Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ta faɗa kawai take yi.
Ta yi wankan tsarkin najasan dake jikinta sannan ta yi shirin kwanciya ta kwanta amma ta kasa barci a daran kuma ba ta san sau adadin nawa ta kira lambar Hamma Lamiɗo ba amma kuma ya yi rufe ta da alamun ba za ta same shi ba.

Ga ta kwance kawai amma ta kasa barci sai tsiyayan hawaye. Tana mai ganin laifin kanta da ta yi hakurin da kowa ya ce ta yi da yanzu ba ta cikin nadama shima ya ba ta hakuri amma taurin kai da kafiya suka hana ta ganin hakurin da ya ba ta, sai ga shi da kalaman bakinta cikin mintina ƙalilan ta bata komai

Juye-juye kawai take yi da ta kasa barci dole ta miƙe ta shiga tiolet ta ɗauro alwala. Dole ne abubuwa su rikice mata ta manta da Ubangijinta. Tunda abubuwa nan suka faru da ita sai dai ta zauna tana koke koke ba ta tunawa da keɓe kanta ta faɗa ma Allah kukanta. Shi ya sa ta zama sai a hankali sai fama da zafin zuciya da fushi. Salla ta fara yi raka'a shidda ta yi sannan ta rufe da shafa'i da wutiri.

Ta ɗaga hannuwana sama tana kuka tana neman ma Baffa gafara tare da fatan Allah ya sanya jaririnta da ta rasa ya zama mai ceton su ranar gobe ƙiyama sauran addu'o'in nata duk akan Hamma Lamiɗo Allah take roko ya sassauta zuciyarsa akan ta, Allah ya yi ramgwame a cikin fushin sa zuwa gare ta. Ita dai ba ta da sauran kalaman kare kanta duk abin da za ta faɗa ta riga ta gama ɓata komai tun daga farko.
Sai uku da rabi na dare ta koma ta kwanta, tana kallon rufin ɗakin kafin barci ya kwasheta ta share hawaye ba ta san iyaka ba.

*

A bangaren Lamiɗo kuwa yadda ya fita a cikin fushi ba ƙaramin ƙokarin iya sarrafa fushin sa ya yi har Allah ya kai shi gida lafiya ba.

Kalaman Ummu Salma na zuwa da dawowa a cikin kunnuwansa, shi bai damu da cewar da ta yi bai damu da rasa jaririnsu ba, amma cewar da ta yi bai san zafin da ta ke ji a zuciyarta ba, tunda shi bai rasa uba ba.

Maganar ta zo masa cikin bazata ne, bai taɓa tunanin haka daga Ummu Salama ba. Da gaske ne ba ta da kunya duk ya shanye rashin kunyarta ya ɗau ƙankanta ya bar mata girman don a zauna lafiya amma duk bai isheta ba sai da ta yi masa gorin ba Baffa ne ya haife shi ba.
Received at 07:52Reactions: ❤ 7, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba domin ita ba ce, da wani ne da yau sai ya gane kuskuran shi. Amma duk da haka itama zai koya mata hankali, in taƙamarta rashin kunya da rashin iya magana to zai koya mata yadda za ta iya magana da shi, yadda anan gaba duk abin da za ta faɗa masa sai ta tauna shi ta tantance shi kafin ta faɗe shi.

Haka ya shiga bangaren Bilkisu a fusace yara duk suna falo har da Hanan suna ganin shi suka nufe shi suna kiran sunan shi da Papa
Amma duk yadda yake son yara bai tsaya kallon su ba.

Bilkisu na yi masa sannu da zuwa bai juyo ba ya shige daki ya banko kofa ya saka key, baya son kowa a kusa da shi saboda yana cikin fushi shi kuma in ranshi ya ɓaci ya fi son zaman shi kaɗai fiye da komai

Gefen gado ya zauna yana dafe kan shi da ya ji yana sara masa.

Ta ce ta rasa jaririnta amma bai damu ba saboda yana da wasu yaran?
Ta manta shi ne uban jaririn, ta manta irin soyayyar da yake yi ma cikin nan tun kafin ya zama gudan jini

Shi fa namiji ne ta ya zai zauna yana nuna mata rauninsa alhalin tana mace, zai iya rantsuwa abin da ya ke ji akan rashin jaririn su ita ba ta ji irin shi ba, ko don bai faɗa mata ba? Ko saboda bai zauna ya yi mata kuka ba? Wani abin ba ka sanin zurfin shi. Wani ciwon ba ya iya bayyanuwa a fatar baki zuciya kaɗai ke iya riƙewa.

A lokacin da ta faɗi maganar ta zo masa da zafi sosai, yana shirin ya dakatar da ita sai ta ɓata komai.

Har Baffa ya koma ga Allah bai taɓa jin sa ba a matsayin mahaifinsa ba. Rashin Baffa gibi ne shima a rayuwarsa domin shi ya fara sani a uba kafin Mai martaba. Yau shi Umma Salma ke yi ma gorin bai san zafin mutuwar uba. Ya runtse idanuwana ya buɗe bai san adadi ba, ya nutsa hannayensa cikin sumar kansa ba adadi huci da fitar da numfashi kamar zai shiɗe sai da ya ta shi ya shiga tiolet ya sakar ma kansa ruwa sannan ya ɗan samu sauƙi sauƙi.

Wayarsa tana silent ne sai da ya fito ya ga kiran Ummu Salma rututu, bai ma san yadda ya ke ji a zuciyarsa ba. Amma for now ba ya son ganin ta ko jin muryanta ta bar shi ya samu nisa da ita ko zuciyarsa za ta huce.

Blooking ɗin ta ya yi, ba ya son ma ya ga sunan ta tana kiran shi saƙon ta kuma ko ɗaya bai buɗe ba.
Ba ta kuma da sauran abin da za ta faɗa masa.
Maganganunta suna neman goge duk wani alherinta a gare shi.

A hankali a hankali ya ke jin kamar ta saka katanga ta katange duk wani hangen shi da zumuɗin shi a kanta, wannan soyayyar da kaunar da suka faro ta, tun daga farko yana jin tana yi masa nisa wannan kalmomin na ta sun sanya tazara mai yawa a tsakaninsu tazaran da suke tunanin sun daɗe da haɗe shi.

Bilkisu tunda ta ga yanayin shi ba ta neme shi ba, shima kuma daman haka yake so ya fi son ya kaɗaice shi kaɗai
Ba ya son ya ganta ballatana ya ji kalaman bakinta gani yake yi yanzu duk abin da za ta faɗa ba zai zama mai daɗi daga gare shi ba.

A daran ya siya musu tiket ɗin zuwa Lagos. Tsarin shi ya ruguje kalaman Ummu Salma sun yi nisa da abin da ya shirya. Da ita ya so su koma a tare a sabon gida da ita domin su gina kyakyawan rayuwa a can har su mayar da jaririn da suka rasa amma a dare ɗaya ta ruguza wannan yaƙinin na shi akanta. Ba zai iya tafiya da ita ba, ko ta je can ba zai taɓa sauraranta ba yana bukatar lokaci mai tsawon da zai yi tunani amma shi ba zai sake yarda da ita ba, sai ta goge waɗanan munanan kalaman nata zuwa gare shi, kuma goge kalamanta abu ne da ba zai taɓa yuyuwa ba magana zarar bunu ce tunda ta fita ba za ta koma ciki ba.

A daran ya canza duka tsarin shi da ita. Ba yanzu ba wataƙika sai ya huce ko zai iya sauraranta amma yanzu ta zauna a gida hakan shi ne mafitarsu gabaɗaya.

Jirgin goma sha ɗaya na safe za su bi zuwa Lagos.
Bayan ya dawo daga masallacin Jumma'a ya shiga ɗakin Bilkisu ya sanar da ita akan su shirya akan lokaci.

Bai yi mata wata magana ba, kuma ba faɗa mata aka yi ba a jikinta take jin koma me ya ɓata masa rai to Umma Salma ne, zuciyarta kamar farar takarda tana ta addu'an Allah ya sa ba da ita za su tafi ba.
Received at 07:52Reactions: ❤ 14, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta fahimci tunda Baffa ya rasu ta kuma haihu ba ɗa shi kenan ta ga ta ɗan yi sanyi ta rage tsiwa da yi ma mutane kallon reni da ta je ta ganta shekaranjiya duk ta fita kammaninta sai da ta yi dariya ta tabbata a haka babu kuma abin da za ta birge Lamiɗo da shi.

Ba ta tambaye shi ba, ta san in ma ba tare da Umma Salma za su tafi ba za ta ga ni in lokacin tafiyar ta yi. Da wuri suka shirya jikinta ya yi sanyi da ta ji ya ce tare da Hanan za su tafi to za a tafi da ɗiya ne a bar uwarta anan sai murnan ta ya koma ciki.

Amma suna zuwa gidan Ammah ta samu amsar tambayanta.
Ammah ce da kanta take tambayan shi, shi ya ce Ummu Salma ta zauna anan sai ta sake warwarewa?

Kai tsaye ya amsa da shi ya ce ta zauna ta sake warwarewa daga baya sai ta biyo su.
Bilkisu murna kamar me, tana ta mirmishi ita kaɗai duk da bai faɗa ba, ta san wani abu ne ya faru a tsskaninsu da ya hana tafiyar Ummu Salma addu'a take yi a zuciyanta da Allah ya sa daga nan auren ya kare kowa ya huta.
Ita kadai za ta dinga juyi a wannan ƙaton gidan da daman baƙin cikinta ɗaya yadda za ta juya a sabon gida itama Umma Salma za ta juya gani take yi ai ba matsayinsu ɗaya ba ma.

Tafiya da Hanan kuma sai yanzu ta fahimci saboda makaranta ne. Ba ta damu ba in dai Umma Salma ta fara barin mata mijinta ita ma Hanan ɗin ba daɗewa za ta bi bayan uwarta.

Kayanta ma Harira aka ce ta haɗa, sannan ko a gilmawa ba ta ga Ummu Salma ba kuma Lamiɗo bai neme ta ba. Daɗi ya yi kusa kasheta tana zaune tana girgiza kafa tana faman mirmishi.
Duk maganganun da aka yi a falo Ummu Salma na laɓe daga ƙofar ɗakinta tana ji.

Ita kaɗai ta yanke ma kanta hukunci, hukuncin da take da yaƙinin shi Hamma Lamiɗo zai yanke, daman ita ta ce ba za ta bi shi ba ta faɗa gaban yan amin, yadda ya ki ɗaukan wayanta ya rufe ma hanyar da za ta same shi ta samar ma kanta mafita.
Bayan ta idar da salla asuba ta samu Ammah har ɗakinta ta yi mata karyan ita anan za ta zauna in ji Lamiɗo Ammah ta ce in ya zo za ta yi magana da shi ta ji.

Tunda ta ji hayaniyarsu ta laɓe, ba za ta iya fitowa ba, ba ta yi mamakin cewar da ya yi ta zauna ba daman ta yi tunanin haka. Itama kunya ba zai barta ta bi su ba, sannan kuma ita ce ta ce daman ba za ta bi shi ba, shi ya sa ba ta shirya ma tafiyan ba. Gwara su tafi daga baya sai ta bi su in ta tabbatar da ya koma bakin aiki sai ta koma zuwa lokacin da zai dawo ya wuce, sai ta tattaro duka kalaman bakinta ta sake bashi hakuri. Amma yanzu ita kanta kunyar abin da ta faɗa masa take ji.

Ta san kuma ba zai taɓa shigowa yi mata sallama ba, itama ba ta san da wani idanuwa za ta kalle shi ba.
Tana zaune gefen gado Harira ta shigo tana ce mata Ammah ta ce a haɗa kayan Hanan ta amsa mata.

Tana sake ganin girman Hamma Lamiɗo da kuma nadamarta duk abin da ta yi masa bai bambanta Hanan da su Sultan ba, kuma bai fasa amsa sunan uba a gare ta ba.

Harira ke tambayan ta su ba tare za su tafi ba? Ta ce mata sai daga baya sai ta koma ganin likita.
Ashe da ba ta ga Hidaya da Sabuwa suna Lagos Bilkisu ta tura su kafin ta wuce Daura suna can sabon gida suna kimtse kimtse ma'aikatan ma sun dawo bakin aiki har su Debora su kaɗai ne masu gidan ba su dawo ba.

Tana jin Harira ne kawai na magana amma ita tunanin ta ya yi nisa, sai da Harira ta gama haɗa kayan a ƙaramar akwati ne, kamar za ta yi magana ganin har da wasu kayan da aka ɗinka mata a can gidan su Habibu, watsar da kayan ma ta so yi daga farko daga baya kuma sai ta fasa.

Tana zaune har Harira ta fice ta yi tagumi kawai, tana jin hayaniya a falo sai da suka yi breakfast itama an shigo mata da nata amma ta kasa ci a lokacin ma ta sake kiran wayar Hamma Lamiɗo ba ta shiga.

Tun da ta ji zuwan Hamma Abdullahi ta san tafiya ta tashi tunda shi zai kai su filin jirgi. Ta maƙale a jikin kofa tana leƙe.
Ta hango Hamma Lamiɗo a durkushe a gaban Ammah ya rike hannunta yana mata magana a hankali ko kana kusa ba lalle ka ji abin da ya ke cewa ba, ballatana ita da take leƙe daga cikin ɗaki.

Bilkisu da yaran sun fita Harira ta ɗaukan musu jakunkuna, Hanan ko nemanta ba ta yi ba, ballatana su yi sallama itama ba ita ce a gabanta ba yanzu.
Received at 07:52Reactions: ❤ 12, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Tana gani ya saka ma Ammah farar evelope jikinta. Tana jin muryan Ammah na godiya da saka albarka.
Umma Balki har da ita a masu fita rakiya lokacin da ya miƙe sai ya ɗan waiwayo kamar zai kalli ɗakin da Umma Salma ke ciki sai ta yi saurin yin baya tana dafe kirji kar ya kamata tana leƙensa.

Bakin yadi ne a jikinsa ɗinkin zamani da bakar hula mai gashi gashi.
Juya baya ta yi tana dafe ƙirjinta dake bugawa.

Ba ta taɓa tunanin zai shigo ba sai ji kawai ta yi an buɗe kofa. Da juyawarta da shaƙam ƙamshin turaran shi duk a lokaci daya ne.

Sun haɗa idanuwana amma shi ya yi saurin kauda kan shi. Baya son kallonta ita kuma tana ganin shi wani irin nadama abin da ta aikata ya ruguzo mata.
Ta yi narai narai har kwarmin idanuwanta ya cika da ƙwalla.

Kafafunta suka shiga rawa ganin yadda ya haɗe fuska ya fito a sak Yarima Daura ko Lamiɗon da ta sani a can baya.
Wanzuwarsa a ɗakin sai ta ji kamar ta matsu, kamar babu wajen iska ƙwarjinsa ya babbake ko'ina da ya sa ta kasa ma numfashi mai ƙarfi.

Duk nacin kallon shi da take yi bai yarda ya kalleta ba a cikin aljihun wandon sa ya fito da farin evelope mai tudu ya ajiye mata a gefen gado.

Ya juya zai fita ba tare da ko hawa da saukan numfashin sa ba ta ji ba.

"Hamma."

Ta kira shi cikin karyewan sauti sai hawaye shar.

"Ka yi haƙuri don Allah.."

Ya tsaya amma bai juyo ba.

"Na tuba ba zan ƙara ba."
Kukan har yana sauti ya lumshe idanuwana ya buɗe.

"Take care of yourself"

"Ummu Salaama"

Yana gama faɗin haka ya buɗe ƙofa ya fita ya barta tana durƙushewa a ƙasan cafet tana kuka yana jin ta amma ba zai bari kukanta ya yi masa tasiri ba.

Daga shi har ita suna bukatar lokaci. Gwara ta zauna tare da Ammah a kula da lafiyanta ta samu natsuwa shima gwara ya yi nisa da ita ko zai samu zuciyarsa ta yi sauƙi. Amma zencen gaskiya yana buƙatar lokaci sannan ko zai saurare ta ba yanzu ba. Yana jin kalamanta har yanzu yana tunanin kuma zai daɗe yana jin maimaicinsu a cikin kan shi, Ummu Salma ta ruguza komai, in ya ce komai yana nufin komai amma soyayyarta dake cikin zuciyarsa ba ta samu rauni ko tawaya ba sai dai hakan ba shi zai hana ya nuna mata kuskuran abin da ta yi ba.

Daman ya yi niyar ya shiga ya yi mata sallama. Ya fuskanci uzirinta ta bangaren halin da take ciki amma ba shi zai sa ta riƙe a matsayin makamin da za ta kwatsa masa wannan maganar ba. Ba ta da lafiya har yanzu tana kan dokokin likita ne, ya bar mata kuɗi masu yawa domin nauyin ta yana wuyan sa ne ta kula da kanta har zuwa lokacin da zukata za su huce.

Yana jin kukanta amma bai juya ba haka ya fita, Ammah ba ta fita ba amma ta bi shi da fatan alheri mai yawa.
A motarsa Hamma Abdullahi ya tuƙa su zuwa filin jirgi a ranar da Baffa ke cika kwana talatin da ɗaya a ƙasa.

Sai da jirgin su ya tashi ya tashi sannan Hamma Abdullahi ya dawo gida da motar ya ba ma Ammah key ɗin motar da na bangaren Bilkisu.

Ummu Salma kuma ba ma wanda ya sake bi ta kanta.
Tun da Hamma Abdullahi ya tambaya ganin ya ga ba da ita aka tafi ba Umma Balki ta ce Lamiɗon ya ce ta zauna daga baya sai ta bi su.
Ko su Hamma Saddam da suka dawo aka ce ta na nan ba ta tafi ba ganin Harira ba wanda ya damu da ya shigo ya duba ta.

Tun a yau ta fara nadama, da a ce ta ji haƙurin da ake bata da tuni tana gidan mijinta. Ga shi tana gidan amma ba ma wanda ya damu da ita.
Baɗɗo kuma ta yi fushi da ita ta daina zuwa ta daina nemanta.

Zaman gidan ma sai ya zame mata kamar a gidan yari kwata kwata ba ta jin daɗi. Ga shi tun da Hamma Lamiɗo ya tafi sama da sati bai taɓa kiranta ba ko ta kira shi ba ta samu sannan tana jin suna waya da Ammah daga baya ma a bakinta take jin ya koma wajen aikinsa.

Ga kewa duk ya sake surkukuta ta, ba wanda ya lura tana ta ramewa.
Mami ma da suka yi waya ba ta san kwanan zencen ba har tana faɗin sai ta yi gyaran jikinta a tsanake, kayan da tunda aka kawo su ba ta duba su ba

Sai ranar ta saka Harira ta buɗe tunda a leda suke ciccibi da kazar sababi sun ɗan fara lalacewa sai kawai ta ce Harira ta zubar garin magunganur kawai ta bari sai maganin sanyi.
Abin ta aikata ne ya zo yana damunta ga shi ta kasa faɗa ma kowa.
Received at 07:52Reactions: ❤ 9, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Baɗɗo ce abokiyar cin mushenta ta kira ta domin ta nemi sulhu ta ce za ta zo amma ba ta zo ba.
Shamsiya sau biyu tana kiranta na farko ta ɗauka.
Na biyun kuma ba ta ɗauka ba, ba ta ga amfaniin kiran wayar ba. Ta faɗa mata Hanan na Lagos ita tana Adamawa.

Har abada ba ta buƙatar Shamsiya a rayuwarta yanzu, ita ta zama past tense a cikin rayuwarta ne.
Daƙyar Baɗɗo ta hakura ta zo ranar Hamma Lamiɗo ya yi sati biyu da ta tafiya da ta zo ta ga Ummu Salma sai da ta yi magana.

"Sisna kin ga yadda kika rame kika lalace?

Mirmishi kawai tayi ba dole ta rame ta lalace ba. Rayuwarta ta yi juyin waina daga sama zuwa ƙasa.

Tunda ta haihu ba ta gyara jikinta ba ita kanta ta san duk ta fita hayyacinta.

"Har da Tumbi kika bari ya zauna miki, fuskarki ta yanƙwane jikin ki ya yi kamar ba na ki ba fuskarki ta sauya kin yi baƙi me ke damun ki?

Da za ta iya da ta faɗa mata amma kuma ba za ta iya ba. Abin da ke damunta zaman da take yi ba rashin dalili.
Ba ta san a wani babi Hamma lamiɗo ya jingine ta ba.

Baɗɗo ta yi ta mata faɗan ta bar jikinta duk ya lalace. Gaskiya ya kamata ta gyara sannan zaman me take yi anan gwara ta shirya ta koma gidanta in ba za ta koma Lagos ɗin ba yanzu.

Sai kuma da Baɗɗo ta faɗa ta yi tunanin haka. Tana son komawa Lagos amma ba ta son ta koma a haka a firgice sai ta yi gyara ta ɗan dawo hayyacinta.
Sai ta ce za ta koma asibiti jibi in ta dawo daga can kawai sai ta wuce gidanta.

Maganar kayan gyara kuma ta ce Mami ta siya mata ga su can za ta fara amfani da su. Tumbi kuma daman ba da yawa ba ne rashin kula ne ma yasa har yanzu bai tafi ba amma za ta miƙe domin ta gyara jikinta amma ita kanta ta san ta fita hayyacinta.

Baɗɗo ta yini tare da ita sai yamma ta koma gida.
A daran ta tura mata dubu dari biyar son da ta yi alƙwarin za ta tura mata ta kafa jari. Baɗɗo har da kuka saboda farinciki.

"Ba zan iya biyan ki ba Sis na, wannan kawai kyautatawa ne daga cikin irin kyautatawarki a gare ni."

Tabbas ba za ta iya biyan Baɗɗo tarin alherin da ta yi mata ba sai dai ta kamanta in tana da shi babu abin da ba za a ta mallaka mata ba.
Sun yi maganar har sabaya za ta haɗa da kanta ta fara sha tunda har nonuwanta sun fara yamutsewa ita dai abubuwa da dama sun yi mata ruku'a a cikin rayuwarta.

Ga abincin mai gina jiki amma ba ta ma sakin jiki ta ci, ta saka tunani da kwazzaba a zuciyanta duk ta bushe dole kishiya ta yi mata dariya.
Ana gobe za ta koma asibiti ta dama garin haƙkin daka na cikin kayan Surayya Dee tunda da safen ta yi mata magana ta turo mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi.

Maganin sanyi ta fara sha da safe da yamma ne ta dama na garin ta sha, sai dai bai ko gama zama a cikin ta bai yi ba, ta fara amai kamar hanjin cikinta zai zazzago.
Cikinta da maranta suka dinga murɗawa a daran ko abinci ta kasa ci bakinta babu daɗi haka ta kwana cikin kasala da tsikewar miyau

Da safiyar litini da ta kama kwanan Lamiɗo goma sha bakwai da tafiya ita da Harira suka koma asibiti
Yanayin da take ji ta yi ma likitan bayani a can ma asibitin tana shan ruwa sai amai Jininta aka diɓa suka sanya mata drip tunda sun ce jikinta ya yi yaushi sannam ba abinci a cikinta suka yi mata alluran barci Hamma Saddam ne ya kawo su daga nan ya wuce wajen aiki.

Harira ce ta kira Ammah ta faɗa mata sun rike Ummu Salma a asibitin.
Ammah ta ce Umma Balki ta bi bayan su ta gani.
Ko da ta je Umma Salma na barci, ba daɗewa likita ya kawo sakamako.

Ciki ne a jikin Umma Salma kimaniin sati biyu da kwana biyu Kwanakinsa kwana sha bakwai kenan a cikin jininta suka gano cikin.
Umma Balki ta yi ta mamaki, likitoci kawai a bar musu kayansu wajen bin kwaf yanzu cikin ma na sati biyu sun iya gano shi.

Sai yamma suka gama saka ma Ummu Salma ruwa, ta samu kwarin jiki, an dakatar da ita daga shan ko wani magani saboda cikin dake jikinta.
Sai ta ji abin kamar a mafarki da ta kirga kwanaki cikin ranar da suka kaɗaice da Hamma ne a bangaren su Saddam a ranar ta samu wannan cikin.

Sai ta rasa me za ta yi, farinciki take ji ko mene ne, gata nan dai ta kasa gane kanta. Ashe rabo ne ya kirata shi ya kai ta wajensa har komai ya shiga tsakaninsu.
Received at 07:52Reactions: ❤ 8, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sun koma gida da tarin dokar likita ta dinga cin abinci sannan ta daina tunanin jininta ya sauka amma kuma zai iya hawa ga ciki a jikinta ƙarami sannan tana da tarihin hawan jini da cutar Eclaampsia sai ta lura sosai wajen kiyaye lafiyanta.

Umma Balki suna komawa gida ta fasa maganar cikin Umma Salma.

"Daman ko haihuwa mace ta yi ɗa ba rai ko ta yi bari za ki ga da wuri take samun wanin cikin."

Ammah dai ta yi fatan Allah ya kara lafiya.

"Ki kula da kanki, tunda yanzu kin ga ba ke kaɗai ba ce."

Abin da Ammah ta faɗa mata kenan.
Umma Balki kuma na faɗin sai ta kira Lamiɗo ta faɗa masa ta amsa da to, amma ta san ba samun shi za ta yi ba. Ta neme sa ba ta same shi sai ta adana takardan gwajin cikin duk lokacin da ya sauko ya saurareta sai ta sanar da shi.
Da kanta ta kira Baɗɗo ta faɗa mata ta dinga tsalle a waya sai ga shi ta taho.

Ba ta fasa komawa gidan ta ba, sati ɗaya ta kara a gida saboda yanayin laulayin da take fama da shi sannan ita da Harira su koma can gidan Hamma Lamiɗo ta buɗe shashenta ta share ta zauna tana jiran Hamma duk lokacin da zuciyarsa ta huce da kan shi zai neme ta.

Ta dage da addu'a ba dare ba rana akan Allah ya sassauta zuciyar Hamma Lamiɗo zuwa gare ta.
Kuma tana da tabbacin ita ce kawai ba ya kira amma yana kira Ammah da su Hamma Abdullahi, ya san halin da take ciki

Please Login or Register in order to submit comment