shinshinar ƙasa.

"Me kike yi haka?

"Kasa ne fa"

Ya faɗa muryansa na yin ƙasa.

"Ina so ne."

Ta amsa mishi, sannan ta kalle shi tana yi masa mirmishi.

"Come here."

Ya faɗa yana ya fito ta da hannunsa guda ɗaya.

"Hamma."

"Ƙamshin turarankaa ne ke saka ni amai da tashin zuciya."

Ya sake yin sakayau kawai yana kallonta.
Ya kasa gane abin da ke faruwa.

"Meke damun ki?

"Ciki gare ni."

Ta ba shi amsa kai tsaye sannan ta bi ta bayan kujera ta wuce.

"Ka jira ni anan."
Received at 17:28
15 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba ta so ya biyo ta ɗakin, kamar daman umarninta yake bi ya yi tsaye yana kallonta har ta shige ɗakin, shi ba ma wannan ba sai ya ji kamar da ya tambayeta abin da ke damunta ta ce ciki gare ta amma sai wata zuciyar ke tunanin bai ji daidai ba ne

Yana nan tsaye ta fito ɗauke da wata farar takarda a ninke ta zo ta ajiye a saman kujera.

"Hamma ka yi hakuri ka duba wannan sai mu yi magana."

Tana gama faɗin haka ta koma ɗaki sai da ta bubbuɗe window amma duk da haka ƙamshin na nan Allah yasa ga kasarta a gefe tana ta shaƙa shi ne ya saukaka mata.

Shi ko takardan ya ƙarisa ya ɗauka tsoro har ya bayyana a saman fuskar shi.
Yana buɗewa ya bi rubutun dake ciki daki daki kafin ya gama karantawa ya ji hannunsa na rawa

Ummu Salama tana da ciki, ashe abin da ya ji ta faɗa gaskiya ne. Date ɗin ya duba tun tafiyar shi ne ba daɗewa. Ko bai yi lissafi ba ya san ranar da suka samu matsalan nan ne ashe akwai rabo mai nauyi a tsakaninsu idanuwansa suka ƙankance da hanzari ya shiga ɗakin nata har ta saka kaya doguwar rigar Abaya.

"Why?
Ta juya tana kallon shi.

"Me ya sa ba ki faɗa mini ba?

"Ba wanda ya faɗa mini kina da ciki Umma Salama."

Ya gama faɗa kamar zai yi kuka. Ba ta yi tsammani ba kawai sai ganin shi ta yi a gabanta tana kallon shi da idanuwanta masu ruwan hawaye.

"A ina zan faɗa maka?

"Ka rufe ni ko na kira ka bana samun ka."

Ta gama faɗa hawayen na kece mata da kuka.
Sai kawai ya rumgumota a cikin jikinsa ƙamƙam tare da takardan a hannunsa kamar tana jira ta saki kukanta mai sauti wannan kukan da kewar wattani biyun da ba ta samu kafaɗan da za ta yi kuka ba, yau shi take yi duk da ƙamshin turaransa na tsinke mata zuciya ba ta damu ba, tana bukatar kafaɗan da za ta yi kuka a lallasheta.

"Hamma.."

"Ka yi hakuri."

"Shii."

Ya faɗa yana ɗan bubbuga bayanta alaman lallashi ita kuma tana ƙara shigewa jikinsa tana rirrikeshi lokaci ɗaya tana kuka.

"Na yi kewarka, na yi kukan rashin ka."

"Wallahi na yi nadaman kalaman da na faɗa maka tun a ranar."

"Na yi nadama."

Take faɗa tana gunjin kuka.

"Is Ok."

"I'm Sorry."

"Na barki ke kaɗai. Am sorry bana tare dake a lokacin da kike buƙata ta."

"I'm Sorry Ummu Salama. I'm sorry."

Shima yake faɗa kamar ya yi kukan haka yake ji, Ummu Salma ta yi ta kuka kukan dake fitowa daga ƙarkashin zuciyanta bai hanata ba ya barta ta yi kukanta har sai kukan ya dawo shessheƙa.

Ya ɗago fuskarta yana share mata hawaye da gefen hannun rigansa.

"I'm sorry."

Ya sake faɗa, ta ƙamƙame hannuwan shi.

"Hamma."

"Yes"

"Ka yafe mini."

"Komai ya wuce Umma Salama."

"Ka yafe mini?

"Na daɗe da yafe miki."

Ya faɗa yana kallon cikin idanuwanta. Wasu hawayen suka sake kece mata.

"Shi ne ba ka nemi ni ba! Ba kira ni ba?

"Am sorry."

"Im here ba zan sake tafiya na bar ki ba."

"Ka tabbata?

"Na tabbata."

Sai ta fara mirmishi tana hawaye, yana share mata.

"I miss you. I miss everthing about you expecially wannan craying face ɗin na ki."

Ya gama faɗa yana jan hancinta amai ta ji ya taso
mata sai ta bar jikinsa ta rarumi gwangwaninta tana shakan ƙamshin ƙasan ta.

"Warin turare na ne ba ki so?

Ya tambaya cikin kulawa.
Sai ta ɗaga masa kai

"To bari na yi wanka ko na sauya kayan ne?

"Ko ka yi wanka zan ji ƙamshin."

"Bana son kamshin komai yana sani amai ƙamshin wannan ƙasar kaɗai nake so."

Ya zura mata idanuwa a zuciyarsa yana faɗin dankari .

"Sai dai ka zo ka yi wanka da sabuluna mara ƙamshi, ba za ka shafa mai ba sannan ba za ka fesa turare ba"

"Ba matsala?

Ya tambayeta domin shi gani yake ka yi ta shaƙan kamshin kasa ai akwai damuwa

"Hamma."

"Baby ke so fa ka gane."

Ta gama faɗa cikin shagwaɓa.

"Oh na gane."

Bai gane ba kawai dai ya ce ya gane ne amma ya saboda ciki kawai sai mutum ya ce ba ya son kamshin komai sai na kasa.
Shi ɗakinsa ya ce zai je ya yi wanka ta ce yana da mayuka da sabulan wanka ma su ƙamshi ba ta so haka nan ya shiga wanka a ɗakinta
Received at 17:28Reactions: ❤ 12, 😁 2
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sabulu ne bai taɓa ganin irin shi ba ko kumfa ba ya yi, ba ƙamshin ko kaɗan daga karshe ma ruwa kawai ya watsa ya fito tuni ta kwashe kayan da ya cire ta tura cikin wadrope wai suna ƙamshi, ta fito masa da riga da wando, babu kamshi a jikinsu domin tunda ta dawo gidan ba ta yi amfani da turare ba yana ji yana gani aka hana shi shafa mai wai zai yi ƙamshi ba ta so dole ya hakura.
Ga wani jidali duk in da za ta je tana tafe da gwangwanin kasanta abinci ta ce mai Harira za ta dafa masa?

"Ke nake so ki yi mini girki."

Ya faɗa mata lokacin yana gaban madubi yana tashe sumar kansa. Sai da ya duba ya ga ba komai duk ta kwashe duk wani mai ƙamshi ta ɓoye wannan cikin na gaske ne.

"Bana iya girki Hamma bana son ƙamshi girki"

Ta cikin madubin ya hangeta ta zauna a tsakiyar gado ta tankwashe kafa kawai tana ta shakan ƙasan hannunta

"Cikin nan ya saka ki rama."

"Na sha wahala ne Hamma."

Ta amsa mishi kafin ta fara ba shi labarin irin wahalan da ta sha tana ma kan sha.

"Tun cikin na 2week ya fara bani wahala."

Ya gama abin da yake yi ya taho zuwa gare ta.
Shima ya hayo gadon ya zauna sannan ya janyota jikinsa tana ta shinshina shi.

"Wari nake yi ko?

Ta kalle shi ba ta yi magana ba.

"Wai da sabulunan kike wanka?

Ta gyaɗa masa kai.

"Tab dole ki yi baki, sabulu ne? Kamar ƙasa ko kumfa ba ya yi."

Ta fara dariya tana faɗa masa Umma Balki ta aiko mata da shi ta ce a can shiyar sokoto ake samun shi ba shi da ƙamshi ko kaɗan.

"Ummu Salama."

Ta kalle shi, shima ita yake kallo.

"I'm Sorry."

"Na barki, kina ta wahala ke kaɗai"

"Ba ni kaɗai ba ne, kowa na tare da ni kai kaɗai ne na yi missing"

Ya jawo jikinsa ya rumgume.
Yana faɗin ya yi mamakin da ba wanda ya faɗa masa halin da take ciki.

"Abdullahi kodayaushe sai ya ce mini kina lafiya. Ammah ma ba ta taba faɗa mini wani abu ba. Gwara ma Mami tafiyata ba daɗewa mun yi waya ta ce ga shi nan Allah ya bamu wani rabon."

"Lokacin ban gane me take nufi ba sai yanzu."

Ya gama faɗa yana kallonta.

"Ammah ba za ta faɗa maka ba kunya take ji saboda ni. Hamma Abdullahi kuma ba zai yi tunanin ba ka sani ba. Kowa ma har Mamin za su yi tunanin ka sani na faɗa maka tunda ban taba faɗa ma kowa abin da ke faruwa a tsakanin mu ba."

"Good, personal life ɗin mu ne ba sai kowa ya ji ba."

Ya amsa mata.

"Ba ni labarin abubuwan da suka faru lokacin da bana nan"

Ta ce ba zai ci abinci ba? ya ce sai anjuma.
Nan ta lafe a jikinsa ta shiga ba shi labarin wahalan da ta sha tana yi tana shaƙan kasanta daga karshe ma shi yake miƙo mata gwangwanin yana hannun shi. Ya ji tausayinta sosai yana ta bata hakuri ita in ta ce ya yi hakuri sai ya ce

"Kar ki kara tuna wannan maganar. Na manta da ita har gaban abada."

Amma shi haƙuri yake bata na yadda ya yi dogon fushi da ita a lokacin da ya kamata ya kasance a kusa da ita, ta ce komai ya wuce tana jin kamar ma komai bai taɓa faruwa na faɗa a tsakaninsu ba wannan tazaran da Lamiɗo ke tunanin akwai tuni ya amince da cewa babu ita a tsakanin shi da Umma Salma har abada.

Suna cikin ɗakin nan manne da juna kiran sallar mangariba ne kawai ya tashe su. Shi daman a Airport ya tsaya ya yi sallar la'asar ba wanda ya san ya dawo mashin ya hawo zuwa gida.

Da ya fita salla mangariba sai da aka yi isha:i ya dawo lokacin har Umma Salma ta sake wanka ta sauya kaya wani riga da wando masu taushi. Abinci kuma Harira ta saka ta dafa masa ruwan tea da ya ji kayan kamshi daman ta yi farar shinkafa da miya da nama sai ta ce ta zufa masa har da salat.
Lokacin da ya dawo ɗakin shi ya shiga ya yi waya da Bilkisu yana ta mamakin ta wannan karon har da murnanta da ya ce mata zai taho Adamawa ya zauna ya yi tunanin dalilin murnan nata ne bai samu lokaci ba.

Abinci shi kaɗai ya ci a dinning tunda Ummu Salma ba ta son ƙamshi ita kuma sauran tuwonta aka ɗumama mata. Shi ko iya kallon tuwon ya kasa yi da bakar miyar nan zai je ya yi magana da Ammah me ya sa za ta dinga cin wannan abincin? Sannan shi ba ya son tana shaƙan ƙasan nan kar wani cuta ya kamaata ga dariya ga tausayi lokacin da take faɗa masa wai kasar kofar gidan Baffa ne kaɗai take ƙamshi, na anguwan nan Harira ta
Received at 17:28Reactions: ❤ 16, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
ɗibo mata babu ƙamshi.

A daran Saddam ya zo ya kawo mata goro da ƙasar sai ya ga Lamiɗo. Kasar ma kamar ta roƙa a wata leda ce ƙarama ta ce ya mayar kawai ita da take da shi da yawa.
Har tana sa Harira na ɗauko masa ya gani yana dariya Hamma Lamiɗo na dariya kasa ne rabin buhun baggo ina lafiya.

Anan ya ci abinci kafin ya tafi Hamma Lamiɗo ya ce sai gobe da safe za shigo ya gaishe da su Ammah ya amsa da to zai faɗa musu.

Da wuri suka yi shirin kwanciya saboda wannan sabulun ko wanka bai sake marmarin yi ba. Kayan barci ma sai da aka zabo waɗanda ba sa ƙamshi bayan an gama shinshinawa aka ba shi ya saka.

Halin da take ciki ya sa bai nuna yana son kaɗaicewa dai ita ba, duk da yana muradin haka.

Sai ita ce suna kwance maƙale da juna hiran na ta ya ƙare shuru na wani lokaci hannunsa dai na kan cikinta yana shafawa.

"In sha Allahu wannan karon za mu samu mai sunan Baffa.'

"In mace ce fa?

"Ki zaɓa mata suna. Gaba in mun samu namijin mai sunan Baffa ne."

"Allah ya jiƙan Baffa."

Ya faɗa cikin wani irin amo.

"Amin Ya Allah."

Shuru ya sake wanzuwa da ta fahimci ba zai taƙaleta ba.
Sai ta ƙara shigewa jikinsa tanakiran sunan shi.

"Hamma."

'uhm"

"Ka taƙale ni"

"Ba matsala ?

"Ko Baby shima ba ya so.."

Ba ta bari ya ƙarisa ba ta fara sumbatar bakin shi, shima sai ya mara mata baya

Ya ɗauka shima baby baya son wannan taƙalen ne sai ga shi ya fahimci yana so sosai ma, domin ta nuna masa hakan kuma ya gani dukkansu sun yi kewar junansu domin gangar jikinsu ta tona musu asiri.
Sai da suka yi wanka suka samu tsarki sannan suka koma suka kwanta.

"Hamma."

"Uhm"

"Ba ka jin ƙamshi a jikina ko?

"I don't care "

"Wari nake yi ?

"Ki bari. Bana so."

A kausashe ya faɗa shi yasa ta san da gaske baya so. Hannun shi na saman cikinta suka yi barci amma ta yi ta tashi cikin dare tana shaƙan kasanta da asuba ma sai da ta yi amai abincin da ta ci amma tunda ta ɗan gutsiri goron da Ammah ta aiko mata da shi ta ɗan samu saukin tashin zuciyar.

Da safe kasa cin komai ta yi, ta ce Harira ta yi zamanta ba sai ta yi mata tuwon ba za ta je gida kila su Ammah sun tara mata kanzo daman suke shanya mata ya bushe Ammah daga zaune ta daka mata a ƙaramin turmin ƙarfe.

Shi ne kawai ya sha tea, karfe goma da rabi suka bar gida key ɗin duka motocinsa yana hannun Umma Salma ne, Hamma Abdullahi ya kawo mata.
A toyota ɗin suka fita suka bar Harira a gidan.

Daman tun jiya Saddam ya sanar da su Ammah zuwan Lamiɗo zuwansa bai yi musu ba zata ba. Gidan ba kowa Saddam da Abdulrahim duk suna wajen aiki.
Sai Ammah kaɗai da Umma A'i sai Ummin ikki sun shigo ba daɗewa sai ga ta tazo gidan

Kanzo nan ko Umma A'i ta daka ma Ummu Salma ta saka mata gishiri da farin magi ta ɗan yayyafa mata ruwa ya yi taushi shi ta ci abu kamar magani amma ita ya yi mata daɗi.
Lamiɗo na zaune mamaki kawai yake yi Bilkisu ta haihu sau biyu amma bai ga wannan matsalan tare da ita ba.

Cikin farko ma bai kai wannan cikin wahalar da Umma Salama ba. Sai da ya yi ma Umma A'i mgana wai kar ta zo ta samu wani cuta ba ta cin abinci mai gina jiki ga shinshinar ƙasa.

"Ko wani ciki da na shi salon Lamiɗo. Auta da tunda ta samu cikin nan take wahala kuma in ka ga irin haka wataƙila har ta haife shi tana laulayi nan."

Ya zaro ido irin abin ya ba shi mamaki

Ammah na gefe tana dariya ba ta yi magana ba.

"Ba komai duk abin da ka ga tana ci shi ne zaman lafiyanta tunda shi take so. Ba kuma abin da zai sameta da yardan Allah."

Ummin ikki ta amsa mishi.
Su Ammah suka amsa da in sha Allahu.

"Haihuwar ce nake fatan Allah ya ba ta da sauƙi. Allah ya sa wannan karon ta haihu da kanta ba sai an farka ta ba."

Umma A'i ta faɗa Ummin ikki na amsawa da Allah ya sa.

"Ai ba anan ƙasar za ta haihu ba. In sha Allahu a Egpyt za ta haihu kusa da kwarrarun likotoci."

tana cin kanzon ta sai da ta kalle shi ya gyaɗa mata kai daman a wancan cikin a can ya tsara za ta haihu shi da Mami sai Allah ya yi ikon sa kafin ma cikin ya isa haihuwa.

Umma A'i ta ce hakan ma ya yi, tunda dai tana da matsaloli a wajen haihuwar gwara aje kusa da ƙwarrarun.
Received at 17:28Reactions: ❤ 12, 👏 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sun bar wannan hiran sun koma hiran Mai martaba Ammah na tambayan yanayin jikinsa.

"Da sauki Ammah har yanzu dai yana kan shan magani."

A tare suka yi fatan Allah ya ƙara lafiya. Ya ce yana so zai je ko bai kwana ba ya dawo a ranar nan da kwana biyu shi da Umma Salama za su koma Lagos.
Ummu Salma ta yi zaraf ta ce za ta je Daura.
Ya ce ba za ta je ba saboda yanayinta ta bari da salla, sannan akwai wata tafiyar a gaban su tunda kuma ya ce ba za ta je ba da gaske yake yi.

A gidan suka yini har dare barin ma da su Saddam suka dawo ga su Hamma Abdullahi kusan

Please Login or Register in order to submit comment