Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yawn ciwon kan da ta ke fama da shi ga ciwon mara, ga zafi daga in da aka yanka ta, ta yi ma likitan magana ya ce a hankali komai zai bari saboda C.S ɗin da aka yi mata ne. Ita a lokacin haihuwar Hanan an yi mata C.S amma duk ba ta fuskanci wannan matsalolin ba sai yanzu.

Fulani ta yi ta lallashinta da kalamai masu daɗi da nuna mata komai ta ga ya faru da bawa mukaddari ne. Ta yi haƙuri Allah zai ba su wani rayayye tun kafin ta ji daga bakin kowa ta san shima mai sunan Baffa bai zo da rai ba, kuma duk da cikin wattaninsa bakwai ko da ana haihuwar bakwaini su rayu amma ƙarancin hakan ya fi yawa.

Ta amsa ma da Fulani da cewa ba komai haka Allah ya so. Ita kuma Fulani ba ta san ma ba a faɗa ma Ummu Salman ba sai da Lamiɗo ya karbi wayar ya fita daga ɗakin yake faɗa mata ba su riga sun sanar da ita ba.

"Lamiɗo Ummu Salma ta san cikin ta bai rayu ba. Ka faɗa mata ba domin ba ta sani ba sai domin ka lallasheta."

Shi yana tamtama a ina ta ji? Tunda ba wanda ya faɗa mata.

"Uwa ce fa, in da abin da ke cikinta na da rai da ta gan shi zuwa yanzu."

Sai ya aminta da maganar Fulani bayan sun gama waya ya koma ɗakin sai ya ga Mami na zaune gefenta tana yi mata magana sannan ga wayar Mamin a hannunta alamun cewa hoton jaririn ta nuna mata

Mami na ganin ya shigo ta mike tana faɗin"Na faɗa mata, ka zauna ka sake ba ta baki."
Tana gama faɗin haka ta fice, Baɗɗo ta je gida ta dawo daga can za ta ɗauko ma Ummu Salma wasu kayan sawa duk da ba ta fara wanka ba sai dai su goge mata jiki tare da gasawa saboda ba a son ruwa ya taɓa wajen aikin kafin a kwance.

In Baɗɗo ta dawo ita Mamin za ta koma gida ta yi wanka, Daddy ya koma Kaduna sai gobe addu'an bakwai zai dawo Hajiya Falmata ma kwanan ta biyu ta koma Kaduna. Su Gimbiya Shahida ma ana yin uku suka koma Daura.

Bayan fitan Mami in da ta tashi ya koma ya zauna wata farar kujera dake gaban gadon da Ummu Salma ke kwance. Ya ƙura mata idanuwana yana so ya fahimci yanayinta.
Hannunta da ba karin ruwa ta riƙe wayar da shi wayar ta ƙura ma idanuwa Lamiɗo ya kasa gane yanayin da ta ke ciki bai ga hawaye ba sannan bai ga tana kuka ba.

Ɗayan hannunta ya kalla na dama in da ake yi mata karin ruwa. Ya ɗan kumbura domin akai akai ake zuwa duba ta tare da kayadde lokacin da za su yi mata allurai da saka mata ƙarin ruwa. Sannan sun fara ba ta kwayoyin maganin tunda ta fara cin abinci. Sannan suna yawan yi mata awon B.P jini akai akai da kuma awon fitsari tunda tana da B.P Sannan ga Eclampsian da ta yi fama da shi lokacin da aka kawo ta.

Miƙa masa wayar ta yi ya karɓa yana kallon ta.

"Kin gan shi?

Ya tambayeta lokaci ɗaya yana ɗan rike hannunta mai ƙarin ruwan
Received at 10:00
13 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta juyo ta kalle shi ta ɗan gyada masa kai, tunda ta farfaɗo ba ta cika yawan magana ba zai gaisheta za ta amsa amma kuma babu wata doguwar hira a tsakaninsu bai damu ya ɗauka shock ɗin abin da ya faru da ita ne ga kuma rasuwar Baffa a tunanin shi nan gaba kaɗan za ta warware. Abin da bai sani ba Ummu Salma komai na duniyar ne ya daina birgeta har shi kan shi ya daina birgeta yanzu gata nan ne kawai tana raye amma kamar ta mutu. Radaɗin dake zuciyarta kawai zai iya barazanar kashe ta a kwance a in da take. Sannan tunda ta farka take ganin duniyar ba daidai ba, ɗakin ma ganin shi take yi wani lokaci ƙarami, wani lokacin babba, daga nesa in ta ga abu sai ta ga ya canza mata gata nan ne kawai yanayinta gabaɗaya ya canza.

"Ya zo da rai ya kwana ɗaya ya rasu."

Ya faɗa yana sake kallon hoton daga wayar Mami.
Hamma Kabiru ne ya ɗau hoton ranar da suka koma gida yana tunanin shi ya tura ma Mami.

"Allah ya kaddara mai sunan Baffa shima zai zo kuma zai tafi ya bar mu kamar Baffa"

Ya faɗa cikin sanyin murya amma a ƙasan zuciyarsa wani abu ke yi masa motsi rashin wannan jaririn ya dake shi, ba shi kaɗai ba da dukkan dangin su ba wanda bai ji ba daɗi ba.

"Allah ya jikan su. Shi kuma Allah ya sa ya cece mu."

Ummu Salma ta faɗa tana ɗan kauda kai.

"Amin."

Yana so su haɗa idanuwana amma ta ki ba shi damar haka.

"I'm sorry."

Ya gama faɗa yana matsa kafafunta da duka hannuwansa duka biyu.

"Allah zai ba mu wani mai sunan baffa in sha Allahu."

Kanta na can gefen ba ta yi magana ba shima shurun kawai ya yi yana ɗan matsa mata kafafuwa
Kiran wayarsa ya katse sa daga abin da yake yi, sai ya ga Bilkisu ce ya ɗauka suka gaisa ƙasa ƙasa tana Abuja ranar kwana huɗu da rasuwar Baffa suka tafi tare da yara da su Hidaya amma kafin tafiyarta ta zo har asibiti ta duba Umma Salama lokacin tana barci.

Yanzu ma cewa ta yi ya jikin Ummu Salma ya ce da sauƙi ga shi ma tare da ita.

"How is she? Kun faɗa mata?

"Ta sani."

"How is she?

"She is fine, ba ta tada hankalinta kamar yadda na yi tunani ba."

"Allah ya ba ta lafiya."

Bilkisu ta faɗa cikin wani yanayi, ba ta son ta amma ta ji tausayinta cutar Eclampsia tana da hatsari sannan ga shi ta rasa jaririnta ga shi ta rasa uba duk a lokaci ɗaya in dai kai musulmi ne za ka ji tausayi ko kaɗan ne.

Wayar ta ce ya ba ma Ummu Salma ta gaishe ta.
Sai ya miƙe ya isa ta wajen kunnenta ya ƙara mata a kunne yana faɗa mata Bilkisu za ta gaisheta.
Ya riga ya saka mata wayar a kunne ta ji Bilkisu na yi mata sannu ta amsa a sanyaye

"Babu wata matsala ko?

Ta amsa mata da cewa babu

"So ki cire damuwa a ranki, ana so jinin ki ya yi ƙasa sosai in kina so a sallameki ki koma gida"

Ta ce mata toh kawai sannan ta ce Allah ya ƙara mata lafiya ta amsa da Amin
Sultan da Beena suna kusa suna ta cewa a basu wayar sai ta ba su ɗaya bayan ɗaya suka gaishe da Ummu Salma sai a lokacin ta ɗan yi mirmishi kaɗan
Bayan ta gama wayar shi ya karɓi wayar yana magana da yaran sai ga likita da wasu nurses sun zo duba ta sai ya fita waje ya ba su wuri suka fara checking ɗinta kamar yadda suka saba a koda yaushe.

A wajen ɗakin ya samu Mami zaune saman wasu kujeren zama dake wajen, sai da suka yi sallama da Bilkisu sannan ya ƙarisa in da Mami ke zaune amma har ya zauna gefenta ba ta sani ba ta zurfafa a tunani.
Sai da ya kira sunan ta sannan ta san da shi a gefenta.

"Ya take? Ina fatan ba ta yi kuka ba?
Wayarta ya miƙa mata ta karɓa.

"Ba ta yi ba."

Shuru suka yi dukkansu na wani lokaci.

"Ka yi haƙuri kai ma. Allah zai ba ku wani in sha Allahu."

Jinjina kai alamun gamsuwa.

"Allah ya sa."

Shuru ya sake wanzuwa a tsakanin su Mami ta kalle shi duk ya rame sai sumar fuska da ya tara daga gani ba shi da natsuwa sai ta dafa kafaɗan shi ya juyo yana kallon ta.

"Kana cin abincin kuwa Muhammadu?

"Ina ci."

"Ka kwantar da hankalin ka, Ummu Salma za ta warke ku koma gidanku ku zauna, Allah zai sake ba ku wani rabon da ikon Allah sai kun haifi mai sunan Baffa"

"In sha Allah."
Received at 10:01Reactions: ❤ 8, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ya amsa mata cikin yaƙini da tabbatarwa. Suna cikin haka ne sai ga Baɗɗo ta dawo tare da Umma Balki.
Zuwan su ya sa Mami ta bi Lamiɗo zuwa gida su kuma suka zauna a asibitin tare da Ummu Salma wacce ta koma barci.

Haka aka yi addu'ar rasuwar Baffa kwana bakwai Ummu Salma na asibiti. A ranar kwananta biyar kenan a asibiti. Kuma ba su da niyar sallamanta domin a washegari mutanen Mubi da za su koma duk sun zo asibtin duba ta, da su Baffa Salihu shi Baffa Umaru sai an yi sati biyu.

An barsu sun shiga amma mutum biyu biyu, sun duba ta da jiki, likita dai ya ce ba yanzu za su sallameta ba sai an kwance ɗinki sannan sai jininta ya daidaita.
Ammah ce kawai ba ta zo duba ta ba, amma dai sun gaisa ta waya.
Kowa dauriyan Ummu Salma yake gani ba ta yi kuka ba da aka ce jaririnta ya zo ba rai nan ko ba su san raɗaɗin dake cin ta a zuciya ba.

Satin ta ɗaya a asibiti aka kwance ɗinki. Har a lokacin ba a wanka sun ce jikinta na da kyau ba ta da ƙwan jiki babu wata matsala sun kara mata kwana uku sai ta yi kwana goma sannan za ta fara wanka. Amma tana shiga ruwan ɗumi saboda tsarki da jini.
Mami da Baɗɗo ne tsaye a kanta shi ya sa suke da wani matsayi mai girma a zuciyarta.
Yayyenta ma suna zuwa duba ta tunda duk suna nan ba su koma ba.

Tana asibitin ne amma hankalinta duk yana gida.
Ita na ta zaman makokin a gadon asibiti ta yi shi.

Sannan ta zama wata shuru shuru magana ma ba ta yi ban da ta amsa ya jiki shike nan. Ba wanda ya damu tunda tana cikin jinya ne ga rashi har sau biyu, ita ko ba su san abin da take hange ba gani take yi tunda ta rasa Baffa ba za ta sake rayuwa mai daɗi ba sannan ta zo ta rasa jaririnta tun daga lokacin ta ji duniyar ma ta fita kanta har cewa ta yi me ya sa ba ta mutu a wajen haihuwar ba! Da ta huta da wannan  raɗadin da duniyar ma gabaɗaya. Yanayinta ne kwata-kwata ba ta gane ba, tana jin ta kamar wata sabuwar hallita.

Kwananta goma sha biyu a gadon asibiti suka sallameta jininta ya sauka ya koma 130 sannan sun yi dukkan gwaje gwaje babu wata matsala an kwancen ɗinki har ta fara wanka. Sun koma gida Baffa na da sati biyu da rasuwa kenan.

Washegarin ranar da ta dawo gida Fulani da Gimbiya Shahida tare da Saleem da Hajiya Kilishi suka dawo gaisuwa suka kuma sake duba ta da jiki.
Mai Martaba dai bai dawo ba amma ya sake turo wakilai ranar da aka yi bakwai.
A ɗakinta dake cikin falon Ammah aka sauke ta, Baɗɗo har lolacin ba ta koma gida ba tana tare da Ummu Salma sai da ta dawo ne ta ga Harira baiwar Allah ita ce ke kula da yaran dake gidan Hanan ma ta zo wajenta tana surutun Mahma ban gan ki ba Papa ya ce kin yi tafiya sai ta amsa mata tana shafa kanta idanuwanta suka kawo ƙwalla Hanan kaɗai ta rage mata a yanzu a duniya.

Ummu Balki da Umma A'i suna nan ba su koma ba. Amma Umma A'i za ta koma ita Umma Balki ce sai an yi arba'in za ta koma Mami na nan ba ta ma saka ranar tafiya ba Daddy ma ya dawo shi ya tafi da Barira za ta je can zamfara ta ga iyayenta kafin Mami ta dawo.
Su Hamma Jibo duk suna nan tare da matayensu suma ba wanda ya saka ranar tafiya.

Baffa ya rasu ranar talata 21 ga wata December, shi kuma jaririn Ummu Salma ranar 22 ya zo duniya ya kuma koma a ranar 24 ga watan december. Ga shi har an shiga sabuwar shekara.

Makota da wasu da ba su samu zuwa gaisuwa ba suna ɗan shigowa yin gaisuwa. Ummu Salma ta koma ba ta uhm ba uhm, duk abin da aka ce za ta ce to kawai jinin haihuwanta kwana sha uku ya yi ya ɗauke amma tana shiga ruwan zafi sannan Mami na yi mata wankan jego na towel tana gasa mata jiki cikin dubara duk da mikin wajen da aka yi mata aiki yana ta warkewa yana haɗewa. Sannan sun rubuta magunguna an siya tana sha, dokar likita ce ta dinga cin abubuwan da za su gina mata jiki sannan ta dinga motsa jikinta sannan wannan haihuwar ta ɗan ajiye tumbi ba kamar na Hanan ba.

Ita ba ta wannan take ba, jikinta ko wani gayun duniya ba ya gabanta yanzu
Received at 10:01Reactions: ❤ 6, 👍 3
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
In ta tuna yau Baffa a duniyar nan sai ta ji ta rasa meke yi mata daɗi, sai da ta dawo gida aka ba ta wayarta.
A status ta ga Hamma Saddam ya saka hoton jaririnta ta yi saving a ɓoye ta ɗauka tana kallo tana kuka haka ma hoton Baffa gani take yi kamar zai dawo gani take yi kamar a mafarki.
Kwata kwata ba ta cikin natsuwarta amma dai tana bin shawaran likita tana kokarin yaki da abin da ke damunta amma dafin da radaɗin rashin Baffa wani abu ne da har ta koma ga Allah ba zai taɓa gushewa ba.

Baffa mutum ne na gari ba domin yana matsayin uba gare ta, ta tuna ranar da ya rasu Hamma Jibo na tambayan ko ana bin shi bashi, tunda ana so kafin akai mamaci makawancinsa a biya masa bashi ko ya yi kwanciyar kabari cikin salama nan take Hamma Abdullahi ya ce Baffa ba ya cin bashi, tunda tare suke kasuwanci ya ce sai dai shi Baffan ne ke bin mutane bashi.

*

Ranar da Baffa yake da kwana da ashirin da biyu da rasuwa Umma A'i da Baffa Umaru suka koma Mubi, aka bar Umma Balki tare da Ammah sai Mami da matan su Hamma Jibo.
Suna nan ba su koma ba, kowa ba ya son tafiya duk da duk sun koma bakin aiki amma suna tunanin acikin satin nan duk za su koma suna ma ta shiri ne.

Lamiɗo ne kawai bai koma aiki ba yana ma shirin tafiya Daura ne. Mai martaba zai koma London ganin likita cikin satin nan.
Mami ma tana nan ba ta ma saka rana ba, itama ba ta son tafiya duk dare haka suke taruwa suna tunawa da Baffa suna kuka, wato mutuwar Baffa rami ne a zukatansu da ba zai taɓa cikewa ba.
Ga Ummin ikki da itama koda yaushe a gidan take yini. Baɗɗo kuma nan wajen Umma Salma ta tare saboda ta ɗebe mata kewa
Duk ba wani hira suke yi ba.
Amma mutum rahama ne.

Ammah ko har yau ba wanda ya ga kukanta kuma ta na nan tsaye kan kafafunta.
Daman Umma Balki ta sha cewa Ammah jaruma ce sai da rasuwar Baffa kowa ya ga tabbaci ko kuka ake yi yanzu za ta fara faɗa da cewa su daina yi ma Baffa kuka addu'a kawai take roƙo su yi masa kodayaushe tana cikin hijabi da casbaha tana cikin ibada da nema ma Baffa gafaran Ubangijinsa kowa jinjina ma dauriyarta yake yi ta yi jarumta matuƙa.

Washegari kuma aka ce za a je maƙabarta ayi ma Baffa addu'a. Baffa Kabiru da Baffa Mustpaha gobe za su koma gidajen su.
Hamma Lamiɗo ma a goben zai bi jirgi zuwa Katsina.
Mami kuma ta ce sai sati na sama Daddy zai zo sai su koma. Hamma Jibo kuma ya ce sai karshen sati za su koma Abuja.

Za a tafi gabaɗaya ne har da Mami da Ummu Salma duka gidan ma gabaɗaya.
Bayan la'asar suka tafi Ummu Salma ma motar Hamma Jibo ta shiga Hamma Lamido kuma motar Amininsa.
Sauran kuma suka shisshiga ta su Hamma Abdullahi.
Harira kawai aka bari a gida sai Islam da yara. Har da su Adda Nauwara aka je maƙabartan.

Maƙabatar ba nisa shi yasa suka isa da wuri.
Sun yi magana da maigadin wajen tunda ana ziyara addini ya hallata amma ba wai mutum ya samu wajen zuwa a kodayaushe ba.
Sunna ta yarje ma iyalan wanda ya rasu su ziyarce su domin su yi musu addu'a amma ba wai a mayar da abin kamar ibada ba.

Alaman da suka sanya yana nan amma zuwa lokacin nan Baffa sun yi nisa a makabarta. Kafin shigarsu Hamma Jibo ya ce kowa ya yi addu'an da muka sani a cikin azkar na shiga makabarta.
Kowa ya yi sannan daman suka shiga, a gaban kabarin Baffa Ammah ta dafa kasar tana yi ma Baffa addua'a.
Sai a lokacin ta yi kuka hawayenta na ɗiga a saman hannunta da kasar kabarin Baffa.

"Allah ya jiƙan ka Baffa. Haƙurin da ka ba ni kafin rasuwarka na yi, ban yi kuka ba. Na gode Baffa Ubangiji ya sanya kabarinka cikin salama Allah ya yalwata maka hasken shi. Mun yi kewarka Allah ya sada ka da rahamarsa."

Sai a lokacin ta fashe da kuka Ummin ikki ta rumgumeta gefe tana lallashinta. Amma da Ummu Salma da su Mami suka fara kuka sai ta fara musu faɗan ba ta so. Hamma Abdullahi kuka Saddam kuka haka ma Abdulrahim
Ummu Salma kam sai da Lamiɗo ya rumgumeta yana ta lallashi kuka har yana sauti.
Received at 10:01Reactions: ❤ 11, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai da kowa ya yi masa addu'a sannan suka bar wajen kamar kar su tafi kamar su ga Baffa ya fito daga kabarin sun tafi gida tare da shi. In da aka binne jaririn Ummu Salma ne ya ɓace ba su gane wajen ba.
Shi ya sa ba su daɗe ba suka bar makabarta.
Suka duba hagu da dama, gabas da yamma maƙabarta babba ce amma ta yi rabi da mutane.

Jama'a mu dinga ziyartan maƙabararta za mu kara imani da tsoron Allah, za ka ga fa cewa kai ma wata rana nan ɗin ne gidan ka na gaskiya. Duk tarin arzikinka nan ne karshen ka, Sarki ma anan za a san ya shi haka ma Gwamna haka ma attajiri , haka ma talaka nan ɗin ne dai shine ƙarshe, za mu ƙara imani za mu ƙara jin cewa mu shirya ma muttuwa ko yau ko gobe ko anjuma tana tare damu.

Ubangiji ya sa mu yi kyakyawan ƙarshe. Allah ya sa mu mutu cikin imani.
Amin.

Sun koma gida kuma sai mutuwa ta dawo sabuwa
Suka haɗu suna ta kuka.
Ammah tana ta faɗan ita ba ta son kukan nan.

"Abdulrahim har da kai? Kai da za ka zama namiji mai lallashi "

Umma Balki ke magana ganin har da shi cikin masu kuka. Mami kuma ɗakin Ammah ta shige tana ta kukanta.
Haka ma Ummu Salma Baɗɗo na tare da ita.
Mazan ne ke zaune a falo masu dauriyan daman su Hamma Kabiru ne da Hamma Lamiɗo da su Hamma Abdulrrahaman.
Ammah dai yau ta yi kukan hawaye shaɓe shaɓe amma a hakan take ce ma wasu su daina kuka.

Hamma Jibo na maganar bayan sallar isha'i za su zauna gabaɗaya su tattauna kafin tafiyar su.
Suna cikin wannan maganar
Sai ga sallaman baki mata.
Mata huɗu ne, ɗaya tsohuwa ce ɗaya kuma ba yarinya ba ce sai yaran mata biyu.
Suna shigowa mazan suka tashi suka fita kuma daman bakin sun ce suna da tare da maza ne a waje.

Har baƙin suka zazzauna ana gaisawa Ammah ko su Ummin ikki dake falon ba su gane su ba.

"Hajiya ba ki gane ni ba?

Gwaggo ta faɗa tana kallon Ammah ganin ba ta gane ta ba. Ammah ta kalleta domin ga shi ta san kamar fuskar amma ba za ta iya tunawa ba. Duk da sun haɗu da Gwaggo lokacin da Umma Salma ta yi ɓarin cikinta na farko.

"Ayya Ban gane ki ba wallahi ki yi hakuri ki yi mini bayani."

Ammah ta faɗa murya a sanyaye.

"Daman na yi tunanin haka, duka duka bai fi sau biyu muka ga juna ba"
Gwaggo ta faɗa tana kallon Shamsiya da kanta ke kasa ta kasa ɗago kanta.
Habiba kuma sai kalle kalle take yi tana taɓe baki daga ganinsu dai masu ragwamen gata ne

"Ɗago kan ki Shamsiya."

Gwaggo ta faɗa tana kallon Shamsiya.

"Na san in ni ba ki gane ni ba wataƙila ki gane Shamsiya."

Daidai lokacin Ummin ikki ta ƙura ma Gwaggo idanuwana sai a lokacin ta ganeta.
Ita ta yi jinyar Ummu Salma asibitin a lokacin da ta yi ɓarin cikin Habib sannan wacce ke kusa da Gwaggo ma ta gane ta matar kanin baban Habibu ne, Hajiya Sahura.

Da ɗago kan Shamsiya tare da maganar Ummin ikki da Ammah duk a lokaci ɗaya ne.

"Shamsiya."

Ammah ta kira sunanta cikin mamaki.

"Wa nake gani kamar dangin Habibu."

In ji Ummin ikki.

"Mu ne ashe kin gane mu"

Gwaggo ta faɗa cikin ɗan yake.
Sai aka fara kallon kallo.
Ammah mamaki ya kama ta.
Ummin ikki kuma ta ma kasa magana.

"Wai wani Habibun na ji kuna magana?

"Ba dai wanman yaron tsohon mijin Auta ba? Mara mutumci mara albarka ba, ba dai dangin shi ba ne nan zaune a gaban mu?

Umma Balki ta faɗa tana kallon su Ammah.

"Su ne."

Ummin ikki ta faɗa cikin gatse.

"Me kuma ya kawo su ni Balki?

"Shi muke son sani Umma Balki."

Ummi ikki ta amsa tana kallon Gwaggo da suka kasa magana.

"Lafiya me ke tafe da ku?  Naga tun bayan sakin wulakancin da ɗanku ya yi ma ɗiyarmu alaqar dake tsakanimmu ta yanke me kuma ya kawo ku?

Ummin ikki ta tsare su da tambaya.

"Alheri muka zo da shi Hajiya."

Gwaggo ta faɗa, tana gyara zama.

"Ku tashi ku koma da alherin ku, duk alherin da zai fito daga ɓarayin ku bama so."

Ummin ikki ta faɗa a fusace.

"Aa Hajiya ba za a yi haka. Ku tsaya dai ku saurare mu ku ji da abin da muke tafe."

Hajiya Sahura ta faɗa cikin kwantar da kai daman ta san haka zai faru.
Shi ya sa Alhaji Sheriff ya da ke ba zai zo ba, darajan Gwaggo ne da ita da ta sanya baki ya sa ya amince ya zo Shamsiya kuwa tana ta sharan hawayen kanta a ƙasa.

"Wallahi ba da sharri muka zo ba alheri ne ya kawo mu"
Received at 10:01Reactions: ❤ 12, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta sake faɗa cikin lalama.

"Gaskiya ba za mu saurare ku ba. Ku tashi ku tafi kawai."

Ummin ikki ce ke magana Ammah ta yi shuru kanta na kasa. Gwaggo da Hajiya Sahura na ta rokon a bar su su yi magana.
Dai dai lokacin Baɗɗo ta fito falon daga ɗakin Umma ta zo ɗaukan ruwa.

Ta ga mata a falo a cikin matan ta ga Shamsiya.
Ta razana ta ja baya ta kwalalo idanuwana ta kira sunanta da karfi.

"Shamsiya"

"Baɗɗo."

Ta amsa mata cikin hawaye

"Ke ce?

Baɗɗo ta tambaya saboda ganin kamar ba Shamsiya ba. Fuska duk kuraje ta yi baki ta rame ga wani hijabi a jikinta mai kama da tsumma.
Mami ma maganar Baɗɗo ya fito da ita ganin Baɗɗo tsaye cirko cirko ya sa ta tsaya tana tambaya.

Nan take faɗa mata Shamsiya ce da dangin Habibu domin ta gane har Gwaggo sauran ne ba ta san su ba.

"Wani Habib ɗin?

Mami ta tambaya tana yi musu kallon wulaƙanci.

"Kuma suke zaune anan ba ku fatattake su ba."

Ta gama rufe baki kenan Ummu Salma ta fito daga cikin ɗakin ita ce daman za ta sha ruwan Baɗɗo ta fito ta ɗauko mata sai ta ji shuru, daga baya sai ta ji kamar tashin maganganu a falo.

Lokacin da ta fito ba ta ma lura da mutanen dake falon ba Jikinta da hijabin da suka fita da shi ba ta cire ba kafarta akwai safa.

"Me ya fa.."

Sai ƙarshen maganar ya maƙale daga bakinta.
Lokacin da ta ga waɗanda ke zaune a kasan cafet a falo.
Tana wurga idanuwanta tsakanin Gwaggo da Shamsiya.

Ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, wani irin ɗaci da raɗaɗi ya dawo mata sabo.

"Bestie"

Shamsiya ta miƙe tsaye tana kiran Ummu Salma.

"Ummu Salma."

Gwaggo ma ta kira ta a muryanta akwai tausayi.
Har idanuwanta na cikowa da kwalla.
Ummu Salma ta kasa amsawa domin sai ta ji kanta ya sara ƙafafunta na rawa tare da jikinta.

Ta damƙe hannun Baɗɗo kawai ta juya za ta koma ciki
Ba za ta iya ganin su ba, ba ta kaunar ta sake ganin wani abu da ya dangancin Habib har abada.

A lokacin kuma sai ga Hanan ta rugo da gudu Faruk ya biyo ta suna guje guje.
Uwarta ta nufa sai jin ta kawai Umma Salma ta yi akan kafafunta ta rumgumeta.

"Mahma Faruk zai kama ni."

Take faɗa da muryanta na yara shi kuma Faruk na faɗin sai ya rama tsungilinshi ta

Please Login or Register in order to submit comment