Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai suna da shi a duka bangarorin su.


Sannan daga can gefe ɗakin yara akwai falo sai ɗaki ɗaya babba in da gadajensu yake falo kuma Tv ne da kujeru sai kayan wasan su, jikin shi kuma bangaren su Sabuwa sun samu babban falo da ɗakunan barci guda biyu.

Gidan ga haraban mai girma da motoci sama da goma za su samu wajen zama. Ga fulawowi masu kyau da Lamiɗo ya sanya James ya siyo aka cuka ana kula da su.
Suma a waje akwai ɗaki ciki da falo wajen kwanan Baban Adila da James.
Wancan gidan yana rufe ne kuma har yanzu ma akwai sauran kayan sawan su a gidan tun da ba siyarwa za a yi ba, shi ya sa ba su damu ba sannan ma kayan sawan ne sun yi musu yawa.

A main falo akwai bangaren Dinning wanda duk wanda ya fito in ba wajen ya zo ba, ba zai gan su ba.
Bangaren Dinning ne sai kitchen daga gefen shi babban ne.
Debora ta gama shirya komai an jera shi cikin tsari.

Su suka fara zama akan dinning ɗin sannan Bilkisu ta je ta zo da yaran suna falon su. Sultan ke wasa da bindigarsa ta roba yana harba ma su Hannan suna buya sun yi kaca kaca da falon.

Sun yi wankan su tas da su kamar yaran turawa.
Suna ganinta suka nufeta suna gaisheta har da Hanan kan yaranta kawai ta shafa ban da Hanan ta ce su je Dinning Papa na jiran su, ba ta nuna ma Hanan tsana amma ba ta sakin ma yarinyar fuska ba ta iya munafunci ba.
Received at 07:54
11 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk da yarinya ce amma an ce ko mahaukaci ya san mai son shi. Hanan ta san Bilkisu ba ta son ta shiya sa itama ba ta shige mata.
In ka ganta da Lamiɗo sai ka yi tunanin shi ne mahaifinta suna da shaƙuwa sosai yana son yarinya kamar yadda yake son uwarta.
Sannan Anitha ma tana son Hanan saboda kwazon yarinyar da daɗin zama har su Hidaya ma in tana magana sukan ce kamar Umma Salma. Wacce ba ta dawo ba kuma ba halin tambayan Bilkisu amma da suka yi waya da Harira ta ce za su dawo in har Yarima ya je Adamawa.

Yaran suna zuwa ɗaya bayan ɗaya Lamiɗo ya ɗauke su
Suna ba shi peck a gefen kumatu suna gaishe shi ya amsa cikin farinciki yana shafa kawunansu.

Daya bayan ɗaya yana kiran sunan su.

"Sultan how are you?

Ya amsa da I'm doing fine Papa.

"Princesss Beena do you miss me?

"Yes Papa. I miss you"

Ta faɗa tana shigewa jikinsa.
Ya rumgumeta yana shafa kanta. Hanan ta ja gefen rigan shi ya juya yana kallon ta.

"Papa."

"My Hanan."

Takaicin Bilkisu yadda ya sauke Beena ya ɗauki Hanan tana yi masa zence da cancan muryanta ɗin nan
Tana kan cinyarsa har ta gama serving ɗin su, sannan ta ce Hanan ɗin ta baro jikin Papa ta zauna su ci abinci.

Sun fara cin abincin wajen ya yi shuru. Bilkisu ke kusa da Lamiɗo a layi ɗaya. Yaran kuma suna layi ɗaya Sultan na tsakiya Beena da Hanan a gefen shi.

Kamar an suɓuto da maganar daga bakin Hanan ta kalli Lamiɗo tana faɗin yaushe zai kai ta wajen Mahma? Ya kalleta yana juya cokalin hannunsa da yake shan romon ferfesun kayan ciki.

Kamar ba zai amsa ba sai can kuma ya ce sai sun yi hutun makaranta tana dariya ta ce har da wajen Mami da Daddy da Islam da Faruk da Barira ya ce duk za a kaita. Sultan da Beena ma suka ce za su je Lamiɗo ya ce gabaɗaya za su tafi.

Bilkisu ta kasa ta tsare tana son ta ji wata magana bai yi wata alama da za ta fahimci wani abu ba.
Ferfesun kayan ciki kawai ya ci da buredi sai tea ya ta shi ya shiga ciki su kuma ya bar su anan. Komawa ɗakinsa ya yi ya zauna a gefen gado ya janyo wayarsa bai taɓa boye wani abu ba sai akan Ummu Salma.

Ma'ajiyar hotunan ta ne waɗanda take tura masa a baya wasu hotunan shi kaɗai ya dace ya kalla shi ya sa ya tarkasu zuwa wani folder ya yi hidden na su sauran ne masu mutumcin ya bar su da kowa zai iya gani.

Wani hoto ne da ta yi masa ta saka wata shimi, lokacin cikin mai sunan Baffa har ya ɗan fara hudowa. Ana ganin shatin kirjinta ta cika ta yi fari ta yi kiba tana dariya a gaban madubi ta yi masa hoton ta tura masa. Hotunan ta sune ke deɓe maasa kewarta in ya taso masa.

Ba ƙaramin dauriya ya yi a cikin wattanin ba. Ratan da ya gina a tsakaninsu saboda ya samu natsuwar zuciyarsa ne da kuma lokacin da zai yi tunani. Kuma bukatar shi ta biya domin ya samu lokaci sosai ya yi tunani kuma ya samu mafita a wattanin biyun da ya hana kan shi kiran Umma Salma da zuwa wajenta ya yi mata afuwa sama da sau goma, ya fahimci rauninta ya fahimci halin da take ciki ya fahimci a lokacin tana cikin wani hali, tana buƙatar lallashi zuciyarta ba daɗi ya fahimci maganar da ta faɗa masa ba da gangan ba ne, wani abu ne da ya fito daga zuciyarta. A lokacin kuma tana cikin rauni wataƙila ba ta ma san ta faɗi maganar ba sai da ta fita. Ya yi mata uziri sannan ya yafe mata. Wattanin biyun da bai neme ta ba horo ne na laifin da ta aikata masa a lokacin da ya taho da ita ya fusata ba zai saurareta ba wataƙila da zukatansu ba su samu natsuwan da za su gano kuskuren junan su da yin afuwa ba.

Amma yanzu ya fahimci a kadamin da take a wancan lokacin, sannan ya yi mata uziri ba ƙaramin dauriya ya yi ba amma ya yi kewar Umma Salma kewar da ke kassara kuzarinsa ba shi da aiki sai kallon hotunan ta ko video ɗin ta bibiyan chart din su kawai yana saka shi jin daɗi ya daɗe da cire ta daga in da ya kai ta amma kuma ba ta kira shi ba, shi kuma ba ya son su tattauna komai ta waya sai ya je ga ta ga shi. Shi ya sa a wannan dawowar ya yanke shawaran zai je can Adamawa saboda Umma Salma sannan ya duba Ammah.
Received at 07:54Reactions: ❤ 10, 👍 1, 👏 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk da yana sanin halin da suke cikibyana waya da Ammah itama Umma Salma yana jin labarinta a wajen su Hamma Abdullahi.
A cikin su kuma ba wanda ya taɓa katarin faɗa masa Umma Salma na da ciki kowa a tunanin shi ya sani ne.

Mami ma farkon tafiyan shi da suka yi magana har wata magana ta faɗa masa ya kasa gane kan maganar kuma bai tambaya ba.
Cewa ta yi Allah ya ga hakurin su ga shi nan ya sake ba su wani rabon. Bai tambaya ba sannan bai damu da bin kadin maganar ba ballatana ya fahimci in da ta dosa. A tunanin kowa a bakin matarsa zai fara ji shi ya sa ba wanda ya yi tunanin bai sani ba.

Yana kallon hoton yana mirmishi ya saka tafin hannunsa ya shafa screen ɗin wayar daidai bakinta. Ya yi kewar komai na ta surutunta, hirarta kiran shi Hamma shagwaɓarta komai na ta, all ya yi missing. Kewarta na murƙuƙusan shi. kewar kasancewa da ita ya sha yin mafarkin sun kaɗaice da juna ya yi mata horo amma shi ne ya hora kan shi komai mene ta yi laifi kuma ya horata, ya yafe mata zai je su haɗu ya ba ta hakuri domin shima ya yi mata laifi, wani abu da ya ji ta ƙara burgeshi shi ne bata faɗa ma kowa halin da suke ciki ba personal life ɗinsu ne su zauna su warware shi.

Ranar lahadi zai tafi Adamawa hutunsa na kwana goma ne kaɗai zai koma bakin aikinsa. Zai je ya taho da ita, domin rashinta a gidan ma duk ba daɗi.

Yana nan zaune har lokacin salla ya yi sai ya fita daga kan hoton ya shiga tiolet ya yi alwala. Sannan ya fito ya saka jallabiya ya saka hula zai fita kenan sai ga Bilkisu nan suka yi sallama domin ta ce kafin ya dawo za ta tafi asibiti.

Yana fita haraba ya ga motar Ummu Salma lullube a cikin tamfol, ɗan kaɗa kai kawai ya yi ya wuce tunani ma ya manta bai nemi Sultan ba shi kaɗai ya tafi masallacin yana dawowa ya iske Bilkisu ta tafi sai su Sultan ya tambaya sun yi salla suka ce aa nan ya tara su zuwa ɗakinsu, suka yi alwala suka yi salla a gaban shi sannan ya ce kowa ya ɗauko littafan makarantan shi wanda ya fi ƙokari za a yi masa kyauta.
Suna rige rige, nan ɗakin yaran ya zauna har La'asar yana tare da su yana biye ma surutunsu.

*
JIMETA.

Yau ta kama lahadi ne, weekend kusan duka ma'aikata suna gida.
Tun safe Umma Salma ke doka ma Hamma Saddam waya ba ya ɗauka ta kira Hamma Abdulrahim shima bai ɗaga wayarta ba.

Kasarta ta daina ƙamshi tun jiya ta yi ma Hamma Saddam magana a chart ya ce yau da safe zai ɗibo ya kawo mata amma kuma ta ji shuru, ƙarfe goma na safe har ta gota kuma in ba ta shaki kamshin wannan kasar ba yau ba zaman lafiya.

Har ƙasan waje Harira ta fito ta ɗibo mata ta jiƙa ta shinshina amma ba ta ji irin ƙamshin da na anguwan su Ammah ke yi ba ta ce ba ta so amai ma ƙamshin ƙasan ya saka ta.
Ta kasa cin komai tunda garin Allah ya waye. Sai ta shaƙi ƙamshin wannan ƙasan sannan za ta samu sukuni da zaman lafiya.

Daman ba ta aiki Harira ke yin komai a gidan.
Sai ɗan abin da ba za a rasa ba kamar gyara ɗakinta girki ma ba ta yi saboda ba ta son shaƙan ko wani ƙamshi in abinci ya tafasa ta shaƙi kamshi yini za ta yi amai sannan ba ta son wari maggi ɗunkule in abinci ne za ta iya ci amma ba ta son ƙamshin shi, shi ya sa in dai Harira za ta yi girki sai ta kulle kitchen ɗin yadda ƙamshin abincin ba zai fito ba. Kamshin ƙasan nan ta anguwan su Ammah kaɗai take so.

Tana zaune falo ne, daga ita sai riga doguwar riga bubu ce mai sakewa, ba ta da nauyi cikin rigunan da Baɗɗo ta saro ne ta siya wajen kala huɗu ta siya ma Harira ma su take sawa tana jin daɗin su domin yanzu ba ta son saka kaya saboda zafi. Wannan cikin iska yake so da A.C ma take kwana ta yi ma likita ƙorafi zuwanta na ƙarshe ya ce saboda da cikin ne sannan da BP. masu hawan jini ba sa shiri da zafi.

Harira ta gama gyaran falon tana kitchen tana wanke-wanke. Ita fa ko warin moneyfresh ba ta so, sabulun wanka ma da na wanki take amfani da shi mara ƙamshi, duk ta tattara showe gel ɗinta da sabulanta ta ajiyesu gefe.
Lotion na shafawa ma a jiki yanzu ta daina shafawa, saboda ƙamshi.
Received at 07:54Reactions: ❤ 9, 🔥 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ko wani mai yana da ƙamshi har mankaɗe Ammah ta aiko mata ta dinga shafawa sau daya ta shafa ba ta kara ba wari warin ya dinga tashin zuciyarta.
Yanzu haka nan take wanka ba ta shafa mai ya fiye mata zaman lafiya.

Gajiya ta yi da zaman sai ta sauko ta zauna a saman cafet sannan ta miƙe kafafunta
Tv na kunne a tashar arewa24 hankalinta ba shi a wajen yana wajen wayarta da ke hannunta tana cigaba da kiran su Saddam amma ba su ɗauka ba.

"Suna can suna ta barci"

Ta faɗa a sarari kafin ta ɗan ja tsaki.
Ita fa in ba ta shaƙi wannan ƙamshin ba akwai matsala.

TV Ta ƙura ma idanuwana suna haska wani hausa film wai tarko. Ita yanzu ta rage ma wannan kalle kallen, tun rasuwar Baffa kamar an sauyata.

Bayan dawowarsu gidan sun daɗe ba sa kunna kallo.
Gabaɗaya komai ya fita kanta na waɗanda take ɗan bi a ma Tiktok ko Youtube duk ta daina bin su, girke-girken ma ta watsar da komai yanzu ta kanta take yi. Rasuwar Baffa ta sanyata cikin ƙunci sannan ga rashin jaririnta ga abin da ya faru tsakaninta da Hamma daga karshe ga cikin da ta samu duk sai rayuwarta ta zama kamar an juya ta daga sama zuwa ƙasa. Gwara ma littafan hausa da Baɗɗo ta matsa mata ta fara ji a youtube a tashar tsakar gida, na Mai sanyi ta fara sauraran wani littafi Ɗingishi kwaɗo na marubuciya Surayya Dee mai bojuwa, ta fahimci dai Baɗɗo na yin matan nan tunda har littafanta take matsa mata ta saurara.

Kuma ba laifi da ta fara sauraran ya fara mata daɗi, tunda karatun yanzu wahala zai zame mata. Ko Ep13 ba ta kai ba ta watsar sai tana cikin ji sai kawai tunani su yi mata yawa sai can in ta dawo ta ga karatu ya yi nisa baya ba ta fahimci komai ba. Tunda kuma ta watsar ba ta sake bi ta kan shi ba sam ba ta da natsuwa.

Kanta da ba ɗankwali ta sosa kalaba ne ya fi sati uku Baɗɗo ce ta zo ta yi mata shi. Ya tsufa shi ya sa yake ta ƙaiƙayi.
Da ta ga sun ƙi ɗaga wayarta sai kawai ta kira wayar Ammah ba ta jima tana ringing ba ta ɗaga wayar suka gaisa.

"Ammah ina tazuran samarin ki?

"Suna bangarensu suna barcin tunda suka shigo nan bayan sun dawo masallaci ban ƙara ganin su ba, ga abin karyawansu ma can a kitchen ba su ga dama sun tashi ba."

"Ammah ina ta kiran su ne ba su ɗauka ba."

Ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Na ce miki suna can suna barci ba yau lahadi ba."

"To Ammah ya zan yi?

"Na me kenan?

Ammah ta amsa mata.

"Kasar ne ta daina ƙamshin Hamma Saddam ya ce yau zai ɗibo mini da safe har yanzu shuru."

"Ai fa shurun ne, to ki yi haƙuri in sun ta shi sai ya kawo miki."

"Ammah ina son in shaƙi kamshin ne, ba ki ji zuciya ta ba."

A shagwaɓe take magana

"Harira to ta ɗibo miki nan kofar gida mana "

"Ta ɗibo ba irin na ku ba, ba ta ƙamshi kamar na kofar gidan mu."

"To"

Ammah ta faɗa a fili a zuciyarta tana faɗin wannan cikin akwai tsirfa. A kullum addu'arta Allah ya sauki Auta lafiya.

"Ammah in ban shaƙa ba ji nake yi kamar sheɗata za ta ɗauke kuma ba zan iya cin abinci ba."

"To ai sai dai ki yi haƙuri su tashi barcin."

Kamar za ta yi kuka tana tambayan Ammah ba wanda zai kawo mata.

"Babu sai ni ko Ummarki A'i."

Baƙa Ammah ta mayar mata ya sa ta fara dariya.

"Ki fara gwada cin ko goro ne. Saboda tashin zuciya."

"To Ammah ki ba ma Hamma Saddam ya kawo mini."

"Ba ni da shi, zan ce ya biya kasuwa ya siyo miki mai yawa ki gwada ki gani."

Ta amsa da yauwa, Umma A'i ce ta karɓi wayar tana mata faɗan ta rage shan kankarar nan da ta ga tana sha, cewa kawai ta yi to domin in za ta kwana tana bayani ba za ta gane ba wannan cikin na dabam ne wahala kawai yake ba ta.

Bayan sun gama wayar har shaƙuwa ma ta fara yi tana jin zuciyarta wani iri kofofin hancinta na buɗewa ƙamshin da take son shaka ba ta samu ba.

Ta ga dai su Hamma Saddam jiran su ma ɓata lokaci ne watakila ma sai yamma.
Sai kawai ta jwala ma Harira kira sai ga shi ta fito tana goge ruwan hannunta a zanin jikinta

"Gani ranki ya daɗe kina bukatar wani abu ne?

Ta faɗa tana duƙawa a gefen in da take zaune

"Harira ni fa na ce ki daina ce mini wani ranki ya daɗe, ki ce mini Anty kawai."

Ta gama faɗa tana hararan Hariran da ta sadda kai ƙasa tana ɗan mirmishu.
Received at 07:54Reactions: ❤ 9, 👍 1, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Aa ranki ya daɗe ai girman ki ne, na saba ne ba zan cewa Antyn ba ne.'

"Ke kika sani dai."

Ummu Salma ta faɗa tana ɗan muskutawa

"Gida za ki zo ki je, ba ma sai kin shiga ba ki yi tashar adaidaita ya tsaya ki samu ƙatuwar leda ki ɗibo mini kasa yadda zan daɗe ina amfani da ita."

"To ranki ya daɗe."

"Kin gama wanke-wanken?

"Saura kaɗan."

"To karisa sai ki zo ki tafi Harira wallahi wani iri nake ji kin san in ba kasar nan yau ba zaman lafiya Hamma Saddam kuma da na dogara da shi ina ta kiran wayarsa ba ya ɗagawa."

Harira ta miƙe tana faɗin bari ta ƙarisa da hanzari.
Ba daɗewa kuma ta gama ta dawo, tana zuwa Ummu Salma ta toshe hanci.

"Harira kina ƙamshin sabulun nan na wanke wanke."

Harira ta shinshina hannunta kuma ƙamshin take yi, shi daman yana da ƙamshi sosai.
Sai ta yi baya tana faɗin

"Kuma na wanke hannu."

"Shiga ɗakina a drower gefen gado ta hannun dama za ki ga kuɗi a farar takarda ki ɗauko dubu biyu"
Ta gama faɗa tana sake toshe hancinta zuciyarta har ta fara tashi da sauri Harira ta amsa ta shiga ɗakin Umma Salma ta ɗauko sakon Harira Amintaciya ce a wajenta ta sha gwadata akan kuɗi ba ta taɓa kama ta da laifin sata ba, tana son Harira domin duk abin da take so kafin ma ta yi magana ta aiwatar.
Shi yasa itama take kyautata mata, tuni ta saka Hamma Saddam ya buɗe ma Harira Opay a wayarta tana tura mata kuɗi ta tura can wajen danginta sannan tana saka mata kati wanda za ta siya data Harira ta yi karatu kawai ba ta gama sakandiri ba ne ta faɗa aikin bauta. Amma tana da burin nan gaba ta ba ma Harira jari da za ta tsayu da kafafunta wata rana in har ta samu miji ita da Hamma Lamiɗo za su aurar da ita.

Harira ta sanyo hijabinta ta fita Ummu Salma na cewa ta yi sauri karma ta shiga gida ta ce to.
Ta bar Umma Salma ita kaɗai TV na ɓaɓatun shi.

Fitan Harira ko minti talatin ba ta yi ba sai gata ta dawo, ta ce ta manta ba ta ɗau leda ba tunda suna da ledojin na cefanen da ake kawo musu, a hanya ta tsaya ta siya bakko ta kusa yin rabin ta da ƙasa.

Jikin Umma Salma har yana rawa ta dinga shinshinawa.

"Kai Harira aikin ki na kyau ta wajena."

Tana shinshina ƙasar har tana sauke ajiyar Zuciya.
Nan ta ce Harira ta ɗauko mata leda ta ɗiba ta jika mata shi da ruwa.

"Ba ki dai shiga gida ba ko?

"Ai kin ce kar na shiga ranki ya daɗe. Mutane ne dai na ta kallona sun ga ina ta ɗiban ƙasa."

Ummu Salma ta yi dariya kafin ta ce.

"Ai sai ki ce lalura ce ba da gangan ba ne."

Harira ta amsa da ba su mini magana ba amma mamaki suke yi na me zan yi da ƙasa haka, mai adaidaitan da yakai ni ma ya jirani sai da ya tambaya na ce masa na mai ciki ne ya ce wallahi shima matarsa ƙamshin yashi take so.

"Gwara da kika faɗa masa kar ya ce na asiri ne."

Dukkansu suka yi dariya. Sannan Harira ta tafi kitchen ta ɗauko mata roban gwangwanin madara da ya ƙare ta ce bari kawai a zuba a ciki ta huta da leda

"Kuma fa hakane, to zuba da sauri ki jiƙa mini, wannan kuma ki ɓoye mini a cikin kitchen"

Harira ta aiwatar da duka umarninta.
Lokacin da ta kai hancinta tana shaƙan kamshin har jikinta sai da ta ji ya samu natsuwa cikinta kuma ta ji kamar ya juya.
Shike nan ta samu zaman lafiya Hamma Saddam kuma sai wajen sha biyu da rabi ya kira ta haushi ya sa ba ta ɗaga wayarsa ba. Ba amfanin da zai yi mata kuma a yanzu ga ƙasarta a hannunta tana shinshina kamar wata mage.

Sallar azahar ya sa ta bar falo ta koma ciki ta yi salla. Ta kwanta tana ta barci saboda likita ya ce ta dinga samun barci sosai wajen uku na rana yunwa ya tashe ta, ta je kitchen ta nemo sauran tuwonta tun na shekaranjiya da Harira ta yi mata da miyar kuka ta ciro a firiza ta kunna gas ta ɗumama miyar ba manja ba maggi dunƙule sai gishiri shima kaɗan sai farin maggi, ba ta son ko wani ƙamshi.

Kodayaushe ta zo kunna gas sai ta tuna da wani abu ya faru farkon dawowarsu kawai ta shigo kitchen ta rasa abin da za ta yi, kawai sai ta kunna gas ta ɗora tukunya ta manta kawai ta koma ɗaki ta kwanta, Allah ya taimaka Harira ta zo kitchen ɗin ta ji ƙauri, da sauri ta kashe gas ɗin ta sauke tukunyar har ta fara ƙonewa da Harira ke faɗa mata shuru kawai ta yi ba ta san ta yi ba
Received at 07:54Reactions: ❤ 15, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
abubuwa suna yi mata wani irin tun bayan abin da ya same ta na rasa jarirnta, sannan tana zaune kawai sai ta dinga jin wani ƙara a cikin kanta, ƙaran mai yawa yana barazanar fasa kunnuwanta, chanje-chanje da dama take fuskata da ta koma asibiti ta yi musu bayanin likitan ya ba ta tabbacin alamomin cutar Eclampsia da ta yi fama da shi ne lokacin da ta haihu, amma ta gode ma Allah ta fita daga haɗari suma canje canje a hankali za ta daina fuskartarsu. Kullum ta yi salla sai ta yi ma Allah godiya da ya tsare ta da wannan cutar, domin tana da haɗari itama za ta iya ba da labarin haɗarin ta.

A kitchen ɗin ta ci tuwon nan ta wanke hannunta sannan ta koma ɗaki Harira na cikin ɗakinta wataƙila ta kwanta ne. Da ta koma ɗaki ba ta kwanta ba sai ta fara gyara kayanta wajen kwana huɗu kenan mai wanki ya kawo su da sauran ƙananun da Harira ta wanke mata ita kuma ta ce ta bar mata za ta gyara su amma ta kasa.
Sai da ta gama tas ta jera a wardrope sannan ta shiga tiolet ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito ba shafa mai take yi ba doguwar rigarta kawai ta material ta saka akwai tattara ta ƙasa sai aka sake ta. Akwai zanen baƙi a cikin material ɗin sai ta saka hula baka ta rufe kitsonta da ya tsufa.

Falo ta fito ta zauna a saman kujera tana canza tasha zuwa Saira movies ta ga suna maimaicin shirin gidan Sarauta.
Ba daɗewa sai ga Harira ta fito, tana tambayan abin da za a dafa.

"Harira ni fa ba cin abincin nan zan yi ba kullum sai kin tambaya ne?

Harira ta sunkuyar da kai ba ta yi magana ba.

"Ki je ki dafa duk abin da kike so Harira nan fa gidanmu ne."

"To ranki ya dade"

Har ta wuce sai ta dawo.
"Ba za a yi miki wani abu ba?
"Tuwo ne kuma ina ɗan da sauran shi, bari da safe sai ki yi mini wani"
Harira ta wuce kitchen tana faɗin Allah ya kaimu.

Ta bar Ummu Salma na kallo. Ta mayar da hankalinta kan kallo amma ba ta jin nishaɗin da take ji a da in tana kallo gata nan dai zaune kawai.

Adaidai lokacin da agogon bangon dake falo ya harba 4:30pm na yamma daidai ta ji ana buga ƙofa an yi knooking na farko ba ta tashi ba, ta ɗauka ma Saddam ne har tana tura baki.
To tun ɗazu ta so zuwansa bai zo ba sai yanzu.

Ta ji daɗin zaman kamar kar ta tashi sannan ga Harira na kitchen akwai ba da wahala ta ce ta baro kitchen ta zo ta buɗe ƙofa.
Sai biyu aka yi knooking sannan ta iya miƙewa ta isa ga ƙofar ta buɗe

Tana buɗe ƙofar ta juya ko kallon wanda ke tsaye ma ba ta yi ba.

"Sai yanzu? Ai Sai ɗan cikina ya bare da na tsaya jiran ka."

Ta faɗa tana komawa ta zauna a in da ta tashi.
Abin da ya ba ta mamaki jin shuru ba ta ji motsi ko surutun Hamma Saddam ba, shi da tun kafin ya shigo ake fara jin karaɗinsa.

Sai ta juya a hankali wanda ta yi

Please Login or Register in order to submit comment