Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi Mami ce ta janye shi gefe.
Jikin Ummu Salma ya fara rawa ba ta san ta juyo ba, sai kuma idanuwam su Gwaggo na kan Hanan suna kallonta itama ganin baki sai ta kura musu idanuwanta na yara har tana dariya.

Tsoron Ummu Salma a yanzu rasa Hanan ba za ta iya jure wannan rashin ba.
Ko ba a faɗa ba duk wanda ya ga Hanan ya ga Habib domin tun a jaririyarta kamar shi ta ɗauko bayan ta fara wayau sai kamanin ma suka sake bayyana.

Da Shamsiya da Gwaggo zuciyarsu na bugawa a lokaci ɗaya suna ƙura ma Hanan ido. Haka ma Habiba da Hajiya Sahura.
Wannan yarinyar jinin Habib ne tabbas Hajiya Sahura ta furta a zuciyarta Habiba kuma haushi ta ji me ya sa Maganar Habib ta tattaba ta?

Jwalla suka ziraro ma Gwaggo ashe da rabon Habib zai ga gudan jininsa.
Hannu ta miƙa ma Hanan tana faɗin" Zo nan y'an mata"
Hanan dake tsaye da jan riga yar kanti a jikinta kanta ba ɗankwali an yi mata kitson shuko.

Kamar ba za ta je ba haka ta nufe Gwaggo tana zuwa ta kamata ta rumgume.
Kowa kuma a falon ya kasa magana ballatan motsi saboda mamaki.

Gwaggo da tsufanta amma hawaye take yi.
Ta ɗago Hanan tana kallonta.

"Ya sunan ki."

"My Name is Hanan."

"Hanan Habib Jimeta"

Gwaggo ta ce magana ta ƙare a zuciyarta
Hannatu Habib wannan jinin Habibu ne.
Shamsiya ta duƙa a gaban Hanan tana kuka tana riƙeta sai Hanan ta turje ganin ba ta san su ba kawai sai ta fara kuka kamar an buga ma Ummu Salma guduma a saman kanta ta dawo hayyacinta ta saki hannun Baɗɗo ta nufe su ta ture shamsiya sai da ta faɗi zaune ta janye Hanan.

"Bestie"

Shamsiya ta kirata cikin kuka.

"Kar ki ƙara kirana da wannan sunan"

Ummu Salma ta faɗa a fusace cikin ƙaraji.
Sanman ta ja Hanan za su koma ciki.

"To ki bar ni na rumgume Hanan"

"Kar ki kuskura, kar ki kuskura ki matso kusa da yata."

"A'a ba su da kunya ne "

Mami ta faɗa tana tafa hannu mamaki duk ya ishe ta.

"Ku fita kawai tun kafin rayukanmu su ɓaci."

A lokacin Hamma Abdullahi ya shigo falon Ammah kamar an jeho shi.
Received at 10:01Reactions: ❤ 12, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Ammah ki ji mini marasa kunyar mutane wai dangin wannan shegen yaron da shi kan shi ne da ya tozarta Ummu Salma sun zo suna mana maganar wai sun zo ba da hakuri duk abin da ɗansu ya yi a lokacin ba su san su ba da haƙuri ba sai yanzu."

Ya faɗa yana huci idanuwansa sun rufe ko ta kan su Gwaggo bai bi ba.

"Na ce a kore su kawai Hamma Jibo ya ce a'a, Ammah wallahi tallahi zan kira musu hukuma."

"Shi Habibun ne ya zo don ba shi da kunya?

Ummin ikki ta tambaya.

"To ai daman an ce in ba ka da kunya ka yi abin da kake so, yana can zaune a koɗe mara mutumcin ba."

"Ku kore su, ga ma sauran nan ku tarkata su bar mana gida."

In ji Mami tana sake tafa hannuwa.
Ummu Salma kuma tun da ta ji an ce har da Habib sai da ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya.

"Nima dai ban ga amfanin zuwan su ba, tun a lokacin ba su zo ba sai yanzu."

Umma Balki ta faɗa.

"A'a ku ƙyale su."

Sai a lokacin Ammah ta yi magana gabaɗaya suka kalleta

"Ku ƙyale su. Ku shigo da su nan a yi maganar."

"Su shigo fa kika ce Ammah?

Hamma Abdullahi ya tambaya.

Ta gyaɗa kanta cikin tabbatarwa.

"Haka na ce, kuma ko Baffa na raye shima haka zai ce"

Jin sunan Baffa ya sa kowa jikinsa ya yi sanyi.

"Wasiyar Baffa ne, a daran da zai rasu tare da ni da su Saddam ya faɗa mana in sun zo mu saurare su in sun nemi gafara mu yi musu afuwa."

Tunda ta ce wasiyar Baffa ne ba wanda ya kara magana
Ummu Salma ta ja Hanan suka shige ciki Baɗɗo ta bi bayanta.
Haushi take ji, me ya sa Ammah za ta ta ce a saurare su ta sha roƙon Allah kar ya sake haɗa ta da Habib ko Shamsiya.

Ba ta ƙaunar su san ma abin da ta haifa balle ya zama yana da alaƙaa da su.
Sai ga shi komai ya kwaɓe mata. Ba ta jin za ta iya yafe ma Habib da Shamsiya sun cutar da ita.

Kulle ɗaki ta yi saboda Hanan na so ta fita.
Ummu Salma kuka kawai take yi komai ya dawo mata sabo. Baɗɗo kuma mamaki kawai take yi na ganin Shamsiya a haka.

"Tab rayuwa Sisna kin ga yadda Shamsiya ta koma?"

Tana jin ta ba ta yi magana ba. Ba wannan ba ne a gabanta ita haɗuwa da su ne ba ta so.
Fargabanta ma Hanan ne, za ta iya yin komai domin Hanan ba ta kasance tare da su ba har abada.



*Janafty*
Received at 10:01Reactions: ❤ 16, 👍 2, 🥰 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Tunda har Ammah ta ce su shigo a ba su dama sannan a saurare su ba wanda zai yi musu da ita. Ko lokacin Baffa na raye ba ya musa ma umarnin Ammah balle kuma yau da ba ya raye maganar Ammah tana saman na kowa duk abin da ta ce shi za a yi. Balle kuma ta ce wasiyar Baffa ne.

Hamma Abdullahi ya mayar da fusatar shi ya fita can haraba in da su Hamma Jibo ke tare da su Alhaji Sharif ya ɗan duka ta wajen kunnensa yana faɗa masa saƙon Ammah.
Shi daman Hamma Jibo ɗan sauki ne ya ce a saurare su.

Hamma Abdullahi ne da Hamma Abdulrahaman sune ke ta bala'i Allah ya sa ma tun a farko ba su gane su ba da ko gaisuwan da suka yi musu ba za su amsa ba.
Su uku ne daga Alhaji Sherif sai Baba Usman sai Habib ɗin da yake ta raɓe raɓe yadda rayuwa ta mayar da shi ne da kuma daman ba wani sanin shi suka yi ba shi ya sa ba su gane shi ba gwara ma Saddam shi ya je gidan Ummu Salma ba adadi sun sha haɗuwa da Habib ɗin amma shi da farko bai gane shi ba sai daga baya ya fara masa kallon sani.

Hamma Jibo kuma ya so ya gane Alhaji Sherif tunda sun taɓa zuwa da Baffa a wancan lokacin amma ya kasa kama suna ballatana ya tuna in da ya san shi. A tunaninsu kawai masu zuwa gaisuwa ne tunda har gobe kafa ba ta ɗauke ba.

Amma sai suka ga bayan sun yi gaisuwan sun yi shuru. Hamma Abdullahi ya fusata ne lokacin da Alhaji Sherif ya gabatar da kan su a matsayin dangin Habib ɗin tare ma da Habib ɗin sai a lokacin ma suka gane shi.
A lokacin Hamma Abdullahi ya ta shi a fusace ya shiga gidan yana sanar da Ammah abin da ke faruwa.

Hamma Abdulrahaman ya ce su ba za su saurare su ba su ta shi su tafi kawai. Hamma Jibo ne ya ce su ɗan dakata tukunna. Habib kawai suke kallo lalle rayuwa juyi juyi na gaba ya koma baya.

Tun daga kayan dake jikin Habib ba sai an faɗa musu ba sun san rayuwa ta juya masa baya. Kallon reni da wulaƙancin ya sha shi a wajen su Hamma Abdullahi.
Lamiɗo ko kallo ɗaya ya yi masa bai ƙara ba wani abu na yi masa rawa a zuciya na haushi da kishi.
Habib kuma ya kasa magana ya kasa haɗa idanuwa da su domin sun yi masa ƙwarjini ga kunya ga nadama sun taru sun natsar da shi a waje ɗaya ba domin Alhaji Sherif ba tabbas zai iya tunkara wannan gidan ba.

"Ku yi hakuri don Allah, mun san abubuwa sun faru a baya mara sa daɗi. Ku ɗan ba mu lokaci ku saurare mu ku ji da abin da muke tafe da shi."

Alhaji Sherif kenan yana sake roƙon su Hamma Jibo ganin ba su yi maraba da zuwan su ba. Ya san daman haka za ta faru shi ya sa ya ce shi ba zai zo ba. Darajan tsufan Gwaggo ya duba da kuma bakin da matarsa Hajiya Sahura ta saka sannan tare da nadamar Habibu shi ya sa kawai ya amince zai zo amma tabbas abin da ya faru a baya ba mai daɗi ba ne ko shi ne a matsayinsu abin da zai aikata wataƙila sai ya fi na su shi yasa ko kaɗan bai ji haushin su don sun ce su bar musu gida ba.

"Ba komai. Mahaifiyarmu ta ce ku shiga ciki domin a zauna a yi magana."

"Allah Sarki mun gode. Allah ya saka da alheri."

Saddam aka tura cikin gida ya fara sanar da su Ammah shigowar maza.
Daman falon daga Ammah ne sai Umma Balki da Ummin ikki. Sai Mami sai su Gwaggo da Shamsiya da suka zo daga baya.
su Adda Nauwara suna dawowa daga makabarta suka bi su Adda Suwaiba gidajen su.

Islam kuma tana ɗayan ɗakin tana ta fama da waya a hannunta. Ummu Salma kuma tana ciki ta rufe ƙofa ita da Baɗɗo da Hanan.

Daman da hijabai a jikinsu sai kawai suka ce su shigo.
Hamma Jibo ya yi ma su Alhaji Sherif jagora har falon Ammah shi dai a saman kujera ya zauna tare da Baba Usman amma Habib a ƙasa ya zauna daga can gefe ya takure ko idanuwana ya kasa ɗagowa.

Ammah kallo ɗaya ta yi masa ta kauda kanta haushin shi take ji a baya amma a yanzu da mutuwar Baffa ta gama zare mata jin haushin kowa tausayin ma ta ji ganin yadda ya koma.
Received at 11:37Reactions: ❤ 14, 🥰 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummin ikki kan haka take hararan shi bai sani ba tunda kansa na duƙe ne, Mami dai fuskar nan ba fara'a ba domin an ce wasiyyar Baffa ba ne da itama ba za ta amince da zuwan waɗanan mutanen a gidan su ba.

Su Hamma Jibo ma duk sun shigo sun zazzauna. Hamma Kabiru na kusa da Lamiɗo.
Shi kuma yana fusƙarta ɗakin da Ummu Salma take ciki ne yana tunanin halin da take ciki wataƙila ma tana can tana kuka haka kurum zuciyarsa ta fara zafi yana jin ɓacin ran da bai san dalili ba.

Bayan gaisuwa da kuma ta'azziya Alhaji Sherif ya kalli Hamma Jibo yana faɗin ina mahaifiyar ta su take anan? Hamma Jibo ya nuna masa Ammah dake zaune a ƙasan cafet da Hijabi.

"Sannu Hajiya Allah ya gafarta masa Allah ya sa ya huta."
Ammah ta amsa da Amin Amin.

"Mun gode Allah ya ba da lada."

Sai falon ya yi shuru, Shamsiya ce kawai ake jin ɗan jan majinanta na alamun tasha kuka.

Alhaji Sherif ya juya kaf bai ga Ummu Salma ba ya san ta tunda lokacin in dai Habib zai zo gaishe shi tare suke zuwa kuma abin da suka zo da shi ya shafeta ya kamata duk abin da za a tattauna tana wajen, Habib ya ba shi tabbacin an ce duka suna gida saboda wannan rashin da aka yi musu balle ma ya ce ai ɗan gida take aure yanzu.

"Na ce in ba damuwa ina son duk abin da za mu tattauna a nan wajen a ce ita wacce abin ya shafa tana wajen nan."

Alhaji Sherif ya faɗa yana kallon fuskokin su Hamma Jibo.

"In ba damuwa ina so ta fito itama domin abin da ya kawo mu saboda ita ne."

Ammah ta ce ba komai, Mami ta yi ma magana akan ta kira Ummu Salma.
Lamiɗo kamar ya ce ba sai ta fito ba sai kuma kawai ya fasa bai yi magana ba.

Habib kuma tunda aka ce aka kira Ummu Salma kirjinsa ke duka.
Shamsiya kanta na kasa tana tsiyayar hawaye ko daga ganin Ummu Salma ta san ta ga cigaba a rayuwarta sabanin su, to ko ba ta faɗa ba ita fa ɗan Sarki take aure wani jin daɗi ne ba ta cikin sa. Ita da suka cuta ne ita ce Ubangiji ya yi ma sakayya su kuma da suka cutar da ita sun girbi gwargwadon abin da suka shuka in da suka gode ma Allah sun yi saurin gane kurkurensu sun tuba ba sai lokaci ya ƙure musu ba.

Sai da Mami ta yi knooking ƙofar sannan Baɗɗo ta tashi ta buɗe mata, duk da Umma Salma na mata tsawan kar ta buɗe ta yi banza da ita ta zo ta buɗe ƙofar sai ga Mami ta shigo cikin ɗakin

Ta samu Ummu Salma na zaune gefen gado tana ta kuka ga Hanan ta saka kafafunta ta matse ta, ta hana yarinya kuka sai hawaye take yi, domin cewa ta yi in dai ta yi mata kuka sai ta yi mata duka shine Hanan ta kama bakinta amma tana ta hawaye tana son fita ne Ummu Salma ta hana ta.

"Me ye haka?

Mami ta faɗa tana jawo Hanan daga kafafun Ummu Salma.

"Mami kin ga ni ko! Tun ɗazu nake yi mata magana tana ƙin kula ni."

Baɗɗo ta gama faɗa cikin jin haushi. Ita fa ba zuwan su Habib take ji ma haushi ba sai Umma Salma meye na zama kina kuka a kan waɗanan mutanen? A yadda ta ga Shamsiya tun kafin ta ga Habib ta san haƙƙin Umma Salma bai bar su sun zauna lafiya ba.

Mami ta hau share ma Hanan hawaye wacce ta yi lamo a jikinta tana sauke ajiyar zuciya.

"Ba ki da hankali ne Ummu Salma.?

Mami ta faɗa tana mai kallon ta. Sai kawai ta fashe da kuka har da sauti.

"Mami me ya sa za ku saurare su?
Take faɗa hawaye na kece mata wasu na zubowa wasu na sake tunkuɗowa.
Zuciyanta na yi mata wani irin zafi.

"To me zai rage mu in mun saurare su?. Su suka neme mu, ba mu ne muka je wajen su ba."

"Mami bana son ganin su, bana son su zo kusa da ni ko kusa da y'ata. Bana so a a raba ni da Hanan."

"To daman wa ya ce za a raba ku? Shi da ya ce ba ya son cikin ya kuma ce ya bar miki ai ba maganar kuma Hanan."

"Mami da gaske kike yi?

Ummu Salma ta tambayeta bayan ta ɗan dakata da kukanta.

"In sha Allahu."

"Nima fa abin da nake ta faɗa mata kenan tana ta kuka wai ba wanda ya isa ya ɗauki Hanan daga wajenta na ce in yana da kunya shi Habib ɗin ai ba zai ma fara wannan maganar ba."

"Ko ma ya yi maganar ba shi da wannan hurumin Aisha. Ɗiya ta Ummu Salma ce har abada."

Jin kalaman Mami sai kukan Ummu Salma ya ragu fargabanta daman a ce za a raba ta da Hanan zuciyarta ba za ta iya ɗauka ba.
Received at 11:37Reactions: ❤ 13, 👏 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Shiga tiolet ki wanko fuskarki. Mu je falo ana magana dake."

"Ni kuma Mami?

"Ke sun ce suna son duk abin da za a tattauna kina wajen."

Kokarin sake fashewa da wani kukan take yi Mami ta ce me ye haka? Magana ce kawai ba wani abu ba.

"Kuma a yadda na ga shi Habib ɗin ai nadama ce fal a tare da shi duk ya lalace daga shi har maciyar amanar ƙawar taki."

"Na gan ta Mami duk ta bushe. Shamsiya yar gayu ce amma ji beta kamar yar gudun hijara."

Maganganun su Mami ya sa ta shiga toilet ta wanko fuskarta Hanan kuma har ta yi barci a jikin Mami sai ta kwantar da ita a saman gado Mami na gaba Ummu da Baɗɗo na bin bayanta har falo, Baɗɗo ce ke rike da hannun Ummu Salma wacce ke tafiya a hankali gabanta na faɗuwa ba ta son ko ganin Habib da Shamsiya domin sun yi sanadiyar samar da wani taɓo a cikin zuciyarta.

Tunda suka shigo falon kallo ya dawo kan su, musamman ma Ummu Salma can gefen Ummu Balki Baɗɗo ta zauna a kasan cafet sannan Ummu Salma ta zauna a gefenta ba ta ɗago kai ba balle ta tantance mutanen dake falon amma tabbas ta ji duka idanuwa a kanta.
Habib ta kasan idanuwa ya yi ta kallon Ummu Salma tun shigowanta wani abu na yin rassa a zuciyarsa.

Ammah ta kalli Ummu Salma sannan ta juya tana ce ma Alhaji Sherif ga Ummu Salman nan ta fito.

"Sannu baiwar Allah. Sannu ya ƙarin haƙuri?

Ta ɗan ɗago ta kalle shi ta gane shi, mutumin kirki ne ta amsa masa da yauwa haƙuri da godiya cikin sanyin murya amma a ɗan shaƙe alamun ta sha kuka.
Habiba na gefe tana ta kallon kowa ɗaya bayan ɗaya addu'a take yi Allah ya sa kar su yafe ma Habib domin tunda ya ƙi sakinta ba ta fatan ya samu salama daga shi har Shamsiya da ta fahimci tunda ya dawo da ita ya canza.

"Na so a ce lokacin da muka zo mahaifinku na raye shima Habibu ya roƙe shi gafara, domin lokacin da abubuwa suka lalace zuciyarsa ta ɓaci matuka. Sai dai haka Allah ya so muna fatan Allah ya yi masa rahama."

Gabaɗaya falon aka amsa da Amin Amin

Ya ɗan yi shuru ya ja fasali sannan ya fara magana.

"A baya ko na ce shekaru huɗu a baya ƴa'ƴanmu sun haɗa mu danganta a waje ɗaya ni ne nan da kaina na zo nan gidan muka haɗu da magabatan wannan yarinyar muka nema ma Habib auranta kuma aka bamu cikin darajawa da ƙimantawa, auren su ya sa alaja ta ƙullu a tsakanin mu, muna ta jin daɗi da fatan alheri kwatsam matsaloli suka dinga faruwa a tsakanin ma'auratan,  matsalan ciki da shi Habibu ya ce ba ya so sai an zubar ita kuma ta ce ba za ta zubar ba. Matsalan da muka kasa gyarawa har ta kai su ga rabuwar, rabuwar da ya yi sanadiyar yanke duk wata alaƙa dake tsakanin mu daku gabaɗaya."

Alhaji Sherif ya yi shuru kansa na ƙasa. Kafin ya cigaba da faɗin.

"Allah ne shaida na, ga Habibu nan zaune ga uwarsa nan a zaune ta san yadda na yi na yi da yaron nan akan ɗiyar ku amma bai saurare ni a wancan lokacin ba. Lokacin da ya saketa shi kaɗai ya yanke hukuncinsa ban sani ba lokacin da Mahaifinku Allah ya jiƙansa ya kirani yana faɗa mini abin da ya faru na ji takaici da bakin ciki dalilin haka yasa na ce na cire hannuna daga rayuwar Habibu tunda ba ya jin magana sannan ba ya jin shawara. Wallahi ɓacin rai ne da baƙinciki suka sanya tunda mahaifinku a wancan lokacin ya fusata ya ce sun yanke dukkan wata alaqa dake tsakanin ɗiyarsu da Habib kar ya sake neman su, nima na aminta da hukuncinsa. Daga lokacin na koma gefe ina jiran ranar da Habibu zai yi nadamar duk abubuwan da ya aikata wannan lokacin ya zo kuma nadamar tasa ne ma ya kawo mu gare ku"

Falon ya yi shuru ana sauraran sa.

"Da farko na ce ni ban zo ba saboda abin da Habibu ya aikata mai girma ne amma nadamarsa da roƙon mahaifiyarsa ya sa na amince na taho. Ga shi nan ya yi nadama duk abin da ya aikata ga ɗiyarku da gare ku gabaɗaya don Allah ku yi haƙuri ku yafe masa muma ku yafe mana gabaɗaya."

Falon ya sake yin shuru.
Alhaji Sherif ya cigaba da faɗa musu irin rayuwar da Habibu ke ciki a yanzu, ya fahimci cewa haƙkin Ummu Salma ne ke bibiyan shi, shi kuma ya matsa sai sun zo sun mara masa baya ya nemi gafaransu gabaɗaya.
Received at 11:37Reactions: ❤ 7, 😁 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Lokacin sheɗan na jagorantan sa, yana ganin duk abin da ya yi daidai ne, ni sai daga baya ma nake ji a she ita matar da ya aura daga baya ƙawar ita yar wajen ku ne, ashe cin amana suka yi, to gabaɗayansu sun ga sakamakon su tunda itama ko wata biyu ba a yi da mayar da auren su ba. Ya sake ta sun rabu sama da shekaru biyu kuma duk hakan na cikin sakamakon cin amanar da suka yi ne."

Baɗɗo ta kalli Ummu Salma itama ta kalleta, Baɗɗo har da mirmishin mugunta tabbas Ubangiji ya amshi addua'anta ya ɗanɗana ma Habib da Shamsiya guɗan su maciya amana ne

Ummu Salma kuma ta kasa jin tana farinciki ne ko baƙinciki, domin zuciyarta a ƙuntace take.
Gwaggo ce ta karɓi Alhaji Sherif tana sake ba da haƙuri tare da bayanin abubuwan da suka faru da Habib marasa daɗi.

"Ya yi nadama ku duba tubansa ku yafe masa kurakuran sa."

"Sai da ya rasa komai ne sannan ya san ya ma ƙanwarmu ba daidai ba ko kuwa tun yana da Habib ɗinsa mara mutumci ne ya gane ya yi kuskure?

Hamma Abdullahi ya watsa musu tambaya domin shi duk ya fahimce su, shegen ya yi nadama ne lokacin da ya rasa duk abin da zai yi taƙama da shi.

"Wannan kuma sai dai shi Habibun ya amsa, Kai Habibu matso kusa ka yi magana."

Alhaji Sherif ya faɗa yana ya fito shi, ya janyo shi ciki ya ƙariso kusa da kafafuwan Alhaji Sherif.

Jikinsa har rawa yake yi, ya ma kasa ɗagowa ballatana ya yi magana.

"Ka buɗe baki ka yi magana wannan ita ce damar ka."

Gwaggo ta yi masa magana ganin yana ta rawan baki  ya kasa magana.

"Ku yi haƙuri, ku yi hakuri."

Habib ya faɗa muryansa na rawa kamar zai fashe da kuka

"Nadamar da na yi wallahi ta gaskiya ce. Duk abin da na yi ma Ummu Salma haƙƙinta ya bi bayana cikin da na ce bana so na wulajanta Ubangiji ya jarabceni da son yara amma bai sake ba ni ba. Domin ya nuna mini ya ba ni kyautar a baya na ce bana so yanzu kuma ina nema ya hana ni. Wallahi summa tallahi na yi nadama. Nauyin dake kirjina daman na nemi gafaranku ne sannan na memi yafiyar Ummu Salma in ba ta yafe mini ba rayuwata ba za ta ga dai-dai ba."

Ya ƙarishe faɗa yana kuka har da sauti. Falon ya sake yin shuru.
Kowa kallon Habib yake yi daman haka rayuwa take ga aikata alheri ko domin watarana.

"Allah ya kyauta ba komai Allah ya yafe mana gabaɗaya."

Hamma Jibo ya faɗa yana kallon Habib.

"A lokacin da abin ya faru min ji ba daɗi amma tunda har komai ya wuce shike nan ka je ka cigaba da rayuwarka mun yafe maka."

"Ko ba komai ya ga sakamakon abin da ya aikata."

In ji Hamma Mustapha.

"Ammah ki yi haƙuri ki yafe mini."

Habib ya faɗa cikin rawan murya.

"Ba komai Habib, Ubangiji ya yafe mana gabaɗaya."

Ammah ta faɗa kanta na ƙasa tana jinjina ma rayuwar nan da komai cikinta sai tarin ƙalubale.
Shamsiya ma tana kuka tana cewa Ammah ta yafe mata.

"Ba komai Shamsiya Allah ya kiyaye na gaba."

Ammah ta sake faɗa tana kallon ta, yadda duk ta lalace kamar da wacce ta sani a baya da wannan Shamsiyar akwai bambamci.

Habib ya ɗaga idanuwana ya kalli Ummu Salma kanta na ƙasa ya kira sunanta

Lamiɗo sai da ya runtse idanuwana.
Me ya sa zai kira sunan ta?
Yadda ya kira sunan na ta ne ya sa kawai ya ji yana fusata.

Ummu Salma ta ɗago ta kalle shi amma ba ta amsa ba.
Akalla dai ya girbi abin da ya shuƙa.
Taji daɗi domin sun ɗanɗani abin da suka ɗanɗana mata aƙalla dai ko ba kai na ta ba suma sun rayu cikin ƙunci.

"Ki yi haƙuri don Allah ki yafe mini."

Ta yi shuru tana mai kauda kai. Wani abu na taso mata sun fama mata gyambonta.
Hawaye suka kece mata amma ta kasa magana.

"Ki yi hakuri don Allah ki yafe mini. Na yi nadamar duk abubuwan da na yi miki."

Nan ma shuru sai hawaye, ji ta keyi kamar ba za ta iya yafe musu ba.
Gwaggo ta saka ba ki tana faɗin.

"An san an ɓata miki, amma don Allah ki yi hakuri ki yafe masa."

Hajiya Sahura ma ta saka baki haka ma Alhaji Sherif amma ya ce ba za a tursasa mata ba. An yi mata ba daidai ba ta yafe wannan imani ne in ma ba ta yafe ba, ba wanda zai ga laifinta.

Mami ta juya tana kallon Ummu Salma yadda take kuka ta kasa magana.
Lamiɗo kuma ya kasa gane yanayinsa, me ya sa taki magana kawai ta ce ta yafe su bar gidan ba ya son ganin Habib kwata kwata.
Received at 11:37Reactions: ❤ 9, 😁 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Shamsiya ce ta tashi daga in da take zaune ta ƙarisa gaban Ummu Salma ta durƙusa a

Please Login or Register in order to submit comment