Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk dare suna gidan saboda ɗebe ma Ammah kewa sai wajen goma na dare suka koma gida Harira ta sha zama ita kaɗai.

Washegari a gida suka yini ba su fita ko'ina ba
Baɗɗo ce ta zo ta kawo mata garin goriba da aya daman ita ta ce ta siyo mata lokacin Lamiɗo na barci ba ta wani daɗe ba ta tafi ba zama yanzu tunda ta zama yar kasuwa.

Ranar Laraba jirgin safe Lamiɗo ya bi zuwa Katsina ya kwana ɗaya ya dawo alhamis da safe.
Ya ce kuma a gobe za su wuce Ummu Salma ta ɗauki ƙalilan abin da za ta buƙata.
Sai gashi tana faɗa masa za ta yi guzirin kasa a jirgi kallonta kawai yake yi ya ma kasa magana.

Tunda ya dawo daga Daura ta ganshi sai a hankali ya shge ɗaki ya fi awa huɗu ta ɗauka ma barci yake yi sai da shiga ta same shi idanuwansa biyu.
Gefensa ta zauna tana kiran sunan shi ya ɗan muskuta yana kwance ne daga shi sai bakin dogon wando jikinsa ba riga.

"Meke damun ka?
Tunda ka dawo ba ka da walwala! Ko wani abun ne ya faru? Ki jikin Mai martaban ne?

Duk a jere ta yi masa tambayoyin tambayar ta ƙarshe na da alaƙa da damuwarsa amma ba zai iya faɗa mata ba.
Kawai sai ya jawo ta jikinsa ya ce ta zo su kwanta.
Lokacin wajen biyu ne na rana.

Ba ta yi musu ba ta lafe a jikinsa yana so hankalin shi ya ɗauke daga tunanin tattaunawar da suka yi da Mai martaba a daran jiya ne.

Shi yasa ya ce ta yi masa hira ko wani iri ne, sai ta fara ba shi labarin littafin da ta fara saurara daga tashar tsakar gida na Ɗingishin kwaɗo.

"Yanzu kuma an daina kallo an koma jin littafin?

"Kallon ne duk baya mini daɗi yanzu."

Mirmishi kawai ya yi, ya tuna a baya yadda har wani shauƙi Umma Salma ke jin in tana kallo ita ta koya masa anma sai yana tare da ita in ba sa tare baya ma tunawa da wani kallo ba shi ke gaban shi ba.

Labarin take ba shi, amma ba ita yake saurarawa ba.
Ya tafi tunani ne, tunanin maganganun Mai martaba kamar na wasiyayya kamar na jaddadawa kamar na umarni.

Sun daɗe ba su yi wannan maganar ba sai jiya ya ɗago masa.

"Muhammadu ina maganarnmu ta kwana? Da gaske nake yi ina so ka gaji wannan karagar, a yan'uwana babu namiji duka mata ne kuma mace ba ta mulki, ɗan mace ba zai yi mulki ba in dai akwai ɗan namiji. A cikin ya'yana kai ne Babba kuma kai ne nake ganin yafi dacewa da ya gaje ni. Bana so sarautar gidan Shitu ta suɓuce mana, ka je ka sake yin tunani wannan shine magana ta ƙarshe. Zan yanke hukunci kuma duk abin da na yanke za ka bi umarnina ne."

Kalaman Mai martaba suna nufin ya ajiye mafarkinsa da burinsa ya zo ya yi sarauta.
Ba zai iya ba, kuma ba zai iya faɗa ma Mai martaba ba zai iya ba ɗin amma ya shiga damuwa bai san dalili ba yana ji kamar Mai martaba zai iya aiwatar da abin da ya faɗa. Maganar ya ce daga shi ne sai Ubangijinsu ko Fulani ba ta san sun tattauna wannan maganar ba ya je ya yi tunanin in ya sake kiran shi Umarni kawai zai bi.

Addu'a yake yi Allah ya ƙara ma mai Martaba lafiya ya yi tsawon ran da zai yi ta mulkin jama'ar garin Daura.

Washegari Jumma'a da za su tafi, Ummu Salma sun je asibiti tare da Lamiɗo ta yi ma likitan bayanin za ta koma Lagos can za ta cigaba da ganin likita ya yi mata rubutu a wata takarda ya ce duk asibitin da ta za ta koma tana ba su wannan takardan za su san matsalolinta su dora daga in da suka tsaya.

Ba su ɗauki kaya da yawa ba akwati ɗaya ne sai ƙaramar jaka na Harira
Ƙaasarta kuwa dakyar Lamiɗo ya lallaɓata bata ɗauka ba ya ce wa zai barta ta shiga jirgi da ƙasa ta bari zai sa ko Hamma Abdullahi ya sako ƙasar a mota a kawo mata har Lagos sannan ta haƙura.
Received at 17:29Reactions: ❤ 17, 🔥 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Shima dai ya faɗa mata ne amma wayau kawai ya yi mata. Sun koma gidan sun yi musu sallama kanzonta an dake mata shi sai ta ɗauka ta saka cikin kaya
Shi ya tuƙa su zuwa filin jirgi a can ya bar motar Hamma Abdullahi zai je ya ɗauka daga baya.
Jirgin karshe 12:30pm suka bi zuwa Lagos.

*

Sun sauka a Lagos bayan azahar ƙarfe ɗaya da wasu mintina. James ne ya zo ya ɗauke su daga filin jirgi zuwa gida.

Sai ga su a sabon gida. Daman ai sun zo gidn tun lokacin da za su duba gabaɗayansu. Da aka saka funitures ne lokacin sun taho Adamawa
James da Baban adila suna gaisheta cikin girmamawa suma sun ji daɗin ganin ta.

Yara suna gida ba makaranta sun shigowa falon suna kallo ai suna ganinsu yaran suka rumtuma wajen Umma Salma sai da Lamiɗo ya janye Sultan yana faɗin su yi mata a hankali ba ta da lafiya. Hanan ta san uwarta sai murnan ganinta take yi tana kiran sunanta Mahma.

Hayaniyar yaran ya fito da su Sabuwa gabaɗayan su.
Suka duƙa suna yi ma Umma Salama sannu da zuwa ita da Lamiɗo.
Bilkisu bata nan tana wajen aikinta.

"Welcome back second Madam."

In ji Debora, haka Anitha ma ta yi ma sannu da zuwa
Harira suka rumgume ita da Hidaya daman ta su ta fi zuwa ɗaya.

Lamiɗo bangarenshi ya wuce ya ce Sabuwa ta raka Umma Salma bangarenta.
Sai kallo gidan take yi, wato funitures ɗin da aka saka masu kyau yan waje duk haɗuwar wancan gidan da ta fara ruɗewa ranar da ta gan shi sai da wannan ya fi mata haɗuwa.

Key ɗin bangarenta na jikin kofar korodin ɗin da zai kai ta cikin bangarenta buɗewa kawai suka yi suka shiga. Falon ta ya yi kyau kalan blue ne kujerun da fentin ma irin na zamani ne irin waɗanda take gani a fina finan turawa. Falon ba shi da wani girma amma ya tsaru ga faskekiyar plasma ta shiga duba bedroom ɗin su masha Allahu babu abin da babu, kitchen ɗin ya fi birgeta. Har da store ga kayan abinci sai ka ga dama za ka fita can main falo.

Ta zaɓi ɗakinta ta ce Harira ma ta zaɓi ɗaya ta shiga.
Na kusa da ita ta shiga ta ajiye kayanta.
Salla suka yi sannan aka gabatar musu da abinci Ummu Salma ta ce ba ta ci, kanzonta da ta yi guziri ta ce da yamma za ta jiƙa ta ci.

Barci Umma Salma ta kwanta sai la'asar ta tashi shima ɗin Hamma Lamiɗo ne ya shigo har ɗakin sai ji ta yi ana yi mata tafiyar tsutsa a kafarta tana buɗe idanuwa ta gan shi da shirin shi na tafiya masallaci ya ce ta tashi ta yi salla.

Bayan ya fita ta miƙe ta faɗa tiolet Allah ya sa bangarenta ba a taɓa amfani da shi ba. Ba ƙamshin komai sai na sabin kaya. Bayan ta idar da salla ta dauko kanzonta ta fito, ta jira Harira a falo ta ba ta, ta ce ta jiƙa mata da maggi kawai da gishiri.
Shi ta samu ta saka ma cikinta tana cikin cin ne ma sai ga su Sultan sun shigo

Beena da Hanan suka saka rigiman sai sun ci sun ɗauka wani kayan gabas ne tana ba su, cin farko suka fara shirin dawo mata da shi.

"Ai sai kun ci shi."

Take faɗa tana musu dariya.
Hanan ta zubar da na bakinta.
Beena ta bi bayanta suna yamutsa fuska.

"Karyan tsiya kuke yi, kun san ba za ku ci ba kuka ce za ku ci?

Kamar za su yi kuka suka yi tsuru-tsuru sai ta koma tana yi musu dariya Sultan na taya ta.
Sai suma suka fara dariyan Harira ce ta gyara in da suka zuzzubar.

Yaran suka ɗebe mata kewa. Da yake duk an haɗa musu tasoshin ta kunna musu Tv a tashar Mbc3 ana cartoon.
Suna ta bidirinsu a falo, ita kuma sai ta shiga ciki ta dauki wayarta ta kira Mami suka gaisa take faɗa mata Hamman ya taho har yau sun dawo Lagos.
Bayan ita ta kira Baɗɗo sun yi magana da yake ba ta faɗa mata za ta zo Lagos ba.
Tana ɗakin ma suka biyo ta ciki dole ta tarkata su zuwa falo nan suka sha zamansu itama tana biye musu.

Har mangariba sannan ta ce a tashi a yi salla.
Sai ga Hamma Lamiɗo ma ya shigo ya ce Sultan ya zo su tafi massllaci. Su Hanan kuma tare suka yi na su salla a falo. Bayan sun idar ta ce su karanta azkar suka fara rerawa tana ɗan yi musu gyara kaɗan. Har bayan isha'i suna bangaren Ummu Salma Bilkisu ta dawo tun bayan la'asar Sabuwa ta faɗa mata Yarima ya dawo amma ba ta faɗa mata dawowar Ummu Salma ba ganin ba huruminta ba ne.
Received at 17:29Reactions: ❤ 10, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Wanka kawai ta yi a bangarenta ta je bangaren Lamiɗo shima kuma bai faɗa mata ba, ita kuma ta sakankance da cewa ya saki Ummu Salma tafiyar da ya yi wannan karon shi yasa ba ta damu ba. Yara kuma da ta ga ba ta ji motsin su ba, ta dauka suna bangarensu ne ba ta neme su ba.

Sai da za su yi dinner ta ga Sultan a falo babu Hanan ba Beena ba ta yi magana ba ta ɗauka suna ciki ne. Lamiɗo ya yi wanka sannan ya fito sanye da dogon wando da riga mai gajeren hannu.
Ya zauna a saman dinning Debora ta jera abincin cikin birgewa.

"Sultan ina Beena?

Bilkisu ta tambaya tana serving ɗin Lamiɗo.

"Suna wajen Anty Umma."

Kaɗan ya rage cokalin hannunta bai faɗi kasa ba tsabar yadda ta razana.

Ta zaro ma Sultan idanuwana amma ta kasa magana.

"Go and call them"

Lamiɗo ya faɗa yana kallon Sultan yaron ya mike har zai tafi sai ya dawo.

"Papa Anty Umma? har da ita?

"No."

Ya tuna ba ta son ƙamshin komai.

"Ba ta son ƙamshi."
Ya samu kanshi da ba ma Sultan amsa.
Sultan yaro ne bai fahimta ba sai ya yi wucewarsa kawai.

Bilkisu ta kasa iya motsa hannunta tsabar firgici.
Wata Anty Umma? ba dai Ummu Salma ba.
Kafafunta suka fara rawa, da hannunta ta kasa cigaba da abinda take yi.

Ba ya saketa ba? Me ya dawo da ita?

"Akwai matsala ne?

Ya faɗa yana kallonta ganin ta tsaye ta kasa cigaba da abin da take yi.
Lokacin ne ta farga ta yi saurin zuba masa ta tura masa filet ɗin faten dankalin turawan gabansa.

Ta koma ta zauna tana jin zufa duk da sanyin A.C dake wajen.

"Is she back?

Ta faɗa tana kallon shi, idanuwanta har sun tara ƙwalla zuciyarta na wani irin rawa.

Ya kalleta amma bai yi magana ba.
Sai da ya fara cin abinci har ta cire rai da zai yi magana.

"She is."

Kaɗan ya rage zuciyarta ba ta buga a lokacin ba. Ta yi masa zuru da idanuwana kawai tana kallon shi.

"Bilkisu."

Ya kira sunanta.

"Ummu Salama."

Sai ta ga ya yi mirmishi har gefe da gefen bakin shi ya motsa.

"She is pregnant."

Kirjinta ya buga dam!.

"Ciki?

"Ba ka sake ta ba?

Maganar ta fito ne daga zuciyarta ba tare da ta sani ba.

Sai da ya tsaya da cin abinci yana kallonta.
Sai ta yi saurin cewa.

"A'a na ɗauka kun rabu ne."

"Na ga ita ta ce ka sake ta."

Ta faɗa ne domin ta kare kanta. Ba ta san ta sake kwaɓa komai ba ne

Lamiɗo ya kalli Bilkisu kafin ya kauda kai ya cigaba da cin abincinsa tana so ta yi magana ta kasa bakinta ya yi nauyi ga zuciyarta na rawa, tana tunanin Ummu Salma ta bar mata mijinta ashe zaune ba ta kare ba ciki ma gare ta.

Dowawar su Sultan ya dakatar da ita daga kan maganar da ta yi niyar yi, kanta ta dafe ta bata komai kishi ya sa ta furta abinda ke cikin zuciyarta.

Sultan ne ke ba da labarin yadda su Beena suka ce za su ci abincin Anty Umma da yadda suka zubar da na bakin su. Lamiɗo har yana murmusawa wa zai iya cin wannan abincin na Umma Salma ai sai ita. Bilkisu na zaune kamar ba ta wajen ta kasa cin abinci tana ta wasa da cokalin hannunta Lamiɗo kuma kallo ɗaya bai sake yi ma Bilkisu ba.

Abinci ma bai ci da yawa ba ya tashi. Ya bar Bilkisu anan ya wuce bangaren Ummu Salma.
Har ta yi shirin kwanciya Harira kuma tana bangaren su Sabuwa.

Gefen gado ya zauna ya janyota kan cinyarsa ta zauna yana shafa cikinta.

"Kin ci abincin ki?

"Uhm"

Ta faɗa tana toshe hanci domin ya yi wanka da sabulu mai kamshi kayan jikinsa ma suna ta ƙamshi.

Fuska ya kwaɓe kamar zai yi kuka.

"Wari nake yi?

"Ni yanzu ba a son ƙamshi na."

Yadda ya yi da fuska ne yasa ta fara masa dariya shi kuma yana ɗan mirmishi.

Sakinta ya yi tunda ta ce kar ya saka ta amai.

"Hamma to yaushe za a aiko mini da saƙon?

Ya kalleta domin shi ya ma manta da wayaun da ya yi mata.

"Kasar da ka ce kar na ɗauko."

"Oh na tuna."

Ya faɗa yana dafe kansa.

"Kasar nan fa babu sai dai a samo miki anan"

Ummu Salma ta fara kallon shi kamar za ta yi kuka.

"James zai samo miki mai ƙamshi."

Ya faɗa yana jan karan hancinta.
Sannan ya sumbaci goshinta.
Cewa ya yi ta kwanta ba gaddama ta koma ta kwanta ya rufa mata bargo.
Ya rike tafin hannunta yana mata wani irin kallo.

"Good night Sweetheart."

"Good night Darling."

Ya yi dariya mai sauti.

"Ni Hamma Darling"
Received at 17:29Reactions: ❤ 19, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ya gama faɗa yana dariya.

"Ni ƙanwa ni Sweetheart."

A tare suka yi dariya sannan ya saki hannunta.
Ya yi mata bye itama ta yi masa hasken wutar ya kashe mata ya kunna mata A.C tunda yanzu tana son sanyi sosai.

Yana fita falo ya haɗu da Harira ta shigo ta duka ta gaishe ya amsa.
Ya kalleta sau ɗaya ya kauda kansa.

"Me sunan ki ma?

In da amana ya kamata ya haddace sunan nan saboda yadda Ummu Salma ke jadadda masa


"Sunana Harira. Harira ranka ya daɗe."

Ta faɗa kanta na ƙasa cikin ladabi

"Umma Salama."

"Ki kula da ita"

"In sha Allahu ranka ya daɗe."

Ya wuce ya fita sannan Harira ta ƙarisa ɗakin Umma Salma ta leka ta ga har ta kwanta sai kawai ta rufe mata ƙofa ta shiga na ta ɗakin.

*
Bilkisu ta kasa zuwa bangaren Lamiɗo ko bai yi mata magana ba. Kallon da zai yi mata kaɗai zai kassara sauran ɗan kuzarinta.

Ta firgice da dawowar Ummu Salma, ba ta taɓa tunanin za ta dawo ba. Ta ɗauka ta bar mata mijinta kenan har abada. Abincin ma ta kasa ci Lamiɗo na ta shi itama ta tashi ta shige bangarenta.
Yaran ma Sabuwa ta kira ta ce in sun gama a kai su ɗakinsu a yi musu shirin kwanciya.

Tana cikin wannan fargaban ne sai ga kiran Lamiɗo ya ce ta zo, jikinta ya kama rawa ta riga ta yi ɓaramɓarama, ta furta abin da ke cikin zuciyarta.

Jikinta a sanyaye ta tafi bangaren shi. Ta same shi tsaye hannayensa harɗe a bayan shi.
Tana shigowa ya juyo yana kallon ta.

"Ranka ya daɗe."

Ta faɗa tana kakaro mirmishi.
Lokaci ɗaya tana gyara zaman rigar barcin dake jikinta.

Hannayenta ta ɗora a saman kafaɗan shi sannan ta sumbaci bakin shi.
Bai mayar mata da martani ba sai sunanta da ya kira.

Tana jin yanayin kiran sunan jikinta ya sake saki.
Kamar zai yi mata magana sai kuma ya fasa
Maganganunta ya sa ya fahimci bincike ta yi masa a waya ta karanta saƙonnin Ummu Salama, ya goge ma dukasaƙo sannan ya yi abin da bai saba ba ya saka ma wayarsa password.

Bilkisu tana da wani hali da ya fahimta, son shiga rayuwar shi da Umma Salama ahalin ita Umma Salama ba ruwanta da wannan. Yana so ya ce ta bari ba ya so sai kuma kawai ya ƙyaleta. Tambayarta ba ta bukatar amsa tunda ga Umma Salma har da ciki
Cikinta ya ɗuri ruwa ta ɗauka zai yi mata fada ne sai ta ji shuru.

Cikin farinciki ma suka kwana. Washegari asabar yana gida bai fita ba yara kuma sun tafi makaranta. Ummu Salma ta fara rigiman ita fa a samo mata ƙasa James ya yi magana ya ce ya shiga cikin gari ya diɓo kasa kala kala ya kawo masa.

An kawo mata duk wanda ta shinshina sai ta ce ba ta ƙamshi James wajen sau uku yana fita.
Shi kan shi mamaki ya kama shi mai oga zai yi da ƙasa? Bilkisu na bangarenta ba ta san ma abin da ke faruwa ba tunda yau tana gida ba ta je aiki ba. Ba ta son ma fitowa ballatana su haɗu da Umma Salma itama Umman Salman ko fitowa ba ta yi daga bangarenta ba tun jiya.

Ƙasa dai karshen ta na wajen flowers na cikin gida aka samo mata tace tana so yana ƙamshi. Saboda da safe lokacin da James ke ba ma wajen ruwa ta ji ƙamshin ƙasar.

Harira ta samo mata wata roba mai murfi ta jiƙa mata sannan ta kara jiƙa mata da ruwa. Sai goro da ta ce tana so ya hana ta tashin zuciya shima James aka tura kasuwa ya siyo mata.

Abinci kuma Harira ta yi mata irin tuwonta da miya daga kuka sai gishiri da farin maggi ba wanda ya sani tunda a kitchen ɗin bangaren Ummu Salma ta yi girki.

Sai litini da safe Ummu Salma da Bilkisu suka haɗu a main falo.
Lokacin da za su yi ma Lamiɗo rakiya zai koma wajen aikinsa.

Ummu Salma ta gaishe ta ta amsa tana kallonta.
Ko ba a faɗa ba ga cikin nan a tare da Ummu Salma. Tun kuma da Lamiɗo ya tafi sai su yi kwanaki ba su ga juna ba kowa na bangaren shi yara kuma yawanci a bangaren Ummu Salma suke duduma.

Suna waya da Mutanen jimeta, sannan suna waya da Lamiɗo maganar asibiti da ya ce ko za ta je in da Bilkisu ke aiki ne kamar na farko? sai ta ce aa, shi kuma bai matsa mata ba ta ce za ta samu wani asibitin ta je.
Received at 17:29Reactions: ❤ 16, 👏 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai da ta yi sati ɗaya da dawowa sannan ta fita. Motarta an kai wanki an saka ƙamshin nan da masu car wash ke sakawa sai da ta bari ƙamshin ya fita sannan ta fara fita da ita.
Ta nemi wani asibitin kuɗi anan anguwan Apapa ta je ta ga likita ta nuna masa takardan da aka bata a asibitin Jimeta.

Nan da nan suka buɗe mata fayel aka ɗora ta kan kulawa. Magani dai daga na karin jini sai na cin abinci kawai suka bata cikinta ya kusa shiga wata uku in ya yi wata uku za ta fara awo saboda conditioon din da take ciki, sun ce ta dinga cin abinci sosai ta ce ci amma tana amai sosai likitan ya ce ta ci ko da za ta yi aman ne.

Sannan ta dinga cin kayan marmari to gwara su tana son su musamman ayaba su Debora ta aika kasuwa suka siyo mata ayaba da yawa da su kankana ta saka a firizanta tana diɓa kaɗan kaɗan tana ci.

Zuwanta Lagos ya sa ta ɗan fara kiba ba kamar lokacin tana Jimeta ba. Hakan kuma nasaba ne da ta samu kwanciyar hankali.
Damuwarta guda ɗaya ne yanzu rashin Baffa wanda ta kasa daina kukan mutuwarsa ga azumi bai fi saura kwana ashirin ba.

Tabbacin Ammah ta kusa fita takaba. A group ɗin Ammah da Baffa ta ga Hamma Jibo ya ce za su taho da salla. In an yi salla an gama za a zauna a yi maganar rabon gado. Tabbacin da gaske Baffa ya tafi ya bar su. Ubangiji ya yi masa rahama amma har abada ba za ta manta da rashin Baffa ba.





*Janafty*
Received at 17:29Reactions: ❤ 16, 👎 1, 😢 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.


Tunda Lamiɗo ya tafi sai da ya yi kwana ashirin sannan ya dawo. Dawowarshi ya sa zuciyar Bilkisu ya kusa bugawa saboda kishi da baƙinciki.

Tunda ya tafi sai su yi kwanaki ba su haɗu da juna da Ummu Salma ba, Bilkisu na zuwa wajen aiki in kuma ta dawo tana bangarenta.
Yayin da Umma Salma ke yini a bangarenta ba abin da ke fito da ita duk abin da take so akwai shi a bangarenta. Yara ma nan suke dudumarsu in sun dawo makaranta in ma suna gida yanzu sun fi zama a bangaren Ummu Salma.

Su yi karatu tare, ta koya musu Qur'ani tana kuma koya musu azkar domin yadda za su tsare kansu sannan ta zaunar da su ta yi ta basu tarihin Annabawa.

Zamansu da Bilkisu kamar yadda faro ne haka ya cigaba da wanzuwa. Har Lamiɗo ya dawo ko sau ɗaya a cikin kwana ashirin ɗin nan wata ba ta ga wata ba. Sai da ya dawo ne suka haɗu da juna.

Abin da ya fara baƙanta ma Bilkisu rai shi ne Lamiɗo da kan shi yake bin Ummu Salma bangarenta ko ita ke da girki ko ba ita ba ce, ba ya jira shi da kansa yake bin ta har bangarenta.
In ranar girkinta ne kuma a bangarenta yake kwana.

Ta so ta share kar ta yi magana amma ta ga ba za ta iya ba. A matsayin Lamiɗo na Yariman Daura bai da ce yan aiki na gidan nan su gan shi yana kara kaina a bangaren Ummu Salma ba, sannan ga wani ririta da yake yi, ko cikinta na farko albarka na yanzu kam ko ƙoda in da yana da dama ba zai bari ya taɓa ta ba.

Kishi ya dinga murkukusanta daman ranar da zai tafi a ɗakinta yake da ya dawo sai ya sauka a wajen Ummu Salma sai da ta bari ya dawo ɗakinta ranar ma ita ce ta same shi a bangaren shi. Sau tari ita ke samunsa a bangaren shi ba ta jiran shi saboda shi shugaba ne, ta amince ita ce za ta bi shi, amma yarinya ƙarama daga zuwanta ta na neman ƙwace mata matsayinta sannan duk ta sauya mata miji a lokaci ɗaya.

Sai da ta bari sun kwanta sannan ta yi masa maganar.

"Ranka ya daɗe, ina so na yi wani gyara."

"I hope babu matsala ko?

Tana kwance a kan jikinsa ne, bai yi magana ba ta san kuma ba zai ce komai ɗin ba shurunsa na nufin yana sauraranta.

"Gyara zan yi maka. A matsayinka na Yariman Daura ko ba a matsayin miji ba. Kai Shugaba ne a gare mu bai dace a ce kai ne za ka dinga bin Ummu Salma bangarenta ba. Ba mu kaɗai ba ne a gidan nan Hadimai suna nan kuma suna ganin duk shige da ficen ka, koma mene ne ita ya kamata ta dinga biyo ka."

Ta ɗan yi shuru tana sauraran shi, amma ya yi shuru kamar ma ba ya wajen
Sai ta ɗago tana kallon shi a ɗan hasken dumlight ɗin dake ɗakin ta ga idanuwansa biyu kuma yana sauraranta ya kuma ji duk abin da ta faɗa.

"I'm sorry in na yi shisshigi amma na ga kamar bai dace ba ne."

"In kana son magana da ita. You can call her sai ta zo bangarenka ta same ka."

"Amma ka yi hakuri in ba ka ji ɗadin magana ta ba"

Shuru na wasu mintina kamar ba zai yi magana ba.

Ta sake ɗagowa tana kallon shi. Gashin ƙirjinsa take shafawa tunda ba riga a jikinsa.

"Ni na yi magana ne saboda matsayinka. Sannan bai dace ba ta kiran ka da girmamawa ba. Ya kamata ta dinga sakaya sunan ka a gaban mutane kai shugabanta ne."

"Ba ta da lafiya ne."

"Ba ta son ƙamshin komai."

Ya ba ta amsa sannan ya ɗan matseta a ƙirjinsa.

"Ba ta son ƙamshi?

Ta faɗa da sigan tambaya, domin daman ta ga ko yana gari ba ya kiran ta cin abinci sai ta fara zargin akwai wani abu.

"Cikin ne ba ya so ƙamshi."

"Tana yin amai."

Wani malolan abu ya tsaya ma Bilkisu a maƙoshi ya kasa wucewa.

"Tana buƙatar kulawa. Ke ma in bana nan ki kula da ita."

"Zan ji daɗin haka."

Sai ta kasa ma magana ita ai ta yi cikin nan har sau biyu ta haihu amma ba ta son wannan tsirfan

Please Login or Register in order to submit comment