Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gabanta.

"Bestie."

Ta faɗa muryanta na rawa Baɗɗo ta yi mata wani mugun kallo.

"Sunan ta Ummu Salma, wannan sunan kin daɗe da cire shi a tsakanin ku."

Baɗɗo ta amsa ma Shamsiya a fusace.

"Ki yi haƙuri Aisha."

"Ba komai Shamsiya. Ki yi hakuri kema amma ko tausayinku ban ji ba. Na ji ɗaɗi ma wataƙila kuma kun ɗanɗana irin zafin da muka ɗanɗana a zukatan mu a baya."

Shamsiya ta kasa magana sai kuka. Ta janyo hannuun Ummu Salma tana riƙewa a cikin nata hannun da sauri ta janye hannunta
Sai Shamsiya ta kece da kuka tana ba ta hakuri lokaci ɗaya ta tsinke da ba ta labarin duk abin da ya faru.

"Ni na ba ma Habib shawaran ya zubar da cikin jikin ki, sai ga shi ni da nake son na haihu da shi Ubangiji ya hana ni sau uku ina samun ciki yana zubewa, likitoci sun ce ina da raunin mahaifa, zai yi wahala mahaifana ya iya rike ciki, wannan ba alhakin ki ba ne? Habib ɗin dana ke so na raba ki da shi ni na aure shi, daga baya nima ya guje ni, ya sake ni lokacin da na ke bukatarsa na koma gida cikin halin baƙin ciki na rasa karatuna a lokacin na kuma rasa mahafina. Ummu Salma na shiga jarabawa mai tsanani amma da wuri na gane kurakuraina na gyara, na daɗe ina tunanin hanyar da zan same ki, domin na nemi gafaranki ban samu ba, kunya kuma ta sa na kasa neman gidan nan. Ubangiji ya jarabeceni da Soyayyar Habib da duk abin da ya yi mini na kasa cire shi a raina shi na yi ta jira yana dawowa da nadamarsa na ƙarbe shi, ni da shi mu muka faro komai dole tare za mu karkare shi, fatanmu mu haɗu dake mu ba ki hakuri Habib ya samu labarin kin yi aure kina auran ɗan uwanki ɗan Sarkin Daura daga nan muka san kin yi mana nisa, wani matashi ne a anguwan nan Habib ya sa ya saka masa ido duk ranar da ya ganki ya faɗa masa domin mu samu damar neman gafaran ki, sai kawai ya kira sa yana faɗa masa Baffa ya rasu da shi aka yi jana'izar Baffa sannan aka raka shi har gidan sa na gaskiya. Mun bari ne sai zukata sun sanyaya sannan muka zo, ki yi hakuri ki yafe mana wallahi Habib ya yi nadama kuma duk abin da ya yi miki da shawarata in akwai wanda za ki fi ganin laifin sa ne ni ce Ummu Salma ni ce silan komai."

Ta ƙarishe faɗa cikin kuka, kowa a falon jikinsa ya yi sanyi. Shamsiya kuka take yi kamar ranta zai fita amma Umma Salma ta kasa magana itama hawayen take yi.
Ammah ce ta juya tana kallon Umma Salma.

"Ki yi hakuri ki yafe musu, a daran da Baffa zai rasu ya yi mana wannan tunasarwa ya ce muma muna laifi amma Ubangiji ya yafe mana sannan ya ce mu zama masu afuwa da yafiya domin Allah na tare da masu hakuri."

Umna Balki ta jinjina kai tana faɗin gaskiya ne ita da Ummin ikki.
Ummu Salma ta runtse ido ta buɗe, tun da aka ce Allah sannan aka kira sunan Baffa an gama magana

Za ta yafe musu amma ba ta son wata alaka ta sake haɗa su har abada.
Murya a shaƙe ta ce komai ya wuce ta yafe.

"Mun gode Ummu Salma Allah ya saka da alheri."

Ta amsa da Amin tana kallon Shamsiya. Shamsiya ce ta koma haka? Lalle rayuwa kenan ta tuna a baya ba ta da ƙawar da ta fita sai Baɗɗo amma yau an wayi gari Shamsiya ta ba da gudummuwa wajen jefa rayuwarta cikin baƙinciki.

Shamsiya ta riƙe hannuwan Ummu Salma da karfi domin kar ta ƙwace.

"Mun gode sosai Ubangiji ya cigaba da dauwamar da rayuwarki cikin farinciki, kin ga yadda rayuwa ta yi danmu ko? Na kasa haihuwa Umma Salma itama Habiba ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba tunda Habib ya aure ta."

Ta gama fada tana juyawa sannan ta nuna Habiba.

"Ɗiyar Baba Usman ce ita ya aura bayan mun rabu."

Ummu Salma ta bi ta da kallo, sai da Shamsiya ta yi magana sannan ta gane ta.
Ta san ta tabbas ɗiyar Baba Usman ce suka kalli juna Ummu Salma ta kauda kanta kawai, rai suka wulaƙanta kuma wannan haƙƙin sai ya tambaye su amma ko Habib zai mutu bai haihu ba ne, ba za ta ba shi Hanan ba
Kowa ya ɗauka za su yi maganar Hanan amma ba su yi ba sai godiya da suke yi suna shirin tafiya.
Ammah ta ce su dakata sannan ta kalli Ummu Salma wacce tunda ta ce su dakata gabanta ke zikiri.

"Ina ɗiyar su?
Received at 11:37Reactions: ❤ 8, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba Ummu Salma ba hatta su Hamma Jibo sun sha mamaki, sun ɗauka daga neman gafara shike nan cikin nan cewa ya yi baya so, suma kunya ce ai ta hana su tambayan labarin cikin Lamiɗo ya ji maganar Ammah a zuciyarsa amma ko a fuska bai nuna wani alamu ba.

"Ammah ba fa ɗiyarsu ba domin cewa ya yi baya so ya bar ma Auta wannan cikin halak malak."

Hamma Abdullahi ya sake maimaitawa.
Sai Alhaji Sherif ya kalli Baba Usman, shima ya kalle shi cikin mamaki domin ba su gane kan maganar ba. Habib kuma  jin sa yake yi wani iri yana ganin a kamar mafarki daman kunya ce da nauyi ya sa bai tambayi cikin jikin Umma Salma ba amma abin na ran shi cewa ya yi ba zai taɓa tambaya ba.

"Alhaji cikin da Umma Salma ta fita da shi ta haife shi, mace ce sunan ta Hannatu kamar Habibu ne yana ƙarami "

Gwaggo ta faɗa ma Alhaji Sherif tana dariya lokaci ɗaya da hawaye.
Shamsiya kusa da Habib ta koma tana faɗa masa Umma Salma ta haifa masa yarinya mai kama da shi
Ya kasa magana bakin shi da jikinsa ma rawa suke yi.

"Na sani, amma Baffa ya ce ko bayan ran shi mu haɗa Hannnatu da mahafinta tare da ahalinsa."

"Why Baffa?

"Me ya sa?

Su Hamma Abdulrahaman ke tambayan kan su.
Su Hamma Jibo kuma sun yi shuru domin ta wani fannin sun hango manufar Baffa

Ammah ta kalli Baɗɗo sannan ta ce ta ɗauko Hannan ta kawo musu itama duk jikinta ya yi sanyi.

"Barci fa take yi Ammah."

Mami ta faɗa domin itama a ɗauko musu Hanan din bai yi mata daɗi ba

"Ku taso ta."

Ammah ta faɗa kai tsaye. Sai kowa ya kasa motsi barin ma Ummu Salma da ta ji kamar numfashinta zai ɗauke me Ammah take nufi? A ɗauko Hanan a bawa Habib ina ba zai saɓu ba yau ko duniya za ta haɗe ba za ta bari Habib ya ga Hanan ba, ballatana har ya taɓa jikinta.

Baɗɗo ta miƙe ta wuce ɗaki ta ɗauko Hanan dake barci, tana ɗauko ta kuma kamar ta sani ta farka tana mutsike idanuwana.
Ummu Salma ta ji kamar an zare mata lakka, lokacin da Ammah ta ce wai Baɗɗo ta miƙa Hanan ga su Habib.

Ba ta san ina ta samu wannan karfin ba, ganin ta kawai ta yi a gaban Baɗɗo ta warce Hannan ta ƙanƙameta a jikinta.

"Ba zai taɓa mini ƴa ba, shi ya ce ba ya so ya bar mini. Saboda haka har abada ta haramta a matsayin jininsa."

Take faɗa tana kuka, Mami ta miƙe tana yi mata magana ta matsa baya ta fashe da kuka.

"Mami har da ke! Raba ni da ƴa ta za su yi wallahi ƙwace ta za su yi"
Tana wani irin gunjin kuka.
Nan fa su Alhaji Sherif suma suka mimmiƙe cikin tashin hankali.

"Ba wanda zai kwace miki ƴa' ai tunda ya ce ba ya so ya bar miki ta ki ce har abada.'

Alhaji Sherif ke faɗa cikin sigan lallashi amma Ummu Salma ta kamkame Hanan ta hana su, su ganta

Hamma Jibo ya yi magana ta sake fashe masa da kuka har tana ya taimake ta.
Ko zafin jikinta ba ta ji yadda take jijjiga ga kuka.

"Ki saki yarinyar nan Ummu Salma, ba ki ji me na ce ba ne?.
Ammah ta sake magana amma Ummu Salma ba ta amince ba da gudu ta nufi Hamma Lamiɗo ta duka a gaban shi.

"Hamma ka saka baki, ka faɗa ma Ammah kai ne Baban Hanan, ka hana ta ba su ita."

Take faɗa tana wani irin kuka mai ban tausayi
Baya son kukanta shima hukuncin Ammah bai yi masa ba amma tunda umarninta ne ba zai ja da ita ba.

"Is okay amma dai yanzu ki yi abin da ta ce, miƙa ma Aisha Hanan ɗin."

Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya da ƙokarin riƙe ta, wani kallo take yi masa na kaima har da kai za a raba ni da farincikina kawai sai ta tashi ta manta akwai mikin ɗinki a jikinta bai gama warkewa ba ta juya ta saka Hanan a baya wacce ta yi zuru zuru har ta fara kuka ganin abin da ke faruwa.

Habib na tsaye amma kafafunsa rawa suke yi.
Shamsiya ta duka a gaban Ummu Salma.

"Ba ƙwace ta za mu yi ba Ummu Salma ganin ta kawai za mu yi."

"Ba za ku ganta ba. Ba ke kika ce a zubar da cikin ba shi kuma ya bi abin da kike so ba, ya so Hanan ba ta rayu ba Ubangiji ne ya fisa wallahi ba za ku taɓa ƴata ba ku je na yafe muku amma har abada kar ku sake tunkaran in da nake "

Nufinta ta gudu ɗaki ta rufe Ammah ta miƙe tana sake daka matsa tsawa.

"Kar ki matsa daga in da kike."
Received at 11:37Reactions: ❤ 8, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Maganar Ammah ya hana ta motsi amma ba ta daina gunjin kuka ba
Mami tausayi ya kamata sai hawaye haka ma Baɗdo da Ummin ikki.

"Jamila bi ta a hankali."

In ji Umma Balki cikin tausayawa.

"Ai a hankali na bi ta da farko na ga za ta yi mana hauka "

Ammah ta faɗa,sannan ta ƙarisa kusa da Umma Salma.

"Ba ki da hankali ne daga cewa za su ga yarinya sai ki fara ma mutane hauka? Ba ni ita."

Ammah ta gama faɗa tana mija mata hannu.
Amma ina Umma Salma ta kasa.

"Ba za ki sauke ta ba?

"Ammah."

"Na ce ki sauke ta kar in mare ki anan wajen"

Ammah ta fusata ranta ya ɓaci, kan ta farau haihuwa ji wani haukar da take yi.

"Kan ki farau haihuwa ko nan duk ba mu haihu ba ne sai ke? Daga cewa a kawo yarinya su ganta sai ki fara mana hauka in aka barki da ita za ki iya ba ta sunan Uba ne? Koma me ya faru shi ne mahaifinta mun sani kin sani suma sun sa ni."

"Ammah Hamma Lamiɗo ne mahaifinta."

Ummu Salma ta faɗa cikin gunjin kuka kuma ba ta sauke Hanan ɗin daga bayanta ba.

"Na ji shima mahaifinta ne amma kowa ya san ba shi ya haife ta ba. Cewa fa kawai na yi za su ganta ba tafiya da ita na ce za su yi ba amma tunda na ga abin da kika yi na ma fasa."

Ammah ta juya tana kallon Baɗɗo.

"Aisha shiga ciki ki haɗa kayan Hannatu ki ba ma mahaifinta su tafi da ita ta kwanan musu biyu."

"Ammah."

Ummu Salma ta kira sunanta da karfi tana kuka.

"Ammah don Allah ki yi haƙuri."

"Wallahi sai sun tafi da ita, in ta ga dama ta mutu saboda haka, shanshanci kawai kika rasa ma uba kika dangana balle wata ƴa?

Yadda Ammah ke faɗa kowa yasan ranta ya baci shi ya sa ko su Hamma Jibo ba su yi gaddama ba.
Gwaggo ne da Alhaji Sherif ke ba da hakuri.

Baɗɗo ko ta shiga cikin ɗaki a wata ƙaramar jaka ta haɗa ma Hanan kaya kala biyar da komai da komai ta zage ta fito, tun kafin ta miƙa ma Shamsiya ta yi saurin karɓan kayan Hanan kuma Ammah ta sauke ta daga bayan Ummu Salma, tana kuka Hanan na kuka ta tura ta Shamsiya ta ɗauketa itama tana kuka tana dariya.

"Mun gode Ammah, za mu dawo da ita in sha Allahu."

Habib kuma yana kallon Hanan yana kuka, daga karshe ma fita ya yi daga falon daga gidan gabaɗaya ya fita waje ya je can yana kuka shi kaɗai. Nadama ta kara kama shi yanzu cikin da ya so ya salwantar da karfin tsiya ita ce Hanan da ya ke gani mai kama da shi.

A cikin falon Ammah kuwa Gwaggo na faɗin ba sai an yi haka ba.
A bar Hanan kawai in an kwana biyu sai ta je kowa ya ganta amma yanzu tunda uwar babu daɗi ta zauna tare da mahaifiyarta shima Alhaji Sherif haka ya ce.

"A'a ku je da ita, itama ba daɗewa za su yi ba za ta bi mijinta su koma Lagos. Wannan kukan da take yi na jaririn da ta haifa ba rai ne kwana biyu da rasuwan Baffa."

Ammah ta faɗa musu, domin ita a ganin ta shi ya sanya Ummu Salma shiga wannan halin nan Gwaggo ta dinga addu'an Allah ya kawo mai tsayawa
Shamsiya kuma tuni ta yi waje ɗauke da Hanan da take ta kuka har tana faɗin ta daina kuka nima maman ki ce, Baɗɗo ta dinga hararanta kamar idanuwanta za su faɗo ƙasa.

Habiba ta bi bayanta, ita tausayin Umma Salma ta ji bai kamata a ji tausayin Habib ba.
Fitar Shamsiya da Hanan tana kuka ya fito da su Adda Safina da Islam da Harira.
Suka ga wata ta fita da Hanan suka shigo falon Ammah nan suka ga Umma Salma ta faɗi a tsakiyar falon Ammah tana gunjin kuka.

"Wayyo Allah na an cuce ni."

Haka take faɗa kamar ta zare, a lokacin kukan rashin Baffa take yi, da kukan rashin jaririnta yanzu a ce kuma an raba ta da Hanan

"Ba ma wanda ke sona sai Baffa wayyo Baffa, Allah ya jiƙan ka da kana nan da ba ka bari an cuce ni ba."

Take faɗa tana birgima tana kuka Mami na yi mata maganar ta tashi, ta manta akwai miki a jikinta amma ba ta ji ba. Har Hamma Jibo ya yi mata magana Hamma Kabiru har tsawa ya yi mata amma ba ta ji ba.
Ran Ammah ya kai kololuwa wajen ɓaci, har Umma Balki sai da ta yi magana Umma Salma ta duƙa tana kokarin tayar da ita amma ba ta ji ba sai ma fizge jikinta da ta yi tana cigaba da kuka.

Ammah ta kalleta wasu hawaye suka ziraro mata.

"Yau da ko wata Baffa bai yi da rasuwa ba har za ki fara tona mini asiri Ummu Salama? Ni ce na cucen ki kenan?
Received at 11:37Reactions: ❤ 8, 😱 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Ammah kin cuce ni, Hanan kaɗai gare ni kika raba ni da ita."

"Are you Mad?

"Will you keep quiet."

A tare ya yi magana cikin tsawa lokaci ɗaya yana miƙewa. Sai da ta yi ɗif da kukanta domin tsawan Hamma Lamiɗo mai razanarwa ce.
Tun ɗazu yake ganin abin da take yi ya ɗauke kan shi, duk da shima hukuncin Ammah ya yi masa tsauri amma ba zai iya gaddama da ita ba.

Kowa ya yi mata magana amma ba ta ji ba, har tana cewa wai Ammah ce ta cuce ta. Me take so a yi mata? Ko can gidan take son komawa saboda an tafi Hanan.

"Yauwa gwara ka yi mata  magana tunda mu ta ƙi jin namu."

In ji Ummin ikki itama ranta ya ɓaci. Haba Ummu Salma kuma ta fara fita daga hayyacinta.

"Sakarci ne kawai ku yi mata dai a hankali."

Umma Balki take faɗa domin tausayi Ummu Salman ke ba ta. Ammah kuma kuka ta fashe da shi ta koma ta zauna

"Allah ya jiƙan ka Baffa, ka tafi ka bar ni yau ga shi Auta na cewa na cuce ta."

Kukan da Ammah take yi ya ɗaga musu hankali.
Ummu Balki na faɗin ta daina kuka wannan ba wani abu ba ne, ita Umma Salma duk cikin rashin da aka yi mata ne ta faɗi haka amma ba cikin hayyacinta take ba Mami kuma ta duka tana ba ma Umma baki da hakurin kan ta tashi.

Hamma Kabiru ya ce su ƙyaleta gwara ma da Ammah ta yi haka ko gabaɗaya ma za su karɓi Hanan ɗin sai ta mutu don ubanta.

"Ummu Salma me ke damun ki? Wannan ai sakarci ne"

In ji Hamma Jibo yana mata faɗa. Lamiɗo kuma yana tsaye kawai yana huci ga cewar da ta yi Ammah ta cuce ta sannan ga abin da take yi sai kawai zuciyarsa ta haska masa Habib ɗin take so, da za a ba ta zaɓi shi za ta zaɓa saboda Hanan.

Ganin Mami da Baɗɗo suna ta lallashinta amma ta ki yin shuru ya sa Lamiɗo ya ce duk su ƙyaleta.

Cewa ya yi ta miƙe ta zauna. Ta ƙi tashi ya sake daka mata tsawa da sauri ta miƙe tana rufe idanuwanta hawaye na sake kece mata.

"Ka yi mata a hankali mana."
Mami ta faɗa ganin ya harzuƙa Ummu Salma kuma tana cikin wani halin da za a tausaya mata.

"Mami Ammah ce fa ta yi magana, ta yi mata gaddama a gaban mutane ta kyauta abin da ta yi?

Ya faɗa yana nuna ta da yatsa hannunshi na hagu.

"Ko ba ta so hukuncin ba tunda Ammah ta yi mata umarni me ya sa ta yi gaddama is she is ok? Bayan kuma ta kunyata ta a gaban mutane yanzu kuma look at her.? Kina ji fa ta ce wai Ammah ta cuce ta! Ammah ce za ta cuce ta?

Yanayin yadda yake magana ya sa kowa ya san a fusace yake.

"Ba ta kyauta ba. Amma a yi haƙuri."

In ji Umma Balki, Mami kuma cewa ta yi ya yi shuru kawai tunda dai ya faru kuma ba cikin hayyacinta ta yi ba.

"Ga zafin rasuwar Baffa ga na rasa jaririnta rana tsaka kuma ga Hanan dole za ta rikice."

"To ta tashi ta bi su can, tunda Ammah ta cuce ta. Ta bi su can if she want to stay with her Daughter sai na sake ta ta je ta aure shi sai ta samu daman zama tare da Hanan sosai."

Cak kukan Umma Salma ya tsaya. Ta ɗago da jajayen idanuwanta tana kallon Lamiɗo cikin ido, yau ba kallon soyayya yake yi mata ba wani irin kallo ne da ya kusa sanyata bugun zuciya ta ɗauka shi zai fi kowa fahimtarta ta ɗauka zai fi kowa sanin yanayinta baƙincikinta ɗaya yadda ya kasa gane halin da take ciki

Ammah ma sai da ta tsaya da kukan Mami da Umma Balki har suna haɗa baki wajen kiran sunan shi a firgice.

"Ƙul kar na sake jin wannan maganar a bakin ka."

Mami Ta faɗa cikin ƙaushin murya.
Hamma Jibo ya ce abu bai yi daɗi ba tunda ran Lamiɗo ya ɓaci sai ya ce Kabiru ya janye su fita waje

"Gaskiya ya faɗa abin da ta nuna kenan sai ya sake ta, ta je can ta ƙara ta."

Ammah ta faɗa da iya gaskiyanta.

"Haba Ammah."

Hamma Abdulrahim ya faɗa, da tunda aka zauna bai ce komai ba sai yanzu.

Hamma Kabiru ya ja hannun Lamiɗo yana faɗin ya zo su fita.

"Ba ta kyauta ba, Amini kar ka biye mata."

Ummu Salma ta ga tunda ta rasa Baffa sai me don ta rasa Lamiɗo? Tunda ya iya cewa zai iya sakinta ai ya yi rugurugu da yardan dake tsakanin su.
Sai kawai ta miƙe tana kuka.

"Sai me in ka sake ni? Ka sake ni mana ai ba zan mutu ba, na rasa ma Baffa ban mutu sai me don na rasa ka? A baya ma an sake ni kuma ban mutu ba yanzu ba.."

Ba ta kai ƙarshen maganar ba Mami ta buge mata baki.
Received at 11:37Reactions: ❤ 9, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Rufe mini baki, ba ki da kunya ne?

"Umma Salma kin yi hauka ne?

In ji Hamma Jibo.

"Sisna.."

Baɗɗo ta kira sunan ta a zafafe domin ta fahimci ta fara zarewa.
Lamiɗo kuma cak ya tsaya ya juyo suka kalli juna.
Ya ga duk abin da take faɗa a cikin idanuwanta kenan da gaske ne zarginsa ta fi son Habib akan shi.

Da gudu ta ruga ta shige ɗaki ta kulle kanta ta kwanta a saman cafet tana wani irin kuka mai cin rai da ƙuna ga gunji. Tana jin mikin ta na aiki na yi mata zafi amma ba ta jikinta take yi ba kuncin dake cikin zuciyarta ne ya fi raunin da ke waje zafi.
A falo kuwa Lamiɗo bai sake magana ba ya fita lokacin ma har an fara kiraye kirayen sallar mangariba.

Suma sauran mazan fita suka yi domin ɗaura alwala suwa masallaci. Ammah kuma ɗakinta ta shige.
Mami ta zauna tana faɗa ma su Umma Balki Umma Salma na cikin damuwa su yi mata uziri. Ga shi a gaban su Islam aka yi duk sun yi wiƙi wiƙi.

Umma Salma kuma ta ƙi buɗe ƙofa Baɗɗo ta yi ta magana shuru.
Daga karshe ma Ummin ikki tabi suka koma gida Ammah kuma kamar an yi mata fami ta shige cikin ɗaki tana ta kuka haka su Adda Nauwara suka dawo gidan duk a rikice Adda Safina ce ta kora musu abin da ya faru suma jikina su duk ya yi sanyi.
Lamiɗo kuma bai dawo cikin gida ba sai da safe a gidan shi ma ya je ya kwana tunda Hamma Saddam ya zo ya karɓi key ɗin bangaren Bilkisu a daran.

Da safe kuma jirgin karfe goma ya bi zuwa Katsina
Ya shigo ya yi ma Ammah da su Mami Sallama.
Mami ta bi shi har haraba in da Hamma Abdullahi ke jiran shi zai kai shi filin jirgi

Wai kar ya biye ma maganganun Umma Salma tana cikin halin tausaya mata ne. Shi mai zai ce ban da ya ce to kawai.
Mamin na faɗa masa sai da safen nan Ummu Salma ta buɗe kofa ta damu kar wani abu ya same ta. Ko a fuska bai nuna ga yanayin da yake ciki ba, amma tabbas kalaman Umma Salma sun dake shi matuƙa.

Shi na shi maganar ya faɗa ne cikin ɓacin ran abin da ta yi, amma ita ba cikin bacin rai ta furta na ta kalaman ba, har a zuciyarta ne.
Zai yi mata abin da take so, tunda ya fahimci ta fi son zama da Habib ɗin sama da shi. Bayan tafiyan shi Baffa Kabiru da iyalansa suka ɗau hanya, kusan lokaci ɗaya suka wuce da Hamma Mustapha.
Zaman da suka ce ma za su yi kafin tafiyarsu abin da ya faru ya sa bai yuyu ba.

Kowa ya yi banza da Umma Salma Mami ce kawai ke shiga wajenta.
Umma Balki ma ta ce abin da ta yi rashin kunya ne.
Su Adda Safina duk sun shiga sun yi mata sallama tana kwance idanuwanta har sun kumbura saboda kuka.
Ba nadamar maganganunta na jiya take yi ba.

Tunanin yau Hanan ta kwana can tare da mutumin da ta yi alƙwarin har abada ba zai kusanci ƴarta ba.

Me ya sa ita ba za a ga damuwarta ba? Ai itama tana da haƙƙi me ya sa ba za a bari a ji ta bakinta ba.
Duniyar ne gabaɗaya ba ta mata daɗi, abinci ma Mami ce ta matsa mata ta karya saboda shan mangunguna amma yadda ta ji rayuwar ma ta fita kanta ba ta ƙi ta mutu ba.

Baƙinciki take ji yadda duk yadda ta sadaukar da zuciyarta ga Hamma Lamiɗo ya kasa fahimtarta.

A wannan halin da ta ke ciki ta ɗauka zai fi kowa fahimtarta. Rashi ta yi na uba da jaririnta amma bai damu da wanman ba har yana faɗin zai sake ta, shi ne zai kalleta ya ce zai sake ta in ta tuna da kalamansa sai ta ji ba ta ma son ganin shi, tunda dai shi ya kasa fahimtarta to kowa ma in bai fahimceta ba ba za ta damu ba.

Ya sake ta ɗin ai ba mutuwa za ta yi ba. Ita tunda ta rasa uba ma da jaririnta in ta ƙara rasa wani ai ba mutuwa za ta yi ba.



*Janafty*
Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Hanan kuma tunda Shamsiya ta fita da ita take kuka, kuka har da hawaye da majina. A cikin mota ma kukan take yi duk ko da yadda Shamsiya da Gwaggo suke lallashinta ba ta yi shuru ba, su ɗin baki ne a gare ta in ta juya ta sake juyawa ta ga ba wanda ta sani sai ta sake fashewa da kuka.

A motar Alhaji Sherif suka zo daman. Su matan suna baya gaba kuma Alhajin na tuƙi Habib da Baba Usman suna mazaunin gaba.

Kukan take yi amma

Please Login or Register in order to submit comment